*page 1* "Wallahi Allah shine shaidata bani da masaniya akan yanda akayi kudin nan suka bata. Kowa a nan ya gani ga lissafi nan na duk abinda ya shigo kuma ya fita saga duka companies dinmu tun farkon shekara zuwa yanzu. Idan har duka lissafin da accountants dinmu suka kawo daidai ne tayaya za'ayi ace yanzu an sake lissafi an rasa wasu kudade? Nidai ban ci ba sedai a sake lissafi tun daga qasa ta yuwu a nan aka samu kuskuren lissafi" AMINU BECHI ya fada cikin tsananin tashin hankali. Sati biyu kenan da al'amura suka rikice a BECHI GROUP OF COMPANY lokacin lissafin shekara yayi bayan daya gama hada komai a matsayinsa na AG lissafi yasha banban da abinda aka bashi a rubuce da kuma tsurar kudi da suke a qasa inda aka samu rarar naira na gugan naira har Miliyan dubu biyu da dari biyar (2.5Billion) wadda bayan bashi damar yayi bincike da MD da kuma Chairman sukayi yauce ranar da aka taru duk wani daya isa a company domin jin ta yanda akayi aka haihu a ragaya. Alhaji ZAKARIYYAH BECHI dake ta jujjuyawa a kujerarsa yana wani miskilin murmushi da babu wanda ya tantance kona menene ya kalle shi yace "To Aminu kaida kanka kace dukka lissafin da aka gabatar maka daidai suke kuma baka karba ka saka hannu har seka bincika komai ka tabbatar da haka yake. Sannan a iya saninmu ku biyu kuke da access da central account dinmu dakai da Chairman duk wani wanda ze shigar ko fitar da kudi bayan ku biyun seya samu approval a gurinku to tayaya kake zaton zamu yarda idan kudi ya bata kuma kace mana bakada masaniya akai kenan Chairman ne da kanshi ya kwashi kudaden ko kuma me kake nufi?" Aminu ya kalli Chairman din da tun zamansu bece komai ba ya tallabe haba da hannaye biyu yana bin duk wani da yayi magana a cikin su da kallo, Dattijo ne da a qalla zeyi shekaru 70 zuwa sama, dukda a zaune yake amma kana kallonsa zaka san Zabgegen mutum ne Jindadin rayuwa yasa har yanzun yake da sauran kwarinsa. Aminu ya hadiye yawu muqut saboda yanayin fuskar Chairman daya gani, bashi da yawan fara'a daman amma kuma yanayinsa na yau ya banbanta da kullum kana gani kasan zuciyarsa a kusa take koda yake ai dole, batun kudi akeyi fa, kudin daya qare rayuwarsa yana nemansu ya tara ace lokaci daya wasu su ringayi masa zari daidai dole hankalinsa ya tashi. Seda ya daidaita nutsuwarsa kafin ya kalli MD dake jiran jin ta bakinsa yace "Nidai na gama magana, ban ci kudin nan ba ban kuma san wanda ya dauke su ba. Amma dai kamar yanda nace kowanne gida (sector) su sake turo mana da lissafinsu na shekara a qaramun lokaci zan sake bin komai daki daki zan zauna da duka Bank Managers dinmu in Allah ya yarda za'a gano duk ma inda kudin suka shiga" ya qarasa muryarsa na rawa kuma cike da roqo da yaqinin Alhajin ya yarda dashi ya bashi wannan damar. Idan ya rasa besab ina ze dosa ba, abu biyu ne dole daya ya faru, dukda kasancewar Dan Chairman na cikinsa a sabgar Company basa kawo wannan relation din, ya sani kodai yayi Aman kudaden nan tas Miliyan dubu biyu da dari biyar wanda ko an siyar dashi da matarsa da yayansa da abinda ya mallaka baza'a hada wannan kudi ba abu na biyu kuma in wancan be samu ba yasan garqameshi za'a yi a prison still kuma A siyar da duk abinda ya mallaka Company ya rage Asara maganar aikin sa daman tun ranar da kudin sukayi batan dabo ya rubuta resignation letter ya ajiye dan ko be bari ba korar sa za'ayi. "Maganar wani lokaci ko a sake bincike duk bata taso ba dan a tsayin faruwar abun zuwa yanzu da da wani abu da zakiyi tuni kayishi, just admit it Aminu kai kaci kudaden nan ka dawo dasu baki alaikum base magana tayi tsayi ba" NAZIRU BECHI ya fada yana wani zazzare masa ido "Nima dai abinda na gani kenan, idan kuma yayi taurin kai Maigirma Chairman ina ganin a barshi da Legal department suyi aikinsu nasan su zasu sna ta yanda zasu tirsasashi yayi aman kudin ko kuma su miqashi inda ya dace" Alhaji Zakariyya ya qarasa miyar gishiri, cikin Aminu ya kada, ya ringa raba ido tsakanin Alhaji BABANGIDA BECHI da kuma YAKUBU BECHI da yake matsayin mataimakinsa AAG wanda tun fara taqaddamar kamar ma baya gurin wayarsa yake dannawa kunnensa saqale da Bluetooth tabbacin ba jinsu yakeyi ba hakan yasa ya tsayar da idonsa kan Alhaji Babangida cike da roqon ya saka baki amma seyaga ya saukar da kansa qasa bece komai ba. Dakin ya sake daukan shiru na wani lokaci kafin cikin murya me cike da Izza irin ta wanda suka ci suka tada kai Chairman, Alhaji AUDU BECHI ya fara magana yana cewa "Duk naji bayanan ku kuma na duba takaddun da aka rigada aka gabatar mun tuntuni. Account general, ina so daga yanzu zuwa qarfe biyu ka gabatar da takaddar barin aikinka da kanka saboda idan muka koreka zamu bata maka career be zama lallai ka sake samun aiki a wani gurin ba, kudi kuma duk wanda ya dauka yaje dan kansa" yana gama fadar haka ya tsuke bakinsa yana kallonsu daidai. Aminu ya sauke ajiyar zuciya me nauyi tamkar wanda ya hadiyi kunama, jiki da bakinsa suna rawa ya zame daga kan kujerarsa ya durqushe yana cewa "Nagode Alhaji, Allah ya qara girma nagode nagode". Naziru da Zakariyya wanda farkon maganar Alhaji yayi musu dadi, sun dana kuma ta kama suka kalli juna tareda yin signa akan idon Alhaji Babangida dake lura da duk wani motsinsu ya girgiza kai kawai. Bazeyi kaffara ba idan ya rantse cewar shirinsu ne saboda sun nuna baqin ciki qarara da kujerar ta Aminu amma baze saka baki a cikin maganar na domin rayuwar gidansu rayuwa ce irin ta kowa tasa ta fishsheshi shida Yan dakinsu. Tunda Aminu ya samu wannan matsayi qarara mutane da yawa a gidan suka nuna qyashi da hassada bayan rasuwar Mr Adekunle Balogun wanda shine AG na BECHI GROUP din tun kafuwarsa Alhajin bisa shawarar Legal Department da sukaga cancantar Aminun aka dorashi, shekaru biyu kenan tun kuma hawansa abubuwan da ba'a saba dasu ba suke faruwa amma wannan al'amari shine mafi girma wanda baze yuwu a dauke kai ba. Cikin zafin ran dake nuna hassada qarara Alhaji Zakariyya yace "Ranka ya dade (haka suke kiransa muddin sabgar data shafi aiki ce) naji kace yayi resigning kawai banji maganar dawo da kudi ba ko wani hukunci da za'a dauka akansa?" "Da alama kunnenka ya soma samun matsala ko? To ka tambayi na kusa da kai su maimaita maka abinda nace, maganar wanda ze maye gurbinsa for now Yakub should take over kafin mu sake zama muga abinda ya dace da ayi ina ganin mun gama abinda ya taramu you can all dismiss" Alhajin ya fada ba tareda ya kalleshi ba. Alhaji Zakariyya ya hadiye yawun takaici ta wani bangare kuma yaji dadin cewar YAKUB BECHI ne zeyi taking over dukda sunso ace anyi confirming nasa ne take as the newa AG amma hakan ma nasarace sunyi nasu Hajiya zata qarasa aikin a gida. Shiya fara miqewa ya kalli Aminu dake harhada takaddun gabansa cikin izgili yace "Dama anyi gadon farar qafa dole a tsammaci abinda yafi wannan, Allah dai ya sauwaqa ya kuma tsayar iya kanku kar a bata mana sauran iri da halin bera" yana gama fadar hakan ya juya ya fice daga gurin dukkan su kuma sunji abinda ya fada, Da daddaya suka ringa ficewa daga conference room din ya rage Alhaji Audu, Alhaji Abdullahi wanda yake heading bangaren Siminti kuma dane a gurin Alhajin Audun ma'ana dan Yayansa ne da suka hada uba se Mustapha Manzo, shugaban Legal department na rukunin kamfanunuwan Bechi. Alhaji Abdullahi ya kalli Alhaji Audu dayayi shiru da alama yayi nisa a tunani, cikin ladabin da yake masa tun usulan yace "Gaskiya Baba a iya fahimtata da kuma binciken da nayi bana zargin cewar Aminu yana da saka hannu a cikin batan kudaden nan" "Nima dai abinda zan fada kenan, nayi amfani da duk wasu measures da muke using gurin gano me laifi banga wasu alamu na rashin gaskiya a tattare dashi ba. Amma abinda yake bani mamaki shine tabbas kudi sun bata amma babu wata alama da za'a iya tracing a ga inda kudin suka tafi tunda ba transfer akayi ba and we don't deal with huge cash here ballantana ace cash aka debe su. Ni dai what I'm thinking is that kudin nan dama babu su, lissafin bogi aka bashi kawai kuma ina ganin matsalar badaga ko ina aka samota ba se daga Oil Sector. Tunda Naziru ya fara heading gurin nan ake samun runton lissafi Mr Obasaki yana yawan kawo mun qorafin idanna sanar maka Alhaji baka daukan wani mataki na sosai and i don't know your reasons for that. Ire iren wadannan abubuwan ya saka mutane da yawa basa mixing Family with business saboda abinda bare zeyi maka ka dauki mataki idan Jininka ne dole ka daga amsa qafa, amma maganar gaskiya idan ana so a ga daidai se an gyara saboda kowa yasan can ne bangaren dayafi kowanne kawo profit idan aka cigaba da irin wannan tafiyar ina tsoron kar wata rana a wayi gari babu uwar kudi ma balle riba" Mustapha Manzo ya fada, yanda yake maganar duk wanda ya saurareshi dakyau ze fahimci jirwaye yakeyiwa Alhajin me kamar wanka. Kai tsaye baya so ya dora alhakin batan kudin akan Naziru tunda bashi da hujja amma yana so Alhajin ya bincika da kansa ya tabbatar. Alhaji dake sauraronsu a zahiri yana gyada kai amma a badini kanzil bazece yaji daga abinda suke ta babatu akai ba maganar farar qafa da Zakariyya yayi ce take masa yawo a zuciya wasu shudaddun Al'amura da suka faru a baya suka shiga dawo masa kamar auransa da Mahaifiyar Aminun, abubuwan da suka gidana a tsakani har zuwa rabuwarsu. "Nidai Baba idan ze yuwu a janye maganar korar Aminu daga company nan, za'a iya suspending nasa na wani lokaci amma Yaron yana da matuqar qoqari kuma ya dace da gurbin da aka sakashi akai" Alhaji Abdullahi ya sakeyin magana se sannan Alhaji Audu ya dubeshi, kallon dansa na cikinsa yakeyiwa Abdullahin saboda shi ya fara riqewa kafin ya samu nasa yayan, haka kuma yana yi masa biyayyar da qalilan daga cikin wadanda ya haifa a cikinsa ne sukeyi masa irinta. Cike da Izzar data zame masa jiki yace "My decision is final, idan shi Barrister Manzo be sani ba, kai kasan Hadiza ka kuma san dalilin rabuwata da ita dan haka bazan yi ganganci a matsayin kuskure ba" daga haka ya miqe tsaye yana gyara zaman babbar rigarsa datasha wani aiki irin na sarakai. A baya suka biyo shi duk rayukansu babu dadi har suka shiga Elevator Barrister Manzo yana so ya sake magana amma Alhaji Abdullahi ya hanashi. Tun kafin qofar Elevator ta gama budewa gaba daya suke jin hayaniya, Reception din cike da ma'aikata da sukayi cirko cirko se muryar Naziru dake tashi kamar ana yaqi. Cikin karadi da kwaroroto irin na Mahaifiyarsa yake cewa "Wlh Babu inda zaka je se ka bude jakar nan mun cajeta, hauka ma akeyi kenan. A kamaka dumu dumu da laifin sata a koreka daga aiki sannan ka lullubo jaka zaka fita bamu duba munga meye a ciki ba salon ka kwashi sirrikan mu ka fitar ka saidawa Yan hamayya ko to baka isa ba" ya fada yana kiciniyar fincikar Bag pack din Aminu daya saka duk wani abu nasa me muhimmaci da yake a tsohon office dinsa tunda an sallameshi daga gurin. Alh Abdullahi da Barr Manzo suka nufesu da sauri jin abinda yake faruwa, Alhaji Audu kuwa ko a jikinsa ya nufi qofar da zata fitar dashi daga building din. Daf da ze fita kunnuwansa suka jiyo masa wasu mata biyu ma'aikata dake saga gefe suna kallo daya tana cewa "Nidai Safna da arziqi irin na wadannan mutanen gara talauchi da kwanciyar hankali, su fa basu san abin kunya ba, wlh Chairman dai bewa kansa tanadi na kwarai ba Allah ya baka arziqin zuria amma ka tarwatsasu babu soyayya bare shaquwa a tsakaninsu kowa so yake yaga kasawar dan uwansa yanzu idan baka sani ba wlh ba zaka taba yarda MD Oil and Gas da AG ubansu daya ba dan ko barene beci yayi masa irin wannan tozarcin ba ballantana jininsa." Dayar tace "Uhm kedai bari Halisa kinsan su CMD yayan Mowa ne shiyasa suke sharafinsu, bandama AG da MD Agric wa kika gani a yayan nasa yana aiki a nan se yayan yan uwa dana abokanai ragowar kina kallo duk wanda yazo baya zama yake neman hanyar da zata bulle dashi to ko nice wlh ba zan zauna ba Arziqin ubana amma a fifita wasu su zasu amfana ai dai idan Chairman ya sheqa be gyara kan gidansa ba to kuwa kwanciyarsa qalilan ce a kabari dan kullum se an tashe shi yaga tsiyar daya bari a duniya da ransa ma ji yanda suke akan dukiyar inaga an raba gado wani be samu yanda yake tsammani ba" suka tafa hannu suna cewa "Allah dai ya kyauta. Alhaji Audu ya daga qafa dakyar ya qarasa ficewa daga gurin bayan ya gama sauraron hirar tasu. Tunanin maganganunsu yakeyi a ransa, ba yau aka fara fada ba ko ya faraji wasu su fada masa akan idonsa wasu a boye suti gulma kamar dai wadannan kuma tun abin baya damunsa yana daukar sa ba a komai ba har ta kawo matsayin da shida kansa ya hangi illar da yayiwa kansa da rayuwar Ahalinsa gaba daya. A lokacin daya dora tubalin ginin sam be hango rashin ingancinsa ba, be hasaso ranar da ze iya ruftawa dashi ba seda lokaci ya qure masa akazo matakin da ko yana so ya gyara mawuyaci ne hakan ta yuwu. A yanzu da yake cikin Shekara ta Saba'in da uku a duniya yaci ace yana kwance a gida yana hutawa da kuma shirye shiryen tarar da ubangijinsa ta hanyar yawaita tuba da ayyukan Alkhairi amma a maimakon haka tashin hankulan da be san suna wanzuwa ba a baya yanzu suke riskarshi. Bashida kwanciyar hankali a gidansa, tsakanin Matansa koda ace ba dukka kullum ta Allah idan ba safiya ba rana idan ba rana ba Dare se Binta ta tayar da tashin hankalin da ze kwana ya wuni cikin quncin zuciya. Ubangiji yayi masa ni'ima ta Yaya Maza zarata wadanda ya dora buruka da yawa a kansu sedai be gino rayuwar ta sigar da baze cimma mafarkin sa ba ya shuka barna yanzun kuma yana girbinta ne, yayan daya kwallafa rai akan zasu taimake shi a lokacin da qarfinsa ya tashi qarewa sedai sam hakan ta gagara a maimakon nutsuwa a kullum tukuicin tashin hankali yake samu daga garesu wanda shine silar komai ya sani ba laifinsu bane laifukansa na bayane suke farautarsa a yanzun. Yayi zurfi cikin tunani har besan sun isa gida ba seda Dtiver sa ya bude ma murfin qofar bangaren da yake. Ya fita ya tsaya yana qarewa Tamfatsetsiyar harabar gidansa kallo ga motoci nan birjik kamar a gurin saida su. Gida ne daya amsa sunan gida wanda ko baka shiga ciki ba zaka iya wassafa tsaruwarsa, Get din gidan me kama da qofar Gari kansa abin kallo ne ga wasu shuke shuke da akayi a harabar na dogaye da gajerun bishiyoyi da suka qara qawata gurin se manya manyan Street Light jere da Zanqaleliyar Katangar gidan kamar ta mutanen Niger kana gani base an fada maka ba kasan idan dare yayi haske har yawa yakeyiwa Harabar. Gini ne Duplex a tsakiya yana kallo ka idan ka shigo nan ne kuma turakar Alhajin dakuna uku ne a sama da falo a qasan kuma kantamemen falo ne da aka zubawa kujeru saiti uku da bandakin baqi a gefe se kuma wani qarami Daga can gefen wanda fadar tsaruwarsa bata baki ne a nan Alhajin yake saukar baqinsa na Mutunchi Babban Falon kuma na Meeting ne tsaf yake dauke jama'ar gidan duk yawansu. A cikin harar akwai qofofi biyu dama da Hagu, ta hagun ce zata kaika cikin gida inda bangaren Matansa yake ta Dama kuma ta kasu biyu, daya ta inda dakunan samarin gidan yake ne dayar kuma dakunan masu aiki maza. daidai qofar da zata shiga dakai sashin samarin gidan ya hango Faisal yana tahowa da wasu kwaftara kwaftaran takalma a hannu irin na taqadiran Black Americans din nan yana waigen bayansa, baya tsammanin ma ya lura da tsayuwarsa ya giftashi yana cewa "Dan kutumar uba da ka biyo ni mana da wallahi sena farke ka a gidan nan" ya fice abunsa ya bar Alhaji da zuciyarsa take tsalle da lugude, dawa Faisal yake fada da har yake furta wadannan munanan kalamai wai ze farke shi kamar wani Dan Daba? Salim daya fito daga qofar shima kamar an harboshi yana kwalawa Issa daya daga cikin Buzayen fa suke gadin gidan kira ya taho da gudu ya durqusa cikin maganarsa ta buzaye yace "Gani Alhajji me kuke da buqata?" "Ina Faisal?" Ya fada a fusace, Issa ya daga hannaye sama yana cewa "Ya fita Alhajji yanzun ya fice ta qofa" "Zonan Salim" Alhaji Audu ya fada ganin shima be lura da tsayuwarsa a gurin ba. Ya wani ja iska kafin ya matsa inda Alhajin yake, kadan ya rusuna yace "Barka da Rana Alhaji" "Meya hadaku?" Ya tambayeshi ba tareda ya amsa gaisuwar tasa ba wadda idanda ace a shekarun bayane ma tabbas seya kife shi da mari kan wannan gaisuwar rainin daya masa. Cikin qunquni Salim din yace "Takalma na ya diba kuma na rantse da Allah sena masa dukan mutuwa idan muka hadu" babu tsoro ko shakka a muryarsa ya fada. Alhaji ya qara tsumewa dukda cewar zuciyarsa tsinkewa take ta ciki akan al'amuran dake wakana dashi yace "Me yasa kuke haka? Saboda dan uwan ya dauki takalminka shine zaka fito kana daga murya kuna zubar da mutunchinku a gaban masu aiki kamar wanda ya daukan maka wani abu me muhimmanci? Bana son haka kar kuma na sake ji, shi ya wuce yana zage zage kai kana cewa zaka masa dukan mutuwa me kukeyi hakan" Salim ya daga kai ya kalli Alhajin da wani irin duba kamar wani sa'an sa yace "Shi daya wuce ka tsayar dashi kaji ba'asin zage zagen da yakeyi?" "Ban tsayar dashi ba saboda.." "Base ka fada komai ba saboda shi dan so ne basa laifi, nida ya daukarwa abu nayi magana nine mara gaskiya to se a biyani kudin takalmina idan ba haka ba kuma na rantse da Allah sena kwantar da yaro" Salim ya datse Alhajin babu dar bare shakka tsabar mamaki kallonaa kawai Alhajin ya ringayi ya kasa cewa komai. Shi Audu ne yayi lalacewar da Kalan Hanji a cikin yayansa ze ringa mayar masa da magana? "You are very stupid Salim Alhajin kake gayawa wannan maganar saboda baka da hankali?" Ahmad da shigowarsa kenan ya tarar dasu ya fada, Salim ya kada qeyarsa ya juya yana cewa "Ai gaskiya na fada Yah Ahmad da ace ni na daukarwa Faisal din abu da yanzu an hada Family meeting ance mun barawo shi kuwa tunda dan gaban goshi ne kaga ni ya bawa laifin ina masa hayaniyaba gida a biyani abu na kawai a zauna lafiya" daga haka ya barsu tsaye kamar sokaye saboda mamaki. "Kayi haquri Alhaji gaba dayansu se na bata musu zan zauna dasu" Ahmad ya fada cikin girmamawa, Alhaji ya jinjina kai irin na wanda Idea ta qarewa kafin ya juya ya shige Falonsa maganganun daya sha yau suka masa rufdugu a kwakwalwa tabbas makomar gidansa tana cikin garari, idan kuma beyiwa tukfar hanci ba za'a samu gagarumar matsala. Sama ya haye dakinsa ya zauna bakin gado bayan daya rage babbar rigar jikinaa ya qara gudun Ac, tunanin baya ya shigayi, so yake ya gano bakin zare ta inda ya kuskure ko Allah zesa ya samo hanyar gyarawa. Kamar Film ya shiga hasko rayuwarsa tun daga tushe. *MATAR MUTUM* *NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER* *FIKRA WRITERS ASSOCIATION* *LITTAFIN KUDI NE* *PAY 400 (PROMO PRICE BAYAN KAMMALA FREE PAGES ZE KOMA 500) A ASUSUN* *7061838488* *OPAY DIGITAL SERVICES* *MARYAM FAROUK* OR *0709290797* *ACCESS BANK* *SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488* *IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705* *NAGODE* *FREE PAGE 2* ABDULWAHAB TIJJANI Shine Asalin sunansa, AUDU da mutane da suka sanshi dashi yasa ake daukar cewa ABDULLAHI shine sunansa kamar yanda duk inda kaji Audu a gurin bahaushe tunanin na karkata da cewar Abdullahi ne sedai shi Alhaji Audu ya samu sunan ne ta dalilin wata kakarsu tun suna yara ya tashi da bala'in son kudi, da sallah idan ya samu yan silallarsa na barka da sallah ya ringa yawo dasu kenan a aljihu yana karkadawa suna qara idan ka tambayeshi menene se yace "Kudina ne tara su zanyi se sunyi yawa sosai" shikenan take kiransa da Audu kudi tun befi shekara biyar a duniya ba kuma sunan ya bishi aka manta da Abdulwahab sedai Audun kawai har girmansa kuma wannan dalili ya saka koda Yaransa suka Shiga makaranta Malamai sukayi musu register da ABDULLAHI TIJJANI BECHI a cewarsu Audu ba suna bane. Alhaji Audu haifaffen wani qauyene da ake kira Bechi cikin qaramar hukumar Kumbotson Jahar Kano. A yanda labari ya iske su kakansu daya haifi Mahaifinsu Tijjani wato Malam Lawan shine me garin Bechi na farko ance seda suka shekara Talatin da matarsa Asabe kafin Allah ya basu haihuwar Tijjani hakan yasa suka dauki son duniya suka dora masa sedai Allah beyi zasuyi doguwar rayuwa tare ba domin kuwa shekarun Tijjani bakwai a Duniya Mahaifinsa Malam Lawan Me gari ya rasu wata hudu tsakani ya rage kwanaki goma Goggo Asabe ta fita daga takabarsa itama ta amsa kiran Mahaliccinta shikenan Tijjani ya tashi maraya gaba da baya riqonsa ya koma tsakanin dangin Mahaifinsa yau yana wannan gida gobe yana na can wanda gaba dayansu sunayi ne saboda tarin dukiyar qasar da Mahaifinsa ya mutu ya bar masa ba kuma sun bari ya girma ya samu komai ba se wata gona kwalli daya wadda itama wani qanin mahaifiyarsa ne yayi tsayin daka gurin ganin bata salwantaba se fili wanda gidan da iyayensa suka zauna ya kamachi a bashi amma Sabon me garin da aka nada wanda yake qanin Mahaifinsa ya gaje ya shiga ya zauna a ciki dukda cewar gadon Tijjani ne, badan ma suna tsoron tijarar Kawun nasa ba shine dalilin daya saka ya bashi wani fili daban yace ya gina. Da wannan gona daya tsira da ita yaci gaba da kula da rayuwarsa ita yake nomawa abinda ya samu ya siyar yayi buqatunsa har yayi aure ya auri Fadi yar Kawunsa yayan mahaifiyarsa haka suka zauna tsayin shekaru cikin rufin Asirin Allah har tayi yaya biyar Maza uku mata uku Lawan da suke kira Baba se Hashimu, Maryam, Amina, Aminu da kuma Zulai. Bayan Baba da Hashimu sun tasa su suka cigaba da taimaka masa da gonar da ita kadai ce hanyar samunsu, abinda suka noma a ciki zaau cire abinci, ragowar a siyar a ringa buqatun yau da kullum wannan dalili ya saka rani damina koda yaushe cikin shuka yake musamman da Allah ya taimakeshi gonar tasa tana kusa da wata fadama dan haka bashida matsalar ruwa sabodan noman rani sannan tana da girma babu laifi shiyasa yake noma nau'ikan abici kala kala. Suna zaune lafiya da Fadi lokaci daya ya bijiro da zancen son qarin aure bayan daya hadu da Hafsatu Farar bafillatana baquwa da sukazo qauyensu kawo Amarya Tijjani na ganinta yace tayi masa, be samu matsala da Fadi ba, inda ma yar tangardar take be wuce damuwar yanda al'amura zasu kaya musu ba idan ya qaro auran dalili da cewar lallaba rayuwa sukeyi ba shida wata hanyar samun kudi idan ba noman nan da yakeyi ba dukda rayuwa nada sauqi a wancan lokacin amma nauyi ze qarar masa idan yayi auran, rarar da suke samu ta amfani gona har a siyar bw zama lallai aci gaba da samu ba tunda wacce ze auro din itama haihuqa zatayi wata rana wannan Fadi taso ta fahimtar dashi amma ya nuna komai na Allah ne shi yake ciyarwa kuma yanda ya nufeshi da qarin auran ze hore masa abinda ze cigaba da kulawa dasu haka kuwa akayi ya auro Hafsatu zaman au gwanin dadi da Fadi tana bata girma sosai a matsayinta na wadda ta girmeta kuma tana sama da ita a gidan aure wannan ladabi nata yake qarawa Malam Tijjani sonta. Shekara daya ta haifi Da Namiji aka saka masa Yakubu, shekarar biyu ta haifi Audu se Bilkisu, Aisha da kuma Muktar me sunan Babanta suna ce masa Baballiya. Rayuwa ta qarayiwa Malam Tijjani da iyalan sa tsanani saboda sun qara yawa kuma madogarar tasu dai guda daya ce wannan gona, qari da haka hatta da Maryo da Amina yayan Goggo Fadi da aka aurar mazajensu duk suma ba masu qarfi bane se ya zama har dasu ake noma gonar Malam Tijjanin abinda aka fitar a raba kowa yaje yayi ta jalautawa da iyalansa wannan matsatsin rayuwa ya saka Audu tashi da burin son yayi kudi saboda Baffansa ya huta da wahala. A lokacin farko shigowar Boko Yaro dayane a garin yake karatun Bokon Shamsu wanda yake dan Me gari shima ya kaishi cikin Kano ne yana zaune gidan wani Hakimi se shekara shekara yake zuwa gidan. Sa'an Yakubu ne amma duka Abokanai suke dasu Audu tunda tazarar shekarun ba yawa kuma tare suke karatun Allo kafin aka kaishi birni idan Shamsu yazo kuma zeyita bawa su Audu labarin Birni da Turawan da suke koya musu karatu har yace suyiwa Baffansu magana suma akai su dan Malamansu sun gaya musu idan suka dage sukayi karatu zasu samu aiki a ringa biyansu Albashi wadanda suka iya turanci kuma har Ingila zasu tafi dasu. Zancen kudi da Audu yaji yasa hankalinsa ya tashi ya kuma quduri niyyar zuwa Birni Yakubu kuwa da tun qaraminsa ya tashi da Burin Zama Alqali, ko wasa akeyi zece shine Alqali ayita zuwa gabansa ana kawo shari'a shima Shamsu yace masa a birni da akwai Kotu ba irin yanda ake shari'a anan ba sedai aje gaban me gari. Audu yacewa Yakubu suyiwa Baffansu maganar zuwa Boko amma se yace Aa dan shi yana da sanyi ba kamar Audun ba yana gudun yiwa Baffan magana yayi masa fada dan lokacin da aka kai Shamsu be manta ba harda Baffansu a masu cewa an kaishi ze koyo yahudanci Audu beyi qasa a guiwa ba ya samu Mahaifiyarsu da suke cewa Dada da zancen tayiwa Baffa magana ya samu me gari idan Shamsu ze koma birni su bishi take kuwa ta nuna rashin amincrwa itama dai kamar Yakubu ta tuna masa da Mahaifinsa na Adawa da Karatun Boko da ya shigo daga nan aka bar maganar badan har zuciya Audu ya haqura ba sedai yayi shiru ne kawai zuwa wani lokaci saboda tunda yaji zancen kudi fa hankalinsa yayi kan Birni kuma kota halin qaqa dai se yaje shi. Seda aka shekara kafin dama ta sake zuwar wa Audu a wannan Karon a gurin Malamin da yake musu karatun yaji cewar ze kai Yara Birni can tsangayar Malaminsa Gwani Musa a unguwar Kabara. Audu najin wannan batu yana komawa gida ya sanarwa da Dada a wannan karon itama bata ce Aa ba tasan kuma shima mahaifinsu baze hana ba inda zaa iya samun matsala be wuci yanzu da suka tasa ba suna taya sauran yan uwansu aikin Gona amma tasan hakan baze zama wani abu ba. Haka kuwa akayi ta damu Malam Tijjani da batun yayi na'am har yace ze samu Malam Tsalha malamin tsangayar tasu yaji kanun maganar, bayan duk shirye shiryen da suka kamata Audu da Yakubu suka bi tawagar Yaran Gari zuwa birni Almajiranci, dukda Malam Tijjani yaso iya Audu ya tafi Yakubu ya tsaya amma Audu ya kafe kaida fata se sun tafi tare saboda shirinsu na karatun Boko wanda Yakubu ya fishi buri akan abu shi neman kudi kawai yake so yaje yayi a Birni ba wani Karatun Allo kona boko ba. Seda suka shafe wata uku a tsangayar Gwani Musa suna kuma karantar birnin na Kano, basu san inda zasu nemi Shamsu ba balle ya kaisu makarantarsu, Audu a shige shigensa yayi Abokanai anan cikin Magashi suka shaqu da wani Yaro Sa'an sa Hayatu yaron gidan da Audu yake yiwa aikace aikace ne. Hayatu da sauran yan uwansa suna makarantar boko dan haka Audu ya nuna masa shida dan uwansa Yakubu suna sha'awar karatu kuma abinda ya fito dasu daga qauye kenan. Hayatu ya sanarwa da Mahaifinsa wanda a lokacin suna cikin mutanen da suka karbi Boko sosai yaji dadi kwarai da wannan abu dan haka ba tareda bata lokaci ba yaje da kansa ya samu Gwani Musa ya sanar masa da buqatar su Audu tayin karatun Boko. Da yake Malami ne me fahimta kuma shi kansa cikin yayansa akwai wadanda suke Bokon saboda yanda Sarakuna da masu kudi da suke samun damar fita Waje suke fada musu Alfanun Bokon be hanasu Audu ba, ya kafa musu sharadi dai na dole zasu cigaba da daukar Karatu, da safe suje bokonsu su dawo Yamma da dare su zauna a makaranta suyi karatun Qur'ani haka kuwa akayi su Audu suka fara zuwa makaranta shekara daya da haka yace shi ya gaji saboda Shamsu ce masa yayi idan anyi karatu za'a samu aiki a samu kudi shi kuwa kullum karatu ake dora musu bema ji ranar da za'a gama ba dan shekaru ake lissafowa Yakubu ne yayi ta tausarsa akan yayi haquri da sannu zasu kai matakin da suke buri. Haka suka ci gaba, Yakubu na matuqar maida hankali ga Karatu yayinda Audu turanci kawai ya saka zuciyarsa ze koya saboda idan ta tabbata sun gama makaranta za'a kaisu turai kar yaje ya rasa bakin magana. A hankali ya faratiwa Makarar asha ruwan tsuntsaye, Sadi, da aka kawosu Almajiranta tare amma shi dan Bagwai ne shiya fara nuna masa hanyar Kasuwa. Da safe idan sun tafi Boko shida Yakubu ze zame ya tafi bakin Asibiti anan zeyi duk wani aiki daya samu, dako ne, aike, duk wani abu da zeyi a biyashi haka ya ringayi kan jiki kan qarfi dake ya saka abin a ransa kuma yana da zuciyar yi se gashi baya jin wahalar kowanne irin aiki indai ze kawo masa kudi. Da Yakubu ya gane baya zama a makaranta yace ze gayawa Malam seya dakata da zuwa Kasuwa, cikin yan kudaden daya samu ya auno Aya da gyada ya kaiwa Matar Malam da suke kira Nene dayake suna shiri yace tayi masa gyada me gishiri da Aya me siga ya daura abarsa a Boko ya siyar a Allo ya siyar se gashi an gane shi a unguwa Audu me gyada da Aya kuma sosai yake ciniki abinsa. Seda suka shekara biyu kafin sukaje gida, a lokacin sun fara zama samari dan Yakubu nada shekaru sha biyar Audu nada Sha uku. Cikin yan kudaden jarinsa yayiwa Dada da qannensa harda Baffansu tsaraba. Kowa yaji dadin yanda ya gansu, Dada ce ta ringa masa fada akan ina ya samu kudi yayi wannan siyayya be boye mata ya sanar mata da duk abubuwan da yakeyi harda zancen Boko da sukeyi shida Yakubu ya kuma qara da fada mata gaskiyar dama saboda ya samu damar neman kudi Yakubu kuma yayi karatu yasa sukace zasu Makarantar Allon. A wannan karon kafin su koma seda ta sanar da mahaifinsu gaskiyar komai gudun kar wata rana ya gane yace sun hada baki sun munafurceta, da fari ya ringa fada dan sosai yake Adawa da karatun Boko har yana cewa ba zasu koma Birnin ba se kuma daga baya basu san yanda akayi ya canza ra'ayi ba da kansa yayi musu shirin komawa ya kuma yi musu nasiha tareda gargadin su tsaya a turbar Allah karsu yarda masu jajayen kunnuwa su dorasu akan wata hanya sabanin wadda Addinin Islama ya dora mu akai. Ya sake jawa Audu kunne sosai akan banbance tsakanin Halal da Haram tunda yana zuciyar nema baze daku she shi ba, abinda ya janyo masa sakkowa harya haqura zasu koma dinma bayan sunyi magana da Hashimu dansa na biyu shiya nuna masa Alfanun abinda su Audun sukeyi tunda baya kaucewa shari'a bane. Yace masa "Baba idan ka dubi yanda rayuwa take tafiya a kullum abubuwa qara yi mana wahala sukeyi dan abinda muke nomawa ba wadatar mu yake yi ba balle har mu samu na siyarwa muyi sauran buqatu kuma ko a cikin karkarar nan idan ka duba masu fita fatauci Abokanan mu zakaga suna samun Abun rufin asiri har su taimaka mana muma, da ace tun muna qanana kamar su muma mun tashi da wannan tunanin qila da rayuwar ta mana sauqi amma yanzu tunda Allah yasa su sun himmatu zasuyi a barsu muyita rakasu da Addu'a Aminu ma da ze bisu suje can birnin yayi Bokon koya kama sana'a kamar Audu duk da hakan yayi". To haka su Audu suka koma ba tareda Aminu ba dan yace ba zashi ba da yake Auta ne Goggo Fadi bata takura masa ba kuma shi kadai ya rage gabanta tunda duk an aurar da Maryo da Amina Mazan ma Hashimu da Lawan sunyi Aure. Rayuwa taci gaba da garawa Audu da Yakubu a birni, iya wuya Audu neman kudi yakeyi yana kuma riqe da hudubar Mahaifansa akan ya tsaya ga halal karya kuskura yaci abinda Allah be halasta masa ba kuma da yake a lokacin duniya na zaune lafiya cuta da bata gari basuyi yawa ba shiyasa abun yazo masa a sauqaqe. Tun yana Dako a kasuwa ko aikace aikace har ya fara kayi nayi, ze karbi kaya ya fita dasu ya siyar ya cire ribarsa har ta kai ya hada yar tireda yana kasa kayan koi gefe gida kuma ya ajiye Baro duk wani dan itace na marmari da ake yayi a lokaci ze saro ya ringa siyarwa yan kasuwar har mamakinsa suke ganinsa yaro qarami dukda yana da baragen girma amma zafin neman sa ba duk babbaba shiyasa yayi shura a bakin Asibiti babu wanda besan AUDU BECHI ba haka suke masa inkiya da garinsu. Duk qarshen shekara suke zuwa gida kuma duk sanda zasu tafi haka ze hada tsaraba himili duk wanda ya shafe shi seya riqe masa wani abu ya kai masa dan badaga nan ba Audu akwai kyauta kuma a wannan yanayi Girma da Wahala suka fara kwantar da mahaifinsu dukda shekarunsa basu kai ace ya kwanta tun yanzu ba amma yanda rayuwar ta faro tun quruciya jiki yana wahalar data zarce abinda ze dauka shiya janyo masa ciwo yayi masa kwaf yau lafiya gobe babu haka yasa idan zasu je gida Audu ze siyi magungunan ya tafi masa dasu da irin mayukan zafi saboda qorafin ciwon jiki da yake yawanyi. A wannan gantafalfala suka kammala Primary tareda Saukar alqur'ani ta biye wadda Audu dai ba zuwanta yake ba a sati befi ya leqa sau daya ba ita kanta Allon Karatun dare kadai yake zama Gwani yayi fadan yayi nasihar amma Audu ya toshe kunne, dadinta daya yana biya karatu daidai ya wanke Allonsa akan lokaci wannan yasa Gwani yake daga masa qafa Bokon ma idan ana jaraba zeje yayi kuma zeci ga turancin daya saka kansa ya iya radau dan ko Yakubu me qulafucin Bokon Albarka shiyasa Malaman suke ji dashi, Audu akwai rashin ji amma akwai kwakwalawar daukar Karatu. Yakubu ya tafi makarantar kwana dan cigaba da karatun sa, burinsa ne ya zama Alqali Audu kuwa yace yayi sallama da Boko ya kama neman kudi kuma. Shi yayiwa Yakubu duk wani shiri na tafiya makarantar, haka kuma yana kai masa ziyara idan anyi hutu Yakubun Bechi yake tafiya yayi hutunsa acan Audu kuma ana Kano ana ta fafutukar rayuwa. Inda ya kafa yar tiredar tasa aikin fadada titi yabi ta gun dole ya tashi daga qarshe ya koma zuba kayan kolin nasa a Baro yayi ta zaga kasuwa yana waqa ta kiran customers yanda yake waqar abin dariya yake saka wasu siya badan ma sunyi niyya ba. Yakubu yana shekara ta uku a makaranta lokacin kuma aka aurar da Bilki wadda take bin Audu, ba qaramar Bajinta Audu yayi a auran nan ba dan dama ya dade yana tanadi saboda mutuniyarsa ce ko irin fadan sako da sakon nan basa yi da akwai fahinta sosai a tsakaninsu a kuma Bikin Bilkin ya dabbaqa soyayyarsa ga Bara'atu wadda tayiwa Bilki babbar qawa. Tun suna yan yara Audu yake sonta an dauka yarinta ce ashe shi har ransa ya riqe abun yanzun daya furta yana son ta da yawa wasa suka dauki abun saboda idan ka dubi a yanda akewa yara aure Bara'atu ta isa kaiwa daki dukda shekarunta sha biyu ne a sannan amma ga Bilki da take sa'arta an mata aure itama Audu kuwa yana shekara sha bakwai koda Maza suna saurin Aure a qauyen amma be isa ba tukunna, ga Yakubu me sha tara da Aminu me Ashirin da biyu nan basuyi aure ba bare Azo kansa haka dai ya ringa hurewa Bara'atu kunne da soyayyarsa seda ya tabbata ta mato ta yanda ko ya koma birni ba zata saurari wani ba zata jira shi kafin ya koma Birni ya bar Audu da suke hutun makaranta zasu shiga Aji hudu a sannan. Satin Audu daya da tafiya jikin Malam Tijjani ya motsa kuma ciwon yafi na ko yaushe zafi dole Yakubu ya bazamo Kano neman Audu saboda Malam din da yake ta nanata a kira masa Audu gashi babu waya a sannan, kwanansa daya suka juya hankali tashe yanda ya tarar da jikin Mahaifin nasa ya tayar masa da hankali ya shawarci manyan yayyensu akan su tafi da Malam Kano a akaishi Asibiti amma suka qi a cewarsu anayin na gargajiya wai a yanda ya ganshi ma jikin da sauqi, cikin daren Ranar Malam Tijjani ya amsa kiran Ubangiji har yaja numfashinsa na qarshe kuwa be dena maimaita musu su tsaya akan gaskiya ba kuma duk rintai duk wahala karsu yada zumunchi suci gaba da hada kansu kamar yanda suka tashi. Sunyi kuka sosai da jimamin rasuwar mahaifin nasu, daga Audu har Yakubu suka kasa komawa inda suka fito saboda mahaifiyarsu da mutuwar Malam din ta tabata sosai har itama ta kwanta jinya, ita din bata da kowa a yanzu se Malam dasu yayanta dan Iyayenta duk sun rasu Yayyenta biyu suma shekara uku kenan Babban Ya rasu me bi masa kuma be cika shekara da rasuwa ba shima yanzu ga Malam shima ya tafi. Seda sukayi dagaske suka qarfafa mata guiwa kafin ta dangana taci gaba da zaman takaba. Audu ya damu Yakubu akan batun komawa makaranta dan tuni hutu ya qare an Koma amma duk sanda yayi masa maganar se yayi shiru yaqi ce masa komai. Audu be fahimci dalilin Yakubu naqin komawa makaranta ba seda akayi sadakar Arba'in din Mahaifinsu, a ranar kuma dattawan qauyen suka zaunar dasu akan maganar rabon gado. *Batoul Fashion and Boutique* online store ne na sai da kayan 'yan gayu dandasa-dandasa na gani na fada, na kece raini a taro, masu tashin kan Habeeby ❤️ Kuma masu sa kishiya kwalla😂🏃🏻‍♀ Muna da Laces, Atampa, Voiles, Shoes, Bags, Gowns, Veils and Jewelry masu kyau a farashi me sauqi, Muna Bada sari Kuma Muna siyar da daidai, Muna hada lefe masu Aji🔥🍻kada na cika ku da surutu😌ku garzaya IG page dn www.instagram.com/batoul_fashion_and_boutique don shaida bayanan da na muku da Kuma tabbatarwa ko ku shiga WhatsApp group dn ta https://chat.whatsapp.com/Fi0iCJcvtGKEYcVrbZwxfw za ku iya tuntubarmu a 07025420431 *MATAR MUTUM* *NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER* *MARUBUCOYAR* *WATA KISHIYAR* RUBUTACCIYAR QADDARAH* *HALIN KISHI* *FIKRA WRITERS ASSOCIATION* *LITTAFIN KUDI NE* *PAY 400 (PROMO PRICE BAYAN KAMMALA FREE PAGES ZE KOMA 500) A ASUSUN* *7061838488* *OPAY DIGITAL SERVICES* *MARYAM FAROUK* OR *0709290797* *ACCESS BANK* *SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488* *IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705* *NAGODE* *FREE PAGE 3* Malam dai sun sani Gona guda daya ya bar musu se gidan da suke ciki, aka raba musu komai yanda shari'a ta tanadar, ba'a samu wani surutu ko hayaniya ba saboda yawansu daya kowanne bangaren sunada Maza uku mata biyu se iyayensu mata. Zancen gida duk sun yarda akan kar a raba iyayensu suci gaba da zama ciki tunda kowa yasan bangaren da yake mallakinsa haka Gona sun yarda akan za'a ci gaba da nomata yanda aka Saba ana raba amfanin kuma lokacin daman yayi daidai dana girbi dan haka kwana kadan akayi girbi aka kawo amfanin Gona gida kuma daman abinda ake dan jalautawar yayi qasa banda ma Audu da ya zo da yan kudade shi yake ta hidima da gidan tun bayan Rasuwar Malam. Su Audu sunyi zaton za'ayi rabo ne matsayin cewar kowa yana da gado cikin abinda aka girbe din amma se sukaga sabanin haka. Sanda akayi rabon baya gida yana gurin Bara'atu yaje tadi. Yakubu da akayi a gabansa kuma kanzil bece musu ba suka kacaccala kayan suka ware musu nasu wanda dama ba dukka aka fito dasu ba kadan aka yafito daga Rumbu aka zuzzuba musu Masara, Gero, dawa buhu bibbiyu Alhalin a shekarar an samu amfanin gona ko wanne launin Abinci yafi Buhu Hamsin amma abinda suka basu kenab se shinkafa da sukeyi wadda yawanci daman ita Siyarwa akeyi to bata isa girbi ba. SedaAudun ya dawo ya tarar da kayan a bakin qofar dakin Dada inda suka ajiye musu, duk da cewar Rumbun gidan a kasonsu ya fado amma su Hashimun sun kulle tulin abinci sun tafi da muqulli. Sanda Malam yana raye duk nan ake ajiye komai duk wadda zatayi girki ta shiga ta diba su kansu su Hashimun sedai su dibi wanda ze ja musu lokaci idan ya qare a kuma diba. Audu ya gama kallon kayan kafin ya shiga dakin Dada suna zaune suna cin tuwon Dawa da Aisha ta tuqa musu suna hira jefi jefi ya ajiye musu qullin soyayyar karfasa daya taho musu dashi Dada ta saka masa Albarka tareda tura masa nasa kwanon tuwon da aka ajiye masa. Kai ya girgiza alamar ya qoshi dan yaci a gidansu Bara'atu, Innarta Da takeyi dashi shiyasa dui sanda yaje gidan seta tisa dole ya shiga in da darene se yaci tuwo tun yana kunya har ya sake dan ko beci ba zata hado shi dashi ya taho gida. Seda ya bari sun gama cin tuwon kafin yayi magana yace "Dada naga Hatsi a qofar daki na waye?" "Yawwa daman kai nake jira ka kamawa Yayanka ku shigar dasu dakin Malam (shima Rabon su ne) wannan uban sakalcin wai baze iya ba" ta nuna Baballiya dake rakube gefen gado wai bacci yake so yayi ita kuma ta hanashi tace se tuwon daya ci ya ratsa masa. "Abinda ban gane ba Dada waya kawo Hatsin?" Ya sake tambayarta. Ta miqe tana cewa "Rabon mune na amfanin gona da aka fitar dasu yayyenku suka raba, to kaga Rumbun nasu ne yanzu shiyasa nace ku saka a dakin Malam tunda nan babu guri" "Wancan abun ne rabon mu rai shida a cikin sama da buhu dari da aka fitar, kenan buhu daddaya muka tsira dashi cikin gadon uban mu ba wai kyaimuta aka bamu ba?" Audu ya fada cikin zafin rai yana miqewa se a sannan Yakubu yayi magana yace "Abinda suka ga ya kamata su bamu kenan kuma kar kace zakayi magana muje mu shigar dakin kamar yanda Dada tace" "Wallahi Baze yuwu ba, banda ma tsabar rainin wayo roqarsu mukayi da zasu tsammana wannan abun ko kuwa? Dole a fito da komai a sake rabo me yasa ma da zasu fara baka kirani ba" yana gama fadar haka fuuu yayi waje Dada da Yakubu na kiransa amma beko saurare su ba yayi dakin Goggo Fadi. Dada da Yakubi sunfi Audu sanin yanayin zaman gidan a yanzu saboda kusan shekara bakwai kenan daya fara zaman birni idan yazo yan kwanaki yakeyi ya koma kuma duk sanda zezo da abin hannunsa dan haka kowa haba haba yake dashi. Yakubu kuwa tunda ya fara makarantar kwana nan yake hutunsa dan haka yasan duk wata kitimurmura dake faruwa tsakanin Goggo Fadi da yayanta da yawan qorafin da sukeyi akan Abinci wanda a cewarsu su suke wahala su Noma Hafsatu da Yayanta sedai kawai suci harda Bilki da ake aikawa dukda shi Mijinta babu laiifi yana da rufin asiri dan haka be shiga cikinsu ana noman tare ba amma in akayi girbi se Malam yasa an loda itama an kai mata acewarsa tana da haqqi cikin gonar. Iyakar qoqari Malam yayi gurin ganin cewar kan Ahalinsa be rabu ba kuma har ya mutu yana musu wannan nasihar wadda kuma sunyi qoqarin boye taciki sun hada kai a gaban idonsa to amma yanzun basa jib zasu cigaba da bautawa Hafsatu da yayanta shiyasa suka fara da haka a ganinsu ma sun musu Adalci da suka basu wannan din ladan Aikin da Malam yayi kafin ya kwanta dama. Audu kuwa da sallama ya shiga dakin Dada yana qoqarin danne bacin ransa, suna zaune ita da Baba da Hashimu suna hira. Ya tsugunna daga gefe ya gaidasu suka amsa fuska a sake kafin sukayi shiru gaba daya. Seda ya saisaita muryarsa ta yanda zasuyi magana cikin risilama kafin yace "Yaya Daman naga hatsi a qofar mune dana tambayi Dada se tace mun wanda aka rana aka fitar mana ne" "Na'am, haka akayi" Hashimu ya fada yana karkacewa dukda cewar shi Audu da Baba yayi magana, shiru suka kumayi ganin da yayi basu da niyyar tanka masa dan Goggo Fadi ma wata hira take neman jefo musu tana tambayarsa yaushe ze koma Birni dan haka yace "Yaya tambaya fa nakeyi shi wancan abun ana nufin shine rabonmu mu biyar da Mahaifiyarmu kenan?" "Ga amsa ka bawa kanka Audu me kuma kake da buqata?" Baban ya magantu sannan yaci gaba da cewa "Ko yayi yawa ne? Tunda kai ba mazauni bane Yakubu ma Makaranta ze koma Innartaku daga ita se Aisha da Baballiya Aisha ma jiya na hadu da Hayatu yake roqar arziqin a basu ita tadan taya Bilki zama inaga an samu qaruwa ne ko yace bata da kafiya dama yanzu nake so idan zan fita na leqa nayiwa Goggon maganar to gaka ma seka shaida mata idan ka koma kaga wannan abinci ai ya isheta ita da Baballiya". Ran Audu ya qara baci amma ya daure murya a daure yace "Amma dai Yaya koda ace cikin Dada ne ita kadai kamata yayi a raba komai kai daya yanda shari'a ta tsara tunda dai muna da gado a ciki wannan ruwan mune bisa Adalci mu qara muku tunda kun fimu buqatar abincin" "Babu shakka rashin kunya zaka manq Audu mu kake kallo kana cewa mun fiku buqatar abinci wato ga mayunwata ko?" Goggo Fadi ta fada tana tafa hannu. Ko a jikinsa yace "Ni ba abinda nake nufi ba kenan Goggo, nufina su Yaya suna da Iyalai mu kuwa bamu da nauyin komai kamar kuma yanda ya fada mu ba mazauna bane dan haka abincin zeyi mana yawa ku kuma ya muku kadan" "To yanzu me kake so ayi?" Baba ya tambayeshi, Audu ya gyara zama yace "Rabo za'a sake na gaskiya a fitarwa da kowa haqqinsa idan ma ta kama a kirawo su Liman da me gari su raba" "To ba za'ayi hakan ba ubanmu, kai karfa kaga wai ka fara riqe yan kudade ka dauka kafi mu ko zamu bika to baka isa ba wlh da zaka zo kana yiwa mutane magana da sigar umarni. Bari ma kaji wannan rabon da kaga an baku dan dai Goggo ta saka baki ne amma da mu bamuyi niyyar baku kamar hakan ba saboda babu guminku ciki mu muka sha wahala muka noma abinci dan haka daga yanzu in har kuna son kuci abinda aka noma cikin gonar nan to sedai ku shiga ayi daku" Hashimu ya fada, Audu ya kalle shi kafin ya miqe yana cewa "Amma dai muna da gado a cikin gonar ko?" "Su kuma ai ba bayin ubanka bane da zasu sha wahala su noma kuna zaune su baku kuci" Goggo Fadi da se yanzun ta saka musu baki ta fada wannan ya tabbatar masa da cewar shawararsu daya dan haka ya fice yana cewa "Ai kuwa in har haka kuka zaba sedai a raba gonar idan yaso se na gani in abinda kuka samu ze isheku ku noma abincin shekarar". Goggo Fadi ta hau tafa hannu tana salallami wai yazo har daki ya qare musu tanadi. Audu kuwa yana fita dakin da suke kwana ya shige zuciyarsa na tafarfasa dan yasan idan ya koma dakin Dada ma fada zatayi masa ta bashi rashin gaskiya amma ya qudure a ransa kome za'ayi sedai ayi tunda ta haka suka zaba to su zuba su gani su waye zasu sha wahala. Kenan ita Goggo Fadi luf luf tayi musu sanda Malam na raye suke zaune lafiya da Dada shine yanzu daga mutuwarsa ko kwana sittin be cika ba fitina zata fara bullowa daga barayinta. Idan taqamarsu su suke noma gona ai su kuma suna da kaso a cikin qasar ya zama tamkar sun basu aro ne suna biyansu shikenan tunda dai basu hango wannan maslahar ba to za'ayita yanda suke so dan idan rigima ce kowa ya sani kaf karkarar bashida mahadi. Tun yana dan mitsitsi fada ne dashi kamar dage babu randa baz fita wasa ba tareda an kawowa Dada ko Baffa qarar ya daki wani ba shiyasa ma ya dena wasa da sa'anninsa ya shiga cikin su Yakubu amma ko su din idan kaga yanda yake a cikinsu seka dauka ya girme su kura ce tayi lafiya kuma tunda aka tabota kowa ze dandani kudarsa. Yana kwance yana saqa da warwarar ta inda ze bullowa al'amarin, yanzu idan ya koma Birni Yakubu ya koma makaranta kenan zaman gidan in ba'ayi wasa ba gagarar Dada zeyi to kuwa baze taba barin haka ta faru ba. Yakubu ya shiga dakin rai a hade yace ya tashi su kwashe kayancan amma ko gezau Audu beyi ba, daya isheshi da magana yace "Ka qyaleni baza'a kwashe ba se gobe tayi an sake Rabo sannan su kwashe nasu daga Rumbu tunda ai ba rabonsu bane ba" "Audu kasan me kake so ka taso kuwa?" Yakubu ya fada yana zama a gefen qafafunsa Audu ya wuntsila ya tashi zaune yace "Na sani, naje na same su sunce tunda bamu noma ba dan haka iyakar abinda zasu bamu kenan kuna daga yanzun ma muddin muna son Abinci sedai mu shiga ayi Noma damu" "To ai gaskiya suka fada, shiyasa nace maka bazan koma makaranta ba na haqura da karatun zan zauna na kula da Dada dasu Aisha kai kuma ka shirya ka koma Birni kaci gaba da Buga bugar ka" Yakubu ya fada cikin sanyinsa, Audu ya galla masa harara tsabar takaici daya rasa me zece masa kawai yayi tsaki ya koma ya kwanta. Haka Yakubu ya gaji da masa maganar ya tashi su kwashe kayan qarshe se Aminu daya shigo gidan ne ya taimaka masa suka kwashe, shima seda ya tambayi Yakubun kayan menene wannan yayi shiru bece masa komai ba. Daya shiga gurin Goggo Fadi lokacin su Hashimu sun tafi gidajensu ya sake tambayarta nan ta wassafa masa qarya da gaskiya akan Audu, Aminu yayi shiru kafin ya kalli Mahaifiyar tasa yace "Amma zancen gaskiya wannan ba Adalci bane Goggo, wannan hatsin da ake magana fa Malam ne ya noma shi a gonar sa mu duk mun tayashi aiki ne a matsayinmu na yayansa, kinga kenan duk wani Magajinsa yana da rabo daidai da kowa a ciki koda kuwa Jinjirine yau aka haife shi. Sannan maganar kuce idan basuyi Noma ba baza'a basu abinci ba bata taso ba saboda yau idan sukace a raba gonar nan kun sani Kason da zamu samu baze isa mu ringa noma abinda ze riqe mu ba, kuma ko cewa sukayi mu ringa haya muna biyansu bamu da abinda zamu basu. Nidai a ganina ayi maslaha koda kuna ganin ba za'a ringa raba daidai ba tunda mun fisu yawan Ahali a ringa fitar musu da abinda ze ishe su har su saida suyi sauran buqatu hakan duk taimakon kaine". Goggo Fadi tayi kasaqe tana kallonsa kafin tace "Babu shakka Aminu wato Hafsatu da Yayanta sun fimu a gurinka kenan ko?" "Ba abinda nake nufi kenan ba Goggo, ni wlh kece ma kike bani mamaki gaba daya kin biyewa Yaya Hashimu yana doraku akan wata hanya ta daban dan Yaya Baba ma babu ruwansa sedai idan yanzu shima ya dauki hudubar tasa, har Malam yaja numfashin qarshe yana mana nasiha da mu hada kanmu kar mu bari baraka ta shiga tsakaninmu me yasa kuka zauna tsayin shekaru lafiya dasu se yanzu daya mutu sanda yafi buqatar mu hada kai mu cigaba da yi masa addu'a sanann ne kuma fitina da rabuwar kai zata bullo? Kowa ya sani Dada bata da matsala kuma kome zakuyi ba zata daga kai ta kalle ku ba amma ai mutum ya kamata yasan daidai ba se an tunatar dashi ba ina amfani cikin danne haqqin wani wannan abun fa magana ake ta dukiyar marayu da wanda ya cinye kudi da kadarori daku da kuke shirin cin kwayoyin hatsi a gurin Allah baku da banbanci Goggo, nidai shawarata tun wuri ku farga karku bari shaidan yayi tasiri a zukatanku. Yanzu an fara rigima akan Gona gobe kuma se ace za'a raba gida shikenan zumunchin da Malam yake ta mana takarar mu riqeshi kinyi sanadin murqusheshi" "Nice ma zan raba muku zumunchin?" Goggo Fadi da jikinta yayi sanyi da maganganun Aminun ta fada, ya miqe yana cewa "Eh mana saboda duk fitinar da su Yaya Hashimu zasu zo da ita idan kika tsawatar musu dole su bari amma idan kika basu goyon baya kinga gaba zasu qarayi" daga nan ya fice ya wuce can dakinsu inda suke kwana dasu Audu. Tun Asuba da suka fita masallaci Audu be dawo ba kaitsaye qofar gidan Liman ya tafi ya jirashi yana zuwa kuwa ya zayyane masa abinda ya faru dan ya rantse baze bar maganar ba, shirye shiryen komawa Birni yakeyi tayaya hankalinsa ze kwanta a can Alhalin an fara irin haka ga Yakubu yana maganar ze haqura da mafarkinsa saboda ya zauna ya kula da mahaifiyarsu shi kuma baze yarda ba shiyasa zeyi iyakar qoqarinsa yaga komai ya daidaita sannan su rankaya su koma Kano dan yayi rantsuwa muddin yana numfashi seya cikawa Yakubu burinsa na zama Alqali. Liman ya gama jin bayaninsa yace yaje ze samu me gari daga nan za'a kira duka yan uwan nasa su zauna haka akayi kafin yamma duk an kai musu sammaci bayan sallar isha'i suka hallara gaban me gari Hashimu se muzurai yakeyi Baba dai fuskarsa kadaran kada han. Liman yace Audu ya maimaita abinda ya faru tsaf ya sake rattabo musu Yakubu se faman harararsa yakeyi aka tambayi su Hashimu sukace haka ne daga nan Liman ya fara musu shari'a ya karanto musu abinda Shari'a ta tanada akan rabon gado, koda ace wani da Guda daya shine kan ragamar juya dukiyar Ahali gaba daya, muddin dai wannan dukiya mallakin mahaifinsu ce duk randa ya mutu hatta da Jinjiri idan ya bari yana da gado a ciki, babu zancen kai kasha wahala ka tara dukiya tunda dai ba taka bace to ta kowace gaba daya. Liman yace gobe za'aje a fito da Hatsi gaba daya a rabawa kowa nasa idan yaso se su sake hadewa su ajiye duk inda suka ga dama. Hashimu zeyi magana Baba ya hanashi, haka aka tashi rayuka babu dadi washe gari kuwa Liman da wakilan me gari sukaje aka sake rabon Hatsi dukda cewar a cikin daren Hashimu yasa an kwashe fiye da rabi an kai gidansa ya boye a hakan seda aka fiddo da huhunhuna hamsin da biyar, aka hada dana gurinsu Audu shida ya zama sittin da daya nan aka raba musu kowanne bangare suka tashi da Talatin, guda dayan kuma aka bawa masu rabo ladan aikinsu wanda ba shari'a ce tace a bayar ba tsabar son zuciya ya saka su karba. Cikin zafin rai Hashimu yace "Toh tunda anyi haka se a fadi yanda za'a cigaba da kasafin Abincin dan wlh babu yanda za'ayi musha wahala muyi noma suna zaune mu ringa raba komai daidai dasu. Audu yayi tsugul yace a raba Gona kowa ya dauki kasonsa. Yakubu ya zabga masa harara yana cewa "Idan an raba kai zauna ka nomata?" "Se mu bada haya, idan kuma su zasu karba ma bismilla ayi qiyasin abinda zasu ringa biyan mu duk shekara" Audu ya sake fada. Dada dai ta rasa abin cewa dan duk bata san tsiyar da aka qullo ba seda aka zo rabon abincin kiran da aka musu jiya da suka dawo babu wanda ya fada mata inda sukaje. Haka dai aka tashi a matsayar zasu bar musu barin gonarsu suci gaba da nomawa, ladansu duk shekara abinda aka samu za'a raba uku, su dauki biyu su basu kaso daya matsayin ladan hayar gona kowa yayi na'am da hakan dukda zuciyar Hashimu da Sama'ila Mijin Amina dan karere sunyi wani qullinsu na daban. Audu be koma Kano ba seda suka tabbatar sun saita komai, sun siyarda wani kaso na abincin suka barwa Dada kudin a hannunta saboda laluran yau da kullum kafin ya tasa Yakubu a gaba kamar shine qanin suka koma lokacin tuni zangon karatu yayi nisa har ana shirin jarabawa dakyar aka karbeshi yaci gaba. Audu yaci gaba da buga bugarsa a birni yana hada kan kudade, sana'a babu wacce baya gwadawa, idan kasuwar ta gusa seya saki ya koma leburanci, shine aikin gini shine zuwa gidan Burodi har sannan kuma yana zaune a makarantar Gwani Musa dan bashida wani guri da zeje ya ringa kwana idan ba nan din ba. Yana lissafe da su Yakubu sunyi hutun makaranta har an dawo wata rana ya shirya zuwar masa Visiting kamar yanda ya saba sedai bayan yaje makarantar aka shaida masa Yakubu be dawo hutu ba. Kwana biyu tsakani ya tasamma Bechi dan yaje yaga meya hanashi komawa makarantar, bayan isarsa ya tarar da Dada bata da lafiya,a yanda aka gaya masa wai Barayine suka diro tsakar dare suka kwashe musu abinci sannan suka farmaki dakinta suna neman Murjaninta da wata sarqar Zinare data gada gurin Mahaifiyarta da basu samu bane shine suka mata duka ita da Aisha har Aishar ta samu karaya a hannu. Audu rasa abin cewa ma yayi, tunda aka haife shi a qauyen be tabajin ance barayi sun haura wani gida ba, ba wannan bama ace da suka shigo iyakar Rumbunsune ya tsone musu ido basu taba nasu Goggo Fadi ba sannan zancen Murjani tana dashi wanda ya taka na Dadansu a Daraja dan har shagube takeyi tace se Auran Aminu Autanta ya tashi zata bayar aje birni a siyar dashi tayi hidima duk basu bi sun dauka ba se na Dadarsu. Yayi niyyar tayarda balahira Dada tace Akul, ko bata sani ba idan yayi magana bata yafe ba wannan yasaka jikinsa yayi laqwas, tsanar da be taba zaton zeyiwa jininsa ba ta dirar masa domin yasan shirin sune. Haka yayi sati daya ya juya dan Yakubu ya rantse masa baze sake komawa makaranta ba gaba besan abinda ze faru da su Dadar ba. Har kuka Audu yayi akan shi ze zauna Yakubu ya tafi ya qarasa karatunsa amma yaqi, yace to sedai su zauna duka nan Yakubu ya ringa lallabashi akan ya tafi shiya haqura da Boko haka Allah ya qaddara bakin abinda ze samu kenan ze zauna ya fara sana'ar dinki daya koya a zamansa a Kano yaci gaba da kula da mahaifiyarsu. Da banbaki ya yarda ya juya Kano da burin nema domin ya samu ya fiddo da mahaifiyarsa da yan uwansa daga Bechi suzo suyi rayuwa me kyau. *Batoul Fashion and Boutique* online store ne na sai da kayan 'yan gayu dandasa-dandasa na gani na fada, na kece raini a taro, masu tashin kan Habeeby ❤️ Kuma masu sa kishiya kwalla😂🏃🏻‍♀ Muna da Laces, Atampa, Voiles, Shoes, Bags, Gowns, Veils and Jewelry masu kyau a farashi me sauqi, Muna Bada sari Kuma Muna siyar da daidai, Muna hada lefe masu Aji🔥🍻kada na cika ku da surutu😌ku garzaya IG page dn www.instagram.com/batoul_fashion_and_boutique don shaida bayanan da na muku da Kuma tabbatarwa ko ku shiga WhatsApp group dn ta https://chat.whatsapp.com/Fi0iCJcvtGKEYcVrbZwxfw za ku iya tuntubarmu a 07025420431 *MATAR MUTUM* *NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER* *MARUBUCOYAR* *WATA KISHIYAR* RUBUTACCIYAR QADDARAH* *HALIN KISHI* *FIKRA WRITERS ASSOCIATION* *LITTAFIN KUDI NE* *PAY 400 (PROMO PRICE BAYAN KAMMALA FREE PAGES ZE KOMA 500) A ASUSUN* *7061838488* *OPAY DIGITAL SERVICES* *MARYAM FAROUK* OR *0709290797* *ACCESS BANK* *SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488* *IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705* *NAGODE* *FREE PAGE 4* Haka rayuwa taci gaba da garawa, iya wuya Audu ya dukufa gurin neman Halalinsa kuma ubangiji ya sanya masa Albarka a abun duk abinda ya taba nan da nan se ya karbeshi sedai kuma wani ikon Allah daya fara ganga ganga se sana'ar ta turgude sedai ya saketa ya kama wata wannan yasa aka koma yi masa laqabi da Audu sana'a Goma dan da yawa suna ganin kawai zafin nema ne ya saka komai seya taba. Wata shida shida yake kai ziyara gida idan kuma ya tashi tafiya haka ze hada tsaraba tuli ya kaiwa yan uwansa harda yan Dakin Goggo Fadi da tun abinda ya faru akan Gona aka koma zaman doya da manja idan ka cire Aminu shikadai ne suke mu'amalla dashi yayi Aure har matar ta haihu sun samu Abdullahi yaron idan ka ganshi se kace Audu ne ya haifeshi su Yaya Hashimu kuwa ana fama da baqin rai amma hakan be hana idan Audu yaje da kayayyaki ya basu babu kunya su karbe, a kwai zuwan da yayi Malam babban dan Yaya Baba yace ze bishi Birni Goggo Fadi tayi kicin kicin ta hana a cewarta baze tafi dashi ya koyo masa fitsara da rashin mutunchi irin nasa ba dukda Yaya Baban yaso hakan amma babu yanda ya iya Audu ya koma cike da baqin cikin Yakubu da duk zuwan da zeyi seya masa magiyar ya koma yaci gaba da karatunsa amma yaqi. Shekaru uku suka shude a sannan Audu nada shekaru Ashirin a duniya ya zama cikakken saurayi ta kowanne fanni, neman Kudi kuwa se abinda ya qarun masa, tuni an aurar da Aisha Yakubu ma yakai kudin aure a can rigar su Dada ya samo budurwa Balaraba kyakykyawar bafilatana har an tsayar da rana watan Azumin tsofaffi wata uku kenan masu zuwa shirin Auran yasa Audu ya qara qaimi gurin neman kudi, a cikin gidansu suka yanki fili Yakubun ya gina daki ciki da rumfa saboda gurin yana da yalwar tsakar gida kowa dai yasan yanda akw gini a zamanin da, mutum daya na iya faro gida yaya su tasa duk suyita yankar fili suna tada dakuna a ciki suma. Hada qarfi sukayi shida Audu sukayi ginin dan shima yana taba Dinki kuma da yake yazo da zamananci za'ace ba kamar yanda aka saba a karkarar ba se ya zamana yayi suna har daga maqwaftan qauyukansu ana kawo masa dinkin. Tsaf suka gina daki dukda ginin qasane amma anyi Sumunti da daben qasa wanda daga Kano Audu ya taho da simintin haka dakin Dada ma an daga mata shi anyi dabe da fulasta, dakinsu da suke ciki a da wanda yake Rabon yaran Goggo Fadi ta zugasu sun karbe wai Hashimu ne yake ajiyar Hatsi dan yanzu ya siyi gona tasa daban yana nomawa kuma a tasun ma haka zeyi bake bake idan an girbe yafi kowa kwasa wannan dalili yasa Audu ya gyara Asalin dakin Malam wanda suka mayar na ajiyar shigi shima yayi dabe da fulasta ya zama gurin saukar sa idan yazo, da ana aikin ma so yayi da ayi katanga a raba gidan tunda har Bandaki sukayi dan Asalin na gidan a barayin Goggo Fadi yake sunyi wani tun rashin lafiyar da Dada tayi bayan rasuwar Malam akayi mata bandaki daga kusan dakunan ta yanzun ma kuma anyi a gefen dakunan Yakubu wanda Audu yace za'a dan kewaye masa bangaren saboda sirri. Ya koma Kano da niyar se bikin Yakubu ya rage sati biyu ze dawo kafin nan ya sake roro abinda za'ayi hidimar biki. Da akwai Malam Mudan dan Bechi ne amma yana yawan shiga Kano dan baya rufa wata biyu beje ba ta hannunsa Audu yakeyin aike ko su aika masa daga nan. Wata sabuwa ce ta bullo daga bangaren Bara'atu yarinyar da Audu yake mutuwar so yake kuma burin aure, tun dama dai Babanta ya matsanta matuqa akan ta fidda miji, duk sa'anninta an musu aure har sun fara haihuwa kullum ta Allah se yayi wannan mitar amma Inna tayita danneshi saboda ita tana son Bara'atun da Audu to wannan karon yace ya gaji duk danginsu babu yarinyar data taba shekara goma sha Shida a gida se a kanta kuma bawai bata da masoya ba dan haka seji kawai Inna Hajara tayi ya karbi kudin auran Bara'atun da saka rana wata uku kusan lokaci daya ze kama dana Yakubu kenan. Bara'atu tasha kuka hankalinta ya tashi batayi qasa a guiwa ba tayi tattaki ta samu Yakubu dukda yar kunya da suke a matsayinsa na yayan saurayinta haka ta ringa masa kuka akan yaje ya gayawa Audu karya bari a aura mata wani ba shiba, yana komawa gida kuwa ya sanarwa da Dada tace yayi shiri ya taho Birni dan daman tasan za'ayi haka, duk sanda Audun yaje seta masa zancen ya kamata yasan me suke ciki da Bara'atu se yace mata ba yanzu ba yana so abubuwa su qara daidaitar masa akwai shirye shiryen da yakeyi. Dole Yakubu yayi tattaki ya tafi Kano wanda rabon shi da zuwa tun hutun makaranta wanda daga shi be sake dawowa ba shekaru hudu kenan. Yakubu Kano be zarce ko ina ba se Tsohuwar makarantar Allonsu wato makarantar Gwani Musa dan yasan Audu bashi da wani masauki se can, sedai yayi rashin sa'a Malam ya sanar masa tuni Audu ya bar nan, ya kan dai kawo musu ziyara lokaci lokaci dan ba'afi sati bama yazo kuma Almajirai suna ganinsa a Kasuwar bakin Asibiti idan sunje yawo yace musu yanzu a Goron dutse yake zaune bedai san takamaiman wani guri a can din ba. Yana zaune a bakin Masallaci yana jira ko Allah ze kawo daya daga cikin yaran da sukace sun san inda yake zama a Kasuwa su rakashi sega Hayatu, yaron gidan da Audu ya yiwa aiki wanda Babansu ya kaisu makarantar Boko a lokacin. Cikin mamakin ganin juna suka gaisa yace suje gida a can yaci Abinci yanata kallon Hayatun daya zama kalar yan gayu da gani ya fara jiquwa a Boko. "Tunda ka tafi makarantar kwana shikenab bamu sake haduwa ba shekaru kusan takwas kenan amma banji dadi da Audu yace mun ka bar Boko ba, kaga ni yanzu haka ina shekarar qarshe a Jami'ar ABU zaria ina karantar Engineering da ace ka cigaba kaima yanzun ko baka gama ba kana kan hanya" Hayatun ya fada. Yakubu yayi murmushi kawai amma bece komai ba, duk wanda ze so masa da yayi Boko a bayan kansa ne dan mafarkinsa ne ya zama Alqali tun besan me hakan yake nufi ba. Ganin bazeyi magana ba yasa Hayatu cewa ya tashi suje ya kaishi inda Audun yake dan shi suna haduwa sosai har inda ya kama hayar shago yake zaune a can Goron dutsen ya sani. A kasuwa suka samu Audu yamma tayi anata hada hadar kasuwa dan a sannan ma ake cin kasuwar sosai, kayan yaji yake siyarwa a sannan da sauran kayan qamshi zuwan Yakubu tasa dole ya tattara komai suka tafi masauki. Seda sukayi sallar Magriba da isha, ya rasa ma me ze ajiyewa Yakubun, ya kwaso Wasu yadika dinkakku kala biyu kowanne saiti uku a ajiye masa sannan ya sake dakko Shadda dinkin babbar riga shima guda biyu ya ajiye yana cewa "Na Baballiya ne ba'a gama ba, daman Juma'ar nan nake cewa idan Malam Mudan ya shigo zan hada masa yayo mun gaba dasu kar kaya suyi mun yawa idan na tashi tahowa" "Yanzu dai duk ka ajiye wadannan ka saurari maganar da nazo maka da ita" Yakubu ya fada yaba tattare kayan gefe, Audu ya zauna yana kallonsa se a sannan ma ya lura da cewar Yakubun bashida walwala dukda dai shi daman bame hayaniya bane sosai. A taqaice Yakubu ya bashi Labarin daya gigitashi jin cewar an sakawa Bara'atu rana da wani dan uwanta ya shiga share zuba dukda qofar Shagon a bude take ga iska na busowa amma Audu zufa yakeyi kansa ya shiga sarawa jin ze rasa Bara'atunsa macen daya gama kwallafa duk wani buri na duniya akanta. Shikadai yasan irin tanadin da yakeyi akan auransu shine yanzu Babanta zece ya bawa wani ita. "Shiyasa kullum Dada take maka magana akan kasan me kake ciki saboda gudun haka, ban dama Inna Hajara tana tataka ai kasan tuni Bara'atu ta dade a daki Bilki da suke sa'anni kana gani da ciki yana tsaya mata ai tayi yaya biyu ko uku yanzu tunda dai ga Aisha nan da ciki Auran bana se ita kake so tayita zama har se sanda ka gama shirinka duk sa'annin ta sunyi Aure har an fara zundenta a gari " Yakubu ya fada. Audu dai bece masa komai ba haka suka kwanta amma fa be iya bacci ba, cikin daren ya hada yar jakarshi, Asubar fari suka dauki hanya dan yace baze tsaya ganganci ba dole yaje a san me ake ciki amma da ransa baze bari wani ya auri Bara'atu ba. Bayan dogon tirka tirka da yayyensu daga qarshe suka yarda zasuje tambaya masa Auran Bara'atun, sunje da fari Babanta yaso yayi gardama akan shi ya rigada ya amshi maganar wani ya basu haquri suka taho gida Hashimu har yana Allashi qara ai gara haka, seya koma can Birnin da ya liqe yagani idan ze samu macen da zata aure shi babu wanda yasan saga inda yake kujifa. Kwana biyu tsakani Audu na kwance yana jinya tunda yaji cewar baza'a bashi Bara'atu ba sega dan aike daga gidansu akan Babanta yace ya turo yau a daura musu Aure ashe wai Rijiya ta durfafa dagaske zata fada idan ba'a fasa auranta da wancan ba, harta tsoma qafa daya babanta yaga dai dagaske bata hayyacinta shine yace ya janye amma fa sedai Audu ya turo yau a daura Aure dan muddin aka kai ranar daya saka da wancan tofa sedai ta mutu shine Innarya ta tashi Yayanta ta aikoshi, Audu najin batun ya miqe beyi wata wata ba ya kama hanyar Gona inda su Yakubu suke can suna gyaran kunya kamar wani yaro ya zube yana basu labarin abinda akace. Daga qarshe dai Yaya Baba da wasu Abokanan wasansu biyu ne suka sake zuwa dan Hashimu yace ba inda zeje, an samu Baban Bara'atu ya haqurq da zancen daura aure ranar aka tsaida magana akan rana daya dana Yakubu. Da wannan farin ciki Audu ya koma Kano, dukda ba haka yaso ba. So yayi ace se yayi gida a Kano sannan zeyi aure dan biki yake so yayi irin wanda akeyi A Kano yayiwa Bara'atu lefw na yargata wanda ze zama abin tarihi a garinsu harda kewaye, amma yanzun ma bata baci ba, zeci gaba da qoqari kuma ko ba yanzu ba seya biya bashin duk abinda ya qudurci yi mata. A haka kwanakin Biki sukazo, a zatonsa za'a daura aurene kawai tunda kowa yasan bashida Mahalli yayi qoqari ya siyowa Bara'atu kayayyakin fitar Biki daga Kano aka dinko harda takalma da mayafai kala hudu yayi mata na yan birni. Ana saura kwana hudu daurin Aure ya tafi Bechi bayan yayi sallama da Abokanasa na kasuwa dana unguwa dukya shaida musu zeyi aure, amma biki ba yanzu ba suka hada masa gudummawa kuwa sosai har seda yayi mamaki, koda yake shidin ba daga baya ba gaskiya bashida rowa ko kadan, haka Biki, suna, ta'aziyya sedai idan beji ba suma duk sun masa Alqawarin idan biki ya tashi zasuje tunda yanzu abin yazo a qurarren lokaci basu shiryi tafiyar ba. Ranar Juma'a aka daura Auran, na Yakubu aka fara daurowa da safe a can Rigarsu Balaraba suka dungumo da Amarya da yan uwanta, se bayan sallar Juma'a aka daura na Audu da Bara'atu. Murna kam ba'a cewa komai a gurin Dada da tasha kwalliya cikin kayan da Audu ya dinka mata, haka qannensa Bilki da Aisha sun sha Anko Baballiya kuwa shaddarsa iri daya data angwaye wanda dama Audu ya dinka musu da niyyar suyi fitar bikin Yakubu se gashi abu yazo a daidai. Qarfe tara suna can Majalisa da Abokanai ana ta shaqiyanci sega Baballiya da gudu yake fada musu wai an Kawo Amaryar Yaya Audu. Kowa yayi mamaki dan ko jiya da yaje gurinta seda suka sakeyin maganar tace masa Innarta tace se daga baya zata tare tunda abin yazo babu shiri Babanta kuwa Magriba nayi ya tada ballin se an kaita, an ce masa babu daki yace ta rakuba a na Babarsa da ya san be shirya auran ba yayi haka yan uwa suka rakota ita kam ko a jikinta dan ko cikin Rumbub gidan aka ce ta zauna shiga zatayi tunda dai burinta ya cika ta Auri Audu. A dakin sa aka sauketa da qawayenta da zasu kwana, daren ranar Audu tunanin yanda zeyi kawai yake, da yasan za'ayi haka da ya ququta ko babu dabe itama an tayar mata da daki ko ciki dayane, haka dai gari ya waye, da hantsi yan uwan Balaraba suka gama mata jere tsaf irin na yar gata harda Kumbo nan suka fara shirin tafiya bayan sun qara damqa Amarta a hannun yan uwan Yakubu. Daga bangaren Bara'atu dai babu wanda yazo se qawayenta da suka kwana. A can gidansu ana ta taqaddama tsakanin Babansu da Innarta akan yace ko tabarma baze kai mata ba tunda bata bi abinda yake so ba, ita kuma ta rantse se yayi, da yasan haka ne seya bata lokaci ita da take son auran zatayiwa yarta komai amma yanzu banda kwanuka babu abinda ta tanada dan haka dole ya fito da kayan gado danbaze barwa yarta abin gori ba bayan ba rasa abinda zeyi mata yayi ba gashi tun rana bata daga ba labarin jeran da akeyiwa Balaraba ya fara bazuwa a gari dan itama Babanta Attajirine a rugarsu kuma itace Auta a mata dan haka sun mata bajinta. Hayaniyarsu har dakin Ilu Abokin Audu da suka kwana a gurinsa maqota suke dasu Bara'atun kuma dakinsa jingibe yake da dakin Soron su Bara'atu inda Innar tata da Baba suka shiga wai suna sirri saboda yan biki dake ciki se gashi Audu yaji komai, sulalewa yayi ya tafi cikin garin Kumbotso saboda yafi masa kusa akan yace ze tafi Kano, yasan gurin lokaci lokaci yana zuwa dan har Aboki yake dashi kai tsaye gurinsa ya tafi bayan sun gaisa be bata lokaci ba ya zayyane masa abinda yake tafe dashi na batun kayan daki saboda garinsu Babu Kafinta meyin kayan katako, gadon qarfe kuma a gurinsa shi da yake zaune a birni yake ganin kayan gado da akeyi na Alfarma ya fitar masa yayi. Nura ya kaishi gurin wani Kafinta da ake ji dashi a Kumbotso dan a Kano ya koyo aiki wasu kayan ma daga can yake dakkowa ya kawo. Ya numa masa wani Gado Lamba 1 da Kobud dinsa me biyu ta yan gayu dan harda mudubi a jikin murafenta ga kuma mudubi shima me durowa uku a jiki kayan sunyi kyau gasu Ruwan Hoda irin kalar da Bara'atu take so sedai kudin da aka saka musu a yanayin da yake ciki sun masa yawa ga Katifa da ze siya da pillo, aka tirza aka tisa dakyar dai kaya suka siyu, shima seda Nura yayi masa ciko daga baya zasu warware tunda suna haduwa A Kano, aka loda masa su a A kori kura da dundumemiyar katifa da pillow biyu harda Abin shimfida dana rufa ya kama hanyar gida. Sanda ya dawo yamma tayi rana na gabda faduwa, a waje ya bar masu mota ya shiga ciki nan ya tarar da Dada da yan uwanta da basu wuce ba suna ta kiciniyar kwashe yan kayayyakinta ana shigar dasu dakinsa nasa kuma suna waje da alama dakinta za'a mayar dasu daman ba wani shirgi ne dashi ba Gadon qarfe ne da wata Katifa da yake ta saka ranar canzata tunda ba kullum yake kwana a kai ba se yayi ta mantawa se akwatinsa guda daya. Kunya ta kamashi yanda aka faka kayan a gefe, kenan Dada dakinta zata basu kuma wannan Gadon za'a sakawa Bara'atu "Yawwa ga Audu" Matar Yayan Dada da basu yada zumunchi ba ta fada dan tun safe ake nemansa an rasa shi ga babu waya bare aji inda ya tafi. Dada ta yafa gyale ta yafice shi suka yi soro, Goggo Fadi, Maryo da sauran Maqwafta yan tsogumi da suka baza tabarma, sun gama kallon dakin Balaraba suka fito aka kafa gulmar ana jira aga me za'a sakawa Bara'atu ita kuma, "Koda yake ina dakin ma?" Fadar Goggo Fadi, Maryo ta karkace baki tace "Dukdai qaryar Birnin ta qare, ayita zuwa ana burga a bikin jama'a ga nashi ya tashi ko dakin da za'a ajiye Amarya babu idan da gaske da kudin ai daga tsaida rana yaci a dora ginin Bulon sumunti ma bana qasa ba" suka tafa da matar Hashimu dake kusa da ita. Dada kuwa suna zuwa zaure tace "Ina ka tafi Audu bayan kasan halin da ake ciki babu inda dan uwanka bw zaga a garin nan ba amma ba'a ganka ba Jama'a har ana cewa ka gudu". Dariya ta kwace masa yace "Na gudu kuma Dada naje ina kamar wani mara gaskiya?" "Oho dai duk ba wannan ba, Hasiya tazo ta gaya mun Baban Bara'atu yace bazeyi mata kayan daki ba, da ace mun san da tariyar nan da tuntuni mun fara shiri amma yanzun ma se ayi amfani da abinda Allah ya hore, na bar muku dakina tunda kaga yafi girma ni se na koma na Malam, Babana kuma ya shiga cikinsu Idrisa (Yaran Yaya Baba da suke zama a gidan) kafin muga abinda Allah zeyi, idan an kwana biyu filin can na gefe seka shigo mata dashi ayi bandaki da gurin girki irin na Yayanka kaga shikenan a sannu Allah ze hore duk kuyi muhalli irin wanda kuke buri, wancan gadon naka ma gaskiya Audu ba'a bawa Amarya ba ga Katifa duk Babana yaci qaniyarta idan da sarari ko katifa ce ka siyo da ledar daki a shimfida mata". "mma Dada da baki fita daga dakinki ba wancan dinma ya isa ta lallaba kafin muga abinda Allah zeyi" Audu ya fada, Dada ta juya tana cewa "Kaje dai muga ko katifar da Ledar zasu samu" ya tsayar da ita yana cewa "Shaf na manta da Ledar wlh sedai ko Bilki taje yanzu inda za'a samu, leqa kiga ga kaya nan dai na samu dukda dai nasan basu kai yanda akeyi ba". Dada ta leqa, baki ta saki ganin kaya tuni kuma yara da matan Unguwa da sukazo shiga gidan suka baibaye motar ana kallo dan ba'a taba ganin irinsu a garin ba. "Audu, Kano kaje har ka dawo wannan kaya haka?" Dada ta fada cikin mamaki, Audu yayi murmushi yace "A turo Bilkin ta samo Ledar tunda ita akw fara shimfidawa ko anjima zan miki bayani. Dada ta koma ciki bakinta a washe yaqi rufuwa ta tura masa Bilki. Gidanta ta tafi ta dakko ledar data siya take shirin canza ta dakinta bata rigada ta shimfida ba dama ta bari se an gama hidimar Biki nana da nan aka hadawa Amarya daki ga gado na Alfarma kamar wani gidan zoo haka mata keta leqawa masu gyaran daki na korarsu dan sun hanasu yin aikinsu yanda ya kamata tuni kuma labari yakai wa Innar Bara'atu, ta fashe da kuka tana cewa "Allah na gode maka daka nunawa masu gulma da munafurci qarshensu" tun safen suke qullawa da warewa da yan uwanta akan yanda za'ayi, ta hada dan abinda ya samu, Gadon katako taso tayiwa Bara'atu dan ance Amaryar Yakubu ma shi aka mata amma abinda suka hada baze isa ba kuma wanda za'a tasa ya tafi Kumbotso a yammar shine aiki har sun saddaqar a dauki na qarfen anje shima me siyarwar wai baya nan abin duniya duk ya mata yawa sega wannan labarin farin cikin dukda tasan wata sabuwar gulmar za'a samu ace Miji ne yayi mata ko babu komai sabon salo ne dan babu yarda Miji yaso haka a garin har yayi mata kayan daki.*Batoul Fashion and Boutique* online store ne na sai da kayan 'yan gayu dandasa-dandasa na gani na fada, na kece raini a taro, masu tashin kan Habeeby ❤️ Kuma masu sa kishiya kwalla😂🏃🏻‍♀ Muna da Laces, Atampa, Voiles, Shoes, Bags, Gowns, Veils and Jewelry masu kyau a farashi me sauqi, Muna Bada sari Kuma Muna siyar da daidai, Muna hada lefe masu Aji🔥🍻kada na cika ku da surutu😌ku garzaya IG page dn www.instagram.com/batoul_fashion_and_boutique don shaida bayanan da na muku da Kuma tabbatarwa ko ku shiga WhatsApp group dn ta https://chat.whatsapp.com/Fi0iCJcvtGKEYcVrbZwxfw za ku iya tuntubarmu a 07025420431 *MATAR MUTUM* *NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER* *MARUBUCOYAR* *WATA KISHIYAR* RUBUTACCIYAR QADDARAH* *HALIN KISHI* *FIKRA WRITERS ASSOCIATION* *LITTAFIN KUDI NE* *PAY 400 (PROMO PRICE BAYAN KAMMALA FREE PAGES ZE KOMA 500) A ASUSUN* *7061838488* *OPAY DIGITAL SERVICES* *MARYAM FAROUK* OR *0709290797* *ACCESS BANK* *SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488* *IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705* *NAGODE* *FREE PAGE 4* Haka rayuwa taci gaba da garawa, iya wuya Audu ya dukufa gurin neman Halalinsa kuma ubangiji ya sanya masa Albarka a abun duk abinda ya taba nan da nan se ya karbeshi sedai kuma wani ikon Allah daya fara ganga ganga se sana'ar ta turgude sedai ya saketa ya kama wata wannan yasa aka koma yi masa laqabi da Audu sana'a Goma dan da yawa suna ganin kawai zafin nema ne ya saka komai seya taba. Wata shida shida yake kai ziyara gida idan kuma ya tashi tafiya haka ze hada tsaraba tuli ya kaiwa yan uwansa harda yan Dakin Goggo Fadi da tun abinda ya faru akan Gona aka koma zaman doya da manja idan ka cire Aminu shikadai ne suke mu'amalla dashi yayi Aure har matar ta haihu sun samu Abdullahi yaron idan ka ganshi se kace Audu ne ya haifeshi su Yaya Hashimu kuwa ana fama da baqin rai amma hakan be hana idan Audu yaje da kayayyaki ya basu babu kunya su karbe, a kwai zuwan da yayi Malam babban dan Yaya Baba yace ze bishi Birni Goggo Fadi tayi kicin kicin ta hana a cewarta baze tafi dashi ya koyo masa fitsara da rashin mutunchi irin nasa ba dukda Yaya Baban yaso hakan amma babu yanda ya iya Audu ya koma cike da baqin cikin Yakubu da duk zuwan da zeyi seya masa magiyar ya koma yaci gaba da karatunsa amma yaqi. Shekaru uku suka shude a sannan Audu nada shekaru Ashirin a duniya ya zama cikakken saurayi ta kowanne fanni, neman Kudi kuwa se abinda ya qarun masa, tuni an aurar da Aisha Yakubu ma yakai kudin aure a can rigar su Dada ya samo budurwa Balaraba kyakykyawar bafilatana har an tsayar da rana watan Azumin tsofaffi wata uku kenan masu zuwa shirin Auran yasa Audu ya qara qaimi gurin neman kudi, a cikin gidansu suka yanki fili Yakubun ya gina daki ciki da rumfa saboda gurin yana da yalwar tsakar gida kowa dai yasan yanda akw gini a zamanin da, mutum daya na iya faro gida yaya su tasa duk suyita yankar fili suna tada dakuna a ciki suma. Hada qarfi sukayi shida Audu sukayi ginin dan shima yana taba Dinki kuma da yake yazo da zamananci za'ace ba kamar yanda aka saba a karkarar ba se ya zamana yayi suna har daga maqwaftan qauyukansu ana kawo masa dinkin. Tsaf suka gina daki dukda ginin qasane amma anyi Sumunti da daben qasa wanda daga Kano Audu ya taho da simintin haka dakin Dada ma an daga mata shi anyi dabe da fulasta, dakinsu da suke ciki a da wanda yake Rabon yaran Goggo Fadi ta zugasu sun karbe wai Hashimu ne yake ajiyar Hatsi dan yanzu ya siyi gona tasa daban yana nomawa kuma a tasun ma haka zeyi bake bake idan an girbe yafi kowa kwasa wannan dalili yasa Audu ya gyara Asalin dakin Malam wanda suka mayar na ajiyar shigi shima yayi dabe da fulasta ya zama gurin saukar sa idan yazo, da ana aikin ma so yayi da ayi katanga a raba gidan tunda har Bandaki sukayi dan Asalin na gidan a barayin Goggo Fadi yake sunyi wani tun rashin lafiyar da Dada tayi bayan rasuwar Malam akayi mata bandaki daga kusan dakunan ta yanzun ma kuma anyi a gefen dakunan Yakubu wanda Audu yace za'a dan kewaye masa bangaren saboda sirri. Ya koma Kano da niyar se bikin Yakubu ya rage sati biyu ze dawo kafin nan ya sake roro abinda za'ayi hidimar biki. Da akwai Malam Mudan dan Bechi ne amma yana yawan shiga Kano dan baya rufa wata biyu beje ba ta hannunsa Audu yakeyin aike ko su aika masa daga nan. Wata sabuwa ce ta bullo daga bangaren Bara'atu yarinyar da Audu yake mutuwar so yake kuma burin aure, tun dama dai Babanta ya matsanta matuqa akan ta fidda miji, duk sa'anninta an musu aure har sun fara haihuwa kullum ta Allah se yayi wannan mitar amma Inna tayita danneshi saboda ita tana son Bara'atun da Audu to wannan karon yace ya gaji duk danginsu babu yarinyar data taba shekara goma sha Shida a gida se a kanta kuma bawai bata da masoya ba dan haka seji kawai Inna Hajara tayi ya karbi kudin auran Bara'atun da saka rana wata uku kusan lokaci daya ze kama dana Yakubu kenan. Bara'atu tasha kuka hankalinta ya tashi batayi qasa a guiwa ba tayi tattaki ta samu Yakubu dukda yar kunya da suke a matsayinsa na yayan saurayinta haka ta ringa masa kuka akan yaje ya gayawa Audu karya bari a aura mata wani ba shiba, yana komawa gida kuwa ya sanarwa da Dada tace yayi shiri ya taho Birni dan daman tasan za'ayi haka, duk sanda Audun yaje seta masa zancen ya kamata yasan me suke ciki da Bara'atu se yace mata ba yanzu ba yana so abubuwa su qara daidaitar masa akwai shirye shiryen da yakeyi. Dole Yakubu yayi tattaki ya tafi Kano wanda rabon shi da zuwa tun hutun makaranta wanda daga shi be sake dawowa ba shekaru hudu kenan. Yakubu Kano be zarce ko ina ba se Tsohuwar makarantar Allonsu wato makarantar Gwani Musa dan yasan Audu bashi da wani masauki se can, sedai yayi rashin sa'a Malam ya sanar masa tuni Audu ya bar nan, ya kan dai kawo musu ziyara lokaci lokaci dan ba'afi sati bama yazo kuma Almajirai suna ganinsa a Kasuwar bakin Asibiti idan sunje yawo yace musu yanzu a Goron dutse yake zaune bedai san takamaiman wani guri a can din ba. Yana zaune a bakin Masallaci yana jira ko Allah ze kawo daya daga cikin yaran da sukace sun san inda yake zama a Kasuwa su rakashi sega Hayatu, yaron gidan da Audu ya yiwa aiki wanda Babansu ya kaisu makarantar Boko a lokacin. Cikin mamakin ganin juna suka gaisa yace suje gida a can yaci Abinci yanata kallon Hayatun daya zama kalar yan gayu da gani ya fara jiquwa a Boko. "Tunda ka tafi makarantar kwana shikenab bamu sake haduwa ba shekaru kusan takwas kenan amma banji dadi da Audu yace mun ka bar Boko ba, kaga ni yanzu haka ina shekarar qarshe a Jami'ar ABU zaria ina karantar Engineering da ace ka cigaba kaima yanzun ko baka gama ba kana kan hanya" Hayatun ya fada. Yakubu yayi murmushi kawai amma bece komai ba, duk wanda ze so masa da yayi Boko a bayan kansa ne dan mafarkinsa ne ya zama Alqali tun besan me hakan yake nufi ba. Ganin bazeyi magana ba yasa Hayatu cewa ya tashi suje ya kaishi inda Audun yake dan shi suna haduwa sosai har inda ya kama hayar shago yake zaune a can Goron dutsen ya sani. A kasuwa suka samu Audu yamma tayi anata hada hadar kasuwa dan a sannan ma ake cin kasuwar sosai, kayan yaji yake siyarwa a sannan da sauran kayan qamshi zuwan Yakubu tasa dole ya tattara komai suka tafi masauki. Seda sukayi sallar Magriba da isha, ya rasa ma me ze ajiyewa Yakubun, ya kwaso Wasu yadika dinkakku kala biyu kowanne saiti uku a ajiye masa sannan ya sake dakko Shadda dinkin babbar riga shima guda biyu ya ajiye yana cewa "Na Baballiya ne ba'a gama ba, daman Juma'ar nan nake cewa idan Malam Mudan ya shigo zan hada masa yayo mun gaba dasu kar kaya suyi mun yawa idan na tashi tahowa" "Yanzu dai duk ka ajiye wadannan ka saurari maganar da nazo maka da ita" Yakubu ya fada yaba tattare kayan gefe, Audu ya zauna yana kallonsa se a sannan ma ya lura da cewar Yakubun bashida walwala dukda dai shi daman bame hayaniya bane sosai. A taqaice Yakubu ya bashi Labarin daya gigitashi jin cewar an sakawa Bara'atu rana da wani dan uwanta ya shiga share zuba dukda qofar Shagon a bude take ga iska na busowa amma Audu zufa yakeyi kansa ya shiga sarawa jin ze rasa Bara'atunsa macen daya gama kwallafa duk wani buri na duniya akanta. Shikadai yasan irin tanadin da yakeyi akan auransu shine yanzu Babanta zece ya bawa wani ita. "Shiyasa kullum Dada take maka magana akan kasan me kake ciki saboda gudun haka, ban dama Inna Hajara tana tataka ai kasan tuni Bara'atu ta dade a daki Bilki da suke sa'anni kana gani da ciki yana tsaya mata ai tayi yaya biyu ko uku yanzu tunda dai ga Aisha nan da ciki Auran bana se ita kake so tayita zama har se sanda ka gama shirinka duk sa'annin ta sunyi Aure har an fara zundenta a gari " Yakubu ya fada. Audu dai bece masa komai ba haka suka kwanta amma fa be iya bacci ba, cikin daren ya hada yar jakarshi, Asubar fari suka dauki hanya dan yace baze tsaya ganganci ba dole yaje a san me ake ciki amma da ransa baze bari wani ya auri Bara'atu ba. Bayan dogon tirka tirka da yayyensu daga qarshe suka yarda zasuje tambaya masa Auran Bara'atun, sunje da fari Babanta yaso yayi gardama akan shi ya rigada ya amshi maganar wani ya basu haquri suka taho gida Hashimu har yana Allashi qara ai gara haka, seya koma can Birnin da ya liqe yagani idan ze samu macen da zata aure shi babu wanda yasan saga inda yake kujifa. Kwana biyu tsakani Audu na kwance yana jinya tunda yaji cewar baza'a bashi Bara'atu ba sega dan aike daga gidansu akan Babanta yace ya turo yau a daura musu Aure ashe wai Rijiya ta durfafa dagaske zata fada idan ba'a fasa auranta da wancan ba, harta tsoma qafa daya babanta yaga dai dagaske bata hayyacinta shine yace ya janye amma fa sedai Audu ya turo yau a daura Aure dan muddin aka kai ranar daya saka da wancan tofa sedai ta mutu shine Innarya ta tashi Yayanta ta aikoshi, Audu najin batun ya miqe beyi wata wata ba ya kama hanyar Gona inda su Yakubu suke can suna gyaran kunya kamar wani yaro ya zube yana basu labarin abinda akace. Daga qarshe dai Yaya Baba da wasu Abokanan wasansu biyu ne suka sake zuwa dan Hashimu yace ba inda zeje, an samu Baban Bara'atu ya haqurq da zancen daura aure ranar aka tsaida magana akan rana daya dana Yakubu. Da wannan farin ciki Audu ya koma Kano, dukda ba haka yaso ba. So yayi ace se yayi gida a Kano sannan zeyi aure dan biki yake so yayi irin wanda akeyi A Kano yayiwa Bara'atu lefw na yargata wanda ze zama abin tarihi a garinsu harda kewaye, amma yanzun ma bata baci ba, zeci gaba da qoqari kuma ko ba yanzu ba seya biya bashin duk abinda ya qudurci yi mata. A haka kwanakin Biki sukazo, a zatonsa za'a daura aurene kawai tunda kowa yasan bashida Mahalli yayi qoqari ya siyowa Bara'atu kayayyakin fitar Biki daga Kano aka dinko harda takalma da mayafai kala hudu yayi mata na yan birni. Ana saura kwana hudu daurin Aure ya tafi Bechi bayan yayi sallama da Abokanasa na kasuwa dana unguwa dukya shaida musu zeyi aure, amma biki ba yanzu ba suka hada masa gudummawa kuwa sosai har seda yayi mamaki, koda yake shidin ba daga baya ba gaskiya bashida rowa ko kadan, haka Biki, suna, ta'aziyya sedai idan beji ba suma duk sun masa Alqawarin idan biki ya tashi zasuje tunda yanzu abin yazo a qurarren lokaci basu shiryi tafiyar ba. Ranar Juma'a aka daura Auran, na Yakubu aka fara daurowa da safe a can Rigarsu Balaraba suka dungumo da Amarya da yan uwanta, se bayan sallar Juma'a aka daura na Audu da Bara'atu. Murna kam ba'a cewa komai a gurin Dada da tasha kwalliya cikin kayan da Audu ya dinka mata, haka qannensa Bilki da Aisha sun sha Anko Baballiya kuwa shaddarsa iri daya data angwaye wanda dama Audu ya dinka musu da niyyar suyi fitar bikin Yakubu se gashi abu yazo a daidai. Qarfe tara suna can Majalisa da Abokanai ana ta shaqiyanci sega Baballiya da gudu yake fada musu wai an Kawo Amaryar Yaya Audu. Kowa yayi mamaki dan ko jiya da yaje gurinta seda suka sakeyin maganar tace masa Innarta tace se daga baya zata tare tunda abin yazo babu shiri Babanta kuwa Magriba nayi ya tada ballin se an kaita, an ce masa babu daki yace ta rakuba a na Babarsa da ya san be shirya auran ba yayi haka yan uwa suka rakota ita kam ko a jikinta dan ko cikin Rumbub gidan aka ce ta zauna shiga zatayi tunda dai burinta ya cika ta Auri Audu. A dakin sa aka sauketa da qawayenta da zasu kwana, daren ranar Audu tunanin yanda zeyi kawai yake, da yasan za'ayi haka da ya ququta ko babu dabe itama an tayar mata da daki ko ciki dayane, haka dai gari ya waye, da hantsi yan uwan Balaraba suka gama mata jere tsaf irin na yar gata harda Kumbo nan suka fara shirin tafiya bayan sun qara damqa Amarta a hannun yan uwan Yakubu. Daga bangaren Bara'atu dai babu wanda yazo se qawayenta da suka kwana. A can gidansu ana ta taqaddama tsakanin Babansu da Innarta akan yace ko tabarma baze kai mata ba tunda bata bi abinda yake so ba, ita kuma ta rantse se yayi, da yasan haka ne seya bata lokaci ita da take son auran zatayiwa yarta komai amma yanzu banda kwanuka babu abinda ta tanada dan haka dole ya fito da kayan gado danbaze barwa yarta abin gori ba bayan ba rasa abinda zeyi mata yayi ba gashi tun rana bata daga ba labarin jeran da akeyiwa Balaraba ya fara bazuwa a gari dan itama Babanta Attajirine a rugarsu kuma itace Auta a mata dan haka sun mata bajinta. Hayaniyarsu har dakin Ilu Abokin Audu da suka kwana a gurinsa maqota suke dasu Bara'atun kuma dakinsa jingibe yake da dakin Soron su Bara'atu inda Innar tata da Baba suka shiga wai suna sirri saboda yan biki dake ciki se gashi Audu yaji komai, sulalewa yayi ya tafi cikin garin Kumbotso saboda yafi masa kusa akan yace ze tafi Kano, yasan gurin lokaci lokaci yana zuwa dan har Aboki yake dashi kai tsaye gurinsa ya tafi bayan sun gaisa be bata lokaci ba ya zayyane masa abinda yake tafe dashi na batun kayan daki saboda garinsu Babu Kafinta meyin kayan katako, gadon qarfe kuma a gurinsa shi da yake zaune a birni yake ganin kayan gado da akeyi na Alfarma ya fitar masa yayi. Nura ya kaishi gurin wani Kafinta da ake ji dashi a Kumbotso dan a Kano ya koyo aiki wasu kayan ma daga can yake dakkowa ya kawo. Ya numa masa wani Gado Lamba 1 da Kobud dinsa me biyu ta yan gayu dan harda mudubi a jikin murafenta ga kuma mudubi shima me durowa uku a jiki kayan sunyi kyau gasu Ruwan Hoda irin kalar da Bara'atu take so sedai kudin da aka saka musu a yanayin da yake ciki sun masa yawa ga Katifa da ze siya da pillo, aka tirza aka tisa dakyar dai kaya suka siyu, shima seda Nura yayi masa ciko daga baya zasu warware tunda suna haduwa A Kano, aka loda masa su a A kori kura da dundumemiyar katifa da pillow biyu harda Abin shimfida dana rufa ya kama hanyar gida. Sanda ya dawo yamma tayi rana na gabda faduwa, a waje ya bar masu mota ya shiga ciki nan ya tarar da Dada da yan uwanta da basu wuce ba suna ta kiciniyar kwashe yan kayayyakinta ana shigar dasu dakinsa nasa kuma suna waje da alama dakinta za'a mayar dasu daman ba wani shirgi ne dashi ba Gadon qarfe ne da wata Katifa da yake ta saka ranar canzata tunda ba kullum yake kwana a kai ba se yayi ta mantawa se akwatinsa guda daya. Kunya ta kamashi yanda aka faka kayan a gefe, kenan Dada dakinta zata basu kuma wannan Gadon za'a sakawa Bara'atu "Yawwa ga Audu" Matar Yayan Dada da basu yada zumunchi ba ta fada dan tun safe ake nemansa an rasa shi ga babu waya bare aji inda ya tafi. Dada ta yafa gyale ta yafice shi suka yi soro, Goggo Fadi, Maryo da sauran Maqwafta yan tsogumi da suka baza tabarma, sun gama kallon dakin Balaraba suka fito aka kafa gulmar ana jira aga me za'a sakawa Bara'atu ita kuma, "Koda yake ina dakin ma?" Fadar Goggo Fadi, Maryo ta karkace baki tace "Dukdai qaryar Birnin ta qare, ayita zuwa ana burga a bikin jama'a ga nashi ya tashi ko dakin da za'a ajiye Amarya babu idan da gaske da kudin ai daga tsaida rana yaci a dora ginin Bulon sumunti ma bana qasa ba" suka tafa da matar Hashimu dake kusa da ita. Dada kuwa suna zuwa zaure tace "Ina ka tafi Audu bayan kasan halin da ake ciki babu inda dan uwanka bw zaga a garin nan ba amma ba'a ganka ba Jama'a har ana cewa ka gudu". Dariya ta kwace masa yace "Na gudu kuma Dada naje ina kamar wani mara gaskiya?" "Oho dai duk ba wannan ba, Hasiya tazo ta gaya mun Baban Bara'atu yace bazeyi mata kayan daki ba, da ace mun san da tariyar nan da tuntuni mun fara shiri amma yanzun ma se ayi amfani da abinda Allah ya hore, na bar muku dakina tunda kaga yafi girma ni se na koma na Malam, Babana kuma ya shiga cikinsu Idrisa (Yaran Yaya Baba da suke zama a gidan) kafin muga abinda Allah zeyi, idan an kwana biyu filin can na gefe seka shigo mata dashi ayi bandaki da gurin girki irin na Yayanka kaga shikenan a sannu Allah ze hore duk kuyi muhalli irin wanda kuke buri, wancan gadon naka ma gaskiya Audu ba'a bawa Amarya ba ga Katifa duk Babana yaci qaniyarta idan da sarari ko katifa ce ka siyo da ledar daki a shimfida mata". "mma Dada da baki fita daga dakinki ba wancan dinma ya isa ta lallaba kafin muga abinda Allah zeyi" Audu ya fada, Dada ta juya tana cewa "Kaje dai muga ko katifar da Ledar zasu samu" ya tsayar da ita yana cewa "Shaf na manta da Ledar wlh sedai ko Bilki taje yanzu inda za'a samu, leqa kiga ga kaya nan dai na samu dukda dai nasan basu kai yanda akeyi ba". Dada ta leqa, baki ta saki ganin kaya tuni kuma yara da matan Unguwa da sukazo shiga gidan suka baibaye motar ana kallo dan ba'a taba ganin irinsu a garin ba. "Audu, Kano kaje har ka dawo wannan kaya haka?" Dada ta fada cikin mamaki, Audu yayi murmushi yace "A turo Bilkin ta samo Ledar tunda ita akw fara shimfidawa ko anjima zan miki bayani. Dada ta koma ciki bakinta a washe yaqi rufuwa ta tura masa Bilki. Gidanta ta tafi ta dakko ledar data siya take shirin canza ta dakinta bata rigada ta shimfida ba dama ta bari se an gama hidimar Biki nana da nan aka hadawa Amarya daki ga gado na Alfarma kamar wani gidan zoo haka mata keta leqawa masu gyaran daki na korarsu dan sun hanasu yin aikinsu yanda ya kamata tuni kuma labari yakai wa Innar Bara'atu, ta fashe da kuka tana cewa "Allah na gode maka daka nunawa masu gulma da munafurci qarshensu" tun safen suke qullawa da warewa da yan uwanta akan yanda za'ayi, ta hada dan abinda ya samu, Gadon katako taso tayiwa Bara'atu dan ance Amaryar Yakubu ma shi aka mata amma abinda suka hada baze isa ba kuma wanda za'a tasa ya tafi Kumbotso a yammar shine aiki har sun saddaqar a dauki na qarfen anje shima me siyarwar wai baya nan abin duniya duk ya mata yawa sega wannan labarin farin cikin dukda tasan wata sabuwar gulmar za'a samu ace Miji ne yayi mata ko babu komai sabon salo ne dan babu yarda Miji yaso haka a garin har yayi mata kayan daki. https://chat.whatsapp.com/Hi7n2ddpUxZ24e1tJyREqZ *Assalamualaikum, My name is Maryam hassan, I sell Laces range from 35k to 250k beautiful n classic designs, kids clothes , materials, shadda gezner men materials range from 30k to 120k , women veils , 8k,12k,15k,25k,all available muna bada sari muna maraba da masu siyan daya, muna hada na lefe da kayan barka , location Kano, FREE DELIVERY NATION WIDE BI MA'ANA FA DILIBIRI KYAUTA A TSADAR KUDIN MOTAR NAN YAR UWA ME KIKE JIRA? MAZA KI TUNTUBE MU🌹 just buy what u want n we deliver safely in Sha Allah,,,,,,,, 07088361522* *MATAR MUTUM* *NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER* *MARUBUCIYAR* *WATA KISHIYAR* *RUBUTACCIYAR QADDARAH* *HALIN KISHI* *FIKRA WRITERS ASSOCIATION* *LITTAFIN KUDI NE* *PAY 400 (PROMO PRICE BAYAN KAMMALA FREE PAGES ZE KOMA 500) A ASUSUN* *7061838488* *OPAY DIGITAL SERVICES* *MARYAM FAROUK* OR *0709290797* *ACCESS BANK* *SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488* *IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705* *NAGODE* *FREE PAGE 5* Kafin dare dakin Amarya Bara'atu ya dauki haske bakin yan gulma yayi muqus qiri qiri Goggo Fadi ta kasa boye baqin ciki da wannan abu ta ringa yada magana wai Dada tadai tsananta binciken inda Audu yake samunkudi haka ya za'ayi ace daga fita ya dawo da irin kayan nan waya sani ma ko wasu ya bige ya dakko? Ita dai Dada tun tana mamakin lamarinta harta dena, a zamansu idan aka ce mata wata rana Goggo Fadin zata zama yanda take a yanzu qaryatawa zatayi se gashi da ido ta take gani bawai fada mata akayi ba. Innar Bara'atu ta aiko da kwanuka da tayi tanadi aka jere masu reras tun daga qasa har sama. Tana can bagaren Balaraba tun safe Dada tace suje can da qawayenta suyi wanka suka karya nan suka hade da qawayen Balaraba ana ta raha har dare kafin suka fara shirin tarar Angwaye. A bangaren Balaraban tayi wanka tsaf ta shirya cikin daya daga kayan daya dinko mata daga Kano, Balaraba ta bata Humra ta shafa dan ita dai babu shiri aka hankadota, suna zaune Aisha tazo tace au koma can an gama gyara mata daki suka bar Balaraba da nata qawayen can kuwa se santin daki sukeyi qaunar Audu ta sake linkuwa a zuciyarta ko banza ya fitar da ita kunya ya mata abinda tasan ko Baffabta bazeyi mata kamarsa ba. Se qarfe Goma Aka rako angwaye, Yakubu aka fara rakawa tunda shine babba kuna duk Abokanan nasu daya, bayan barkwanci da abinda aka saba akayi siyan baki sukayi musu yar nasiha da tunasarwa akan aure da qalubalen dake ciki dan gaba daya Abokanan da sukayo rakiya su bakwai mutum daya ne mara aure wasu da yayayensu dan haka sun san yanda lamarin yake nan akayi addu'a suka sallami yammata wadanda zasu tafi gidan Fadima Amaryar da su Balaraban suka kawo garin harta hadu da Yakubu. Daga nan aka raka Audu, basu jima ba nan ma akayi addu'a kowa ya watse suka raka Abokanan qofar gida kamin suka koma ciki, Yakubu ya shige bangarensu bayan yayiwa Audu sallama ya sakace qofa, Audu ya tsaya kawai yana tunani, duk yanda yaci burin ranar auransa gashi bata zo masa a yanda yake mafarki ba. Lissafi yake yanzu Yakubu Asirinsu a rufe suna da komai a bangarensu babu wanda ze san me suke ciki amma shifa? Rufin asirin ma bandakin da yake kusa da ace har yanzu da tsohon suke Amfani da tareren yayi yawa. Haka ya shiga daki jiki babu karsashi sosai ya saka a ransa bazeyi komai ba har se randa ya samu yanda yake so dangane da muhalli. Bara'atu ko harta fara gyangyadi akan sabuwar Katifa daman jiya ba wani baccin kirki sukayi ba kuma sun tashi da wurwuri motsinsa ya farkar da ita ta shiga jan mayafi tana boye fuska. Ya bude musu Kazar da suka shigo da ita dakyar ta iya ci saboda Yunwar da takeji taci kadan tasha ruwa tace ta qoshi. Qofa yaji ana kwankwasawa, seda ya tambayi waye yaji muryar Inna Hasiya, ya bude ta miqo masa wani qaton Flask din ruwan zafi wanda ya siyawa Dada a Kano guda biyu saboda lokacin sanyi dukkansu cike da ruwa tana cewa "Da akwai na sirki nan cikin bambu", ta sake miqo masa wani kantamemen baho irin na wankan Jego tana cewa "Allah ya tashe mu lafiya". Kamar wani munafuki haka ya tattara bahon da fulasan gefe ya ajiye ya kalli Bara'atu data takure a gefen gado kamar jinjirar kyanwa yace "Kiyi shiri ki kwanta dare yayi" Da "toh" ta amsa masa ta miqe amma duk ta diririce ta rasa abinyi fahimtar kamar kunya takeji yasa ya fita ya tsaya daga qofar dakin, yana fita ta bude jakar da aka sako mata yan kayanta. Doguwar rigar yadi me laushi ta ciro da qaramin Hijabi. A gurguje ta shirya, ta ninke wanda ta cire kafin ta haye gado ta duqunqune kamar me bacci daidai nan Audu ya shiga dakin. Shirin baccin shima yayi, ya hau kan gadon yanajin wani banbara kwai wai yau shine gado daya da mace. Dukda yanda yayiwa kansa Alqawarin baze tabata ba har se sunyi kebantaccen guri kamar nasu Yakubu amma ya kasa, cikin tattali da tsantsar So ya mayar da ita tasa, a cikin daren ya taimaka mata ta gyara jikinta kamar yar baby haka ta shige bahon ta gasa jikinta tsaf kamar yanda yayarta ta gaya mata kafin tayi wankan Ibadah dukda kunyar idon Audu haka ta shirya shi kuma ya juye ruwan bokiti ya fita dashi ya dawo ya goge gurin tas kafin ya sirka wani ruwan ya dauko fitila ya wuce bayi. Seda yayi wanka shima ya shirya kafin ya kwanta gefen Bara'atu da tuni bacci ya kwasheta, wani irin farin ciki da annushuwa yake ji, daman haka auran yake? Kai dole ashe Abokanan sa su ringa cewa Aure da dadi. Ya tuna Yakubu ma yana can yana kashe Arna qilan yanzu shi kadai kamar sabon kamu ya fashe da dariya a haka bacci ya dauke shi shima cike da nishadin samu Bara'atun tasa a yanda beyi tsammani ba. Kiran sallar farko ya farka dan ya rigada ya zame musu jiki tun suna qanana da an kira sallah Malam ze tayar dasu suyi nafila kafin lokacin Asuba su fita masallaci shiyasa jikinsu ya saba duk gajiya duk bacci basa tsallake wannan lokacin se sun farka. Motsin saukarsa daga gado ya farkar da Bara'atu wadda itama bata da nauyin bacci. Ta kasa kallonsa yayi murmushi yace "Ki kwanta, kiran farko ne". Seta tashi zaune sosai a kunyace tace "Ai bazan iya komawa baccin ba". Audu ya dakko baho ya zuba ruwan zafi ya sirka, ya sake hada wani a buta kafin ya kalleta yace "Toh gashi nan ko zakiyi amfani" yana fadar haka ya dauki wata butar daya cika da ruwa ya fita daga dakin dan bata sarari. Seda ya kalli bangaren Yakubu da suka garqame qofa Asirinsu a rufe babu wanda yasan halin da suke ciki kafin ya wuce Bandaki ya kama ruwa yana cikin daura Alwala aka haskoshi, ya kare fuskarsa tareda kallon inda hasken yake tahowa saga bangaren Goggo Fadi ne, da alama kuma inda yake take nufowa seya dauke kai yaci gaba da Alwalarsa harta iso kansa tana cewa "Har gabana ya fadi wlh na dauka gamo nayi" banza ya mata ya miqe ta sake cewa "Aa, angwayene har aka iya miqewa da farar Asuba? Kaga bayan gudan namune ya fara alamun fadawa shiyasa naji tsoron karna shiga da duhu na rufta kafin a kawo mun agaji ma qila na nutse ina Amaryar, ta tashi ko se an kawo Agaji?" Tsabar takaici harya tsaya ze bata amsar maganarta ta farko amma qarshen yasa ya wuce ba tareda ya ce mata komai ba, wai a kawo agaji ita dai tana tsufa amma se a hankali. Dakin ya koma lokacin Bara'atu ta fita daga ruwan data ji dadinsa sosai ta daura alwala tana tsaye tana tunanin yanda zatayi da ruwan ya shiga dakin. Kamar dazun ya sake juyewa a Bokiti ya dauraye ya fita dashi ya zubar can bakin rariya ya kife bahon qofar Dada tunda ya gama amfaninsa ya koma dakin, seda yayi Nafila kafin aka kira sallah dan haka ya dauki carbinsa ya fita daidai nan Yakubu ya fito daga bangarensa suka rankaya suka tafi masallacin duk su biyun babu me cewa komai suka zama kamar wasu surukai kowanne fuskar sa cike da annuri irin na sababbi Angwaye. Bayan an Idar da sallah Abokanan su suka tare su da tsokana, nan suka zauna har gari yayi haske kafin suka doshi gida seda sukaje soro kuma suka tsaya saboda jiyo muryoyin mata alamar kowa ya tashi har an fara hidimar gida. Audu ya kalli Yakubu kamar tababbu suka fashe da dariya lokaci daya harda duqewa kowanne shiyasan dalilin dariyarsa. Yakubu ya kalli Audu yace "Bazan iya shiga gidan nan ba kunya nakeji" "Ai gara kai daka sha kunu ka wuce ka sakayo qofa shikenan ka gama abinda zakayi a ciki ka fice ni kuwa komai zanyi akan idon mutane" cewar Audu. Shigowar Aminu ta sakasu shiga gidan dole yana ta tsokanarsu shima, a dakin Dada suka yada zango suka gaisheta kamar yanda suka saba, bakinta kamar ze yage saboda farin ciki, yau din wata ranace ta musamman a gurinta burinta ya cika na ganin Yakubu da Audu a matsayin magidanta sauran mata Autanta Baballiya da tasan ba lallai tayi tsahon ran da zataga wannan lokacin ba. Seda gari ya gama wayewa tangarau kafin kowanne ya koma dakinsa. Bara'atu na kishingide ya shiga ta miqe ya kalleta da murmushi yana cewa "Aa yi kwanciyarki Jaruma" Ta rufe fuska da Hijabin jikinta jin abinda yace wai jaruma, to jarumtar me tayi?" Muryar Inna Hasiya dake magana ta sakashi fita ya dawo ya kwashi fulasan jiya ya kai mata ya tambayi Bara'atu Qaramin fulas din Shayi ko Jug ta nuna masa inda suke ya dauka ya fita ya kaiwa Innan daga can ya wuce dakin Shafi'u inda yayi ajiyar kaya. Inna Hasiya tayi sallama Bara'atu ta amsa kafin ta shiga da fara'a Bara'atu ta miqe ta karbi kayan dake hannunta kafin ta duqa har qasa ta gaidata ta amsa tana tambayarta kwanan baqunta ita dai se murmushi take Innan tace mata "Ga ruwan wanka can a kewaye kije kiyo se ki karya sannu ko" ta fada cikin tausasawa. Kan Bara'atu na qasa tace "Toh Inna, amma Kwandon wankana yana bangaren Yaya Balaraba a can na barshi jiya" Cikin jin dadin Yayar da ta kira Balaraba dashi Inna Hasiya ta fita da zummar karbo mata, a hasashe dai Hafastu tayi dacen surukai masu tarbiyya da kuma kunya. Seda ta dauki abin karin su Yakubu wanda Bilki ta ware kafin ta kai musu ta kuma karbowa Bara'atun kayan wankanta. A bandakin ta tarar da Ruwa har bokiti biyu, tayi wanka me kyau ta gasa jikinta dan ruwan da zafinsu kafin ta fito tana sunne kai dan Inna Hasiya da Bilki na tsakar gidan, dab da zata shiga daki Goggo Fadi ta taho tana cewa "Aa Amarsu wanka akayi?" Bara'atu ta durqushe tana gaisheta ta amsa fuska washe da fara'a, Inna Hasiya da fuskarta ta hade bayan fitowar Goggo Fadin tace "Tashi maza kije ki shirya karki bushe". A dakin bayan ta shafa mai ta ciro wata yaluwar Atamfa me ratsin fari dinkin Tazarce riga ta wuce guiwa an tsagata daga gefe gefe se zani ta saka. Ta bude qaramin kwandon da aka zuba mata kayan kwalliyarta. A qyalle ta zazzaga powder ta shafa ta dakko jagira tana niyyar zanawa se kuma ta dakata. Kwalliyar Balaraba ta jiya ta tuna, daga ita har qaqayenta da sukazo daga ruga babu wadda zakaga dambareriyar kwalliya a fuskarta hoda kawai suka saka se kwalli da man lebe kuma sunyi kyau kodan kasancewar su fararene oho? Dukda cewar a ruga suke amma sun fita ita da nata qawayen wayewa ta ta'allaqa hakan da cewar garinsu Wailari yafi nasu kusada Birni har wasu daga cikinsu sukan kai tallar Nono cikin Kano qila a can suke gano kwalliya irin ta matan Birni wanda daman Audu yana kwatanta mata sam baya son wannan Jagira dasu jambakin da suke cike fuska dashi amma ita a ganinta idan ba tayi haka ba ba kwalliya tayi ba. Zuciyarta ta shawarta mata ta gwada simple kwalliya irin ta Balaraban dan haka ta ajiye jagirar, brush ta dauka ta taje girarta da take a cike me kyakykyawan yanayi kamar an zanata fitina take sakata dambara baqin jagira akai ta qarawa fuskarta da bata haske baqi. Bayan ta taje girar ta saka kwalli a dara daran idonta, bazata iya haqura da jambaki ba dan haka ta shafa kadan ta kawo man lebe me kyalli da Audu ya sako mata a kayan fitar biki ta dora akai ita da kanta ta ringa sakin murmushi ganin yanda tayi kyau, fuskarta har qyalli take cike da Annuri irin na Amare. Ta mayar da kayan kwalliyar ta feshe jikinta da turare kafin ta ware dankwari bayan ta gyara zaman ribbon din data tufke jelar Shukun da aka mata. Daurin Maryam Babangida tayi wannan kam gwance ita a gurin kashe dauri, ta ringa juyi a gaban Kwabarta me mudubi daga sama har qasa tana dariyar yarinta dan tayiwa kanta kyau Addu'a take Audu ya shigo ya ganta taji me zece. Motsin qofa yasa ta nutsu ta shiga neman farin gyalen data fitar tareda kayan. Audu ya shigo da sallama hannunsa riqe da Baqar leda babba kana gani kasan gwangwanaye ne a ciki ya kalli Bara'atu fuskarsa ta sake washewa zuciyarsa tacika da alfaharin kasancewar ta mallakinsa ita kuwa se sunne kai take na kunya. Ya kalli kayan karin da aka ajiye musu alamar bata ci ba yace "Kar abincin ya huce kizo kici" a kunyace ta zauna qasa, ya fitar da gwangwanin Madara Peak dana milo se sukarime iyali kwali biyu ya ajiye mata ya juya da ragowar yana cewa "Bari na kaiwa su Yakubu". Kicibus sukayi da Bilki, ta miqo masa Babban farantin silba da aka dora kwanukan samira guda biyu se ledoji farare da aka qullo Madara, Milo da sugar tace "Gashi farfesun Inna tace nata ne ita kadai ta ci ta shanye romon" ta fada cike da shaqiyanci tana kallon Bara'atun, ta dago kuwa ta maka mata harara, idon Audu ne yasa bata bata amsa ba tunda su din qawayene daman sun saba da caccakar juna. Audu ya karbi Farantin ya ajiye ya kwashe kayan shayin cikin ledar wanda yasan cikin manyan gwana gwanan da yake siyowa Dada duk sanda ze zo aka debo yace "Maida su na taho mana da namu mantasu nayi dakin Shafi'i" "Toh Yaya" Bilkin ta karba ta cigaba da tsayuwa dan so take ya fita ta tsokani qawar tata, karantarta yasa yace mata "Muje toh" ba yanda ta iya ta fita amma dai ze fita ya barsu a gidan yau kam Bara'atu ta banu a gurinta dan dalilin daya sakata kwana a gidan kenan ma. Tare suka karya da Bara'atun dukda yanda take ta noqewa bayan sun gama ya miqe yana cewa "Zanje dakin Shafi'i nayi wanka, idan kina buqatar wani abu ki aiko yara su gaya mun" "A dawo lafiya" ta fada tana miqewa itama bayan ta hada kwanukan da sukaci abinci dasu suka fito a tare bayan ta saka takalmi. Gurin da taga an tara wanke wanke ta ajiye na hannunta Audu kuma ya fita daidai nan Balaraba itama ta fito da nasu kwanukan tasha kwalliya kamar dai Bara'atun, suka sakarwa juna murmushi ta ajiye kayan hannunta kafin suka shiga gaisawa. Dakin Dada suka nufa tare suka tarar suma sun gama karyawa kenan Bilki na tattare guri Baballiya na kwance kamar gawar sababi yana tabara ko kunya bayaji waishi Auta. Inna Hasiya ta dana masa duka tana cewa "Dallah tashi ka basu guri su zauna", Dada da bakinta yaqi rufuwa se sannu take musu suka zauna kowacce na sunne kai suka shiga gaishe su. A mutunce suka amsa, tamkar ba surukai ba haka Dadan ta ringa jansu da hira suna amsa mata daddaya cike da kunya Inna Hasiya ta fice tsakar gida se Bilki dake tsokanarsu Dada tana tare musu. "Kuje ki rakasu su gaida Goggonku" Dadan ta fadawa Bilki, ta miqe suka bi bayanta suna fita ta dafa Bara'atu tana cewa "Qawata ya kikaji Auran?" Inna Hasiya ta rafka salati tana cewa "Kin banu Bilki wannan fitsara har ina sirrin Yayan naki kike kiji kome? To bari Audun yazo daidai yake dake". Bilki ta ringa dariya su Bara'atu dai se murmushi da haka suka qarasa dakin Goggo Fadi sun tarar da ita da Aminu wanda tun Asuba daya shigo gidan yana can kome suke tattaunawa se Allah. Cike da girmamawa suka gaidata ta amsa itama basu jima ba suka basu guri, bayan sun fito Bara'atu ta kalli Balaraba tace "Muje kiga dakina nima" suka rankaya Bilki ta wuce gurin Inna Hasiya data kirata. A dakin Balaraba ta ringa santin kayan Bara'atu, hira suka shiga tabawa Bilki ta dawo nan ta tasasu gaba da tsokana suka ringa hira gwanin dadi kafin qawayen Bara'atu suka fara zuwa yan kwadayin ragowar kazar Amarya. Kazar ta basu Balaraba ma taje ta dakko musu sauran tata dan ita qawayenta tasan yanzu sun kai gida tunda Asubanci me motar da ze mayar dasu yace zasuyi ze wuce Kano dakko kaya. Wuni guda tsakanin bangaren Balaraba da dakin Bara'atu sukayi shi, Inna Hasiya kuwa bata gaji da hidimta musu ba wanke wanke da shara babu yanda basuyi ta basu ba taqi tace su huta. Haka aka ci sati Angwaye da Amare na tsinkar furen qauna hankali kwance. Dukkaninsu sunyi bulbul abinsu kana kallonsu kasan basu da damuwa banda ma matsalar rashin sirri da take hana Audu yanda yaga dama wannan yasa ya quduri a ransa dole idan ya koma Kano kafin ya dawo ya gyara musu bangare a katange kamar na Yakubu dan gaskiya wannan zaman na kwarar sa. Seda akayi sati hudu da biki kafin hankalinsa ya fara komawa Kano dalilin yan kudaden hannunsa sunyi qasa ga hidimar yauda kullum a wannan rutsin kuma ya sake fahimtar cewar a yanzu ne ma yake da dalilin tashi tsaye ya nemi kudi ka'in da na'in kodan Iyalan da suka fara ajiyewa. Ya fara shirin tafiya, da daddaren ranar ana saura kwana uku ya koma Kano ya samu Dada da zancen ya kamata Yakubu ya koma yaci gaba da karatunsa. "Dada yanzun nauyi ya hau kanmu, bazan so mu qare rayuwarmu cikin wahala tamkar ta mahaifinmu da sauran yan uwanmu ba kina kallo dai yanda suke fama basu da wata tartibiyar madogara se Noman da sukeyi. Karatun Yakubu nada muhimmanci na farko Burinsa ne na biyu kuma idan ya kammala ze samu madafar da ze riqe kansa tunda shi ya gaza maida hankali akan Kasuwanci kamar ni kuma gaskiya bazan zuba ido ina kallo da quruciyarsa aikin wahala ya kashe shi ba dan haka kiyi masa magana ya bar duk wani abu daya dauka yazo mu koma Kano ya zana jarabawa yaci gaba da karatunsa". Dada tayi shiru tana nazarin maganganun Audu tabbas gaskiya ya fada yanzun nauyi ze qarar musu kuma baze yuwu ace shi kadai zeci gaba da daukar ragamar gidan gaba daya ba. Ta numfasa tace "Zanyi masa magana babu damuwa da yardar Allah". Hakan kuwa akayi Dada tayiwa Yakubu magana take ya nuna rashin Amincewa da maganar a cewarsa idan duk suka tafi Birni waye ze ringa Kula da Dadan da yaran mutane da suka Auro? Dada tayi dariya tace "Kai dai kace bazaka iya tafiya kabar matar kaba" Yakubu ya sunkuyar dakai kamar ya nutse dan kunya ya kasa cewa komai se Dada ce taci gaba da cewa "Kodan saboda su karatun naka nada muhimmanci Yakubu a yanda Audu yayi mun bayani. Idan ka duba kwanannan nauyi ze qarar mana, badi iyanzu idan muna da rai kun dauki Yayanku akwai buqatu marasa yankewa da zasu qaru kaga dan uwanka yana matuqar qoqarinsa akan mu, idan ka gama Karatun zaka samu madogara tunda ga Fa'izu (yaron me gari da shima ya kaishi Kano yayi karatu) kaga yanzu maganar da akeyi yayi hanyar da Gwamnati zata gina mana Firamare a nan qauyan dole za'a nemi malamai, kaga ko wannan aikin ka samu tunda ance biya akeyi ai an samu madogara seka hada da yar sana'ar da kakeyi Asiri ze rufu kodan saboda dan uwanka ka daure ka cika burinka wanda har ya fika damuwa da hakan". Haka dai Dada da Audu sukayi nasarar tausarsa ya yarda ze koma Kano ya ci gaba da karatunsa, tafiyar Yakubu data taso ya saka Audu qara kwankin tafiyarsa dan su shirya a tsanake. Ana saura kwanaki biyu su tafi da daddare Hashimu da yayi balaguro tun daurin auran su Audu da kwana hudu ya dawo gari. A daren ranar suna zaune a dakin Dada Malam, dan gurin Mairo ne yayi kiransu inji Baba Hashimu. Audu da Yakubu ne sukaje, yana zaune tareda Goggo Fadi suna hira gabansu Kaza ce gasashshiya suna ci Audu da Yakubun suka samu guri suka zauna suka gaishe su. Hashimu ya cire tsinken da yake sakace dashi ya kalli Audu yace "Naji labarin kuna shirin Tafiya Birni shine nace kafin ku wuce ya kamata mu zauna muyi magana, so nake yi ku siyar mun da barin gonarku ya zama mallakina tunda dai ba nomawa kukeyi ba, abincin ma idan an baku saidawa kuke kun koma cin kalar na Birni se shinkafa da Taliya ko?" Ya qarashe cikin sigar tambaya. https://chat.whatsapp.com/Hi7n2ddpUxZ24e1tJyREqZ *MATAR MUTUM* *NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER* *MARUBUCIYAR* *WATA KISHIYAR* *RUBUTACCIYAR QADDARAH* *HALIN KISHI* *FIKRA WRITERS ASSOCIATION* *LITTAFIN KUDI NE* *PAY 400 (PROMO PRICE BAYAN KAMMALA FREE PAGES ZE KOMA 500) A ASUSUN* *7061838488* *OPAY DIGITAL SERVICES* *MARYAM FAROUK* OR *0709290797* *ACCESS BANK* *SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488* *IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705* *NAGODE* *FREE PAGE 6* Yakubu ya nisa yace "Ban fahimce ka ba Yaya, kaji labarin muna somu siyar da gonar ne ko yaya?" "Ko daya, ina dai so ne nasiya kuma a shirye nake ko nawa kukayi mata kudi zan biya" Hashimun ya sake fada, Yakubi ze sake magana Audu ya tareshi yace "Shikenan zamu siyar, Allahya kaimu safiya se a kira su Malam Audi suyi mata daraja daga nan se muga yanda za'ayi" yana gama fadar haka ya miqe dole Yakubu ya bishi ze fara masifa Audu yayi masa alamar da yayi shiru, daga cikin dakin suka jiyo dariyar Goggo Fadi Hashimu kuma yana cewa "Sunyi kyan kai dan ko basu siyar munta arziqi ba to zasuyi Asararta a banza" Wannan magana ta daurewa Yakubu kai ya kasa fassara abinda yake nufi a haka suka koma dakin Dada take Audu ya gaya masa dalilin kiran, Dada tayi shiru kafin tace "To me kuka ce masa?" "Nace masa zamu siyar da safe zan nemo au Malam Audi ayi mata kudi" "Amma meyasa Hashimu duk gonakin da suke garin nan se tamu zece ze siya kuma..." "Dada, dan Allah kar a tada maganar nan, gona yake so ko za'a siyar masa daga nan a raba kudin kowa ya kama abinda zeyida kasonsa" Audu ya katse Dadan se sannan Yakubu yayi magana yace "Wannan ma ai maganar banza ce, ta yaya zamu siyar da abinda ita kadai muka mallaka ciki muke ci muke sha? Kai me yasa baka lissafi ne kawai abinda kwakwalwarka ta gaya maka kakeyi?" "Kadaiji da kunnenka abinda ya fada shawara ta rage taka ko ka bari a karbi kudin ko kuma ta salwanta a banza kaga munyi asara da hujja" Audun ya fada yana miqewa yayi musu sallama ya fice daga dakin yana tafe yana tuna Gonar Baffaye wani tsohon Abokin Malam ne da gonarsa take gabas da tasu, bara waccen shekaru uku kenan Hashimun ya nemi ya siyar masa dan harkoki suna ta bude masa babu kuma wanda zece ga inda yake samun kudi Baffayen yaqi, daminar Bana yayi shuka lafiya har ta fara yabanya haka kawai aka wayi gari komai ya bushe shekarar haka ta qare ko Kara be cire a gonar zancen da akeyi yanzu gonar ta zama tamkar kufai, aciki ne ma ake zaton Gwamnati zatayi ginin firamaren da za'a bude wadda me gari ya bashi shawarar ya bayar dan abinda za'a biyashi ya nemi wata ko qarama ce ya siya. A labarin daya ringa kewaya gari ance anga Hashimu yana zagaya gonar da dare bayan sunyi zancen cinikin Baffaye yaqi wanda ba'a kwana biyu ba wannan ibtila'i ya fadawa Baffaye, bawai ya yarda da abinda aka fada ba amma kalaman Hashimun na dazu sun saka qara masa hujja nacewar ze iya yi musu mugunta a kan Gonar. Ransa fal da baqin cikin hanyar da yan uwan nasu suka dauka bayan gushewar Malam da bashida burin daya wuce ganin sun hada kansu amma abu ya gagara, haka ya kwana da takaicin abin a zuciyarsa washe gari kuwa qarfe goma na safe gaba dayansu suka hallara yan dakin Goggo Fadi dana dakinsu. An kirawo Dillai a gaban kowa sukayi wa gonar kudi da daraja abinda ya qara qonawa Hashimu rai dan kafin zuwansu seda ya samu daya daga ciki har cin hanci ya bashi akan su kassara farashin gonar, haka ya tishe kudin cas ya basu abinda ya qara bawa kowa mamaki su kam sun rasa a ina Hashimu yake samun kudi haka. Audu da yan uwansa suka qule a dakin Dada, Yakubu nata fada akan abinda ya faru, Bilki da Aisha ma dai sunbi sahun Audu nayin amanna da siyar da gonar dan har Bilki na cewa daman taji a bakin Mijinta Hashimun na fadar koda tsiya se ya mallakin barin gonarsu ya zama nasa to gara da kayi ta arziqi shikenan. Audu ya kalli Dada yace "Yanzu ya za'ayi da kudin nan?" "Ni a ganina a nemi wata gonar a siya idan yaso ko haya ce a bayar ko kuma a nemi ma'aikata su ringa nomawa ana biyan su lada" Dada ta bada shawararta, Audu yayi shiru kafin ya kalli Yakubu yace "Kai kuma ya kake gani?" "Daka zarce hukuncin a siyar da baka shirya abinda za'ayi da kudin ba?" Yakubu ya fada a cikin fada Dada ta daga masa hannu tana cewa "Bana son haka, karka kuskura ka saka wannan abin a ranka balle har sabano ya shiga tsakaninka da dan uwanka. Kaifa ka gaya mun abinda kukaji ya fada jiya, kasan hatsabibancin Hashimu, ladan hayar da suke bamu kana kallo lalataccen da kwari suka taba ake tattarowa a bamu duk dan a zauna lafiya yasa ban taba magana ba yanzun daya nuna yana so gara a bashi dan qarshe zamu iya rasata baki daya". Yakubu be iya cewa komai ba tunda Dada ta goyi bayan Audu, qarshe bisa shawarar Audu da Bilki suka yanke cewar za'a tada gini Jikin katanga a fitar da qofar shago ta waje da kuma ta cikin gidan inda zasu zuba duk wasu abubuwan buqata da suke wahala a Qauyen, mutum daya ne yake shiga Kano yayo sarin kaya shima se yafi wata beje ba dan haka abubuwan buqatu da yawa sedai a haqura ayi amfani da wanda ya samu sannan Bilki tace tana so Audun ya ringa aiko mata da zannuwa da sauran kayan kwalliyar Mata daga Kano tana siyarwa dan shima Mace daya ke wannan sana'ar Asabe Dillaliya, sunyi na'am da shawarar, aka kasafta kudin kowa aka fidda masa rabonsa kafin suka sake hadesu Audu ya adanasu cikin kayan tafiyarsa. Cikin abinda ya masa saura a hannu ya tafi Kumbotso dan yiwo musu siyayyar abubuwan amfani, dayace Yakubu yazo su tafi qi yayi dan har sannan a qule yake dashi, yasa an siyar da Gona kuma ba'a siyi wata ba an tattare kudi wai za'a juya su. Se ya liqis ya dawo Bechi niqi niqi da siyayyar da yayiwo, a qofar gidan ya tarar da magina sun jiqa gefe ga bulo da alama gini ake a cikin gidan. Ne damu dasu ba yayi musu sallama ya shige sedai abinda ya gani ya sakashi dakatawa tareda tsayar da yaran da suka tayashi daukar kaya. Hashimu na tsaye da Malam Sha'aibu magino suna magana, ga katanga nan da aka fara dorawa daga bakin qofar soron har jikin katangar baya ta gidan da Alama an tasarma raba gidan ne. Bawai Rabawar ne ya bashi mamaki ba Aa yanda aka tada katangar idan aka gine ze zaman su basu da hanyar shiga bangarensu kenan ko kuwa Katanga zasu ringa tsallakawa oho. Aminu ya fito daga dakin Goggo Fadi kana ganinsa kasan a fusace yake beko lura da Audu ba ya kalli Hashimu yana cewa "Tun wuri ka dakatar da wannan ginin wai me yasa duk abinda ze janyo tashin hankali a gidan nan shi kakeyi? Yanzu ta ina kake so su ringa shiga barayinsu?" Cikin ko in kula Hashimun yace masa "Ko su fasa wata qofar ko su siyi fukafukai duk matsalarsu ce gida ne dole a raba kuma a sannu yanda na raba su da gonar shima gidan seya gagre su zama sun barshi". Zuciyar Audu ta harzuqa amma ya daure bece komai ba ya wuce da qafa ya tunkude bulon da basu gama kamawa ba aiki Yar katangar da ta fara tsayi ta ruguje ya shige abinsa yaran da sukayo masa dako suka bishi, a fusace Hashimu yabi bayansa har qofar dakin Dada seda Audun ya dire kayan hannunsa kafin ya kalli Hashimu dake numfarfashi ze fara bala'i yace "Idan ka manta bari na tuna maka soron a cikin rabon gadon mu yake, saboda idan muka ja katanga baku da ta inda zaku fasawa Mahaifiyarku qofar fita shiyasa muka barshi amma da tuni na dade da sakawa an toshe qofa mun canza mata fasali" yana gama fadar haka ya shige ciki ya bar Hashimu da yayi shiru yana tunani, tabbas gaskiya Audun ya fada Soron rabonsu ne tsabar shaidan da yake masa kururuwa yasa ya manta ganin yafi kusa da bangarensu idan kuma suka toshe din da gaske basu da kusurwar da zasu bullawa Goggo qofa dan ta bamgarensu sun fisu yawan dakuna haka zakila Kudun su da yamma jingine suke da gidaje babu damar su fasa qofa sabanin su Audu da suke ta gabashin gidan inda fili yafi yawa kuma babu gini jikin katangar ta bangaren. Cike da borin kunya ya tafi yana cewa "To se kuzo kuyiwa soron kudi a biyaku dan babu fashi gidan nan se an raba shi". A cikin daki kuwa Dada ta girgiza kai mamakin lamarin Goggo Fadi da yaranta ya kasa sakinta a kullum sabon abu suke tsiro dashi to wai me yasa tun Malam na raye basu bayyana halinsu a fili ba se yanzu daya kau? A daren Audu da Yakubu suka tara matansu nan dakin Dada suka qara jan kunnensu tare dukda basu da matsala, lafiya lau suke zaune Dada kuwa a yaya ta daukesu ba surukai ba idan kaga yanda suke gwanin sha'awa. Kamar yanda suka fara girki daya sukeyi kuma a hakan zasu cigaba, Sadiya yar wajen Bilki zata ringa taya Balaraba kwana, da farko Innar Bara'atu tace zata turo mata qanwarta se daga baya kuma tace Babansu ya hana. Daga qarshe Abdullahi mutumin Audu dan gurin Aminu aka bata dukda Goggo Fadi da Hashimu basu so ba, da yake shima Aminun tsayayye ne yayi musu fes yace dan sa ne kuma ya bawa Audu halak malak ko bayan ransa yayi Tijara kafin magana ta Mutu Abdullahi ya dawo dakin Bara'atu lokacin shekarunsa hudu a duniya. Audu da Yakubu sun dawo Kano cike da kewar Matayensu kowanne yana jin jiki haka suka duqufa abinda ya maido su, sunyi register rubuta jarabawar kammala Sakandire da suka ci sa'a daidai lokacin an fara kwana kadan suka rubuta cikin yardar Allah sakamako ya fito dukkaninsu sun samu sakamako me kyau. Yakubu ne ya tirsasa masa kan cewar seya rubuta dukda yace shi ba karatu ze ci gaba ba amma idan ya ajiye takaddar wata rana zatayi masa Rana. Kudin da suka zo dashi Audu ya zuba suka fadada kasuwancinsu, yayi sarin kaya masu yawa ya aika dasu Bechi an bude shago wanda dama sun bar alhakin aikin a hannun Mijin Bilki Baballiya ne yake zama kuma ba qaramin ciniki akeyi ba dan kusan komai na buqata an kai harda ma sababbin abubuwa a gurin mutanen qauyen ba'a rufa sati biyu is anyi sabon sari an aika idan suka aiko da cinikin da akayi ta hannun Qanin Hayatu Mijin Bilki da yake jan motar kaya yanzun. Tareda Yakubu suke fita kasuwa, tuni kuma an tayar da ginin filin da Audu ya siya a nan Goron dutse inda yake zama, filin nada girma babu laifi dan haka aka rabashi biyu shida Yakubu kamar yanda daman ya tsara. Gini aka tada daki ciki da falo kowanne se safaya guda daya da kuma kitchen da bandaki ginin bulo, idan ka shigo soron gidan daya ne sannan zaka tarar da qofofi guda biyu na shiga kowanne bangare. Yakubu ya dage akan Audu ya maida hankali gurin gyara nasa bangaren dan shi fa bega abinda ze rabo shi da Bechi ba, koda ya fara Karatu ze ringa tafiya duk hutu irin yanda ya ringayi lokacin yana makarantar kwana dan baze yuwu su tattaro su dawo Kano su bar Dada ita kadai a can ba ko bayan haka sam shi bashida sha'aqar zaman Kano ma baki daya haka dai aka ci gaba da rarrafa rayuwa watansu uku a Kano kafin sukaje ganin Matansu niqi niqi da abin Arziqi dan a watannin ba qaramin Alkhairi aka samu da kudin da aka juya ba ga can Shago da Sana'ar Bilki ma se sambarka. Sun tarar da matansu da Dadarsu lafiya sumul ga qarin abin farin ciki Balaraba nada shigar ciki, wannan abu yayi wa kowa dadi, satin Audu biyu ya koma ya bar Yakubu dayace seya qara hutawa shi kuwa daya baro dukiya be bar me juya masa ba dole ya koma, kwanansa biyu da komawar shima saqo ya riskeshi wanda yakeyiwa Yakubu cuku cukun samun gurbin karatu ya aiko masa da cewar an samu dan haka Yakubu ya shirya ya tafi Domin har Samista ta fara nisa acan makarantar dole Audu ya juya Bechi. Dan qaramin yaqi sukayi da Yakubu sanda Audu ya gama wassafa masa abinda yake faruwa. Ya rasa me zeyi, ashe wai Audu can Jami'ar Ikko ya nemawa Yakubu gurbin karatun Shari'a ta hannun Tsohon Abokinsu na Magashi wato Hayatu duk a tunanin Yakubu anan kwalejin Shari'a da aka bude a Kano ze nemar masa Gurbin ashe shine dalilin daya sa be gaya masa komai ba akan zancen makarantar. Yakubu yace ba zeje ba, ya za'ayi ma ya tsallake ya tafi har Kudu da sunan karatu? Idan jami'ar ce baga ta nan a Zari'a ba tunda ta kano basu fara karatun shari'a ba a sannan ko ba wannan bama shi karatun Jami'a ya masa girma a lokacin baze iya ba, seda Dada tayi masa wuji wuji sanna ya haqura. "Me yasa Yakubu duk qoqarin da dan uwanka yake akanka baka gani ko da yaushe cikin gwasaleshi kakeyi? So kakeyi kuma ku zama kamar su ace babi jituwa bazaku hada kai da baki shawararku ta zama daya ba? Idan kuna haka suma qannenku abinda zasu dauka kenan ni kuwa fatana ko bayan raina ace duk abinda zaku zartar a tsakaninku se kun shawarci juna kuma babu babba ko yaro in har daya ya bada shaqara me kyau da zata amfane ku ku karba ku zartar amma gashi kai da kake babba kai ne duk abinda aka kawo se kayi Adawa da hakan bana so bana jin dadi ka dena hakan" Dada ta fada masa. Yakubu yayi shiru, har ga Allah baya jin dadin yanda Dadan take goyon bayan duk wani hukunci da Audu yake zartarwa dukda dai ba abu mara kyau yakeyi ba amma yin hakan ze saka ya dauka cewar komai yayi daidai ne ba kuma ze ringa duba muraden waninsa ba in har abinda zuciyarsa ta raya masa kawai shine daidai. A komai na rayuwa shawara nada kyau amma ya za'ayi ya ringa zartar musu da hukunci kamar wasu Yayansa ai ko Baballiya beci ace Audu ya turashi wani gari can karatu ba tareda son ransa ba balle shi da girmansa harda iyali ya ajiye ayi masa wannan abun yanzu haka ze tattara ya tafi ya bar yar mutane har tsayin wane lokaci ze dauka kafin yazo? Nan da Kano ma suna daukar watanni inaga Ikko da tafiyar kwanaki ce kafin kaje, anan cikin qauyensu da akwai Abokanansu biyu da suka tafi neman Arziqi shekara uku kenan zuwansu daya gida kuma sun basu labarin yanda Kudu take tayaya ma ze iya zama a can fisabilillahi amma ya ya iya? Yanda ran Dada ya baci yasan ko yayi mata bayani ba lallai ta fuskanta a fuskar salama ba. Haka ya fara shirin tafiyar jiki a salube danma Balaraba ta dage da qarfafa masa guiwa tana gaya masa duk saboda ita da abinda zata haifa zeyi wata rana kuma komai ze zama labari a sannu idan yaje garin ma ya gane kan komai zasu iya tafiya tare dan ita akwai Yayanta da yake kai Shanu can Kudun saboda yawan zuwan da yakeyi ya kai matarsa daya can take zaune wannan yasa hankalinsa ya dan kwanta amma idan ya tuna ze tafi ya barta da ciki qila har se abinda zata haifa ya fara zama ko rarrafe ze zo ya ganshi duk se yaji abin ya qara fita a kansa. Haka ya shirya, duk wani abu da ze iya nema na dangin abincin da ba lallai ya samu can ba Dada da Balaraba sun hada masa. Harda dambun nama Dada tayi masa, gasu Yaji, quli quli harda Alkaki Audu ya ringa dariya wai kamar me tafiya qasar waje. Randa zasu tafi Kano Balaraba ta kasa daurewa ta ringa kuka duk ta qara sanyaya masa jiki dakyar ya iya tafiya Goggo Fadi da yan fadarta suka ringa yadawa Dada magana wai ta watsa yara sun tafi Bariki ga Yaran mutane sun auro sun ajiye wannan ai ba daidai bane iya dai bata kulasu ba suka gama jajanta tafiyar su Audun kafin kowa ya dauki dangana sukaci gaba da rayuwa yanda suka saba. Audu kuwa seda ya raka Yakubu har Ikko, tafiya ce kamar ta yada shege musamman su da basu taba zuwa ba a hakan ma wai dan mota me kyau suka hau basu bi motar Arha wadda ake loda mutane ba. Satinsa daya ya juyo bayan Yakubu ya samu gurin zama ya gama duk wasu abubuwa har ya fara shiga aji. A dan tsukin Seda Audu ya leqa kasuwa ya gano sabgogin arziqi aiko ya qyarawa Yakubu da zarar ya gama gane kan gari ya shiga kasuwar Hayatu ze taimaka masa ya dubo musu abubuwan da ake buqata a Arewa da suke sauqi acan. Ya dawo Kano cike da kewar Dan uwansa ya kuma cigaba da kasuwancinsa ka'in da na'in, sabanin da da yake share watanni yanzu wata biyu yakeyi yaje Bechi wani lokacin ma wata daya da kadan zeje ya kwana uku ko hudu ya juyo haka ze musu siyayya kuma ya hada harda yan uwansa dukda barakar da suka samu be fasa yi musu ba suma kuma babu kunya basu qi karba ba. Balaraba nata rainon cikinta daya fito sosai yana wata na bakwai sannan. Ba yanda Audu beyi akan suje Kumbotso Asibiti ba tunda su nan babu amma Dada taqi a cewarta Ahalinsu kaf babu wadda ta taba zuwa wani Asibiti kuma lafiya lau suke rainon ciki su haihu duk wani taimako kuma daya kamata tana bawa Balaraban shima zaman Birni yasa har yake wani zancen Asibiti banda haka a garin kaf wayaga tana zuwa wani Asibiti banda Matar Shafi'i Hedimastan primary su Baballiya da aka bude. Har fushi yayi amma Dada taqi saurararsa, ya samu Balaraban akan ta shirya a sace ze kaita dan shi fa ya daukarwa Yakubu Alqawarin kula masa da iyalinsa ba kuma yason kowanne tsautsayi ya gifta wani abu ya same su ma se Balaraba tayi dariya tace "Bana jin komai Yaya Audu lafiyata qalau kamar yanda Dada ta fada in sha Allahu zan haihu lafiya base munje Asibiti ba daga can Rugar mu ma Innata tana yomun aiken saiwoyi babu wata damuwa da yardar Allah". Badan yaso ba ya barta, watan Haihuwar Balaraba na tsayawa ya dawo Bechi yanda kasan shi za'ayiwa Haihuwar, kwanan sa biyu da dawowa Balaraba ta fara Naquda cikin dare har garin Allah ya waye bata haihu ba duk irin taimakon da Dada da Goggo Fadi tareda Unguwar zoman da suka kirawo suka baya amma abu ya gagara, haka ta sake wuni sur cikin ciwo kuma abin takaici sun hana akaita Asibiti acewarsu dama haihuwar fari akan dade, hankalin Audu ya tashi ganin har duhun Magriba ya fara kawo kai amma Balarana shiru zuwa sannan kuwa ko baa fada ba ka kalleta kasan qarfinta ya fara qarewa. Beyi shawara da kowa ba ya fita neman motar da zata kaisu Kumbotso, duk masu motocin daukar kaya na garin abin takaici kamar hadin baki duk gurin wanda yaje ae yace masa bashi da Mai yau ko aiki be fota ba. Har gurin Alhaji Magaji yaje wanda a lokacin shi kadai yake da motar hawa a garin amma be samu alfarmar ya taimaka masa su kai Balaraban Asibiti ba ga duhu yayi dan tuni anyi magriba Isha ake shirin yi. Zuciyarsa ta quntata ya rasa abinda zeyi, be taba jin burin mallakar abin hawa na irin na wannan dare. Hankalinsa be qara tashi ba seda Bara'atu ta fito tana kuka hankali a mugun tashe take sanar masa Jikin Balaraban ya qara rikicewa har ta fara zubda jini gasu Dada can duk sun rude suna salati. Suna tsaye nan cikin rashin mafita kamar daga sama sega Kasim, Abokinsa ne amma irin wanda alaqar bata da qarfi sosai. Audu ya sauke ajiyar zuciya yana yiwa ubangiji godiya daya kawo masa Kasim din. Alfarmar Baburinsa ya nema ya bashi haka aka cocciba Balaraba da sam bata cikin hayyacinta Dada ta hau bayanta suka sakata a tsakiya suka tafi Kumbotso aiko wannan abu ya qara hura wutar gori Goggo Fadi ta ringa masifa tana fadar maganganu cewar Dada batayi kara ba. Ita kuwa Dadan tsabar rudu da tashin hankali yasa sam bata san sanda ta haye mashin dinba dan gani takeyi idan wani abu ya samu Balaraba itace sila tunda babu yanda Audu beyi suje Asibiti ba tun gari nada haske. Assalamualaikum, My name is Maryam hassan, I sell Laces range from 35k to 250k beautiful n classic designs, kids clothes , materials, shadda gezner men materials range from 30k to 120k , women veils , 8k,12k,15k,25k,all available muna bada sari muna maraba da masu siyan daya, muna hada na lefe da kayan barka , location Kano, FREE DELIVERY NATION WIDE🌹KWARAI KUWA DILIBIRI KYAUTA FA just buy what u want n we deliver safely in Sha Allah,,,,,,,, 07088361522 *MATAR MUTUM* *NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER* *MARUBUCIYAR* *WATA KISHIYAR* *RUBUTACCIYAR QADDARAH* *HALIN KISHI* *FIKRA WRITERS ASSOCIATION* *LITTAFIN KUDI NE* *PAY 400 (PROMO PRICE BAYAN KAMMALA FREE PAGES ZE KOMA 500) A ASUSUN* *7061838488* *OPAY DIGITAL SERVICES* *MARYAM FAROUK* OR *0709290797* *ACCESS BANK* *SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488* *IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705* *NAGODE* *FREE PAGE 7* Cikin hukuncin Allah isarsu Asibitin babu jimawa Balaraba ta sauka sedai yar tazo babu rai wanda ko ba'a fada musu ba sun san wahalar data sha a ciki ce tayi Ajalinta ita kanta Balaraban babu yanda take hankulansu basu dan kwanta ba seda Likita ya tabbatar musu da Balaraba zata samu lafiya da yardar Allah. A nan cikin Asibitin suka kwana, da sassafe Audu ya tafi Bechi tareda gawar yarinyar can aka shiryata akayi jana'iza kafin Bilki ta hada duk abinda Balaraba zata iya buqata suka juya Kumbotso tareda Bara'atu da Mariya matar Aminu se Maimuna Amaryar Hashimu da itama tana hulda dasu Balaraban dukda mijinta baya so. Goggo Fadi data kwafe tun jiya cewa tayi ba zataje ba dan haka sula tafi. Seda Balaraba ta kwana uku Asibiti kafin aka sallamota dan ba qaramin jiki taji ba. Ta rame fiyau se haske data qara kamar mara jini duk wanda ya ganta seya tausaya mata ga rashin jaririyarta ga Yakubu baya kusa yana can nisan duniya bema san abinda ya wakana ba. Haka sukayi ta tausarta harta saki zuciyarta, kwananta Ashirin da haihuwa Dada tayi mata izinin tafiya can Rugarsu dukda yan uwanta sunzo sun dubata har sun bar mata yayarta daya ita ke kula da ita amma Dadan tace taje ta huta kota qara rage kewa a sannan tuni Audu ya koma Kano ya kuma aikawa da Yakubu wasiqa ya sanar masa da abinda ya faru. Haka aka cigaba da lallaba rayuwa, Su Yakubu sun samu hutun shekarar farko a karatunsu ya taho gida cike da kewar matarsa da kuma Alhinin yarsa daya rasa. Tsaraba niqi niqi yayo daga ikko, kowa seda yasan da dawowarsa domin dangi kaf kowanne gida seda abin Alkhairinsa ya leqa. Yaya Baba da kansa yake cewa "Tabbas yaran nan sun san Alkhairi, ka dubi duk abinda mukeyi musu amma basu riqe mu ba ba kuma su canza daga kyautatawar da sukeyi mana ba" Hashimu da yayi maganar a gabansa yayi tsaki zuciyarsa tayi baqi, haka siddan shedan yake hura tsanar su Audu a zuciyarsa yana qissima masa cewar duk abinda suke samu shida yan uwansa ya kamata ace sun same shi amam basu Audun ba. Shidin mutum ne me shige shigen zuwa gurin Malamai, a yawonsa aka binciko masa cewar Yayan Dadan suna da taurarin arziqi, yabi malamai sun fi nawa amma kamar hadin baki duk inda yaje se a ce masa su dun zasu daukaka irin daukakar da beyi zato ba, da yake yayi ammana da zancen Malaman nasa shikenan qyashi da hassada ya darsu a ransa ya kuma dage ta duk wata hanya dayake tunanin daukakar zata zo musu yake qoqarin tosheta sedai rashin sani irin nasa fadar Malaman tsibbunsa ba gaskiya bace, idan kuma anyi katari sun canki daidai to wayo ko dabararsa basu isa su canza abinda ubangiji ya qaddara faruwar iya wuya se abinda ubangiji ya qaddara ya faru. Cikin tsarabar da Yakubu yayiwo wa matarsa data qaninsa harda qananan kaya irin wanda Arna suke sakawa, a cewarsa daya kalli haram a jikinsu gara ya kawowa Balaraba ta saka masa yasan zasuyi mata kyau matuqa ya kuma hado da Bara'atu itama tayiwa dan uwansa kwalliya harda Bilki da Aisha dasu Amina ya warewa kayane riga da skirt wasu da wando irin me roba idan an saka suna kama jiki a lokacin su kansu Arnan basu fara shigar badala ta rabi tsirara suna yawo a gari ba amma dukda haka su a gurinsu irin wadannan dinma sababbin abu ne. Aiko da yar bafulatanat tasa ta saka ba qaramin kyau tayi ba, seda Audu yazo Bechi Bara'atu ta tsantsara masa kwalliya da nata kayan, yanda tayi kyau ta burge shi ya sakayi cewa Yakubun mezzo hana su fara kawo ire iren qananan kayan na Mata dana yara harda ma na Maza dan suma yazo musu da Jeans da shirts tunda yace duk akwai su kuma suna da sauqi a can. Haka kuwa akayi Bayan Yakubu ya koma ya qullo dila guda ya aikowa Audu. Tun kafin kayan su iso daman yayi tallarsu dan haka yana bude dila bata rufe sati ba se burbudi masu siyan daidai da sari sun kwashe, yanda mata suka dinga zuwa suna siya da siyawa yaransu ya bashi mamaki, kuma a lokacin bakin Asibiti kaf shi kadai ya bude irin kayan wannan dalili yasa saya tashi turawa Yakubu kudi ya ninka wanda suka siyo da farko kamar wasa se gashi sana'ar ta karbeshi ya zama wata dilar ma idan ya kwance bata kwana dan ya dena siyar da guda daidai ma yan sari ne suke kwasa a qasa da wata shida se gashi ya kama hayar Rumfa a cikin kasuwar sabon gari inda akafi siyar da ire iren wadannan kayayyakin ya kumayi suna idan ka shiga kasuwar tun daga qofa daka tambayi shagon BECHI za'a kaika. Cikin wannan yanayi ludufi da budi yayi ta zuwar masa, be kuma tsaya kan iya kayan nan ba yaci gaba da gwada duk wata sana'a daya san zata kawo kudi, kantin da suka bude a gida kuwa kullum sake habaka yakeyi dukda kwanaki sun samu Asara an farke shagon an kwashi kaya daga baya aka kama yaran da sukayi kuma sukace Hashimu ne ya sakasu, Dada ce ta hana su daga maganar, an dai je har gaban Me gari akan ayi musu iyaka da Hashimun wanda a wanann karon Goggo Fadi kanta ta nuna masa bacin rai akan abinda yayi Audu kuma ya sake sarar kaya harma da wanda da babu a shagon ya zuba. Tun haihuwar Bara'atu ya qudurce a ransa cewar ze kafa sana'ar siyar da fetur a Bechi, koda masu Ababen hawa da suke da buqatar Fetur din daidaikune amma abinda ya faru na rasa wanda ze taimaka masa ya kai Balaraba Asibiti yasa ya yanke shawarar ze fara Bunbutun koda kuwa ba za'a siya kullum ba wata rana tana iya daurowa a samu me siyar. Aiko ya samu wani Abokinsa Falalau da suke cewa Fala dan bakin Kasuwa ne a nan cikin Kano tare suke a bakin Asibiti kafin ya kuma bunburu da kuma siyar da kayan gyaran mota, a gurinsa ya sari Mai harda su man juye da sauran yan abubuwan buqata, anan qofar gidansu ya kafa Katako inda ya dora jarakunan Man, Baballiya na kula da shago yana kuma kula da Man shida Abdullahi kuma cikin ikon Allah da masu motocin daukar kaya suka gane da yawa basa damuwa da su shawo Mai a Kano kafin su dawo gida tunda sun san da akwai. A cikin Kanon ma ya bude guri nan cikin Goron dutsen ya ajiye wani yaro yana kula masa da Man shi kuma ya tafi Kasuwa, an samu shekara daya a haka zuwa sannan Ya fara damuwa da rashin samun cikin Bara'atu domin Balaraba harta kuma samun wani cikin yanzun bayan zuwan Yakubu hutun qarshen shekara ta biyu a karatunsa na shari'a. Damuwarda Bara'atun take nunawa yasa ya danne tasa sannan kullum Dada na nuna musu cewar Haihuwa lokaci ne idan Allah ya kawo zasu samu tunda ga yar uwarsa Bilki nan me shekara biyar a daki har yau bata samu ba itama toh suyi haquri suyi addu'a ubangiji ya basu a lokacin dayafi musu Alkhairi. Da Abokinsa ko muce Amininsa Lado ya tattauna maganar, shiya ke ce masa daman yawanci Matan matafiya basu cika samun ciki da wuri ba, Audu yace ya akayi Ita Balaraba ta samu ciki toh bayan yafi Yakubu yawan zuwa gida? Lado yayi dariya yace "Ta yuwu lokutan da kake zuwa basu dace da irin lokutan da mace take daukar ciki ba, shi kuwa kaga idan yazo ya kanyi wata guda ko sama da haka a gida kai kuwa zuwanka a tsitstsinke ne wani sa'ilin ma baka wuce kwana biyu uku ka juyo, nima wani Abokina da yake karatun lafiya naji ya fada an musu a karatunsu cewar da akwai wani lokaci bayan gama Al'ada da kwayayen halittar mata suke nuna su shirya daukar ciki to idan anyi dace an samu tarayya a irin lokutan nan shine zakaga an samu rabo bawai yawan kwanciya da mace ne yake kawo ciki ba". Wannan magana da sukayi da Lado ta sakashi bayan yaje Bechi ya roqi Dada akan yana so su tafi Kano tareda Bara'atu ze kaita Asibiti dan yana so a gaya musu wanne lokaci ne mahaifarta take shirya daukar ciki, Dada bata qi ba suka tafi satinta daya ya maidata bayan tasha yawo a Kano ya kaita gurare dan wannan shine karonta na farko da taje, ya nuna mata gininsu da qiris ya rage a kammala ta ringa murna kuwa tana komawa ta qyarawa Balaraba dukda Audun ya gargadeta akan karta gayawa kowa tukunna amma murnar zasu koma Kano yasa ta kasa daurewa cikin ikon Allah kuwa komawarsa babu jimawa ta fara amaye amaye ko ba'a fada ba ansan ciki ne Dada ta ringa cewa gashi nan da suna garaje harda zuwa Asibiti ashe da cikinta ma lokacin bayyanarsa ne beyi ba. Da Audu ya sake zuwa kuwa haka ya kwashe su da Balaraba sukaje Kumbotso inda take Awo akayiwa Bara'atun itama register zata fara zuwa idan cikinta yayi wata hudu a sannan watansa biyu da kwanaki. Ko tari Dada batayi ba dan ba zata so a maimaita abinda ya faru a cikin Balaraba na fari ba shiyasa ko Audu bezo gari ba ranar Awonsu tazo da kanta take tasa su gaba ta rakasu ko kuma Bilki ba kuwa qaramin surutu take sha gurin Goggo Fadi ba wai rashin kunya ce. Wani lokaci Audu yazo gida kamar yanda ya saba, a lokacin cikin Balaraba nada watanni takwas na Bara'atu kuma yana wata biyar. Da yammaci ta tasashi gaba da wai makani take so taci, ya rasa inda ze samoshi anyi shukar makanin amma ba'a fara kawoshi gida ba. Cikin Bara'atun irin me dan banzan tsirfa ne idan kuma ta rasa abinda take so haka zata wuni ranar tana kuka da baqin Rai haka Audu ya fita akan Sabon Mashin din daya siya saboda zirga zirgar kaisu Asibiti ya ajiyewa Baballiya, gurin Shamsu Abokinsa ya tafi yana tambayarsa inda za'a samu Makani, ya ringa tsokanarsa suka hau mashin din suka tafi gonar Usman da Shamsun yace yayi shukar makani kuma ko babu yawa za'a iya cirar wanda ya nuna. Gonar tasa tana can kusan babban titi wanda tanan zaka gangaro ka dauki hanyar shiga Bechin sun samu Usman din ya debo masa da yawa kuwa cikin wanda ya fara cirewa. Sun fito daga Gonar suna magana hankalin Audu nakan wata mota can daya hango tsallken Titi tun shigarsu gonar ya ga motar a tsaye yanzu kuma har mutanen ciki sun fito sun bude gabanta da alama ko lalacewa tayi. Seda ya daure ledar Makanin a kan mashin kafin ya cewa su Shamsu yana zuwa ya tsallaka can gurin motar, tun kafin ya qarasa yake jiyo muryar mutumin da yake zaton shine me motar yanayiwa Driver sa fada cikin harshen turanci shi kuma se faman haquri yake bashi. Audu ya qarasa yayi musu sallama dukda bashida tabbacin Musulmaine, mutumin ya juyo ya kalle shi, tabon sallah daya gani a goshin sa ya tabbatar masa da cewar Musulmi ne. Mutumin ya amsa sallamar Audu yana qare masa kallo kamar yanda shima Audun yake kallonsa, Dattijo ne dan a qalla ze iyayin shekaru Hamsin da biyar zuwa sama fari tasa me matsakaicin jiki ya tsuke cikin Coat baqa kana kallonsa kasan ya juqu a Bako sannan motarsa zata sanar maka cewar babban mutum ne da gani. Cikin Turanci Audu ya gaishe shi yana tambayarsa meya faru dan beyi zaton yanajin hausa ba tunda turancin yaji yana yiwa Direba ga mamakinsa se yaji ya mayar masa da Hausa yace "Wallahi Motar muce ta tsaya, na dauka ma wani gyara ne kuma wai Ashe mai ne ya qare mana qarqaf kuma saboda shashanci wannan Direban be duba man ba kafin mu kamo hanya gashi yanzu a nan bansan yanda zamuyi ba babu kuma service din kira a nan gurin ballantana nayi waya cikin Kano a kawo mana wata motar" ya qarasa yana daga qata waya da sau daya Audu ya taba ganin irinta hannun wani Bature da yake siyan kaya a gurinsa. Direban ya sakeyin qasa da kai yana cewa "Kayi haquri Sir, nidai nafi zaton malejin motar ne ya samu matsala dan seda na duba komai kafin mu taso kuma naga man da muke dashi ze iya kaimu gida har yayi ragowa lokaci daya ya sauka kuma motar ta mutu" Mutumin ya galla masa harara ba tareda yace komai ba tunda motar ta tsaya yake nanata masa maganar wai malejin ne be nuna masa daidai ba yaci gaba da daga wayarsa yana neman service yana kuma dan waige waige a fakaice dan a tsorace yake, koda yake duniya na kwance a sannan amma wannan Titi da yake shiru tun tsayuwarsu ko Keke be gifta ba balle mota se Audu daya fado musu katsaham kamar Aljani kar suje ba shi kadai bane a mamaye su ayi musu wani mugun abun. Audu yayi murmushi yana cewa "Ayya lamarin qarfen nasara babu tabbas, ku jira bari na shiga cikin gari sena kawo muku Man yanzu indai shine matsalar" yana fadar haka ya juya cikin sassarfa ya tsallake titi ya koma inda su Shamsu suke jiransa. Su ukun suka hau Mashin din suka koma cikin gari. Hankalin mutumin da Driver sa ya tashi, karfa gayya zeje yayo azo ayi musu wani abun? Suka kalli juna kowanne kana iya karantar firgici a fuskarsa, ga mota taqi tashi idan sukace su kwasa da gudu kan suje ko ina su Audun zasu iya cimmasu gaba daya nadamar zuwa Taron daya kawo shi Kano ta kamashi, yana zaman zamansa qungiyarsu ta masu lasisin haqar man futur ta shirya musu taro a Kano kamar baze zo ba ashe Ajaline ya kirashi. Jiki a sabule ya shige motar ya zauna ya hada kai da kujera danya gama saddaqarwa yau kam tasa ta qare, qarar mashin dayaji tasa shi dagowa a firgice sedai ganin Audu tareda Shamsu daya rungumo Qatuwar jarka ga bututu da tiyo a hannunsa yasa shi sakin ajiyar zuciya babu shiri zufar dake keto masa ta fara qafewa har iska na fifitashi. Fitowa yayi daga motar lokacin har Audu ya bude jarkar yana jiran Direba ya bude gida man a zuba musu shi kuma yana kallon ubangidansa cikin jiran umarni, kai ya gyada masa alamar bada dama ya bude musu, seda ya cika musu tanki taf da mai kafin ya rufe jarkarda dan ragoqar daya rage ciki yana kallon Direban yace "To ka kunna mu gani" Direba ya kunna mota se gashi kuwa ta tashi, fuskar Alhajin ta sake washewa yana kallon Audu yace "Amma a ina ka samo Fetur haka?" "Ina siyarwa ne anan cikin garinmu" ya bashi amsa. Alhaji ya zura hannu a Aljihu ya zaro kudaden da besan yawansu ba ya miqawa Audu yana cewa "Nagode kwarai samari" "Aa ka bar kudinka Alhaji kyaiuta na baku" "Amma kace siyarwa kakeyi" Alhajin ya fada yana sake miqa masa kudin. Audu yayi murmushi yace "Eh siyarwa nakeyi amma ku kyautana baku, da zan karbi kudinka tun farko zance maka ina siyarwa ka fadi na nawa za'a zuba maka" Alhaji ya gyada kai cike da gamsuwa har sannan fuskarsa dauke da murmushi yace "Hakane, nagode kwarai, yanda ka kaimakeni kaima Allah ya kawo maka wanda zero taimake ka a lokacin da bakayi tsammani ba" suka amsa da Amin. Ya sake saka hannu a Aljihu ya ciro wani dan kati me kyau ya miqawa Audu yace "Ga katina, idan ka samu dama ka nemeni kaji, Nagode kwarai dagaske Allah ya saka" Audu ya karbi katin da aka rubuta 'ZAKARIYYA PAKI AND SONS' ya jefa a Aljihu daga nan Alhaji ya shiga mota yana daga musu hannu har suka bar gurin. Audu da Shamsu suka hau mashin Shamsun nata mita akan me Audu be karbi kudinba yace shi taimakonsu yayi saboda Allah kuma iya addu'ar da yayi masa ma ta ishe shi. Yanayin garin lokacin sanyi ne dan haka Dada nata fama da mura me zafi wadda daman tanayinta duk sanyi har da daukewar numfashi wani lokacin take samu tun su Audu na qanana haka suka tashi sukaga tana shan wahalar nan duk sanyi shiyasa ya siya mata manyan fulasan ajiye ruwa sannan sanyi na shigowa zasu cire labule me saukin da yake a jikin qofa a saka mata jibgege haka dakin baya rabo da rushi amma dukda haka data fita tsakar gida ta shaqi hazo da sanyi haka zatayita haki tana jan numfashi. Maganin gargajiya take sha tuntuni wannan karon kuma tun zuwan Audu yake fama da ita akan suje Asibiti dan zamansa a Kano yasan cutar Asthma, akwai qanin Hayatu Magashi da yake da ita kuma duk yanayin ciwon nasa haka Dadar take fama sedai taqi yarda suje Asibi balle a dorata akan magani tace tafi gane na gargajiyar da take sha tun tana yarinyarta. To wannan karon ciwon nata yadan ta'azzara dan dalilin daya hanashi komawa Kano kenan kusan satinsa biyu a Bechi se jikin yayi sauqi se kuma ya dawo. A daren ranar ma kwana sukayi zaune saboda yanda ta kasa bacci tana jan numfashi dakyar tun bayan data dafawa su Bara'atu makani hayaqin Karan datayi girkin dashi ya cika mata qirji shikenan numfashi ya fara sama sama washe gari kuwa da sassafe Audu ya kwasheta duk yanda take tirjewa seda sukaje Asibiti. An mata Allura an kuma rubuta mata magunguna ya siya bayan dokoki da sharuddan da likita ya kafa mata akan ta kiyaye duk wani abu daze hadata da qura ko hayaqi suka dawo gida. Wunin ranar zur a dakinta yayi shi haka qannensu da matansu duk suna nan suna hidima da Dadan da gaba daya tayi wani laushi dukda tace taji dadin Allura da maganin data sha abinda take ji a qirjinta ya yaye amma jikinta babu qarfi dama kuma likitan ya gaya musu magungunan akwai me kashe jiki yasa bacci dan haka Audu yace ta kwanta ta huta. *MATAR MUTUM* *NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER* *MARUBUCIYAR* *WATA KISHIYAR* *RUBUTACCIYAR QADDARAH* *HALIN KISHI* *FIKRA WRITERS ASSOCIATION* *LITTAFIN KUDI NE* *PAY 400 (PROMO PRICE BAYAN KAMMALA FREE PAGES ZE KOMA 500) A ASUSUN* *7061838488* *OPAY DIGITAL SERVICES* *MARYAM FAROUK* OR *0709290797* *ACCESS BANK* *SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488* *IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705* *NAGODE* *FREE PAGE 8* Goggo Fadi ta ringa sakin maganganu a tsakar gida wai Lamarin Dada dai ta rasa ma abinda zatace akai wannan rashin kunya har ina ta ringa hawa mashin Yara na goyata sannan danbata da lafiya kamar wata jinjira ta langwabe duk se wani zuruftu yara suke akanta, lokacin da take maganar Dada ta fito Aisha ta rakata kewaye ta fito tana daura Alwala. Seda ta idar ta kalli Goggo Fadin da murmushi tace "Yaya kenan, indai nice kin kusa ki dena ganina ballantana nayi abinda ze sakaki surutu". Goggo Fadi ta ce "Eh ba shakka Hafsatu wato daman naji ance zakuyi qaura Birni yo ni ai haka nake so ku tattara ku tafi ku barmin gidana yanda kuka zo kuka sameni, bari ma wannan yaron yazo kuyiwa gurin naku kudi kawai ya fiddaku shikenan wanda ya hada ya raba" Har Dadata zura qafarta a daki ta sake waiwayawa tana murmushin da seda gaban Goggo Fadi ya yanke ya fadi haka kawai tace "Toh ai Malam ba sauri yayi ba Fadi, zan bishi kema kuma komai dadewa zaki biyo bayanmu" daga nan ta shige dakinta tabar Goggo Fadin na sababi ita kadai. Da dare Audu ya kawo mata Kaza gasashshiya da Madara sabuwar tatsa dan gama tafasata kenan ya karbo ko hucewa batayi ba. Dada na cin naman Baballiya na gefenta yana so yaci Audu ya hanashi Abdullahi daman tuni ya gudu gurin Bara'atu tunda yaga Audun ya shigo da ledoji kuma har Goggo Fadi seda ya miqawa. Dada taci ta qoshi ta turawa Baballiya tana cewa "Ci ubana kaji haka kawai yabi ya takuramun kai" "Wlh Dada ke kike dada sangarta yaron nan ya girma amma baze dena sakarci ba a haka kake cewa zakaje aikin Sojan" Audu ya fada, Dada ta kishingide tana sakace tace "Ze dena ne, aikin Soja kuma nasan indai kana raye seka cika masa burinsa kamar yanda ka dakko hanyar cika na dan uwanka. Ina Alfahari dakai Abdulwahabu ina kuma roqon Allah yaci gaba da hada kanku ya baka ikon ji gaba da jajaircewa akan zumunchinku, ina fatan har yaya da jikoki kuci gaba da hada kanku karku yarda qata baraka ta shiga tsakanin ku, Banida haufi domin kunyo dacen mata na kwarai saboda rayuwar Namiji komai nagartarsa idan yayi kuskuren dace da macen aure anan yake samun tawaya dan haka ina horar ku cewar ko gaba koda ace kunyi sha'awar qara aure kuyi qoqari gurin zabo matar da zata tayaku kuci gaba da hada kan gidanku ba wadda zata tarwatsa muku farin cikin da kuka ginu akai ba. Sannan yan uwanku kuci gaba da haquri dasu kuna jan su a jiki da sannu wata rana zaku koma tamkar baya sanda Malam yana raye". Haka ta ringa masu nasiha me shige da wasiyya, Baballiya na gama cin kazarsa ya sheme a gurin ita da Audu sukaci gaba da yar hira har ta fara gyangyadi kafin ta hau gadonta yaja mata abin rufa bayan ya shafa mata man zafi a tafin qafarta ta saka safa. Seda ya zubo toka me zafi a babban kaskon da ake ajiyewa a dakin yayi masa mazauni me kyau saboda gudun tsautsayi kafin ya tashi Baballiya ya gyara kwanciyarsa yaja musu qofar ya fita jikinsa a sanyaye saboda maganganun da Dada ta fada masa, yanda take nanata masa hadin kan Iyalinsa kamar wadda take hango wani abu a gaba haka ya shiga dakinsu Bara'atu har tayi bacci ya raba gefenta ya kwanta sedai be jima da kwanciya ba bugun qofar gida ya farkar dashi. Da mamakin wayake musu bugu cikin dare ya dauki fitila ya fita, seda ya tambayi waye, muryar Yakubu dayaji ta sakashi bude qofar da sauri ya rabe ya shigo ganin yanda yake rawar Dari dan rigar jikinsa bata da nauyi haka nan kansa babu hula ga dare ya tsala dan haka gari yayi sanyi qarara. Yakubun na goye da Jakarsa medan girma kana kallonsa ko baa fada maka ba zaka san yasha wuyar tafiyar da yayiwo ya wuce ciki Audu yabi bayansa zuciyarsa na bugawa abinda ya fara zuwar masa Yakubun ya samu matsala da karatunsa ne. Yana so ya tambayeshi daga ina haka cikin dare ba kuma ya so hayaniyarsu ta tayar da Dada ko Goggo Fadi ta samu abin sharri dan haka yabi Yakubun daya doshi dakin Dada kai tsaya ya tura qofar ya shiga Audu yabi bayansa. Tana kwance tana bacci hankalinta kwance ya kai hannu ze tayar da ita Audu ya riqeshi yana cewa "Haba dai ya zaka tayar da ita tana bacci" "Na kasa nutsuwa saboda ita na baro Ikko babu shiri me ya samu Dada kullum cikin tunaninta nak abin kuma har ya zarce misali?" Yakubun ya fada yana duban Audu, Audu yayi waje yana cewa "Babu abinda ya sameta kaje ka kwanta kaga dare yayi da safe se muyi magana" suka wuce, seda yayita kwankwasa qofar barinsu kafin Balaraba ta taso a dan rikice da alama tana baccin itama bugun ya riske ta, ganin Yakubu ne kuma se fuskarta ta washe da murna suka shiga suka maido qofa se sannan Audu ya shiga dakinsu zuciyarsa fal da wasi wasin abinda ya taso Yakubun haka koda yake ya sani shidin me qulafucin uwa ne ta yuwu rashin lafiyar Dadan ce ta taba shi har ya kasa zama ya taho ya ganta haka ya ringa juyi a gado sedai sam bacci ya qauracewa idonsa dan haka ya tashi ya dauro Alwala ya shiga Nafila Bara'atu dai tayi daidai abinta a gado dan cikin nata irin me baccin nan ne da se a iya sace mutum sedai ya farka ya ganshi a wata Nahiyar. Asubar Fari kururuwar Baballiya ce ta saka Audu sallame sallar da yakeyi babu shiri ya fita daga daki da gudu, a bakin qofa sukayi kicibus da Yakubu da shima ya fito a rikice dan da gani ma daga wanka ya fito ya saka dogon wando ga rigarsa nan a hannu ko sanyin da ake busawa ma bayaji suka shiga turereniyar shiga dakin Dada inda Baballiyar yake qarawa Ihunsa qaimi matan kuma da duk suka fito suma harda Goggo Fadi sun tsaya daga waje kowanne abinda zuciyarsa ta bashi wuta ce tunda lokacin sanyi ana yawan samun wannan matsalar saboda Rushi da ake kaiwa daki dan aji dumi idan yazo da tsautsayi abinda ze iya kama wuta ya shiga ciki se kaga gobara ta tashi amma kuma basu hango jan wuta a cikin dakin ba ko kuma hayaqi to ko wani mugun kwaron ne ya cije shi? Yakubu ne akan gaba, burki yaci yana kallon Dada dake kwance idanuwanta a bude tana kallon rufin dakin hannunta daya na dafe da qirjinta dayan kuma ya saki ya sakko qasa, dukda cewar gawa daya ya taba gani ido muraran wato ta Malam amma baya buqatar a gaya masa cewar Dadan ta rasu. Lokaci daya wani kuka me cike da rauni ya kufce masa, ya durqushe gaban gadon Audu ya tsallake shi ya qarasa shigewa dakin dan be fahimci dalilin tsayuwar Yakubun ba ga Baballiya dabe fasa ihu yana kiran ya shiga uku ba. Hannun Dadan dake qasa ya daga ya maida kan gadon, sanyi qalau yaji shi, ya shiga jijjigata yana kallon fuskarta tareda kiran sunanta ganin ta zubawa guri daya ido Yakubu dake kuka kamar qaramin yaro, ashe Alhinin rasa mahaifiya ne ya hanashi sakat har seda ya kamo hanya ya dawo sedai an saba haduwar, bashida rabon zasu sake zantawa da ita rai yayi halinsa. Kama hannun Audu dake jijjiga Dadan yayi cikin kuka yace masa "Bari jijjigata ta rigamu gidan gaskiya" Ze iya cewa be fahimci abinda Yakubu yake nufi ba dan kwakwalwarsa gaza fassara hausar tayi dan haka ya shiga qoqarin dagata yana cewa Yakubun ya tayashi su fita da ita ya kaita Asibiti Yakubu ya miqe yana janye shi cikin daga sauti yace masa "Ka dena wahalar da ita Audu na gaya maka ta rasu" kalaman da suka fi duk wasu kalamai daya tabaji a rayuwarsa Muni, Dada ta rasu? Dadar da suka gama hira dazu daman duk wasiyya take masa? Kalaman Yakubu suka janyo hankalin su Goggo Fadi dake qofar daki take suka fasa kuka kafin kace me maqota sun jiyo aka fara shigowa rayuwa kenan tabbas dan Adam abin tausayi ne yanzun kaine qiftawar ido ana iya cewa babu kai. Duk wanda yaji rasuwar Dadan se yace jiya fa da La'asar sakaliya ya ganta a Mashin Audu ya dauke ta har sun gaisa, a masallaci ana idar da sallah aka bada sanarwar Jana'izar, kafin ko gari ya gama wayewa tangararau har an shiryata tsakanin Yayanta baka iya fidda wanda mutuwar tafi duka. Bilki suma tayi sanda saqon ya risketa Aisha tafita dauriya kuka ta ringayi Audu kansa duk taurin rai irin nasa ya koka hada kai sukayi da Yakubu suka ringa kuka gwanin tausayi. Bayan an kaita an dawo aka zauna zaman karbar gaisuwa, Goggo Fadi tayi wata zugewa lokaci daya, mutuwar Dadan ta daketa matuwa ta kuma yi nasarar maidata cikin hayyacinta. "Malam beyi sauri ba, nima zan bishi kuma kema kina tafe komai daren dadewa" kalaman Hafsatun na jiya suka ringa mata yawo a kwakwalwa ashe mutuwa Hafsatu zatayi? Da tasan haka da bata takaleta ba, data nemi yafiyarta akan abubuwan da ita da yayanta suka ringayi mata. Hashimu kansa yaji mutuwar amma da yake Dan Adam ne ana kwana daya ya ci gaba da sabgoginsa be ko sake zama gurin karbar gaisuwar ba ya bar su Audu dasu Aminu da idan ka ganshi zaka dauka mahaifiyarsa ce ta rasu. Su Audu kuwa ba'a magana duk sun sukurkuce bayasu ba baya matansu ba amma ya zasuyi haka aka share zama bayan anyi bakwai Abokanan Audu na Kano sunyi masa kara mota guda suka yi sukaje masa gaisuwa bayan da suka samu labarin rasuwar a bakin masu daukar kaya yan garinsu. Wannan karon tsakanin Audu da Yakubu rasa wanda ze lallashi wani ya koma bakin nemansa akayi. Seda Dada tayi sati biyar da rasuwa, Yaya Baba ya kirasu cike da Alhini bayan ya sakeyi musu gaisuwar rashin da sukayi kafin yace musu "Naga dukkanku baku da alamar komawa bakin neman ku musamman kai Yakubu da kuke tsaka da Karatu ka taho ya kamata kuyi haquri ku dauki dangana zamanku bashi ze maido da Goggo ba A yanzu Addu'a kadai take da buqata daga gareku sannan kuci gaba da jajircewa akan abinda take da burin ganin kun cimmasa". Maganar Yaya Baba tasa suka fara shiri jiki a sabule babu wani karsashi sun kasa sabawa da Rashin Dada, tunanin yanda rayuwarsu zata cigaba ba tareda ita ba sukeyi yanzu dawa zasu ringa barin matansu? Tunanin Audu kenan. Da dare ya samu Yakubu a bangarensu yana zaune shiru Balaraba na gefensa itama shiru duk ta fice hayyacinta tamkar Bara'atun sa ga tsohon ciki haihuwa ko wanne lokaci na iya zuwa shigowar Audun yasa ta cicciba ta basu guri. "Wata shawara nake da ita Yakubu" Audu ya fada bayan daya gyara zamansa. Yakubu ya kalle shi Audu yaci gaba da cewa "Daman akan Iyalanmu ne, kaga yanzu Babu Dada gaskiya hankalina baze taba kwanciya ace mu barsu a nan ba kaga dai halin da gidan nan yake ciki lokacin da ranta ma yaya balle yanzu da babu idonta" Yakubu ya jijjiga kai yace "Hakane, ni kaina ina wannan tunanin ga yanayin da suke ciki gaba daya kowacce na da buqatar kulawa ta musamman, amma kai menene shawararka me kake gani za'ayi?" "Dama dai tun zuwansu Ma'aruf na gaya mishi ya dauki kudi cikin cinikin da akayi a qarasa ayyukan da suka rage na gidan nan mu koma can kawai gaba daya da zama kaga hankalina zefi kwanciya na kuma tsaya a guri guda amma kai me kake gani?" Audu ya fada. Yakubu ya muskuta yana cewa "To wannan shawara ce amma kana nufin kenan zamu bar Bechi da zama gaba daya?" "To me muke dashi a nan da ze sa muci gaba da zama? Karka manta mun rasa uwa da uba dangi kadai suka rage mana kuma zamu ringa kawo musu ziyara lokaci lokaci musamman kaga Bara'atu iyayenta suna nan baze dauki lokaci me tsayi ba zamu ringa leqowa muna ganin dangin mu" Audu ya sake fada. "To gida kuma fa haka zamu barshi ya lalace?" Yakubun ya sake fadaz cike da qosawa Audu yace "Nidai na rigada na yanke shawara bazan iya cigaba da zama a gidan nan ba idan na kalli dakin Dada gani nake kamar zata fito daga ciki zuciyata bazata iya ci gaba da dauka ba" yayi maganar a raunane sukayi shiru baki daya kafin can Yakubun ya sake cewa "Ina ganin zan kama daki a Ikko da zamu iya zama da Balaraba zuwa na qarasa karatuna kafin muga abinda Allah zeyi" "Wannan shawara ce me kyau, amma kuma a halin da take ciki baze yuwu ka dauketa ba dole sedai a jira har seta haihu kuma kaga lokaci yana qara tafiya kamata yayi ka fara yin gaba kaje ka shirya duk abinda ya kamata idan ta sauka ta yada wanka se kazo ka dauke ta ku tafi ko ba haka ba?" Shawarar Audu. Yakubu yayi na'am da maganar tasa dan haka suka shiga shiri, sun sanar da matayensu abinda ake ciki haka yan uwansu da suke uba daya, Goggo Fadi ta fasa musu kuka sanda suka gaya mata shirin nasu tana cewa wai me yasa zasu ce zasu bar gidan kenan ita basu dauketa uwa ba ba zata iya kula musu da matansu ba? Daga Yakubun har Audu babu wanda ya kula maganganunta dan gani sukeyi ihu ne kawai bayan hari basu yarda wai har zuciya Goggo Fadin tayi tuba na gaske ba. A satin suka shirya tafi, sun tsara da gida ya kammala Audu ze kwashi Bara'atu da Balaraba duk su koma Kano da zarar Balaraban ta haihu kuma zata koma Wailari tayi wanka inda daga can zata bi Audu, da akwai Yayanta da yake zama a Ikkon shima Shanu yake kaiwa daga baya kuma yayi zamansa can matansa biyu ya kai daya can sunzo ganin gida zasu jima dan haka suka bari akana idan Yaya Iron ya tashi komawa zata bisu su tafi tare. Ana i gobe zasu tafi da maraice Balaraba ta haihu ta samu ya mace wannan karon Ubangiji ya bata da sauqi dan da tasowar ciwon gaske da haihuwar beyi awa daya ba, Audu ya fita qaraso musu siyayyar dan abinda zasu buqata kafin su koma Kano se dawowa yayi ya tarar da yar Baby me kama da Dadarsu sak haka ya kwasheta seda sukaje Asibiti aka tabbatar ita da yarta duk lafiyarsu qalau, farin ciki ba'a magana, Yakubu yayi mata hudu ba da Hafsatu zasu ringa kiranta Dada dan duk wanda ya gabta se ace Dada ta tafi Dada ta dawo. Haihuwar tasa suka qara kwana biyu, yan Uwan Balaraba suka dauketa zuwa gida wanka Audu ya wuce Kano tareda Yakubu daze koma Ikko. Wata daya bayan haka Audu da Bara'atu tareda Baballiya sukayi qaura Kano, qarshen zamansu a Bechi kenan. Ranar da zasu tafi mota guda ya dakko aka kwashi yan rakiya dan an kwashe kayansu daman tuni. Yan uwan Bara'atun uku Yayarta daya se Matar wanta da qanwar Babarta sauran sukace a hankali zasuje suga inda suka koma se murna suke tasu ta koma Birni suma sun samu gurin zuwa haka Inna Hajara har wani qafafa take tana yadawa wanda suka ringa Adawa da Auran Bara'atun da Audu magana ciki harda Babanta. Yan gidansu Audu ma kafataninsu su Bilki dasu Amina harda Matar Yaya Baba data Aminu da Amaryar Hashimu wadda se bayan sun tafi ya samu labari ya ringa tijara yana rashin mutunchi Goggo Fadi da tabi hanyar Allah tuni tun bayan rasuwar Dada batace masa qala ba, ita kanta taso zuwa amma ciwon qafa daya sakata gaba kwana biyu ya hana amma Audu ya mata Alqawarin da kansa ze dawo ya dauketa taje ta kwanar musu biyu kuma tafiyarsu ba tana nufin sunmanta dasu bane, basu da wasu dangi a duniya bayan su, su goman nan da Mahaifinsu ya haifa sune dangin Kansu. Yan Bechi suka ringa santin gida, kwanan su daya suka juyo Audu ya hado su da sha tara ta Arziqi qememe Abdullahi yaqi bin Babarsa Audu yace a barshi daman ai Abdullahi Dansa ne, uwar bata so ba dan daman ita ba wai son zaman da yake a gurin Bara'atun take ba kawai dai dan Aminun tsayayyae ne yasa ta kasa magana yanzun da Audu yace a barshi tace "Amma Babansa be sani ba zeyi fada idan aka koma babu shi" "Idan kin koma ki gaya masa ni Audu na riqe Abdullahi idan yana da jaa yazo ya dauke shi da kansa" ya fada mata zata sake magana Amina ta harareta tana cewa "Sedai kece zaki cr bakya son zamansa a nan dan dai Yaya Aminu ya dade da fadawa kowa ya barwa Audu Dan nan kuma wannan baqin ciki kikewa Danki ze zauna a Birni yayi Karatu me kyau ya tashi a waye" "Meye haka Yaya Amina?" Audu ya katseta, ta sake cewa "Gara na fada mata ai idan kuma ta ce se a bata danta gashi nan ta tarkata su tagi dana Koma zan hadowa Muzammilu kayansa a kawo maka shi ga Yaran nan tuli a dangi har wanda zaka riqr ze gagara ne?" "Audu yayi murmushi kawai jin abinda tace ya tashi ya fita bayan ya Ajewa Aminar saqon maganin ciwon qafa yace ta kaiwa Dada, haka suka koma Bechi aka bar su Bara'atu a sabon guri. Sannu sannu rayuwa taci gaba da tafiya, Balaraba ta yada wanka har taje Bechi daga nan tayo Kano ta kwanarwa su Balaraba Biyu kafin suka kama hanya da Audu daze rakata dan Yayanta Iro ya tafi da Shanu matarsa kuma tana da ciki ta kusa haihuwa wannan yasa Iyayensu sukace ta zauna ta haihu tukunna ta koma. Seda Audu yayi sati ya dawo rayuwa taci gaba. Sosai kasuwancinsa yake garawa. Kudin gonar su da suka siyar ya qara jari da shekara ta zagayo sun ninka kansu wannan yasa ya shawarci Bilki data kawo musu ziyara akan me ya kamata suyi, sun yanke cewar su nemi qananan Gonaki a ringa siya ta yanda a hankali kowa ze mallaki tasa aci gaba da juya kudaden kamar yanda yakeyi yana kuma fitar da riba yana bawa kowa saboda buqatu, gidansu ma Bilkin cewa tayi suyiwa su Hashimu tayi ko zasu siya dan ya mayar da gurin Rumbu kayan gonarsa yake ajiyewa a ciki Audu yace mata Aa su barshi saboda idan sunje su samu gurin sauka ze dai saka a gyara gurin a hankali. *MATAR MUTUM* *NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER* *MARUBUCIYAR* *WATA KISHIYAR* *RUBUTACCIYAR QADDARAH* *HALIN KISHI* *FIKRA WRITERS ASSOCIATION* *LITTAFIN KUDI NE* *PAY 400 (PROMO PRICE BAYAN KAMMALA FREE PAGES ZE KOMA 500) A ASUSUN* *7061838488* *OPAY DIGITAL SERVICES* *MARYAM FAROUK* OR *0709290797* *ACCESS BANK* *SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488* *IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705* *Kuyi following dina a Arewabooks @Maryamfarouk01 inda zaku karanta wannan littafin tareda sauran littattafaina* *NAGODE* *FREE PAGE 9* Ranar wata Talata Bara'atu ta sauka a Asibitin Murtala inda Audu ya yankar mata katin Awo tun bayan dawowarsu Kano ta samu Da Namiji murna gurin Audu dasu Baballiya ba'a magana, wata maqociyarsu Baba Larai da suke mutunchi da Bara'atun tun tarewarsu ce tayi mata biqin kwana biyu kafin Audu ya tattarasu suka tafi Bechi, se ganinsu sukayi da jinjiri aka ringa murna a gidansu ta zauna seda akayi suna yaro yaci sunan Malam wato Tijjani suke kiransa da Babangida, Raguna biyu manya Audu ya yanka haka ya mata kayan barka irin na Birni duk inda ka shiga a Bechi labarinsu akeyi, lafiya lau tayi wankanta kwananta Hamsin da Haihuwa suka dawo Kano rayuwa taci gaba da garawa cikin ludufi da Amincin ubangiji. Kasuwancin Audu kam yana habaka dukda dai har sannan yana kan canje canjen sana'a dalili da duk wadda ya fara tabawa da an kwana biyu se abin ya fara sakin hannunsa tilas yake sake cafkar wata sana'ar ya dora wannan dalili yasa yana da ido acin kusan duk wata sana'a da ake juya kudi a samu riba, ba babbab ba qarama duk yana tabawa ita kanta Bara'atu be barta a zaune ba ya sakata tana taba sana'oi na mata na cikin gida kuma tana samu babu laifi ga Kitso da daman ta iya shima tanayi shiyasa idan suka tashi zuwa Bechi Sallah, Biki ko suna bayan abinda Audu ze bata haka itama zatayi ta Alkhairi wa yan uwanta da nasa, gida su kuwa baya rabo da dangi duk wanda ya samu dama ze zo Kano ya kwanar musu biyu ya koma. Yakubu na Ikko abinsa tunda Balaraba ta bishi seda suka shekara biyu kafin suka zo lokacin ya rage masa shekara daya ya kammala karatunsa kenan. Daga shi Har Balaraba idan kalle su seka qara, Yakubun ya waye ya zama wani baqin Bature hatta shigarsa ta canza zuwa coat baqa da farar yar ciki irin dai shigar su ta masu karatunshari'a ita kanta Balaraba Turanci har ya kama bakinta saboda suna tsakiyar wanda zo in kashe ka basu sani ba da Hausa. Ga Dada data jima da yayewa tayi kubibi abinta fatarta me haske irinta uwarta har sheqi take saboda zama cikin lullumi ga cin naman ruwa da suke se tsohon cikin da take dashi haihuwa ko wanne lokacin dalilin dawowar tasu ma kenan. A Kano suka sauka suka ringa yiwa Juna tsiya ita da Bara'atu da itama take dauke da ciki na Biyu watannin Babangida goma sha daya ta samu ciki sati daya kenan Inna Hajara ta dauke mata shi tunda ta kusa sauka amma ba bisa son ran Audu ba. Seda suka kwana biyu suka huta kafin suka tafi Bechi gaba daya niqi niqi da tsaraba daga can Balaraba taje garinsu su kuma suka juyo Kano seda ta gama kwanakinta ta dawo. Zamansu gwanin dadi, idan safiya tayi Mazajensu suka fita Kasuwa inda Yakubu yake bin Audu Baballiya da Abdullahi su tafi makaranta duk wadda ta riga gama aikin bangarenta zata shiga gurin yar uwarta, nan ma girki daya suke kowa ta dibarwa iyalanta. Wannan karon ma Balaraba ce ta fara haihuwa ta sake samun Mace kwana biyar tsakani Bara'atu ma ta haihu ita kuma Namiji wannan Dalili yasa Audu da Yakubu da duk sukace babu wadda zataje gida aka hade taron suna, ranar kwana bakwan Balaraba akayi mata yanka yarinya taci suna Maimunatu amma taro seda da dan Bara'atu Yusuf dayaci sunan babanta ya kwana bakwai akayi Yan Bechi sunzo da dangin Balaraba an sha buduri sosoi taro ya watse se yan zaman wanka da kowacce aka kawo mata daga gida Yakubu ya koma Ikko saboda makaranta haka suka cigaba da wanka Balaraba na yada wanka taje garinsu da Bechi tayi musu sallama Audu ya kaita tasha da Yayanta suka bi Yakubu Bara'atu kuma taci gaba da rainon Babannan da Babangida wanda Audu ya kafa kwarzaba seda aka dawo masa da Dansa ga kuma Baballiya da Abdullahi abinsu gwanin Dadi suke zaune. Bayan Baballiya sun rubuta jarabawar kammala sakandire wadda tsallaken Aji akayi masa saboda girmansa akayi sa'a kuma yana gane karatun daman yana Aji Takwas suka baro Bechi dan haka suna zuwa Kano Audu yasa aka kaishi Aji biyu na babbar Sakandire, ya dage akan shidai aikin soja yakeyi, tun Audu baya daukar abinda muhimmanci har nacin Baballiyar yasa shi tambayar yanda ake shiga makarantar sojojin. Wani Maqocinsa a Kasuwa ya tambaya dan yanajin yana fadar da akwai qaninsa daya tafi aikin soja, shiya gaya masa qanin nasa yana makaranta a Kaduna shima wani Dan uwan mahaifiyarsu ne dayake zaune a can ya samo masa kuma ance daya gama ze fito a babban soja ne ba kurtu irin wanda mutanen mu a wancan lokacin suke zuwa suyita wahalar banza ana kashe su a yaqe yaqe ba. Wannan dalili ya saka Audu shirin tafiya Kaduna kai Baballiya makaranta. Yace masa ya shirya kayansa kala hudu zuwa biyar a jaka ya kuma hada takaddunsa, Bara'atu ta ringa musu dariya tana cewa "Dukda dai bamyi karatu ba amma nasan ba haka taka ake kai mutum makaranta ba dole se anbi matakai ka nemi gurbi idan ka samu kafin ka tafi ko?" "To ai nima ba cewa nayi zan kaishi kaitsaye ba, zuwa zamuyi can muji yanda tsarin komai yake saboda ban gsu da bayanan Labahani ba besan takan komai ba kawai shirme yake gayamun gara muje kinga idan abin babu wahala kinga ba se anyi jeka ka dawo bazan baro shi can kawai" Audu ya bata amsa. A daren tana hada masa nasa kayan Babannan dake wasa ya zubo da wata jaka da Audu ya cukuikuye takaddar kammala sakandirensa ya jefa a ciki da takaddun gonakin da suka siya a Bechi, ta tattare ta mayar tana masa fadan ya fiya qiriniya, Babangida ne ya daga wani qaramin kati ta bata ankare dashi ta mayar ba ya fita dashi. Audu na qofar dakin inda ta baza musu tabarma saboda zafi suna Hira dasu Baballiya da murna tasa ya kasa bacci. Abdullahi Babangidan ya kaiwa katin hannunsa, ya haska da yar fitila yana karanta abinda aka rubuta a jiki kafinya miqawa Audu yana cewa "Baba ga abinka Baba ne ya dauko" Audu ya karbi katin ya haska shi tunaniya tafiyi na menene, duk sonya tuna kuma ya kasa, Kaduna daya gani a Address din dake jiki ya sakashi bawa Abdullahin yace ya miqawa Ummansu ta saka masa cikin jakar da ze tafi dashi, komana wanene yana da yaqinin zeyi masa amfani tunda zashi Kaduna. * MAMAN MARYAM ONLINE BUSSINESS* *Ina kuke Mata Yan kwalisa , Ina nufin isassun Mata ,Wai shin Kuna da labarin shahararren company nan namu na *GHT wato good health treatments *Wanda yazo muku da fitattu Kuma* *ingantatattun suppliment ,na dukkan matsalolin ku*❓ *Ina maisan tayi kyau,irin na isassun Mata ya fitar Miki da shef dinki tayi Miki gyara in and out ,nemi royal jelly dinmu na company GHT* *Wanda aka yishi da xuma ,kundai San amfanin Zuma basai na fada miku ba , hajiya ta kixo ki Yi gyara domin ki kerewa sa,a kije taro ko baki da ko sisi kiji Ana rangada Miki hajiya , saboda yanda Zaki Kara kwarjini ,kina walwali acikin mutane , magungunan ght anti agen ne suna maida tsohuwa* *yarinya ,yarinya Kuma ta koma jaririya* *Muna da magunguna iri iri * *NA GYARAN JIKI* *NA GOGE NANKARWA* *NA RAGE QIBA* *NA CIRE TUMBI* *NA QARIN HIPS* *NA GIRMAN BREAST* *NA QARA TSAHON GASHI* *NA QARIN NI'IMA WANDA ZAI SAUKAR MIKI DA NI'IMA YA QARA MIKI DADI DA ZAQI A GURIN OGA* *Muna da hadin bita zai zai ,indai kishiyar ki tana Shan magungunan GHT, tohh lallai sunan ki sorry domin kuwa tazarar dake tsakanin ku kamar tazarar sama ne da kasa* *Muna da Wanda zai matseki ciki da waje Andai na yayin dinki uwargida*, *Sannan company mu na GHTBai tsaya anan ba* *Ya kawo muku maganin dukkan matsalolin ku* *INA MASU HAWAN JINI?* *INA MASU CIWON ZUCIYA?* *INA MASU CIWON QODA?* *INA MASU CIWON HANTA?* *INA MASU SICKLER?* *INA MASU HIV?* *INA MASU CANCER?* *INA MASU NEMAN HAIHUWA?* *Tohh Ku matso GHT taxo muku da magungunan matsalolin ku* *Kuma muna da testimonys da yawa ,na wadanda suka gwada suka da ce* *Munanan a KANO KUNTAU* *Kuma muna tura Kaya ko wanne gari cikin aminci da gaskiya , kuma kayan mu muna badashi ne cikin price Mai rahusa ga kyau ga inganci sannan ga Rahusa* *Kutuntube mu ta wannan number 📞08129249549* *📲07011401314* *Seda suka hau mota har sun wuce Zariya kafin katin ya fado masa take kuma ya tuna inda ya samo shi, wannan Alhajin daya taba taimaka ya basu Mai shekaru kusan uku kenan nasa ne. Farin ciki ya kamashi, a ransa ya ringa Addu'a Allah yasa yana raye kuma yana Kadunan idan sunje ze neme shi su sada zumunchi. Ikon Allah kenan, qila rabon su sake haduwa yasa Babangida binciko katin dan ko da kudi bazece ga a inda ya ajiyeshi ba, zaton sa ma ya fadi tun a ranar. Haka suka sauka Kaduna, Baballiya nata dan banzan raki wai tafiyar Nisa ya gaji Audu ya balbaleshi da masifa yana cewa a haka zeje aikin sojan qato dashi amma se ragonci kamar Mace. Ganin yana nema yayi masa kuka ya sakashi neman gurin me abinci a cikin tasha ya siya masa, suna zaune yana tunanin ta ina zasu fara, gashi la'asar harta kawo kai dan motar da suka hawo se a hankali kamar sun hau Jaki. Wani akwatun waya ya hango wanda ake biya ayi kira ya miqe yana laluba Aljihunsa inda ya saka katin Alhaji Zakariyya ya tafi gurin. Ya bada lambar aka kira masa, kiran farko ba'a daga ba seda akayi na biyu muryar mace cikin harshen turanci ta ratsa kunnensa. Gyara nasa harshen yayi suka gaisa kafin ya shiga tambayar mamallakin lambar wanda a katin yaga an rubuta Zakariyya, "wa za'a ce masa?" Ta tambayeshi yace mata "Kice masa Audu Bechi ne" Audu ya fada duda yasan babu tabbacin Alhajin ya gane tunda ba gaya masa sunansa yayi a wancan lokacin ba idanma ya tuna ya taba haduwa da shi kenan. Matar tayi shiru kamar me tunani kafin tace ya riqe waya tana zuwa. A can bangaren sakatariyar Alhaji Zakariyya ce ta dauki wayar wadda take a cikin ainihin office dinsa, ta sani lamba ce da yake magana da mutane masu muhimmanci dan haka duk wanda ya kira tabbas yana da muhimmanci gurin Ogan nata. Kwankwa qofa tayi, Alhaji Zakariyya ya bata damar shiga. A taqaice ta sanar masa da kiran daya shigo din, sunan Bechi data fada kawai ya sakashi zabura kamar wanda akace anga Dan uwansa daya bata. Fuskarsa a washe har haqoransa sun bayyana cikin son tabbatarwa yake tambayarta "Kikace BECHI" "Yes sir, haka yace sunansa Audu Bechi" ta bashi amsa. Alhaji Zakariyya ya daga kan wayar dake ajiye kan teburinsa wadda take a hade da ta teburin sakatariyar, Audu nacan saqale da waya a kunne cikin jiran tsammani yaji sallamar Alhajin kamar daga sama har wata Ajiyar zuciya ya sauke ya shiga gaishe shi. "Har na fitar da rai da zaka kirani, kullum da tunaninka nake kwana nake tashi, na kasa manta Alkhairin dakayi mun" Alhajin ya fada cikin tsananin murna. Audu yayi murmushi yace "Haba dai Alhaji dan wannan abin ka kasa mantawa tsayin shekaru?" "Kai kake kallonsa a qanqanin abu, badan Allah ya kawo ka ka taimakemu ba a wannan rana bansan ya zamuyi ba. Ya bayan saduwa ya Kano? Kasan tun wannan ranar ban sake zuwa Kano ba amma duk idan naji wani zece sena bada sallahun a dubamun kai a wannan hanyar gashi bansan sunanka ba ballantana ko yan karkararku a tambaya" Alhaji ya sake fada. Audu ya jinjina kai cike da mamaki kafin yace "Ikon Allah, nima yau Allah ya kawoni Kaduna shiyasa na taho da katin nan nace idan baka mantani ba na kiraka muyi zumunchi" "Kace kana Kaduna?" Alhaji ya fada har yana miqewa, Audu ya nanata masa kafin ya fada masa yana Tashar Kawo tareda qaninsa, Alhaji be bashi damar sanar masa da abinda ya kawo su ba yace ya tambayi me wayar Adireshin gurin da suke ya kuma jira a nan ze tiro direba yanzu a kaisu masauki ai baqonsa ne shi. Haka ya zauna a gurin, ba'ayi ci mintina ashirin ba sega Direban Alhaji da sukaje Kano tare Audu na ganinsa ya gane shi ya qarasa gurin fuskarsa dauke da fara'a. "My brother" ya fada yana buga kafadar Audu ko ba'a fada ba cike yake da farin cikin ganinsa. Shi ya daukar musu jakar kayansu suka tafi inda ya faka wata luntsumemiyar mota yayin waccen shekarar suka shiga Baballiya se zare ido yake. Suka ringa ratsa titunan Kaduna da gine gine masu kyau da burgewa a nan kuma Audu ya tabbatar da cigaban da Kaduna tafi Kano ta bangaren tsarin birni wanda ake fada su zauna kasuwa suyita tafka musu yau gashi ya gani kuma ya yarda. Gine ginensu a tsare ga Titi ko ina Malam Baballiya ko kasa rufe baki yayi dan wasu ginin ma be taba ganin kalarsu ba saboda ko a Kanon daga makaranta se gida se ranakun hutu da Audu kan tafi Kasuwa tare dasu babu inda ya sani shiyasa Aljannar duniyar da yake gani yanzu ta mugun tafiya da tunaninsa. A unguwar Sarki inda katafaren gidan Alhaji Zakariyya yake kutsa cikin wani gida. Gini ne na Alfarma wanda ko a yanzu kwaskwarima kadan za'ayi masa ya tafi daidai da zamani. Gurin da aka tanada dan ajiye motoci Direbam da yanzu Audu yasan sunansa Tunde ya faka motar. Seda ya dallewa Baballiya qeya kafin ya dauke idonsa daga kallon taswirar gidan tamkar kwayoyin idonsa zasu zazzago. Tunde ne yayi musu jagora har zuwa can gefen gidan inda sukaga qofofi guda hudu jere ya bude ta farko ya shiga suka take masa Baya Baballiya ne kan gaba Audu na daga baya saboda ya tsammaci bangaren matan gidan aka kawo su dukda sunbaro wancan qaton ginin me Bene qila na megida ne can amma ga mamakinsa cikin madaidaicin Falo yaga sun shiga. Tunde na murmushi ya nuna masa qofa dake cikin falon yace "Ga daki nan, ku shiga kuyi uzurin da zakuyi bari a kawo Abinci" daga haka ya juya ya fita. Audu ya ringa kallon Falon dake malale da Kafet irin wanda daka taka qafarka zata lume a ciki ga wasu shimfida shimfidan kujeru na Alfarma, ya taba ganinsu sau daya a gidan wani Hamshaqi a Kano daya kaiwa Takalma wanda suma yana siyar dasu yanzu. Wani qamshi da sanyi ya ringa ratsasu, ya kalli Baballiya dake nan kamar gaula har digar da yawu yake tsabar kallo kafin ya zauna akan kujera kamar me tsoron ace ya tashi. Babu dadewa Tunde ya dawo da wani mutum a bayansa ya saka Apron da hular girki hannunsa dauke da wani qaton Try har mamaki ya kama Audu na tunanin yanda ya iya daukar wannan Try da hannayensa biyu ba taredaya nemi taimako ba. "Ya naganku a nan ga jakarku ma baku kai ciki ba?" Tunde ya fada yana tsince jakar su Audu da Baballiya ya watsar a garin qauyanci. Cikin dakin ya kai musu Kuku kuma ta aje kayan hannunsa ya fita ya sake kawo wani madaidaici dabe kai na farko ba daga nan ya fita ya barsu Tunde ma ya fita bayan ya jaddada musuga abinci nan suci su qoshi tamkar suna gida. Kiran la'asar da akayi ya saka Audu miqewa ya shiga dakin. Nan dinma lailaye yake da Kafet ga gado na Alfarma da sif irin ta cikin Bango se mudubi daga gefe. Qofar da yake zaton itace ta bayin ya bude ya shiga. A zuwansa Lagos sun taba zuwa gidansu wani Abokin Yakubu da suke karatu tare a can ya koyi kunna irin famfon daya gani anan idan ba haka ba da yau an sha kunya. Ya kunna Famfo ya tara hannu da niyar Alwala yaji ruwan zafi sabanin na sanyi. Wannan dalili ya sakashi canza shawara, sosaiya ya gaji jikinsa na ciwon wahalar mota dan haka ya dakko soso dan yaga sabon sabulu a kwalinsa ya koma bandakin ya tara ruwa me zafi a bokiti ya sheqa wanka a bandakin yan gayu yayi Alwala ya fita. Tsaf ya shirya yana jinsa kamar yau ya fara wanka a rayuwarsa. Idanbeyi qarya ba fatarsa har wani sulbi tayi taji sabon sabulu. Anan yayi sallah seda ya idar ya tuna da Baballiya sukazo ya fito falon, nan ya ganshi Baje kan kafet yana bacci ga Abincin daya kacaccala nan ya barsu bude se zuba munshari yake kamar wanda yayi awanni da kwanciya baccin. Tsabar takaici besan sanda ya kai masa hauri da qafa ba ya kuwa miqe a zabure ze kurma ihu Audu ya zare masa ido dole ya nutsu ya hau sosa inda ya haureshin yana tura baki girman Banza yake dashi amma ya ringa abu kamar qaramin Yaro. A gaba Audu ya tasashi seda ya tara masa ruwan wanka ya kuma zuba masa wani a Buta yaja masa kunne akan karya kuskura ya kunna musu famfo ya lalace kafin ya koma falon ya harde kamar gidansa ya shiga cikin Abinci yana ayyana abubuwa dayawa a ransa. Yana da manyan burika da yake fatan Allah ya cika masa. Ze ginawa Bara'atu irin wannan Aljannar duniyar, ya hasko kansa yana tuqa mota irin wadda aka dauko su a ciki ha ma'aikata ko ta ina idan ya wuce su ringa zubewa suna gaishe shi dan shidin mutum ne me Izza yana so a girmama shi matuqa. Seda yayi damkafin ya tattare sauran gefe ya rufe, can dakin ya leqa ya hango Baballiya kan gado yayi rashe rashe yana bacci ya girgiza kai kawai yana murmushi, falon ya koma ya kishingide kan kujera bacci ya sace shi besan tsayin lokacin daya dauka ba sunansa da ake kira ya farkar dashi ya hau murza ido. "Sannunku, na tayar dakai ko?" Tunde ya fada fuskarsa da Fara'a. Audu ya zauna sosai yana cewa "Aa babu komai ina zaune ma bansan bacci ya dauke ni ba" "Ai kun sha gajiyar hanya, daman Alhaji ne ya dawo sannan kuma anyi Magriba shiyasa ma yace a kirawo ku masallaci" Tunden ya sake fada. Audu ya kalli qaton Agogon dake jikin bango kafin ya miqe da hanzari ya wuce dakin Tunde kuma ya fita. Seda ya dalawa Baballiya dukan gaske dan ya gaji da kiran sunansa yana jijjiga qafarsa kafin ya miqe yana soshe soshe. Audu ya wuce yayo Alwala, a bakin gadon ya ganshi ya sake kifewa aiko ya kuma kai masa mari ya farka da gudu ya fada bandaki. A rayuwarsa zece be taba bacci me dadin na yau ba. Yana ganin babu wata Katifa data kai tasu ta gidan Yaya Audu dadi da laushi seda ya hau wannan yaji ashe shi akan sumunti yake kwana. Yanda Alhaji ya ringa haba haba da Audu har seda abin ya bashi kunya, mamakin daya sake kamashi ganin tamkar duk mutanen gidan sun san labarinsa, "Aboki nane na Kano da na gaya muku" abinda Alhajin yake fada kenan kowa se ya fara "Ikon Allah shine sannu da zuwa ya hanya" a haka sukayo sallah suka dawo cikin gidan kai tsaye Alhaji dake riqe da hannun Audu ya wuce dashi Asalin ginin da suka wuce dazun. Falo na Alfarma da ya qawatu da jere tamkar a qasar turawa. Alhajin ya zauna kan Kujera Audu yayu qasa ze zauna ya riqo shi yana cewa "Haba zauna nan sama mana, kaima samu guri ka zauna" ya fada yana kallon Baballiya daya zubawa chandler ido kamar ze kamota. Qofar glass din dake cikin falon ta bude, wata farar Mace kalar Madara ta fito cikin kwalliya ta kece raini tamkar me tafiya biki qamshinta ya baza gurin ya hade da sanyin Ac dana freshner da aka saka. Fuskarta dauke da murmushi take takowa tamkar yanda shima Alhajin dake kallonta yake murmushin. "Lale maraba da baqin Kano" ta fada tana zama gefen Mijinta. Audu ya zame ya shiga gaisheta ta amsa tana tambayarshi Hanya, seda ya mintsili Baballiya kafin ya shiga hayyacinsa ya gaisheta itama. Da daddaya yaran sa suka fara shigowa falon, Namiji daya fara shigowa wanda zasuyi sa'anni da Audu se mata guda biyar da suka biyo bayansa gaba dayansu farare ne tamkar Alhajin da Hajiyar gasu yan gayu abinda ya burgeshi dasu yanda suke da fara'a sunata haba haba dasu babu kyama ko nuna banbancin sun fisu matsayi. A kan qaton Dining din gidan suka zauna duka sukaci Abinci dukda Audu yaqi da farko Amma Alhaji yace se sun zauna shima Dansa ne kuma baqonsa a dole ya dan tsakuri abincin dukda damab cikinsa a cike yake har sannan Baballiya kuwa be kwari kansa ba yaci iyakar geji, har addu'a Audu ya ringa masa a zuciyarsa ta cewar Allah rabashi da lalacewar ciki irin yanda ya zage yana narkar Abinci kamar kwancen Yunwa koda yake sabon dandano yaji a harshen sa. Seda suka gama cin abincin gaba daya suka koma cikin falon. Alhaji ya kalli iyalansa yana cewa "Wannan shine bawan Allahn dana baku labari ya taimake ni a Kano, duk tsayin lokacin nan babu ranar da ba zanyi Addu'a Allah ya sake gama fuskokinmu ba se gashi ubangiji ya karbo Addu'ata" "Aiko dai ranaku daddaya ne Dady bazeyi maganarka a gidan nan ba, babba da yaro dan gida da me aiki babu wanda be haddace Abokin Dady na Kano ba ni na dauka zanga wani tsoho irinsa ashe ma Dan Saurayi ne" Daya daga cikin yammatan ta fada wadda kuma da alama duk ta fisu kaudi da iyayi. Baze iya fadar ko ta nawa bace a jerin haihuwa saboda su biyar din kusan kansu daya, da gani irin haihuwar kwanika ce kuma da yake suna da garin jiki shiyasa suka tashi kai daya. Namijin ya kalleta yace "Kodai kin qyasa ne kike kiransa wani dan saurayi?" "Kai Yaya" ta fada tana rufe fuska alamar kunya, Alhaji yayi dariya cike da nishadi ya nuna Namijin yana cewa "Wannan shine babban Da na Jamal, likita ne ya kammala karatunsa shekara biyu data wuce a Jami'ar qasar Ingila harya fara aiki kuma ina kan kammala gina masa Asibiti nasa na kansa daze cigaba da kulawa dashi, wannan Sakina kenan ita take bi masa se Salima, Ummulkhairi, Mamana Binta se kuma Auta Munira" ya qarasa yana shafa kan Autar da ita ce bata kai girman sauran ba. Ya sake nuna Sakina,Salima, da Ummu yace "Wadannan duk suna da Aure Sakina nada Yara biyu ragowar nada daddaya kaga jikokina hudu kenan, saboda zuwanka yasa duk suka zo Mamana da Auta kadai suka rage se Yayansu" "Masha Allahu" Audu ya fada yana sake kallonsu gasu nan abin sha'awa. Sakina ce tace masa Mijinta yana zuwa Kano da akwai Yayansa acan yake zaune shi a unguwar goron dutse. Audu ya washe baki jin an an bato unguwarsu yace "Wurin ina a Goron dutse? Ai anan nima gidana yake" Da mamaki Alhaji ya kalle shi yace "Oh daman a cikin Kano kake da zama?" Ya shafa kai yana cewa "Eh a nan nake gwadago, da ina zuwa ina komawa gida amma yanzu bayan rasuwar Innarmu nayi qaura gaba daya da Iyalina muka koma cikin Kanon" Take fara'ar dake kan Fuskar wadda aka ambata da Binta ta bace, yanda ta hade ran lokaci guda yasaka kowa ya fahimci sauyin nata banda Alhaji da ke jajantawa Audu rasuwar Dada yayi masa ta'aziyya ya dora da cewa "Kace kana da Iyali? Ikon Allah" "Kwarai kuwa Alhaji, idan watan Sallar tsofaffi ya kama shekarata biyar kenan da Aure ina kuma da Yara biyu Maza" Alhaji da Hajiya suka hada baki gurin cewa "Ikon Allah ashe harda zuri'a, kai amma abu yayi kyau masha Allahu Allah ya raya yayi musu Albarka, wannan dai qaninka ne ana gani base an tambaya ba" ya fada yana nuna Baballiya dake zuba gyangyadi, bayan ci ai se a kwanta kuma a huce gajiya. A fusace Binta ta miqe, Mamanta dake ankare da ita ta kalleta tana cewa "Ina kuma zakije ana hira?" Tayi kwalwal da ido kamar haqaye zasu zubo mata tace "Kaina ne yake ciwo Mama kwanciya zanyi" bata ko jira me zata ce mata ba ta wuce har tana hadawa da sassarfa saboda yanda take qoqarin fashewa a gurin, wani irin tuquqin bacin rai takeji data rasa na menene. Ta rasa gane meye hadinta da wannan dan qauyen da daga jin yace yana da mata zuciyarta ta fara kumbura wannan shi ake kira da daukar Dala babu gammo kenan. *MATAR MUTUM* *NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER* *MARUBUCIYAR* *WATA KISHIYAR* *RUBUTACCIYAR QADDARAH* *HALIN KISHI* *FIKRA WRITERS ASSOCIATION* *LITTAFIN KUDI NE* *PAY 400 (PROMO PRICE BAYAN KAMMALA FREE PAGES ZE KOMA 500) A ASUSUN* *7061838488* *OPAY DIGITAL SERVICES* *MARYAM FAROUK* OR *0709290797* *ACCESS BANK* *SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488* *IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705* *Kuyi following dina a Arewabooks @Maryamfarouk01 inda zaku karanta wannan littafin tareda sauran littattafaina* *NAGODE* *FREE PAGE 10* Qarfe tara na bugawa daya daga cikin ma'aikatan ya shigo cike da ladabi ya sanarwa da Alhaji Mijin Sakina da Mijin Ummu na waje Alhajin yace yayi musu iso. Irin alaqar da ya gani tsakanin Alhajin da surukan nasa ya burgeshi. Wato su Yan boko komai nasu da birgewa yake (nada kenan da suka hada Boko da Addini se rayuwar ta zama me burgewa da ban sha'awa ba Yan Bokon yanzu da suka dauki fitsara a matsayin wayewa ba). Ya tuna lokacin da Mahaifinsu na raye, ko a masallaci baya hada sahun sallah da Mijin Mairo da Amina wai surukuta daga gaisuwa babu wata magana da take qara shiga tsakaninsu babu wata shaquwa a tsakani su kuwa bayan gaisuwar gashi har an zarme hirar aiki suna fadawa Alhan abubuwan da suke ciki. Ya nuna musu Audu wanda sun gaisa tun shigowarsu yace "Ga Abdullahi nan shine baqon da matanku suka zo wa sannu da zuwa" aka sake maimaita gaisuwa data fi tada, matan kuwa tuni kowacce ta shige cikin gidan se gata da mayafi da jaka se yaga kamar har hoda da gazal suka qara da turare dan suna shigowa falon ya sake rikicewa da sabon qamshi, sukayiwa Iyayensu sallama suka fice harda Salima wadda su Ummu zasu sauketa dan unguwarsu daya, a yanda Yaji Mijinta Soja ne baya gari. Bayan fitarsu Mama ta miqe itama tana cewa Mijinta bari ta shiga ciki taga koda abinda za'a qara kawowa su Audun, ta kalli Baballiya dake zuba gyangyadi tace "Kaje ka kwanta abinka dan idan ba'ayi wasa ba Yayanka da Alhaji yau kwanan hira zasuyi" Alhaji yayi dariya yace "Kamar kin sani, a kawo mana shayi dan muji dadin hirar" ta wuce tana dariya. Alhaji ya kalli Audu yace "Gaba daya murnar ganinka tasa na manta na tambayeka dalilin zuwanka Kaduna, ko kuwa dai ziyara kawai ka shirya kawo mun?" Audu ya sosa qeya yana murmushi yace "Kusan haka Alhaji, Allah ya nufi zamu sake haduwa shiyasa ya kawo mun tafiyar babu shiri" ya nuna Baballiya yaci gaba da cewa "Wannan yaron ne ya dage akan aikin soja yake so yayi, nayi tambaya acan aka gayamun da akwai Jami'a ta karatun Sojoji da aka bude a nan Kaduna shiyasa na shiryo na taho dashi dan muji ya tsare tsaren makarantar yake". Alhaji ya gyada kai cikeda gamsuwa yace "Aiko kazo akan gaba dan suna cikin dibar dalibai ne idan banyi kuskure ba a cikin satin nan nakejin kamar zasu rufe ma dan haka gobe idan Allah ya kaimu zan hadaku da Tunde ya kaiku can NDA din, Abokina General Hanna Balogun shine mataimakin shugaban makarantar nasan babu matsala da kunje zeyi muku duk abinda ya kamata". Murna ta cika Audu, wato ubangiji ya soshi da rahma shiyasa ya bayyano masa da katin Alhaji Tijjani, ya ringa masa godiya Alhajin yace "Haba Abdullahi, ai tsakaninmu babu godiya Allah ne ya hadamu kaga kuwa duk abinda nayi maka ai banfadi ba domin kai ka fara taimako na". "Binta ta shigo da qaramar sallama hannunya dauke da qaramin Try da aka fora butar shayi ta qarfe irin ta buzaye da qananan kofuna suma na qarfen guda biyu akai, Alhaji dake bawa Audu taqaitaccen tarihinsa shidin mutumin Paki ne tanan Kaduna Mahaifinsa haifaffen nan ne mahaifiyarsa Baturiya ce tun zuwan turawa Mahaifinsa suna cikin na farko farko da suka karbi Karatun Boko har ya samu damar tafiya qasar Ingila acan kuma ya hadu da mahaifiyarsa Janet sukayi Aure su uku suka haifa shine na biyu akwai Yayarsa Ketrina se qaninsa Muhammad, su biyun sun bi Addinin Mahaifinsu banda Babbar Yayarsu dukda daga baya dabda Mahaifiyar tasu zata rasu ta karbi Musulunci shekaru biyar da suka wuce kenan ta mayar da sunanta Fatima amma ita Ketrina Allah be nufa ba suna dai yi mata fatan karbar shiriya kafin mutuwa ta risketa. Binta ta Ajiye Try Alhaji ya kalleta yace "Sannu Mamana, ban lura ba dazu ashe kin tashi ba'a qarasa hira dake ba" Ta dan yatsina fuska cikin salon sangarta tace "Dady kaina ne yake ciwo shine naje nasha magani" "Sannu Allah ya sauwaqe" Alhajin ya fada cike da kulawa Audu dake kallonta irin kallon qurilla yana hango siffar Turawa a tattare da ita se yanzu ya gano dalilin da yasa Yayan Alhajin har shi kansa suke kamar wanke hannu ka taba, jikin da suke dashi kuma gurin mahaifiyarsu suka gada kenan tunda a cike take qosasshiyar mace bawai irin shirgegeiyar nan da tsoka da kitse yayiwa yawa ba. Tsakin data buga a daidai saitinsa ya maidoshi hayyacinsa, ya sosa kai, Alhaji dake ankare dash yayi murmushi kawai Binta ta wuce tana qunquni. Kadan yasha shayin dalilin Alhaji ya matsa masa suna sha yana tambayarsa Kasuwa da irin harkokin da yake tabawa. "Har yanzu kana siyar da Man kuwa?" Alhajin ya tambayeshi. Audu ya kurbe dan saurab shayin cikin kofinsa yace "Aa wlh, tunda na bar Bechi na saki harkar dan dama dalilin farata saboda haihuwa data zowa matar yayana cikin dare muka rasa wanda ze kaimu Asibiti duk masu Ababen hawa sukace basu da Mai hakan yayi sanadi har aka rasa jaririyar wannan yasa na fara sana'ar daman kuma Baballiya ne yake zama a gurin to yanzu muna tare babu wanda zeci gaba da kulawa dashi shiyasa na bari" "Yanzu se bige bige kenan kakeyi?" Alhaji ya sake tambayarsa, Audu ya danyi jim kafin yace masa "Eh" dan se yaji kamar maganar bata dace ba a tunani da izza irin tasa yana ganin sana'arsa ta wuce a kirata da Bige bige, shida yake da Jarin kusan Dubu dari tasa ta kansa a wancan zamanin banda na Gadonsu da yake juyawa gaba daya idan an hade kudaden da ya zuba a Kasuwa sun kai dubu dari uku ai kuwa ya zarce ace yana bige bige. Alhaji ya nisa yace "Yanzu dai ku gama da abinda ya kawo ku tukunna zamu san abinda ya dace ayi, meye matakin karatunka tunda naji jar turanci ka iya sosai?" "Iyakacina Sakandire Alhaji" Audu ya bashi amsa, gani kamar ya gaji da hirar Alhaji yace suje su kwanta sa qarasa da safe, seda akayi da gaske kafin Baballiya ya tashi dan kan kafet ya baje yake jan Rago son ransa. Da sukaje kwanciya ya ringa tuna Bara'atunsa da yara suna can gashi babu waya ballantana ya kira ya sanar musu sun sauka lafiya da halin da suke ciki. Ya rufe ido, Binta ta shiga yi masa gizo. A yanzu da yake qara shekaru da wayewa tareda sanin kan duniya kwakwalwarsa cike take da burika da mafarke da yake son cinma. Tun Asali yana da qawazucin auran mace me garin jiki, bawai qatuwa ba Aa cikakkiyar macen da babu qashi a jikinta. A irin shekarun da akeyiwa Mata aure a sannan kuwa yasan cewar baze samu irin kalar da yake da burinba, daga baya ya gane cewa se bayan Matan sun haihu jikinsu yake budewa su koma irin yanda yake kwadayin, tunda Bara'atu ta haifi Babangida yake baza ido yaga ta fara qiba saboda Balaraba tun qibar ciki bata sace duka ba tana nan yar duma duma da ita ga Ikko data karbeta tasa ta qara wani kyau idan ka ganta ba zakace Matar Yakubu Bechi bace to hakan yayi ta fata daga gurin Bara'atuntasa sedaihar yau data yi haihuwa biyu tana nan tamkar yar matashiyar Budurwar daya aura qirjinta ne kadai zece abinda ya qara girma daga yanda ya aureta gani yake ma kamar qara qanqancewa takeyi idan suka fita se a ti ga dauka qannensa ne ita dasu Abdullahi wannan abin yana damunsa kuma iyakar dadi daze saka jiki budewa yana siyo mata. Duk daren duniya se sunci Balangu ga fura da zasu dora da ita banda sauran cimaku masu rai da Lafiya amma sedai su suyi bindin bindin har Babangida idan ka gansu girmansu yafi shekarunsu amma banda ita kuma mahaifiyata nada qiba, Babanta kansa ba siriri bane ya rasa inda ta gado rashin Auki ita, ganin Binta ya tada masa da tsohon tsumi da kwadayinsa na Auran mace irinta. Sedai da yake wargima guri yake samu ita zuciyar batayi gigin hasaso masa ita a matsayin tasa ba, Aa yana lissafin samun wata me dama dama kamarta dukda yana matuqar qaunar Bara'atu baya kuma jin akwai wata mace da zata kamo qafarta a zuciyarsa sedai ya dibar mata wasu shekaru da muddin bata kai muradinsa ba ze qara Aure, badan baya sonta ba ko ya raina Halittarta Aa sedan kawar da qawazucinsa ya kuma kade hankalinsa daga kallon manyan matan da zuciyarsa take so. Haka ya kwana yana mafarki harma ya qara Aure ya samo yar duma duma. Washe gari haka aka sake kiransu cikin gida sukayi karin kunallo tareda Iyalan Alhajin. Dankali kadai suka iyaci daga shi har Baballiyan se Burodi da ruwan shayi, tare suka fita da Alhaji seda Tunde ya sauke shi a gurin aiki kafin suka wuce NDA wanda Alhajin ya rigada ya sanar da Abokinsa zuwansu dan haka basu sha wahala. Anyiwa Baballiya duk wani sikirinin daya kamata sun karbi takaddunsa sun kuma gaya musu zasu sanar da ranar da za'a fara tirenin a gidajen Radio da kuma Talabijin dan haka su ringa saurara. Da wuri suka koma gidan, A tsakar gidan suka tarar da Binta da Munira wadda da alama itama dawowarta kenan daga makaranta dan Uniform ne a Jikinta suka gaisa har yayi mamakin sakin fuskar Bintan yau sabanin jiya da tunda ta tashi da sunan ciwon kai taketa fushi har dazu da safe kafin su fita. Seda ya leqa ya gaida Mama tace za'a kai musu Abinci yanzun yayi godiya ya wuce masauki a ransa yana tunanin daya san da wuri zasu gama da sunyi sallama da Alhaji kawai sun wuce Kano, amma babu damuwa gobe zasuyi Asubanci da yardar Allah su tafi. Da la'asar yana zaune gurin megadi suna hira Baballiya ana daki ana shan Ac tsabar tsiya hancinsa ya toshe saboda rashin sabo amma yaqi haqura wai idanya tafi babu tabbacin ya sake ganin ta. Binta ta qarasa gurinsu Audu tasha kwalliya da Atamfa dinkin tazarce, tana da tsayi da jiki ba qaramin kyau kayan ya mata ba ga kalar Atamfar da take da duhu ta sake haska farar fatarta tayi daurin gaban goshi, Audu besan kallonta yake ba seda Malam Saminu ya tabashi ya wayance da kallon qasa. "Sannu Abdullahi hira kukeyi?" Ta fada bayan data tsaya kusa dasu. Audu ya daga kai ya kalleta ita dinma shi take kallo tana masa murmushi dan haka ya qaqalo murmushin shima ya amsa mata. "Ko zaka dan rakani nan bayan layi zan karbowa Mama saqo a gidan qawarta?" Ta sake fada, kamar yace Aa danbega dalilin da zata jera dashi ba se kuma ya miqe ko ba komai ya sake zagawa ya bawa idonsa abinci. Gwanin sha'awa suna tafe suna hira wadda Bintan ce take takalarsa har besab sanda ya ware ba yana maida mata har suka isa gidan qawar Maman ta shiga bata jima ba ta fito da Leda ya karba suka juyo. "Kace sunanka Abdulwahab suna me dadi ya akayi ka bari aka bata maka suna wai Audu?" Binta ta tambayeshi, yayi murmushi yace "Kinsan mu mutanen karkara ba kamar ku na birni bane" "Ai kai bakayi kama da mutumin qauye ba ko kusa idan ba an fada ba, ni da Dady yace iyakarka Sakandire ma nayi mamaki amma ya akayi ka iya turanci haka?" Ta sake jefa masa wata tambayar yayi murmushi yace "Kinsan ni ina da son kudi, da za'a kaimu Kano Almajiranci Abokina da yake karatun boko a can yace mun Malamansu sunce idan sukayi qoqari zasu tafi dasu ingila zasu samu kudi sosai, shiyasa dana shiga makaranta nafi mayar da hankali akan koyan turanci saboda idan naje ingila kinga bazan sha wahala ba na iya yarensu se daga baya na gane duk qaryace Ashe na watsar da Bokon na kama Kasuwa, amma Yayana da muka fara tare saura wata kadan ya kammala karatun Shari'a a Jami'ar Ikko" Binta ta ringa dariya jin abinda yace, tace masa "Wato Ingila kake so kaje, kaga ni kuwa ko yanzu naga damar shiga tikitin jirgi kawai zan yanke saboda inada katin zama yar qasa nacan" "Haba dai?" Ya tambayeta kamar be yarda ba dan shaf ya manta da Mahaifiyar Alhaji kakarsu kenan Baturiya ce. Binta tayi murmushi tace "Dagaske a can aka haifeni lokacin Dady yaje qara karatu kuma na zauna a gurin Mah seda ta fara rashin lafiya me muka da wo nan tare gaba daya harta rasu shekara goma kenan, idan kaima kana son zama dan qasar to ka Aurkjioieni Hawaii se Hawaiixna tafi dakai kaga shikenan zaka samu katin zama Dan Ingila" Tuntube yaci, badan Allah ya taimakeshi wani takalmin dafaffen danqo ne sauciki a qafarsa da idan ka ganshi zaka dauka na fata bane da yasan babu abinda ze hana faratansa ficewa yau dukda haka seda yaji zafi ya dage qafar dayayi tuntuben da ita yana kada hannu Ledar daya ruqo mata ta fadi Binta ta dauke tana masa sannu, seda ya daidaita kafin sukaci gaba da tafiya, ita da bata san dalilin tuntuben nasa ba taci gaba da cewa "Kaga shikenan ka zama baqin Bature, semuyi komawarmu can da zama dan ni daman nafi jin dadin can akan Nigeria, ko dan can nayi wayo shiyasa?" *MAMAN MARYAM ONLINE BUSSINESS* *Ina kuke Mata Yan kwalisa , Ina nufin isassun Mata ,Wai shin Kuna da labarin shahararren company nan namu na GHT wato good healthtreatments* *Wanda yazo muku da fitattu Kuma* *ingantatattun suppliment ,na dukkan matsalolin ku*❓ *Ina maisan tayi kyau,irin na isassun Mata ya fitar Miki da shef dinki tayi Miki gyara in and out ,nemi royal jelly dinmu na company GHT* *Wanda aka yishi da xuma ,kundai San amfanin Zuma basai na fada miku ba , hajiya ta kixo ki Yi gyara domin ki kerewa sa,a kije taro ko baki da ko sisi kiji Ana rangada Miki hajiya , saboda yanda Zaki Kara kwarjini ,kina walwali acikin mutane , magungunan ght anti agen ne suna maida tsohuwa* *yarinya ,yarinya Kuma ta koma jaririya* *Muna da magunguna iri iri* *NA GYARAN JIKI* *NA GOGE NANKARWA* *NA RAGE QIBA* *NA CIRE TUMBI* *NA QARIN HIPS* *NA GIRMAN BREAST* *NA QARA TSAHON GASHI* *NA QARIN NI'IMA WANDA ZAI SAUKAR MIKI DA NI'IMA YA QARA MIKI DADI DA ZAQI A GURIN OGA* *Muna da hadin bita zai zai ,indai kishiyar ki tana Shan magungunan GHT, tohh lallai sunan ki sorry domin kuwa tazarar dake tsakanin ku kamar tazarar sama ne da kasa* *Muna da Wanda zai matseki ciki da waje Andai na yayin dinki uwargida*, *Sannan company mu na GHTBai tsaya anan ba* *Ya kawo muku maganin dukkan matsalolin ku* *INA MASU HAWAN JINI?* *INA MASU CIWON ZUCIYA?* *INA MASU CIWON QODA?* *INA MASU CIWON HANTA?* *INA MASU SICKLER?* *INA MASU HIV?* *INA MASU CANCER?* *INA MASU NEMAN HAIHUWA?* *Tohh Ku matso GHT taxo muku da magungunan matsalolin ku* *Kuma muna da testimonys da yawa ,na wadanda suka gwada suka da ce* *Munanan a KANO KUNTAU* *Kuma muna tura Kaya ko wanne gari cikin aminci da gaskiya , kuma kayan mu muna badashi ne cikin price Mai rahusa ga kyau ga inganci sannan ga Rahusa* *Kutuntube mu ta wannan number 📞08129249549* *📲07011401314* Rasa abinda zece mata yayi dan ya rasa zolaya ce maganar tata ko kuwa har ranta da gaske take? Idan zolaya ce to irin wannan maganar gaskiya bata dace ba domin dai sanin sa ba'a wasa da maganar Aure, idan kuma da gaske take to abune bame yuwu ba kai qarya ne ma me zatayi dashi baqauye da besan komai ba dan talakawa ita kuwa yar gata jikar Turawa gata nan son kowa qin wanda ya rasa kai wannan qanzon kurege ne kawai ba abune me yuwu ba. Zuciyarsa ta tambaye shi to idan da gaske take shin ze amince ne ko kuwa? Seya rasa amsar da ze bawa kansa dan haka yaci gaba da shiru har suka isa gida Itama da taji yayi shiru seta bar maganar, a Get ya sake zama tayi masa godiyar rakiya ta shige ciki Malam Saminu ya shiga zolayarsa yana cewa "To kodai yar gida za'ayi da uwar masu gida da Baqon Alhaji?" Audu ya kalleshi bedai ce komai ba Saminun yaci gaba da magana yana cewa "Nayi mamakin yanda yarinyar nan ta shiga sabgarka, ka ganta nan sedauwar da uban suka tashi tsaye kafin ta saitu tabi hanyar kwarai farkon dawowarta saga Turai ma'aikatan gidan nan iska me dadi bama iya shaqa idan tana nan. Ta tsani Talaka a yanda take fada da bakinta ta kuma tsani duk wani abu da ze hadata da takauchi. Juma'a Juma'a Alhaji na sadaka a qofar gidan nan zaka ga an cika danqam haka zata fito ta watsa mutane tayi musu rashin mutunchi seda uban ya zaneta wata rana kuma da quruciya lokacin yanzun dai komai ya lafa dukda dai bazan ce ta bar halinta kaf ba amma ta rage sama da kaso Saba'in a ciki yanzu dai babu ruwanta damu idan kaga tayi rashin mutunchi to sabgarta ka shiga da muke taka tsantsan da ita kuwa lafiya lau ake zaune dama bata gaida mu bamu isa ba mu muke gaisheta kuma uban duk cikin Yaran yafi sonta shiyasa ma da Mahaifiyarsa ta karbi shahada ya bata irin sunan ta". Audu dai jinsa kawai yake sedai ko kadan be hango wani hali na rashin mutunchi da Saminun yace tana dashi ba domin kuwa tun zuwansa jiya tsaki kadai tayi masa wanda yanzu yake tunanin ma qila ba dashi take ba tunda gashi har ta nemi ya rakata guri sunje sub dawo suna hira idan da ta tsani talaka kamar yanda ya fada baya zaton ko kallo ya isheta tunda dai yasan Alhajin ya gaya musu inda ya sanshi, ya kuma kwatanta musu qauyensu to me ze saka tayi masa wasan ya aureta in har bata son talaka? Suna nan Saminu nata bashi labaran gidan Alhaji ya dawo, Audu ya rakashi har bakin qofar falo kafin ya koma masaukinsu yayo Alwala saboda magriba da aka kira. Sanda suka zauna zaman cin abinci ya sanarwa da Alhajin gobe da safe zasu juya Kano, gaba daya mutanen gidan suka nuna rashin jin dadinsu. Alhaji yace "Na dauka zakayi mana sati ko sama da haka? Ga tafiya da zanyi zuwa Rivers da ina cewa zamu je tare" Audu yayi qasa da kai cikin ladabi yace "Ai Alhaji saboda na baro abubuwa da yawa a can gidan kasan komai idan babu idon mutum ba lallai ayi yanda ya kamata ba" "Hakane ga iyali kam an baro kodan saboda su yaci a Koma" Mama ta dora abinda ya qara dagulawa Binta lissafi kenan farko damuwar tafiyar da yace zeyi ga kuma zancen iyali da Mama tayi. Miqewa tayi kamar jiya ta bar gurin, Alhaji ya kira sunanta ta tsaya "Lafiya Mamana baki gama cin abincinki ba zaki tashi?" Ya fada cike da kulawa, ta kwararrabe fuska tace "Dady kaina ne naji ya fara ciwo" "Ke kanki baya tashi ciwo se ana maganar Audu kenan" Mama ta fada tana hararar ta, ta juya ido tana kallon Audun tace "To ni ina ruwana dashi kawai kaina ne yake ciwo bari naje nasha magani" daga haka ta shige ciki Mama tace "Kyaji da gulmarki dai" Alhaji yayi murmushi yace "Aa fa karki saka mun Mamana a gaba" ya juya kan Audu dake juya cikalo a kan farantin dayaci abinci yau tuwo akayi ya kuma san saboda su ne yaji naman kaji da man shanu yace "Da zaka daure kayi satin da akwai dalilin da ya saka nake so ka zauna" Audu yayi jumm, baya so yayi masa musu dan haka kawai yace "Toh, Allah ya kaimu amma inaga zan tura Baballiya ya koma shi saboda Kasuwa" "Hakan yayi kyau" Alhaji ya fada. Tun a daren ya cewa Baballiya ya shiya dan Asubanci zasuyi Tunde ne ze mayar dashi kamar yanda Alhaji yace. Baballiyan ya ringa qunquni ya baqin rai amma da yake babu damar wargi dole ya hada yan komatsansa yana tunanin yanda ze koma yaci gaba da kwana akan Katifarsu ta gida me kama da Dakin din sumunti idan aka hadata data gidan yan gayu. Washe gari kuwa qarfe shida suka dauki hanya Bayan Alhaji da Mama sun hada masa sha tara ta arziqi da tsarabar da ze kaiwa su Bara'atu. Audu ya rubuta wasiqa ya bashi ya kai mata a ciki ya sanar da ita duk abinda ya faru da dalilin zamansa zuwa ranar da ze dawo. Shi yayiwa Tunde cikakken kwatancen zuwa inda yasan idan Baballiya ya gani ze iya kaisu gida kafin suka dauki hanya suna musu fatan sauka lafiya. A ranar tare suka fita da Alhaji gurin da yake aiki wato Matatar Mai ta Kaduna. Audu na zaune a office dinsa tsayin lokaci bayan Alhaji ya fita ya barshi sannan ya dawo ya same shi. "Na barka kai kadai ko? Meeting muka yi" Alhaji ya fada yana zama akan kujera, Audu yace "babu komai ina ta kallon Talabijin ma bansan lokacin ya ja haka ba". "Dalilin da ya saka na taho dakai saboda kaga gurin da nake aiki, ko ban fada maka ba kasan nan din ina ne, matatar Mai ce, itace Ma'aikata mafi girma da daraja da kuma kawo kudin shiga a Arewa baki tana kuma takewa ta Legas data fatakwat baya. Na so ace kayi karatu me zurfi ko da Diploma ce saboda a nan gurin takardar sakandire sedai a daukeka a matsayin lebura bawai babban Ma'aikaci amma dukda hakan bata baci ba, na dade ina so na bude gidan Mai a Kano, sedai rashin Ido ya saka ni daqile qudurin nawa amma yanzu dana hadu dakai ina ganin lokacin ne yayi ina so ka gwada harkar mai domin ana samun Alkhairi sosai da sosai a ciki" Audu yaji abin ya masa girma, domin a sanda yake bunburutu yayi bincike cikin sabgar yaso ya shigeta da gaske amma irin maqudan da aka karanto masa wai a talauce ze zuba a matsayin jari bashi dasu baya kuma tsammanin nan da shekaru goma ze mallake su sedai kuma lamarin ubangiji babu yanda baya zuwa se gashi ya samu tayin shiga harkar daga sama duk se ya rasa abinda zecewa Alhajin. Sunyi maganganu sosai, Alhajin yace masa idan ya koma Kano ya nemi guri da yake ganin zasu fara bude gidan Man ze hadashi da wakilai da zasuje tare da zarar guri yayi za'a fara aikin ba tateda bata lokaci ba domin tuntuni ya samu lasisin yin hakan Allah ne bai nufa ba se yanzu. Suka yita hira Alhajin yana fada masa yanda harkar take, sirrikan kasuwar da yanda ake tafi da ita dashi kansa abubuwan daya mallaka a ciki da wadanda yake shirin mallakar. Se yamma lis suka koma gida cike yake da murna yana hasaso yanda zata fashe nan da wani dan lokaci Audu ze zama manajan gidan Mai. Ya ringa hasaso nan da shekaru kadan shima ze mallaki nasa idan Allah ya yarda. Seda yayi sati cif kafin ya shiryi tafiya Kano tareda wakilan da Alhaji ya hadashi zasuje duba gurin da za'a assasa gidan Mai, a cikin satin kullum se sun fita da Alhajin haka yayi ta sakashi cike ciken takaddu, ana gobe zasu tafin kusan raba dare sukayi a tsakar gida da Binta suna hira wadda ke cike da Alhinin rabuwa da juna. Wata irin shaquwa ce ta qullu tsakaninsu, shidai Audu a bangarensa babu wani abu face ya dauki Bintan a matsayin qanwa kuma diyar mutum mai daraja a gurinsa da yake shirin canza rayuwarsa. Sedai ita ba haka bane a bangarenta, duk yanda taso hana kanta ta kasa tilas ta amince da tana qaunar Audun kuma duk sanda ta tuna haka se taji kamar ta rufe kanta da duka tsabar takaici. Bata san sanda haka ta faru ba, yaushe zuciyarta ta yanke mata wannan danyan hukunci dukbata sani ba kawai dai ta tsinci kanta dumu dumu a soyayyar Audu Bechi kuna ta gagara boye hakan ta nuna masa sedai sam yaqi nuna mata ya gane abinda ta ke ciki ita kuma ba zata iya karya bille ta zubda girmanta ta fada masa da fatar baki ba domin ta wuce da Ajin haka, zuciyace me aiki gaba gadi ta janyo mata ba tareda tayi shawara da ita ba koda yake bataga laifinta ba, Audun Namiji ne ingarma irin zabinta. Dukda cewar be yi wayewar Azo a gani bata tabbatar zuwa gaba za'ayi Namijin gaske musamman yanzu da ta fara hango haske a gobensa saboda yanda Dady yake tsamo tsamo cikin Al'amarinsa, a kuna dan zaman da sukayi yanda yake bata labarin Harkokin da yake tabawa ta tabbatar Gobensa zatayi kyau. A tsarinta kuma tana so ta auri Namijin da zasu ginu tare suyi Arziqi tare ta yanda babu wanda ze bigi qirji yayi mata kankanba akan sa. Haka ya tattaro ya dawo Kano, beko huta ba suka shiga neman lokashon inda za'a kafa gidan Man. A cikin kwanaki biyu aka samu, filin a bakin titi yake sukayi dace na Magada ne ana kan gabar yin rabo daman neman me siya sukeyi babu bata lokaci akayi ciniki suka karbi fili a bisa qololuwar darajarsa. Abinda ya qara bawa Audu mamaki hatta da Filin da sunansa aka yi takarda, be manta ba gidan man kansa Alhaji ya tambayeshi sunan da yake so ayi masa register dashi yace masa meze hana ya saka sunansa Zakariyya Paki amma Alhajin yace masa Aa, shiya bawa zabi daga qarshe BECHI ENERGIES akayiwa gidan man suna sannan ga fili an siya da sunan Audu. Cikin qasa da watanni biyar aka bude gidan Man wanda ya kasance na farko a Kano mallakin mutum ba kamfani ba, dangi yan uwa da Abokai sunyi masa murna. Yan Bechi duk sunzo bude gidan Man dukda yana gayawa kowa bana sa bane na ubangidansa ne, ya kuma debi ma'aikata harda Yayan yayyensa silar barowasu Bechi kenan suma. A taqin lokacin Audu yaje Kaduna babu adadi, soyayya ce ta qullu tsakaninsa da Binta wadda besan sanda shima ya afkawa soyayyar tata ba. Abinda ze iya cewa kawai Bintan tayi daidai da tsarinsa, kuma ita ta bashi fuska shiyasa beyi shayi ko jin dar na amincewa da buqatarta ba dukda ya kanga kamar abin bame yuwuwa bane amma tabbas yana son Binta kuma in har ya samu dama ze aureta. *MATAR MUTUM* *NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER* *MARUBUCIYAR* *WATA KISHIYAR* *RUBUTACCIYAR QADDARAH* *HALIN KISHI* *FIKRA WRITERS ASSOCIATION* *LITTAFIN KUDI NE* *PAY 400 (PROMO PRICE BAYAN KAMMALA FREE PAGES ZE KOMA 500) A ASUSUN* *7061838488* *OPAY DIGITAL SERVICES* *MARYAM FAROUK* OR *0709290797* *ACCESS BANK* *SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488* *IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705* *Kuyi following dina a Arewabooks @Maryamfarouk01 inda zaku karanta wannan littafin tareda sauran littattafaina* *NAGODE* *FREE PAGE 11* Kamar da wasa magana ta qullu tsakaninn Binta da Audu, da kanta ta sanarwa da Mahaifinta wanda yayi matuqar murna da Al'amarin saboda shidai Allah ya saka masa qaunar Audub a ransa tamkar dan cikinsa haka yaje jinsa. Mahaifiyar ta dai saisa saisa, bata nuna qinta ga Al'amarin ba haka kuma batayi murna ba saboda a ganinta Audun barene. Haduwar hanya bata isa tasa Alhaji ya daukake shi haka bayan aminta dashi akan dukiyarsa kuma yace zero dauki Yarsa mafi soyuwa ya aura masa ba. Yan uwanta kuwa kaf da sukaji take suka nuna qin Amincewarsu. "Allah ya sauwaqe, ke wace kalar wawiyace Binta? Kodai irin Asirin da yayiwa Dady duk ya rikice a kansa kema yayi miki? Daman qauyawan nan da surkulle suke wlh ban yarda da wannan Al'amarin ba Asiri yayi muku daga ke har Dadyn kuma dole mu tashi tsaye mu karya" Salima da take takewa Binta baya a fannin tsiwa ta fada aiko Bintan ta maka mata harara tace "Idan ma Asirin ya mun meye naki a ciki? Ke zaki aure shi ko kuma ke zaki zauna dashi? Da kika Auro Inyamuri waya ce miki qala seni da zan auri Bahaushe dan uwana. Ni bana fada muku dan ku yarda ko karku yarda bane kawai dai a matsayinku na yan uwana ya kamata ku sani Aure da Audu kuma babu fashi in sha Allahu" ta fada tana murguda baki. Haka aka ringa dauki babu dadi, sun nuna qin Amincewarsu qarara Jalal ne kadai da yake Namiji beqi abun ba dukda be nuna dokinsa a fili ba tamkar dai mahaifiyarsu amma da yake Bintan ta kafe kuma Alhaji yayi na'am haka aka qulla magana. A bangaren Audu kuwa sanda ya sanarwa da Yakubu da sukaje hutu maganar tashin farko shima ya nuna be yarda ba. "Haba Audu, daga ka fara samun duniya sakayyar da zaka farayiwa Bara'atu da ita kenan ta qarin aure? Karka manta sadaukarwar da yarinyar nan tayi maka. Kwata kwata ma shekarun mu nawa da auran matan namu nawa suke? A bariki fa sa'anninsu har yanzu suna gaban iyayensu ana musu kallon qananan yara kai ko me yasa ba zaka barta taci arziqin da kuka tara tare cikin kwanciyar hankali ba?" Yakubu ya fada. Audu ya karkace, shi fa a yanzu Jin Binta yake kamar daga sama aka yo masa wahayinta tsabar so. Ba wai ya dena son Bara'atu bane Aa, yanda Bintan ta iya magana da tattala Namiji idan yaje Kaduna har ya dawo Kano yayi satittika kafin ya sake komawa cike yake da bege da shauqin kalaman data ciko shi dasu. Ga tarin wasiqu datake rubuta masa masu dauke da kalamai masu gigita tunani, haka ze ringa dauka kullum yana karantawa idan sun qara ya ringa maimaitawa har se yaje ta sake hadoshi da wasu ya dawo yaci gaba da tisa karatun kalaman soyayya. Irin wadannan abubuwan yasa ya fara ganin baiken Bara'atu wadda bata san komai ba bata kuma iya komai ba se abinda ya koya mata ko ya nuna mata. Ya kasa gane banbancinta da Binta wadda ta kereta a shekaru, sannan ta bangaren wayewarsu babu hadi Binta haihuwar cikin Turawa girman Kaduna zagaye take da gogaggun yan Boko yan uwa da qawaye baya ga haka ita din tana cikin mutane da Allah yayi masu dan banzan wayo da iya magana. Duk dakiyar mutum tana iya canza masa akala a cikin ruwan sanyi yayi abinda take so ba tareda ya ankare ba. Tana da wayo kamar me, ga kissa kamar rainon Tsofaffi da wadannan halayen ta sake kanainaye shi yanda take nuna masa yafi kowa a duniya ya kai matsayin da shi da kansa yasan qaryane be kai dinba kambama shi kawai take amma da yake shi mutum nr me Izza da kuma son a girmamashi a yabe shi hawa yake ya zauna kan duk abinda ta fada baya ko tunanin Izgilanci take masa domin ta fishi ta kowacce fuska amma take nuna masa ita din banza ce akan sa. Gyara zama yayi ya kalli Yakubu da yayi shiru cikin mamakin abinda Audun yazo dashi yace "To amma da farko akwai haramci a cikin abinda nazo dashine? Naga qarin auran nan halal ne. Dafa ba'a qara aure da ba'a haife mu ba domin mahaifiyarmu a ta biyu taje gidan Baban mu sannan ita Bintar nan ka san komai game da Alkhairin da mahaifinta yayi mun. Kana kallon laimar Arziqin daya lulluba mun a cikin watanni kadan na damu abinda na shekara goma ina fafutuka ban samu ba meye aibu idan na karbi tukuicin auran yarsa wanda ita tayi mun tayin haka da kanta baka tunin zan zama butulu mara godiyar Allah idan nace zan qita? Tunda har su basu dubi matsayinsu da nawa ba suka amince zasu bani auran yarsu aikuwa ni bai kamata nace Aa ba kaima kuma be kamata kaqi abin ba domin Alkhairin da yake tattare dashi ba iyakar kaina ze tsaya ba gaba daya ya shafe mu. Kuma ni Bara'atu bani da matsala da ita, mun samu fahintar juna domin ban boye mata komai ba tun farkon maganar kuma ta amince dan haka yanzu abinda ya rage kawai zamuje can Bechi mu sanar dasu Yaya Baba idan yaso se a saka rana da zakuje ku nema mun auran. Ni yanzun duk bama wannan ya dameni ba, tunanin gurin da zan ajiyeta nakeyi". Duk yanda Yakubu yaso fahimtar da Audu abu yaci tura dole ya haqura tunda dai kamar yanda Audun ya fada abinda yake shirin yi ba haramun bane sedai shima ba qarin auransa ne baya so ba, Audu qaninsa ne kuma Aboki koma yace Amini, duk wani sirrin junansu sun sani yasan da cewar Audu baze iya zama da mace daya ba kuma irin Bara'atu saboda tayi masa kadan sannan a tsari na halitta har yanzu bata kai cikar da yake fata ba amma yaso ace idan ma auran zeyi ya nemo daidai dashi ko a can gida ko a nan cikin Kanon amma dai ya samu yarinya yar Talakawa irinsa da zasu yi zaman lafiya ba irin wannan aure daya gingimo ba. Shi gaba daya ma gani yake abin kamar da wani qulli ciki, tayaya mutum daga haduwar hanya ze ringa masa irin wannan hidima haka sannan har ya dauki ya ya bashi Aure bayan matsayinsa be wuci na me gadi ko share sharen gidansa ba. Sanda yayiwa Balaraba zancen yanda ta firgice seka rantse ita aka ce za'a wa kishiyar, ta ringa masifa tana Bala'i wa Bara'atu daga qarshe dai dole ta barta tunda ita da za'ayiwa kishiyar ko a jikinta ina dalilintana daukar dumi? A can Bechi ma haka Bilki ta ringa fada akan me Audu ze qara aure me Bara'atu tayi masa, amma tunda dai duk basu za'ayiwa kishiyar ba kuma me zama da ita tace taji ta gani dole suka haqura suka zubawa sarautar Allah ido. Anje an tambayowa Audu Aure, Yaya Baba, Hashimu da Aminu se Yakubu sukaje Kaduna bisa jagorancin Audu. Tarba ta mutunchi akayi musu, basu taso ba seda aka tsaida ranar Aure watanni uku masu zuwa suka dawo kowa na jinjina gidan da Audu yaje neman auran. Hashimu ya ringa yawo a gari yana cewa Auran kwadayi zeyi tunda gashi tun be aureta ba ubanta ya gina gidan mai ya bashi gaba kuma ba'asan me zeyi masa ba. Takanas ya samu Baban Bara'atu akan seya tursasawa Audu ya sakar masa yarsa domin qarshe boyi boyi zata zama a gidan daya auro wannan yar Attajiran Azabatar masa da Ya kawai zasuyi hankalin Inna Hajara ya tashi sanda ta samu labarin irin Amaryar da ake shirin yiwo wa yarta, takanas ta tashi qanwar Bara'atun ta turata tace idan ta samu sarari tazo Bechi tana son magana da ita. Haka kuwa akayi ta gayawa Audu yayi mata shiri kamar yanda ya saba duk sanda zataje gida ta tafi, Innarta ta ringa nuna mata qalubalen dake cikin auran da yake shirin yi amma se tayi murmushi tace "Duk hasashe kukeyi Inna kuma Audu yana qaunata na tabbata babu wata mace da ze aura da zata zarceni a zuciyarsa sannan ita kanta da kuke magana tana da kirki. Tun yanzu bakiga yanda duk sanda yaje seta hadoshi da abin Arziqi ya kawowa yara ba dani kaina kuma ya fada mun sam bata da matsala dan haka kuyi mana Addu'a kawai Allah ya bamu zama lafiya" da haka ta kashe bakin Innarta da duk wani dake shirin saka mata rudu a zuciya. Ba kuma wai bata damu ko kuma bata kishin Auran da Audun yake shirin yi ba, ta damu kwarai dan tana son mijinta, irin rawar qafar da yakeyi akan Amaryar tasa na daga mata hankali amma ta yarda da cewar Damuwarta ba zata saka a fasa abinda Allah ya hukunta ba sannan meye ribar ta tayar da hankali ta rasa mutunchinta da qimarta a gurinsa kuma daga qarshe yayi auran su zauna? Shiyasa ta maida komai ga Allah shi take roqo kullum dare da rana akan duk fitinar dake cikin aura Allah ya kade musu ita ya sanya zaman lafiya da fahimta a tsakaninsu kuma wannan haqurin da tayi da ake mata kallon wawiya ko yarinta ce take damunta ya saka Audun ya mayar da ita Abokiyar shawara akan duk wani abu da zeyi ko yake shirin yi. Daidai da zancen muhalli ita ya tuntuba akan yanda take ganin za'ayi. "Gurin saukar baqin gidansu kadai duk unguwar nan babu gida me kyau da tsaruwarsa, gaba daya abinda ya dameni kenan yanzu inda zan ajiyeta saboda kinga ko a shari'ance be kamata ace ka dauko Mace daga cikin daula ka muzguna mata a bangaren muhalli ku sauran buqatu ba" Audu dake faman lissafin kayan lefe ya fada, Bara'atu ta hadiye yawu tace "Gaskiya idan hakane kuwa ya kamata ace kayi mata tanadi na musamman domin nasan ba zata iya zama a cikin gidan nan ba" "A ina ma zan ajiyeta toh?" Ya fada yana kallonta, cikin iyakar gaskiyarta tace "Na dauka zaka toshe qofar tsakiyar dakin nan seka huda mata qofa ta wajene mu tashi da falle daya" Daya rasa abin ce mata kawai ya fashe da dariya, ya gama rubutunsa ya tattare takaddun ya fita. Daya tuntubi Yakubu zancen gida ce masa yayi "Ka sakata a bangarenmu kawai" "To ku kuma fa?" Audu ya tambayeshi, "Wannan ba matsala bane tunda kaga idan muka tafi yanzu se mun shekara ko fi kafin muzo, zuwa sannan se musan abinyi" Yakubun ya bashi amsa. Cike da rashin jin dadi Audu yace "Wai dagaske kake ba zaka zauna ayi Bikinnan kuna nan ba? Wai me nayi da yayi maka zafi har haka ka qullaceni?" "Bakayi mun komai ba Audu tafiya kuma ka sani ina shekarar qarshe ya kamata ace na ninka mayar da hankali akan Karatuna sannan itama Balaraba na gaya masa tana zuwa makaranta acan to sun koma kaga be kamatu daga farawarta kuma ta ringa wasa ba. Nidai abu dayane da yake damuna na rasa dalilin da sam auran nan be kwanta mun a zuciya ba, ina tsoron ka auro matar da zata wargaza maka zaman lafiya, ta gurgubtar da kyakykyawan tushen daka soma ginawa. Haka kawai nake jin baka dace da matar Aure ba Audu amma Allah shine masanin gaibu ina kuma yi maka addu'ar Allah ya kawai da duk wani abun qi daga hadinku". *MAMAN MARYAM ONLINE BUSSINESS* *Ina kuke Mata Yan kwalisa , Ina nufin isassun Mata ,Wai shin Kuna da labarin shahararren company nan namu na GHT wato good healthtreatments* *Wanda yazo muku da fitattu Kuma* *ingantatattun suppliment ,na dukkan matsalolin ku*❓ *Ina maisan tayi kyau,irin na isassun Mata ya fitar Miki da shef dinki tayi Miki gyara in and out ,nemi royal jelly dinmu na company GHT* *Wanda aka yishi da xuma ,kundai San amfanin Zuma basai na fada miku ba , hajiya ta kixo ki Yi gyara domin ki kerewa sa,a kije taro ko baki da ko sisi kiji Ana rangada Miki hajiya , saboda yanda Zaki Kara kwarjini ,kina walwali acikin mutane , magungunan ght anti agen ne suna maida tsohuwa* *yarinya ,yarinya Kuma ta koma jaririya* *Muna da magunguna iri iri* *NA GYARAN JIKI* *NA GOGE NANKARWA* *NA RAGE QIBA* *NA CIRE TUMBI* *NA QARIN HIPS* *NA GIRMAN BREAST* *NA QARA TSAHON GASHI* *NA QARIN NI'IMA WANDA ZAI SAUKAR MIKI DA NI'IMA YA QARA MIKI DADI DA ZAQI A GURIN OGA* *Muna da hadin bita zai zai ,indai kishiyar ki tana Shan magungunan GHT, tohh lallai sunan ki sorry domin kuwa tazarar dake tsakanin ku kamar tazarar sama ne da kasa* *Muna da Wanda zai matseki ciki da waje Andai na yayin dinki uwargida*, *Sannan company mu na GHTBai tsaya anan ba* *Ya kawo muku maganin dukkan matsalolin ku* *INA MASU HAWAN JINI?* *INA MASU CIWON ZUCIYA?* *INA MASU CIWON QODA?* *INA MASU CIWON HANTA?* *INA MASU SICKLER?* *INA MASU HIV?* *INA MASU CANCER?* *INA MASU NEMAN HAIHUWA?* *Tohh Ku matso GHT taxo muku da magungunan matsalolin ku* *Kuma muna da testimonys da yawa ,na wadanda suka gwada suka da ce* *Munanan a KANO KUNTAU* *Kuma muna tura Kaya ko wanne gari cikin aminci da gaskiya , kuma kayan mu muna badashi ne cikin price Mai rahusa ga kyau ga inganci sannan ga Rahusa* *Kutuntube mu ta wannan number 📞08129249549* *📲07011401314* Biki ya rage saura wata daya, ba qaramin raraka Audu yayiwa jarinsa ba ya hadawa Binta lefe na yar gata aka kai, be bar Bara'atu a baya ba dan itama seda yayi mata lefen dukda be kai na Bintan ba, ya kuma bada aikin sababbin Gado da kujeru daze chanza mata. Yakubu sun kwashe kayansu wanda Bechi ya aika dasu Bilki ta dauki Gado Aisha Kujera ragowar tarkacen yan uwa suka raba sun rabu da Audu akan ze nemi fili nan kusa a tayar masa da wani gini domin siyan bangaren Yakubun yayi dukda Yakubu yace Aa ai gida gaba daya na Audu ne dan da kudinsa ya siyi fili ya gina amma shi yace ba haka ba koda shi ya gina kyauta ce yayiwa Yakubun dan haka yanzun siya yayi kuma in Allah ya yarda kafin su zo Kano ze maida masa da wani. Ya tada gyaran gurin, anyi toshe toshe da liqe liqe, maginin gaske ya dakko Injiniya akayi masa aikin se ga guri ya fito fes an fitar da Sef cinten daki biyu da falo a tsakiya harda bandakin tsakar gidan aka shigar mata a daki se kitchen aka lailaye ko ina da Torazo gida dai ya fito na zamani a ganin ba za'a kushe ba dukda yasan dai a matsayin Bintan tafi haka amma ai ita tace taji ta gani ko a bukka ze ajiyeta zata zauna. Bara'atu ma ta samu arziqi an saka mata torazo a dakunanta dana su Abdullahi da tsakar gidan, Gadonta ta maida musu can aka saka mata sabon da Audu ya mata ga kujeru da kafet harda kayan Kallo se danqareriyar firiza duk a kayan fadar kishiya ita kuwa me ta manta? Audu nata doki da murna sanda yan uwan Binta sukazo ganin guri se kuma murna ta koma ciki. Babu kara suka ringa kushe gurin da yada maganganu akan an asirce musu yar uwa banda haka me Binta zatayi dashi balle har ta yarda ta zauna a gurin da ko Boyis kwatan su Albarka. Basu kwana a gidan ba kamar yanda ya shirya musu otal suka kama washe gari suka juya sukaje can sukayi ta cece kuce da fadar maganganu abinda ya saka Mamansu magantuwa kenan saboda yanda suka fasakta muhallin Bintan abin yayi muni. Tayi tsammanin yanda ya zage yayi lefe haka ze qerawa yarta gida kodan ya rage mata radadin auransa da bata so yar tayi, meye amfanin Kudin da Ubanta ya sakar masa domin tana da labarin qanin Kyauta yake bashi mai, idan an kai masa tanka goma kudin Biyar Alhajin yake karba haka tsayin shekara daya bata taba jin yace ga kudi Kaza na Ribar Mai da Audu ya kawo ba amma shine zeyiwa yarta wani Akurkin kaji a sakata a ciki. Cikin fushi da tari Alhaji da maganar, takanas ya tashi Tunde suka tafi Kano kwanaki biyu bayan komawarsu su Salima a sannan Biki ya rage saura kwanaki goma se ganinsa kawai Audu yayi ba zata. Shidai Alhajin bega aibun gurin da suka ringa fada ba domin a abinda ta rasa a gidansu baze wuce girma da kuma taswirar gini ba dukda haka domin gujewa duk wasu surutai na matar tasa da bata taba qalubalantar wani hukuncinsa ba yasan tayi kawaici matuqa akan lamarin auran tunda har ta magantu yanzu tabbas abin ya kaita maqura dan haka yacewa Audu "Me yasa baka sanar dani baka da gurin da zaka ajiye Mamana ba?" Audu yaji wani iri, wato shima ya raina gidan kenan? Amma dai a qarfinsa sunsan yayi abinda ze iya harma ya zarta. Shiru yayi bece komai ba gudun kar zuciya ta kwashe shi ya gayawa Alhajin mara dadi dan be gama hucewa daga fushin cin zarafin da Yayansa suka masa ba daman. "Ina ganin zan saka a duba gida ginanne idan yaso se a siya a sakata ciki ko ya ka gani?" Alhajin ya sake fada se sannan Audu ya daga kai ya kalleshi. Wato zancen Labahani gaskiya ne da yake cewa idan ka auri yar masu kudi rainin arziqi se abinda ka gani sannan su zasu ringa yi maka iko da gida to idan kuwa haka ne shi ba za'ayi akansa ba, baze bada qofa ba balle daga baya idan ya hana ace yayi Butulci. "Kayi haquri Alhaji ba ina nufin raini a gareka ba amma maganar gaskiya wannan ne muhallin da nake dashi da zan saka Binta a ciki. Ka sanni ka san Asalina haka itama tun gabanin tafiya tayi nisa a tsakaninmu tasan komai a kaina kuma ta yarda da hakan zata zauna dani a kowanne. Kayi haquri ka barni na ajiyeta a inda Allah ya horemun a yanzu, ina fatan zuwa gaba na gina mata daidai da tsarinta amma a yanzu abinda ya sawwaqa kenan". Badan Alhaji yaso ba gudun kuma karya takurashi yaga kamar ya masa kutse a cikin lamarin gidansa yasa ya haqura ya tafi kuma kamar yanda Audun ya fada ita Bintan taji ta gani dan ya zaunar da ita kafin a kawo kudin Aure ya tambayeta ta amice tace koda can Qauyensu ze kaita tana sonsa a haka zata aureshi. Haka akayi Biki Amarya ta tare, iyayenta sun zuba mata abinda dakin ze iya dauka. Danma kuma babu laifi ginin an fitar da dakunan da baga dan haka sun dauke gadajenta Biyu kantama kantama yan Dubai. Kujerune dai seda aka canzo ainin wanda aka siya mata saboda falon ya matse ga Divida bango guda yar waje kujerun ma irin bajaj din nan ne 1 sitter su takai girman two sitter matsakaitan kujeru dan haka suka matse matuqa dole aka mayar aka canzo mata wanda gurin ze dauka. Kwana biyu yan uwanta sukayi suka juya dalilin seda suka kaita Bechi wanda basu kwana ba ko banda ruwan gora da aka basu babu abinda suka iyaci na daga abincin tarbar Amarya yamma lis suka tada jaraba seda aka kaisu Kano gidan Amarya dan sunce ba zasu iya bacci a garin ba wannan Abu ya qona ran Yan uwan Audu ya ku.a darsa tsanar Binta a ransu duk da ba ita ta musu ba amma sun ce itama haka halinta yake kenan tunda bata hana yan uwan nata yar musu da magana da izgilanci ba Audu kansa ya qara hasala wannan karon dan haka babu wata sallamar Arziqi suka koma Kaduna suka yita fadar qarya da gaskiyar abinda ya faru na wai an aura masa ita buqata ta niya ya fara musu rashin mutunchi. Todai babu yanda suka iya aure ya qullu Amarya da Ango na son junansu sedai fatan a zauna lafiya. Sati gudan da Audu yawa Amarya Binta an barji soyayya irin wadda ya dauka a fina finan turawa kadai ake irinta. Baiwar Allah Bara'atu aikinta ta dafa abinci wanda take qure duk basirarta da abubuwan da Balaraba take koya mata idan sunzo tayi musu takai musu idan sunci ta debo kwanuka safe rana dare haka take wannan Bauta tsakaninta da Audu kuwa da safe idan ya dawo sallar Asuba ze shiga ya duba su shikenan se wata safiyar ko idan taje kai musu abinci baya fita ko ina yana daki suna barzar Amarci a haka ya kwashe sati dayansa gurin Amarya wadda zuwa sannan ba zatace ta mata wani abu ba tsakaninsu gaisuwa ce tana da Fara'a da kuma son yara dan kullum zata kira su Abdullahi ta basu abin dadi ita Bara'atun cema wani lokacin take hana su zuwa saboda karsu takurawa Babansu da kullum yana daka. Sati daya Audu ya tara su yayi musu nasiha sannan suka raba girki kwana bibbiyu kuma kowacce girkinta zata ringayi. Hakan yawa kowacce dadi, a falon Binta akayi zaman dan haka bayan ya sallame su Bara'atu tayi mata seda safe ta tafi. Yara duk sukayi bacci ta sake gyarawa tayi kwalliya da wasu kayan bacci da ta siya gurin Maman Kabir Maqociyarta saboda wannan rana. Tayi gyaranta daidai gwargwado na cikin jiki dana fata ga sabon kitso da lalle da tayi dukda kullum ta kalli Amaryar tata Da take Jajir ga jiki duk madara da tsoka se taji kamar Audu ba ze sake yi mata kallon Mace ba wannan tunanin ya sakata damuwa har tayi yar rama daman babu jikin se ta sake komawa yar yarinya firit da ita. Tana nan zaune falo tana kallon Tv da tsumayen Audu har bata san bacci ya kwasheta ba. Motsin rufe qofa ya farkar da ita, ta kalleshi kafin ta kalli Agogo, sha biyu da rabi a saninta tun Tara da mintina take zaune a gurin kusan awa uku kenan. "Bakiyi bacci ba?" Tambayar daya fara jefa mata yana shigewa cikin daki, ya gotata qamshin turaren Binta ya bigeta yanda kasan yanzu ya shafashi. Ta yunqura tabi bayansa tana cewa "Ina zaune bansan bacci ya kwasheni ba" ta dakata ganin harya kwanta. A tausashe tace "Har zaka kwanta bakaci abinci ba?" Fuskarsa washe da murmushi me kama dana rainin wayo yace "Au na manta qanwarki tace kiyi mata aikin gafara ta bani abinci". Tayi zukudi tana kallonsa kafin ta sauke ajiyar zuciya ta juya to me zatace? Kwanukan Tuwon shinkafa miyar gyadar datayi wanda ciki ta dibarwa Bintan iyakar cikinta dan tun da safe yace a gurinta zeci abincin dare yanzu kuma ya canza shawara yaci a gurin Amaryarsa "to Allah yasa ya ishe su" ta fada a fili tana Adana abincin a cikin Fridge duk Balaraba ce ta koya mata tace a can miyar sati takeyi ta saka abarta a firinji sedai ta dumama idan zasuci haka sauran abinci duk adanawa takeyi shiyasa itama tunda ya siyo mata ta fara wannan dabarar da yake koda yaushe da wuta hankalinta kwance yanzu bata rasa abinda zata bawa yara kafin ta gama abinci. Seda ta gama kintsa komai ta dauke Babannan da bata san sanda Abdullahi ya kawo mata shi falon ba dan ya saka rigima a gurinsu ze kwanta dukda bata yaye shi ba ta kaishi daki abin mamaki har Audu yayi bacci, jiki a sanyaye ta kwanta itama ranta cike da saqe saqe. Washe gari da safe tana hada abin kari ta jiyo sallamar Binta. Tun daga cikin kitchen din take jn tashin qamshin turarenta, gabanta ya fadi sanda suka hada ido. Kwalliyarta kamar me zuwa zaben sarauniyar kyau. Har qofar kitchen din ta qarasa fuska dauke da fara'a suka gaisa daidai nan Audu da gama wankan sa kenan ya shiga yana shiryawa dan yau ze fita aiki ya leqo haqoran nan a washe yana cewa "Aa, wa nake ji kamar Amarya da sassafen nan?" "Nice, na zo bikon Ango naji shiru har gari yayi haske baka leqa mu ba" ta fada cikin wani salo da ya saka Bara'atu sakin baki kwan datake soyawa akan wuta ya fara qauri yayi baqi kafin ta ankare ta sauke. Abdullahi da Babangida suka fito daga daki suka gaida Binta, ta karbi Babannan tana masa wasa ta shige falon Bara'atun suka barta tsaye a kitchen. A sanyaye ta gama soya kwan ta fara shigar musu da abin karin. Ta jere komai a tsakiyar daki na Audu daban se nata dana yara daban. Abdullahi ta fara hadawa shayi shida ze tafi makaranta ta zuba masa wainar kwansa da Biredi ya dauka ya tafi dakinsu Babangida ya bishi dan haka ta zuba nasa ta bisu dashi ta bar Audu da Binta dake zuba hirar da bama fuskanta take ba dan rabi turanci sukeyi. Tana dawowa ta tarar sun baje suna karyawa tare. Wani abu ya soketa amma ta daure "Kin ganni da kwadayi ko?" Binta ta fada tana mata murmushi seta girgiza kai tana murmushin yaqe itama. Nata abin karin ta dauka ta shigar daki ta dawo ta dauki Babannan dake musu didifniya yana shirin zubar da shayi suka shige ciki. Binta na zaune har Audu ya shiga ya qarasa shirinsa kafin ta rakashi har qofar gida ya fita, ta rasa ma me zataji, haushi ko mamaki ko me? Daga rakiyar Audu binta bata dawo ba bangarenta ta wuce. A sanyaye Bara'atu ta ringa ayyukanta saboda abinda ya faru daga jiya zuwa yau din. Da Asuba duk sun makara tashi shiyasa ma Audu be fita masallace ba. Daga gaisuwa wata magana bata hadasu ba ta fita hada abin kari shi kuma ya shiga wanka, tana Allah Allah ta gama idan sun zauna karyawar tayi masa magana Bintan tazo ta kasa ta tsare har seda ya bar gidan kudin cefane ma seda ta fito falo ta gansu a inda ya tashi ta daiji sanda yake ce mata gasu nan kafin ta fito kuma har sun bar falon to abinda take so ta fahimta shin abinda Bintana tayi da gayya ne ko kuwa dai tayine bada wata manufa ba? Kasancewar Audu baya dawowa cin Abincin rana yasa se gurin uku ta tashi dora girki. Haka siddan Babannan ya tasa mata rigima, Babangida ya tafi makarantar Allo wadda akeyi nan cikin layinsu gida uku ne tsakaninsu qiriniyarsa tasa Audu kaishi dukda be cika shekaru uku bama sannan amma da yake yana da barage kuma bakinsa ya bude shiyasa seka dauka ya wuce shekarunsa. Ta rasa yanda zatayi da Babannan din ta goyashi yaqi ta aje masa kayan wasa duk a banza ga aiki ta dakko dan Funkaso take so tayi da miyar Tantakwashi se Zobo da Balaraba tace mata duk in tayi girki ta ringa hada masa Lemo ta kuma koyi kala kala su Jinja harda wani farau farau me dadi idan yayi sanyi. Gaba daya kukan yaron ya hanata sakat gata ita bata iya aiki idan yaro yana mata rigima ba. Hijabinta ta zura ta dauki Babannan din da kayan wasansa ta doshi bangaren Bintan, qofar a bude dan haka ta shiga da sallama tana kallon wurin tana qara sha'awarsa, kullum tayi sallah se tayi addu'a Allah ya qarowa Audu budi itama ya maida mata da gurinta irin haka komai a ciki. Tayi sallama shiru ba'a amsa ba daga inda take tana jiyo tashin kidan turawa qila Tv ce qila radio ta kunna kusan sallamarta uku dan haka ta tura qofar falon da itama ba'a rufeta ruf ba ta shiga da sallama. Bintan na kwance kan kujera Idonta akan qofar ga Tv na aiki a ciki ake waqar da take jiyowa. Ta sake maimaita sallama tana fadada fara'arta, ba yabo ba fallasa bintan ta yunqura ta zauna tana kallonta ba tareda ta amsa sallamar tata ba. Kujrar dake dabda ita ta nufa da niyyar zama yanda Binta ta zaburo mata tana cewa "Karki zauna mun a kujera" ya saka ta dage da sauri har tana shirin yarda Babannan tayi saurin dafeshi tana kallon Binta data miqe tsaye fuska a hade tamkar wadda aka aikowa da saqon mutuwa. Follow this link to join my WhatsApp community: https://chat.whatsapp.com/I8xKHGurk7EBf5ZqQdxHKG *MATAR MUTUM* *NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER* *MARUBUCIYAR* *WATA KISHIYAR* *RUBUTACCIYAR QADDARAH* *HALIN KISHI* *FIKRA WRITERS ASSOCIATION* *LITTAFIN KUDI NE* *PAY 400 (PROMO PRICE BAYAN KAMMALA FREE PAGES ZE KOMA 500) A ASUSUN* *7061838488* *OPAY DIGITAL SERVICES* *MARYAM FAROUK* OR *0709290797* *ACCESS BANK* *SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488* *IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705* *Kuyi following dina a Arewabooks @Maryamfarouk01 inda zaku karanta wannan littafin tareda sauran littattafaina* *NAGODE* *FREE PAGE 12* "Karki zauna mun a kujera" ya saka ta dage da sauri har tana shirin yarda Babannan tayi saurin dafeshi tana kallon Binta data miqe tsaye fuska a hade tamkar wadda aka aikowa da saqon mutuwa. Kallon kujerar tayi dan ta gani ko wani abun cutarwa ne akai da ya sakata hanata zama amma bataga komai ba seta sake kallon Bintan dake jifanta da wani kallo data kasa fassarawa. Cikin kaushin murya tace "Meya shigo dake dakina?" Mamaki da Al'ajabi suka cika Bara'atu, ita Binta take tambaya me ya shigo da ita dakinta? Matar da idan tazo kawo musu abinci take nacin ta zauna suyi hira itace take ganin rashin dacewar zaman musu ta tafi amma yau take mata magana haka cikin zafi da gatsali, tsawar data sake buga mata ta maidata hayyacinta, Babannan ya fasa kuka dan shi baya son Hayaniya tamkar Yakubu ne ya haifeshi. Qofa ta nuna mata tana cewa "Fita, kuma wannan ya zama karo na qarshe da zaki tako qazaman qafafunki ki shigo mun daki, wato kinzo ki shafamun tsiya da talauci har da zaman mun a kan kujera? Wlh karki kuma idan ba haka ba sena banbance miki tsakanin aya da tsakuwa fita" ta qarasa cikin sigar bada umarni. Kamar kazar da qwai ya fashewa a Ciki Bara'atu ta fita daga dakin tama rasa tunanin da zatayi, to me hakan yake nufi? Haka ta goye Babannan yana kuka da komai ta shiga aikin Jiki babu kuzari ga rigimarsa ga mamakin Binta Allah ya taimaketa yayi bacci taje ta shimfideshi dukda yamma tayi taci gaba da aikin girkin. Bata samu ta gama ba seda aka kira sallar Magriba, su Abdullahi sun dawo dan haka shi ta hadawa wanke wanke yayi mata ita kuma ta kama Babangida da Babannan tayi musu wanka itama tayi, seda ta idar da sallah kafin ta shiga kwalliya. Tana zaune da yara suna cin abinci ita kuma ta zuraww Tv ido tana tunanin abinda ya faru tajiyo sallama daga tsakar gida, mamaki ya sake tiqe ta to me tazo yi mata kuma? Ko kuwa Tijarar da ta mata dazu ce bata isheta ba ta sake biyota nan? Tsoro da fargaba ya kamata, ta san idan dukane tsaf Bintan seta babballata ta zubar ita bama zata iya takalar fitinarta ba kamar yanda tace karta sake shigar mata daki in Allah ya yarda anyi na farko anyi na qarshe to akan me kuma ita zata biyota. Bata gama tunanin ba Binta ta daga labule ta shiga Falon, tayi kwalliya ta kece raini da Leshi ga qamshi tana bulbulawa fuskarta washe da fara'a ta sakeyin sallama. Kasa amsa mata tayi se kallonta da takeyi a dan tsorace harta zauna akan kujera Abdullahi ya gaisheta sannan ta kalli Bara'atun tace mata "Ina wuni Maman Baba? Ya yaran yau duk basu shigar mun ba" Tsabar mamaki Bara'atu seta hangame baki ta kasa ce mata komai, Binta na shirin sake magana suka jiyo sallamar Audu a tsakar gida, Yaran suka fita da gudu tararsa Binta ta sake qyara zama Bara'atu kuwa tama rasa ya take har ya shigo dakin. Fara'arsa ta sake fadada ganinsu duka a gurin, ya zauna a kan two sitter kusada Bara'atun yana cewa "Aa kace Uwargida da Amaryar duk suna nan me kuke tattaunawa haka?" "Sirri muke nida Yayata" Binta ta fada tana fari da ido, Bara'atu kuwa a salube ta zame qasa tana masa sannu da zuwa tare da gaishe shi ya amsa cikin walwala. A fakaice Binta ta galla mata harara, ta gani amma idon Audun be kai ba yana qoqarin ciro alawa daga Aljihunsa ze bawa Babannan. Cikin yauqi Binta tace "Barka da dawowa Ango, akwai idon yara da nayi maka maraba ta musamman" Wani abu ya sako qirjin Bara'atu, shi kuwa kamar wani gaula haka ya bita da kallo yana cewa "Allah ko, to ki ajiye mun bashi". Hawaye taji sun zubo mata tayi saurin sharewa tareda miqewa ta fice daga falon dan kawo masa ruwa. Wannan ai cin fuska ne, a dakinta a kuma ranar kwananta zasu ringa irin wannan maganganun daman haka akeyi ko kuwa nata Mijin da kishiyar ne suka raina mata wayo? Ta hado Ruwa da Zobo a Try daidai zata shiga dakin taji Bintan na ce masa "Ai nan na wuni, can din yayi mun shiru da yawa shiyasa na taho muka sha hirar mu ina tayata ayyuka se dazu babu jinawa na koma nayi wanka" "Kai amma naji dadi, Allah yaci gaba da hada kanku" Audun ya fada daidai nan ta kai ajiye Ruwan a gabansa mamakin Binta na neman ya sumar da ita. Tana ajiyewa tsulum Binta ta sakko tana cewa "Bari na tayaki" ta zuba masa Ruwan a kofi daya ta zuba zobon a wani kafin ta dauka duka biyu tana kallonsa da murmushi tace "Wanne zaka fara sha?" "Bani ruwan" ya fada ta kai masa Bakinsa babu shiri Bara'atu ta miqe daga durquson da tayi tunda ta ajiye kayan tabi bayan yaran da Abdullahi ya hada kansu suka fita, yaron nada hankali da tsinkaye. Baya taba zama ya tisa su gaba sedai idan ita ta kirashi ko Audun. "Haka fa ta ringa mun duk qoqarina na ta saki jiki dani taqi, ni kadai nayita surutu kamar lalatacciyar Radio se naga kamar bata jin dadin shigowar da nakeyi" Binta ta fada. Audu daya bi Bara'atu da kallo cikin ransa yana jin babu dadi ya kalli Bintan yace "Haka take bata da yawan magana, kije dakinki zan shigo idan na dawo" Yanayinta ya nuna bata ji dadin amsar daya bata ba amma da yake uwar kisisina ce seta wayance ta miqe tana cewa "Shikenan, da wai zan jira muci abincin dare tare kaga ci da yawan yafi dadi amma bari naje ko shayine na tafasa nasha kawai daman ba yunwa nake ji sosai ba" "To ki zauna idan munci abincin se ki tafi" Audu ya sake fada kafin ya miqe ya fita tsakar gida inda Bara'atu ke zaune daura da Kitchen ta zabga uban tagumi kamar wadda innarta ta rasu. "Nan kika zauna kuma? To ina ruwan wankana?" Ya fada yana tsayawa a gabanta. Ta miqe a sabule ta shiga Kitchen, ruwan sata jona ta dauko ta kai masa bandakin. Yabi bayanta suka shige uwar daka kamar Binta ta bisu kota fizgo Bara'atun haka taji, a ciki kuwa duk qoqarin Audu nason ta hada ido dashi taqi. Ta dauko masa Jallabiyyar da yake shiga wanka da ita da tawul din goge jiki ta ajiye kan Gado ta dauki kwandon sabulunsa ta fita dashi ba tareda ta kalli inda Binta ke zaune ba. "Nazo na tayaka?" Bintan ta fada cikin salon cusa takaici, taji diran abun amma bata tsaya ba seda ta dangana da bandaki, bata san meya ce mata ba se gashi ya fito yana dariya ya karbi kayan wankansa ya shige ita kuma ta juya dakin. Badan zata fidda masa kaya ba da a wajen zatayi ta zamanta. "Bakiga komai ba yarinya da qafarki zaki fita ki bar gidan nan" Bintan ta fada mata daidai zata shiga dakin, bata tanka ba a ranta ta ringa jan A'uziyya tana roqon ubangiji da yayi mata tsari da wannan matar me fuska biyu a haka Audu ya fito daga wanka ya tarar da ita a dakin buqui tana kallon qofa tayi zurfi cikin tunani. "Maimakon kije falon kuyi hira da yar uwarki kin barta ita kadai da Tv me yasa kike haka? Ita bata ji qyashin tazo inda kike ba kece zaki daure rai kuka kiqi kulata? Bana son irin haka kije ku zauna tare kafin na fito" Audu ya fada yana kallonta, "Kayi haquri" ta fada muryarta na karyewa kafin ta miqe tabi umarninsa. Kamar ba dakinta ba haka ta samu guri ta rabe ita ko hamshaqiyar ta bararraje akan kujera tana jefa masa hira yana amsawa daga cikin daki seta fadi abu tace da Bara'atun "ko ba haka ba Maman Baba" ita dai ta zama kurman dole. Ya gama shiri daidai nan aka kira sallar Isha Audu ya fito Binta ma ta miqe tana cewa "Bari naje nayi Isha se na dawo" "Nima fita zanyi" ya fada suka rankaya suka barta nan zaune tana ajiyar zuciya. *MAMAN MARYAM ONLINE BUSSINESS* *Ina kuke Mata Yan kwalisa , Ina nufin isassun Mata ,Wai shin Kuna da labarin shahararren company nan namu na GHT wato good healthtreatments* *Wanda yazo muku da fitattu Kuma* *ingantatattun suppliment ,na dukkan matsalolin ku*❓ *Ina maisan tayi kyau,irin na isassun Mata ya fitar Miki da shef dinki tayi Miki gyara in and out ,nemi royal jelly dinmu na company GHT* *Wanda aka yishi da xuma ,kundai San amfanin Zuma basai na fada miku ba , hajiya ta kixo ki Yi gyara domin ki kerewa sa,a kije taro ko baki da ko sisi kiji Ana rangada Miki hajiya , saboda yanda Zaki Kara kwarjini ,kina walwali acikin mutane , magungunan ght anti agen ne suna maida tsohuwa* *yarinya ,yarinya Kuma ta koma jaririya* *Muna da magunguna iri iri* *NA GYARAN JIKI* *NA GOGE NANKARWA* *NA RAGE QIBA* *NA CIRE TUMBI* *NA QARIN HIPS* *NA GIRMAN BREAST* *NA QARA TSAHON GASHI* *NA QARIN NI'IMA WANDA ZAI SAUKAR MIKI DA NI'IMA YA QARA MIKI DADI DA ZAQI A GURIN OGA* *Muna da hadin bita zai zai ,indai kishiyar ki tana Shan magungunan GHT, tohh lallai sunan ki sorry domin kuwa tazarar dake tsakanin ku kamar tazarar sama ne da kasa* *Muna da Wanda zai matseki ciki da waje Andai na yayin dinki uwargida*, *Sannan company mu na GHTBai tsaya anan ba* *Ya kawo muku maganin dukkan matsalolin ku* *INA MASU HAWAN JINI?* *INA MASU CIWON ZUCIYA?* *INA MASU CIWON QODA?* *INA MASU CIWON HANTA?* *INA MASU SICKLER?* *INA MASU HIV?* *INA MASU CANCER?* *INA MASU NEMAN HAIHUWA?* *Tohh Ku matso GHT taxo muku da magungunan matsalolin ku* *Kuma muna da testimonys da yawa ,na wadanda suka gwada suka da ce* *Munanan a KANO KUNTAU* *Kuma muna tura Kaya ko wanne gari cikin aminci da gaskiya , kuma kayan mu muna badashi ne cikin price Mai rahusa ga kyau ga inganci sannan ga Rahusa* *Kutuntube mu ta wannan number 📞08129249549* *📲07011401314* Alwalar ta fita ta dauro itama ta leqa dakinsu Abdullahi Jin shirunsu yayi yawa ta tarar da Babangida da Babannan sunyi bacci se Abdullahin yana duba takaddun makarantarsa. "Ashe bacci sukayi?" Ta fada tana gyarawa Babangida wuyansa daya karkace "Eh umma, muna gama cin abinci duk suka kwanta" Abdullahi ya bata amsa. Ta sabi Babannan tana cewa "Ai gara suyi baccin, shi wannan da yayi wunin kuka daman dole yau yayi baccin wuri. Ka tashi kaje masallaci yau Baban naku ya manta ya tafi ya barka" daga haka ta wuce daki. Seda ta gyarawa Babannan inda ze kwanta tayi masa shimfidar Fitsari kafin ta tayar da sallah. Harta idar da shafa'i da wutri ta zauna zaman lazumi babu Audu babu labarinsa har ta jiyo an fara labaran qarfe tara abinda ya saka ta shafa addu'arta ta fito tsakar gida kenan ta leqa Abdullahi taga harya kwanta shima ya kashe musu fitila alamar ya dade da dawowa kenan. Mamakin inda Audu ya tsaya takeyi, duk zamansu daga sallar Isha baya zuwa ko ina a gida ze zauna suyita hira har lokacin bacci yayi kuma da Binta tazoma be fasa ba daya dawo daga Isha ze garqame qofar gida to yau ina yayi kuma. Zaure ta leqa, mamakinta ya ninku ganin qofar a kulle da sakata, ya shigo har ya kulle kenan to ina ya shiga "Gurin Amaryarsa mana" zuciyarta ta bata amsa. Gabbanta suka qara yin sanyi ta koma ciki tana ayyana wato wannan ne abinda mutane sukayita hango mata amma wauta da yarinta ta hanata fuskanta, so da yardar da tayi da Audu yasa bata taba hasaso ze iya wofantar da ita akan wata mace ba koda yake Amarya ance kota Kare ce ana dokinta sedai shi nasa zirgillin yayi yawa bata tsammanin haka sauran maza da suka qara aure sukeyi tun ba'a je ko ina ba su fara nuna da uwargidansu da bola babu banbanci a gurinsu. Yunwar data kusan wuni da ita tana aikace aikace ta sakata zuba funkason ta shiga ci badan dadi ba sedan maganin yunwa zuciyarta cunkushe da tunani. Wa zata kaiwa kukanta ya bata mafita dan ita a iya wayo da dabararta bata san me zatayi ta kaucewa afkawa wannan wawakeken ramin dake a gabanta ba. Makirci da tuggun da Binta ta tsiro dashi ga kuma megidan dataga alamar sam ba zasu daidaitaba. Domin bashi da fahimta, ta sani a koda yaushe hasashe da maganarsa itace daidai babu ruwansa da jin bangare domin yin alqalanci akan abu wannan halin ko akan yaran yana gwadawa duk wanda ya fara kawo masa qara yakan bashi gaskiya ba tareda ya tsananta binciken bin ba'asin ainihin abinda ya faru ba ta sani yanzu koda zata fada masa abinda Binta tayi mata a bayan idonsa baze taba yarda ba, tunda bata san meta gaya masa dazun da har yake mata fadan ta barta ita kadai zaune ba. Ta gama cin abinci ta matsar masa da nasa gefe ta fita da kwano ta daurayo bakinta kafin ta shiga shirin kwanciya itama. Tana tsaka da shafe jikinta da Addu'a ya shigo tayi saurin jan bargo ta rufa har kai a zuwan bacci take tana jinza yana kiran sunanta taqi amsawa saga kwancen da take tana iya shaqar qamshin turaren Binta tamkar jiya, wani abu me daci ya taso mata se hawaye suka shiga zubar mata ya fita daga dakin yana cewa "Har kinyi bacci bari naci abinci toh" Siririn kuka ta saki murya bata fita. Wannan wani irin abu ne? Sati daya da qara auren har zata fara karbar wannan wulaqancin haka, jiya be shigo da wuri ba da safe tazo ta kasa ta tsare bata barsu ko gaisuwar kirki sunyi ba sannan yanzu ta janye shi se yanzu ya dawo shin shi be san abinda yakeyi babu kyau ba idan ita tanayi da gayya da mugunta ne shi ya kamata ya biye mata su shiga haqqinta? Tana sharar hawaye ya gama cin abincinsa da duk uzurin da zeyi kafin ya kwanta a bayanta. Wani kuka ya sake taso mata sanda ya jata jikinsa tana jin qamshin turaren Bintan a ainihin fatarsa da alama jiki suka hada. Ya dade yana koya mata abubuwa wanda se tayi da gaske take iya maida masa da martani saboda kunya yau kam bata da qarfin jiki dana zuciyar da zata kulashi. Tana jinsa yana zabga tsaki bayan daya samu nutsuwa, be ko jira ta saka musu ruwan zafi ba ya fice ko ya dumama koda na sanyi yayi oho ita dai seda ta fara jin saukar numfashinsa alamar bacci ya kwashe shi kafin ta fita ta saka ruwa tayi wankanta. Tunanin abinda ya sakashi tsakin ta ringayi, duk sharrinsa bazece yaji wani abun daban tattare da ita ba saboda gyara gangariya Innarta tayi mata ruwan Ni'ima har diqa yake a jikinta kuma ko yanzun dukda jikinta be wani karbi abinda ya mata ba amma tasan taba da ruwan da ze bashi duk nutsuwar da yake nema to kodai shirun data masa ne ya bashi haushi dan yasha gaya mata baya so tana barinsa yana abu shi kadai. Da safe ma haka ya fita yana faman daure dauren fuska, qarfe biyar na yamma Babangida ya shigo da Biskit yace mata Babansa ne ya bashi ta tambayeshi yana ina yace yana dakin Amarya, be leqasu ba seda ya dawo daga sallar isha shima daga bakin qofa yayi mata seda safe ya juya daman ko qyallin idon Binta bata gani ranar ba. Haka al'amura suka cigaba da gudana, a watanni biyu da auran Binta Bara'atun ta fita hayyacinta seka dauka jinyar shekara tayi saboda rama da baqin da tayi. Wani irin zama sukeyi mara kan gado, Audun gaba daya kamar wanda aka sakawa hannu ya fita a sabgarta tsakaninta dashi idan yana dakinta gaisuwa ce se ranar dayayi sha'awar kulata a shimfida yayi bayaga wannan idan kaji yayi doguwar magana da ita to qorafinta Binta ta kai masa yazo yanayi mata fada wanda bata iya ce masa komai illah ta bashi haquri, to ba se ta aikata abinda ake ce masa tayin ba sannan ne har zata kare kanta. Wata irin annamimiyar matace Bintan, rashin mutunchi da Tijara se kalar wanda ta manta ne batayi mata a gidan da zarar Audun ya fita yamma nayi ta daidaici lokacin dawowarsa idan yana dakin Bara'atun kenan kuna zata sheqo wanka tazo ta kame mata a falo harya dawo sannan ta hillace shi su tafi se sanda ta ganshi a hakan kuma ze zo ya rufeta da fadan Binta tace tayi mata kaza ko tace mata kaza babu bin ba'asi babu tambayar ya akayi yanda kasan wanda Bintan ta wanke gabanta ta bashi yasha haka yake shakkarta yake jin maganarta. Ita kuwa Binta daman a shirye ta shigo gidan Audu, bata tsarawa kanta zama da kishiya ba dan haka ta shirya ta kuma tsara komai yanda zata ringayiwa Bara'atun gashin quma har se ita da kanta ta fita ta bar mata gida. Sanda tazo taga yar yarinyar a matsayin matar Audun ma abin dariya ya bata tasan ba zata sha wahalar kada taba, tayi amfani da nakasun Audun tayi galaba akansa. Ta karanci shidin mutum ne me son a riritashi, kalar soyayyarsa da wayewarsa har mamaki abin yake bata tamkar wanda ya tashi cikin Turawa ko wasu gogaggun mutane shiyasa take qure basirarta ta tabbatar da ta tashi kansa da nata salon wayo da dabarar. Da baki kadai idan ta zauna ta ringa tsara masa zance baya sanin sanda yake aikata duk abinda ta sakashi ta kuma fahimci Bara'atun wawiyace babu abinda ta sani se Biyayya wa Audun kamar zata kwanta masa irin abubuwan da Bintan take masa yasa gaba daya ya raina Bara'atun dan qoqarinta da yake gani a baya duk ya disashe, a yanzu kuma da damuwa tayi mata yawa tasa abinda take iya tabukawar ada ma ta dena Shiyasa ya fita a sabgarta. A ganinsa baqin kishi ta saka a ranta shiya hanata walwa ta takura kanta shi kuwa bashi da lokacin da ze zauna yana lallashinta ko tambayarta me take so tu da dai be tauyeta da komai ba yanzu da budi ya qarar masa ma jin dadi da abubuwan mora rayuwa sedai suyi Kyautarsu amma dukda haka a maimakon ta saki ranta taci arziqi Aa se rama take tana qara qarmashewa tana ja masa zagi dan duk wanda ya ganta se ya zargi wani mugun abun sukeyi mata da ya saka ta fita hayyacinta. Bara'atu bata sake shiga uku ba seda Binta ta fara laulayi, duk wata hidimar Bintan kanta ta koma bisa umarnin Audu, haka zata kwanta kamar ruwa idan yana gida tayita malele kuwa ita a dole ciwo take daidai da dan kamfai idan ta cire Bara'atun ce zata wanke mata girki kuwa se tayi kala uku a rana kuma taqi ci idan ya dawo tace masa ai ta fada mata abinda take so taci taqiyi haka ze hau kanta da fada da bala'i baiwar Allah sedai tayita kuka tana kuma kaiwa Allah kokenta gashi ya hanata zuwa Bechi a fadarsa idan ta tafi waze kula da Binta tunda shi yanzu sabgogi sun masa yawa dan har tafiye tafiye ya fara. Wannan bala'i yasa ta qara figewa tayi zuru zuru. Ana haka ya tada zancen gyaran gida saboda ya samu isassun kudin da zasu gina masa abinda yake so. Sunyi shawara da Binta akan Bangaren Bara'atu za'a rushe tunda shine gefen hanya zefi kyau ya zama fuskar gida dan haka ya samu Bara'atu da zancen murna kamar ta fasa ihu sanda yace mata zata tafi Bechi ta zauna na wani lokaci kafin a gama gyaran gidan, a cikin sati daya suka tattara ita da Yaran suka tafi Bechi, cikin bangaren Yakubu na da suka zauna wanda Audun ya saka aka gyare shi daman idan sunje can suke sauka nan fa gulma ta ringa yawo a gari kan cewar auren ta ne ya mutu. Ramar da tayi ta qara bawa mutane abin fadi aka ringa yawo da zance kala kala kowa da irin abinda yake fadi. Hankalin Bilki ya tashi da ganin Bara'atun, ita kadai ta iya budewa cikinta ta fada mata halin da take ciki a gidan dan uwanta dan hatta da Innarta duk yanda tayi da tasan me yake damunta qin fada mata tayi kawai tace mata rashin lafiya tayi amma ta samu sauqi. Ran Bilki ya baci da labarin da Bara'atu ta bata, ta ringa fada qarshe ta dora mata laifin cewar koma menene ita ta jawa kanta da tun farko ta basu damar yi mata rashin mutunchi. "Akan me zaki zauna kinemi ki kashe kanki da damuwa? shi Yaya Audun mala'ika ne da bazaki iya kallinsa ki gaya masa abinda yake ranki ba. Kin zauna kin bari zuciyarki ta cika da tsoro mara dalili kina cutar da kanki to wlh idan kika cigaba da wannan salibancin kina ji kina gani seta rabaki da gidan kamar yanda ta fada" Bilkin ta fada cikin qunar rai. Zamanta a Bechi se yafi mata kwanciyar hankali da nutsuwa, a qasa da wata daya ta fara maida jikinta ta murmure to bata da matsalar komai, ga kayan abinci nan jibgi ya ajiye musu haka kudin kashewa ya bata isassu tayi bacci cikin nutsuwa ta farka tayi abinda zatayi ta fita gurin Goggo Fadi suyi hira da Amaryar da Aminu yayi ya ajiyeta nan suke zaune tareda Goggo Fadin saboda qafa data sakata a gaba, idan kuma taji marmarin fita ta tafi gidansu ta wuni can dare yayi ta koma gida a haka suka ci wata daya sannan Audu ya je musu kwanansa biyu ya juya haka kuma yaci gaba dayi duk qarshen wata zeje yayi musu kwana biyu har suka shafe watanni hudu a Bechi. A bangaren Audu da Binta kuwa filin gida suka samu suna zuba sharafin soyayya babu kama hannun yaro. Ginin daya tayar kuma yayi nisa, ginin Bene ne akeyi na zamani taswira me kyau da qawatarwa qasan na Mandiya Binta ne se Benen da aka dora da zata zama turakar me gidan bangaren da Bintan take ciki yanzu kuma ya barshi akan Bara'atu seta koma can dukda Binta a ranta ta quduri cewar Bara'atun ta tafi kenan ba zata dawo mata cikin gida ba. Kwana biyu da yake zuwa yi musu qarshen wata seda yayi da gaske Binta ta barshi, Allah ya sani bawai baya son Bara'atu bane Aa mugayen halaye data tsiro dasu ne suke bashi a ganinsa Kishi ne yake damunta ya hanata walwala. https://chat.whatsapp.com/I8xKHGurk7EBf5ZqQdxHKG *MATAR MUTUM* *NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER* *MARUBUCIYAR* *WATA KISHIYAR* *RUBUTACCIYAR QADDARAH* *HALIN KISHI* *FIKRA WRITERS ASSOCIATION* *LITTAFIN KUDI NE* *PAY 400 (PROMO PRICE BAYAN KAMMALA FREE PAGES ZE KOMA 500) A ASUSUN* *7061838488* *OPAY DIGITAL SERVICES* *MARYAM FAROUK* OR *0709290797* *ACCESS BANK* *SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488* *IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705* *Kuyi following dina a Arewabooks @Maryamfarouk01 inda zaku karanta wannan littafin tareda sauran littattafaina* *NAGODE* *FREE PAGE 13* Gini ya kammalu har Binta ta tattara ta koma sabon bangarenta. Sababbin kayan daki Babanta yayi mata jere na garari irin wanda ba'a samu filin yi a wancan dakin ba se yanzu saboda wannan me yalwa sosai akqa debe su dan har rabin Filin maqocinsu da suke jingine ya siya ya shigo dashi shiyasa ta samu maka makan dakuna biyu ga Falo da kitchen da store, an rushe katangar tsakiyar bangarorin gidan ya hade se ya sake tada daki babba a tsakar gida guda daya aka kumayi Kitchen shima na tsakar gidan se Bandaki. Tsaf aka fente ko Ina har inda Bintan ta tashi dukda babu abinda gurin yayi amma yaga be kamata Bara'atu ta shiga a haka ba. Ya sake aiya mata gado daya tunda daya take dashi nan kuma daki biyu ne yasa aka kwaso kayanta ta aka ajiye a store din gidan Alhaji Idi gidan qawarta qwara daya duk unguwar, da ita kadai ta iya sakewa ragowar dai idan sabga ta tashi aka gayyaceta zataje amma bata shiga gidan kowa suma tun suna shigo mata ganin bata sakewa yasa suka bari. Binta na zuwa suka ringa shishige mata duk suka zama yan korarta dan ta wuce da Ajin ace qawayenta ne, amma da yake yawancinsu gulma ce wasu kuma kwadayi ya sakasu neman qawancen haka suke jure duk izgilancinta suna manne da ita. Ranar da aka maido kayan Bara'atu Binta bata tare suka fita da Audu ya ajiyeta a Gadon qaya dan ya siyi mota a tsukin. Gidan wani sabon Abokinsa Mustapha shima harkar Mai yake dan haka yanzu Audun yana mu'amala sosai da su dan qungiya guda garesu. A Asibiti suka hadu da Matarsa Baturiya gurin awo, hali yazo daya aka qulla qawance. Se daga baya suka fahimci sudin matan Abokanai ne shikenan zumunchi ya qullu har ta gabatar da ita ga sauran matan Abokanan mazajen nasu dan suma guruf suke dashi kowacce naji da kanta Mijinta hamshaqi. Data dawo gidan bata ma lura da an zuba kaya ba tunda qofar a kulle take, taci gaba da sabgoginta. Washe gari Audu yace mata gobe zeje Bechi. A fili tayi masa fatan zuwa da dawowa lafiya a zuciyarta kuwa tace "A haka dai Auran ze balbalce badai ta dawo gidan nan ba". Da Asuba bayan sun tashi kuma yace mata ta shirya kayanta kala biyu su tafi tare saboda duk sanda yaje se yan uwansa sunyi qorafin rashin zuwanta kuma ya manta Gobe daurin Auran Saleh Yaron Yaya Baba na Biyu. Rabonta da Bechin tunda aka kaita tana Amarya se zuwa daya da sukayi gaisuwar rasuwar Wan Baban Bara'atu shima a tsaitsaye ba kwana tayi ba watanni takwas kenan. "Yanzu a sanyin nan kake so na tafi qauye?" Ta fada tana kumbura baki sanda yace ta shirya din, Audu ya kalleta yace "Gida fa zamuje ba Jeji ba balle kice zakiji sanyi. Yaushe ma rabonki da can? Karki manta Bechi tushe na ne. Badan iyayenmu basu da rai ba kin san baki isa ki kwashi wata daya ba ba tareda munje kin gaishe su ba, ko yanzun ayyuka ne suke shan kaina su hanani zuwa ziyara akai akai amma ina ganin zan nemi direba wanda ze ri ga kaiku duk hidima Biki ko suna be kamata ace kuna qin halarta ba tunda ba kullum bane sannan tunanin da nakeyi zan gyara gidan mu nacan duk sallah mu ringa tafiya munayi tareda yan uwa" "Tabdi" ta fada a ranta, a fili kuma ganin yanayin da yayi maganae kamar ransa a bace yake yasa tace masa "Nima bawai ina nufin wani abu bane kawai dai saboda cikin jikina kaga ya girma be kamata na ringa dogayen tafiye tafiye ba" "Kwananki nawa da dawowa daga Kaduna? Bechin ta kai nisan can ne? Ko da qafa zaki tafi? Kinga karki bata mun rai idan ba zakije ba ki zauna" ya fada yana ficewa daga dakin. Ita da take neman hanyar da zata kama shi a hannu ina ita ina neman fitinarsa shiyasa ta tashi ta shiga shirya kayan kamar yanda yace a ranta kuma tana ayyana irin abinda zatayi idan taje. Ta tsani qauyen da mutanen cikinsa. Su ba kowan komai ba se Izza da girman kai ya yayan Sarakai wannan shegiyar Bilkin ko nan Kanon tazo haka take mata rashin mutunchi Audun na kallo ba zece komai ba ti duk zatayi maganinsu. Ta shirya kala biyun kamar yanda yace sannan ta kwashi kayan shayi, Biskit da cincin din da Mero matar da ta samo tana mata girki tayi mata harda dubulan se Sauran Miya duk ta hada kamar me zuwa wata qasar. Audu be shigo ba se gurin takwas lokacin har tayi wanka ta karya da Mairo da Lantana ita kuma share share take mata duk da suka zo cewa tayi su tafi se bayan kwana biyu zasuje qauye. Ganin ta shirya ya saka shima shiga wanka a gaggauce ya shirya suka kulle gidan suka tafi. Sun isa Bechi ana ta hidimar daurin auren da za'ayi washe gari. Gaisuwar ma kamar sun roqa haka tayiwa wanda taga zata iya. Wadanda ta raina kuwa ko kallon Arziqi basu samu ba. Bara'atu na cike da murnar zuwan Audu sedai ganinsa da Bara'atu ya saka duk karsashin ya barta, gabanta ya ringa faduwa dan ita tsoronta takeyi ko kuma tace tsoron kaidinta. Ita wlh daze barta a nan Bechin yaci gaba da zuwa koda ba duk sati ba zata yarda. A zaman da tayi harta murmure tayi tas abinta babu damuwar Miji babu ta kishiya kuma idan yazo mata kwana biyun sosai yake tarairayarta yana riritata sabanin a Kano da a suna ne kadai take da girki dan ko Binta ta barshi ya kwanta a dakinta to fa ba zasuyi bacci zur ba tareda tazo ta tashe su ba da sunan ciwo na damunta wanda se a ranakun girkin Bara'atun take ciwo. Audun da kansa yake ce mata idan a can yake watara ta kwanta ko farkawa batayi se Asuba. A dakin Bara'atun Binta ta sauka kamar yanda ya tsaya. Ta haye mata gado tunda ta zauna Sallah kadai ke saukar da ita abinci da duk wasu tarkace dataci nan ta zubar sedai ta matsa gefe ta miqe qafa tana hura hanci mutane na tsakar gida ana hidimar girkin gobe, lokaci lokaci Bara'atu na leqata taji koda abinda take da buqata shara kuwa tayi takai sau biyar daga zuwansu Bintan. Tavi gyada, tasha rake taci goruba duk akan zanin Gadonta na kwalliya data shimfida mata saboda karramawa gashi me haske amma haka tayi daqal daqal dashi kamar yarinya dole ta canza wani da Bintan ta fita yin Alwalar Magriba. Bayan tayi isha ne ita da kanta zaman dakin ya isheta dan haka ta fita tsakar gidan tana Kallon Faccalolinta dake hada miya suna hirarsu gwanin sha'awa. Babu wadda tabi ta kanta tubda suka zo se Laure uwar gidan Hashimu ita ta ringa shishshige mata ta kuwa yi mata qusa daga nan itama ta kama kanta. Can qofar dakin Sauda Amaryar Aminu ta zauna kan Tabarmar da aka shinfida, Bara'atu na kai tana bawa Babannan tuwo Goggo Fadi na daga qofar nata dakin itama kaca niyar tukwane da mata ta cika gidan. "Yanzu nake so na qarasa bashi na kawo miki naki tuwon, ko a kawo nan tunda kin fito? Bara'atu ta fada kamar me tsoronta. Tayi wata yatsina tana kallon kwanon tuwon. Tuwon farar shinkafa ne da miyar gyada taji nama da kayan qamshi Bara'atu ce tayi ta dakanta saboda Bintan. "Kawo" ta fada kamar bataso, ta miqe ta wanke hannunta kafin ta dauko mata fulasan data saka tuwo da miyar a ciki. Yaro yayi sallama ya shigo da qatuwar baqqar leda, Bara'atu ta karba jin yace inji Audu, dumi da qamshin tsire taji ta wuce dashi daki Idon Binta akan Ledar. Seda ta raba tsaf ta zubawa Bintan wanda tasan duk hadanarta ba zata iya cinyewa ba, ta dibarwa Goggo Fadi ragowar ta fita dashi tabi duk Matan dake aiki kowa ta taba. "Amma kinsan ni aka kawowa shine saboda tsabar iyayi da kadifiri kika bude harda rabawa mutane tsabar kwadayi su kuma suka karba, to ze shigo se ki fada masa wanda ya sakaki" Binta ta fada sanda ta ajiye mata nata. Bata tanka ba ta miqe, Bilki ce ta bata amsa tace "Allah ya kawo shi din se ya daketa saboda ta baiwa yan uwansa tsire sunci" "Ni banyi dake ba" Binta ta fada dan bata shiga sharafin Bilki, ta dameta a tijara kuma taga shi kansa Audun yana shakkarta shiyasa bata takakarta ko zuwar musu can tayi. Haka lokacin kwanciya yayi dare dare ta haye nata Gado ita da yara qarshe se a qasa tayi musu shimfida suka kwanta. Washe gari aka tashi da hidimar daurin aure, shayi Bara'atu ta dafa mata da safe ta soya kwai dan an kawo Buredi tun cikin dare. "Ko zakici Waina ko Tuwo a kawo miki?" Bara'atun ta tambayeta. Binta dake shiryawa bayan ta fito daga wankan da har bandakin ta kai mata ruwa tayi banza da ita ganin haka yasa ta fita itama ta shiga wanka. Daurin auran na safe ne, kafin goma gida ya cika danqam da mata harda Mazan ma masu shigowa yiwa Goggo Fadi Allah sanya Alkhairi. Binta tasha kwalliya da Leshi ta baza turare ta kafa kujera a tsakar gida tana kallon kowa daidai. Bara'atu bata daddara ba ta sake yi mata tayin wainar daurin Aure ko tuwo wannan karon tace ta bata. *MAMAN MARYAM ONLINE BUSSINESS* *Ina kuke Mata Yan kwalisa , Ina nufin isassun Mata ,Wai shin Kuna da labarin shahararren company nan namu na GHT wato good healthtreatments* *Wanda yazo muku da fitattu Kuma* *ingantatattun suppliment ,na dukkan matsalolin ku*❓ *Ina maisan tayi kyau,irin na isassun Mata ya fitar Miki da shef dinki tayi Miki gyara in and out ,nemi royal jelly dinmu na company GHT* *Wanda aka yishi da xuma ,kundai San amfanin Zuma basai na fada miku ba , hajiya ta kixo ki Yi gyara domin ki kerewa sa,a kije taro ko baki da ko sisi kiji Ana rangada Miki hajiya , saboda yanda Zaki Kara kwarjini ,kina walwali acikin mutane , magungunan ght anti agen ne suna maida tsohuwa* *yarinya ,yarinya Kuma ta koma jaririya* *Muna da magunguna iri iri* *NA GYARAN JIKI* *NA GOGE NANKARWA* *NA RAGE QIBA* *NA CIRE TUMBI* *NA QARIN HIPS* *NA GIRMAN BREAST* *NA QARA TSAHON GASHI* *NA QARIN NI'IMA WANDA ZAI SAUKAR MIKI DA NI'IMA YA QARA MIKI DADI DA ZAQI A GURIN OGA* *Muna da hadin bita zai zai ,indai kishiyar ki tana Shan magungunan GHT, tohh lallai sunan ki sorry domin kuwa tazarar dake tsakanin ku kamar tazarar sama ne da kasa* *Muna da Wanda zai matseki ciki da waje Andai na yayin dinki uwargida*, *Sannan company mu na GHTBai tsaya anan ba* *Ya kawo muku maganin dukkan matsalolin ku* *INA MASU HAWAN JINI?* *INA MASU CIWON ZUCIYA?* *INA MASU CIWON QODA?* *INA MASU CIWON HANTA?* *INA MASU SICKLER?* *INA MASU HIV?* *INA MASU CANCER?* *INA MASU NEMAN HAIHUWA?* *Tohh Ku matso GHT taxo muku da magungunan matsalolin ku* *Kuma muna da testimonys da yawa ,na wadanda suka gwada suka da ce* *Munanan a KANO KUNTAU* *Kuma muna tura Kaya ko wanne gari cikin aminci da gaskiya , kuma kayan mu muna badashi ne cikin price Mai rahusa ga kyau ga inganci sannan ga Rahusa* *Kutuntube mu ta wannan number 📞08129249549* *📲07011401314* Wainar Masara ce tayi kyau matuqa ta zubota ta ajiye mata ta tafi kawo miya. Ta rage miyar tuwon Jiya daman saboda Bintan dan ta san ba lallai ta iya cin wadda akayi ta taro ba, ta bincike Kitchen din inda ta ajiye babu miya se ganin kwanon tayi ma a wanke an ajiye bata da zabi dole ta debo mata ta Bikin. "Ni zaki kawowa wannan miyar kamar ruwan wankin kan mahaukaciya ni zan ci miki wannan kawai kice kasheni kike so kiyi" Bintan ta fada a fusace sanda ta dire mata miyar, kamar me magana da Babarta Bara'atu tace "Kiyi haquri, na rage ta tuwon jiya bansan waya juye ba. Ki gwada wannan dinma tayi dadi wlh zaki iya ci" "Dama mana tayi dadi a bakin daya sbaa cin gabza dole kice wannan tayi dadi" Binta ta fada tana harararta, Bara'atu ta miqe jiki babu kwari mutane duk sun tsaya suna kallonsu ga Bintan bata magana a hankali, da qafa ta tunkuda kwanon miyar ya fallatsarwa Bara'atu a jiki tana cewa "Zoki kwashe shiyarki banma san me kika zuba a ciki ba da kike ta nacin se naci". "Amma kedai anyi yar marasa mutunchi, yanzu da miyar da zafi ta qona mata fata fa?" Hashimu daya shigo yana saba babbar riga ya fada, Binta ta kama qugu tana masa kallon banza, sedai ta gaza ce masa komai dan yanda yayi maganar cikin hayagaga ta tabbata ze iya rufeta da duka. Mata aka dauki surutu caaa kowa da abinda take fada. Hashimu nata bala'i yana qundumawa Binta da Iyayenta da basu san anyi ba zagi. Ya kalli Bara'atu dake hawayen wannan cin mutunchi data mata cikin taro, tacu kwalliyarta da Shadda Ruwan omo Bintan ta mata wankan Miyar taushe "Ke kuma sakarya kin tsaya kina mata kuka, k wuce ki kwase me zafi a tukunya ki watsawa yar banza a wannan kodaddiyar fuskar tata" Hashimun ya sake fada daidai nan Audu ya shigo yana fama da tasa babbar rigar ya tarar dasu cirko cirko, Binta na ganinsa ta saka kukan zallar kirsa da makirci tana cewa "Saboda ni ba yar cikinku bace shine zaku tsaneni? Me nayi muku? Wani abu ya taba hadani da wani a cikinku ne balle ku qwafeni kuke neman halakani" "Wace irin magana ce haka babu dadin ji wa yake neman halakaki?" Audun ya fada yana qarasawa kusada ita. Ta sake rushewa da kuka tace "Ina zaune kawai Bara'atu tayo kaina gadangadan da wuqa a hannunta, a garin na tureta ta taka kwanonmiyar nan ya fantsalar mata shine cikin su babu wanda yabi kadin ba'asin nufoni da tayi da wuqa sena miyar sata fantsamar mata suka hau zagina har wannan yayan naka yana cemun jinin shadanu" ta nuna Hashimu daya qame tsabar yau yaji wadda tafishi iya hada guri bashi kadai ba gurin kaf shiru sukayi suka daskare da mamaki, Audu ya kalli Bara'atu ya kalli wuqar dake yashe a gefenta ya sunkuya ya dauka yana nuna mata yace "Me zakiyi da wuqa da kika nufota" "Wallahi tallahi qarya take mun" Bara'atun ta fada tana saka kuka, Baba suwaiba wadda qanwace ga goggo Fadi ce tace "Amma kedai wannan yarinya duk yanda akayi Abokanan wasa kuke da Shaidan, yanzu wuqar da ni kika tambaya na baki kika bare muruci shine zakice ta nufo ki da ita? Gaskiya bakya tsoron Allah yanzu ke ko kunyar idanun jama'a bakiji ba ki lafta wannan uwar qaryar da zata iya kashe Aure Allah wadaranki wlh tir da masharrancin harshe irin naki" Nan aka sake daukar surutu kowa nayiwa Binta tofin Ala tsine. Audu ya kalli Bara'atun dake kuka kamar me sannan ya kalli Binta data sunkuyar da kai qasa kunya ta dabaibayeta kamar qasa ta tsage ta shige ciki takeji. Ta manta shaf a inda suke, Tsabar yanda idonta ya rufe tana neman dalilin da ze saka Audun sakin Bara'atu ya sakata hada wannan zancen da bata ma san sanda Dabarar tazo mata ba ta kwakwalwar kuma ta gaza kawo mata kalaman kare kai. Gaba daya sun kasa kunne suji hukuncin daze sauka akan Bintan da abinda tayi sabanin haka se ji sukayi yaja tsaki ya juya buguzun buguzun ya fice daga gidan. "Kin shiga uku Bara'atu ke kuma taki jarabawar kenan a gidan Aure to Allah yasa ta zame miki kaffara" "Bantan uba, yau naga abinda yafi qarfina ni yasu, Bara'atu dama haka kike zaune? Dole ki rame ai kinyi dakyau ma har yanzu kike cikin hayyacinki wannan makirci har ina?" "Wlh bazan iya zama da irin wannan matar ba, dama ace Audun tsayayye ne da sauqi to da alama ta shanyeshi Allah sarki Dada Allah yayi bata da rabon shan takaicin suruka shiyasa ta mutu kafin a aurota dan wlh wannan tsaf zata raba Da da uwarsa kutusi" Haka suka saka Bara'atun a tsakiya kowacce ta ringa surutunta, Binta kuwa jiki babu kwari kamar wadda aka kama da kayan sata ta shige dakin Bara'atun can qurya ta lafe a gado. Tana jiyo surutai ana zaginta amma babu damar tankawa ta rigada ta kwafsa. Haka ta wuni sir a daki ana ta shagalin Biki, Allah sarki Bara'atu, dukda abinda tayi mata haka ta zuba abinci da rana ta bawa Abdullahi ya kai mata bata daije da kanta ba. Bata ma sake shiga dakin ba dan ko kaya da zata sauya Bilki ce ta dauko mata ta kuwa yiwa Binta tatas kamar zata doketa dan bata gidan abin ya faru ta tafi gidanta ta dakko abu. Haka suka kwana. Tun a daren ranar Abokanansa da matansu suka kai musu tsogwamin abinda ya faru suka tareshi da zancen, "Gaskiya ka gyara gidanka Audu tun kana da hali. Wannan hanyar da ka dakko bazata bulle maka ba, idan baka dauki mataki yanzu ba kana ji kana gani gidanka ze ruguje, ba kuma iya matanka abin ze shafa ba harda yan uwanka seta rabaka dasu. Wlh banda qaddara ma wannan ba matar aure bace, mace babu komai a ranta se fitina da tada zaune tsaye? Wai me ka gani a gurin yarinyar nan harya rudeka Audu?" Shamsu Abokinsa ya fada. Audu yasha kunu yana kallonsu daidai dan kowa ya tofa ta bakinsa. "Ana magana kayi shiru kana muzurai da hada fuska, mu nan babu wanda fushinka ze tsorata dan kar muke kallonka kasan mu mun sanka tun muna yawo babu wando, kuma gaskiya ce se mun fada maka ka dauka ko karka dauka wannan ruwanka mudai mu fita haqqin zaman tare" Iliyasu daya fi sauran zafi ya sake fada se sannan Audun ya budi baki yace "To me kuke so nayi ko nace? Dani daku fa duka labari mukaji babu wanda abin nan ya faru a gabansa balle ya fadi haqiqanin gaskiyar yanda akayi" "Amma Audu baka tsoron Allah, ta yaya Mutum sama da Ashirin zasu hada baki su fadi qarya? Idan duka matan gurin sun goyi bayan Bara'atu kana tsammanin Hashimu ma ze bi bayanta ne?" Iliyasun ya sake taso masa, saboda a bar maganar yace musu "Naji, zan mata magana" "Daga baya kenan, ai take a gurin ya kamata ka nuna mata kuskurenta ba wai daga baya ba yanzu ai ka bata qofar da zata taka koma wane tunda ko zakayi fada badai a gaban mutanen data muzanta wancan ba. Wlh ni mamakinka nake Audu, a tasowarmu idan wani yace ko a mafarki ya ganka Mace tana juyaka wlh duk se mun qaryata se gashi a gaske da ranmu muna gani ka zama solobiyon banza a gaban wadda ma bata isa ba" cewar Musa. "Ya isa haka, nace zan mata magana ko, nifa ba wai wani abu yasa nake daga mata qafa ba. Idan na duba matakin dana taka a yanzu Mahaifinta ne sila, shi kuma a duniya bashida abinda yake so kamarta ya gayamun babu abinda zan yi na saka masa irin na kula masa da Binta wannan ne kadai dalili" "Ai shikenan" kusan dukansu suka hada baki gurin fada tsabar takaicin da maganarsa ta qunsa musu daga haka suka watse suka barshi da Muzammilu shine be gaji da magana ba. Washe gari kuwa da farar safiya Audu yace su fito su tafi. Bata san da su Bara'atu zasu koma ba seda taga ana loda kayansu a mota tayi qwafa bata dai ce komai ba dan babu fuska a gurin Audun, tun jiyan dai bece mata komai ba haka kuma be sakar mata fuska ba. Bara'atu dai duk a darare take har suka isa Kano ta wuce sabon dakinta har tsalle seda tayi saboda murna tayi dakin yan gayu. Haka aka cigaba da rarrafa rayuwa, sauqi daya ta samu shine na aikace aikacen Binta saboda masu aiki har biyu data tarar ta dakko wanda taja musu kunne akan ko gaisuwa ta shiga tsakaninsu da Bara'atun a bakin aikinsu. Ko a jikin Bara'atu daman me zata saka suyi mata ita? Gaisuwa kuma babu dole a ciki ita a zauna lafiya babu ruwan kowa da kowa yafi mata. Lantana me share share itace Mara mutunchi a masu aikin ta kuma lura tafi fada a gurin Bintan sama da Mairo me mata girki wadda Bintan ta santa ta taba zuwa gidanta kitso sau daya can qasan layinsu take Lantanar ce bata san a inda ta kwasota ba. Matar sam batayiba, a suffa ma Astagfirulla kalar munafukai ne da ita kuma haka take a zahiri. Ita take zuba gishiri akan ciwon zaman su da Bintan. Yanzu da cikinta yayi nauyi ta kusa haihuwa tadan rage hayaniya da hayagagar da take mata shiyasa har take dan samun damar fita tsakar gida tasha iska. Randa Lantana ta kunno Bintan kuwa ruwa ba zata barta ta hadiye da dadinrai ba, masifa zagi cin mutunchi da gori babu wanda bata mata, tun ba da Hadiza qanwarta tazo, ita take binta an mata aure shekara biyu baya zaman yaqi dadi suka rabu da Mijin nan ma babansu ya tasata gaba shine ta gudo gurin Bara'atun ta kwana biyu tareda Addu'ar ko Allah ze fito mata da Miji a Kano tayi aure ta huta da Fadan Babansu. Nan fa Binta ta samu nayi, gori da yana fita a jiki da bazasu samu sararin shan iska ba, sauqi daya da bata samu goyon bayan Audu ba da tace ya kori Hadizan, da haka zasu tattaro su cika masa gida to da yake har sannan ba a koma daidai ba tun abinda ya faru a Bechi dukda da fatar baki be mata magana ko fada akan abinda tayin ba kawai ya dan dauke mata wuta ne yanda yake rawar jiki yana mata abubuwa ya rage wannan ma na bala'in mata ciwo tadai barine zuwa ta haihu dan ta kanta take yanzun shiyasa ma take sararawa Bara'atun amma da zarar ta haihu zata qaddamar da shirin da tilas ta bar gidan da kareren qanwar tata data kwaso. Kwanci tashi cikin Binta ya shiga watan haihuwa, lamari fa ya zarce nada dan kankat Audu ya tattara ya koma gurinta da kwana dukda daman kusan hakan ake, a girki hudu idan zatayi kwanaki takwas kenan da qyar ya kwana uku tareda ita dasun kwanta Binta zata doko qofa wai bata da lafiya daga qarshe ma tsakaninsa da Bara'atu sedai idan yana da buqatarta yaje da Rana ko da daren kafin lokacin kwanciya yayi daman saman sa Binta tace Turakarta ce ita kadai, daga qarshe dakin tsakar gidan aka gyarawa Abdullahi daya fara zama saurayi su Babangida kuma tare take kwana dasu a dakinta se dayan ya zama dakin Audun to a hakan ma ita bata damu ba tunda dai babu wata fitina ko a haka za'a cigaba da rakawa zata iya haqura. Ranar da Binta ta haihu cikin dare naquda ta tasar mata, Audu baya nan ranar ya tafi Calaba dakko Mai a ranar dai suke saka ran dawowarsa amma har aka kwanta bacci shiru. Guraren sha biyu Ciwon gaske ya tasarwa Bintan, tun tana daurewa har abu yaci tura ta shiga kuka kamar yarinya. Abdullahi ne ya tashi fitsari ya fita tsakar gidan ya ringa jiyo kamar kuka daga dakin Bintan saboda darene guri yayi shiru kuma window dakin a tsakar gidan yake dan haka ya tafi da gudu ya bugawa Bara'atu qofa tana bacci taji bugun ta farka a gigice ta fito ya sanar mata da abinda yaji Tunanin naquda take ne ya fara zuwar mata dan haka ta juya ta tafi dakko zani da Hajib idan yaso ta fita ta kirawo Baba Uwani maqociyarsu. Tana zuwa qofar dakin sukaci karo da Audu, bata gama mamakin sanda ya dawo ba tsaqarsa ta katseta. "Ki kamata muje mota" ya fada rai a matuqar hade, jiki na rawa ta kama Bintan da tasan Azaba ce tasa ta yarda ta riqeta. Haka sukaje Asibitin murtala, kamar ana jira suna isa ko minti biyar ba'ayi ba Binta ta haihu ta samu Da Namiji. Yanda Audu ya ringa murna seka dauka haihuwar fari aka masa. A can suka qarasa kwana hardashi seda safe suka dawo gida Bara'atu ta ringa godewa Allah da zuwan Hadiza, shaf ta manta da batun Yara a gida seda sukaje Asibitin. Da ace Hadizan bata nan bata san ya zatayi ba qila sedai ta tako da qafa ta dawo dan ba zata barsu a gida suka kadai da daddare ba. Kan jiki kan qarfi ta ringa hidima da Bintan da Jaririnta kyara da hantara kuwa babu wanda bata gani. Abinda yafi damunta yanda Audu ya shareta, ko magana ta masa a ciki yake amsawa hidima yake tayi da Matarsa da Jaririnsa kayan fitar suna ma ana saura kwana biyu Abdullahi ya shiga da qatuwar leda ta zazzage taga kayansu ne shida su Babangida ko dan kunne babu nata a ciki. Suna duba kayan ya shigo fuskar nan kamar hadari ya wuce dakinsa ta tashi ta bishi. Seda ta kai masa abincin dare ya gama ci kafin tayi masa godiyar kayansu Babangida da ya bayar ta qara da cewa "Dan girman Allah idan wani laifi nayi maka kayi haquribka sanar dani na gaji da wannan zaman gabar da mukeyi" ta tattara qarfin hali ta fada wanda Sadiya maqociyarta kuma qawarta guda dayace ta bata wannan shawarar ta cewa ta dena shiru, duk idan taga canji a gurinsa ta tuntubeshi suyi magana tunda tasan halin Binta baze wuce ta qulla mata wani abun a gurinsa bane koda ace baze yarda da ita ba in har ya gaya mata laifinta ta kare kanta shikenan ai ba makaho bane kuma ba kurma ba qin Allah ne ya saka idan an gaya masa abu yake hawa ya zauna ba tareda yayi bincike akai ba. Seda ya mula kafin ya fara magana yana cewa "Wato badan Allah ya kawoni ba so kikayi ki bar Binta ta mutu ba zaki fita ki taimaka mata ba? Koda yake dama tasha fadamun kince se kinyi Ajalinta da ita da abinda yake cikinta ba zata haifeshi ba. Wlh mamakinki nake Bara'atu, yaushe kika zama haka? Ko kuwa dama hakan kike kin lullubeni ne baki fito da ainihin kalarki ba is yanzu?" "Ni ya kamata nayi maka wannan tambayar yaushe ka zama haka Audu? A zatona kaine mutum na farko da zaka fara bayarda shaida akaina amma kuma se zaton nawa ya zama ba gaskiya ba, koda ace ba zaka shaideni ba Audu yaci ace kasan me zanyi da wanda bazan aikata ba. A Bechi tace na nufeta da wuqa ka yarda yanzu kuma tace ni nace zan kasheta da dan cikinta shima ka yarda wane mugun abu na aikata maka daya janyo irin wannan rashin yardar a tsakaninmu har takai ayi mun qazafin zanyi kisan kai kuma ka hau ka zauna? Nayi tsammanin ko Qadangarenta tace nace zan kashe zaka qaryata balle ran mutum ba dYa ba harda na Jaririn dabe iso duniya bama" Bara'atu ta fada cikinmatuqar qarfin hali hawaye masu dumi suna sakko mata. https://chat.whatsapp.com/I8xKHGurk7EBf5ZqQdxHKG *MATAR MUTUM* *NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER* *MARUBUCIYAR* *WATA KISHIYAR* *RUBUTACCIYAR QADDARAH* *HALIN KISHI* *FIKRA WRITERS ASSOCIATION* *LITTAFIN KUDI NE* *PAY 400 (PROMO PRICE BAYAN KAMMALA FREE PAGES ZE KOMA 500) A ASUSUN* *7061838488* *OPAY DIGITAL SERVICES* *MARYAM FAROUK* OR *0709290797* *ACCESS BANK* *SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488* *IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705* *Kuyi following dina a Arewabooks @Maryamfarouk01 inda zaku karanta wannan littafin tareda sauran littattafaina* *NAGODE* *FREE PAGE 14 (LAST FREE PAGE)* Hawayen ta suka qara gudu lokacin daya miqe ya fice daga dakin bayan daya antaya mata tsaki me qarfi. Ta dade zaune a gurin tana kuka, meta tsarewa Binta? Ita data shigo ta tarar batayi kishi ta tayar da hankalinta ba se itace zata yita hada mata tuggu da makirci a gurin Miji shi kuma sam babu bincike ya ringa zama kan magana da an gaya masa? Tana tsaka da wannan kukan Hadiza ta kwankwasa mata qofa, seda ta gyara fuskarta ta fita Hadizan ta gane tayi kuka amna tayi shiru bata tambayeta dalili ba kuka kuma ta gaya mata ta daura aure dashi tunda ba zata tashi tsaye akan wannan Kishiyar tata makira ba se ta zauna tayi musu kuka har hawayenta ya qare. "Yace kije ga naman qauri can an kawo a gyara, banda rainin wayo ke zakiyi mata suyar qaurin ma ina yan uwanta sunzo? Dama ace zaman mutunchi kukeyi da sauqi amma keda bola banbanci kadan ne a gidan nan sann.." "Ya isa Hadiza, muje ki kama min" Bara'atu ta katseta daga mitar data kwaso. "Allah ya sauwaqe kedai da zaki iya bismillah" Hadizan ta fada tana zama akan kujera, tasan ba zatayi ba tunda ta fada dan haka ta fita rai babu dadi zuwa gurin gyaran Qaurin. Ta tarar da Mairo na hura ta dora yan ciki lantana kuma tana ware nama da qashi da alama hadosu masu gyaran naman sukayi. "Barka da Rana Hajiya" Mairo ta gaisheta, fuska babu walwala sosai dalilin quncin zuciya ta amsa mata, Lantana kuwa ko kallon arziqi bata mata ba sema tahau waqar Habaici daga Mairon har Bara'atun babu wanda ya tanka mata daga qarshe ta nemi guri ta zauna dan Mairo tace ta bari zasuyi tana kallon Lantana nata jan qwafa da alama zataje tayi abinda ta saba na hadin masifa. Suna kaskon qarshe yan uwan Binta biyu suka zo gurin ta gane Babbar ita tana dan zuwa dalilin akwai yan uwan Mijinta a nan Kanon me bi matan dai sau daya ta taba ganinta se yau na biyu. Dazu da suka sauka har ta fita zataje ta gaishe su suka hadu da Binta a tsakar gida tace ko barandarta ta taka seta mata rashin mutunchi shiyasa ta fasa dan hakan yanzun ta gaishe su suka amsa kadaran kadahan. Robar da aka zuba Nama suka dauke suna barwa Lantana sallahun idan ankwashe sauran a kai musu. "Ko me zasuyi dashi se Allah, a irin arziqinsu ai wlh nama dai yaci ya gunduresu yanzu amma Allah sa suma ba jida zasuyi su tafi dashi su aje qulli qulli a firiza yanda Hajiyar nan takeyi ba su basu ci ba su basu bawa wani yaci ya musu addu'a ba kai Hajiya Binta fa akwai Rowa alqur'an" Lantana ta shiga jero zance babu kai babu qafa. Yanda Bara'atu bata tanka ba haka Mairo kamar bata gurin, wannan nadaga abinda yasa take qara ganin girman matar. Ba ruwanta ta shiga sabgar da bata shafeta ba, aikin daya kawota gidan kawai take yi idan tazo da safe ta gama musu kalaci da wuri take dora na rana wata rana ma sha biyu ta gama data gama ta karbi rabonta zata tafi se kuma gurin qarfe uku ta dawo ta dora na dare shima tana saukewa zata tafi se kuma gobe da safe musamman yanzu da Binta tasa aka hade girkin tun zuwan Hadiza a yanda ta cewa Bara'atu ta dena girki da kanta, kwadayin Nama da Kazar daya kawo qanwar tata seta koma haka idan anyi girkin zata tsaya a raba ta kwashe duk abin arziqi ta hadasu da qasan tukunya ita bata ci ba ita bata bari wani yaci ba ta bakin Lantanar, ba kamar Mairo ba ita lantana idan tazo tun safe seta kai Taran dare har se Audu ya dawo Bintan ta fatattaketa sannan zata tafi yanda kasan bata da Miji balle Yara. Haka suka gama suyar ko dandanon gishiri a harshenta ta koma daki. Washe gari tun sassafe aka ringa shigo da kayan cefane, guraren Goma Binta ta aiko kiranta, A falon Audu na sama ta sameta tasha kwalliya abinta ba zakace jego take ba. Ta gaidasu ta zauna tana satar kallon Audu da tun maganar jiya be sake ce mata komai a gidan ba dubasun da yake da Asuba ma beje ba yau. Kudi ya tura mata murya a daure yace "Gashi nan, ki duba cefanen da aka kawo, abinda babu se a siya sannan su Bilki suna hanya bansan ko su nawa bane ki gayawa Mairo a saka abinci da yawa" Tayi shiru a ranta tana mamakin yau kuma ita aka bawa kudin cefane sannan ita ake cewa ta fadawa Mairo a qara abinci abinda ko ran girkinta Binta ke fadar abinda za'a dafa. "Shikenan na sallameki" ya sake fada seta miqe ta dauki kudin tana jin Binta cikin kissa murya qasa qasa tana ce masa "Ko kaifa, ai ya kamata dai itama ta ringa jin matar gida ce ba wai ace komai sedai taga anayi ba kaga kar suzo a qara tafiya dani a baki ace na kankane komai" Ta tafi tana mamakin Bintan a ranta, wato matar nan ko wagainiya Albarka shiyasa wani sa'ilin bata ganin laifin Audu saboda Bintan tamkar me rufa ido take. Bata taba mata Tijara ko cin mutunchi a gabansa ba, idan yana nan nunawa take nan dunita tafi kowa son su zauna lafiya da Bara'atu amma ita taqi bata hadin kai, da hakan take kanainayeshi kullum tana nuna masa laifin Bara'atu ne ita ce bata so su zauna lafiya, Bara'atu ce take fadawa yan uwansa mugun abu akanta shiyasa kowa baya sonta, Bara'atu ta tsaneta bata da buri illa na taga bayanta sannan ita kuma tayi ta nuna bajintarta da son jan Bara'atun da yayanta a jiki a gaban idonsa idan yana nan har kyautar abubuwa take kai mata ko yara yana fita tabi ta karbo abinta ta dora da Tijara shiyasa baze taba ganin cutar da take mata ba. Maganar girkin kanta da farko ta hana ko gaidata masu aikin suyi da kuna ta canza ra'ayi ta karbe girki ita ta gaya mata ainin dalili amma shi se tace masa saboda Bara'atun ta huta ne hidima tayi mata yawa ga yara ga girki gara Mairo ta ringayi gaba daya tubda dai biyanta akeyi kuma dama kullum se tazo ko ba rabar girkin Bintan bane ire iren abubuwan da suke qara dagula zamansu kenan, shi tunda kunnene kawai se abinda yaji ba ruwansa da bin ba'asin ya akayi cikin kissa zata tunzuro shi ya dauki fushi da ita yanzu kuma da taso qulla wani abun shine zatace ya bata kudin cefanen abincin suna dan ta tabbata ba Alkhairi ya saka Bintan yin hakan ba. Mairo taje ta samu tace ta duba kayan, data tambayeta me za'a dafa toh tilas ta koma ta sake tambayo Bintan tace mata Shinlafa da tuwo kawai zasuyi sauran abubuwan ta bayar da aikatau wannan yasa ta dan samu nutsuwa qila abincin iya jama'ar Bechi za'a bawa shiyasa ta barshi a hannunta. Tun rana suka fara rage aiki, su Bilki da Aisha da matansu Aminu ne suka yo gaba sauran dangi se gobe suna haka suka tasata gaba da tsiya harta rasa inda zata tsoma ranta wai daga dawowa harta tsomare a qauyen ma tafi kyan gani ta bari tsoron kishiya yayi tasiri a ranta. Har an idar da Isha suka karbi baquncin mutanen Ikko, Yakubu da iyalansa Bara'atu ta rasa ina zata tsoma ranta saboda murnar ganin Balaraba. Suka rungume juna cike da kewa, Balaraba tayi kyau ta qara zama wata babbar Mace fata se walwali takeyi ita kuwa Bara'atu abin se godiyar Allah kawai. Daga gefe Aisha dake kallonsu tace "Wato kwanciyar hankali duniyace, ku kalli dai idan daula da jin dadi ne Yaya Bara'atu tafi Yaya Balaraba samunsu amma kalle su ki gani banbancin kamar sama da qasa kowacce da ka ganta base an gaya maka matsayin da take a cikin gidanta ba" "Aisha kenan kedai da Allah yasa kike ke kadai a gun Mijinki kici gaba da gode masa domin ba zaki gane qalubalen me Kishiya ba se kina da ita duk abinda zaki fada ko ki bada shawara akai hasashe ne kawai tunda baki san ya ainihin matsalar take ba" Sauda Amaryar Aminu ta bata amsa. Bara'atu kuwa a dakin Audu ta sauki Balaraba, ta fita ta kawo mata ruwa da abin tabawa tace "Bari na dora muku abinci wannan bazata haka ace zakuzo ko Yaya Audu be sani ba" "Wai injiwa? Audun da shi yaje ya dauko mu daga filin jirgi" Balaraba ta fada. Bara'atu ta gwale ido tace "Filin jirgi? A jirgi kuka zo?" Balaraba ta harareta tana dariya tace "Ji yanda kika gigice kamar wnada nace miki da fiffike mukazo, jirgi muka hawo mana abin Allah in gaya miki yau se ga Balaraba a jirgi qiris ya rage na haihu saboda tsoro" suka kwashe da dariya gaba daya. Bara'atu ta sake cewa "Amma shine be gaya mun zaku zo ba?" "Ba zata yayi miki gashi ai kinfi yin murna da muka zo yanzun, ke ni ba wannan ba ya naganki gaka qashi da fata ko laulayi kikeyi?" Balaraba ta fada tana kallon Bara'atun, seta miqe kawai tana cewa "Bari naje na dora abincin" "Karki wahalar da kanki seda muka ci abinci muka taho tafiya a jirgi kamar wanda Aljanu suka ragewa hanya? Ni banma san minti nawa mukayi ba kedau Allah ya qara mana arziqi me amfani Allah kuma yasa badi mu lula muyi tafiya me nisa a Jirgin muje mu sauke farali" cewar Balaraba. Dukda haka Bara'atu taqi zama tace to bari taje su gaisa da Yaya Yakubu daga haka ta tsere, bata so ta zauna tunda Balaraba ta fara zancen ta rame ko ciki ne da ita tasan yanzu magana zata sake dagulewa sedai tana fita Bilki ta shige ta samu Balaraban ko kyakykyawar gaisawa basuyi ba dan tana sallah suka shigo yanzun taje ta gaida Yakubun kuma jira taje Audu ya matsa ra kwashe duk abinda ya faru da wanda yake faruwa ta gaya masa amma bari ta fara da Balaraban. Tas ta labarta mata komai daya faru basa nan, "Yanda kika san sallamammiya Bara'atu, na fada mata da nice wlh tun daga kan ginin nan gayyar zata watse. Hauka ma akeyi suci Talauci tare sannan dadi yazo ace ta zama yar kallo itafa da Boyi boyin gida babu banbanci. Idan anyi magana tace to ya zatayi? Na gaya mata taci abu ta kazan Yaya Audun tunda shi yake daurewa Bintan qugu tana mata iskanci kafin ta gangara kanta, ko Iskar qarya tayi ta musu rotse wlh duk zasu kiyayeta amma mata kamar Kazar da ruwa ya daka salaf salaf sedai tayita kuka in sun mata abu tana rama a haka fa kin ganta da kyan gani dalilin tajr Bechi kusan watanta biyar a can da ana gyaran gidan dawoqarta ne tayi wannan zabgewar to in aka cigaba a haka wata rana sedai azo a kwashi sauran qasusuwanta ai damuwa ta cinye tsokar tasa" Bilki ta fada cikin kumfar Baki. Tsabar baqin ciki da takaici Balaraba kasa cewa komai tayi se qafa da take girgizawa, a haka Bara'atu ta dawo ta tarar dasu tana ganin Bilkin kuma ta tabbata ta gama kwaza komai. Fada Balaraba ta ringa mata kamar zata daketa da tayi tayi kuma seta koma banbaki da lallami dan lamarin Bara'atun ta rasa wannene ma zeyi amfani a ciki. Banda kuka babu abinda takeyi ita kuma, haka suka kwana ko baccin kirki Balaraba bata iyayi ba, data rufe ido abin ze mintsineta ta tashi ta fara surfawa Bara'atun masifa can kuma tayi qasa tana lallashinta tareda bata dabarun kwatar yanci. "Audu yana sonki, da ace baya sonki a yanda take wannan abun da ba zakiyi qarkon kawowa yanzu a gidannan ba. Wayo da dabara ne baki dasu, idan ta nuna miki wayewar Birni seki nuna mata ta qauye, akan me zaki ringa yiwa Kishiya kuka kin nuna mata kina tsoronta a fili ba dole ta takaki yanda taga dama ba, ai ko a ranki kina tsoronta ki dake idan ta fada ki mayar mata kar ki ganta wata zabgegiya kiji tsoron karta dake ki ai qarfi ba'a jiki bane idan kika qarfafa zuciyarki tsaf wlh zaki kaita qasa idan ma ta kaiku da dokuwa sannan shima karki raga masa tunda be dauki tsagin gaskiya ba. Wlh ki tashi ki kwatarwa kanki yanci idan ba so kike ki bata quruciyarki ki kashe kanki da kanki ba". *MAMAN MARYAM ONLINE BUSSINESS* *Ina kuke Mata Yan kwalisa , Ina nufin isassun Mata ,Wai shin Kuna da labarin shahararren company nan namu na GHT wato good healthtreatments* *Wanda yazo muku da fitattu Kuma* *ingantatattun suppliment ,na dukkan matsalolin ku*❓ *Ina maisan tayi kyau,irin na isassun Mata ya fitar Miki da shef dinki tayi Miki gyara in and out ,nemi royal jelly dinmu na company GHT* *Wanda aka yishi da xuma ,kundai San amfanin Zuma basai na fada miku ba , hajiya ta kixo ki Yi gyara domin ki kerewa sa,a kije taro ko baki da ko sisi kiji Ana rangada Miki hajiya , saboda yanda Zaki Kara kwarjini ,kina walwali acikin mutane , magungunan ght anti agen ne suna maida tsohuwa* *yarinya ,yarinya Kuma ta koma jaririya* *Muna da magunguna iri iri* *NA GYARAN JIKI* *NA GOGE NANKARWA* *NA RAGE QIBA* *NA CIRE TUMBI* *NA QARIN HIPS* *NA GIRMAN BREAST* *NA QARA TSAHON GASHI* *NA QARIN NI'IMA WANDA ZAI SAUKAR MIKI DA NI'IMA YA QARA MIKI DADI DA ZAQI A GURIN OGA* *Muna da hadin bita zai zai ,indai kishiyar ki tana Shan magungunan GHT, tohh lallai sunan ki sorry domin kuwa tazarar dake tsakanin ku kamar tazarar sama ne da kasa* *Muna da Wanda zai matseki ciki da waje Andai na yayin dinki uwargida*, *Sannan company mu na GHTBai tsaya anan ba* *Ya kawo muku maganin dukkan matsalolin ku* *INA MASU HAWAN JINI?* *INA MASU CIWON ZUCIYA?* *INA MASU CIWON QODA?* *INA MASU CIWON HANTA?* *INA MASU SICKLER?* *INA MASU HIV?* *INA MASU CANCER?* *INA MASU NEMAN HAIHUWA?* *Tohh Ku matso GHT taxo muku da magungunan matsalolin ku* *Kuma muna da testimonys da yawa ,na wadanda suka gwada suka da ce* *Munanan a KANO KUNTAU* *Kuma muna tura Kaya ko wanne gari cikin aminci da gaskiya , kuma kayan mu muna badashi ne cikin price Mai rahusa ga kyau ga inganci sannan ga Rahusa* *Kutuntube mu ta wannan number 📞08129249549* *📲07011401314* Washe gari. "Nifa wlh Ji nake kamar na rufeki da duka Bara'atu" Balaraba ta fada kafin taci gaba da cewa "Banda tsabagen abin haushi Bintar me? Me akayi akayi wata Binta da zaki zauna ta shigo gidanki ta mayar dake yar kallo bayan ke kika ci wuyar Audun kika zauna dashi tun bashi da ko sisi har ya zama mutum ta ganshi ta aura na tabbata wlh a rayuwar da kikayi dashi Binta ko a me wanke mata kaya ba zata dauke shi ba. Amma shine kika zauna kika barta take zuba miki mulki a gida kin zama yar kallo jibeki dan Allah yanda kika qwanjale kika fita hayyacinki tamkar me wani ciwo ita kuwa tana walwala da farin ciki Miji na hannunta wlh tun wuri idan zaki farka gara, ki amshi Mijinki da matsayinki, ke kika sha wuya dashi dan haka yanzu kamata yayi duk wadda zataji dadinsa to a bayanki take". "Kema dai kya fada Yaya Balaraba" Aisha ta tsoma musu baki taci gaba da cewa "Koni da nake zaune a qauye wlh bazanyi sokoncin da Yaya Bara'atu takeyi ba banga wata kishiya da zanji tsoro ba, ba daga Kaduna ba ko daga Ingila ya aurota qarewar Bariki sena gwada mata nawa wayon qauyen dukda shima Yaya Audu da laifinsa ko nace ma yafi kowa laifi. Wancan zuwan da sukayi da Yaya Ummaru ya masa magana akan abinda tayi lokacin auran Saleh cewa yayi wai ayi haquri shi baya iya mata fada saboda idan ya duba yaga komai ya samu yanzu a rayuwa Ubanta ne sila kuma shi uban a duniya babu abinda yake so kamarta shi yasa yake mata lamuni kiji wani rainin hankali fa se kace wata diyar Qaruna ko kuma yanke Talauchi suka bashi". Balaraba taja tsaki kamar zata tsinke harshenta kafin tace "Saboda ubanta ya masa silar arziqi se akace tafi kowacce Mace ko yaya? Rabonsa ne a jikinsu kuma ko zasu bashi su haukace se yaci kawai tsabar mugun hali ne irin na maza matar da aka sha wuya tare da ita bola wadda zata diro rana daya itace abokiyar cin arziqi kuma wlh Audu ya bani mamaki a irin yanda kowa yasan yana qaunar Bara'atu ban taba tsammanin ko Gimbiya Elizaabeth ya auro ze fifitata akan Bara'atu ba" "Abin ne nake ga kamar harda Asiri" Aisha ta sake fada Balaraba ta harareta tace "Aikin kenan kullun ace Asiri, shin maza basa isakanci dole se an musu Asiri da yawa da haka suke fakewa ayita daukar Alhakin matan da basu ji ba basu gani ba ace asirce su sukayi, shidai Audu daman halinsa ne be fito ba se yanzu daman kuma kinsan kudi shi yake nuna ainihin kalar mutum ita kuma Binta tayi amfani da wannan damar take zuba sharafinta tunda shi ya bata qofa. Ni da Allah tashi kije ki karbo musu idan ba haka ba kuma naje da kaina" ta qarashe tana kallon Bara'atu data sunkuyar da kai idonta ya tara kwalla dalilin maganganun da sukeyi. Tun jiya Balaraba take mitarzancen nan, babu wanda ze fuskanci halin da take ciki kowa sedai yace mata wawuya ko sakarya ta kasa kwatar yan cin kanta ta sakarwa Kishiya ragamar gidanta daga zuwa to dan Allah base ta samu kwarin guiwa da Adalci daga gurin wanda ya ajiye su ba? "Bari kiga na tashi" Balaraba ta sake fada tana yunqurawa dakyar saboda tsohon cikin dake jikinta nan Bara'atu ta zabura ta miqe tana cewa "Bari naje, ni magana ce ban so wlh da kun barni yanzu se a dora musu wani tunda dai ta bamu iya rabon mu" da haka ta fice daga dakin tana jin Balaraban na zaginta. Yan Bechi na ganinta sukayi mata caa suna cewa "Yawwa Hajiya Bara'atu, tun dazu muke jira a qaro abincin kinga yara se kukan yunwa suke wasu ko karin safe ba suyi ba muka fito". Da wani yanayi tace musu "Kuyi haquri yanzu za'a kawo" ta fice daga falon zuciyarta na bugawa cike da taraddadin abinda ze biyo baya idan taje tace a qara musu abincin, dukda cewar su sukayi wahalar dafashi ita da wasu daga cikin yan uwan Audu da suka fara yowa gaba tun ana jibi suna. Seda suka dafe shinkafa kwano goma sha biyar, dambu kwano bakwai ga tuwon safe na kwano bakwai amma banda su Waina, Funkaso Alale da sauran tarkacensu irin na yan gayu da suka kai akayo musu daga waje amma a ciki tuwo Malmala goma suka basu se shinkafar da bata fi rabin kula madaidaiciya ba tun hantsi be gama dagawa ba kuma suka kusa cinye shi saboda ba'a karya ba duk suna jiran a kammala abinci sannan ga ma'aikatan da suka tayasu duk a ciki ta debar musu suka tafi dashi gidajensu gaba daya yan uwan Bintan suka lode abincin a Kuloli suka kai daki. A hankali take gifta matan dake zaune tsakar gidan yan suna, wasu maqwaftansu ne wasu kuma qawayen Binta da matana Abokanan Audu wanda suke hulda da ita kadai duk kuma rukunin data wuce zata musu sannu wasu su amsa wasu suyi mata banza harta dangana da qofar falon Binta, "Maman Baba" taji an kirata ta waiwaya fuskarta ta fadada da murmushi ganin Maman Kabir ce maqociyarta guda daya da suke sabgar Arziqi gaba daya sauran Binta ta kwace su ko tace sun koma gurin Bintan. "Se yanzu zaki shigo mana" ta fada tana jan kumatun Kabir dake hannunta ya kuwa janye ya lafewa mamansa tayi dariya tace "Maquyacin kawai" "Tun safe naso na leqo baqi nayi wlh se yanzu suka tafi" Maman Kabir din ta fada. Bara'atu tayi murmushi tace "Na sani tsokanarki nakeyi dazu Shamsiyya ta shigo ai tace Yayan Baban Kabir ne yazo, qarasa ciki to yanzu zanzo abu zan karbo gurin Binta". "Ai gara na biki nima naga Jinjiri kafin na zauna" Maman Kabir ta fada hakan yasa suka shiga falon Bintan tare. Yayyenta na tsaitsaye a falon sun hada kai suna magana sallamar su Bara'atu ta sakasu zabura tamkar marasa gaskiya, Yaya Salima ta qaqalo fara'a ta yabawa fuskarta tana kallon Bara'atu tace "Aa uwargida an leqo? Sannunku fa da aiki" "Uhm" Bara'atun tace kafin kanta a qasa cike da taraddadi tace mata "Daman yan Bechi da suka zo yanzu ne Abinci be isa ba shine nace ko za'a dan qaro musu" "Aikin kenan abinci Abinci koda yake ba a saba ci ba, banda jaraba ma suna amma anyo gayya kamar wani Bikin fari wato za'azo aci banza to babu kowa ya nade yunwarsa ya koma da ita" Munira wadda take autarsu Bintan amma ta rigata aure ta fada cikin Fitsara se Yaya Saliman tayi saurin tareta tana cewa "Haba ke kuwa Munira Abinci dai Allah na tuba abin aci ayi kashi kuma fa mutanen nan dangin me gidan ne idan ba'a basu ba to su za'a bawa? Barta dan Allah Bara'atu shiga ciki ki gayawa yar uwartaki se muji kamar Adadin da za'a zuba musu" ta qarasa tana nuna mata qofar dakin Bara'atu. Maman Kabir da takaici ya quleta, ba abin tayi magana ba ta jawa Bara'atun ta juya kawai ta fita tana ce mata "Bari naje an jima kan na tafi ma gaisa da ita" Bara'atu kuwa a sanyaye ta tura qofar dakin Bintan da sallama wanda tun zuwanta gidan shekara guda sau daya ta taba takashi randa aka kawota, ko ranar da zata haihu a qofar falo suka hadu ta taimaka mata suka tafi Asibiti. Zuciyarta duk babu dadi ta shiga, ita abincinma ko kalarsa bata dandana a harshenta ba da suka gama girkin shayi ta kada tasha saboda yanda ta gaji sannan duk taron Jama'ar da suke iqirarin sunzo cin banza Jininta biyu ne a ciki Hadiza wadda dama tare suke zama se Ubaida data biyo yan zuwa suna saboda taga Yan uwan nata ragowar dukfa Dangin Audu ne, qanne da yayyensa da Matan yan uwansa se Maman Kabir Qawarta tilo da ta shigo yanzu wadda tana da tabbacin harta fita be zama lalle ko ruwan fanfon gidan tasha ba. Bata tarar da Binta a dakin ba motsin da taji a Bayi yasa ta ankare da tana ciki, Jinjirin daya ci sunan Babanta Binta Zakariyya na nade cikin showel ta matsa inda yake yanda aka kwantar dashi yayi kusa da bakin gado sosai, dukda cewar jinjirine amma ze iyayin motsi me qarfin da ze fado hakan yasa ta dagashi ta maidashi can tsakiyar gadon yana ta sharar bacci abinsa daidai nan taji muryar Binta akanta tana cewa "Waye wannan? Uban me kikeyiwa Dana?" "Gyara masa kwanciya nayi, naga an barshi a bakin gado" Bara'atun ta fada kanta a qasa. Binta ta galla mata harara ganin itace kafin tace "Akan me zaki shigo mun har quryar daki me kike nema?" "Daman maganar Abinci ce yan Bechi sun qaraso wanda aka bayar kuma ya qare shine nace ko zaki saka a qara musu" "Babu, gayyar yunwa nace babu abincin ko kuwa ni na ce suzo balle na basu abinci?" Bintan ta fada cike da masifa. Bara'atu ta kalleta tace "Yan uwan Yaya Audu ne fa ba wasu daban ba" "Yana sama ai seki hau ki gaya masa ya sakko ya girka musu suci tunda yan uwansa ne ko kuma ke ki je ki sake dora wani amma ni abinci na ban dafa saboda wasu yan qauye ba na baqin dana gayyato ne dan haka malama maza fitarmun daga daki tun ranki be baci ba" Kafin Bara'atu ta sake cewa wani abu burum Yaya Salima ta fado dakin kamar wadda ta labe daman tana jiran lokaci yayi ta shiga. Inda jinjirin yake ta nufa ta dauke shi tana cewa "Bari a fita dashi mutane nata zuwa ganinsa se kuma ta zare ido ta kalli Binta data cire dankwalin kanta zata canza kaya tace "Ke zo ki gani wane irin bacci yaron nan yakeyi haka qirjinsa baya dagawa alamar numfashi?" tana rufe bakinta Babbar Yayarsu Anty Sakina ta shiga dakin ta kallesu sunyi cirko cirko tace "Lafiya kuwa meya faru?" Salima ta miqa mata Babyn tana cewa "Yawwa dubashi kiga Anty se naga kamar baya numfashi" da yake ita malamar jinya ce, nan ta tattaba yaron tayi salati tace "Wannan ai ya rasu". Maganar ta taja hankalin Bara'atu da har ta kai qofa ta tsaya, Binta ta finciki yaron daga hannun Yayarta tana duba qirjinsa babu alamar yana dagawa, ta kai kunnenta zuciyarsa bayan ta saka hannu a hancinsa bata ji dumin numfashi ba nan ma shiru seta sake shi Yaya Saliman tayi azamar tarewa kafin ya kai qasa kamar qiftawar Ido Binta ta dira gaban Bara'atu ta cakumeta tana cewa "Kashe shi kikayi? Na rantse da girman Allah se kin bishi" nan ta shiga kai mata duka kamar me casar gero kururuwarta da ihun Bara'atun ya janyo hankalin sauran dake falo shigo gaba daya, tuni gida ya dauki hayaniya magana ta fasu Bara'atu ta kashe jinjiri gashi can Binta ta riqeta itama tace seta kasheta. Binta ko dukan Bara'atu take babu ji babu gani tamkar ma bata hayyacinta fadi kawai tace "Wlh sena kasheki, sena bi kadin haqqin dana" ta shiga jibgarta tamkar Mahaukaciya ta kama yaron da yake tsokanarta saboda rashin Imani kuma yan uwanta kaf dake tsaye aka rasa wadda zata kwaci Bara'atun daga inda suke tsayen suke ce mata wai ta qyaleta ga gawar Jaririn a Hannun Anty Sakina. Ihun Bara'atu na neman ceto da kururuwan Binta tana fadin seta kasheta ne ya janyo hankalin Yan suna. Hankali tashe yan Bechi suka duru darin, su suka taru suka danne Bintan har Bara'atu ta samu ta kubuta daga hannunta tayi mata jina jina fuska ta haye dan duka tasha ta ko ina. "Meye haka? Kinyi hauka ne Binta zaki kama ta da duka?" Audu da suka sakko da gudu shida Jama'arsa da suka zo mata suna ya fada cikin tashin hankali. "Wlh ban gama dukanta ba, idan anga na haqura to na kasheta kamar yanda ta kashe mun Da" Bintan ta sake fada tana zaburowa yan uwanta suka riqeta. Cikin rashin fahimta Audun yace "Wace magana kikeyi haka? Wane dan aka kashe?" Bayan wasu Awanni. Ihun kuka da hargowar Binta kawai ake ji a falon, "Na rantse da girman Allah yanda ta kashe shi itama seta bishi babu uban daya isa ya hanani daukar mataki akan wannan abun" taci gaba da sheqa kuka. Dazun da akayi jana'izar yaron sanda aka zo fita dashi qaramin hauka ta tayar ta riqeshi qam dakyar Maza suka bambareta ta ringa doke doke qarshe se a daki a ka kulleta se yanzun bayan Isha Audu yaje ya budeta da kansa ya tasa qeyarta zuwa samansa inda Yakubu yace ya tattaro su gaba daya aji abinda ya faru. Babu tsoron Allah ko tunanin bayan wannan rayuwar da akwai wata Munira da Salima suka bada shaidar Bara'atu ce ta kashe jaririn dan Munira cewa tayi ta leqa dakin ta hangota zaune an showel dinsa bata dai tsammaci yana ciki ba seda Salima ta shiga ta tarar da ya mutu. Sakina dai tayi shiru, har ranta bata so abinda sukayi ba, magana ta gaskiya yaron ya rasu tun kafin Bara'atu ta shiga dakin, qus qus din da ta tarar dasu sunayi na taraddadin yanda zasu fada mata ne suma basu san menene silar mutuwarsa ba haka nan suka lura da babu rai tattare dashi shine suka shimfide mata shi a kan Gado ita kuma Bara'atu ta taka sahun barawo kuma tana shiga Salima ta kitsa ai kawai suce itace kuma har yanzun basu fadawa Bintan ainihin abinda ya faru ba. Yakubu ya kalli Bara'atu data zama wata abar tausayi, fuskarta a kumbure ga duka ga uban kukan datasha. Cikin tausayawa yana kallonta yace "Bara'atu menenr gaskiyar abinda ya faru?" "Wallahi Allah shine shaidata ko taba yaron nan banyi ba. Ni daga haihuwarsa ma sau daya na taba riqeshi a Asibiti, sanda na shiga dakin na tarar dashi sun kwantar dashi a gefen gado abinda ya saka na matsar dashi tsakiya saboda naji tsoron karya motsa ya fado shine Binta ta fito ta ganni ko ita idan zata fadi gaskiya a tsaye ta ganni ban zauna mata a daki ba ga yan uwana nan a tambaye su da fitata daga daki zuwa sanda abin ya faru ya isa ace na zauna akan Jariri ya mutu har jikinsa yayi sanyi?" Bara'atun ta fada cikin dasashshiyar murya me ban tausayi. Yakubu ya gyada kai cike da aminta da zancenta ya kalli Audu yace "Kaji daga kowanne bangare se kayi alqalanci bisa Adalci" "Alqalanci? Shi ne ze yanke mun hukunci akan kadin ran dana da aka dauka? To billahillazi huwarrahamanu ba'a isa ba, ku barni na kasheta da hannuna ko kuma gobe na tafi kotu, ina da qwararan hujjojin da zasu saka a zaman farko Alqali ya saka a gillewa muguwa kai ta bishi, wlh ran dan baze tafi a banza ba" Binta ta sake zaburowa tana fada. "Ya isa kiyi shirunki babu wanda yace ran danki ze tafi a banza" Audu ya fada, kafin ya kalli Bara'atu yaci gaba da cewa "Dama ai kinyi furucin se kin ga bayan ta ita da abin cikinta. Allah be baki nasara ba tun yana ciki baki haqura ba seda kika aiwatar da shirinki yanzun ko Bara'atu yaushe kika zama muguwa me baqar zuciya haka? Ina tsoron Allan ki da har zaki iya zama akan Jinjirin kwana bakwai har seda ya daina numfashi me ya tsare miki a duniyar daya saka kika kauda shi?" Shiru ne ya gifta gurin kamar kowa ya mutu koda yake da yawa daskarewa sukayi basa ma numfashi tsabar mamakin Kalaman Audu, Yakubu har zamewa yayi daga kan kujera yana leqen fuskar Audun ya kuma gaza furta komai. Audu yaci gaba da magana yana cewa "Na gaji da wadannan mugayen halayen naki Bara'atu, daman simi simin mutum da yawanku mugayene, zuciyarku cike take da mugunta fal gashi kuwa kin fara fito mana da ita. Yau kin kashe Zakariyya, qila gobe Kan Bintan zaki juya idan aka kwana biyu kuma ki hau kaina na mutu ki gaje abinda na tara dake da yayanki ko ba haka ne shirinki ba shiyasa bakya so Binta ta haihu saboda ya zama yayanki kadai suke da gadona to bazan jure ba, ai se da igiyoyin aurena akanki ne idan na mutu zaki ci gado na ko? To kije kawai Allah ya hada kowa da rabonsa na Alkhairi na sawwaqe miki igiya daya". Tirqashi, wasa farin girki *A nan na kawo qarshen Free pages na littafin MATAR MUTUM, zanci gaba a Arewabooks ku duba @Maryamfarouk01* *Domin samun cigaba a whatsapp maza ki tura da 500 zuwa Asusun* *7061838488* *opay* *ko kuma* *0709290797* *Access bank* *Maryam Farouk* *Se a tura shaidar biya ta wannan layin 07061838488* Idan katine a dauki hotonsa a turo ta lambar sama, VTU kuma a saka a Layin sama. Yan Niger ku tuntubeni kai tsaye domin na hadaku da wadda zaku biya kudinku a gurinta Nagode. https://chat.whatsapp.com/I8xKHGurk7EBf5ZqQdxHKG *MATAR MUTUM* *NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER)* *FIKRA WRITERS ASSOCIATION* *LITTAFIN KUDI NE* *PAY 400 (PROMO PRICE BAYAN KAMMALA FREE PAGES ZE KOMA 500) A ASUSUN* *7061838488* *OPAY DIGITAL SERVICES* *MARYAM FAROUK* OR *0709290797* *ACCESS BANK* *SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488* *IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705* *Kuyi following dina a Arewabooks @Maryamfarouk01 inda zaku karanta wannan littafin tareda sauran littattafaina* *NAGODE* *PAGE 15* https://chat.whatsapp.com/I8xKHGurk7EBf5ZqQdxHKG "Allah ka gani babu saka hannuna a cikin wannan al'amarin, Allah karkasa haqqin baiwar Allan nan da suka dauka ya bibiyeni" Ummu ta fada bayan data gamajin abinda ya gigita mata tunani. Da safiyar sunan aka kirata daga gurin aikinsu, ita din yar jarida ce kasancewar ta dauki uzuri ta tafi Kano se kuma wani aiki ya taso dan haka manajansu ya kira akan taje a maimakon ace se an taso wani daga Kadunan yazo tunda tana tareda abin nadar rahoto da sauran abubuwan buqata shiyasa ta tafi bata san badaqalar da aka kwasa ba seda ta dawo kuma da ace tana nan tabbas da bata goyi bayan abinda suka aikata ba dan ita din itace Mahaifinsu sak gurin dattako. Ta Jinjina abin ta kumayi matuqar mamakin yanda yan uwan nata suka iya aikata wannan ta'asa. Idanunta dauke da hawaye ta kalli Babbar Yayarsu sakina da duk itama abin duniya ya isheta yace "Yanzu Yaya harda ke? Kika bada shaidar zur? Kuna tsammanin idan Dady ko Mama sukaji maganar nan me zasu ce? Wannan wane irin zalunci ne yau koda ace dagaske matar nan ta aikata abinda kuka ce ai wlh ku masu rufa mata Asiri ne idan yaso ku barta da Allah ya kamata da haqqin ran data dauka amma bataji ba bata gani ba kun laqa mata sharrin da ze bibiyrta har yaya da jikoki sannan kunyi sanadin datse mata igiyoyin aure wlh ku kuka da kanku ku kuma shirya ta inda haqqin ta ze bibiyeku domin kuwa Allah baya bacci se ya saka mata kuma. Ke kuma( ta juya kan Binta) tun kina da sauran dama ki koma ga Allah ki bar wannan turbar da kika hau dan wlh babu inda zata kaiki se filin Nadama mara amfani da dana sani. Yanzu ba se anjima ba ki tashi kije ki gayawa Mijinku gaskiyar magana ki warware wannan qullin da kika yi, karki bari Yarinyar nan ta bar gidan nan dan wlh Binta ina jiye miki rayuwar da zakiyi a gaba wuyanki daure da haqqin ta, Kizo ki tarar da mata a gidanta ki gallabi rayuwarta ki hanata sakat da Mijinta meye ribarki a ciki?" "Dan Allah Yaya Ummu ki riqe wa'azinki abinda ya faru dai ya rigada ya faru zance kuma Dady ko Mama sedai idan ke zaki fada musu kuma idan kika janyo suka mana baki kema se Allah ya saka mana akanki dan haka gara mu rufe maganar nan a inda ta faru Allah ya kiyaye gaba" Munira ta fada ganin sauran sunyi shiru har Bintan da Alama maganar Ummu tayi tasiri a zukatansu wannan ya basu qwarin Guiwa itama Bintan ta karkace tana cewa "Allah ne ya kawo mun hanyar fitarta cikin sauqi babu abinda zan fadamasa wlh". Da dai Ummu ta tabbatar sunyi nisan da ba zasuji kira ba dole ta qyalesu, a iya saninta iyayensu basuyi musu kalar wannan tarbiyyar ba ba kuma tasan a inda suka samo ta ba tana kuma musu fatan shiriya a gurin Allah domin basu hau kan layin da ze bulle dasu ba. A bangaren Bara'atu kuwa duniyar ta mata zafi, har ta dangana da cikin dakinta bayan jefa qafa take kawai badan tasan ina take zuwa ba. Ta zauna dabas a qasa, Balaraba da labari ya iske ta dan bata je zamanba itama ta zama kamar wata mutum mutumi saboda mamaki. Suna haka Hadiza qanwarta ta shiga dakin ta shiga sauke kayan Bara'atun tana zubawa a Jakunkuna cikin tsananin fushi. "Wlh se sunga sakayyar mugun abunsu a kansu, shi kuma in sha Allahu har ya mutu yana nadamar wulaqantaki butulu wanda be san Halacci ba" haka Hadizan ta ringa fada tana zuba kaya ta hade mata komai tas dan daman kayan nata ba yawa ne dasu yanzu ba ta kwashe da yawan suturunta ta kyautar kamar yanda ta saba duk sallah kuma zeyi mata dinkuna masu yawan gaske to Bana da abin yazo a zamanin binta kala uku ya mata se lokacin Bikin Saleh nan ma ya mata uku. Hadiza ta gama hada kayan Bara'atu ta fara hade na yaran se a lokacin Balaraba ta iya bude baki tace "Karki hada kayansu ki barsu a gidan ubansu babu inda zataje masa da Da" "Bazan iya barin Yayana ba ba zata riqe su ba" Bara'atun ta fada tana fashewa da kuka kamar wadda ake yankar naman jikinta. A mugun fusace Balaraba yace "Ai ko kashe su zatayi se kin barsu, wlh ba zakiyi masa wahalar yaya ba yanda ya auro ki ke kadai ki tafi su zauna a gidan ubansu kuma dole ta wahalta musu, abinda tayi miki kuma Allah na gani seya saka miki ko ba dade ko bajima se taga sharrinta a kanta da ita da yan uwan nata gaba daya". Haka aka kwana ana maida magana, washe gari Qarfe shida motar yan Bechi ta daga, Bara'atu kuma mota daban Yakubu ya nemo ta dauketa da kayanta tare dashi da Balaraba suka tafi banda yaran dan kamar yanda Balaraba tace ta barsu shima Yakubun da Asuba daya shiga yace a kira masa Bara'atun haka ya gaya mata ta zube masa Yayansa. Watsa watsa sukayi da Audu akan al'amarin, babu yanda beyi dashi akan ya janye furucinsa ba amma ya rantse akan baze maidata ba wannan tasa Yakubun barin gidan a cikin daren be kwana ba da Asuba kuma ya fita ya nemo mota aka balle kayan Gadon Bara'atun tas yasa aka lode su sannan ya samo qarama suka tafi a ciki zuciyarsa cike da baqin ciki da takaicin abinda Qanin nasa yayi. Ya kuma yi rantsuwar cewar babu shi babu duk wata sabga data shafi gidan Audu. Abin seya zamarwa Bara'atu duka biyu domin kafin su isa wanda suka fara tafiya suna kai labari kamar wutar daji ya yadu cewar hassada tasa ta kashe jariri saboda yayanta kadai take so su gaji Audu. Mutane da abin mamaki wasu tamkar a gabansu akayi se kace wani hawan sallah haka aka cika qofar gidansu ana jiran aga ta inda zata bullo tunda ance ya saketa ta hado kayanta tana hanya, aiko da suka isa seda Yakubu ya hada da dura Ashar abinda ba halinsa ba kafin matan da sukayi dandazo suka watse da sabuwar gulmar cewa magana ta tabbata gata nan harda kayanta gaba daya da alama auran ya qare saki uku yayi mata. Seda tayi matuqar dagaske kafin ta iya shanye wannan jarabawa. Yanda mata suke musu zuruftu suna yada musu magana ita da mahaifiyarta har ciwo ya kwantar da Innar tata. Babanta kuwa nasa bala'in yafi na kowa dan da farko ma cewa yayi ba zata zauna masa a gida ba. Duk kuwa sa Yakubu ya sameshi qafa da qafa ya gaya masa komai daya faru amma mutumin nan ya hau kan qarya ya zauna ya dora mata laifi har yana cewa uwarta ce ta sakata. Watanta biyu a gida Audu ya tattaro yaran ya aiko mata dasu, tana zaune se gani tayi ana shiga da kayansu da buhunhunan abinci ta tambayesu su dawa sukace Direban Babansu ne ya kawo su a cikin kayansu taga kudi, kudade masu yawan gaske se farar takarda da gajeran rubutu a jiki. "Kiyi amfani dasu gurin kulawa da yarana duk wata zan ringa aiko musu da abun buqata Aminu ze kai su makaranta a nan" abinda takaddar ta qunsa kenan. Hawaye suka wanke mata fuska, wato dagaske Audu ya cireta daga rayuwarsa kenan baze bata damar wanke kanta ba tana roqon Allah daya bayyana gaskiyar abinda ya faru badan tana so ta koma gidan Audu ba aa sedan ya cire zargin kisan kai daya dora mata a ransa. ****************************** A gidan Audu kuwa duniya sabuwa Binta ta bude ta kori Bara'atu ciwon idonta yanzu bata da wata damuwa ta samu gida ta samu Miji yanda ya kamata musamman wannan abin daya faru yasaka yake qara riritata yana lallabata da sunan tausayinta yakeji akan abinda ya faru. Da farko da taga an bar yaran bata damu ba dan ta qulle a ranta ta samu bayi sedai yanda taga Audun ya ninka kulawar da yake musu sanda uwarsu tana nan yasa hankalinta ya tashi dan haka tasan yanda tayi Abdullahi ya tafi makarantar kwana wanda daman an gama masa shirin hakan tafiyar Bara'atu tasa Audu yace an fasa nan ta san yanda tayi ya tafi daman tare suke kwana dasu Babangida shine dawainiyarsu idan Mairo tazo ta karba babu abinda Bintan take musu se Audu na gida dan haka Abdullahi bayan tafiyar Abdullahi makaranta ya zaman yaran su kadai suke kwana a daki, sun saba ana tashinsu suyi fitsari ko basu ruwa da sauran abubuwa yanzun basu da meyi musu cikin dare haka Babannan ze tashi yayi ta koke koke sedai Audun ya sakko yaji dasu tana kwance se ta fake da cewar nauyin bacci ne da ita bama ta jiyo su, randa aka samu akasi suka mata fitsari a kwance ranar wuni zatayi yana gana musu Azaba idan ya fita in ya dawo kuma ta ringa cewa ita ta kasa gane kan yaran nan, qana na dasu amma se nunkufurci tamkar uwarsu haka suke mata duk yanda take jansu sunqi sake mata. Ya gasgata hakan saboda ko a gabansa ta jasu basa zuwa dalili kuwa Izayar da take musu idan baya nan kuma tace in suka fada seta yanka su, daya gaji da dawainiya dasu da dare baya samun bacci ya yanke shawarar a nemo me aiki da zata ringa kwana nan kuma tace bata yarda ba qarshe dai ya yanke shawarar mayarwa da uwarsu su tunda yasan itama ba a sonta ta barsu ba Yakubu ne ya tilasta mata wanda tunda ya koma a Lagos ko sau daya basuyi magana ba, fushi yake na gaske dashi shi kuma bega abinda yayi me girman da har Yakubu da sauran yan uwansa zasuyi fushi dashi haka ba. Basu dubi abinda ita Bara'atun ta aikata ba, idan daya bar Binta niyya tayi ta daga maganar zuwa Kotu sakin da yayiwa Bara'atu ne ya rage kaifin rigimar amma kowa be duba hakan ba laifinsa ake gani hatta da Alhaji Zakariyya Baban Bintan seda yayi masa fada sosai akan abinda yayi dukda ya fahimci da alama Alhajin be san musabbabin sakin ba. Kwanci tashi har aka shekara da rabuwar Audu da Bara'atu a sannan kuma Binta ta sake haihuwa aka maida mata da sunan Babanta Zakariyya, rayuwa taci gaba da gungurawa, budi da Arziqi suna qara zuwarwa Audu a shekarar kuma yaje aikin Hajji tareda Yaya Baba babban Yayansu da Goggo Fadi, da Yakubu yaso suyi tafiyar amma yace ba zashi ba dan har sannan be sauka daga fushin da yayi da Audun ba, wannan dalili ya saka Audun bawa Yaya Baba kujerar ita kuma Goggo Fadi Yakubu ne yace ya biya mata, a cewarsa iyayensu Malam da Dada duk basuyi tsahon ran da zasuci arziqinsa ba dan haka yayi mata yasan zasuyi Alfahari dashi a inda yake ai kuwa taji dadi yayanta sunji dadi suka ringa masa Addu'a kamar me wannan abun da yayi ya saka Yan uwan zage jin zafinsa akan rabuwa da Bara'atu, dukda tafiyar ba'a son ran Binta akayita ba amma ba yanda ta iya tunda tana da danyan Jego a sannan haka sukaje suka dawo Audu ya koma Alhaji Audu. Bayan dawowar Audu daga aikin Hajji ya tattara kudade daya dade yana tarawa tun bayan daya fara harkar mai. Kaduna ya nufa dasu ya samu Alhaji Zakariyya. Sanda Alhajin ya gama sauraron jawabinsa tsaf yana kallonsa yana murmushi. Shikam haka nan Allah ya dora masa qaunar Audun, tamkar sun hada jini ta wani gurin. "Da gidan Mai, da jarin dana baka duk kyautace Abdullahi shiyasa hatta da filin da sunanka aka siyeshi haka nan na baka zabin sunan da za'a sakawa Kamfaninka. Ina fatan ya zame maka hanyar riqe kanka da Ahalinka gaba daya kuma Al'umar annabi su amfana da dukiyarka" Alhajin ya fada yana kallonsa. Haka Audu ya dawo Kano cike da mamakin karamci irin na Alhaji Zakariyya, wannan ya saka ya qara daura aniyar kulawa da Binta domin yana ganin babu wani abu da zeyiwa Alajin ya biyashi tamkar kyautata mata. Yanayin Budi da sana'arsa ta sakashi haduwa da sababbin Abokanai matasa masu tashen kudi kamarsa a lokacin, kamar kuma yanda rayuwa take a kowanne fanni mutum yakan hadu da Abokanai na kwarai dana banza, ya rage a karankanka kayiwa kanka Alqalanci kabi wanda Tarbiyya da dabi'arku tazo daidai to hakan ce ta faru da Audu yayi sababbin Abokanai da suka kasance Yan cikin kwaryar Birni wayayyu kuma yan Boko sun fantsama cikin harkar Man fetur domin sannan itace harka data bullo da akeyin kudi da ita a dare daya. Alhaji Bashir da Alhaji Ali sune mutum biyu da suka fi shaquwa da Audu saboda koda tafiya ta kamasu zuwa inda suke dakko Mai tare sukeyi sannan suna wasu sabgogin Kamar fitar Kayayyaki irinsu Cocoa da Qaro zuwa qasashen dake da buqatarsu. Wannan shawarar Audu ce dan tun yana zaman bakin rimi yakan tsince hirar ana zuwa daga waje ana siyan wadannan Abubuwa. A yawace yawacen kasuwancins yasan duk inda ake samunsu dan haka suna haduwa da Alhaji Bashir wanda shi kuma yana da kyakykyawar Alaqa da wasu Turawa dan a qasar waje yayi karatu nan da nan aka qulla kasuwancin se Ali ya shigo ciki shi kuma ya nemo musu masu siyan Qaro nan da nan Kasuwa ta bude musu Arziqi kamar ana ruwansa ta ko ina zubowa yakeyi. *MAMAN MARYAM ONLINE BUSSINESS* *Ina kuke Mata Yan kwalisa , Ina nufin isassun Mata ,Wai shin Kuna da labarin shahararren company nan namu na GHT wato good healthtreatments* *Wanda yazo muku da fitattu Kuma* *ingantatattun suppliment ,na dukkan matsalolin ku*❓ *Ina maisan tayi kyau,irin na isassun Mata ya fitar Miki da shef dinki tayi Miki gyara in and out ,nemi royal jelly dinmu na company GHT* *Wanda aka yishi da xuma ,kundai San amfanin Zuma basai na fada miku ba , hajiya ta kixo ki Yi gyara domin ki kerewa sa,a kije taro ko baki da ko sisi kiji Ana rangada Miki hajiya , saboda yanda Zaki Kara kwarjini ,kina walwali acikin mutane , magungunan ght anti agen ne suna maida tsohuwa* *yarinya ,yarinya Kuma ta koma jaririya* *Muna da magunguna iri iri* *NA GYARAN JIKI* *NA GOGE NANKARWA* *NA RAGE QIBA* *NA CIRE TUMBI* *NA QARIN HIPS* *NA GIRMAN BREAST* *NA QARA TSAHON GASHI* *NA QARIN NI'IMA WANDA ZAI SAUKAR MIKI DA NI'IMA YA QARA MIKI DADI DA ZAQI A GURIN OGA* *Muna da hadin bita zai zai ,indai kishiyar ki tana Shan magungunan GHT, tohh lallai sunan ki sorry domin kuwa tazarar dake tsakanin ku kamar tazarar sama ne da kasa* *Muna da Wanda zai matseki ciki da waje Andai na yayin dinki uwargida*, *Sannan company mu na GHTBai tsaya anan ba* *Ya kawo muku maganin dukkan matsalolin ku* *INA MASU HAWAN JINI?* *INA MASU CIWON ZUCIYA?* *INA MASU CIWON QODA?* *INA MASU CIWON HANTA?* *INA MASU SICKLER?* *INA MASU HIV?* *INA MASU CANCER?* *INA MASU NEMAN HAIHUWA?* *Tohh Ku matso GHT taxo muku da magungunan matsalolin ku* *Kuma muna da testimonys da yawa ,na wadanda suka gwada suka da ce* *Munanan a KANO KUNTAU* *Kuma muna tura Kaya ko wanne gari cikin aminci da gaskiya , kuma kayan mu muna badashi ne cikin price Mai rahusa ga kyau ga inganci sannan ga Rahusa* *Kutuntube mu ta wannan number 📞08129249549* *📲07011401314* Audu be tsaya iya nan ba yana Noma, manyan gonaki ya siya a Bechi sannan a Gadonsu da yake juyawa an fitar kowa ya siya masa tasa Bilki da Aisha sun bawa Mazajensu suna kula musu da ita shi kuma ya karbi hayar ta Yakubu data Baballiya yana Nomasu, babu abinda baya Nomawa haka nan be yada saide saiden Kasuwa ba Shagonsa na kayan yara da mata na nan ya qara bunqasa ya zuba yara suna kula masa dasu. Alhaji Bashir shine me rawar kai a cikin guruf dinsu kuma shi ya fara diban Audu suna yawo a gari, shine rakashi gurin waccen yau gobe gurin waccan, tun yana zuwa rakiya kawai har ya zama shima ya fara kule kulen Mata. Dukda dai iyakar hirace take hadashi dasu sabanin Abokin nasa da yake taba shashanci da Matan. Ya kashe musu kudi su biyashi da Jikinsu bayan harkar mata har ruwa yana korawa kuma duk abubuwan da yakeyi yakan nunawa Audu hakan ba komai bane, a nan Nigeria ne ake daukarsu a wani Abu amma yej turai yaga rayuwa kuma menene amfanin neman da sukeyi idan ba zasuji dadin rayuwarsu ba? Ali ma yana kula mata amma shima kamar Audun hirace kawai amma kuma su ukun ko da yaushe suna tare, duk yawon da Bashir zeje zasu rakashi su suka bude masa Ido da zuwa Hotels, su kama daki su wuni suna hira da yan mata a kashe musu kudi. A tun ana fitar rana har ta kai an koma ta dare. Idan ya dawo gida da Magriba ya gama uzurinsa ze salla wanka ya fita, Binta ta bararraje a gida hankali kwance ita kadai Babu Bara'atu. Bata wani damuwa da fitar tasa tunda tana samun duk wasu buqatunta idan ya zauna a gidan ma.me zeyi mata kuma a tunaninta be kawo mata cewar gurin Mata yake zuwa ba musamman data san yana harkoki da yawa yanzun. A irin wannan yawaye yawacen Bashir ya kwashe su gari ya gari har kwantagora, basu san inda zasu ba seda suka gansu tsulum a gidan Karuwai, wai Ashe Ajo za'ayi shi kuma Bashir din da yake babban kwastoma ne kusan duk wata Karuwa data amsa sunanta a Kano yasan da zamanta to dalilinsa na zuwa kenan harya kwashi Abokanansa suka tafi tare. Ashe qaddarar Haduwa da Zubaida Yar Dagwas ce takai Audun Kwantagora, kyakykyawar yarinya Baqa me matsakaicin jiki yana ganinta Bara'atu ta fado masa a rai, idan yace be damu da rabuwarsu ba yayi qarya amma yakan danne zuciyarsa da cewar tayi abinda ya cancanci ya rabu da ita. A yanda ya fahimta ko a cikin Karuwan Zubaida me Aji ce domin daga shigarta zuwa yanda take kamewa a gefe tanawa kowa kallon be isa ba ga Maza nata zuwa suna mata magana amma taqi koda yi musu kallo arziqi balle ta karbi tayinsu, bayan an tashi daga Ajo Bashir ya wuce sharholiyarsa Ali da Audu na zaune a dakin da suka sauka. Babu irin macen da Bashir be tura musu ba amma Ali ya kore su. "Bana fatan na daukarwa Ahalina bashin zina dan ban san wanda ze biyashi ba, iya abinda mukeyi Allah ya yafe mana shima ina masa fatan ya shiryu ya dena abinda yakeyi" Ali ya fadawa Audu sanda yaga shaidan yana qoqarin ingizashi ya karbi tayin wata Kilaki datazo kansu tana duk wani abu data san zeja hankalin Namiji gareta, Alin ya mata korar kare. "Nifa Ali da akwai yarinyar dana gani, kuma wlh ba sha'awarta nake ba ji nayi kamar sonta ya kamani a kallon farko" Audu ya fadawa Ali abinda yake zuciyarsa dan tunda ya zauna Tunanin Zubaidan yakeyi duk kuma macen data shiga se yayi fatan Allah sa idan ta fita ita ce zata biyo baya amma be ganta ba. "A nan kaga macen da kake so? Ko kuma kawai kace mun kaima zaka fada ruwa" Ali ya fada yana gyara kwanciyarsa. "Wallahi dagaske nakeyi, baka kuka da ita ba? Wata yar baqa haka ta saka jan kaya, dana kalleta se na ganta kamar Matata ta farko da muka rabu tunda na zauna a nan nake tunaninta" Audu ya sake fada. Ali ya juya masa baya yana cewa "Lallai ka haukace Audu" daga haka yayi shiru. Audu kuwa be iya runtsawa ba se gabanin Asuba, tunanin Zubaida ya addabi ransa. Jin ta yakeyi a zuciyarsa kamar wadda ya shekara da sani abin tamkar Asiri a dan baccin da yayi kafin gari ya waye ma har mafarki ta yayi. A daren ranar sun shirya washe gari zasu taho dukda Bashir be so ba sedai gari na wayewa Audu yacewa Ali su bari se gobe su tafi" "Sedai na tafi na barku a nan dan ni banga abinda ze saka na qara kwana a gurin nan ba" Alin ya bashi amsa. "To ka rakani na gwada sa'ata, idan ta kulani shikenan ko yau din zamu iya tafiya" cewar Audu. Kallonsa kawai Ali yayi dan lamarin Audun ya fara bashi tsoro. Ya tsoron kar maganar Hausawa ta tabbata da sukace zama da madaukin Kanwa na kawo farin kai, idan Audu ya dauki Halin Bashir to in beyi da wasa ba shima zasu jashi ciki dan haka ya kakkabe rigarsa ya fice daga dakin yana cewa shidai ya tafi ze hau motar Haya. Qarfe goma suna tsaye bakin mota gaba dayansu, Bashir sunyi fada da Karuwar daya kwana da ita har taji masa ciwo da kwalba ya mata dukan mutuwa wannan fushin ya saka ya fasa qara kwanan da yayi niyya yace su tafi shi Ali daman harya fara cigiyar inda ze samu motar Kano yaga sun fito. Bashir na sallama da jama'ar sa Audu har ya shiga mazaunin Direba dan shi ze jasu saboda ciwon hannun Bashir sega Zubaida ta fito daga gidan taci kwalliya daurin nan kamar ze fadi saboda yanda ta tsikara shi hannu ta riqe da jaka madaidaiciya da zata ci kala a qalla Kala uku se qaranar jakar mata a daya hannun da alama wani gurin zataje kuma tafiyar kwana ce. "Yar dagwas, an sauka daga sarautar kenan" Bashir ya fada yana kallonta, tayi far da ido, cikin yanga da iyayi tace "Eh, ina kayi? Naga kamar tafiya zakayi ko?" "Kano na nufa, kefa na ganki da jaka da alama balaguro zakiyi" "Zan sauka a Zariya" ta fada tana wucewa motar, ta aje jakarta akan Boot ta wuce ta bude gaba ta shige kai kace motar tace. Bashir ne ya saka mata motar a Boot haka suka kamo hanya, duk yanda take daurewa seda ta biyesu ta shiga hirar, sun tsaya a hanya zasuyi sallah Audu ya samu damar yi mata magana shida ita. "Kaga malam, nifa ba irin sauran masu Arhar da kuka saba tayawa bace" ta bashi amsa tana farfara ido ta wuce ta barshi a gurin yana murmushi kamar wawa. Dagaske sonta yake, irin soyayyar nan ma me zafi. Har qofar gidan da zataje suka sauketa a Zariya dukda tace su ajiyeta tun akan hanya. "Nan ne sabuwar maboyar taki kenan? To sena rako Abokina" Bashir ya tsokaneta, ta harare shi kafin ta Audu tana taunar cingam qas qasa tace "Nagode Samari, se wani jiqon" "Shege Abokina wlh ka samu shiga, kasan uban nacin da nayi akan yarinyar nan kuwa amma taqi bani fuska? Kai bani kadai ba kowa mararinta yakeyi amma yarinyar nan yanda kasan kudi wahalar samu ne da ita, daga qusoahin gwamnati se Sarakuna take kulawa" Bashir ya fada yana dukan kafadar Audu. Ali yaja tsaki yace "Wlh kayiwa kanka fada karka kuskura ka bari shaidan ya maka ingiza me kantu nidai babu ruwana daga yau ma in sha Allah bazan sake binku fita irin wannan ba" "Nifa na gaya maka sonta nakeyi dagaske" Audu ya fada bayan sun hau titi. Bashir ya ringa dariyar iskanci yana cewa "A sannu dai duk zasu hau saiti, wato ina gaya muku dadin duniya a sha ruwa ga mata, kai Allah ka yafe mana kurakurenmu". Haka har suka iso Kano. Ba'a rufa sati ba ya kama hanyar Zariya ba tareda ya sanarwa da Abokanansa ba saboda yanda tunanin Zuby ya addabeshi, yaje gidan da suka ajiyeta wanda se sannan ya gane nan ma gidanmata masu zaman kansu ne, ya rasa ta inda ze fara nemanta. Har gurin Magajiyar gidan aka kaishi tace babu Zubaida a gidan haka ya haqura ya dawo Kano da qunar zuciya sedai duk yanda yayi akan ya yakiceta ya haqura da tunaninta abin yaci tura. Gaba daya ya shiga damuwa ya zaman har walwalarsa ta ragu. Da Binta ta matsa masa da tambaya se ya ce mata Asara yayi, aiko ta si ta fishi shiga tashin hankali ma dan Binta na son kudi, dukiyar Audu kuwa jinta take kamar tsokar jikinta a kullum zancenta Duk abinda yake dashi nata ne tunda itace sila shiyasa take baqin ciki idan yayi Alkhairi wa wasu, ta bangarenta kuwa duk abinda take dashi ko take samu babu me ci, hatta a karan kanta mugunta takeyiwa kanta dan da wani ya mori abu tareda ita gara ta haqura da abun itama. Wata biyu Audu ya kwashe yana dakon soyayyar Zuby, dayaga abin baze fita daga ransa ba tilas ya samu Bashir ya roqeshi akan ya nemo masa ita. "Wlh sonta nake Bashir kuma da Aure" ya fadawa Bashir din. "Amma dai Audu baka da hankali, to ai koni da nake cikakken dan Bariki iyakata da Karuwa na biya buqata ta mu rabu a gurin duk matan da suke yawo a garin nan ka rasa wa zuciyarka zata so se Karuwa? Hauka kake ko shaye shaye ka fara?" Bashir ya fada cikin madaukakin mamaki. "Nidai idan zaka nemo mun ita kawai ka nemota Malam babu ruwanka ko Magajiya ce a hakan naji na gani kuma ina sonta in har ta amince kuma auranta zanyi" Audu ya bashi amsa cikin tsare gida. Bashir ya kunna sigarinsa yana zuga yace "Babu shakka Haqqin Bara'atu ya fara dabaibayeka tun ba aje ko ina ba, ka saki yar gidan mutunchi me Cikakken Asali zaka maye gurbinta da Karuwa to Allah ya kyauta ka shirya gobe muje Zariyan, da kace musu Yar Dagwas da tuni an nemo maka ita sedai kuma idan suna ta canza a can dan halin matan Bariki ne basa amfani da sunansu na Ainihi. *MATAR MUTUM* *NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER* *FIKRA WRITERS ASSOCIATION* *LITTAFIN KUDI NE* *PAY 500 A ASUSUN* *7061838488* *OPAY DIGITAL SERVICES* *MARYAM FAROUK* OR *0709290797* *ACCESS BANK* *SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488* *IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705* *Kuyi following dina a Arewabooks @Maryamfarouk01 inda zaku karanta wannan littafin tareda sauran littattafaina* *NAGODE* *PAGE 16* Kamar yanda Bashir ya fada suna isa suka tambayi yar dagwas se gasu a dakinta aka rakasu. Zubaidan na kwance kamar mara lafiya suka shiga, ta ringa kallonsu da mamaki dan bata gane Audu bama Bashir dai data fi waya shi ta gane. "Lafiya? Tara ko bashi?" Ta fada cikin tsiwarsu irin ta yan Bariki bayan data miqe tsaye. Audu dai se binta yake da kallo Bashir yace "Ai kya bamu gurin zama musha ruwa tukunna yar dagwas", tayi gatsine kafin ta dauki wani siririn mayafi ta yafa a kanta da babu dankwali ta fita tana tafiya a hankali. "Duk yanda akayi dan Hau ta hadu dashi ya lakada mata na jaki shiyasa ka ganta haka" Bashir ya radawa Audu. Wani duumm yaji a zuciyarsa, shikam So be kyauta masa ba ya rasa macen da ze zargo masa se yar bariki wadda jikinta bashida shamaki da Maza. Zuby ta dawo da kwalabe uku a hannunta, biyu na Giya is Coca cola daya ta ajiye a gabansu. "Ga naka nan wadannan nawa ne" Bashir ya fada yana tura masa Coke din. Seda ya zuqe kwalba guda kafin ya kalli Zubaida dake zaune daga gefe ta jingina tana kada qafa yace "Tafiyar ta Aboki na ce, kwanaki ma yazo yayi ta bulayi ni ban ma san ya akayi yasan sunanki Zubaida ba yazo haka ya koma ba tareda ya sameki ba, bari na baku guri na dan nemi inda zan rage lokaci" ya fada yana miqewa da dayar kwalbar a hannunsa. "Kaga jashi ku tafi ni ba lafiya ta isheni ba kuma ko qalau nake kasan tsadata ba haka nan ake fado mun ba kamar wata mara Aji" ta dakatar da Bashir din, se yayi murmushi yace "Al'amarin da yake tafe dashi yafi wannan kedai ki saurareshi kawai" daga haka ya fita ya barsu. Audu ya muskuta yana kallonta soyayyarta na qara huda zuciyarsa yace "Bakida lafiya ne" "Matsala aka samu nayi ciki, uban yace ze karba kuma naga kar daga baya yazo ya mun Akuya na zubar" ta fada masa kai tsaye kamar wadda ta aikata abin kirki, is ya kasa cewa komai ya zuba mata ido kawai zuciyarsa na bugawa. Ina jinka fadi abinda ya kawoka dan kwanciya nake so nayi" ta sake fada tana gyara zama, zaman shima ya gyara ya fuskanceta dakyau kafin ya shiga zayyano mata abinda yake cikin zuciyarsa dan ya gaza dannewa, "Kuma ni da Aure nake sonki, ina so ki bar wannan rayuwar ki koma gida gaban iyayenki wannan rayuwar bata dace da Mace kamarki ba, ki je kiyi Istibra'i zan aureki". A duk maganganunsa fadar ta koma gida gaban iyayenta ne ya jefata a wani hali ya tado mata da tsohon mikin dake zuciyarta nan da nana hawaye suka wanke mata fuska. Kewar gidan da Mahaifanta ya taso mata se gani yayi ta hade kai da guiwa tana kuka wiwi. Hankalinsa ya tashi da kukan da take ya kuma shiga mamakin me ya sakata kuka, shidai ba wa'azi yayi mata ba balle ace tsoron Allah ne ya ratsata kawai ya gaya mata yana sonta ne ze Aureta amma take wannan kukan kamar wadda zata mutu take. "Ki dena kuka dan Allah" ya fada cikin rabewar murya. "Ka tashi ka fita" ta bashi amsa cikin bada umarni. Ya tsaya amma tsaqar data buga masa tasa dole ya fita cike da mamakinta ya zauna a qofar dakin. Zubaida kuwa tana kuka ta koma tunanin Baya, gida take tunuwa da mahaifiyarta tareda sauran yan uwanta da kuma dalilin daya fito da ita. Duk ranar da aka ambaci Iyaye ko Gida se tayi irin kukan nan, tana so ta sake ganin nata amma bata da hali. Kalaman Mahaifinta suka dawo mata sanda yake korarta daga gida. "Ki tafi, idan kika sake waiwayarmu Allah ya isa iyakar abin kunyar da kika jamun ya isa ki tafi duk inda zakije Zubaida na yafeki daga cikin Yayana". Cikin dare ya koreta, ba tareda yayi tunanin ina zataje ba wane hannu zata fada kuma ya gaya mata karta kuskura taje gurin danginsa kona mahaifiyarsu. Hatta da yan unguwa da suka tausaya mata suka so bata mafaka Tijara yayi musu yace ze hada duk wanda ya shigar masa hurumin gida da hukuma haka ya koreta se tasha taje ta samu mafaka duk akan dalilin Qaddarar data fada mata wadda shine sila. A dalilin kasa sauke nauyinsu da Allah ya dora masa na ciyarwa da sauran buqatu ya tilasta mahaifiyarta fara dora mata tallan shinkafa da wake tana kaiwa Bakin Kasuwa kuma a nan ne qaddara ta hauta wani Azzalumi yayi mata wayo yayi mata fyade, shekararta goma a sannan, ya gana mata Azabar data fitar da ita daga hayyacinta qarshe ta farka ta ganta a gidansu Kwance ga Mahaifiyarta na Kuka Mahaifinta kuma na Sababi kamar zeyi Aman wuta. Yana ganin kuma ta farka be duba komai ba yace ta tashi ta fitar masa daga gida, a fadar sa daman an sha gaya masa ana ganinta a shagunan Maza, ko a sannan din be yarda Fyade akayi mata ba, a yanda wanda suka tsinto ta suka gaya masa wai ciki ta zubar, wanda ya bata maganin ya gudu se ita suka tsinto cikin Jini a wani kango. Babu dogon tunani babu komai Mahaifinta ya yanke wannan danyan hukunci na korarta a cikin dare. Beyi tsinkayen cewa a sannan ko Al'ada bata fara ba ballantana ace ta dauki ciki, yayi mata korar kare cikin rashin Imani, Mahaifiyarta da qannenta naji suna gani tabar gidan shekaru goma kenan kuma kamar yanda ya fada bata sake koda taka qafarta a qasar Kano ba da Asuba tabi wata mata Mai siyar da Abinci a tasha daman ta santa idan ta kawo tallah tana gaisheta matar tasan abinda ya faru da Zubaidan dan haka data ganta cikin daren bata tambayi ba'asi ba kawai ta dauketa ta kaita dan dakinta na langa langa dake cikin Tashar. A nan ta gyarata tayi mata wanka ta kuma bata Abinci washe gari da Asuba suka hau mota suka bar Kano dan dama taga matar ta hada kayanta tsaf da alama zatayi Balaguro, bata tsinci kanta a ko ina ba se a Kwantagora, da fari Abinci suke siyarwa da giya a nan gidan daga matar ta ingizata zuwa ga wannan rayuwar da take nadama da dana sanin shigarta. Takanyi kuka tace me yasa bata tsaya ba Babanta ya halakata tunda yace idan bata fita ba seya kasheta? Data sani ta zauna ya kashe ta ta mutu tun sannan qila da tana Aljanna abinta da wannan qazamar rayuwar data jefa kanta a ciki. Audu na qofar dakin yana jiyo kukan ta daga ciki, kasa daurewa yayi ya koma ya tsaya akanta yana ganin yanda take kuka har jikinta na jijjiga. "Dan girman Allah kiyi shiru, idanhar maganar so ko aure danayi miki ce ta sakaki wannan kukan na janye na haqura ke dena Kukan haka" ya fada cikin sigar lallashi. Bata bari ba, haka ya kai tsugunne ya ringa lallashinta da kalamai masu kwantar da hankali. Shida kansa yayi mamakin inda ya iyasu, be haqura ba har seda ta dena kukan tana ajiyar rai da jan majina. "Kiyi tunani akan maganata" ya sake fada mata ba tareda ya sare ba. "Ta yaya mutum kamarka me kamala, na fahimci ba halinka daya da Abokinka ba ya za'ayi kace zaka auri Karuwa kamata wadda bata da mutunchi ballantana daraja?" Ta fada hawaye na sake sakko mata. Audu ya zauna da kyau ganin ta sakko tana so suyi magana yace "Nima ban sani ba, amma na tabbatar qila Allah ne yaso dana zama silar fitar dake daga wannan rayuwar shiyasa ya doramun sonki. Sannan maganar Mutunchi ko Daraja, ban sanki ba bansan daga inda kika fito ba amma na tabbatar koma daga ina kike kin kasance Mace me Mutunchi da Daraja a baya, qaddara ce ta kawoki nan domin mata kadan ne suk shiga Bariki da son ransu, mafi aka sari Qaddara ce take afka musu wadda mutane suke kasa yi musu uzuri harsu ingizasu ga zuwa abinda yafi wanda ya same su a baya muni. "Duk abinda dan Adam yake aikatawa muddin be mutu ba yana da damar shiriya ya nemi yafiyar ubangijinsa, kema lokaci be qure miki ba. Ki bar wannan rayuwar da babu komai cikinta se qasqanci, ki koma gida wlh da gaske nakeyi zan aureki bada wasa nake sonki ba". "Mahaifina ya koreni, yace karna sake komawa gidansa idan har naje be yafe mun ba. Ina so naje, ina kewar mahaifiyata amma bana son na sake shiga wani fushin nasa akan wanda nake ciki" ta fada cikin sauti me ban tausayi. "Ke din yar wane gari ce? Kuma meya fito dake daga gida?" Audu ya tambayeta. Bata boye masa komai ba na daga labarin rayuwarta ta gaya masa gaskiya, yaji tausayinta kwarai dagaske ya kuma ga baiken Mahaifinta. Irin wannan qaddarar ta fadawa mata da yawa, idan da ace iyaye suna taya Yayansu karban qaddararsu a yanda tazo musu da an samu raguwar masu fantsama Bariki. Da yawan iyaye Sukan manta cewar Abin kunyar da suke tunqahon yayan sun jawo musu har yasa suka kada su duniya kadan ne akan rayuwar da suke jefasu suyi, ga dakon zunubi domin duk abinda suka aikata na barna tare za'a raba musu Sakamakon da iyayen saboda sune suka turasu zuwa ga barnar. A tunanisa da a ringa zunden mutum ana cewa yarsa ta zama Karuwa gara a kira shi uban wadda aka tabayiwa Fyade ko tayi cikin shege ya barta a gabansa ta shiryu har ya aurar da ita wannan haqurin da mutum yayi se ubangiji ya dubeshi ya shirya masa zuri'a amma korar yara akan wata qaddara mara kyau ba daidai bane, su kansu Iyayen sunyi bankwana da kwanciyar hankali daga ranar da suka kori Yayan nasu basa sake samun nutsuwa. Audu basuje Zariya da niyar kwana ba amma Alamun cin galaba akan Zubaida daya gani ya sakashi kwana a garin. Yayi mata alqawarin ze nemo mata mahaifinta muddin yana raye ze hada su kuma koya mutu ze maida ita gida gurin ragowar yan uwanta. Ya roqeta akan ta shirya su tafi Kano tare, ze bata mafaka har zuwa sanda zata daidaita da iyayenta amma taqi, tace dai yaje ba zata dawo idan har mahaifinta ya mata izini. Haka washe gari suka dawo Kano gaba daya Audu bashi da kuzari, Bashir nata yi masa shaqiyanci da cewar shima ya zama dan hannu dan tunda suka rabu basu hadu ba seda safe da zasu wuce Kano dan haka besan duk abinda ya faru tsakaninsa da Zubaida ba. A gida ya tarar da Binta cikin yanayi na neman tashin hankali dan yana shiga tambayar data fara jefa masa itace "Daga gidan uban wa kake?" A lokacin yanayin sanyin jiki da kuma martabar mahaifinta da ya wuce ya zageshi ya saka ya qi tanka maka amma kaitsaye zuciyarsa ta ringa raya masa ya gaya mata daga gidan ubanta yake ko da abinda zatayi akai. Bata haqura ba ta bishi har daki tana ihu da hargagi tareda fadar maganganu. Baturiya matar Ali ce ta gaya mata Audun sun tafi wani gari gurin Mata tareda Bashir itama tsintar zancen tayi a gurin Mijinta yana gayawa wani Abokinsa daya je gidan shine ta wanke qafa ta tafi gidan Binta ta gaya mata ranar bata iya runtsawa ba a tsaye ta kwana tana jiran taga ta inda ze bullo amma be dawo na se yanzun. Duk kalar rashin mutunchin data ringa zazzagawa be tanka mata ba ya shige daki ya kullo qofa ya shiga wanka. A ranar yake so yaje ya fara binciken iyayen Zubaida data gaya masa ita din haifaffiyar unguwar Alkantara ce, sanda ya fito Binta ta sauka daga saman harya fita kuma beji motsinta ba ya dauki mota ya bi kwatancen da Zubaida tayi masa besha wahala ba saboda sunan Mahaifinta data gaya masa Malam Hassan Na'ibi yana fada aka kaishi har qofar gidan lokacin qarfe biyar na yamma rana tayi sanyi a qofar gidan ya tarar da Malam Hassan din da wasu dattijai guda biyu kan tabarma suna hira. Ya ringa kallon mutumin, kamanninsa daya da Zubaidar, sedai yanayinsa ya nuna kamar bashi da lafiya saboda a kishingide ma yake be iya zama sosai. Audu ya qarasa kan tabarmar ya zauna suka gaisa duk suna masa kallon rashin sani. "Gurinka nazo Baba, idan babu damuwa ina so zamuyi magana ne" ya fada yana kallon Malam Hassan ganin haka ya saka ragowar suka gane baqonsa ne. *MAMAN MARYAM ONLINE BUSSINESS* *Ina kuke Mata Yan kwalisa , Ina nufin isassun Mata ,Wai shin Kuna da labarin shahararren company nan namu na GHT wato good healthtreatments* *Wanda yazo muku da fitattu Kuma* *ingantatattun suppliment ,na dukkan matsalolin ku*❓ *Ina maisan tayi kyau,irin na isassun Mata ya fitar Miki da shef dinki tayi Miki gyara in and out ,nemi royal jelly dinmu na company GHT* *Wanda aka yishi da xuma ,kundai San amfanin Zuma basai na fada miku ba , hajiya ta kixo ki Yi gyara domin ki kerewa sa,a kije taro ko baki da ko sisi kiji Ana rangada Miki hajiya , saboda yanda Zaki Kara kwarjini ,kina walwali acikin mutane , magungunan ght anti agen ne suna maida tsohuwa* *yarinya ,yarinya Kuma ta koma jaririya* *Muna da magunguna iri iri* *NA GYARAN JIKI* *NA GOGE NANKARWA* *NA RAGE QIBA* *NA CIRE TUMBI* *NA QARIN HIPS* *NA GIRMAN BREAST* *NA QARA TSAHON GASHI* *NA QARIN NI'IMA WANDA ZAI SAUKAR MIKI DA NI'IMA YA QARA MIKI DADI DA ZAQI A GURIN OGA* *Muna da hadin bita zai zai ,indai kishiyar ki tana Shan magungunan GHT, tohh lallai sunan ki sorry domin kuwa tazarar dake tsakanin ku kamar tazarar sama ne da kasa* *Muna da Wanda zai matseki ciki da waje Andai na yayin dinki uwargida*, *Sannan company mu na GHTBai tsaya anan ba* *Ya kawo muku maganin dukkan matsalolin ku* *INA MASU HAWAN JINI?* *INA MASU CIWON ZUCIYA?* *INA MASU CIWON QODA?* *INA MASU CIWON HANTA?* *INA MASU SICKLER?* *INA MASU HIV?* *INA MASU CANCER?* *INA MASU NEMAN HAIHUWA?* *Tohh Ku matso GHT taxo muku da magungunan matsalolin ku* *Kuma muna da testimonys da yawa ,na wadanda suka gwada suka da ce* *Munanan a KANO KUNTAU* *Kuma muna tura Kaya ko wanne gari cikin aminci da gaskiya , kuma kayan mu muna badashi ne cikin price Mai rahusa ga kyau ga inganci sannan ga Rahusa* *Kutuntube mu ta wannan number 📞08129249549* *📲07011401314* "To ai babu damuwa samari ina jinka ka fadi abinda yake tafe da kai wadannan ba baqi bane Aminaina ne koma menene yake tafe da kai ka fada suji" Malam Hassan ya fada. Audu ya kalli mutanen da ya kira da Aminansa kafin ya sunkuyar da kai, bashida tabbacin basa cikin wadanda suka zugashi harta kori yarsa tunda yace Aminansa ne su dan haka baze fadi maganar a gabansu ba balle su hanashi karbarta. Qara qasa da kai yayi yace "Kayi haquri Baba amma daka daure munje gefe dan maganar da take tafe dani dakai kadai zan iya tattaunata" "Ka je mana Malam kaji abinda yake tafe dashi" daya daga cikinsu ya fada, Malam Hassan yayi shiru yana kallon Audu kafin ya yunqura ya janyo sandarsa dake gefe ya tashi, Audu ma ya miqe yabi bayansa yana kallon yanda yake tafiya a gicciye tamkar wanda ya taba samun ciwon mutuwar barin jiki". A soron gidan suka tsaya, Malam din ya kwalawa wata yarinya me suna Surayya kira ta fito da sauri, kamarsu daya da Zubaida dan seda gaban Audu ya fadi daya ganta. "Kawo mun kujerata" ya fada mata ta amsa da "toh Baba" kafin ta juya babu dadewa ta dawo da kujera me qafafu hudu irin ta qarfen nan doguwa Malam din ya dogara ya zauna akai yana nunaqa Audu wani tudu me kama da Dakali dake cikin zauren amma da Qaton dutse akayi shi. Audu ya zauna yana fuskantar Malam din. "Ina jinka samari, meke tafe da kai?" "Kayi haquri da abinda nazo maka dashi Baba sannan ina fata ka fahimce ni" "Ka tafi kanka tsaye bana son wannan alayen me yasa kake son magana dani?" "Akan Zubaida ne" Audu ya fada yana kallon Malam din dan ganin yanda zeyi reacting aikuwa ya zabura tamkar ze fado daga kan kujerar Audu ya tare shi. Jikin Malam Hassan ya dauki rawa ya qanqame Audu yana cewa "Zubaida naji kace? Ina ka ganta? Kasan Zubaidata? Dan Allah tana ina daman tana tana raye?" Malam din ya fada cikin rawar baki tareda daga sauti abinda ya fito da yarinyar dazun da gudu kenan tana tambayar "Baba lafiya?" "Sunan Yayarku ya ambata, dan girman Allah ka gaya mun a ina kasan Zubaida tana ina?" Malam din ya sake fada babu tsammani se ganin hawaye yayi a fuskar Malam tamkar yanda Surayya ta fashe da kuka itama tana ce masa "Ina Yayarmu? Dan Allah ka gaya mana a ina ka santa?" "Kayi haquri Baba zan gaya muku amma se ka nutsu ka dena daga murya karka janyo hankalin mutanen waje" Audu ya fada yana zaunar da Malam din a kan Kujerar daya tashi. "Muje ciki Samari wannan maganar bata zau bace muje ka sanar mun inda kaga Zubaida" Malam ya fada yana miqewa, Surayya ta dauki kujerar jikinta na rawa suka shige ciki Audu ya mara musu baya. "Tausayin Malam da Surayya ya rufeshi ganin yanda suke kuka tamkar ransu ze fita bayan daya gama basu labarin inda ya hadu da Zubaida. "Allah ka yafe mun, wlh sharrin shaidan ne da zuciya ya ingizani na kori yarinyar nan. A sanadiyyar haka abubuwa da yawa sun faru. Baqin cikin rashinta ya saka mahaifiyarsu kwanciya jinyar da har tayi Ajalinta nima kuma na gamu da hawan jini har mutuwar Barin jiki na samu seda na shekara biyu ina jinya bayan rasuwar Habiba kafin Allah ya bani lafiya, wallahi nayi nadamar abinda na aikata babu inda kuma ban shiga ba a garin nan ina cigiyar Zubaida, har gidajen Mata masu zaman kansun na ringa zuwa ko Allah ze saka na samu wanda ya ganta amma ba'a dace ba se daga baya wani bawan Allah ya sanar mana wata Mata ce ta tafi da ita amma besan motar garin da suka hau ba. Tu daga nan na fawwalawa Allah na ke kuma Addu'ar idan har Zubaida tana raye Allah ya gama fuskokinmu kafin na koma gareshi kona nemi yafiyarta, dan Allah Samari tana ina? Ka kaini naga yata karna mutu da haqqinta a wuyana" Malam ya fada yana sake rushewa da kuka. "Kayi haquri ka kuma kwantar da hankalinka Baba, naso ace mun taho tare da ita amma taqi tace ba zata dawo Kano ba se idan har kai da kanka kace ta dawo dan bata so ta sake shiga wani fushin naka amma yanzu tunda anyi haka zan koma Zariya gobe idan Allah ya yarda a gidan nan Zubaida zata kwana" da wannan Audu yayi musu sallama tamkar Malam Hassan ze bishi haka ya ringaji, bayan ya fito daga gidan su Zubaida harya dauki hanyar gida ya fasa kaitsaye ya wuce gidan Mai. Full tank yayi, a nan ya tsaya yayi magriba ya dan ci abinci dan rabonsa da abincin kirki tun safiyar jiya kafin su tafi Zariya. Musbahu ya dauka, Dan Yaya Baba ne daya dakko ya sakashi a gidan Mai yace yazo ya rakashi a daren ya dauki hanyar Zariya. Musbahu ya ringa zare ido ganin inda sukaje, to me ya kawo su nan kuma. Zubaida na bacci taji bugun qofa ta tashi ta bude mamaki ya cikata ganin Audu. "Dama baka tafi ba?" Ta tambayeshi, ya kalli Musbahu kafin ya kalleta yace "Ki hada kayanki Asubanci zamuyi na je na samu Baba kuma ya yarda ki dawo gida" "Qaryane, yaushe kaje Kano har ka dawo nan?" Ta fada tana kama qugu, yayi gaba yana ce mata "Qanwarki Surayya ta girma kamanninku daya tamkar Tagwaye" "Innalillahi dagaske kaje gidanmu, kaha Innata me tace maka?" Ta fada tana fashewa da kuka tareda bin bayansa da sauri seya dakata yace "Kije ki hada kayanki, mahaifinki na cike da zumudin ganinki na tabbatar yau baze iya bacci ba". Washe garin kuwa Asubanci sukayi, shidai Musbahu bakinsa fal da tambayoyi amma babu me bashi amsa. Har qofar gidan Malam Hassan ya isa da mota, tun daga nesa ya hangoshi zaune kan kujerarsa ya rafka tagumi gefe Aminan sa na jiya na tsaitsaye. "Ina ga shine wancan" daya ya fada yana nuna motar dake tun karo su, Malam Hassan ya miqe jiki na karkarwa, Zubaida ta fashe da kuka ganin da gaske Mahaifinta ne tsaye qofar gida yanayinsa kuma ya nuna ita yake jira. Audu kasa jure wannan yanayi na haduwar Uba da Ya yayi bayan wasu shekaru, be ko yi mata sallama ba yaja mota suka tafi. "Wlh idan naji zancen nan a bakin wani nida kai ne" ya fadawa Musbahu sanda ya sauke shi a Gidan Mai. Gida ya wuce, yayi tsammanin tarar da yaqi saboda fita daya sakeyi ya kwana amma se yaga akasin haka. Bintan bata nuna damuwa kamar jiya ba daya shiga wanka ya fito ya tarar ta shirya masa abinci ya zauna kuwa ya nadi abinsa dan a yunwace yake yana ci amma zuciyarsa da kwakwalwarsa suna kan Zubaida ko me takeyi oho. Binta kuwa abinda ya faru jiya bayan ya shiga wanka fita tayi ta tafu gidan Baturiya. "Bari kiji, duk matar da kikaga ta isa to wayo, dabara, kissa da kisisinarta ya kaita. Karki bata wayonki a gurinsa bayan kin rigada kin fara kafa gwamnatinki. Wannan ihu da hayagagar baze saka ya fasa abinda yayi niyya ba amma cikin salo da dabara se kiga kin rabashi da koma wacece dan haka ki koma gida ki bashi haquri da sannu ki gano bakin zaren sannan muyi qoqarin daukar mataki, sannan banda abinki ai da kishiyar gida gara ta waje. Kinsan duk Namijin daya saba zama da Mace biyu ma wuyaci ne ya iya haquri da daya dan haka in har ba so kikeyi ya aurota ya kawo miki ku zauna tare ba ki rabu dashi yayi sabgar gabansa" abinda Baturiya ta gaya mata kenan shiyasa ta dawo gida amma fa a zuciyarta bata jin zata iya jurewa kamar yanda tace mata amma zata gwada dauke kai dan kamar yanda Baturiyar ta fada tabbas da Kishiyar gida gara ta wajen. Kusan sati daya da dawowar Zubaida gidansu kafin Audu ya sake zuwa, har cikin gida Malam Hassan ya saka ya shiga. "Nayi ta neman inda zan zameka ashe itama ko sunanka bata sani ba, Yaro na gode, yanda kayi mun wannan Alfarmar ina fatan ubangiji ya jibanci lamarinka ya rabaka da iyayenka lafiya, nagode kwarai daka maidomun da Zubaida gabana, nagode daka zama silar barinta rayuwar barna" Malam Hassan ya fada daga nan ya basu guri shida Zubaidan dayaga tayi wani sanyi qalau tamkar ba ita ba. "Nagode da abinda kayi mun Allah ya biya maka buqatunka na Alkhairi" tace daga nan sukayi shiru kamar kowannensu ya rasa abin fadi shi ya gaji da shirun yace mata "Ina fatan abinda ya faru a baya ze wuce, ki cire komai daga ranki ki faro sabuwar rayuwa. Abinda ya faru qaddararki ce kuma Imanin mumini baya cika har se ya yarda da qaddara me kyau ko mara kyau sannan, ina fatan hakan ya zame miki kaffara. Sannan kuma ina nan akan bakana na neman yardarki, ina so da zarar kin kammala Istibra'i za'a daura mana Aure" "Kayi haquri bana zaton na dace da nagartaccen Namiji kamarka, nagode da abinda kayi mun kuma in Allah ya yarda zan yita yi maka Addu'a Allah ya baka mace daidai da kai" ta fada cikin sanyin jiki. Babanta na cikin daki yana jiyosu yayi gyaran murya yana cewa "Wannan wace irin maganace Zubaida, kana jina ko Yaro kaje in Allah ya yarda bata da wani Miji idan ba kai ba. Banda rashin wayo ki samu miji kamarsa har ki tsaya kinibibi ai yafiki sanin abinda ya dace dashi din kuma yace ke yake so" "Shikenan Baba nagode, in sha Allahu kuma zan turo da magabata na e a tsaida magana". Watanni uku bayan dawowar Zubaida gida, a hankali tun tana sharewa harta yarda ta sakarwa Audu fuska soyayya me sanyi ta qullu tsakaninsu, dukda tana matuqar jin kunyarsa kasancewar yasan komai na rayuwarta ta baya, ta kanga kamar wata rana ze goranta mata bama shi ba babban damuwarta yan uwansa take zaton ya zasu dauketa idan har sukaji ita din wacece a baya gashi yace mata yana da mata ire iren wadannan tunanin yake sare mata guiwa taji kamar ma Auranta da Audun baze yuwu ba. Watanninsu hudu tare Malam Hassan yace ya turo magabatansa saboda yana so ya hada da Auran Surayya ayi gaba daya, su uku suka rage cikin yaya shiga da mahaifiyarsu ta haifa ukun sun rasu suma bayan rasuwar Mahaifiyar tasu se Surayya da Ibrahim Wanda yake bin Zubaida ne suka rage masa be kuma sake Aure ba tun rasuwar Habiba shekara bakwai kenan. Babu damuwar komai Kai tsaye Audu ya tafi Bechi ya samu Yaya Baba ya gaya masa cewar zasuje nema masa Aure nan da sati daya, mamaki ya kama Yaya Baba saboda Yakubu yaje Bechi ba'afi sati daya da tafiyarsa ba kuma beyi musu zancen Auran Audu ba dukda yaga alamar kamar Audun ma be san yaje din ba, tun rabuwar Auransa da Bara'atu abubuwa sukayi zafi tsakaninsa da Yakubu. Yakubun Yayi fushi me tsanani shi kuma Izza da ganin yanzu ya isa ya hanashi ya neme shi su sulhunta. Yaya Baba bashida ta cewa dan haka ya amsa masa da Toh, ya kuma sanarwa da sauran yan uwansu abinda ake ciki take Hashimu yace ba zashi ba. Aminu ya samu Audu ya tambayeshi Yakubu yasan da magabar kuwa yace masa Aa. "Wannan abinda kukeyi sam be kamata ba, kaine qarami dan haka ka nemeshi ku sasanta. Me yasa kakeyin tufka kana warwara? Kayi nasarar hade kanmu sannan kuma ka koma ka bata da Yayanka da kuke ciki daya akan Mace wannan wane irin abu ne?" "To ni Aminu menene laifina a ciki, Shi ya fiya damuwa ne kawai idan ba haka ba menene nayin fushi akan na rabu da Bara'atu nifa nake zaune da ita ni nasan matsalarta amma shi ne da fushi dan na saketa?" "Saboda yafika hango abinda yake daidai ne shi yasa kai kanka kuma da zakayi duba na tsanaki zaka gane abinda ake qoqarin fahimtar da kai. Da ace zaka ji shawara da ka haqura da sabon Auran nan ka maida Bara'atu dakinta" Aminu ya sake fada. Audu yayi shiru kafin ya kalle shi yace "To kai ka aureta mana ko kuma shi din ya aureta tunda kun fini sanin darajarta". https://chat.whatsapp.com/I8xKHGurk7EBf5ZqQdxHKG *MATAR MUTUM* *NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER* *FIKRA WRITERS ASSOCIATION* *LITTAFIN KUDI NE* *PAY 500 A ASUSUN* *7061838488* *OPAY DIGITAL SERVICES* *MARYAM FAROUK* OR *0709290797* *ACCESS BANK* *SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488* *IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705* *Kuyi following dina a Arewabooks @Maryamfarouk01 inda zaku karanta wannan littafin tareda sauran littattafaina* *NAGODE* *PAGE17* Badan Audu yaso ba sedan Yaya Baba dayace muddin ba sanarwa da Yakubu ba bazasuje masa neman Aure ba tilas ya kirashi ta wayar Landilayin wadda ya hada a gidansa shima kuma Yakubun suna da ita a Ofishin da yake aiki dan haka ya kirashi. "Allah ya sanya Alkhairi yasa ayi a sa'a" abinda Yakubun ya fada masa kenan bayan daya shaida masa zancen Auran se kuma yaji babu dadi dan haka yace masa "Amma zaka zo ko? Saboda ina tunanin a daura Auran kawai idan an kai kudin" "Ina da Ayyuka da yawa a gabana bana jin zan samu halarta sedai daga baya nazo naga Amarya amma a ina ka samo matar?" Yakubu ya tambayeshi, Audu yayi shiru kamar mara gaskiya kafin yace "Amm yar nan cikin gari ce unguwar Alkantara, yarinyar nada hankali da nutsuwa sosai se ka ganta ma" "Amma da zan baka shawara ka dauka da nace kayi haquri ka maido da Bara'atu kodan darajar yayanta ka dubi rayuwar da zasuyi a Bechi babu wadataccen Ilimin Islamiyy ada Boko" "To ya kake so nayi da wannan din bayan na sanarwa da Iyayenta zan turo so kake na zama qaramin mutum?" Audu ya fada a dake dan ya gaji da maganar ya maido Bara'atu da suka dameshi da ita, Yakubu yayi murmushi yace "Bance ka fasa ba kana iya hadasu su ukun ai Alhamdulillahi Allah ya hore maka abinda zaka iya riqe su nidai yaranka nake dubawa saboda zuwan nan da nayi na gansu banji dadin yanda suka koma ba gashi sun fara tasawa" "Naga muma a Bechin nan aka haifemu muka girma, yanzu kai bada shekarunka ba harda Aure ka kammala sakandire ka tafi Jami'a? Suma idan sun girma sun kai munzalin da zasu iya wahaltawa kansu se su dawo nan gidan su zauna yanzu dai ba wannan maganar mukeyi ba ka daure dan Allah kazo kasan dai nan duniya bani da kamarka" Audu ya fada. Yakubu yayi dariyar takaici yace "Zanyi maka Addu'a daga nan kuma da ace abinda ka fada da gaske be baka da kamata da baka qi karbar shawarata ba muddin ba cutar da kai nayi niyya ba, yanzu ina aiki ne zamu sake magana idan na samu lokaci" daga haka ya ajiye waya ya bar Audu sororo da waya a hannu seda ya kashe ma sannan ya tuna dayar maganar da yake so ya masa ta jin dalilin daya saka ya dauki Baballiya ya tafi da shi Lagos zeyi hutu ba tareda su. Sanar masa ba seda sukayi magana da Alhaji Zakariyya yake gaya masa dan a gidan Baballiyan yake zama idan sun samu hutu yanzu haka yana ma yana shekararsa ta qarshe shirye shiryen fita sukeyi. Duk yanda Audu yayi da Yakubu akan yazo Auransa qi yayi dole ya haqura badan yaso ba kuma har ransa yaji rashin jin dadin hakan saboda bashi da tamkar Yakubu sannan ya rasa abinda yasa Yakubu ya dauki wannan fushin dashi. Yanzu kenan yana so ya nuna Bara'atu ta fishi a gurinsa kenan? Haka nan ya tura su Yaya Baba da wasu Abokanansa sukaje masa neman Auran wanda ba'a tashi daga gurin ba seda aka daura shi. Yana gida ranar be fita ba yana tsammatar dawowarsu Binta natayi masa gwalgwaso ta aje wannan ta kawar da wancan surutu kuwa har kunnensa ya gaji ga babu halin yace tayi shiru ko ta fita ta barshi ya huta. Lantana ce ta kwankwasa musu qofar saman, rawar kan matar ya zarce misali seda Binta ta taka mata burki sannan ta dena zirgillin shigar mata turakar Miji. Bintan ce ta bude qofar ta leqa fuska a hade tana cewa "Meye? Wai sau nawa zanja kunnenki akan tako benen nan ballantana kiyi tunanin shiga dakin nan? Ke wace irin daqiqiyar mace ce ne Lantana?" "Kiyi haquri Hajia, baqi kukayi shine nace bari nazo na sanar miki" Lantana ta fada cikin qasqantar da kai amma a ranta zagin Binta takeyi. Binta ta yatsina fuska tace "Baqi kuma daga ina? Ni yau babu wanda babu wanda nayi da ita zatazo" "Ai Hajiya Maza ne ba mata ba kuma kamar yan Uwan Alhaji ne dan naga wasu suna yanayi dashi" Tsaki me qarfi Binta taja, ta tsani wannan zaryar maukar da yan uwan Audu suke musu. Ba'a rufa sati se wani yazo daga Bechi badan ta taka burki bama har kwana suke so su ringayi amma duk zatayi maganinsu dan ba zata dauki wannan abun ba suzo su dabaibayeshi su cinye musu dukiya to bada ita ba. Ciki ta juya ba tareda tacewa Lantana komai ba, Audu na kwance kan kujera tace "Kayi baqi" Da gaggawa ya miqe kamar wani mara gaskiya, be ko tambayeta su waye ba ya shige daki ya zuro rigar wandon jikinsa ya sauka qasan seta bishi da sauri dan se anyi komai a gabanta. Haka take duk sanda yan uwansa suka zo seta kasa ta tsare komai zasu fada ko ya basu seta gani idan akayi dace kuwa saqo ya biyo ta hannunta daman se abinda mutum ya gani. Qannensa Mata dai da suke ciki daya tun fitar Bara'atu babu wadda ta sake taka qafarta gidan se yan dakin Goggo Maryo ne suke zaryar zuwa ko gajiya basayi da wulaqancin Binta dan Mazan sun fisu kamewa da wadatar zuci muddin sukaje to dole ce ta saka ko kuma maganar Gonarsa wadda Aminu da Yaya Baba ne suke kula masa dasu yanzu. Bayan Audu ya sauka qasa a tsakar gida ya tarar da Baqin nasa a tsaitsaye. "Bismilla muje can falon" ya fada yana musu jagora zuwa falon da Bara'atu ta fita can ya gyara ya saka kujeru yake sauke baqinsa amma haka Binta zata bisu har can din. Suna zama tana shiga ko gyale bata yafo ba ta dirirce ganin harda Yaya Baba ko babu komai shidin babbane a cikinsu yanayin rayuwa yasa take ganin kamar ma ze girmin Dadynta dan wahala tasa tsufa ya masa sammako banda yanzu da Al'amura suka fara daidaitar musu ya dawo hayyacinsa dalilin Alkhairan da yake samu daga kula da Gonar da yakewa Audu amma da kam anji jiki ga tarin iyali ga Abinda suka Dogara dashi na Noma Hashimu ya ringa Ha'intarsu yana Azurta kansa su da wahala amma shine cikin walwala da jin dadi wannan ya saka suka yada makaman yaqinsu suka rungumi su Audun hannu bibbiyu gashi kuwa suna sharbar romon damakaradiyya har ya sauke farali a dalilin hakan. "Au kune sannunku da zuwa ina wuninku?" ta fada tana jada baya tareda sunne kai, suka amsa mata a tare, ta tsaya daga qofa bata fita ba bata shoga ciki sosai ba Audu ya kalleta yace "Kawo musu ruwa mana" "Ayyo toh, bari a kawo" ta fada ta juya tana dannan masa Ashar a ranta. Mairo ta kwalawa kira ta gaya mata ta kawo ruwa tayi sauri ta koma bakin qofar ta labe. "Munje kuma Babanta ya sanar mana da daman kun gama magana shiyasa bamuyi gardama ba dayace a Daura auran, to Alhamdulillahi anyi komai kamar yanda shari'a ta koyar yanzu ya rage kuma ka saka ranar da matarka zata tare, Allah ya sanya Alkhairi ya sa Abokiyar arziqi ce" Yaya Baba ya fada. Ihun da Binta ta fasa ya hanshi yin magana se ya miqe da sauri ya fita suka rufo masa baya kowa da tunanin abind aya sameta, tana tsaye ta dora hannuwa biyu a kai, ganinsu yasa ta qara fashewa da ihu me firgitarwa da tayar da hankali har tana dira qafafu kamar qaramar yarinya. "Lafiyarki? Meya sameki? Ko kunama ce ta harbrki?" Audu ya jera mata tambayoyin cikin rikicewa yana qoqarin riqeta amma taqi tsayawa, ihu take tsalawa duk qarfinta kuma taqi magana haka nan bata dena dire diren ba. "Kodai shafar jinnu ne tana dasu?" Yaya Baba ya tambaya yana ja baya, takaici ya qume Audu na abinda takeyi ya juya yana ce musu "Muje dan Allah lafiyarta qalau wulaqancine da rashin son a zauna lafiya ya sakata haka" seta ruqo rigarsa ta baya cikin gunjin kuka tace "Wlh baka isa, idanna yarda shegiya uwata ta haifeni aure? Aure fa naji suna zancen an daura maka ni zaka munafunta kayi mun kishiya da kudin ubana har yaushe ka nemi auran ban sani ba? Na rantse da Allah kayi kadan" ta fada tana cukuikuye masa riga, bayaninta ya fahimtar dasu dalilin kukan, Yaya Babba ya baza riga yace "To mu bari mu wuce dan me motar daya kawomu yana waje dama yana jiranmu, Allah ya zaunar lafiya ya kade fitina idan an tsaida ranar Biki ka sanar mana mu shirya a can ai za'a kai Amaryar kamar wannan itama ko?" Ya qarasa yana nuna Binta. "Ku koma ciki Yaya bamu gama magana ba ke kuma sakeni" ya fada yana qoqarim banbare hannunta daga rigarsa amma ta qara riqewa tam tana qara tabbata masa idan ta sake shi shegiya take. "Kaga ka kashe wannan wutar tukunna bari muje Allah ya rufa Asiri" daga haka suka fice suna waiwayen Binta dake ihu tana qara maimaitawa Audu be isa ya mata kishiya da kudin ubanta ba. Mari me kyau ya kwasa mata bayan fitarsu daya saka ta sakeshi babu shiri. Ya nuna ta da yatsa yana cewa "Kinyi na farko kinyo na qarshe ni ba sakarai bane da zaki cimun kwala a gaban mutane, Aure kuma nayi, ba'a qaro mata ke na Auroki ko ba wata kika tarar a gidan ba? To ki kiyayeni wlh" yana gama fadar haka fuuuu ya wuce cikin gida ya barta a tsaye taba sharbar kuka. A haukace ta zari mayafi tabar gidan bata ko dauki Zakariyya ba ta tafi gidan Turai can ta tarar da ita a wani birkitaccen yanayi dan itama gyale ne a hannunta da alama fita zatayi qiris ya rage suci karo kowacce taja baya. Binta ta fashe da sabon kuka tana shigewa cikin falon Turai tabi bayanta tana cewa "Gidanki zani" "Ai gani nazo, Turai ni Audu ze wulaqanta a duniyar nan ni ya tozarta yayi mun kishiya ban sani ba da kudin ubana?" "Danqari, Binta amma Audu ya shammace mu kuma wlh ko a bakin Ali banji zancen auran nan ba se yau, to ya akayi haka? Kin ma san wadda ya aura wai?" Turai ta fada cikin Tashin hankali. Binta na sharar hawaye da Majina tace "Ina na sani, badan nabi bayansa bama da yan uwansa sukazo da qila sedai naji ana gafara za'a shigo da Amarya ki taimaka mun Turai ya zanyi? Wlh bazan dauki wannan wulaqancin ba Audu be isa ya tozartani a duniya ba yayi kadan har marina fa yayi yanzun me kike tsammanin zeyi mun idan matar ta shigo". "Uhm Binta kenan, nifa Auran Audu bashi ya daga mun hankali ba kamar wadda ya auro din, Kilaki fa ya kwaso miki a matsayin kishiya, idan har Auran nan ya tabbata ai kin gama yawo Binta wlh kashinki ya bushe kishi da Karuwa" Sakare Binta tayi kukan ya tsaya mata kamar anyi ruwa an dauke kafin ta lailayo wata Ashariya me maiqo ta maka tana cewa "Kilaki? Ni aka aurowa karuwa a matsayin kishiya? Ashe barinkin Audu har tayi qaurin da ze auro Karuwa ya kawo cikin gidana? Lallai kuwa be siyo zaman lafiya ba ze kuma san ya tsokana tsuliyar Dodo, na rantse da Allah daga ita harshi se sun gane kurensu, zasu san ni Binta ba kanwar lasa bace" yeeyeyey ta cigaba da kuka. Turai ta sauke tagumi tareda yin Ajiyar zuciya me qarfi tace "Qawata wannan Al'amarin fa ya zarce yanda kike tsammani, duk fa iya kissa da manaqisarmu bamu isa mu kama qafar matan bariki ba. Ke iya qoqarinda tayi har ya Aureta ai kinsan ba qaramar kai bace wannan tararta se anyi babban shiri" ta matsa kusada Bi ta dake kuka ta dafata taci gaba da cewa "Kina ji qawata, yanzu dai tunda me afkuwa ta rigada ta afku mataki biyu ne zamu iya dauka a kai,ta siyasa zamu bullowa abun kuma ba mu zamuyi yaqin da kanmu ba, na tabbata yan uwansa basu san waya aura ba dan haka farke mata laya zamuyi duk wanda ya isa ya fada aji a danginsa ki sameshi ki gaya masa wacce Audun ya auro sannan ki sanar da iyayenki abinda ake ciki da kuma abinda ya miki ki qara maggi da gishiri ke kice dukan mutuwa ya miki ma sannan na biyu dole mu binciko ko wacece mu bi ta qarqashin qasa mu watsa auran tun a waje babu yanda za'ayi ta tare a gidanki" Turai ta fada. Haka suka ci gaba da kitsa yanda za'ayi har dare Binta na gidan kafin ta koma wujiga wujiga fuska ta kode saboda kuka ido yayi luhu luhu. Ranar bata ko kalli qafar benen Audu ba, cikin daren ta hada kaya daman Turai ta shirya mata direban da ze kaita Kaduna ai kuwa washe gari Asubar Fari tana jin Audu ya dawo daga masallaci ta dauki Jakar kayanta ta saba Zakariyya a baya ta fice. Can inda sukayi da Direban ze tsaya taje ai kuwa ta tarar dashi babu bata lokaci suka yanki hanya se Kaduna. Yanda ta wuni ta kwana da yunwa ga tashin hankalin da take ciki ya saka duk ta fita hayyacinta, inda Audu ya mareta yayi shati abinka da fuskar Ajebo, saboda iya sharri har kanta ta buga a bango yayi quli ta karci wasu gurare a jikinta da farce saboda ita kadai tasan meta shirya zata fada idan taje gida. A Makeken compound dinsu ta kwanta tana malelekuwa wai ba zata iya takawa ba bayan isarsu, Direban kansa bude baki yayi tsabar mamakin kaidin wannan matar. Qalau suka taho da qafafunta sau biyu suna tsayawa a hanya harta fita tayi uzurinta amma shine da zuwansu zatace bata iya tafiya lallai mata ababen tsorone. Mamansu na Kitchen tana bada umarnin abinda za'a girka na rana ta jiyo ihu da kururuwa a waje babu shiri ta fita tayi tozali da Binta kwance a qasa tana wannan ihu qurjinta ya buga, abinda ya fara zuwar mata shine mutuwa akayi dan haka jiki na rawa ta qarasa ta kamata. "Na shiga uku na lalace Mama wayyo Allah na" abinda take ta fada kenan sanda Maman suka shigar da ita ciki da taimakon Munira qanwarta. A falo suka barta ta sake kwanciya qasa har wani numfashi take ja tamkar wadda ake zarar ranta. "Dan Allah kiyi shiru kimun bayanin meya faru Binta, karkisa ka zuciyata ta buga ki gaya mun meya samu Mijin nako" Maman ta fada cikin tashin hankali. "Meyake faruwa haka? Ke Mamana menene? Accident kukayi ko wanine ya mutu acan?" Alhaji Zakariyya daya taso daga bacci dalilin kuwwar Binta data isa ko ina a gidan ya fada yana isa gareta, ganinsa yasa ta qara rikicewa ta shiga qoqarin miqewa tana miqa masa hannu ya riqota jikinsa har rawa yake saboda tashin hankali "Kiyi magana Binta, zakici ubanki wlh idan baki mana shiru kin fada mana abinda ya faru ba" Mama ta fada cikin tashin hankali ta jimqe hannayenta da suke fitar da zufar fargaba. *MAMAN MARYAM ONLINE BUSSINESS* *Ina kuke Mata Yan kwalisa , Ina nufin isassun Mata ,Wai shin Kuna da labarin shahararren company nan namu na GHT wato good healthtreatments* *Wanda yazo muku da fitattu Kuma* *ingantatattun suppliment ,na dukkan matsalolin ku*❓ *Ina maisan tayi kyau,irin na isassun Mata ya fitar Miki da shef dinki tayi Miki gyara in and out ,nemi royal jelly dinmu na company GHT* *Wanda aka yishi da xuma ,kundai San amfanin Zuma basai na fada miku ba , hajiya ta kixo ki Yi gyara domin ki kerewa sa,a kije taro ko baki da ko sisi kiji Ana rangada Miki hajiya , saboda yanda Zaki Kara kwarjini ,kina walwali acikin mutane , magungunan ght anti agen ne suna maida tsohuwa* *yarinya ,yarinya Kuma ta koma jaririya* *Muna da magunguna iri iri* *NA GYARAN JIKI* *NA GOGE NANKARWA* *NA RAGE QIBA* *NA CIRE TUMBI* *NA QARIN HIPS* *NA GIRMAN BREAST* *NA QARA TSAHON GASHI* *NA QARIN NI'IMA WANDA ZAI SAUKAR MIKI DA NI'IMA YA QARA MIKI DADI DA ZAQI A GURIN OGA* *Muna da hadin bita zai zai ,indai kishiyar ki tana Shan magungunan GHT, tohh lallai sunan ki sorry domin kuwa tazarar dake tsakanin ku kamar tazarar sama ne da kasa* *Muna da Wanda zai matseki ciki da waje Andai na yayin dinki uwargida*, *Sannan company mu na GHTBai tsaya anan ba* *Ya kawo muku maganin dukkan matsalolin ku* *INA MASU HAWAN JINI?* *INA MASU CIWON ZUCIYA?* *INA MASU CIWON QODA?* *INA MASU CIWON HANTA?* *INA MASU SICKLER?* *INA MASU HIV?* *INA MASU CANCER?* *INA MASU NEMAN HAIHUWA?* *Tohh Ku matso GHT taxo muku da magungunan matsalolin ku* *Kuma muna da testimonys da yawa ,na wadanda suka gwada suka da ce* *Munanan a KANO KUNTAU* *Kuma muna tura Kaya ko wanne gari cikin aminci da gaskiya , kuma kayan mu muna badashi ne cikin price Mai rahusa ga kyau ga inganci sannan ga Rahusa* *Kutuntube mu ta wannan number 📞08129249549* *📲07011401314* Dakyar ta iya nutsuwa dukda ba sosai ba ta shiga kora musu qaryar data tsara ta haddace dangane da Auran da Audu yayi ba tareda saninta ba kuma akan ta masa magana yayi mata dukan kawo wuqa dakyar ta kwaci kanta shine ta gudo. Yanda ta tsara labarin babu wanda ya isa ya qaryata ta musamman ga shaida nan jikinta ya nuna. Mamaki madaukaki ya kama iyayenta musamman Alhaji daya ringa dubanta kamar me son ya tabbatar da dagaske take ko qarya takeyi. "Wlh bazan koma ba, sedai ya zaba koni ko ita haka kawai bazanje su shafamun cuta ba kuma idan ya zabi zama da ita Dady ka gaya masa ya maido maka da duk wata dukiya daya samu ta dalilinka ai daman saboda ni ne kuma idan ya sakeni dole ya bayar tunda bata ubansa bace" Binta ta fada cikin gunjin kuka. Alhaji Zakariyya ya wuce bangarensa ba tareda yace mata qala ba ya kasa yarda da abinda ta fada, meya hada Audu da matan banza har ya gano matar Aure a cikinsu sannan da gaske Audu ne yayiwa yarsa gudan jininsa wannan dukan babu kara balle ya taci arziqinsa to kodai shaye ya fara toh? A can falo kuwa da Mama ta gaji da ihu da kururuwar Binta ta daka mata tsawa tace "Ki rufe mana baki, Audun ai ba mahaukaci bane da ze kamaki da duka haka kawai waye be san halin tsiwarki ba a gidan nan kuma Aure daman kin sani a rubuce take zeyi, ba wata kika tarar a gidan ba dan haka ba zaki fitar da ran kema za'a kawo miki wata ba. Abinda na jiye miki tun farko a Auran Tifical Bahaushe kenan wanda be yi Ilimin Boko ba balle ya waye da yanda rayuwa take, irinsu Audu a kullum tunaninsu be wuci su samu kudi su tara mata da Yaya ba basu damu da jin dadinsu ba balle walwala ko yanda zayuwarsu zata kasance, ke kikace kinji kingani dan haka yanzu babu wani dalili da ze saka kice zaki dawo mana nan, Munira ma Addu'ar Allah ya kawo wanda zero dauke mun ita nakeyi ballantana ki kaso Auranki ki dawo mun". "Kai Mama ya zakice haka bakiga abinda ya mata ba se kace ba yarki ba, kuma ko auran zeyi ya rasa wa ze auro is Karuwa haba mana wannan ai ba abune me yuwuwa bama" Munira ta fada aiko ta juya kanta tana cewa "Idan na sake jin bakinki a nan sena gwabjeki shashasha ai kema ba sanin ciwo kanki kikayi ba "Ya isa haka Firdausi, ke kuma Mamana ki shiga ciki kiyi wanka Munira ki rakata clinic a dubata, ku dauke yaron nan daga qasa sannan wanda ya kawoki tafiya yayi ko yana nan?" Alhaji Zakariyya saya sake fitowa shirin shirin fita ya fada. Se sannan suka lura da Zakariyya dake kwance qasa abinsa yana bacci Direban ne ya shigo mata dashi ya watsar dashi a qasa tareda jakar kayanta. Ta miqe tana dingisawa Munira ta dauki Yaron suka wuce ciki. KANO Rai fes Audu yayi bacci babu damuwar komai tattare dashi illah mafarkin Amaryarsa daya kwana yanayi tareda shirya yanda tariyarta zata kasance nan da sati biyu masu zuwa shima saboda ya bata damar yin shirye shirye ne daga bangarenta dan shi a shirye yake fenti kawai ze saka a sakewa dakin can tazo ta zauna. Rashin zuwan Binta dakin be dameshi ba saboda yasan koda taje qarshe rigima zasuyi, da ya dawo daga sallar Asuba har ze shiga ya dubata kuma ya fasa dan yana so ya koma bacci yasan kuma muddin ya shigan bacin rai ze kwaso dan haka ya bari akan sa hade idan gari ya waye sosai. Bugun qofar gidan da ake kamar za'a ballata ne ya tayar dashi. Ya ringa sakin tsaki yana tunanin wanene haka? Jallabiya ya saka ya sakko yana mamakin Ina Binta ta shiga ake irin wannan dukan qofar bataji ba ko itace ta fita qofar ta kulle ta waje. Takaici ya qumeshi ganin Lantana me aiki, ya tsani matar saboda kana ganinta kalar munafukai ne da ita. Ta durqushe a qasa kamar zata kwanta tana gaishe shi ya amsa a dake yana cewa "Wane irin abu ne haka zakizo kina dukan qofar mutane" "Kayi haquri yallabai kasan dokar Hajiya qarfe bakwai nake zuwa gidan nan to Nazo tun bakwan na buga ba'a bude ba na tafi shine na dawo na sake bayi bugun da qarfi ne ko bacci take kar nayi laifi tace banzo da wuri ba" Tsaki yayi ya juya ciki, harya fara hawa sama ya dawo jin tanata qwanqwasa qofar Bintan shiru ba'a bude ba, ta matsa ya isa jikin qofar ya kwankwasa kana ya murda handle din qofar. Fahimta da yayi a kulle take yasa ya zagaya ta window ta da yake a tsakar gidan ya zuge ya leqa ciki, kayana da ya gani barbaje suka fahimtar dashi bata nan, se abin ma ya bashi dariya a fili yace "Yaji tayi kenan" "Ki tafi na manta zataje zata fita yau ta fita da wuri ina bacci" ya fadawa Lantana, kamar zata fasa kuka haka ta ja qafa tana waiwayensa, kamar tace masa zata zauna ta jira tunda ko fita Bintan zata yi tana barinta tayi mata jiran gida gashi ta kwaso yunwar safe ta saka rai zatazo taci me kyau kuma ace bata nan. "Alhaji Mairo tazo ne? Kuma zuwa yaushe Hajiyar zata dawo?" Ta fada tana sunkuyar da kai, "Idan ta dawo zata saka a kiraki ba yau ba ba gobe ba, kija qofar ki tabbatar kuma ta rufu idan kin fita" ya bata amsa yana juyawa tilas ta fita taja musu qofar gidan. Audu kuwa kasa komawa bacci yayi, tunanin inda Binta ta tafi ya shigayi, qila ba zata wuce gidan Baturiya ba dan bata da yar uwa a Kano bare yace gurinsu zataje Baturiyar itace yanzu babbar Qawarta ko yace Aminiya indai ba gidanta taje ba to Kaduna ta tafi. Zabura yayi ya miqe yana salati, idan Kaduna ta tafi ya Alhaji zero dauki maganar? Ze goyi bayansa ko kuma ze goyi bayan yarsa ne? Idan Alhaji ya goyi bayan Binta yace ya sakar masa yarsa ya makomarsa zata zama kenan dan dai Alhajin shine abin tunqahonsa, duk abinda yake ganin ya tasarma zama da bazar Alhajin yake rawa. A gurguje yayi wanka ya shirya, kai tsaye gidan Ali ya fara zuwa suka hade a waje Alin na shirin fita ya kuma tabbatar masa Binta bataje gidan ba dan babu inda zata buya da ze kasa ganinta. "Dan girman Allah kazo ka rakani Kaduna" ya roqi Alin "Kai yanzu? Ina babu wannan magana, ai yanda ka tirko rigimarka se ka san ta yanda zaka kasheta. Amma fa ban taba dauka da gaske kaci kai ba Audu se yanzu, duk matan da suke garin nan yayan mutunchi ka rasa wadda ta burgeka se wannan yarinyar? Kodai Asirinsu tayi amfani dashi ta zarge zuciyarka?" Ali ya fada yana tsareshi da ido. Audu yaja tsaki kafin ya shige mota ya daga ba tare da ya bashi amsa ba Yau dinma Musbahu yaje ya dauka suka tafi Kaduna, seda ya isa qofar gidan kuma ya fara tunanin me zece musu idan ya shiga? Seda sukayi sallar La'asar da Magriba da suka riskesu a hanya kafin ya saka kai cikin gidan. Ko ina tarwai da haske, Tun daga Get suka fara gaisawa da ma'aikatan gidan harya isa qofar falo. Ta ciki Munira ta hangoshi, ta kwasa da gudu tayi daki ta fadawa Binta da tunda tayi wanka taci abinci take rama baccin da batayi jiya ba. "Wlh ko me za'ayi karki koma ai raini nema kamar ke ace a miki kishiya bayan duk fafutukar da daukar hakkin da mukayi muka fitar da waccen shine za'a dakko miki alaqaqai to babu wannan maganar" Muniran ta qara zugata. Tun daga yanda Alhaji ya amsa masa gaisuwarsa yaji guiwoyinsa sun qarayin sanyi dama Mama tana musu iso a tsayw suka gaisa ta shige ciki, yau ko Kayan Alatun da ake tarbarshi dasu be samu ba Ruwa da Lemo ma Alhajin ne yayi magana aka kawo musu. "Bansan ta taho ba Alhaji, na dawo daga sallar Asuba kawai na tarar bata nan" Audu ya fada bayan dogon shirun da sukayi kowanne kamar ya rasa abin fada. Alhaji ya nisa yana kallonsa yace "Me ya hadaku da har yasa ta baro gidan ba tareda saninka ba?". Be boye masa komai ba ya bashi labarin Auran da yayi wanda yake ganin shiya tunzurata ta baro gidan, ya rufe da qaryar cewa "Bansan cewa zasu daura Auran ba saboda tambaya kawai akaje". Shiru Alhaji ya sakeyi yana kallonsa kafin yace "Menene gaskiyar maganara data fada na cewar Yarinyar Karuwa ce?" Seda ya daga kai ya kalli Alhajin saboda kalmar daya fada din se yaga kamar tayi girma musamman ana maganar matarsa ne ina laifin yace tsohuwa, wannan ya tunzuro zuciyarsa ta raya masa ci masa mutunchi Alhajin ya tashi yi amma ya danne dan ko ya masa qarya bashida amfani tunda har magana ta fito amma a ina Binta taji wannan batun? "Kayi shiru" Alhaji ya katseshi, kansa na qasa yace "Gaskiya ne, amma ban aureta ba seda na maidata gaban iyayenta tayi Istibra'i kamar yanda shari'a ta tanadar" "To akan me ka daki Mamana har kaji mata ciwuka a jiki?" Alhajin ya fadi ainihin abinda yafi damunsa a duk cikin maganar, se Audu ya daga kai da sauri ya kalleshi jin abinda ya fada. "Wlh Mari daya nayi mata, shima kuma cin kwalata tayi a gaban yan uwana da sukazo fadamun an daura aure ta labe harta tsinci maganar shine ta shaqemun wuya nace ta sakeni taqi ni kuma zuciya tasa na mareta bayan nan ko yatsa ban nuna mata ba wlh" ya fada cikin kare kai. Alhaji bece komai ba yaja Intercom ya kira cikin gida kan Binta tazo, ba'a dauki lokaci ba ta fito tana jan qafa fuskar nan kamar dafaffen Kunu ta zauna kusada qafar Alhajin tana hararar Audu wanda ke kallonta yana mamakin abinda ya karceta a fuska kamar sunyi dambe da Mage. Ce mata yayi ta maimaita duk abinda ta fada cewar Audu ya mata, tana kuka ta shiga shiryosu harma da abinda dazun bata fada ba na cewar daman Audun ya dade yana yawon ta zubar dinsa har kwanaki yake tafiya yayi acan in ya dawo kuma tayi magana ya zageta koya hada mata da duka qarshema tace idan ta fita har gidan yake kawo mata shidai kasa cewa komai yayi saboda mamaki, maganganunta kuma babu yanda za'ayi ace qarya takeyi tunda tabbas yana yawace yawaceb har yaje ya kwanan amma ai ba abinda take fada yakeyi ba sedai kuma waye ze bada shaidar hakan? Shidai Alhaji na jinta yana kuma kallon Audu daya kasa rufe bakinsa seda tayi shiru kafin ya kalleta yace "Kinaji ko Mamana, duk wani Aure da kika gani tattare yake da qalubale muddin kuma ba ma'aurata sun bude cikinsu ba bazaka taba sani ba dan haka kowa haquri yakeyi kamar yanda kika faro haqurin kici gaba dayi kuma tunda ya auro yarinyar da take dauke masa hankali a wajen ai magana ta qare se ayi fatan kuma Allah ya hada kanku ya bada zaman lafiya. Kaikuma abinda nake so na gaya maka shine ka tabbatar kayi na farko kuma kayi na qarshe da zaka dora hannu da sunan duka a jikin Mamana, zan manta da duk wata alaqa dake tsakaninmu na maka ka a Kotu domin bana hada kowa da yayana, ban daki yar kowa ba dan haka babu hujjar da zata saka wani ya dakar mun yata. Idan tayi maka laifin da ba zau iya sasantawa a tsakaninku ba ka kawo mun qararta nizan hukuntata amma bazan lamunchi duka ba ina fatan ka gane?" Kunya, nauyi da takaici suka rufe Audu gaba daya ya rasa ma abinda zeyi, Alhaji yaci gaba da cewa "Idan Allah ya kaimu gobe yanda kikazo da sassafen nan ki tattara ku koma aje aci gaba da haquri kuma na kashe maganar nan, Aure kuma dakayi Allah ya sanya Alkhairi ya baka ladan Jihadi" "Wlh bazan koma ba, babu yanda za'ayi nayi zamab kishi da Karuwa Dady kawai kace masa ya saketa idan ba haka ba bazan koma gidan ba" ta fada cikin kuka tana bubbuga qafa.https://chat.whatsapp.com/I8xKHGurk7EBf5ZqQdxHKG *MATAR MUTUM* *NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER* *FIKRA WRITERS ASSOCIATION* *LITTAFIN KUDI NE* *PAY 500 A ASUSUN* *7061838488* *OPAY DIGITAL SERVICES* *MARYAM FAROUK* OR *0709290797* *ACCESS BANK* *SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488* *IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705* *Kuyi following dina a Arewabooks @Maryamfarouk01 inda zaku karanta wannan littafin tareda sauran littattafaina* *NAGODE* *PAGE17* Badan Audu yaso ba sedan Yaya Baba dayace muddin ba sanarwa da Yakubu ba bazasuje masa neman Aure ba tilas ya kirashi ta wayar Landilayin wadda ya hada a gidansa shima kuma Yakubun suna da ita a Ofishin da yake aiki dan haka ya kirashi. "Allah ya sanya Alkhairi yasa ayi a sa'a" abinda Yakubun ya fada masa kenan bayan daya shaida masa zancen Auran se kuma yaji babu dadi dan haka yace masa "Amma zaka zo ko? Saboda ina tunanin a daura Auran kawai idan an kai kudin" "Ina da Ayyuka da yawa a gabana bana jin zan samu halarta sedai daga baya nazo naga Amarya amma a ina ka samo matar?" Yakubu ya tambayeshi, Audu yayi shiru kamar mara gaskiya kafin yace "Amm yar nan cikin gari ce unguwar Alkantara, yarinyar nada hankali da nutsuwa sosai se ka ganta ma" "Amma da zan baka shawara ka dauka da nace kayi haquri ka maido da Bara'atu kodan darajar yayanta ka dubi rayuwar da zasuyi a Bechi babu wadataccen Ilimin Islamiyy ada Boko" "To ya kake so nayi da wannan din bayan na sanarwa da Iyayenta zan turo so kake na zama qaramin mutum?" Audu ya fada a dake dan ya gaji da maganar ya maido Bara'atu da suka dameshi da ita, Yakubu yayi murmushi yace "Bance ka fasa ba kana iya hadasu su ukun ai Alhamdulillahi Allah ya hore maka abinda zaka iya riqe su nidai yaranka nake dubawa saboda zuwan nan da nayi na gansu banji dadin yanda suka koma ba gashi sun fara tasawa" "Naga muma a Bechin nan aka haifemu muka girma, yanzu kai bada shekarunka ba harda Aure ka kammala sakandire ka tafi Jami'a? Suma idan sun girma sun kai munzalin da zasu iya wahaltawa kansu se su dawo nan gidan su zauna yanzu dai ba wannan maganar mukeyi ba ka daure dan Allah kazo kasan dai nan duniya bani da kamarka" Audu ya fada. Yakubu yayi dariyar takaici yace "Zanyi maka Addu'a daga nan kuma da ace abinda ka fada da gaske be baka da kamata da baka qi karbar shawarata ba muddin ba cutar da kai nayi niyya ba, yanzu ina aiki ne zamu sake magana idan na samu lokaci" daga haka ya ajiye waya ya bar Audu sororo da waya a hannu seda ya kashe ma sannan ya tuna dayar maganar da yake so ya masa ta jin dalilin daya saka ya dauki Baballiya ya tafi da shi Lagos zeyi hutu ba tareda su. Sanar masa ba seda sukayi magana da Alhaji Zakariyya yake gaya masa dan a gidan Baballiyan yake zama idan sun samu hutu yanzu haka yana ma yana shekararsa ta qarshe shirye shiryen fita sukeyi. Duk yanda Audu yayi da Yakubu akan yazo Auransa qi yayi dole ya haqura badan yaso ba kuma har ransa yaji rashin jin dadin hakan saboda bashi da tamkar Yakubu sannan ya rasa abinda yasa Yakubu ya dauki wannan fushin dashi. Yanzu kenan yana so ya nuna Bara'atu ta fishi a gurinsa kenan? Haka nan ya tura su Yaya Baba da wasu Abokanansa sukaje masa neman Auran wanda ba'a tashi daga gurin ba seda aka daura shi. Yana gida ranar be fita ba yana tsammatar dawowarsu Binta natayi masa gwalgwaso ta aje wannan ta kawar da wancan surutu kuwa har kunnensa ya gaji ga babu halin yace tayi shiru ko ta fita ta barshi ya huta. Lantana ce ta kwankwasa musu qofar saman, rawar kan matar ya zarce misali seda Binta ta taka mata burki sannan ta dena zirgillin shigar mata turakar Miji. Bintan ce ta bude qofar ta leqa fuska a hade tana cewa "Meye? Wai sau nawa zanja kunnenki akan tako benen nan ballantana kiyi tunanin shiga dakin nan? Ke wace irin daqiqiyar mace ce ne Lantana?" "Kiyi haquri Hajia, baqi kukayi shine nace bari nazo na sanar miki" Lantana ta fada cikin qasqantar da kai amma a ranta zagin Binta takeyi. Binta ta yatsina fuska tace "Baqi kuma daga ina? Ni yau babu wanda babu wanda nayi da ita zatazo" "Ai Hajiya Maza ne ba mata ba kuma kamar yan Uwan Alhaji ne dan naga wasu suna yanayi dashi" Tsaki me qarfi Binta taja, ta tsani wannan zaryar maukar da yan uwan Audu suke musu. Ba'a rufa sati se wani yazo daga Bechi badan ta taka burki bama har kwana suke so su ringayi amma duk zatayi maganinsu dan ba zata dauki wannan abun ba suzo su dabaibayeshi su cinye musu dukiya to bada ita ba. Ciki ta juya ba tareda tacewa Lantana komai ba, Audu na kwance kan kujera tace "Kayi baqi" Da gaggawa ya miqe kamar wani mara gaskiya, be ko tambayeta su waye ba ya shige daki ya zuro rigar wandon jikinsa ya sauka qasan seta bishi da sauri dan se anyi komai a gabanta. Haka take duk sanda yan uwansa suka zo seta kasa ta tsare komai zasu fada ko ya basu seta gani idan akayi dace kuwa saqo ya biyo ta hannunta daman se abinda mutum ya gani. Qannensa Mata dai da suke ciki daya tun fitar Bara'atu babu wadda ta sake taka qafarta gidan se yan dakin Goggo Maryo ne suke zaryar zuwa ko gajiya basayi da wulaqancin Binta dan Mazan sun fisu kamewa da wadatar zuci muddin sukaje to dole ce ta saka ko kuma maganar Gonarsa wadda Aminu da Yaya Baba ne suke kula masa dasu yanzu. Bayan Audu ya sauka qasa a tsakar gida ya tarar da Baqin nasa a tsaitsaye. "Bismilla muje can falon" ya fada yana musu jagora zuwa falon da Bara'atu ta fita can ya gyara ya saka kujeru yake sauke baqinsa amma haka Binta zata bisu har can din. Suna zama tana shiga ko gyale bata yafo ba ta dirirce ganin harda Yaya Baba ko babu komai shidin babbane a cikinsu yanayin rayuwa yasa take ganin kamar ma ze girmin Dadynta dan wahala tasa tsufa ya masa sammako banda yanzu da Al'amura suka fara daidaitar musu ya dawo hayyacinsa dalilin Alkhairan da yake samu daga kula da Gonar da yakewa Audu amma da kam anji jiki ga tarin iyali ga Abinda suka Dogara dashi na Noma Hashimu ya ringa Ha'intarsu yana Azurta kansa su da wahala amma shine cikin walwala da jin dadi wannan ya saka suka yada makaman yaqinsu suka rungumi su Audun hannu bibbiyu gashi kuwa suna sharbar romon damakaradiyya har ya sauke farali a dalilin hakan. "Au kune sannunku da zuwa ina wuninku?" ta fada tana jada baya tareda sunne kai, suka amsa mata a tare, ta tsaya daga qofa bata fita ba bata shoga ciki sosai ba Audu ya kalleta yace "Kawo musu ruwa mana" "Ayyo toh, bari a kawo" ta fada ta juya tana dannan masa Ashar a ranta. Mairo ta kwalawa kira ta gaya mata ta kawo ruwa tayi sauri ta koma bakin qofar ta labe. "Munje kuma Babanta ya sanar mana da daman kun gama magana shiyasa bamuyi gardama ba dayace a Daura auran, to Alhamdulillahi anyi komai kamar yanda shari'a ta koyar yanzu ya rage kuma ka saka ranar da matarka zata tare, Allah ya sanya Alkhairi ya sa Abokiyar arziqi ce" Yaya Baba ya fada. Ihun da Binta ta fasa ya hanshi yin magana se ya miqe da sauri ya fita suka rufo masa baya kowa da tunanin abind aya sameta, tana tsaye ta dora hannuwa biyu a kai, ganinsu yasa ta qara fashewa da ihu me firgitarwa da tayar da hankali har tana dira qafafu kamar qaramar yarinya. "Lafiyarki? Meya sameki? Ko kunama ce ta harbrki?" Audu ya jera mata tambayoyin cikin rikicewa yana qoqarin riqeta amma taqi tsayawa, ihu take tsalawa duk qarfinta kuma taqi magana haka nan bata dena dire diren ba. "Kodai shafar jinnu ne tana dasu?" Yaya Baba ya tambaya yana ja baya, takaici ya qume Audu na abinda takeyi ya juya yana ce musu "Muje dan Allah lafiyarta qalau wulaqancine da rashin son a zauna lafiya ya sakata haka" seta ruqo rigarsa ta baya cikin gunjin kuka tace "Wlh baka isa, idanna yarda shegiya uwata ta haifeni aure? Aure fa naji suna zancen an daura maka ni zaka munafunta kayi mun kishiya da kudin ubana har yaushe ka nemi auran ban sani ba? Na rantse da Allah kayi kadan" ta fada tana cukuikuye masa riga, bayaninta ya fahimtar dasu dalilin kukan, Yaya Babba ya baza riga yace "To mu bari mu wuce dan me motar daya kawomu yana waje dama yana jiranmu, Allah ya zaunar lafiya ya kade fitina idan an tsaida ranar Biki ka sanar mana mu shirya a can ai za'a kai Amaryar kamar wannan itama ko?" Ya qarasa yana nuna Binta. "Ku koma ciki Yaya bamu gama magana ba ke kuma sakeni" ya fada yana qoqarim banbare hannunta daga rigarsa amma ta qara riqewa tam tana qara tabbata masa idan ta sake shi shegiya take. "Kaga ka kashe wannan wutar tukunna bari muje Allah ya rufa Asiri" daga haka suka fice suna waiwayen Binta dake ihu tana qara maimaitawa Audu be isa ya mata kishiya da kudin ubanta ba. Mari me kyau ya kwasa mata bayan fitarsu daya saka ta sakeshi babu shiri. Ya nuna ta da yatsa yana cewa "Kinyi na farko kinyo na qarshe ni ba sakarai bane da zaki cimun kwala a gaban mutane, Aure kuma nayi, ba'a qaro mata ke na Auroki ko ba wata kika tarar a gidan ba? To ki kiyayeni wlh" yana gama fadar haka fuuuu ya wuce cikin gida ya barta a tsaye taba sharbar kuka. A haukace ta zari mayafi tabar gidan bata ko dauki Zakariyya ba ta tafi gidan Turai can ta tarar da ita a wani birkitaccen yanayi dan itama gyale ne a hannunta da alama fita zatayi qiris ya rage suci karo kowacce taja baya. Binta ta fashe da sabon kuka tana shigewa cikin falon Turai tabi bayanta tana cewa "Gidanki zani" "Ai gani nazo, Turai ni Audu ze wulaqanta a duniyar nan ni ya tozarta yayi mun kishiya ban sani ba da kudin ubana?" "Danqari, Binta amma Audu ya shammace mu kuma wlh ko a bakin Ali banji zancen auran nan ba se yau, to ya akayi haka? Kin ma san wadda ya aura wai?" Turai ta fada cikin Tashin hankali. Binta na sharar hawaye da Majina tace "Ina na sani, badan nabi bayansa bama da yan uwansa sukazo da qila sedai naji ana gafara za'a shigo da Amarya ki taimaka mun Turai ya zanyi? Wlh bazan dauki wannan wulaqancin ba Audu be isa ya tozartani a duniya ba yayi kadan har marina fa yayi yanzun me kike tsammanin zeyi mun idan matar ta shigo". "Uhm Binta kenan, nifa Auran Audu bashi ya daga mun hankali ba kamar wadda ya auro din, Kilaki fa ya kwaso miki a matsayin kishiya, idan har Auran nan ya tabbata ai kin gama yawo Binta wlh kashinki ya bushe kishi da Karuwa" Sakare Binta tayi kukan ya tsaya mata kamar anyi ruwa an dauke kafin ta lailayo wata Ashariya me maiqo ta maka tana cewa "Kilaki? Ni aka aurowa karuwa a matsayin kishiya? Ashe barinkin Audu har tayi qaurin da ze auro Karuwa ya kawo cikin gidana? Lallai kuwa be siyo zaman lafiya ba ze kuma san ya tsokana tsuliyar Dodo, na rantse da Allah daga ita harshi se sun gane kurensu, zasu san ni Binta ba kanwar lasa bace" yeeyeyey ta cigaba da kuka. Turai ta sauke tagumi tareda yin Ajiyar zuciya me qarfi tace "Qawata wannan Al'amarin fa ya zarce yanda kike tsammani, duk fa iya kissa da manaqisarmu bamu isa mu kama qafar matan bariki ba. Ke iya qoqarinda tayi har ya Aureta ai kinsan ba qaramar kai bace wannan tararta se anyi babban shiri" ta matsa kusada Bi ta dake kuka ta dafata taci gaba da cewa "Kina ji qawata, yanzu dai tunda me afkuwa ta rigada ta afku mataki biyu ne zamu iya dauka a kai,ta siyasa zamu bullowa abun kuma ba mu zamuyi yaqin da kanmu ba, na tabbata yan uwansa basu san waya aura ba dan haka farke mata laya zamuyi duk wanda ya isa ya fada aji a danginsa ki sameshi ki gaya masa wacce Audun ya auro sannan ki sanar da iyayenki abinda ake ciki da kuma abinda ya miki ki qara maggi da gishiri ke kice dukan mutuwa ya miki ma sannan na biyu dole mu binciko ko wacece mu bi ta qarqashin qasa mu watsa auran tun a waje babu yanda za'ayi ta tare a gidanki" Turai ta fada. Haka suka ci gaba da kitsa yanda za'ayi har dare Binta na gidan kafin ta koma wujiga wujiga fuska ta kode saboda kuka ido yayi luhu luhu. Ranar bata ko kalli qafar benen Audu ba, cikin daren ta hada kaya daman Turai ta shirya mata direban da ze kaita Kaduna ai kuwa washe gari Asubar Fari tana jin Audu ya dawo daga masallaci ta dauki Jakar kayanta ta saba Zakariyya a baya ta fice. Can inda sukayi da Direban ze tsaya taje ai kuwa ta tarar dashi babu bata lokaci suka yanki hanya se Kaduna. Yanda ta wuni ta kwana da yunwa ga tashin hankalin da take ciki ya saka duk ta fita hayyacinta, inda Audu ya mareta yayi shati abinka da fuskar Ajebo, saboda iya sharri har kanta ta buga a bango yayi quli ta karci wasu gurare a jikinta da farce saboda ita kadai tasan meta shirya zata fada idan taje gida. A Makeken compound dinsu ta kwanta tana malelekuwa wai ba zata iya takawa ba bayan isarsu, Direban kansa bude baki yayi tsabar mamakin kaidin wannan matar. Qalau suka taho da qafafunta sau biyu suna tsayawa a hanya harta fita tayi uzurinta amma shine da zuwansu zatace bata iya tafiya lallai mata ababen tsorone. Mamansu na Kitchen tana bada umarnin abinda za'a girka na rana ta jiyo ihu da kururuwa a waje babu shiri ta fita tayi tozali da Binta kwance a qasa tana wannan ihu qurjinta ya buga, abinda ya fara zuwar mata shine mutuwa akayi dan haka jiki na rawa ta qarasa ta kamata. "Na shiga uku na lalace Mama wayyo Allah na" abinda take ta fada kenan sanda Maman suka shigar da ita ciki da taimakon Munira qanwarta. A falo suka barta ta sake kwanciya qasa har wani numfashi take ja tamkar wadda ake zarar ranta. "Dan Allah kiyi shiru kimun bayanin meya faru Binta, karkisa ka zuciyata ta buga ki gaya mun meya samu Mijin nako" Maman ta fada cikin tashin hankali. "Meyake faruwa haka? Ke Mamana menene? Accident kukayi ko wanine ya mutu acan?" Alhaji Zakariyya daya taso daga bacci dalilin kuwwar Binta data isa ko ina a gidan ya fada yana isa gareta, ganinsa yasa ta qara rikicewa ta shiga qoqarin miqewa tana miqa masa hannu ya riqota jikinsa har rawa yake saboda tashin hankali "Kiyi magana Binta, zakici ubanki wlh idan baki mana shiru kin fada mana abinda ya faru ba" Mama ta fada cikin tashin hankali ta jimqe hannayenta da suke fitar da zufar fargaba. *MAMAN MARYAM ONLINE BUSSINESS* *Ina kuke Mata Yan kwalisa , Ina nufin isassun Mata ,Wai shin Kuna da labarin shahararren company nan namu na GHT wato good healthtreatments* *Wanda yazo muku da fitattu Kuma* *ingantatattun suppliment ,na dukkan matsalolin ku*❓ *Ina maisan tayi kyau,irin na isassun Mata ya fitar Miki da shef dinki tayi Miki gyara in and out ,nemi royal jelly dinmu na company GHT* *Wanda aka yishi da xuma ,kundai San amfanin Zuma basai na fada miku ba , hajiya ta kixo ki Yi gyara domin ki kerewa sa,a kije taro ko baki da ko sisi kiji Ana rangada Miki hajiya , saboda yanda Zaki Kara kwarjini ,kina walwali acikin mutane , magungunan ght anti agen ne suna maida tsohuwa* *yarinya ,yarinya Kuma ta koma jaririya* *Muna da magunguna iri iri* *NA GYARAN JIKI* *NA GOGE NANKARWA* *NA RAGE QIBA* *NA CIRE TUMBI* *NA QARIN HIPS* *NA GIRMAN BREAST* *NA QARA TSAHON GASHI* *NA QARIN NI'IMA WANDA ZAI SAUKAR MIKI DA NI'IMA YA QARA MIKI DADI DA ZAQI A GURIN OGA* *Muna da hadin bita zai zai ,indai kishiyar ki tana Shan magungunan GHT, tohh lallai sunan ki sorry domin kuwa tazarar dake tsakanin ku kamar tazarar sama ne da kasa* *Muna da Wanda zai matseki ciki da waje Andai na yayin dinki uwargida*, *Sannan company mu na GHTBai tsaya anan ba* *Ya kawo muku maganin dukkan matsalolin ku* *INA MASU HAWAN JINI?* *INA MASU CIWON ZUCIYA?* *INA MASU CIWON QODA?* *INA MASU CIWON HANTA?* *INA MASU SICKLER?* *INA MASU HIV?* *INA MASU CANCER?* *INA MASU NEMAN HAIHUWA?* *Tohh Ku matso GHT taxo muku da magungunan matsalolin ku* *Kuma muna da testimonys da yawa ,na wadanda suka gwada suka da ce* *Munanan a KANO KUNTAU* *Kuma muna tura Kaya ko wanne gari cikin aminci da gaskiya , kuma kayan mu muna badashi ne cikin price Mai rahusa ga kyau ga inganci sannan ga Rahusa* *Kutuntube mu ta wannan number 📞08129249549* *📲07011401314* Dakyar ta iya nutsuwa dukda ba sosai ba ta shiga kora musu qaryar data tsara ta haddace dangane da Auran da Audu yayi ba tareda saninta ba kuma akan ta masa magana yayi mata dukan kawo wuqa dakyar ta kwaci kanta shine ta gudo. Yanda ta tsara labarin babu wanda ya isa ya qaryata ta musamman ga shaida nan jikinta ya nuna. Mamaki madaukaki ya kama iyayenta musamman Alhaji daya ringa dubanta kamar me son ya tabbatar da dagaske take ko qarya takeyi. "Wlh bazan koma ba, sedai ya zaba koni ko ita haka kawai bazanje su shafamun cuta ba kuma idan ya zabi zama da ita Dady ka gaya masa ya maido maka da duk wata dukiya daya samu ta dalilinka ai daman saboda ni ne kuma idan ya sakeni dole ya bayar tunda bata ubansa bace" Binta ta fada cikin gunjin kuka. Alhaji Zakariyya ya wuce bangarensa ba tareda yace mata qala ba ya kasa yarda da abinda ta fada, meya hada Audu da matan banza har ya gano matar Aure a cikinsu sannan da gaske Audu ne yayiwa yarsa gudan jininsa wannan dukan babu kara balle ya taci arziqinsa to kodai shaye ya fara toh? A can falo kuwa da Mama ta gaji da ihu da kururuwar Binta ta daka mata tsawa tace "Ki rufe mana baki, Audun ai ba mahaukaci bane da ze kamaki da duka haka kawai waye be san halin tsiwarki ba a gidan nan kuma Aure daman kin sani a rubuce take zeyi, ba wata kika tarar a gidan ba dan haka ba zaki fitar da ran kema za'a kawo miki wata ba. Abinda na jiye miki tun farko a Auran Tifical Bahaushe kenan wanda be yi Ilimin Boko ba balle ya waye da yanda rayuwa take, irinsu Audu a kullum tunaninsu be wuci su samu kudi su tara mata da Yaya ba basu damu da jin dadinsu ba balle walwala ko yanda zayuwarsu zata kasance, ke kikace kinji kingani dan haka yanzu babu wani dalili da ze saka kice zaki dawo mana nan, Munira ma Addu'ar Allah ya kawo wanda zero dauke mun ita nakeyi ballantana ki kaso Auranki ki dawo mun". "Kai Mama ya zakice haka bakiga abinda ya mata ba se kace ba yarki ba, kuma ko auran zeyi ya rasa wa ze auro is Karuwa haba mana wannan ai ba abune me yuwuwa bama" Munira ta fada aiko ta juya kanta tana cewa "Idan na sake jin bakinki a nan sena gwabjeki shashasha ai kema ba sanin ciwo kanki kikayi ba "Ya isa haka Firdausi, ke kuma Mamana ki shiga ciki kiyi wanka Munira ki rakata clinic a dubata, ku dauke yaron nan daga qasa sannan wanda ya kawoki tafiya yayi ko yana nan?" Alhaji Zakariyya saya sake fitowa shirin shirin fita ya fada. Se sannan suka lura da Zakariyya dake kwance qasa abinsa yana bacci Direban ne ya shigo mata dashi ya watsar dashi a qasa tareda jakar kayanta. Ta miqe tana dingisawa Munira ta dauki Yaron suka wuce ciki. KANO Rai fes Audu yayi bacci babu damuwar komai tattare dashi illah mafarkin Amaryarsa daya kwana yanayi tareda shirya yanda tariyarta zata kasance nan da sati biyu masu zuwa shima saboda ya bata damar yin shirye shirye ne daga bangarenta dan shi a shirye yake fenti kawai ze saka a sakewa dakin can tazo ta zauna. Rashin zuwan Binta dakin be dameshi ba saboda yasan koda taje qarshe rigima zasuyi, da ya dawo daga sallar Asuba har ze shiga ya dubata kuma ya fasa dan yana so ya koma bacci yasan kuma muddin ya shigan bacin rai ze kwaso dan haka ya bari akan sa hade idan gari ya waye sosai. Bugun qofar gidan da ake kamar za'a ballata ne ya tayar dashi. Ya ringa sakin tsaki yana tunanin wanene haka? Jallabiya ya saka ya sakko yana mamakin Ina Binta ta shiga ake irin wannan dukan qofar bataji ba ko itace ta fita qofar ta kulle ta waje. Takaici ya qumeshi ganin Lantana me aiki, ya tsani matar saboda kana ganinta kalar munafukai ne da ita. Ta durqushe a qasa kamar zata kwanta tana gaishe shi ya amsa a dake yana cewa "Wane irin abu ne haka zakizo kina dukan qofar mutane" "Kayi haquri yallabai kasan dokar Hajiya qarfe bakwai nake zuwa gidan nan to Nazo tun bakwan na buga ba'a bude ba na tafi shine na dawo na sake bayi bugun da qarfi ne ko bacci take kar nayi laifi tace banzo da wuri ba" Tsaki yayi ya juya ciki, harya fara hawa sama ya dawo jin tanata qwanqwasa qofar Bintan shiru ba'a bude ba, ta matsa ya isa jikin qofar ya kwankwasa kana ya murda handle din qofar. Fahimta da yayi a kulle take yasa ya zagaya ta window ta da yake a tsakar gidan ya zuge ya leqa ciki, kayana da ya gani barbaje suka fahimtar dashi bata nan, se abin ma ya bashi dariya a fili yace "Yaji tayi kenan" "Ki tafi na manta zataje zata fita yau ta fita da wuri ina bacci" ya fadawa Lantana, kamar zata fasa kuka haka ta ja qafa tana waiwayensa, kamar tace masa zata zauna ta jira tunda ko fita Bintan zata yi tana barinta tayi mata jiran gida gashi ta kwaso yunwar safe ta saka rai zatazo taci me kyau kuma ace bata nan. "Alhaji Mairo tazo ne? Kuma zuwa yaushe Hajiyar zata dawo?" Ta fada tana sunkuyar da kai, "Idan ta dawo zata saka a kiraki ba yau ba ba gobe ba, kija qofar ki tabbatar kuma ta rufu idan kin fita" ya bata amsa yana juyawa tilas ta fita taja musu qofar gidan. Audu kuwa kasa komawa bacci yayi, tunanin inda Binta ta tafi ya shigayi, qila ba zata wuce gidan Baturiya ba dan bata da yar uwa a Kano bare yace gurinsu zataje Baturiyar itace yanzu babbar Qawarta ko yace Aminiya indai ba gidanta taje ba to Kaduna ta tafi. Zabura yayi ya miqe yana salati, idan Kaduna ta tafi ya Alhaji zero dauki maganar? Ze goyi bayansa ko kuma ze goyi bayan yarsa ne? Idan Alhaji ya goyi bayan Binta yace ya sakar masa yarsa ya makomarsa zata zama kenan dan dai Alhajin shine abin tunqahonsa, duk abinda yake ganin ya tasarma zama da bazar Alhajin yake rawa. A gurguje yayi wanka ya shirya, kai tsaye gidan Ali ya fara zuwa suka hade a waje Alin na shirin fita ya kuma tabbatar masa Binta bataje gidan ba dan babu inda zata buya da ze kasa ganinta. "Dan girman Allah kazo ka rakani Kaduna" ya roqi Alin "Kai yanzu? Ina babu wannan magana, ai yanda ka tirko rigimarka se ka san ta yanda zaka kasheta. Amma fa ban taba dauka da gaske kaci kai ba Audu se yanzu, duk matan da suke garin nan yayan mutunchi ka rasa wadda ta burgeka se wannan yarinyar? Kodai Asirinsu tayi amfani dashi ta zarge zuciyarka?" Ali ya fada yana tsareshi da ido. Audu yaja tsaki kafin ya shige mota ya daga ba tare da ya bashi amsa ba Yau dinma Musbahu yaje ya dauka suka tafi Kaduna, seda ya isa qofar gidan kuma ya fara tunanin me zece musu idan ya shiga? Seda sukayi sallar La'asar da Magriba da suka riskesu a hanya kafin ya saka kai cikin gidan. Ko ina tarwai da haske, Tun daga Get suka fara gaisawa da ma'aikatan gidan harya isa qofar falo. Ta ciki Munira ta hangoshi, ta kwasa da gudu tayi daki ta fadawa Binta da tunda tayi wanka taci abinci take rama baccin da batayi jiya ba. "Wlh ko me za'ayi karki koma ai raini nema kamar ke ace a miki kishiya bayan duk fafutukar da daukar hakkin da mukayi muka fitar da waccen shine za'a dakko miki alaqaqai to babu wannan maganar" Muniran ta qara zugata. Tun daga yanda Alhaji ya amsa masa gaisuwarsa yaji guiwoyinsa sun qarayin sanyi dama Mama tana musu iso a tsayw suka gaisa ta shige ciki, yau ko Kayan Alatun da ake tarbarshi dasu be samu ba Ruwa da Lemo ma Alhajin ne yayi magana aka kawo musu. "Bansan ta taho ba Alhaji, na dawo daga sallar Asuba kawai na tarar bata nan" Audu ya fada bayan dogon shirun da sukayi kowanne kamar ya rasa abin fada. Alhaji ya nisa yana kallonsa yace "Me ya hadaku da har yasa ta baro gidan ba tareda saninka ba?". Be boye masa komai ba ya bashi labarin Auran da yayi wanda yake ganin shiya tunzurata ta baro gidan, ya rufe da qaryar cewa "Bansan cewa zasu daura Auran ba saboda tambaya kawai akaje". Shiru Alhaji ya sakeyi yana kallonsa kafin yace "Menene gaskiyar maganara data fada na cewar Yarinyar Karuwa ce?" Seda ya daga kai ya kalli Alhajin saboda kalmar daya fada din se yaga kamar tayi girma musamman ana maganar matarsa ne ina laifin yace tsohuwa, wannan ya tunzuro zuciyarsa ta raya masa ci masa mutunchi Alhajin ya tashi yi amma ya danne dan ko ya masa qarya bashida amfani tunda har magana ta fito amma a ina Binta taji wannan batun? "Kayi shiru" Alhaji ya katseshi, kansa na qasa yace "Gaskiya ne, amma ban aureta ba seda na maidata gaban iyayenta tayi Istibra'i kamar yanda shari'a ta tanadar" "To akan me ka daki Mamana har kaji mata ciwuka a jiki?" Alhajin ya fadi ainihin abinda yafi damunsa a duk cikin maganar, se Audu ya daga kai da sauri ya kalleshi jin abinda ya fada. "Wlh Mari daya nayi mata, shima kuma cin kwalata tayi a gaban yan uwana da sukazo fadamun an daura aure ta labe harta tsinci maganar shine ta shaqemun wuya nace ta sakeni taqi ni kuma zuciya tasa na mareta bayan nan ko yatsa ban nuna mata ba wlh" ya fada cikin kare kai. Alhaji bece komai ba yaja Intercom ya kira cikin gida kan Binta tazo, ba'a dauki lokaci ba ta fito tana jan qafa fuskar nan kamar dafaffen Kunu ta zauna kusada qafar Alhajin tana hararar Audu wanda ke kallonta yana mamakin abinda ya karceta a fuska kamar sunyi dambe da Mage. Ce mata yayi ta maimaita duk abinda ta fada cewar Audu ya mata, tana kuka ta shiga shiryosu harma da abinda dazun bata fada ba na cewar daman Audun ya dade yana yawon ta zubar dinsa har kwanaki yake tafiya yayi acan in ya dawo kuma tayi magana ya zageta koya hada mata da duka qarshema tace idan ta fita har gidan yake kawo mata shidai kasa cewa komai yayi saboda mamaki, maganganunta kuma babu yanda za'ayi ace qarya takeyi tunda tabbas yana yawace yawaceb har yaje ya kwanan amma ai ba abinda take fada yakeyi ba sedai kuma waye ze bada shaidar hakan? Shidai Alhaji na jinta yana kuma kallon Audu daya kasa rufe bakinsa seda tayi shiru kafin ya kalleta yace "Kinaji ko Mamana, duk wani Aure da kika gani tattare yake da qalubale muddin kuma ba ma'aurata sun bude cikinsu ba bazaka taba sani ba dan haka kowa haquri yakeyi kamar yanda kika faro haqurin kici gaba dayi kuma tunda ya auro yarinyar da take dauke masa hankali a wajen ai magana ta qare se ayi fatan kuma Allah ya hada kanku ya bada zaman lafiya. Kaikuma abinda nake so na gaya maka shine ka tabbatar kayi na farko kuma kayi na qarshe da zaka dora hannu da sunan duka a jikin Mamana, zan manta da duk wata alaqa dake tsakaninmu na maka ka a Kotu domin bana hada kowa da yayana, ban daki yar kowa ba dan haka babu hujjar da zata saka wani ya dakar mun yata. Idan tayi maka laifin da ba zau iya sasantawa a tsakaninku ba ka kawo mun qararta nizan hukuntata amma bazan lamunchi duka ba ina fatan ka gane?" Kunya, nauyi da takaici suka rufe Audu gaba daya ya rasa ma abinda zeyi, Alhaji yaci gaba da cewa "Idan Allah ya kaimu gobe yanda kikazo da sassafen nan ki tattara ku koma aje aci gaba da haquri kuma na kashe maganar nan, Aure kuma dakayi Allah ya sanya Alkhairi ya baka ladan Jihadi" "Wlh bazan koma ba, babu yanda za'ayi nayi zamab kishi da Karuwa Dady kawai kace masa ya saketa idan ba haka ba bazan koma gidan ba" ta fada cikin kuka tana bubbuga qafa. https://chat.whatsapp.com/I8xKHGurk7EBf5ZqQdxHKG *MATAR MUTUM* *NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER* *FIKRA WRITERS ASSOCIATION* *LITTAFIN KUDI NE* *PAY 500 A ASUSUN* *7061838488* *OPAY DIGITAL SERVICES* *MARYAM FAROUK* OR *0709290797* *ACCESS BANK* *SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488* *IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705* *Kuyi following dina a Arewabooks @Maryamfarouk01 inda zaku karanta wannan littafin tareda sauran littattafaina* *NAGODE* *PAGE 18* Ki bude kunnenki dakyau kiji abinda zan fada, dukiya da kike tutiya akanta ta Abdullahi ce, duk abinda nayi masa kyautace halak malak dan haka ko ki bishi ki koma, ko ki dage ya sake ki zabi ya rage naki amma ki sani sisin kwabo baze maidamun ba dan ya rabu dake ko wani abu saboda dama badan ya aureki na bashi ba, tashi ki bani guri karki qara mun ciwon kan da yake damuna" Alhaji ya dakatar da Binta dake ihun kuka. Sanin halin mahaifin nata kaifi dayane yasa ta tashi ta koma ciki tana cigaba da kukan ta labartawa Mama yanda sukayi. "Ahto seki shirya ki koma daman duk tsuntsun daya ja ruwa ai shi ruwa ze doka, ke kika zabe shi dan haka dole ki jure duk wasu tazgado dake tareda zama dashi kishiya kuma naga wata kika tarar kowa da halinta zata zauna ai ba kuma kanki ze ajiyeta ba" abinda Mama ta sake gaya mata kenan haka tana ji tana gani suka kama hanya da farar Asuba ba tareda ta hadu da sauran yan uwanta ba wadanda su ta saka ran zasu bata shawarar yanda zata yida wannan Al'amari, da Munira suka sake tattaunawa da dare ta qara masa karatun yanda zatayi ta hana Amaryar shigo mata gida dan basu hasko ma ta shigo balle ta zauna. Haka suka sha tafiyar bata ko kula Audu sedai shine yake tankata lokaci lokaci daya gaji da yanda ta shareshi yayi shiru har sukazo Kano, yana Ajiyeta ya fita itama bata zauna ba jakarta kadai ta shigar daki ta fice gidan Turai. "Wlh Turai ko a jikinsu, babu fa wanda ya daga maganar Asalin matar daya aura din kamar ma basu fahimta ba haka suka share zancen har a gabansa Dady yana wani jaddadamun duk kudin daya bashi ba Aro bane kyautace kuma ba saboda ni ya masa ba, wlh da na shirya rabuwa dashi amma wannan dalilin yasa na fasa. Babu yar iskar dazan tafi na barwa gida tazo ta wataya da kudin ubana". Duk da yanayin jimamin da suke ciki seda Turai tayi dariyar maganar Bintan ta kuwa sake harzuqa tace "Au ga mahaukaciya ko ina magana dariya ma kike mun" "Ba haka bane, ke dince da abin dariya waini in tambayeki Binta tsakaninki da Allah Audu kike so ko kuma Dukiyarsa?" Turai ta fada tana kallonta. Ta zabga tsaki kafin tace "Duka gaba daya, kinga Audu yayi mun daidai da tsarin Mijin da nake burin na Aura cikas dinsa daya rashin wayewar Boko amma abinda yaja hankalina harna yarda na Aureshi saboda yanda Dady ya ke labarinsa na san gobensa zatayi kyau zeyi Arziqi. Turai ina son kudi ina so kuma na auri me Kudi, dukda nayi samari masu kudi yayan masu kudi abinda yasa na zabi Audu a cikinsu saboda shi be waye ba, zan iya masa wayo na samu abinda nake da buqata a gurinsa sannan na hana kowa rabar sa ya zamani ni kadai zan moreshi se yayana, ba qaramin takaici naji ba dana samu labarin yana da mata harda yaya kuma tun sannan na daura Aniyar seta fita ta barmun gidan, bayan nayi nasara sannan ga Arziqi nan yana qara habaka se kuma na bari wata tazo ta tayani ci? Wlh baze yuwu ba dole koda tsiya koda Arziqi matar nan ta koma inda ta fito babu yanda za'ayi na zauna da kishiya a gidan Audu". "Yanzu dai plan A ya ruguje se mu tafi ga shiri na biyu, kuma ina so ki kwantar da hankalinki qawata shi yaqi akace fan zambo ne, yanda kikayi da Bara'atu haka zakiyi da wannan ma koda ace ta shigo cikin gidan, yanzu abinda zakiyi, lambo lambo zaki masa ki nuna masa kinyi nadamar abinda kikayi ki bashi haquri kisan duk yanda zakiyi yabyarda dake ta haka ne zaki yi komai ba tareda ya zargeki ba, kamar dai lokacin Bara'atu ai kinga kin nuna masa kina sonta harta fita be taba sanin irin gallazawar da kika ringa mata ba" Turai ta fada "Turai! Wannan fa ba Bara'atu bace, kefa kika ce mun kilaki ce ta ina zan iya goga kishi da yar Bariki Turai?" Bintan ta fada cikin yanayin dake nuna tabbas ta tsorata da Amaryar da Audun yayiwo mata. Turai tayi murmushi tace "Dadi na dake Damusar takardace, ga tsoro ga ban tsoro, yanzu har akawai wata kisisina da matar bariki ta iya waddda mu bamu iyata ba? Meye a cikin barikin ne da har zata naki tsoro? Kinga fa yaqin nan dole se kin dage idan ba haka ba kina zaune zata shigo kuma ta kwace Mijin" "Allah ya rufa asiri, wlh ko zan mutu bazan bari naga wannan rana ba" Binta ta fada tana fashewa da kuka Turai tayi dariya tace "Bama zaki mutu ba sedai ita me shirin yi mana kutse ta mutu, yanzu dai kamar yanda na gaya miki kije ki lallabashi ku daidaita, da an kwana biyu kic zaki Bechi ki gaishe su a can zaki kwarkwance komai ki gaya musu wacece ita son samu ki fara sanar da Yayansa na Lagos nasan ko beji maganar na qauyen ba shi baze qijin ta tasa ba" da wannan shawara suka rufe ta koma gida ta yi matuqar qoqarin danne zuciya tayi duk abinda Turai tace. Kuka wiwi ta ringayi tana bashi haquri da rantsuwar ba zata sake ba yanzun ma sharrin shaidan ne tayi iyayinta har seda ya sakko shima ya bata haqurin yanda Al'amuran suka kasance a qaryarsa wai besan za'ayi haka ba. "Amma banji dadin yanda kika kwanceni a gaban Dady ba, na dauka ko abinda kika fada gaskiya ne ke me rufamun Asirice a ko ina" ya fada in relevant to zancen yawonsa data gayawa Dady. Kanta na qasa tana share hawayen kissa tace "Kayi haquri, wlh bansan abinda ya shiga kaina ba kan yafemun Mijina kaji dan Allah" "Ya wuce, Allah ya yafe mana gaba daya sannan in Allah ya yarda nan da kwana Goma Zata tare, ina so ki lissafa duk abinda kike da buqata da wanda za'ayi amfanin yinin Biki a can Bechi" Wani abu ya caki ranta amma ta shanye tace "Shikenan zan lissafa, yaushe zamu tafi Beechin toh?" Da mamaki ya kalleta jin yau anyi zancen zuwa Bechi salin Alin ba ta fadi mara dadi ba, ransa ya qarayin fari yana qara gasgata da gaske tayi nadama dan haka yace mata se saura kwana uku zasu tafi da anyi yini yau washe gari au dawo gaba daya da Amarya ta amsa da Allah ya nuna mana a Ranta tana ayyana Bura'ubar da zata tafka a Bechi idan sunje. Haka ko akayi, tana kallo aka ringa fenti aka shigo da sababbin kayan gado da kujeru aka saka a tsohon dakin Bara'atu baqin ciki kamar ya murqusheta ta mutu wato cikin dukiyarsu yayiwa Tsinanniyar Amaryar kayan daki, takaicin kanta ya sake rufeta datayi wautar cewa ya barshi bata buqatar komai duk a salon wanke kanta gurinsa. Ranar Laraba suka tafi Bechi ita da Direba daya hadata dashi tareda kayayyakin amfanin girkin da ba za'a samu a can ba, Juma'a za'a kai Amarya can ayi yini su Kwana Asabar su juyo. Wai se ga Binta na bi gida gida daki daki na yan uwan Audu da sunan taje su gaisa abin dariya ita ce har gidansu Bara'atu. Duk gidan data shiga bata fitowa seta kwance Amaryar Audu ta fada musu tsohuwar kilaki ya auro, Bilki da tun sakin Bara'atu ta fita a sabgar Audu da gidansa farko cin mutunchin Binta taso tayi da ta je mata gida amma zancen data kai mata ya tayar mata da hankali. Me yake damun Audu? Wace hau ce ta haushi da ze auri Karuwa? Hankali tashe ta tafi gida ta samu su Yaya Babba duk sun tattaru dan kowanne na komawa gidansa da yamma ya samu saqon da Binta ta bari shiyasa suna idar da sallar Isha suka tattaro suka taho gidan gaba daya ita ko Binta tana masaukin su da aka qara gyareshi, rabon su duka ya siye banda na Yakubu dan nan yake sauka idan yaje se ya qara fadada nasan yayi dakuna manya da bandaki a ciki. "Nifa tun ranar da mukaje neman auran kun tuna sanda na fita zagayawa a lokacin naji wasu suna qus qus din wai anya wadannan sun san labarin Yarinyar suka zo nema dansu aure? Basu dai fadi komai ba amma wannan magana tasu ta jefani a wasi wasi sedai tunda shi ma'auri wakilci kawai ya nadamu shi yasa nayi shiru bance komai ba" Yaya Baba ya fada, Aminu yace "Haba Yaya, menene amfanin girman idan ba zaka ga abin da ba daidai ba ka gyara mana? Yanzi da kaji wannan magana ai ko a tsakanin mu seka gaya mana idan yaso mu basu kudin Aure mu tafi ba zamu yarda a daura ba har se an bincika munji dar din maganar halin nata, na tabbatar shima be sani ba yanzu ya za'ayi?" "Amma ku kuna ganin gaskiya wannan yarinyar ta fada, kun manta sharrin ta kenan?" Hashimu da be manta kitimurmurar Binta ba ya fada. Bilki tace "Bana jin qarya ne, tunda ga Yaya Baba ma yace yaji wata magana, yanzun dai mu jirayi Yaya Yakubu ya iso gobe idan Allah ya kaimu in yaso se mu san abinyi kafin Audun ya qaraso shima" inji Bilki, haka taron ya tashi, washe gari ko da Rana Yakubu da Iyalansa suka sauka Bechi. Binta batayi qasa a guiwa ba ta shige ko gajiya bata barshi ya ware ba yana aje haqarqarinsa a kujera ta zube a gabansa ko kallon inda take Bakaraba batayi ba taja yaranta suka shige daki. Bilki tayi turus da kayan abinci a hannunta tana kallon Binta dake rusa kuka a gaban Yakubu tana masa bayani se ta fara jin anya maganar nan da gaske ce kuwa kodai wasan kwaikwayonta data saba ne ta hadashi? "Yanzu saboda Allah ba zaki barshi ya ko huta ba zaki tasashi a gaba da wannan maganar?" Bilki ta fada taba harararta. "Zauna Bilki" ya bata umarni kafin yaci gaba da cewa "Menene gaskiyar abinda ta fada?" "Yaya muma ita tazo mana da maganar, amma Yaya Baba yace..." Ta fada masa abinda Yaya Baba yaji sanda sukaje neman aure. "Shikenan tashi kije, zamuji ta bakinsa idan ya qaraso" "Dan girman Allah kar kuce masa ni na gaya muku" "Dama ba zamu fada ba tashi kije abinki" da haka ta fita rai fes dan koda Yakubu beyi wata magana ba daga fuskarsa ta fahimci ya kadu da maganar. Tana fita Balaraba ta fito daga daki tace "Yanzu kun yarda da maganar wannan annamimiyar matar? Matar data laqawa wata sharrin kisan kai sena Bariki ne ba zata dorawa wata ba? Koda yake Allah ya kawoshi gara yaji abinda ta hada ko idonsa ze washe ya gane da wadda yake zaune ai". Yamma Lis Audu ya isa Bechi, seda sukayi sallar Isha kafin Yakubu ya tareshi a wajen dan baya so sauran yan uwan su fara masa magana ta yanda laifin Binta ze fito. Cikin siyasa da kwarewar aikinsa ya saka masa maganar a baki, yana da labarin yawace yawacen da yakeyi da wannan yayi amfani yace an gaya masa acan ya hadu da Amaryar tasa. "Haka ne, amma ban aureta ba seda na maida ita gidansu tayi Istibra'i tukunna" ya bashi amsa kai tsaye. Yakubu ya ringa kallonsa ya gaza cewa komai, dakyar ya iya bude baki yace "Amma yanzu na tabbatar da Audu baka da tunani sam, duk matan duniya ka rasa macen Aure se karuwa ko kuma asiri tayi maka?" "Ni babu Asirin da tayi mun kuma ka dena cewa Karuwa tunda ta tuba ta bari sannan babu inda Shari'a ta haramta Aurena da ita tunda dai tayi tsarki sannan ni ina sonta a haka kuma nasan har a gurin Allah nayi aikin alkhairi jihadi babba nayi" Audun ya fada cikin yanayin ko in kula, "Haka ne" Yakubu ya bashi amsa daga nan yasa kai ya shige gida ya bar Audun a tsaye. *MAMAN MARYAM ONLINE BUSSINESS* *Ina kuke Mata Yan kwalisa , Ina nufin isassun Mata ,Wai shin Kuna da labarin shahararren company nan namu na GHT wato good healthtreatments* *Wanda yazo muku da fitattu Kuma* *ingantatattun suppliment ,na dukkan matsalolin ku*❓ *Ina maisan tayi kyau,irin na isassun Mata ya fitar Miki da shef dinki tayi Miki gyara in and out ,nemi royal jelly dinmu na company GHT* *Wanda aka yishi da xuma ,kundai San amfanin Zuma basai na fada miku ba , hajiya ta kixo ki Yi gyara domin ki kerewa sa,a kije taro ko baki da ko sisi kiji Ana rangada Miki hajiya , saboda yanda Zaki Kara kwarjini ,kina walwali acikin mutane , magungunan ght anti agen ne suna maida tsohuwa* *yarinya ,yarinya Kuma ta koma jaririya* *Muna da magunguna iri iri* *NA GYARAN JIKI* *NA GOGE NANKARWA* *NA RAGE QIBA* *NA CIRE TUMBI* *NA QARIN HIPS* *NA GIRMAN BREAST* *NA QARA TSAHON GASHI* *NA QARIN NI'IMA WANDA ZAI SAUKAR MIKI DA NI'IMA YA QARA MIKI DADI DA ZAQI A GURIN OGA* *Muna da hadin bita zai zai ,indai kishiyar ki tana Shan magungunan GHT, tohh lallai sunan ki sorry domin kuwa tazarar dake tsakanin ku kamar tazarar sama ne da kasa* *Muna da Wanda zai matseki ciki da waje Andai na yayin dinki uwargida*, *Sannan company mu na GHTBai tsaya anan ba* *Ya kawo muku maganin dukkan matsalolin ku* *INA MASU HAWAN JINI?* *INA MASU CIWON ZUCIYA?* *INA MASU CIWON QODA?* *INA MASU CIWON HANTA?* *INA MASU SICKLER?* *INA MASU HIV?* *INA MASU CANCER?* *INA MASU NEMAN HAIHUWA?* *Tohh Ku matso GHT taxo muku da magungunan matsalolin ku* *Kuma muna da testimonys da yawa ,na wadanda suka gwada suka da ce* *Munanan a KANO KUNTAU* *Kuma muna tura Kaya ko wanne gari cikin aminci da gaskiya , kuma kayan mu muna badashi ne cikin price Mai rahusa ga kyau ga inganci sannan ga Rahusa* *Kutuntube mu ta wannan number 📞08129249549* *📲07011401314* Tabbas yasan wannan lokacin zezo shiyasa yake yawan nunawa Dada rashin amfanin baiwa Audu damar yanke duk hukuncin da yayi masa ba tareda ya shawarci kuwa ba. Ita ta bashi wannan damar, shi a matsayinsa na babba bata taba daukar Maganarsa da muhimmanci ba domin a sannan tana ganin Audu ya fishi wayewa da sanin rayuwa, yasha gaya mata hakan bashida kyau domin idan ya yanke hukuncin daidai qata rana ze yanke akasin haka kuma baze taba ganin cewar yanayin abinda ba daidai din ba tunda ya saba cewar akoda yaushe shi yake bada shawara ba dai a bashi ba, yau da ace ta gina su akan turbar su shawarci junansu sannan su yanke hukunci akan duk wani al'amari na rayuwarsu ya tabbatar koda Audu na da taurin kai da kafiya tilas a wani bangaren yayi yanda ake so, gashi yanzu yana yankewa kansa danyan hukuncin da idan ba'ayi wasa ba se yayi nadamar su a gaba. Tamkar dai Yakubun dmsanda su Yaya Baba suka tareshi suma tabbacin gaskiyar maganar ya basu be kuma saurari komai daga bakinsu ba ya shige daki inda Binta ta kasa kunne tana jira ta jiyo magana ta tashi amma shiru, washe gari Juma'a yan uwan Amarya Zubaida suka yiwa Bechi tsinke, su biyar se ita ta shida, dayan dakin dake kusada na Binta aka shigar da ita Mata nata turuwar zuwa ganin fuskar Amarya amma babu dama dan a rufe take daman gulma da munafunci ne kawai ya kaisu suga fuskar tsohuwar Karuwa. Binta na cikin Dakinta a kwance abin duniya ya isheta ta kasa fita har sanda aka fito da Amarya tsakar gida inda akayi shimfidu aka zaunar da ita Bilki ta shiga ta kira Bintan saboda Al'adace za'a danqa amanar Amarya a hannun uwargida. Daurewa tayi ta qara barbada hoda, daman Leshi tasa me kyau daya qara fitar mata da suffar ta gaba gaba ta tura dauri gaba ta fita tana qoqarin danne shadan dake raya mata data fita ta cakumi Amaryar ta mata dukan mutuwa. Haka ta ringa yaqe har aka gama komai aka bude fuskar Amarya, ganinta tayi yar yarinya da kadan ta fi Bara'atu cika amma kyakykyawace kwarai duk da baqace, kaso ashirin na fargabarta taji ya ragu dan ta saka ran ganin matar da idanunta kadai zasu firgitata amma se ta raina zubinta. "A haka dai gata kamar salaha amma wai tsohuwar kilaki kai jama'a Allah ka tsarkake mu ka tsarkake mana zuri'a" wata da bakinta bashida birki wadda kuma ta fita danyan kai ta cafe tana cewa "Kedai bari Tsahare, aini abinda yafi bani mamaki ma Audun daya dakko wannan aba, anya ba juyar masa da hankali tayi ba dan dai wannan al'amari beyi kama da na wanda yake cikin hayyacinsa ba sedai aikin sihiri" seka rantse su kadai ne a gurin yanda sukayi maganar hankali kwance babu wata damuwa tattare dasu kamar wadanda aka saka maganganunsu kuma sun isa kunnen kusan duka mutanen gurin, Zubaida ta sake sadda kai qasa kuka na neman kwace mata, abinda take gudu kenan wanda ta tabbatar da seya faru, shi yasa bata tsarawa kanta yin aure ba koda ace ta bar rayuwar bariki sedai komai ya faru kafin ta farga, haduwarta da Audu, komawarta gida ga kuma aure ubangiji ya fita sanin hikimar yin hakan kuma koma yayane ta godewa Allah daya tsamota daga mummunar rayuwar data fada ba kuma zata butulce masa ba zatayi haquri ta jure duk wani qalubale da zata fuskanta amma tabbas tana tausayawa kanta tana kuma tausayawa Yaran da zata haifa a gaba dan ta bar musu abin gori har jikokinta idan ba'ayi wasa ba. "Meye haka Jamila? Ke Tsare wace irin magana kukeyi haka saboda Allah?" Goggo Fadi ta tsawatar musu, a maimakon maganar ta mutu se ya zama abin cece kuce, wanda a kunji kunji sukaji labarin suka gasgata qus qus ya tashi ko ace qaramar hayaniya kowa na tofa albarkacin bakinsa masu fadar Alkhairi nayi masu tofin ala tsine sunayi wannan ya tilastawa Zubaida da qanwarta Surayya fashewa da kuka sauran yan uwansu kuwa jikinsu yayi laqwas tamkar an watsawa Kaza ruwan zafi. A can Kano a unguwarsu ba kamar yanda ake taammata ba Zubaidan bata samu qalubalen kyara ko hantara ba domin har wanda basu santa ba labarinta suka samu a sanda ta dawo sun karbeta hannu biyu saboda wannan ya taimaka mata gurin sakewa ta fara manta rayuwarta ta baya ta fuskanci gaba. Sun dauka yanda suka manta komai haka sauran Al'umma zasu manta sedai basu san wasu yanzu nema suka samu abin jajantawa da gorantawa. Yanda maganganu suke tashi ya saka dole aka maida Amarya daki tana rusa kuka kamar me domin babu shamaki suke aibatata, tamkar Binta zata taka rawa saboda murna, gumu yayi gumu, masu tsawatarwar basu da yawa dan haka maganar taqi mutuwa har seda. Maza suka shigo ciki, Tsahare uwargidan Yaya Baba data fara tada zancen seda ta karbi Tukuicin saki daya, Jamila matar Aminu data tayata dai ya aikata gida itama amma be furta saki ba, wannan yasa washe gari Asubar fari Audu ya kwashe su suka bar Bechi bayan ya kaftawa Matan Yayyen nasa da sauran Jama'a dake gutsiri tsomar warning, Yan uwanta dai saboda mutuwar jiki basu ko iya rakata dakinta sukace da Direban daya kaisu ya maida su inda ya kwaso su, saga ita se Audu da Binta suka wuce gida. Kwanakin Amarcin Zubaida dai basu zowa Audu a yanda ya tsara su ba dan abinda ya faru a Bechi ba qaramin tabata yayi ba gaba daya ta rasa nutsuwarta balle ta samar masa da tasa. Abin yawa Binta sugar har ta ringa ganin wautarta da tun farko bata hasaso haka ba, data sani Bechi ta tafi tun farko ba Kaduna ba, qila da yanzu gori ya saka Zubaidan neman saki da kanta amma yanzun ma ta samu nayi, ba duka ba zagi amma In sha Allahu da kanta zata tafi dan ba zata barta tasha ruwa a gidan ba. Yanda Angon duk yake a wani sukurkuce ya qara bata damar kafa kanta da nuna masa ita ta Allah ce har a gabansa ta ringa tausar Zubaidan tana gaya mata ta cire komai a ranta ta bar ta mutane. A haka Audu ya gama kwana ukunsa ya komawa Bara'atu kafin yayi kwana biyu ya dawo Qanwar Mahaifiyar Zubaida ta kai mata ziyara. Ita tayi mata maganar data maido da ita hayyacinya, ta gaya mata damuwa ko kuka ba zata mata maganin komai ba qaddararta ce a haka kuma me afkuwa ta afku dan haka ta manta baya ta toshe kunnenta daga jin duk wasu munanan Kalamai ta kuma maida hankali ta gyara gidan Auranta domin a yanzu bata da kowa bata da komai se Mijinta da gidan Auranta, ta dage ta nemi Aljannarta ta kuma tabbatar da cewa tayi tuba na gaske, abubuwan data aikata a baya da suke laifi yanzu lada zata samu akansu dan haka ta dage ta kama Mjinta. Wannan ya zaburar da ita randa Audu ya koma Dakinta Binta bataviya bacci ba saboda lukutin tashin hankalin daya sameta, a garin muguwar dabi'arta ta labe ta jiyo abinda ya kusa zauta mata tunani. Ta yi qoqarin shiga dakin ta dakatar dasu daga abinda sujeyi amma qofar a kulle dole ta wuce dakinta tana kuka wiwi qarin takaici da baqin cikin yanda Audun ya bude baki yana ihu tamkar farin shigan Hauka yanda kasan yau ya fara sanin Mace, washe gari kuwa taga qarshen bariki dan bata tsammatar Audu ya fita sallar Asuba kuma bataga kyallin idonsa ba se yamma lis shima tareda Amarya suka fito suna raha da dariya hannayensu sarqafe da juna yanayin shigarsu ya nuna mata cewar fita zasuyi. "Idan na yarda Allah ya tsine mun albarka" ta fada yana miqewa tsaye harda cire dan kwali tayi damara. *MATAR MUTUM* *NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER* *FIKRA WRITERS ASSOCIATION* *LITTAFIN KUDI NE* *PAY 500 A ASUSUN* *7061838488* *OPAY DIGITAL SERVICES* *MARYAM FAROUK* OR *0709290797* *ACCESS BANK* *SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488* *IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705* *Kuyi following dina a Arewabooks @Maryamfarouk01 inda zaku karanta wannan littafin tareda sauran littattafaina* *NAGODE* *PAGE 19* "Idan na yarda Allah ya tsine mun albarka" ta fada yana miqewa tsaye harda cire dan kwali tayi damara. Duk su biyu suka dakata suka kalleta, fuskar Zubaidan dauke da murmushi harda rausayar da kai tace "Ina wuni Yaya Binta?" "A gidan ubanwa na zama yayarki? Ni zako gwadawa Karuwanci? Koda yake na manta sana'arki ce ai ba a qasa kika tsinta ba" Bintan ta fada murya a sama, "Meye haka ne Binta? Ke baki iya magana a hankali bane dole se kin daga murya kamar meyi da mutanen sama sannan wannan damarar da kikayi ta mecece haka?" Audu ya fada yana kallonta se kuwa ta shiga qara tamke damararta tana cewa "Ba shakka dole ka tambayeni me nakeyi haka wato kaima an dora maka darasi irin nasu na tsofaffin kilaki ko? Saboda tsabagen rashin Adalci tun daren jiya rabona dana sakaka a ido, haka ka kwana kana kurma ihu a gidannan kamar wanda ya samu abinda baze qare ba sannan yau ko kyallin qeyarka ban gani ba se yanzu zaku fito cikin shiri da alama ma waje zakuyi wato ga banza jaka ka ajiye wlh ba zan yarda ba" ta qarasa maganar tana qoqarin fashewa da kukan takaici saboda tuno daren jiya da tayi. Wani murmushi me tafe da qaramar dariya Audun yayi ya kalli Zubaida data sunkuyar dakai, Karuwa da Binta ta kirata ya soki ranta amma tayi shiru tana qoqarin danne damuwarta tareda hana kanta karaya a gaban Bintan, "Ashe dagaske kike da kika ce duk maqota suna jina yanzu yaya zan kalli mutanen waje idan na fita bayan na tafka abin kunya qato dani ace yar yarinyar kamar ke ta sakani ihu a daki? Gaskiya mu koma an fasa fitar nan gara na hada kunyar jiya data yau gaba daya gobe na fita dan bazan fasa ihu ba" Da Binta ta rasa abin fadi se kawai ta fasa kuka me kama da ihu ta juya ta shige daki, Zubaida kuwa dariya ta fashe da ita tana kare fuska saboda kunyar maganar tasa, "Mu koma ciki" ya sake fada yana kama hannunta ta zame tace "Babu ruwana kaje ka rarrashi Yaya Binta kar kasa ta qullaceni" "Ki barta zan lallasheta gobe dan bazanso abinda ze sosa mun rai ba bare harya hanani ware murya dakyau nayi ihun dadi" "Allah ya isa tsakani na dake yar iskar Karuwa, idan ma kuma Asiri kikayi kika shigo gidan nan na rantse da Allah sena karyashi zaki gane dani kike zanje" Binta data fito da Hijabi a jirkice ta fada cikin kuka kafin ta fice daga gidan ko ina zata se Allah, "Ka bita mana kana kallo ta fita" Zubaida ta fada cikin yanayin damuwa, ko a jikin Audu ya juya ciki yana cewa "Duk inda taje ma zata dawo" daga haka ya jata suka koma ciki fitar da suka niyyata aka fasa. Binta kuwa bayan fitarta rasa inda zata nufa tayi, Turai bata nan ta tafi Gumel suna Yayarta ta haihu kaf Kano kuma ita kadai ce qawar da take kaiwa kukanta. Haka nan tasha kwana ta tasamma gidan Lantana wanda tunda ta fara mata aiki shekara uku kenan sau daya ta taba zuwa sanda Salisu Babban dan Lantanar ya rasu se yau data rasa gurin zuwa kawai zuciyarta ta raya mata taje can. Lantana da makwaftanta biyu na tsakar gida sun baza faifan Binta suna caccaka, haka nan kullum aikinsu kenan yanzu labarin kishiyar da aka mata dake neman zauta ta take basu "Ai in gaya miki alqadarinta ya karye, badai ta kori ta Allah ba ai gashi nan an hadota da wadda zataci ubanta ta kowanne fanni, kilaki fa akace yo har a gaya mata iya kissa da kisisina" daya saga cikin matan ta fada, Lantana ta buga cinya ta bude baki zata bada sharhi Binta ta doko sallama suka zabura gaba daya daka kallesu kaga marasa gaskiya "Hajiya, kece?" Lantana ta fada bayab data miqe tana sosa kai kamar me kwarkwata, Bintan ta kallesu irin kallon raini kafin ta nufi wata Farar Kujerar roba dake ajiye a tsakar gidan, "Allah yasa lafiya dai Hajiya keda kanki kika zo gidan nan idan wani abu ne aida se ki aiko a kirani" Lantanar ta sake fada. Cikin muryar qunquni ba tareda ta kalleta ba tace "Lafiya lau, zaman gidan ne ya isheni shine na fito" "Ai to barka, kuma ke kikace na taho da wuri yau ai da yanzu ina can na tayaki hirar to ina wuni?" Cewar Lantana sauran matan da se sannan suka iya magana duk suka gaisheta. "Bari naje Lantana inaga su Shamsiyya sun taso daga Allo yanzu, mace daya ta fada se dayar ma ta miqe tana cewa "Bari na biki ki lallabemun kan nan nawa, Lantana Allah bamu Alkhairi" "Duk tafiya zakuyi? To ku gaida gida nagode" Lantana ta fada ta na miqewa ta taka musu. Binta na zaune tana qarewa tsakar gidan Lantanar kallo yanda kasan wani filin baje koli can kwanukan wanke wanke can kayan yara sun cire sun zubar a qasa harda zannuwanta ga abinci da akaci aka zubar ba'a kwashe ba banda tiqar rake da qutsirarrun Kara gurin murhunta kadai abin kallonne. "Bari na kawo miki ruwa Hajiya" Lantana ta fada Binta ta kalli Randarta ta kalli Lantanar kafin ta zabga tsaki tace "Kika ce mun Mijinki yana aikin Malanta ko? Yana ina? So nake a karyamun duk asirin da waccen tsinanniyar tayiwa Audu a yau nake so ba se gobe ba ta yanda ze mata korar kare ta tafi gidansu komai dare" "Tirqashi" Lantana ta fada a zuciyarta a fili kuwa seta gyara zama tace "To yanzu kin hau saiti kenan Hajiya" "Da ba a saiti nake ba? Karki gayamun magana Lantana saboda kinga nazo gidanki, ki kiramun shi ayimun aikin da yake gabana ba surutun banza nazo muyi ba" "Allah ya baki haquri Hajiya nima ba surutu nake miki ba, amma yanzu dai Malam baya nan ya tafi qauye kuma kwana uku zeyi a can, da ace jiya kikazo da zaki tarar dashi amma da akwai Mijin qawar nan tawa da suka fita yanzu shi yana nan a gida Malam me makarantar Allon nan ta kan kwanar shigowa idan kina so yanzu sena rakaki gurinsa duk abinda Malam zeyi miki shima irinsa yakeyi" Lantana ta fada cikin ladabi. Binta tayi shiru na wani lokaci, zata so ace a yau din nan an karya mata duk wani Asiri da Zubaida tayiwa Audu amma kuma bata son terere, shima Mijin Lantanar data zo gurinsa saboda tasan zatayi komai cikin sirri ne Lantanar ba zata fitar mata da sirri ba wannan da take fada kuwa bata da tabbas a kansa dan haka ta nisa tace "Jibi kikace ze dawo ko?" "In Allah ya yarda Hajiya" "Shikenan, bari naje na dawo" ta fada tana miqewa tsaye, Lantana taso ta jata da wata maganar ta zauna ko Allah zesa taji yanda ake ciki dan daga ganin idanun Bintan da kuma kawo kanta da tayi gurin Mijinta da tayi mata Qaryar yana aikin Malanta tun farkon fara aikinta a gidan tasan banza bata kao zomo Kasuwa kuma duk abinda ya koro Kifi daga ruwa ya fada wuta toh tabbas yafi wutar zafi, zata so taji komenene dan ta samu na yamadidi a unguwa kamar yanda ta saba raba zancen Bintan lungu da saqo a unguwar amma yanzu babu fuska dole ta haqura ta rakata zaure tana jaddada cewar Jibi da Malam ya dawo zata sanar mata. "Ko na biki na tayaki zaman ne Hajiya?" Bata dai sare na ta fada, Binta ta mata Banza tayi gaba. A maimakon ta tafi gida kai tsaye seta bige dabi ta wancan lungun ta bulla wancan seda taji ana kiraye kirayen sallar Magriba kafin ta kama hanyar gidan ranta na quna da tunanin me zataje ta tarar, tana shiga Soro hawaye ya balle mata, wai yau ita Binta ce gidan Audu ya gagareta zama har ta fita tana garari a titi saboda qata Mace? Wlh bata isa ba, taci alwashin seta tozarta Zubaida, yanda ta kori Bara'atu Salin Alin haka itama zata fita ta bar mata gida, Audu da duk abinda ya mallaka nata ne wata mace bata isa tazo ta mata katsalandan a sabgarta ba. A tsakar gida sukaci karo ya fito da Alama masallaci zeje, "Kin dawo? Ga Alhaji can an maidoshi bakya nan yana gurin Yar Dagwas" Audun ya fada mata kafin ta bashi amsa ya rabeta ya fice daga gidan dan har an tayar da sallah. Kamar kububuwa ta doshi dakin Zubaidan babu sallama.bare neman iso ta bankada labule ta fada ciki. "Wane Dan abu ta kazan ne ya baki izinin taba mun yaro? Dana tsarkakakke zaki shafa masa Dattin zina? To bari kiji karki dauka kinga gurin zama a gidan nan, yanda kika shigo da qafa biyu idan bakiyi wasa ba sedai a kwasheki a wilbaro dan sena karairayaki na zubar. Se kinyi nadamar auran mun Miji, sena illataki yanda ko kin koma yawon Karuwancin naki ba zaki samu masu tayawa ba, bani Dana, kuma ki fito ki doramun abincin dare yanzun ba se anjima ma". Zubaida na tsaye da goyon Zakariyya wanda yake ta rigima tunda wata yarinya ta kawo shi daga gidan da Binta take kaishi raino yana ganin Audu ze fita kuma ya saka kuka wannan yasa ta goyashi harya rufe ido da alama daman rigimar bacci ce hargagin uwarsa ya tadashi. Kwanto mata danta tayi ta direshi kan Kujera, Binta ta fizgeshi ya saka kuka saboda yanda taja hannunsa ko tsoron yaji ciwo batayi ba ta fara jansa tana cewa "Kinji abinda nace ai karki bari na maimaita miki" "Bana tsammanin yace miki ya miki bayanin ni wacece a gidan nan, to idan beyi miki ba ni yanzu bari na gaya miki. Yanda kike matar aure da aka auro da sadaki nima haka nake, matsayinmu daya na yar aiki ko me dafa abinci aka kawo miki ba dan haka ke baki da qarfin ikon da zaki sakani na dafa miki abinci a gidan nan kici, idan kinga haka ta faru to Mijina ne ya bani umarni wannan kuwa zanyi saboda shidin shugaba nane, kuma neman Aljanna ya kawoni gidansa bazan tsallake umarninsa ba muddin be sabawa shari'a ba" Zubaidan ta bata amsa kafin ta angizo daurin dankwalinta gaban goshi tace "Karuwa kuma bakiga komai ba daga cikin halinta, ki saka ido ki gani, tsakanin nidake za'aga wadda zaman gidan nan ze gagara" tana gama fada ta wuce cikin daki tana kada jiki tabar Binta tsaye baki a sake, seda ta bugo qofa kafin Bintan ta farga ta fara dura mata Ashar tana cewa idan ta isa ta fito ta gani seta sauke mata rainin da take taqama dashi yau, ta gama hayagagarta taja Zakariyya suka wuce daki tana cigaba da bala'i kamar tsohuwar karya. Zubaida kuwa Alwala ta daura tanayi tana kuka, a duk sanda aka kirata da Karuwa takanci ciwon abin yanda bata taba tsammata ba. A sanda take cikin rayuwar Alfahari take da sunan amma yanzu tana jn muninsa fiye da misali. Yanzu haka za'a ringa alaqanta yayanta da wannan mummunan sunan? Bayan ta idar da sallah bata tashi ba har akayi Isha'i ta dora shafa'i da wutri tayi addu'a kana ta nade abin sallar ta tashi. A gurguje tayi wanka ta shirya, cikin irin dinkunan da Kilallu irin tane a wancam zamanin ta saka riga da siket daya matuqar kamata ta baza qamshi ta ko ina sannan ta kafa dauri a gaban goshi. Audu ya gaya mata kartayi girki ze shigo musu da abinda zasuci dan haka ta dora ruwan shayi baqi ta zuba kayan qamashi sannan ta dauki Kankanar data hada tun yamma tashanye ta koma falo ta zauna bayan ta kunna waqar Aliko makaho tana bi hankali kwance tana gyada kai. "Baki a washe kamar wawa Audu ringa binta da kallo sanda ta karbi ledojin Kaji da kayan Marmarin daya shigo dasu, "Aa kaga yar dagwas, irin wannan Ado haka gaskiya kinci sunan naki na yar dagwas" ya fada yana washe mata haqora. Ta dan bata rai irin na shagwaba dukda tace "Nace maka bana so ka canza mun wani sunan amma banda wannan" har ranta ta tsani sunan a yanzu amma bata so ta nuna masa hakan cikin fushi ko fada, ya zauna yana sake ce mata "Barni kinji, dadi sunan yake mun. Je ki kawo faranti muci Naman nan tun da zafinsa". Ta wuce Madafa tana juya mazaunanta da basufi rabin na Binta ba amma da yake ta iya sarrafasu bala'in dauke masa hankali take idan tana tafiya. A da gani yake ba Macen data kai Binta iya gwalangwaso da kisisina wannan abin ya qara dakusar da Bara'atu a idonsa yaji sam ta dena birgeshi saboda bata ko kamo qafar Bintan ba babu abinda ta iya se wanda ya koya mata amma yanzu daya auro Macen gaske se yaga ashe duk wani sanaben Binta sharar fage ne, wato jiya yaje cloud 9, yaga abinda ya dauka a gurin Hurul'ayni matan Aljanna kadai ze samu yanzu ita kanta Bintan ganinta yake kamar shi dan yanzu ne ya tabbatar ya auri Mace. Yana can lissafin ta dawo, yanda take duqawa ta ajiye kayan ma abin birgewa ne sannan ta kalle shi tayi masa wani farrr da ido se yaji kamar ze suma dan dadi. "Ina na Maman Zakariyya? Kona kirata muci tare?" Ta fada tana bude ledojin. Ya sauka qasa ya zauna yana cewa "Ai tana da Kaji a firinji, kema gobe za'a kawo miki saboda ajiyar Danyan Nama da sauran kayan amfani" ya bata amsa yana daukar kofin data tsiyaya masa baqin shayi a ciki kurba seta shagwabe fuska tace "Haba dai, ya za'ayi muna gida daya ka siyo abu muci mu kadai banda ita da yaronmu? Aa gaskiya bari na dibar mata dan wannan ai ya mana yawa Kaji biyu Manya ina zamu kaisu" taja faranti ta fara dibar Naman, wata qaramar Leda da taji dumi ta bude taga Tsirene a ciki ta aika masa hararar qasa tace "Harda tsirema duk a wane cikin zamu zuba mu kadai?" *MAMAN MARYAM ONLINE BUSSINESS* *Ina kuke Mata Yan kwalisa , Ina nufin isassun Mata ,Wai shin Kuna da labarin shahararren company nan namu na GHT wato good healthtreatments* *Wanda yazo muku da fitattu Kuma* *ingantatattun suppliment ,na dukkan matsalolin ku*❓ *Ina maisan tayi kyau,irin na isassun Mata ya fitar Miki da shef dinki tayi Miki gyara in and out ,nemi royal jelly dinmu na company GHT* *Wanda aka yishi da xuma ,kundai San amfanin Zuma basai na fada miku ba , hajiya ta kixo ki Yi gyara domin ki kerewa sa,a kije taro ko baki da ko sisi kiji Ana rangada Miki hajiya , saboda yanda Zaki Kara kwarjini ,kina walwali acikin mutane , magungunan ght anti agen ne suna maida tsohuwa* *yarinya ,yarinya Kuma ta koma jaririya* *Muna da magunguna iri iri* *NA GYARAN JIKI* *NA GOGE NANKARWA* *NA RAGE QIBA* *NA CIRE TUMBI* *NA QARIN HIPS* *NA GIRMAN BREAST* *NA QARA TSAHON GASHI* *NA QARIN NI'IMA WANDA ZAI SAUKAR MIKI DA NI'IMA YA QARA MIKI DADI DA ZAQI A GURIN OGA* *Muna da hadin bita zai zai ,indai kishiyar ki tana Shan magungunan GHT, tohh lallai sunan ki sorry domin kuwa tazarar dake tsakanin ku kamar tazarar sama ne da kasa* *Muna da Wanda zai matseki ciki da waje Andai na yayin dinki uwargida*, *Sannan company mu na GHTBai tsaya anan ba* *Ya kawo muku maganin dukkan matsalolin ku* *INA MASU HAWAN JINI?* *INA MASU CIWON ZUCIYA?* *INA MASU CIWON QODA?* *INA MASU CIWON HANTA?* *INA MASU SICKLER?* *INA MASU HIV?* *INA MASU CANCER?* *INA MASU NEMAN HAIHUWA?* *Tohh Ku matso GHT taxo muku da magungunan matsalolin ku* *Kuma muna da testimonys da yawa ,na wadanda suka gwada suka da ce* *Munanan a KANO KUNTAU* *Kuma muna tura Kaya ko wanne gari cikin aminci da gaskiya , kuma kayan mu muna badashi ne cikin price Mai rahusa ga kyau ga inganci sannan ga Rahusa* *Kutuntube mu ta wannan number 📞08129249549* *📲07011401314* Ta cika faranti da Kazar da tsire ta lullube da takarda sannan ta bude kayan Marmarin suma ta diba a Leda tana kallonsa tace "Bari na kai mata". Da kai ya amsa mata ta dauka ta fita ya bita da kallo yana tuna lokutan baya a zamanin Amarcin Binta. Kullun ta Allah se sunci Gasashshiyar Kaza da tsire da wani damun fura me shegen dadi da yake siyo musu suci su biyu ko takardar Naman Bara'atu da Yaranta basa gani balle suji qamshi. A sannan ma yakan siyo hardasu amma indai ya fara shiga bangaren Binta dashi to ya zama haramiyarsu daga baya ma ya dena siyowa dasu ta cusa masa ra'ayin ai suna ci a Miya kuma sanda tana Amarya itama an mata dan haka yanzun lokacinta ne taci ita kadai shiyasa yanzun yayi amfani da maganarta ya siyo musu shida Zubaida kadai itace Amarya ai itama tana ci a Miya. Zubaida kuwa a qofar dakin Binta ta tsaya ta rafka sallama, Bintan na zaune ta zabga Tagumi, abin duniya ya isheta taji sallama, bata dauka Zubaidan bace ta amsa harda bada izinin a shiga. Ta shiga tana qara wata qaramar sallamar ganin itace ya saka Binta zabura tana binta da kallo tundaga sama har qasa, dukda kyashi da hassadarta daya cika mata zuciya seda ta yabi kyan da shigarta tayi to ina ga Audu? "Ke bakida hankali koM meya kawoki dakina? Da izinin ubanwa kika shogo?" Ta fada cikin hargowar data zame mata jiki, Zubaidan tayi murmushi tace "Seda nayi sallama fa kika amsa kafin na shigo, kuma ba wani abu ya kawoni ba, kazar Amarci Mijinmu ya sake siyomun shine nace bazanci ni kadai na na raba na kawowa Dana" ta dangwarar mata da Farantin a qasa ta juya tana tafiyar yanga Binta tayi kukan kura ta kai mata cafka, a yanda ta cakumeta Allah ya dubeta kamar jifa sega Audu ya fado dakin badan haka ba ta tabbatar da tace seta ballata ta zuba a wilbaro tabbas abinda tayi niyya kenan. "Baki da hankali Binta meye haka zaki kamata da dambe?" Ya fada yana janye Zubaida da zuciyarta ke buga tsalle daga hannunta. Bata dauka jarabar Matar nan takai haka ba, ita ko doguwar cacar baki ba iyawa tayi ba ina dmga yar bawa hammata iska kuma ace da wannan qansamemiyar basamudiyar ai wata rana murus zata kasheta idan akace suyi dambe. "Dole kace bani da hankali mana wato kai ka aikota tazo tamun cinikinta Abinda aka saba ko? Ni zaka wulaqanta Audu da abinda zaka sakawa ubana kenan bayan duk halaccin da yayi maka a duniya? Karka manta mahaifina shi yayi maka rigar da har ka ringa yawo a gari ka kwaso wannan karuwar, to wlh bazan zauna baqin ciki ya kasheni ba tattarawa zanyi na bar maka gidan ka idan yaso ka auro irinta goma ka ajiye gara na koma gidanmu inda ake sona" tayi bal da farantin kazar da aka kai mata ta shige daki tana kuka wiwiwi, diri diri yayi ya rasa me zeyi, ya bita ne ko kuma su fita su bar mata dakin? "Ka bita mana karfa ta jiwa kanta ciwo kamar watsi take da kaya" Zubaida ta fada jin Binta na zubar da kaya a qasa se ya tafi solo solo ya shiga dakin ita dai Zubaida ta juya ta fice har sannan jikinta be dawo daidai ba daga tsoron shan suburbuda a hannun Binta. Bata san ya suka qare ba dan har bacci ya fara fizgarta kafin ya shigo ransa duk babu dadi ganin haka yasa daman tayi shirin bacci a kwance take tana jiransa se kawai ta gyara kwanciya dakyau tayi baccinta shima ya gama abinda zeyi be nemeta na duk yanda yake cike da zumudin kebewarsu amma ya gagara yin komai, yanda Bintan ta ringa kuka tana fadin zata tafi kawai ta shiga duniya yana wulaqantata ne saboda yaga Dadynta ya goyi bayansa sanda ta koma gida ita kawai gara ta tafi koma inane tunda babu me qaunarta ya shiga tsakaninta da Iyayenta kuma yazo yana wulaqantata akan Matar daya hadu da ita daga baya tasan baya qaunarta tun sanda aka kashe mata Da amma be dauki matakin komai ba. Haka ya kwanta ransa duk babu dadi sedai da Asubahi da yar dagwas ta kaishi gari me nisa tuni ya manta da wata Binta da Emotional blackmail dinta. Tana can ta saki baki tana jiran ya bugo Asubanci yaci gaba da rarrashinta dan jiyan Data gama surutai bandaki ta shiga ta kulle yayi yayi ta fito taqi tace ya fitar mata a daki in ba haka ba zata kwana a ciki sannan ya tafi to ta dauka daya dawo masallaci ko kafin ma ya fita se shiga ya dubata amma taji muqus har gari ya waye tarwai se Tara saura na safe suka fito da Amarya yayi shirin fita, tana zaune kan barander dakinta Lantana na share tsakar gidan suka fito ta zube tana gaishe su. Kamar jiya yauma harda dan risinawar Zubaida ta mata ta gaidata, bata tanka ba ta zabga tsaki bata dai yi masifar data sababa shirun nata kuma se yaji babu dadi dan haka yacewa Zubaida yana zuwa. Falon Bintan ya shiga ya tsaya a tunaninsa zata bi bayansa amma shiru, ya leqo ya mata magana nan ma ci kanka bata ce masa ba wannan ya hasalashi ta wulaqantashi gaban me aiki dan haka ya fice fuu ko Adawo lafiyar da Zubaida take masa be amsa ba. "Zaki san ni ba sa'ar wasanki bace wlh yau se kin gane kurenki badai jiya ya ceceki ba? Yau naga ubanda ze kwaceki a hannuna" Binta ta fada tana miqewa bayan data tabbatar Audu ya fice daga gidan tabi bayan Zubaida data qarawa tafiyarta sauri jin abinda take fada, gudu ta saka ganin dagaske kamata take shirinyi tana fadawa daki ta turo qofa Binta ta saka hannu zata dannata ciki bisa tsautsayi ta datse mata yatsa da qarfi take ya fashe ya fara jini. *MATAR MUTUM* *NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER* *FIKRA WRITERS ASSOCIATION* *LITTAFIN KUDI NE* *PAY 500 A ASUSUN* *7061838488* *OPAY DIGITAL SERVICES* *MARYAM FAROUK* OR *0709290797* *ACCESS BANK* *SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488* *IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705* *Kuyi following dina a Arewabooks @Maryamfarouk01 inda zaku karanta wannan littafin tareda sauran littattafaina* *NAGODE* *PAGE 20* "Akan me zaki kulle qofa? Dukanki zatayi ko cizo da ze saka ki kulle qofa har ki hada da hannunta ki matse?" Audu ya fada cikin kaushi yana duban Zubaida dake durqushe gabansa kanta a Qasa Binta kuma na daga gefe tana yarfe hannu yatsanta data datse da qofa ya kumbura idanun nan sunyi fici fici da alamun tasha kuka ba kadan ba yau din. Audu na yin sallama Lantana da bata tafi ba ta zube a gabansa tana fada masa uwar dakin nata babu yanda take tana daki, hankali tashe ya doshi Dakota n nata can ya tarar da ita tayi zaman dirshan a qasa tana yarfe hannu tana kuka harda majina, shiri sukayi da Bintan akan hakan dukda dagaske take jin azabar ciwon yatsan amma tuggun da take so ta hada da faruwar hakan shi ya saka ta sake rakwarkwabewa ba iyakar zafin ciwon ba. Daya tambayeta ya akayi taji ciwon take ta gaya masa Zubaida ce, akan ta bita daki su sulhunta kamar yanda ya roqeta jiya akan tayi haquri ta kwantar da hankalinta su zauna lafiya to bayan tafiyarsa tayi tunani akan hakan kuma taga ya kamata ace tayi shine yau taje dakinta da niyyar ta bata haquri akan abinda tayi mata jiya a maimakon ta saurareta se kawai ta hau zaginta tace ta fitar mata a daki, data tsaya ta dafa qofar shine ta hada harda hannuta ta datse shi kuma kamar fulawar da aka zubawa Yeast ya shiga kumbura ya tafi fuuu ya kira Zubaidan nan gaban Binta ya titsiyeta yana tambayarta ba'asin dalilin rufe qofa. "Ni ba a sanina na bigeta ba kuskure ne" ta fada cikin sanyin murya, Binta ta zabura tace "Wlh qarya takeyi tana sane ai Lantana na gurin ka tambayeta kaji" "To a tambayi Lantanar mana in har zata fadi tsananinta da Allah ko ita ta san ba ina sane na bige miki hannu ba, sannan ni bani na nace ki shigar mun daki ba bare har ki saka hannunki qofa ta datse ki" Itama Zubaidan ta katseta "Ke! A gaban nawa ma rashin kunya zaki mata? To bari kiji daga yau koda wasa karki sake kullemun qofa tunda dai gida nawane ba na wani ba, sannan dukanku matana ne babu wadda nayiwa shamaki daga shiga dakin wata a cikinku, yanzu kalli ciwon da kikaji mata ji yanda hannun ya kumbura fisabilillahi hakan da kikayi yayi kyau?" Audu fada yana zare mata ido, Zubaida sadda kai qasa saboda kukan dake shirin bada ita tace "Amma dai tsakani da Allah ba haka ya kamata kayi ba, seka tambayeni abinda ya hadamu tunda dai kaji daga bangarenta" "Ke zaki tsara mun abinda zanyi a cikin gidana? To banyi hakan ba nace banga damar yin hakan ba koda abinda zakiyi?" Ya hayayyaqo mata seta fashe da kuka saboda takaici tama rasa abinda zata kuma ce masa "Tashi kije" ya bata umarni yana wani dauke kai dan kukan nata ya tabashi amma shi a dole ta masa laifi shiyasa ya dauke kai. Cikin kuka guiwoyinta a sanyaye ta wuce dakinta. Zubaidan na fita itama Binta ta fashe masa da kuka tana cewa "Yanzu shikenan ta jimun ciwo taci bulus iyakar abinda zaka ce mata kenan sannan saboda makirci ta fita tana kuka kamar ita aka zalunta?" "To ya kike so nayi, so kike na rufeta da duka ko kuma na riqe hannunta ki rama abinda tayi miki? Ina kinji dai tace kuskurene?" Audun yayi kanta a fusace, yanda yayin yasa tayi shiru bata kuma cewa komai ba wato tuggunta be samu shiga ba so tayi ya rufe Zubaidan da fadan koma ya falla mata mari koya rufeta ma da duka amma dai ko banza hakan ma babu laifi tunda ya sakata kuka a gabanta da haka zata cigaba da nunawa Zubaidan ita din ba kowa bace a gurinsa Audu, kuma duk yanda ta dama haka za'a sha. Qarawa kukanta volum tayi babu ko dadin sauraro Audu yaja tsaki yace ta tashi suje gurin wani wanzami dake qasansu a duba hannun. "Wlh ba zani ba idan ba zaka kaini Asibiti ba sedai na zauna da hannun haka kuma gobe karka saka ran zaka fito ka tarar dani a gidan nan Kaduna zan wuce" ta fada cikin kuka. Wannan tasa ya kaita Asibitin suka bata magu gunan rage radadi bayan an mata allurar kashe kwayoyin cuta sannan suka dawo gida lokacin goma harta gota, seda taci abinci tasha magani kafin ya wuce dakin Zubaida. Tana zaune a falo ta kunna Tv amma hankalinta baya ga abinda ake nunawar tayi nisa cikin tunanin da tunda ta baro dakin Binta takeyinsa. Se taga kamar shari'ar ta Audu ba haka ya kamata ya gudanar da ita ba, tambayarta ya kamata yayi abinda ya hadata da Binta har wannan tsautsayin ya faru bawai ya dora mata laifin matsewa matarsa hannu haka nan ba kuma da yake maganar kowa tana iya shigar dakin yar uwarta babu shamaki a ina ake haka fusabilillahi? Yanda ya shiga fuska a daure haka tayi masa sannu da zuwa jiki babu karsashi guiwoyinta suka sake sanyi da Al'amarin Audun, to fushin na menene kuma? Ba an gama magana ta wuce ba? Ya gama uzurirrikansa data bashi abinci yace ya qoshi, bata sake tsinkewa da lamarin ba seda ya juya mata baya da sukaje kwanciya a ranta tace lallai abin babbane. "Kayi haquri in dai akan abinda ya faru jiya ne kake fushi wlh ba ina sane na matse mata hannu ba ita ta biyo ni tana zagina tace zata dokeni ni kuma tsoron haka yasa na shigo na tura qofar bansan ta saka hannunta a ciki ba" Zubaidan ta fada hawaye na saukar mata sanda Audu ke shirin fita da safe ba tareda ya ko kalli kayan karin data jera masa ba. "Oh, bayan abinda kikayi shine kina da bakin sake magana harda sharri zaki mata a yaushe ta zageki harta biyoki zata dokeki?" Ya fada yana dakatawa daga fitar dayayi niyya. Hawaye suka balle mata na takaici, wato sharri tayi mata? Ita Bintan Allah kadai yasan abinda ta fada masa wato natane gaskiya se ita data fadi ainihin abinda ya faru shine zece ta mata sharri? Muryarta na rawar kuka tace "Akan me zan mata sharri? Sannan ai kaima zaka iya bada shaida akai dan ba shibe karo na farko data zageni ba ko tayi yunqurin dukana a gabanka ma anyi shekaran jiya ba kai ka kwaceni daga hannunta ba?" Ta fada tana tsare shi da ido. Yayi jummm alamar ya gasgata abinda ta fada din amma saboda qi fadi da rashin son gaskiya irin nasa se ya murje yace "Rashin kunya zakiyi mun har kina tsareni da ido kamar wani sa'anki? To bari kiji muddin kina neman zaman lafiya a gidan nan dole ki zauna lafiya dani da kuma matata. Mu bamu saba fadace fadace da kuka iya har ana fidda jini ba a gidan nan dan haka ki san a inda kike" daga nan yasa kai ya fita ya barta tsaye kamar ya dasata tana juya kalamansa. Ita da suwa suka saba fadace fadacen da zubar da jini? "A bariki mana yake nufi" zuciyarta ta bata amsa, dabas ta zauna dafe da kunci hawaye suka shiga mata tsere, wato abinda yake nufi kenan, a fakaice yana gaya mata cewar nan ba irin gidan daya dakkota bane kenan da suka saba Fada kamar Kaji suna jiwa junansu rauni Yau Audu da kansa yae goranta mata wani al'amari daya shude a rayuwarta kenan. Wannan abu yasa gaba daya jiki ta yayi sanyi, sararin data samu ta fara baje kolin sharholiyarta duk karsashin ya barta shima kuma be bi takanta ba yana ta tattalin Binta da hannu ya saka a gaba har ya saukar mata da zazzabi me zafin gaske seda ta kwana uku a kwance kullum kuma is Zubaidan ta shiga ta dubata safe da dare idan yana nan zata amsa cikin sakin fuska idan baya nan kuwa har Lantana samun damar yaba mata magana take suce mata mayya wai ta kama mata hannu to kurwarta kur. Ita Binta ko abinda take mata ma sam be dameta ba irin na Audun, qiri qiri yaba ganin gaskiya amma ya take yabi qarya shin wane irin mutum ne shi haka? Ya za'ayi rayuwa ta yuwu a haka ace duk abinda aka gayawa mutum walau shine gaskiya walau qaryane se ya hau ya zauna kuma idan ya gano gaskiyar daga baya girkan kai da izza su hana shi karbar kuskurensa ai ko baze furta da baki ya karbi gyara ba se ya nuna hakan a aikace amma shi babu daya daga ciki da yakeyi sedai ya dora fushi wannan ai ba daidai bane. Data lura da gaske fushi yake da ita kuma bashi da alamar sakkowa dan har ranakun girkinta da suka zagayo bacci ke shigar dashi dakinta safiya nayi ze fice dole ta sauke nata fushin ta sake samunsa ranar ta tattara duk wata wayo da dabarar da take dasu ta wanke kanta a gurinsa ta hanyar karban laifin da bata aikata cikin sani ba ta kuma tabbatar masa da ba za'a sake ba har da kukanta tace kuma ya rakata a gabansa ta baiwa Bintan haquri sukaje ta bata haqurin ganin idonsa yasa Binta tace ta haqura ai ita komai ya dade da wucewa a gurinta daman wannan tasa ya sakko daga fushin da yake suka koma zamansu lafiya abinda yayi mugun batawa Binta rai. A zaman tsamar da sukayi ba qaramin qara samun kan Audun tayi ba, a wayo da dabara take dada kwarkwarashi shi kuma dake kan keke ne ya hau daram ya zauna. Shiryawarsu da Zubaidan se ya zama silar warewar nata shirin musamman da taga kamar Zubaidan ta ganota duk irin tuggun data hada mata a gurin Audun ta dena musawa zata amsa laifinta ta durqusa har qasa ta bashi haquri tana hawayen munafunci a cewar Bintan shi kuma me son girma kansa ya sake fasuwa shikenan kome ta shirya ya wargaje. Tun daga wannan kuma Zubaidan ta hankaltu duk laifin da Binta ta dora mata zata amsa ta bashi haquri tunda ta fahimci abinda yake so kenan babu ruwansa da jin ainihin magana yanda take hakan kuwa da takeyi ya sama musu zaman lafiya se a dade ba'aji kansu ba idan ba kuma Bintan ta shammaceta ta tunzuro shi ta yanda harta gaza kare kanta ba. A haka aka kwashi watanni biyar da Auro Zubaida a kuma wannan yanayi ta fara laulayi wanda yazo mata da zafin gaske ga Amai ga Zazzabi lalurori dai iri iri ba qaramin Jiki take ji ba, wannan cikin ya sake gigita Binta, wato Zubaida zama tazoyi ma kenan tunda gashi har tayi ciki ita tana me haka ta faru yama za'ayi Mata suyita haihuwa a gidan Audu Bara'atu tayi biyu ita tana da daya kamar rai kuma a auro wata a bayanta tazo ta goga da ita wannan baze yuwu ba ta shiga takalar masifa kala kala fatanta Zubaida ta tanka mata ta samu dalilin lakada mata na jaki ta yanda cikin zebi rariya tun be gama samun gurin zama dakyau ba sedai bata samu hakan ba, Zubaida da ko a baya bata biye mata ba balle yanzun da take ta kanta. Abin ya hadewa Binta biyu dan Audun shima yanzu duk ya maida hankali kan Zubaidan sosai wannan yasa ta kasa jurewa ta fiddo haukarta fili take baje musu ita watarana ya tanka mata wata rana kuma ya qyaleta a haka abinda ya sassuta lamarin ganewar da tayi itama tana da shigar ciki saboda batan wata da tayi amma tayi shiru bata gayawa Audu ba sannan kuma cikin Zubaida yayi watanni uku a lissafinsu na daga sanda ta fara laulayi kenan ita kuma nata yana wata daya. Koda Zubaida sukaje Asibiti likita ya tambayeta yaushe rabon da tayi Al'ada ce masa tayi watanni uku, tayi lissafi da watan data fara laulayi dukda maganar gaskiya ba zata iya cewa ga lokacin da tayi al'ada ta qarshe ba tun zuwanta gidan sau daya tayi watanninbaya da suka biyo idan Al'adar tazo kwana daya ne kuma dan kadan ba kamar yanda ta sabayin kwanaki Bakwai ba kuma ba se qarshen wata ba ko yaushe tana iya ganinsa kuma ya dauke har ta fara zaton ko Sanyi ne ya kamata to tunda tasha magani kuma jinin be sake zuwa ba babu dadewa kuma ta fara laulayi. *MAMAN MARYAM ONLINE BUSSINESS* *Ina kuke Mata Yan kwalisa , Ina nufin isassun Mata ,Wai shin Kuna da labarin shahararren company nan namu na GHT wato good healthtreatments* *Wanda yazo muku da fitattu Kuma* *ingantatattun suppliment ,na dukkan matsalolin ku*❓ *Ina maisan tayi kyau,irin na isassun Mata ya fitar Miki da shef dinki tayi Miki gyara in and out ,nemi royal jelly dinmu na company GHT* *Wanda aka yishi da xuma ,kundai San amfanin Zuma basai na fada miku ba , hajiya ta kixo ki Yi gyara domin ki kerewa sa,a kije taro ko baki da ko sisi kiji Ana rangada Miki hajiya , saboda yanda Zaki Kara kwarjini ,kina walwali acikin mutane , magungunan ght anti agen ne suna maida tsohuwa* *yarinya ,yarinya Kuma ta koma jaririya* *Muna da magunguna iri iri* *NA GYARAN JIKI* *NA GOGE NANKARWA* *NA RAGE QIBA* *NA CIRE TUMBI* *NA QARIN HIPS* *NA GIRMAN BREAST* *NA QARA TSAHON GASHI* *NA QARIN NI'IMA WANDA ZAI SAUKAR MIKI DA NI'IMA YA QARA MIKI DADI DA ZAQI A GURIN OGA* *Muna da hadin bita zai zai ,indai kishiyar ki tana Shan magungunan GHT, tohh lallai sunan ki sorry domin kuwa tazarar dake tsakanin ku kamar tazarar sama ne da kasa* *Muna da Wanda zai matseki ciki da waje Andai na yayin dinki uwargida*, *Sannan company mu na GHTBai tsaya anan ba* *Ya kawo muku maganin dukkan matsalolin ku* *INA MASU HAWAN JINI?* *INA MASU CIWON ZUCIYA?* *INA MASU CIWON QODA?* *INA MASU CIWON HANTA?* *INA MASU SICKLER?* *INA MASU HIV?* *INA MASU CANCER?* *INA MASU NEMAN HAIHUWA?* *Tohh Ku matso GHT taxo muku da magungunan matsalolin ku* *Kuma muna da testimonys da yawa ,na wadanda suka gwada suka da ce* *Munanan a KANO KUNTAU* *Kuma muna tura Kaya ko wanne gari cikin aminci da gaskiya , kuma kayan mu muna badashi ne cikin price Mai rahusa ga kyau ga inganci sannan ga Rahusa* *Kutuntube mu ta wannan number 📞08129249549* *📲07011401314* Bayan tabbatar da lafiyarta data abinda take cikinta aka bata sati hudu ta dawo daga Asibiti, kafin zagayowar sati hudun nan tamkar wadda aka bugawa iska cikinta yayi wani girma na ban mamaki. A watanni ukun da tayi muddin ba wanda ya karanci yanayi na masu ciki ba shine ze iya tantance samuwar cikin a jikinta dan idan ka cire Laulayi babu wata halittarta data canza kota nuna samuwar wani abu tattare da ita. Cikinta na nan yanda yake be qara tudu ba haka nan batayi qiba ba se gashi a sati hudu cikin ya bude yayi girma haka jikinta da fuskarta duk sun sauya idan ka ganta seka dauka in kun rabu yanzu anjima za'ace maka ta haihu. Binta bata nan ta tafi Kaduna sanadin jikin Alhaji Zakariyya daya motsa harya kwanta a Asibiti dan haka suka tafi tareda Audu ya kwana biyu ya barota a can kuma zuwan yayi daidai da bikin yaye su Baballiya da akayi dan haka suka hada tafiyar harda Yan Bechi duk sunje sun duba jikin Alhajin kuma a gidansu Bintan aka musu masauki suka kwana biyu suka juyo tare aka baro Binta a can satin ta uku kafin ta dawo Kano. Ranar da Binta ta dawo ita kuma Zubaida bata nan taje gidansu yini se dare Audu ya dakkota koda suka shigo kuma bata ma san Bintan da dawo ba dan be gaya mata ba se da ya shiga tareda Zakariyya wai yaje mata sallama sannan ta sani ta kuwa cika da mamaki amma batace masa komai se fatan wayewar gari lafiya tayi kwanciyarta ita kadai. To washe garima bata fita ko tsakar gida ba dan a yanayin da take yanzun tafi ko yaushe buqatar samun hutu da nutsuwar zuciya bata shirya dibar hauragiyar Binta ba dukda tana so taje su gaisa tayi mata yame jiki amma ta bari akan se da dare idan yana zaune seta shiga ko ganinsa ze rage kaifin duk rashin mutunchin data so yi mata. Hakan kuwa akayi, bayan isha ta shirya taje Audu na zaune yana cin abinci tareda Zakariyya Binta na cikin daki tana buruntu tayi sallama ya amsa yana tsokanarta da cewa "Uwar biyu kin shigo?" Haka yake ce mata tunda cikin ya fara wannan girma me ban mamaki yace kodai yan biyu ne shi yasa wata hudu cikin ya ninka girmansa se tace masa to qilan tunda ita ba sanin ya cikin yan biyun yake tayi ba. "Baquwa mukayi?" Binta data fito ta fada tana zama akan kujera idonta akan Zubaidan, Audu ya murmusa yace "Baki ganeta ba? Kallarta dai da kyau kiga dawa tayi miki kama?" Ta zuba mata ido tana so ta gano wacece din kamar yanda ya ce, tai fici fici da ido se ko ta zabura sanda ta gama ganota ta nunata tana cewa "Ke..meye wannan? Me zan gani haka?" Yanda tayin ba Zubaida ba hatta Audu seda ya bushe da dariya yanda kasan wadda taga wata fatalwa haka rikice tana jera mata tambaya yace mata "Kinga abin mamaki ko? Yanda kika san cikin nan na jira ki tafi ya fara girma qila da baki dawo yanzu bama sedai kizo ki tarar ta haifeshi" "Au Namiji ma zata haifa?" Maganar ta subucewa Bintan, Zubaida ta kalleta Audu da be gane inda maganarta ma ta dosa ba yace "Yan tagwaye ma kuwa muke tsammata dan wannan cikin daga ke har Bara'atun ban taba ganin wadda tayi me girmansa ba" ya furta sunan Bara'atu a fili karo na farko tun bayan rabuwarsu da ita. "Zancen banza ma kenan, ita zata haifi yan tagwayen a gidan nan? Wlh baze yuwu ba" ta idasa kwancw qullin haukarta. Zubaida ta gyara zama ganin cin kan Bintan gaba yakeyi tace "Yaya ina wuni? Ya aka baro yan gida? Ya me jiki kuma? Ubangiji ya qara afuwa yasa kaffara ne" daga nan ta shiga yunqurin miqewa tsaye tana jin Bintan dake kallon Audu tace "Lallai ma wannan rainin wayo ne qarara kuma wlh bazan dauka ba, ni za'a mayar mahaukaciya cikin da be ko cika qata hudu bane zeyi wannan girman sannan saboda jaka ce ta raineni na yarda ai kuwa ba'a isa ba" Zubaida bata tsaya sauraronta ba ta wuce dan dai kamar maganar bata shafeta ba haukanta da bata gajiya dashi ne ya motsa ga Mijinta nan seta sauke shi a kansa amma ba ita ba ciki kuma dai ba mutum ke bayarwa ba balle tace zatayi fito na fito da wanda ya bata dan haka tana zuwa daki taci abinci tasha saiwoyin data jiqa jiya dataje gida Baba Zayya Amaryar da Malam Hassan Babanta yayi watanni biyu kenan ta hado mata saiwoyi wai na taimakon sauqin naquda ne da rage zaqi a yanda Baba Zayyan tace wai cikinta ya nuna alamun ta kusa haihuwa ta ringa dariya tana cewa Baba Zayyan kace a kanta za'a fara haihuwar hudunni kenan ita kuma tace mata to su daura tsakanin su za'a me gaskiya dan bata yarda da lissafin Asibiti ba ko makaho yaga cikin Zubaida yasan ya haura zuwa watanni bakwai ko takwas. "Idan kika lissafa watanninki a daki ai cikinki ya kusa isa haihu ina watan Sallar Tsofaffi akayi Bikin wata na takwas fa kike ciki yanzu ai dab kike da ki haihu" Baba Zayya ta nanata mata. Ita dai bata dauki batun da muhimmanci ba, wata hudun nan shi take lissafawa kanta dukda girman cikin da motsin da takeji abin dubawane, ba wannan ne cikinta na farko ba ciki biyu tayi a rayuwarta ta baya sedai dukkansu baau kai matakin da aka busa musu rai ba ta ciresu dan haka ba zata dorar da komai game da yanayin girma ko sanda yake fara motsi ba. Ta dafe cikin da hannu biyu tana jin wani yanayin nadama mara misaltuwa yana shigarta. Yanzu fa Al'umma zasu iya ringa jifan abinda zata haifa da rayuwarta ta baya ko? Washe gari Audu na fita Binta ta fice itama, daren jiyan basu kwashe shi qalau ba, Bintan da tayar da bala'i babu rufa rufa tace Audu ya raina mata wayau, watau ciki yayiwa Zubaida a waje can gurin tambadarsu shine ya aurota dan su rufawa kansu Asiri kenan ko to billahillazi ba zata yarda ba seta bankada kowa yaji wannan aika aikar da sukayi baze gurbata musu zuri'a ya hada yayansu da yan uba Shegu ba ta ringa masifa tana bala'i seda ya zabga mata mari ya korata dakinta kafin ya samu sa'ida hayagagar da take masa akai da safe kuwa ko leqata beyi ba dan tayi bala'in bata masa rai akan maganar tata Zubaidan kanta daga bakin qofa suka gaisa ya fita shine Bintan najin fitarsa daman ta shirya itama ta tafi gidan Turai. "Yanzu ke meye abin daga hankali a nan yanzu? Wannan ai abinda zaki koma gefe kiyi dariya kisha kallo ne idan ma da cikin ta shigo ke ai gaba ta kaiki dan magana na fita dayan biyu ne dole ya sawwaqe mata ta tafi ta nemi uban cikinta idan ma nasa ne dai ta saku tunda dai ba'a Aure da ciki to ai gaba ta kaiki gobarar Titi a Jos Qawata" Turai ta fada bayan da taji bayanin Binta. Ta numfasa tace "Zancenki gaskiya ne amma ta yaya kike tsammanin haka zata faru? La shakka idan cikin ba nasa bane wannan kuwa na san ze iya sakinta amma muddin na sane kema kinsa babu inda zataje kuma zama sunyi auran ne daman saboda kauda idon mutane da kuma zargi" "Banyi muku katsalandan ba Hajiya amma watan auran nan da kuke magana akai nawane tukunna?" Barira me Aikin Turai dake ta goge goge hankalinta na kan hirar su Bintan ta fada. Turai ta harareta tace "Wai sau nawa zan hanaki tsoma mun baki idan ina magana da mutane? Aiki kikeyi dama ko kuwa zaman gulma shiyasa kika maqalw gaban Tv tun dazu kin kasa gama gogewa kenan?" "Kiyi haquri hajiya ba gulma bace ba maganar gaskiya ce wanda a ganina duk abinda zaku shirya dole ya zamani kunyi akan saitin da ba za'a ruguzaku ba. Akwai hanya me sauqi da zakubi ku heganta cikin nan kona Alhajin ne tunda dai an samu tangardar lissafi girman ciki ya zarta watanninsa" Barira ta sake fada bayan ta saki duster da take goge goge da ita ta juya ga abinda tafi iaywa wato hada tuggu da munafunci, abinda ya kaso mata aure kenan kuma ya korota daga qauyensu saboda an mata tambari duk wata Masifa data taso tsakanin kishiya da kishiya a garin In sha Allahu se kaji sunan Barira a ciki ita ta qullota kuma lafiya lau take zaune da nata Mijin tsabar yanda kawa qara da zuwa shari'a gaban me gari akanta yaqi qarewa yasa ya sallameta shine wata qawarta da ta fito Aikatau Birni ta janyota itama suka taho a gidansu Turai waccen take aiki dan haka da sukazo ita kuma tata me aikin sannan ta tafi gida se Mamarsu tace ta dauki Bariran dukda bata so ba dan bata son me aiki babba kodan irin Mazansu ido a mata amma ganin ta iya aiki kuma dai ta ganta kalar gidadawa kamar ba zata yarda da irin wannan abin ba yasa ta karbeta kuma se take jin dadin zama da ita dan Barira badai ladabi da duk cikin iya takunta. Bi ta da Turai suka shiru sunasauraronta ita kuma ganin sun bata hankali yasa taci gaba da cewa "Ina itace naji kunce tsohuwar kilaki?" Turai ta gyada kai alamar haka ne, Barira ta gyara zama tana buga cinya tace "Yo Allah na tuba kwace goruba a hannun kuturu ai shiyafi komai sauqi, ai kamar yanda Hajiya tace miki ki koma gefe kihya kallo to haka zakiyi amma kafin nan se kin basa bam din da ze tayar da kowa, abu daya zafi fada da ze maida Alhaji hayyacinsa in ma cikinsa ne in ma ba nasa bane kawai kice masa kin gano da cikin ta shigo, zuwa sukayi aka kwantar dashi se yanzu da suke ganin ta dan kwana biyu aka tashe shi kina fada masa hala kija gefe kiyi zamanki kawai ki saka ido, in cikinsa nema zaki gane idan ma na wani ne kin haska masa hanya duk ma yanda akayi ze binciko" "Amma Barira kanki yana kawo haske, to tsaya dagaske ana kwantar da cikin kar kuma mu fadi abinda ba haka ba" Turai ta fada tana jinjina tunani irin na Barira. Barirar ta sake washe baki tace "Kai Hajiya yo wannan har wani abun mamakine ko a nan cikin Binni ai anayi. Mu a karkarar mu kihiya tanawa kihiyarta asiri a kwantar mata da ciki se kiga Mace ta hekara goma da ciki ayita cewa Aljanune nan ba asan Asiri aka mata ya kwanta ba in ta dage da neman magani se kiga ya tahi an haife dan to haka idan Yara suka dakko abin kunya hima zuwa ake a kwantar hi se an kwana biyu a daki lissafi yayi daidai se tayar dahi kiga yarinya ta haihu qalau babu me cewa komai" "To amma ai ita watanta takwas yanzu fa" Binta ta fada bayan data gama hada lissafi akanta. Barira ta sake sheqewa da dariya irinta shegun qauye tace "Kai Hajiya yane muke ta maimaita magana amma kamar baku ganewa. Dama ai kintatar lokaci akeyi se a daga cikin kinga in ta haihu nan da sati ko biyu ne ai babu me cewa komai tunda ta shiga wata na tara a daki to amma idan kika bullo da wannan maganar ko shekara tayi kanta haihu kin saka kokwanto a zukatan jama'a musamman da daman tana da tambari sannan shi kansa me gidan kinga lissafin da yakeyi na cikin ai be kai asalin watannin qiyasin girmansa ba ko?" https://chat.whatsapp.com/I8xKHGurk7EBf5ZqQdxHKG *MATAR MUTUM* *NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER* *FIKRA WRITERS ASSOCIATION* *LITTAFIN KUDI NE* *PAY 500 A ASUSUN* *7061838488* *OPAY DIGITAL SERVICES* *MARYAM FAROUK* OR *0709290797* *ACCESS BANK* *SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488* *IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705* *Kuyi following dina a Arewabooks @Maryamfarouk01 inda zaku karanta wannan littafin tareda sauran littattafaina* *NAGODE* *PAGE 21* Rai fes Binta ta koma gidase da tayiwa Barira kautar Naira Dari biyu tukuici. Ita kadai ta ringa sakin murmushi a hanya harta koma gida nan ta tarar da Lantana rabe qofar daki tana jiranta. "Ai nazo tuntuni ashe kin fita, Mairo ma tazo ta tafi kin santa ita ba zata iya jira ba" Lantanar ta fada bayan data karni muqullin daki ta bude mata. Binta ta shiga tana cewa "Eh ai ita da yake ta fiki tunani tana kuma da abinyi a gida shiyasa ba zata zauna ba tunda babu aikin da zatayi" "Kai Hajiya" Lantanar ta fada tana yaqe dan taji zafin maganar Bintan kullum haka take yaba mata su da tana da zuciya yaci ace yanzu ta haqura da aiki a gidan gaba daya. Binta ta shimfide Zakariyya tana miqa tareda wash "Ai yaci ki dena goyashi haka Hajiya kar ku ringa danne na cikin, in fita ta kama ki ringa cewa na turo miki Aisha ta mana tana tayaki da daukarsa" Lantana da bata daddara ba ta sake fada, se kuma akaci sa'a Bintan ta yarda da shawarar tace zata ringa yin hakan. Tana zaune a Falo tana ayyana yanda maganar nan zata tashi Lantana na share share sega Audu kamar an jefoshi ya fado falon, ta miqe da sauri tana tambayarsa lafiya kuwa yace "Babu lafiya, yanzu Suleiman ya dawo daga Bechi yake shaidamun Allah yayiwa Babansu Bara'atu Rasuwa, ki shirya yanzu zamu tafi can dukda dai nasan ba zamu samu jana'iza ba amma gara muje din in yaso ma dawo gobe". Binta taja tsaki bayan data koma ta zauna tana cewa "Shine ka shigo a gigice har kana fadar mun da gaba na zata ma qata asarar ce ta fadawa Dukiyarmu? To Allah ya jiqan musulmi amma babu inda zani da ranar nan fatsar fatsar". Zubaida na bacci bacci ya shiga itama ya shaida mata rasuwar, iyakar abinda ta sani kan Bara'atu tsohuwar matarsa ce ba'a fi watanni biyu bama data san itace uwargidansa ba Binta ba a bakin Mairo mewa Binta Girki ranar ta roqeta ta koya mata yanda akeyin Gero da wake shine tace ai Maman Baba ma tana son Abincin a sannan ta tambayeta wacece ita tace mata Bara'atu uwargidan Audun tayi mamaki kwarai jin har yara biyu ne tsakaninsu dan be taba gaya mata ba data yi masa zancen kuma har yajin kwanaki ya mata saboda tace be kyauta ba dakyar suka shirya bayan yaja mata kashedin babu ruwanta da sabgarsa wadda bata shafeta ba, bata san meya rabashi da Bara'atu ba dan haka karta kuskura ta tsoma kanta a ciki shiyasa kidimewar da yayi yanzun da ya gaya mata rasuwar Baban Bara'atun ta bata mamaki, matar daya cire daga rayuwarsa ita da Yayan da suka haifa tare na menene ze dawo dan ta rasa mahaifi? Haka ta cicciba ta hada abinda zata buqata a yar jaka tana hasaso yanda yan Bechin zasu karbe ta wannan karon, bata sake zuwa ba tun bayan da aka kaita wancan Al'amarin ya faru haka suma A matan Aisha ce kadai tazo babu dadewa tana ciwon Nono Audu yace tazo Kano taga Likita ta kwana hudu a dakin Zubaidan kuma dai lafiya lau babu abinda ya hadasu har suka rabu ta koma. Bata san banda Binta za'ajwe ba seda yaceta fito su tafi, ta kulle qofarta tana tsaye jikin dakin Tsakar gida wanda Abdullahi yake kwana ciki kafin a kaishi makarantar kwana tun daga nan kuma idan anyi hutu Bechi yake tafiya da Audu ya tambayi ba'asi yace babu komai be matsa ba ya qyale shi kuma dai be fasa yi masa komai ba tamkar yana gidansa ze aikawa da Aminu kudin komai nasa ayi masa. "Ba tare da Maman Zakariyya zamuje ba?" Ta tambayeshi jin yace suje, "Badani za'aba uwar azagwai" Binta dake tsaye kan Baranderta ta turo dauri gaba irin wanda Zubaidan takeyi ta fada kome ta tuna kuma se tayi saurin sakin fuska ta matso kusada ita tana cewa "Yauwa kar in manta, idan kun dawo daga Qauyen nan akwai taimakon da zakimun. Wlh in gaya miki qanwar qawatace Ibtila'i ya hauta wani shege ya dirka mata ciki, to kuma ta samu Miji Aure nan da wata biyu wannan abu ya faru shine nace ko zaki taimaka ki kaimu inda kuke zuwa a kwantar muku da ciki a samu asiri ya rufu ayi Auran nan idan yaso intayi wata kamar biyar a tayar dashi ko kinga sahu a likafa babu me cewa wani abu". Sak Zubaidan tayi tana kallonta har ta kai qarshe yanda take doka murmushi kadai ya isa yasa ka gane babu Allah a ranta makirci ne zallah ta hado, waiwayawa tayi ta kalli inda Audu yake tana fatan ace ya rigada ya fita beji wannan maganar da Bintan takeyi ba amma se taga yana tsaye ya zuba mata ido tamkar yanda Bintan take kallonta tana murmushi. "Kinyi shiru baki ce komai ba" Bi ta ta sake fada har tana dafata fuska dauke da murmushin makirci se ta saka hannu ta tureta tana cewa "Bani da lokacin Amsa shirmenki" Binta tayi shewa harda rangada guda tace "Allah nawa Annabi na uwata, yarinya ba kecw bakida lokacin amsani ba nice bani da lokacinki, kuma shirme da kikace a tsakaninmu za'a tantance wadda take shirme kwanannan, kiyiwa Bara'atu gaisuwa injini kinji Allah ya jiqan Babanta" daga haka ta juya tana kada Mazaune tana waqa abinta. Zubaida na tsaye inda take ta kasa motsi har seda Audu yayi mata magana kafin ta shiga daga qafa dakyar har suka fita. Seda suka dauki hanya sosai motar shiru babu me cewa qala kafin ya yanke shirun ta hanyar yi mata maganar data saka qirjinta bugawa dam kamar ze fashe. "Sanda kikace kin zubar da ciki dagaske kike ya fita ko kuwa qaryarku ta yan bariki kikayimun?" A razane ta kalleshi, hankalinsa na kan titi fuskar nan a hade tam kamar ta shanu. Shiru tayi zuciyarta na tsinkewa, takalarta yakeyi da masifa ita kuma bata shiryawa hakan ba bata da kalaman da zata kare kanta dasu a yanzu ta tabbatar matarsa ta rigada tayi masa famfo shiyasa ta tayar da wannan maganar a gabansa qila kuma ta rigada ta fada masa abinda take so ta fada wannan da tayi fami ne ta barbadawa ciwo gishiri. "Ba magana nake miki ba kin mayar dani dan iska kinyi shiru" ya fada cikin masifa harda buga sitiyari, Zubaidan ta zabura saboda tsawar ta shigeta amma a maimakon tayi magana se kawai ta fashe da kuka. To me zata ce masa dan Allah? Kwafa yayi be sake ce mata komai ba har suka isa Bechi, sun tarar da Anyi Jana'izar Babansu Bara'atu, a qofar gidan suka tsaya daman ya fice ya barta a motar ya tafi gurin Maza masu karbar gaisuwa Tilas ta fita ta shige qofar dataga Mata na shige da fice. Bata san kowa ba dan haka ta tsaya tana raba ido, "Ashe tare kuke" taji an fada daga bayanta ta waiwaya ganin Aisha yasa ta saki ajiyar zuciya a qalla taga wanda ta sani. "Muje ciki" ta sake fada mata se tabi bayanta suka ratsa matan dake zaune ta gaishe su tareda yi musu ta'aziyya kafin suka dangana da Rumfar Inna Hajara. Anan taga Bara'atun tana rakube gefe ta sake zama fiyat da ita ga tashin hankalin mutuwar data riskesu ta farat daya idan ka ganta gwanin tausayi. Aisha ce ta gabatarwa da Bara'atu da ita. a matsayin Amaryar Audu, suka sake gaisawa kafin Aishar tace su koma tsakar gida dan yafi iska. Bayan su. Zauna Bara'atu da kanta ta fito ta kai mata ruwa da Kunun Tsamiyar da aka kawo na sadaka tace "Ki dan sha wannan kafin a sauke abinci" "Nagode" Zubaidan ta fada a sanyaye badan zata iya sha ko cin wani abu ba dan jiki da zuciyarta gaba daya batajin dadin da zata iya saka wani abu a bakinta a halin yanzu. Sunyi jugum jugum Aisha tace "Itace matar Yaya Audu ta farko, Makircin Binta ne ya fitar da ita daga gidan ta qulla mata sharrin wai ta kashe mata Jariri ranar suna" Qirji Zubaidan ta dafe tana zare idanu, tuna a inda suke yasa ta saisaita kanta cikin kaduwa tace "Kashe jariri?" "Wlh fa, kuma sharri tayi mata dan wlh ko kiyashi Bara'atu ba zata kashe da gangan ba balle mutum sahun barawo ta taka yaron dama ya rasu shikenan suka liqa mata sharri daga shiga dakin shi kuma Yaya Audu babu binciken komai ya yanke hukunci dalilin mutuwar Auranta kenan shekara Uku yanzu". "Uhm" kawai Zubaida ta iya cewa, wato ashe nata tuggun da take shirin qulla mata me sauqi ne akan na Bara'atun kisan kai fa kuma na rashin Imani ace Jariri ka kashe wannan ai tayi mata tambarin da ba kowanne Namiji ne ze iya dauke kai ya aureta ba wadda ta iya kashe dan Jinjiri babu tausayi ai kisan babban mutum qaramin abu ze zama a gurinta. Haka ta ringa jimanta maganar jikinta ya qarayin sanyi qalau da Al'amarin gida Audu, taga Babangida da Babannan sun girma Masha Allah musamman da suna da garin jiki irin na gidansu se suka tashi kamar yan biyu sedai duk su biyun suna nan a hargitse yaran qauye dai sak to uwarsu bata da nutsuwar zuciya balle ta iya samun damar kulawa dasu yanda ya kamata, Manema uku ta samu bayan rabuwarta da Audu biyu duk ba yan garin su bane amma da sunyi zuwa daya biyu za'a samu wani annamimin da zeje ya soke maganar sedai taji shiru ba zata sake jin duriyarsu ba wannan abin yasa ta shiga damuwa matuqa ga tunanin Audu da soyayyarsa data qi barin zuciyarta sedai ta sani ya mata nisa bama ta yiwa kanta fatan komawa gidansa Addu'arta daya ce a kullum ubangiji ya warware mugun qullin da Binta tayi mata ya wanketa a idon Audu da duk wanda ya yarda da sharrin da aka mata. Se Yamma Aisha da Zubaida suka bar gidan rasuwarz babu motar Audu a waje hakan ya tabbatar musu ya wuce gida dan haka ta rakata can kafin ta wuce gidanta itama dan Magriba ta kawo kai. "Kace badan wannan rasuwar ba qila da sedai kuzo kawo mana Jariri ko Jinjira" Goggo Fadi ta fada sanda Zubaidan ta shiga dakinta gaisheta ta tarar da Audu a ciki. Bece komai ba itama bata amsa ba se kanta data qara yin qasa dashi. "Ya kamata ka ringa qoqartawa Iyalanka suna zuwa gida akai akai cikin dangi, kaga dai Amarya rabonmu da ita tun randa aka kawota kuma kai kana zuwa koda ba ka kwana yaci karinga tahowa dasu a haka za'a saba sosai ai" Goggo Fadin ta sake fada se sannan Audun yace "Za'a gyara in sha Allah, bari naje an fara kiran sallah" ya miqe ya fita Zubaidan ma fita tayi ta dauro Alwala tayi sallah nan dakin Goggo Fadi Saude ta kawo mata tuwo bayan ta sauke ta dan tsakura saboda yunwa ta fara sakadarta tana nan zaune Goggo Fadi na janta da hirarraki duk a takure take ta gaji tana so ta kwanta amma bata san inane masaukinta ba bataga kayanta a dakin Goggo Fadi ba balle tace a nan zata kwana shi kuma tunda ya fita be dawo ba balle ta tambayeshi. Be shigo gidan ba se da goma ta gota lokacin ta gaji ta kwanta a dan gadon Goggo Fadi da take tayi mata tayin tun da taga tana gyangyadi daga zaune amma taqi hawa tana kwanciya kuwa bacci ya kwasheta se ji tayi yana tashinta sukayiwa Goggo Fadin sallama tana biye dashi har bangaren dake gefe wanda aka kaita randa sukazo Bechi tana Amarya. Daki daya ya bude ya shiga tabi bayansa, dakin da aka sauketa ne wancan lokacin se yanzu ta kalleshi da kyau cikin dakin ba zakace a qauye kake ba tamkar Dakunansu na Kano Bango yasha Fenti haka qasan dakin Malale da Kafet ga bandaki a ciki har wayarin din ruwa da akwai. *MAMAN MARYAM ONLINE BUSSINESS* *Ina kuke Mata Yan kwalisa , Ina nufin isassun Mata ,Wai shin Kuna da labarin shahararren company nan namu na GHT wato good healthtreatments* *Wanda yazo muku da fitattu Kuma* *ingantatattun suppliment ,na dukkan matsalolin ku*❓ *Ina maisan tayi kyau,irin na isassun Mata ya fitar Miki da shef dinki tayi Miki gyara in and out ,nemi royal jelly dinmu na company GHT* *Wanda aka yishi da xuma ,kundai San amfanin Zuma basai na fada miku ba , hajiya ta kixo ki Yi gyara domin ki kerewa sa,a kije taro ko baki da ko sisi kiji Ana rangada Miki hajiya , saboda yanda Zaki Kara kwarjini ,kina walwali acikin mutane , magungunan ght anti agen ne suna maida tsohuwa* *yarinya ,yarinya Kuma ta koma jaririya* *Muna da magunguna iri iri* *NA GYARAN JIKI* *NA GOGE NANKARWA* *NA RAGE QIBA* *NA CIRE TUMBI* *NA QARIN HIPS* *NA GIRMAN BREAST* *NA QARA TSAHON GASHI* *NA QARIN NI'IMA WANDA ZAI SAUKAR MIKI DA NI'IMA YA QARA MIKI DADI DA ZAQI A GURIN OGA* *Muna da hadin bita zai zai ,indai kishiyar ki tana Shan magungunan GHT, tohh lallai sunan ki sorry domin kuwa tazarar dake tsakanin ku kamar tazarar sama ne da kasa* *Muna da Wanda zai matseki ciki da waje Andai na yayin dinki uwargida*, *Sannan company mu na GHTBai tsaya anan ba* *Ya kawo muku maganin dukkan matsalolin ku* *INA MASU HAWAN JINI?* *INA MASU CIWON ZUCIYA?* *INA MASU CIWON QODA?* *INA MASU CIWON HANTA?* *INA MASU SICKLER?* *INA MASU HIV?* *INA MASU CANCER?* *INA MASU NEMAN HAIHUWA?* *Tohh Ku matso GHT taxo muku da magungunan matsalolin ku* *Kuma muna da testimonys da yawa ,na wadanda suka gwada suka da ce* *Munanan a KANO KUNTAU* *Kuma muna tura Kaya ko wanne gari cikin aminci da gaskiya , kuma kayan mu muna badashi ne cikin price Mai rahusa ga kyau ga inganci sannan ga Rahusa* *Kutuntube mu ta wannan number 📞08129249549* *📲07011401314* Fita yayi ya barta a dakin, ta shiga bandaki tayi uzurin da zatayi ta fito ta bude jakarta data gani ta canza kaya kafin tabi Lafiyar Katifa bata sake motsawa seda aka fara kiraye kirayen sallah ta farka ta ganta ita kadai Babu Audu a dakin yanayin gurin kwanciya kuma ya tabbatar mata da ita kadai ta kwana kan katifar dan babu shaidar an kwanta daya barin to Ina ya kwana? Data tuna da wani dakin a gurin seta bar zancen a ranta tana jinjina wato lamarin yayi tsamarin da baze kwana daki daya da ita ba kenan ai shikenan. Tayi wanka bayan da tayi sallah ta shirya tsaf abinta be shigo ba seda gari yayi haske lokacin har Saude ta kai mata abin Kari Ruwan shayi a fulas se wainar kwai da qaton Burodi ta fita kawo mata Madara da Bonbita ya shiga dakin yana wani cin magani ta gaishe shi ya amsa a daqile yana gaya mata tayi sauri da wuri zasu tafi. Haka suka kamo hanya bayan sun biya gidan Rasuqar sun sake musu gaisuwa, tana zaune cikin mota tana leqensa suna tsaye da Bara'atu daya saka aka masa magana da ita, bata san me suke cewa ba hankalinta yafi tafiya ga Yaran da suka zagaye shi amma daga nesa kowanne ya tsaya irin suna son zuwa gunsa amma babu shaquwa ko fuskar yin hakan se taji wani iri a ranta, to su kenan ma da aka rabasu da ubansu ta qarfi da yaji inaga ita da Ake shirin sheganta abinda zata haifa ta yanda ma baze samu ko Alfarmar kiran kansa jininsa ba? Kwalla ta ziraro mata tayi saurin dauketa ganin ya nufo motar, taga sanda ya bawa Bara'atun Kudade masu kauri amma ta girgiza kai taqi karba kana taja yaranta suka shige cikin gida da alama wannan abun ya sake tunzurashi dan motar kanta fizgarta yake kamar zasu tashi sama ita dai ta qanqame jikinta har sukaje gida babu wanda yacewa dan uwansa qala. AUDU Tunda suka baro Kano abin duniya ya taru yayi masa yawa haka nan maganganun Binta suka samu matsuguni a zuciyarsa dukda ba kaitsaue tayi magana dashi ba amma se ya ringajin kamar saqo ta bashi, girman Cikin Zubaidan ya jefashi a kokwanton da sam be taba shiga ba se yanzu da Binta ta soko wannan maganar sannan tambayar da yayi mata akan Cikin datace masa ta zubar a baya da shirun datayi ya sake jefashi cikin rudani wannan tasa bayan sun Isa Bechi yabkasa zama har seda ya nemi qarin bayani akan Kwantar da ciki da tayarwa da yaji a zancen Binta. "Falalu ya fara tara da zancen a gurin zaman makoki da suka hadu a maimakon ya bashi amsa se kawai yayi dariya yace me ya hadashi da shirmen Mata a bakinsu yake jin wani Kwantaccen ciki amma shi be yarda da akwai shi ba. Shaidan ya rigada ya samu abinda yake so yayi kane kane a zuciyarsa haka nan ya jefa masa wasi wasi kala kala, sam ya kasa nutsuwa shiyasa daya fita salkar Magriba kai tsaye ya wuce gidan Bilki dukda ba shiri suke a yanzu ba tun bayan abubuwan da suka faru amma da yake buqatarsa ce yau ta tashi se gashi a gidanta. Tasna Yazo Bechi dan tun rana Labari ya isar mata ta bar gidan raauwar babu dadewa su kuma suka shigo daman kuma Audu na shiga Bechi labari ze karade ko ina kafin Alkhairin kyautar sa ya isa gida gida wannan lazim duk zuwa zeyi rabon abinda ya samu wa jama'ar gari musamman a baya zamanin da suke tare da Bara'atu sunfi zuwa garin sosai yanzun yakan jima beje ba amma duk in ya shiga dai zeyi Alkhaiti daidai yanda hali ya bayar. A dakin Bilki ya zauna ya rafka tagumi yana sauraronta bayan da yayi mata tambaya akan gaskiyar ana iya kwantar da ciki tsayin wani lokaci sannan a tayar dashi sanda ake so? "To zancen gaskiya anayi dukda dai ban tabayi ba kuma ban taba ganin wadda taje akayi mata ba amma na samu labarin mutane da yawa da hakan ta faru dasu, kaga babu nisa nan gidan Malam Ado ai kasan Ila Abokin Baballiya ta shima ba'a jima ba anyi irin wannan dambaruwar gidansa yayi Aure matar watanta shida ta haihu. Yar Umarawa ce ya aurota daman dai tun lokacin bikin aketa surutai akan yarinyar kamar magana ta dakko shine iyayenta suka tada auranta babu shiri, hatta dakin da ya sakata fa ubanta ne ya bashi kudi ya qarasa ginashi saboda yace be shirya Aure ba basu karbi Lefe ba kuma karka so kaga uban kayan garar da aka hadota dashi bana tsammacin sun qare har yanzu. To a yanda Zainabu dai take cemun (kishiyarta) kasan Qanwarsa ce yayan Maza suke wai Amaryar watanta biyar sega Ciki ya fito qato kamar zata haihu gobe, kuma sunce sudai lokaci daya sukaga wannan abun mamaki da fara laulayinta da girman cikin befi watanni ba tofa ciki nayin qato daman akwai qanwarta da aka hadota da ita ta shirya ta tafi can garinsu satinta daya sega Babarta tazo ganinta wai ya akayi ya akayi ta tattarata suka tafi gida wai bata da lafiya za'a nema mata magani ba'a rufa wata ba akace ta haihu, su Zainabu sunje sun gano yar ance musu bakwaini ce to tace Aradun Allah wannan ya idan ka kalli idonta ma zakace ta shekara a ciki kuma qatuwa da ita tabarakallah in taqaita maka zance dai anyi wata uku da haihuwar yanzu Auran yake da wata tara tana can gidansu har yanzu bata dawo ba". Wannan labari na Bilki ya sake bashi tabbacin maganar da Binta ta fada ana haka kenan, amma wace hujja ze kama ta cewar Zubaida ta shigo gidansa da ciki? Sannan wane tabbaci yake dashi akan kwantar da ciki tayi ta shigo masa dashi gida? Dole ya tsananta bincike ya gano koma menene amma yanda al'amarin ya kasance lokaci daya ciki yayita girma kamar na Aljanu ya bashi mamaki shi kansa. Be gayawa Bilki dalilin tambayar ba duk nacin data yi masa ya tattara ya tafi amma ya kasa komaqa cikin gidan can wani guri ya samu ya zauna yana ta lissafin ya zeyi idan ta tabbata da ciki Zubaida ta shigo masa ba nasa bane ba? Seda yaga dare ya farayi ya koma gidan ya rigada ya cusawa ransa wani abu na daban shi yasa ya kasa koda kwana daki daya da ita ya bude dakin da Binta take sauka ya kwana a ciki. Har mamakin kansa ya ringayi yanda ko sau daya be taba tunano rayuwarta ta baya yaji ya qyamaceta ba ko ya kasa mu'amalantarta amma yanzu yaji ta fita a ransa akan abinda be gama tabbatarwa ba. Haka suka dawo Kano nan kuma zamansu ya dauki sabon zama ya fita a sabgarta tsakaninsa da ita ya ajiye mata kudin cefane idan ya kwana a dakinta kenan in tayi abinci bayaci gaba daya ya birkice saboda rashin nutsuwa daya sakawa ransa. A bangaren Zubaida kuwa gaba daya ta maida hankalinta gurin Ibada ne da kuma kula da lafiyarta data abinda yake cikinta tayi matuqar qoqari gurin ganinbata bari damuwar Audu tayi tasiri a ranta ba haka duk iskancin da Binta zata mata bata daga kai ta kalleta yanda kuma be sake mata tambayar da yayi mata randa sukaje Bechi be itama bata daga maganar ba a haka suka kwashi tsayin sati biyu cikin wannan hali. Da safiyar ranar Asabar tana zaune daga bakin qofarta ta cire saiqoyin data jiqa ta shanya su kafin ta gama shanye ruwan daya jiqun seta maidasu, tana zaune kan Tabarmar data shimfida da yar Radionta a gefe tana sauraro ita kadaice a gidan tun safe Audu da Binta suka fita kamar yanda taji a bakin Bintan tana bawa qawarta da taje gidan labari Audun ya biya mata Aikin Hajji fitar da sukayin tana kyautata zaton duk cikin shirye shiryen tafiyar ne dan abin ya matso a kwanakin kusan kullum se sun fita. Taja Qaton kofin robar dake cike da ruwan magani ta kurba ta ajiye ta saka hannu biyu tana shafa cikinta da taga kamar yayi qasa sosai kuma ya dan rage girma, sam bata ji shigowa ko sallamarasu ba saboda ta nitsa cikin tunani se maganar Binta taji akanta tana cewa "Ahaf, ka gani ba? Wasu jiqe jiqen aka qara kawo mata bana gaya maka wannan tsohuwar Matar Babanta ce take mata safara ba kullum tana tafe gidan nan yau ta kawo wannan gobe ta kawo wancan gashi nan kuwa cikin ya fara komawa za'a sake danne shi qila ace mana anyi bari se wata shekarar a haife shi tunda mun ramfo wannan wayon ko?" Bintan tayi maganar tana zuba mata ido fuska a washe irin duniya ta mata dadi babu abinda yake damunta duk da cewar bata tsammaci za'aja lokaci ba wannan Bam din data dana be tashi ba amma kamar yanda Turai ta gaya mata tabi komai a hankali dai kar suyi gaggawa to tana zuba ido taga yanda wasar zata kaya. Audu bece komai ba ya wuce samansa, jiki a sanyaye Zubaida ta miqe ta shiga tattara abubuwanta Binta natsaye tana zubda mata habaici, "Ke kin dauka zaki kawo mana shege wato kici bulus bamu gane ba? To qaryarki tasha qarya wlh tun wuri ma ki nemo farkan daya dibga miki ciki ki nana masa abinsa badai a gidan nanba kar muke kallonki" "Wlh Binta ki tsoraci gamuwarki da Allah" Zubaidan ta fada hawaye na sakko mata, Binta tayi shewa tace "Nan da sati i yanzu ina gaban Ka'aba yarinya in shafata in roqi Allah yayi gaggawar tona miki asiri ki tattara ya naki ki barmin gida gayyar tsiya gayyar na'ayya" "Allah baya bacci" Zubaidan ta sake fada daga haka ta shige dakinta. Tana zaune Audu ya shiga ya zauna akan Kujera yana fuskantar ta, irin zaman da yayi yass gabanta ya shiga faduwa, cikin kaushin murya yace "Zan sake tambayarki bana buqatar qarya ko wani alaye ki fada mun gaskiyar magana Cikin da kikace kin zubar dagaske kike ko kuwa kwantar dashi kikayi?" Kuka ta fashe dashi ba tareda ta sgirya ba tace "Yanzu ka dauki maganar da take fada dagaske kenan? A ina ka taba ganin an kwantar da ciki? Idan ma anayi tayaya ciki ze kwanta tsayin sama da shekara daya a Jikina ace baka lura ba wai me yasa akai baka amfani da kwakwalwarka se abinda matarka ta kitsa maka ba tareda bincike ba ka hau kai kawai ka zauna?" "Nine bana amfani da kwakwalwata?" Ya fada yana nuna kansa, a duk maganganun babu abinda ya tsinta se wannan, ta miqe cikin kuka tace "Kwarai, kwakwalwarka hotoce Audu domin bata aiki se abinda wani ya kitsa maka dashi kake tunani. Ya za'ayi ka kasa tantance gaskiya da qarya? Se yaushe idonka ze bude ka gane tuggu da makircin da matarka take shirayawa a cikin gidan nan? Ta laqawa uwargidanka sharrin Kisa shine zata shegantaka maka Da ko Ya ka hau kai ka zauna? To wlh na gaji bazan iya wannan rayuwar ba, ba zan zauna da mutumin da besan daidai ko abinda ya kamata yayi a matsayinsa na Namiji ba, bazan cigaba da zama ace Kishiya ita zata tsara mun irin zaman quncin da zanyi a cikin gidan aurena ba. Ka fito fili ka fadi abinda yake ranka ka fadi cewar kana kokwanton cikin jikina karka sake sakayawa ko ka titsiyeni da tambayar abinda ya shafi rayuwata ta baya, ka fadi kai tsaye Matarka ta kitsa maka cewar cikin jikina ba naka bane kuma ka hau ka zauna babu abinda zance maka kuma banida amsar da zan baka a yanzu se dai nace maka mu jira lokaci, ubangijin daya wanzar da samuqar cikin ze qarware duk wani qulli da ake qoqarin laqaba masa amma kafin nan ka sani bazan iya cigaba da zama da kai ha Audu gidanmu zan tafi zanje na qarasa rainon cikina a can har Allah ya saukeni lafiya abinda na haifa ya raba gardamar zargin da kake neman laqabamun" tana gama fadar haka ta shige daki tana Kuka ta hau hada kaya. Laqwas yayi akan Kujera kamar kazar dataji ruwan zafi, ya yunqura ze miqe kenan Burum Binta ta fado dakin tana cewa "Babu shakka daman ance tabarmar kunya da hauka ake nadeta kana zaune tayi maka wasan kwaikwayo da salonso na Tsofaffin kikali ko? To ai idan kina da gaskiya fitowa zakiyi ki kare kanki baqai ki hau koke koke kina hada kaya ba kaga magana ta tabba da ciki aka shomigo mana so take ta tafi se ta koma inda za'a rufe maka baki ruf ka kasa cewa komai koda yake yanzun ma naga kamar bakin naka a rufe yake ai" "Banida lokacinki ki kuma jirayi sakamakonki komai nisan tsahon zamani" Zubaida data fito da jaka ta fada tana gotata. Tana fita Audu da Bintan suka rufa mata baya Binta na shewa kamar sabon shigan hauka tana tafa hannu. "Subhanallahi me yake faruwa haka" suka tsinkayi muryar Yakubu da shigarsa gidan kenan yana fada, Zubaidan taci burki kuka yana sake kwace mata Binta ta gyara tsayuwa murya a sama tace "Me fa ya faru Yaya Yakubu? Abin kunya tayi asirinta ya tonu kuma shine take mana qaramin hauka". Zuciyar Yakubu ta tsinke ya tafi wani tunani na daban seya kalli Audu dake nan tsaye qato dashi kamar wanda kwakwalwarsa ta bata se zare ido yake yace "Me ya faru? Ban fahimci abinda take cewa ba?" "In maka gwari gwari Yaya Yakubu, ciki. Shege tayo take neman laqawa qaninka ta gurbata muku Zuri'a" Binta ta sakeyin caraf ta amshe tamkar sunanta ya koma Audu. "Hasbunallahu wani'imal wakeel, Audu dagaske ne abinda take fada?" Yakubu ya fada yana ja da baya dan ya samu balance sosai jin wannan babbar magana. https://chat.whatsapp.com/I8xKHGurk7EBf5ZqQdxHKG *MATAR MUTUM* *NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER* *FIKRA WRITERS ASSOCIATION* *LITTAFIN KUDI NE* *PAY 500 A ASUSUN* *7061838488* *OPAY DIGITAL SERVICES* *MARYAM FAROUK* OR *0709290797* *ACCESS BANK* *SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488* *IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705* *Kuyi following dina a Arewabooks @Maryamfarouk01 inda zaku karanta wannan littafin tareda sauran littattafaina* *NAGODE* *PAGE 22* Wuta ta daukewa Yakubu sanda Binta ta gama rattaba masa abinda ya faru dan ita ta zama bakin Audu yau. Ya ringa kallon Audun yana jira yaji ya qaryata ko ya fadi akasin abinda Bintan ta fada amma yaga yadauke kai gefe yana wani cin magani se ya maida kallonsa kan Zubaida dake irin kukan nan da meyinsa ya gaji dayi, tausayinta ya rufeshi gefe daya takaici da tsanat Bi ta me girma tareda qyamatar Hali irin na dan dan uwansa suka kamashi. "Ku Fita ki bamu guri" ya fadawa Binta da Zubaida. Zubaida ta miqe ya kalleta yace "Kar kije ko ina ki koma dakinki" ta juya ta fita Binta ko ta gyara zama, cikin kaushin murya yace mata "Zaki fita ko sena kwasa miki mari a nan gurin?" shidin ba ma'abocin zafi bane amma bashida wasa musamman a gurinta sam basa ga maciji yanda kuma ya hade gida ya tabbatar mata ze iya kwasa mata mari idan bata tashi ba kamar yanda ya bara umarni dan haka ta miqe tana qunquni. "Nayi maka uzuri domin bayan Kaidin Mace Jahilci da duhun kai suna dawainiya dakai Audu lokaci yayi daya kamata ace ka koma Makaranta Both Islamiyya da Boko" Yakubun ya fada bayan fitar Binta wadda ta labe a bakin qofa ta kasa kunne tana jiran taji me zasu tattauna. A zabure Audu ya kalle shi yace "Ni kake kira jahili?" "Qasurgumi ma kuwa" Yakubun ya bashi amsa idonsa fes a kansa kafin yaci gaba da cewa "Banda kai wawane wanda bashida tunanin kansa se abinda aka kitsa masa kuma Jahilci yana dawainiya da kai ta yaya Mace zata zo maka da irin wannan maganar shirme wadda ko yaro qarami aka gayawa dariya zeyi amma ka hau kai ka zauna harka sheganta cikinka da kanka wane kalar wawanci ne yake damunka Audu? Binta ce ta auro maka Zubaida da zatayi maka lissafin cikinta ka yarda ko kuwa? Watanta nawa yau a gidanka? A lissafin watan sama auranku ya shiga wata na goma ma kaga kenan cikinta har yazarce watannin da Da yakeyi kafin a haife shi kuma da zata ce maka Da ciki ta shigo kwantar dashi tayi kai mahaukacine da ka kwashe tsayin lokaci tare da Mace da ciki amma baka gane ba ko kuwa akanta ka fara Aure balle kace baka san yanda alamar ciki take ba? Wato ita da yan uwanta sun laqabawa Bara'atu sharrin kisan kai sunci banza shine yanzu ta sake fitowa da wannan sigar kai kuma ga Raqumi se yanda aka juya akalarka ta fada ka hau ka zauna akai..." "To ai ba qarya Binta ta fada ba hakan zata yiwu tunda ita Zubaidan da bakinta ta gaya mun tayi ciki tun kafin na dawo da ita gidansu kuma ni ban tabbatar da tace ta zubar dagaske ne ko qarya takeyi ba. Sannan ba Binta kadai ba har Bilki seda na tambaya ta tabbatar mun ana iya kwantar da ciki yafi shekara sannan a tayar dashi idan ba haka ba tayaya za'ayi ace ciki yayi wannan girman a wata daya" Audun ya fada a fusace zuciyarsa na tafarfasa na yanda Yakubun ya zageshi ya kirashi Jahili. A fusace shima Yakubun yace "Ta yanda Allah ya rangwanta maka hankali da tunani kake kasa banbance tsakanin daidai da rashi Sa ta haka yayi ikonsa ya girmar da ciki a wata daya, Kai wane irin mutum ne Audu? Anya kwakwalwarka a daidai aka dasa maka ita kuwa?" "Karka sake zagina kuma karka sake dangantani da hauka" Ya fada yana miqewa tsaye, "Idan na kuma zaginka zaka rama ne? Na fada kai wawane shashasha wanda bashida tunanin kansa se abinda waccen yar iskar Yarinyar da idan tayi wasa ba zataga annabi ba ta shirya maka. Ka auro shaidaniyar Mace tana neman ta Halakar da kai, to bari kaji ka farka tun kana da sauran lokaci idan ba haka ba kana ji kana gani zaka tafi lahira yanda haqqi ze kaita wuta haka zata kama hannunka ku shiga tare...." "Na shiga uku ni kake kake cewa yar wuta Yaya Yakubu?" Binta ta fado musu hannu aka tana kwakwazo, cikin daga murya Yakubun yace "Ke munafuka ce, munafuki kuma Allah da manzonsa sun rigada sun fada mana makomarsa idan har ya mutu be tuba ba. Cikin Halayan manyan munafukai wannene bakiyi? Qarya, Ha'inci, Zalunci, Annamimanci sannan ga tulin haqqin mutane da kika dauka dana Aure da kika lalata kina tsammatar idan baki nemi yafiyar wadanda kika zalunta ba zaki wanye lafiya da duniya ne? To dakai da ita kar ku fasa duk abinda kukeyi duniya ce gaku gata nan kuma kanku kuke rusawa, Zubaida kuma babu infa zataje a gidan nan zata haife abinda yake cikinta tunda kai baka san shari'a ba bari na gaya maka koda ciki ta shigo gidanka muddin ta yi watanni shida kafin ta haihu Shari'a ta baka Dan koda kana kokwanton ba naka bane balle kuma wane tabbaci zamu samu idan ma da cikin Tazo ace ba naka bane tunda a yawon tambadanci daman kuka hadu? Baka ga komai bama tukunna Abdulwahab kabi duniya a sannu idan ba haka ba ranar kuka na tafe" yana gama fadar haka ya fice daga falon. Seda Binta ta tabbatar da ya sauka qasa kafin ta kalli Audu tace "Lallai wannan shi ake kira ga Mari ga tsinka jaka, yanzu shi Yaya Yakubu saboda qin Allah shine ze ringa fadar maganganun nan saboda ba shi ake shirin liqawa shege ba? Ni anya kuwa cikinku daya da Yaya Yakubu nan?" "Karki kuskura ki zagarmun Dan uwa babu ruwanki duk abinda ya fada a kaina dan ya isa ne" Audun ya dakatar da ita cikin kaushi idanunsa sun kada sunyi jajir saboda bacin rai, ta sunkuyar da kai irin na shahararrun Makirai tace "Allah ya baka haquri ai ba wani abu nale nufi ba kawai dai gani nayi kamata yayi ace ya tayaka qyamatar wannan abin ba wai ya goyi bayan a cuceka ba amma kayi haquri idan ba bata maka rai" sum sum ta fice daga dakin itama zuciya fari qal dan tasan ko iya tijarar da Yakubu yayi masa dalilin Zubaida ta isa ta qara tunzurashi tunda shi mutum ne me Izza da tsananin son girma. Bayan fitar Yakubu daga Bangaren Audu dakin Zubaida ya nufa, tana zaune bakin qofa tayi tagumi bata ko bude ba balle ta shiga cikin ta zauna kamar yanda ya ce mata ganinsa yasa ta miqe tsaye a yanayi na bacin ran da yake ciki ya ce mata "Bude qofar ina son magana dake" Ta bude suka shiga ya zauna akan kujera ita kuma ta zauna a qasa sukayi shiru na dan wani lokacin kafin ya nisa yace "Ina so ki gaya mun tsakaninki da Allah shin da akwai wani abu da kika aikata da har ya sakawa Audu kokonton cikin jikinki a ransa" Tayi raurau tana shirin fashewa da kuka, abin ya hade mata biyu ga damuwa ga yanayi na ciki Yakubun yayi saurin cewa "Ki bar koke koken nan haka kodan lafiyar abinda yake cikin ki kiyi mun magana kawai" "Allah shine shaidata babu abinda nayi wanda har ze cefa kokontona a zuciyar Audu. Haduwata da shi zuwa maidoni gida da yayi gaba daya ya faru a dan taqin lokaci shi shaidane akan cewar tunda na dawo gidan mu nayi tuba na gaske babu inda nake zuwa babu wanda yake zuwana wata magana bata qara hadani da Namiji ba idan ka cire mahaifina she shi Audun ballantana har wani mugun Al'amari ya faru har aka daura mana aure na tare a gidansa, kuma a cikin gidan nan ma nayi Al'ada balle yace da ciki na shigo kuma har sanda cikin ya bayyana duk be nuna wata damuwa akai ba seda Matarsa ta dawo daga gidansu sannan abubuwan suka canza" "Ita ta kitsa maganar kenan, Binta! Binta! Wannan yarinya anyi shaidaniya amma babu komai karki saka damuwar komai a ranki ki kyalesu daga shi har itan kici gaba da kula da kanki da abinda yake cikinki. Idan kinji gidan ya miki qunci ki taho gidanmu tare mukazo da Balaraba kuma zata jima a nan dan zan tafi na barsu se na dawo sallah sannan zamu koma baki daya sannan dan Allah maganar nan ta tsaya ikar cikin gidan nan karki gayawa kowa in sha Allahu komai ze warware kansa kinji" Yakubu ya fada mata cikin lallashi. Ta share kwalla tace "Shikenan zan zauna kamar yanda kace zan kuma cigaba da roqon Allah daya zabamun mafi Alkhairi, tabbas nayi dana sanin Auran Audu saboda bansan haka yake ba. Ban taba tsammanin bayan tsamoni da yayi daga rayuwata ta baya ba kuma zeyi amfani da hakan ya rusamun rayuwar dana ke qoqarin ginawa a gaba. Yanzu idan yaqi karbar dan da zan haifa ya zanyi? Da wane ido duniya zata kalleni?" "Karki sake fadar haka babu abinda ze faru da kuma halastacce da ne da kansa ze amshe shi ba tare da wani ya tilasta masa ba, kedai Allah ya sauke ki lafiya kawai kinji kiyi haquri kuma kici gaba da Addu'a" daga haka yayi mata sallama ya tafi ta maida jakarta daki amma bata bude ta ba domin har zuciyarta bata aminta zata iya cigaba da zama da Audu ba. Bata shiryi qare rayuwarta cikin qunci da baqin cikin Miji da kishiya ba. Ta sani daman dole zata riski qalubale masu tarin yawa a rayuwarta amma bata tsammaci ta haka zasu bullo mata ba. Shiru shiru ta tsammaci Audun ze shiga ya mata masifa amma har wayewar gari bataji duriyarsa ba haka suka kwana biyu ko qofar dakinta be leqa ba se a kwana na uku da dare tana zaune ya shiga ya tsaya daga bakin qofa ya miqa mata takadda fara a linkife fuska babu Annuri ta karba ta bude bata iya karatun boko ba dan haka ta mayar ta rufe ta ajiye a gefenta ba tareda ta tankashi ba. "Baki ce komai ba, ko bakiga abinda yake rubuce a ciki bane" ya fada cikin murya me kauri, ta daga kai ta kalleshi irin kallon nan na daidai nake da lokacinka kafin tace "Ka rubuto mun da Ajami idan kana so na gane abinda yake ciki har na baka amsa". Yaja tsaki ya koma inda ya fito. Tun randa Yakubun yazo yake auna daya da biyu akan yuwuwar ya amince da cikin jikinta amma ya kasa, Shaidan ya rigada ya yi kane kane a zuciyarsa yana raya masa abubuwa kala kala ga qaramar shaidaniyar dake nan gefensa tana qara ingizashi, duk yanda yaso daya daure yayi mata uzuri ya kasa musamman idan ya tuna dalilinta Yakubu ya yaba masa baqaqen maganganu ya kirashi jahili se yaji babu abinda zeyi ya huce irin ya saketa kawai hakan ko yayi ya rubuta mata saki har biyu a takarda ya linke ko Binta bata san da ya rubuta sakin ba se da kuma ya bata sannan yaji cewar yayi wauta data bude yaga babu damuwa ko kidima a fuskarta. Tuna masa da tayi bata iya karatu ba ya sanyaya masa zuciya kenan bata san me takaddar ta qunsaa ba da wannan sanyin ya juya ya tafi yana ayyana ze dawo ya dauke takardarsa kawai ya fasa. Safiya nayi ta shirya ranar Asabar baya fita da wuri kuma da yake yanayin sanyi ya fara kankama kowa na daki yayi luqui a ciki. Ta dauki jakar kayanta da takardar daya bata ta kama hanya, tsakaninsu da gidan Yakubu babu wata tazara me nisa dan dayan tsallaken Titin Audun ya maida masa da filin sa daya karba yayi madaidaicin gida. Ta zabi da taje gidan Yakubu ne saboda ko babu komai shidin ya jibanci lamarinta sannan tana tsoron yanda Mahaifinta ze karbi wannan Al'amarin idan taje tana buqatar wanda zeyi masa bayanin da ze sauqaqa masa tashin hankalin da komawarta gida da cikin da ubansa yake kokonto ze jefashi a ciki. Balaraba na tsakar gida tana kauda kayan wasan yara da bata samu ta kwashe jiya da suka gama wasan ba taji ana qwanqwasa Get ta bude ganin Zubaidan ya bata mamaki sedai labarin da Yakubu ya bata na abinda ke faruwa a gidan Audun ya kauda mamakin nata ta matsa mata ta shigo tana mata sannu kafin ta karbi jakar hannunta. Bayan sun nutsu a falo, ta kawo mata Ruwan shayi da su madara da burodi tace "Bari na soya dankali, bari nayi da se sun tashi a bacci tukunna" "Ki barshi wannan dinma ya isa" Zubaidan ta fada a sanyaye amma Balaraba ta wuce kitchen tana ce mata yanzu zata gama. Daidai wanda zataci ta soyo mata da kwai ta kawo, ta kalli kayan shayin na nan yanda ta ajiye su tace "Na dauka kin hada shayin ya sarara kafin ma gama? To bari na hada miki" "Baqi mukayi ne?" Suka jiyo muryar Yakubu dake fitowa daga daki yana tambaya. Balaraba ta amsa da cewar "Baquwa dai" ya qaraso ciki yana kallon Zubaidan sam beyi mamakin ganinta ba domin yasan halin taurin da kafiya irin na dan uwansa. Yayi mamakin da har aka kwana hudu ma sannan ya ganta a gidan nasa. *MAMAN MARYAM ONLINE BUSSINESS* *Ina kuke Mata Yan kwalisa , Ina nufin isassun Mata ,Wai shin Kuna da labarin shahararren company nan namu na GHT wato good healthtreatments* *Wanda yazo muku da fitattu Kuma* *ingantatattun suppliment ,na dukkan matsalolin ku*❓ *Ina maisan tayi kyau,irin na isassun Mata ya fitar Miki da shef dinki tayi Miki gyara in and out ,nemi royal jelly dinmu na company GHT* *Wanda aka yishi da xuma ,kundai San amfanin Zuma basai na fada miku ba , hajiya ta kixo ki Yi gyara domin ki kerewa sa,a kije taro ko baki da ko sisi kiji Ana rangada Miki hajiya , saboda yanda Zaki Kara kwarjini ,kina walwali acikin mutane , magungunan ght anti agen ne suna maida tsohuwa* *yarinya ,yarinya Kuma ta koma jaririya* *Muna da magunguna iri iri* *NA GYARAN JIKI* *NA GOGE NANKARWA* *NA RAGE QIBA* *NA CIRE TUMBI* *NA QARIN HIPS* *NA GIRMAN BREAST* *NA QARA TSAHON GASHI* *NA QARIN NI'IMA WANDA ZAI SAUKAR MIKI DA NI'IMA YA QARA MIKI DADI DA ZAQI A GURIN OGA* *Muna da hadin bita zai zai ,indai kishiyar ki tana Shan magungunan GHT, tohh lallai sunan ki sorry domin kuwa tazarar dake tsakanin ku kamar tazarar sama ne da kasa* *Muna da Wanda zai matseki ciki da waje Andai na yayin dinki uwargida*, *Sannan company mu na GHTBai tsaya anan ba* *Ya kawo muku maganin dukkan matsalolin ku* *INA MASU HAWAN JINI?* *INA MASU CIWON ZUCIYA?* *INA MASU CIWON QODA?* *INA MASU CIWON HANTA?* *INA MASU SICKLER?* *INA MASU HIV?* *INA MASU CANCER?* *INA MASU NEMAN HAIHUWA?* *Tohh Ku matso GHT taxo muku da magungunan matsalolin ku* *Kuma muna da testimonys da yawa ,na wadanda suka gwada suka da ce* *Munanan a KANO KUNTAU* *Kuma muna tura Kaya ko wanne gari cikin aminci da gaskiya , kuma kayan mu muna badashi ne cikin price Mai rahusa ga kyau ga inganci sannan ga Rahusa* *Kutuntube mu ta wannan number 📞08129249549* *📲07011401314* Seda suka gaisa kafin ta zaro takardar da Audu ya bata ta miqa masa ba tareda tace komai ba, ya bude ya karanta yayi shiru kamar ruwa ya cinye shi kafin ya ninketa yana sauke ajiyar zuciya ya miqe tsaye. "Ki gyara mata dakinki seta zauna ciki kafin muga abinda Allah zeyi" ya fadawa Balaraba ya shige ciki. Balaraban ta miqe a sanyaye tabi bayansa ita kuwa Zubaida Fulas taja ta shiga hada shayi daidai wanda ze isheta ta tabbata dai saki ne a cikin takardar, ita kuma a kullum ta tashi Addu'a bata mantawa da neman zabin Allah a dukkan lamuran rayuwarta dan haka duk abinda ya sameta zata karbeshi da kyakykyawan Ikilasi. A dakin Balaraba tayi masauki tana ta jaddada mata ta saki jikinta tamkar tana gida. Bayan da su Dada da qannenta biyu suka tashi daga bacci su suka ringa debe mata kewa harta manta da damuwar data kawota gidansu ta ringa jin zumudin itama dan cikinta ya fito duniya ta tabbatar koshi ya isa ya ringa bata nishadi yana debe mata kewa. Ta tuna sanda tayi cikin da bayan zubar dashi Audu ya maidota gida a lokacin taso ta bar cikin ta haifeshi saboda ta shirya barin rayuwar Bariki. Ta so ta haife dan ta raineshi da yaqinin wannan abin ya saka ta samu rangwame a gurin ubangiji na daga tarin zunuban data dibarwa kanta sedai daga baya tunanin irin rayuwar da Da ko yar da zata haifa da qalubalen da zasu fuskanta yasa ta kasa idar da qudurinta. Sanda wannan cikin ya bayyanar mata tayi murna kwarai musamman dataga irin tarin murna da Zumudin da Audun ya ringayi shima ta ringa hasaso yanda zasu raini abinda zata haifa tare ashe duk mafarki takeyi zanen qaddararta daban abinda take tsarawa a zuciyarta daban. Bayan fitar Yakubu har ya dauki niyyar zuwa gidan Audu se kuma wani tunani yasa ya fasa hakan, a karo na biyu kenan daya sake yanke danyan hukuncin da yake ganin hakan daidai ne a rayuwarsa. A bangaren Audu seda hantsi ya daga kafin ya shirya ya fito ya nufin dakin Zubaida dan ya karbo takardar jiya. Ya tura qofar dake a bude ta sakayata yana sallama ciki ciki shiru babu motsi Tv da Radio da take yawan kunnawa duk a kashe dan haka ya dauka bacci takeyi seya wuce uwar daki nan ma qwalam bata nan. Tsaf ya bincike ko ina be ganta ba kuma bega takardar ba, yanayin dakin da be nuna alamar an dauki wani abu ko an hada kaya ba yasa yayi tunanin ko maqota ta leqa amma wannan ba halinta bane musamman da duk maqotan yan fadar Binta ne dukda haka ya qaddara wani gurin ta leqa seya koma daki da niyyar kafin ya gama shiryawa ta dawo. Binta ta kawo masa abin kari yau din jinta take kamar wadda akawa Bishara da Aljanna. Lantana ce tayi mata albishir din taga Zubaida a hanya da jaka sanda take tahowa ta gaji kenan ta tafi ba kuma zata dawo ba. Tana so ta zungureshi da maganar taji ko ya sani amma dai tayi shiru harya karya ya fito ta rakoshi ta ringa dariya qasa qasa ganin ya doshi dakin Zubaidan yana kwazara mata kira nan ma shiru bata amsa ba. "Wai ina wannan yarinyar ta tafi?" Ya jefawa Binta tambayar ta watsa hannu tace "Yo ka bani ajiyarta ne da zan san inda zataje?" "Shikenan sena dawo" ya fada daga nan ya fice yana mamakin ina zataje dan sam be kawo gida ta tafi ba tunda ai bata san abinda takardar daya bata ta qunsa ba, haka ya dawo gida da yaqinin ze tarar da ita amma wayam bata nan, ya diririce, ta tabbata gidansu ta tafi kenan amma me yasa zata tafi to? Ya jefawa kansa tambayar rainin wayo. Bayan Isha ya shirya tsaf ya cewa Binta zeje wata unguwa, gidansu Zubaidan ya tafi zuciyarsa ta ringa tuhumarsa me ze kaishi gidan amma hakan nan ya zungura kai yaje. Malam Hassan ya rasa ina ze sakashi saboda murna bayan sun gaisa ya tambayeshi Iyali yace "Dazun Babarsu take cewa gobe In Allah ya kaimu zata leqa ta ganota kuwa jiki yayi nauyi har tana cewa ko zata dakkota tazo gida tunda haka akeyi a Al'ada haihuwar fari" Cikinsa ya bada wani sauti quuuu, bata zo nan ba kenan? To ina yarinyar nan ta tafi kardai fa ta hefashi a masifa in duniya ta sake shiga ai da seta bari seta zo gidansu ta gayawa Mahaifinta komai sannan seta tafi amma yanzun ta ina ze fara yi masa bayanin shima nemanta yazo? "Aa bafa abin dole bane idan baka so ta dawo gidan se tayi zamanta dan naga fuskarka ta canza daman matane da Al'ada kasansu basa wasa da ita" Mala Hassan ya katse masa tunani a zatonsa zancen dawowarta gida ne ya canza fuskar Audun besan Al'amarin yafi gaban haka ba. Tilas ya masa sallama a gurguje ya taho bayan ya ajiye masa na goro. A gida ma rkicewa Binta yayi da tambayar ina zasu nemo Zubaida ina ta tafi? "Ya wuce ta koma inda ta fito ne, wai kai meye ma naka na damuwa ina ka saketa duk ma inda zataje taje mana kana da matsala da ita ne?" Ta fada cikin jin haushin yanda yake ta safa da marwa cikin damuwa. Washe gari da farar safiya ya tafi gidan Yakubu ya ringa buga musu qofa kamar za'a tashi duniya Yakubun ya fito yana ganin shine ya shiga surfa masa fada shima yana tambayar ba'asin wannan bugu kamar ya masa sata. Daya masa bayanin abinda ya kawoshi qiris ya rage Yakubun yayi dariya amma ya kanne a ransa yayiwa Allah tasbihi wato tun ba'aje ko ina ba aiko ze gane kuskurensa domin baze fada masa tana gidan ba. "Ni meye nawa a ciki yanzu Audu? Kashedi nawa kamun akan na fita daga sabgar gidanka? Ashe da nace kayi haquri ka bar maganar nan baka daddara ba to ka saketa ta bar maka gida meye kuma abin damuwa a ciki ko daman ka dauka zata zauna ne kuci gaba da ci mata mutunchi kuna aibatata kaida matarka?" Yakubun ya fada yana tsareshi da ido. Audu yaja tsaki yace "Ni bance ta zauna ba amma data tashi tafiya ai seta tafi gidansu ko amma yanU naje jiya bata can yanzu me take so na gayawa mahaifinta idan suka zo ganinta basu sameta ba?" "Se ka gaya musu ka saketa ita kuma tana tsoron ta tayarwa da mahaifinta hankali idan ta koma gida shine ta sake shiga duniya, ni dana san wannan shirmen ne ya kawoka wlh bazan bude qofata ba haka nan ina bacci na me dadi ka daga mun hankali da bugu. Ka tafi ka nemo yarinyar mutane dai kafin iyayenta su farga, kaga daman ba'a jima nayi wani case Mata ta bata Iyayenta sukace Mijin ne ya siyar da ita yayi kudin jini AAllah ya tsareka kaima kar suce kayi kudin jinin da ita daman an fiyi da masu ciki" yana gama fada masa hakan ya maida qofarsa ya rufe ya bar Audu cikin tashin hankalin daya ninka na farko akan maganar da yayi ta karshe. Daman a Bechi ana rade radin qungiyar Asiri ya shiga yayi kudi farat daya da yawa sun qaryata cewar wai sirikinsa kuma ubangidansa ne ya buda masa yake samun kudi haka? Su kance shi din har nawa ya mallka da yake bawa Audun kudi haka? Zancen da akeyi yanzu rabi da kwatan Gonaki da filayen da suke a Bechi mallakinsa ne saboda duk wanda ya daga fili ko gona ze siyar da an tallata masa ze siya a farashi me daraja kuma shiyasa wasu ma haka nan suke siyar masa suje wani gurin su sake siya ragowar kudinsu susha shagali yanzu idan wannan magana taje Bechi ace matarsa ta bata da tsohon ciki la shakka cewa zasuyi yayi tsafi da ita kawai. https://chat.whatsapp.com/I8xKHGurk7EBf5ZqQdxHKG *MATAR MUTUM* *NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER* *FIKRA WRITERS ASSOCIATION* *LITTAFIN KUDI NE* *PAY 500 A ASUSUN* *7061838488* *OPAY DIGITAL SERVICES* *MARYAM FAROUK* OR *0709290797* *ACCESS BANK* *SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488* *IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705* *Kuyi following dina a Arewabooks @Maryamfarouk01 inda zaku karanta wannan littafin tareda sauran littattafaina* *NAGODE* *PAGE 23* Sati guda ya shude Audu na bulayin neman Zubaida sedai sama ko qasa babu ita babu kuma wanda ya ganta bare asan labarin inda tayi. Har Zariya sukaje da Bashir gidan daya dakkota suka tarar an tashi gidan ma gaba daya titi ya biyo ta kan hanyar haka suka juyo Kano babban abinda ya qara daga masa hankali ya bazama nemanta zuwan da Baba Zayya tayi akan taje duba Zubaidan Allah ya taimake shi yana gida ranar, daya rasa abin fada mata dole ya rangada mata qaryar Zubaidan tana Bechi, kuma daman yaso yaje ya sanar dasu tana can har se bayan ta haihu zata dawo Kano to Allah be nufa ba. Dake akwai yarda da Amana sam Baba Zayya bata kawo komai a ranta ba tunda ana hakan mace ta tafi garin su Miji haihuwa dan haka tayi musu sallama ta koma gida ta shaidawa Malam Hassan yanda akayi. Wannan dalili ya qara zaburar da Audu ga neman Zubaidan, nadama mara amfani ta dirar masa biya hukuncin daya yanke ba tareda zurfin tunani ba. Haka ya ringa raba kudi wa malamai akan ayi masa Addu'a Allah ya bayyana Zubaidan ya kuma kareta a duk inda take. Cikin wannan yanayi Alhazai suka fara tashi, Binta taje gida tayi sallama da danginta ta dawo tana ta shirin tafiya sauke farali bacci ragagge takeyi saboda jiran ace su fito. Ita sam ta manta ma da wata Zubaida balle batun ba'a ganta ba, yanda Audun be cika nutsuwa ba a lokacin yasa ta tsahirta masa, ita kadai take ta shirinta tunda dai ya sallameta ya bata Guzuri me auki ita kam ya gama da ita se jiran ranar tashi kawai takeyi. Acan gidan Yakubu kuwa hankali kwance Zubaida ke zamanta, tsakanin Balaraba da Yakubun ba zata tantance wanda yafi tattalinta ba. Duk wani abu da zata buqata suna mata haka nan basu barinta ta zauna shiru balle ta fada tunani ko wata damuwa a koda yaushe cikin hikima sukanyi mata nasiha akan rayuwa da qalubalen da yake tattare da ita. A dan taqin zaman ta fahimci banbance banbance masu tarin yawa da suke cikin rayuwar Haske data duhu ma'ana rayuwar da akeyinta cikin sani da wayewa ta Addini da kuma rayuwar Bidin bidima irin wadda tayi a baya ta koma dora yinta a gidan Audu. Yakubun jajirtaccen Namiji ne wanda yake tsaye akan lamuransa dana iyalinsa. Ga daishi be tara dukiya tamkar dan uwansa ba amma rayuwar gidansa ta zamo abar sha'awa wadda duk me hankali idan aka bashi zabin kudi ko nutsuwa irin ta gidan Yakubun tabbas baze tsallaketa ba. A kullum da Asuba seya dorawa matarsa da Yayansa karatu haka bayan sallar Isha'i idan sun zauna a maimakon hirarrakin banza na duniya sukan yi tasu hirar ne akan karatuttukan da sukayi. Ya tambayesu su tambayeshi, hatta da Qaramin dansu Tijjani me shekaru uku a sannan Alqur'ani ya fara zama a bakinsa, haka qananan Hadisai da ake dorawa Yayinsa yana tsinta har idan Yakubun yana tambayarsu sukayi kuskure Tijjanin da suke kira da Alhaji ze gyara musu ga wayewa ta boko turanci yafi hausa Nuna a bakinsu kodan inda suke zaune yaren da suka fi amfani dashi kenan? wannan abin ya matuqar birgeta ya kuma zaburar da ita kan cewar itama bata makara ba tana da damar da zata nemi ilimi tana kuma burin abinda zata haifa ya tashi cikin irin wannan rayuwar ta ilimi ba irin ta gidan ubansa ba. Zata iya bada shaidar Audun yana salloli na farilla kuma yana qoqarin yinsu akan lokaci kuma cikin jam'i, a zamansu daya tasamma shekara a watan Azumi kadai zata bada shaidar yana zuwa sallar Tarawi da kuma Qiyamullaili tun bayan daya shude kuma a ranakun girkinta dai bata sake ganin yayi ba bata sani ba ko idan yana dakin Binta. Dama shi bame jurar Ibadar Azumi bane domin Ramadanan ma da qyar yake kaishi, bayan Alqur'ani bata tsammaci ya karanta wani littafi ba bata taba ganinsa dashi ba haka ko a magana ba zatace ga inda ya kawo misali daga cikin Hadisi ko wani littafi na Addini ba. Ba zata manta ba akwai sanda ta taba shawartarsa shiga karatun Asuba da akeyi a masallacin dake cikin layinsu wani baqon babban Malami ne yazo yake bada karatun Fiqhu da Hadisi se Tauhidi take yace mata ai ya gama karatu, seda ya shekara biyar yana qolanta to wane karatu ya rage masa da beyi ba kuma? Da tace ita zata ringa zuwa gurin matar Malamin da take karantar da Mata a cikin gida harya yarda bata san ya akayi ba ya dawo yace babu maganar ta tambayi dalili kuma yace babu dole ta haqura badan taso ba domin Allah ya sani tana sha'awar ta nemi ilimi shiyasa yanzun data samu wannan damar tayi amfani da ita. Dada take ja tana biya mata karatun, dayake tasan baqi dan haka karatimu da takardar Alqur'ni be bata wahala sosai ba dukda tafi gane rubutun warshu amma da yake ta saka kanta se gashi tana ganewar in ta biya mata kuma ta ringa nanatawa kenan har seta haddace. Balaraba ce ta sameta akan ta ringa fitowa suna daukar karatun tare bayan da Dada ta sanar mata tana yiwa Inna Zubaidan qarin karatu, daga nan itama ta zama yar Aji ta kuma maida hankali sosai akan abinda ake koya mata. Irin nutsuwar da take tsintar kanta a ciki ta qara tabbatar mata da cewar tabbas akwai banbanci me tarin girma tsakanin rayuwar da akeyinta cikin sani da kuma ta jahilci. Satinta uku a gidan wata safiya ta tashi da naquda, kafin nan sunje Asibiti har sau biyu Yakubu da kansa ya kaisu tareda Balaraba an dubata an kuma tabbatar da lafiyarta data abinda yake cikinta suka basu kwana goma daya zagayo suka koma kwanaki biyu kenan da zuwan nasu da safiyar ranar Laraba ta tashi da naquda nan da nan suka wuce Asibiti da ita, daman Yakubu yana nan ya jinkirta komawarsa Ikko saboda yana taraddadin ya zasuyi idan haihuwr tazo mata cikin dare gida babu Namiji daga ita se Balaraban dalilin daya saka ya daga tafiyarsa kenan saboda a Asibiti zuwansu na farko sun bashi tabbacin ba zata qara sati biyu nan gaba bata haihu ba gashi kuwa kwanaki goma sha biyu kenan da wanacn zuwan haihuwar tazo. Cikin taimakon Allah bata dauki lokaci mai tsaho ba ta sauka, ta haifo wasu runtuma runtuman tagwaye wanda ko a Da guda daya aka haifi wannan tabbas se an jinjinawa wadda ta santaloshi se gashi har biyu ubangiji ya bata a sauqaqe cikin Aminci. Lokacin da aka nunawa Yakubu yaran kasa cewa komai yayi se tasbihi daya ringayi a zuciyarsa. Duk wanda yasan Ahalin gidansu baya buqatar a fada masa yaran tsatsonsu ne ze iya cewa ma ba'a taba haifar Jarirai masu kama da Mahaifinsu Malam Tijjani Kwabo da kwabo irin wadannan ba har hasken fatarsa basu bari ba abinda ya banbantasu da Audu kenan saboda shi yana da duhu kadan. Ya rasa ta ina ze fara ma, Balaraba nata murna ta kasa tsayuwa guri daya shi kuwa tunanin waze fara shaidawa zancen haihuwar yake tayi. Gadai Arziqi Allah ya basu wadannan ne tagwaye na farkoba zuri'ar gidansu amma haihuwar su tazo cikin rudani. Seda ya tabbatar babu abinda ake da buqata a Asibitin kafin yacewa Balaraba zeje ya dawo. Can kamfanin da Audu yake ginawa inda kuma nan su Musbahu suke zama ya nufa. Yaci sa'ar tarar da Musbahun be tafi gidan Mai ba, bayan sun gaisa yace yazo ya rakashi gidansu Zubaida Amaryar Audu babu musu ya hau mota suka tafi a ransa yana mamakin meyake faruwane domin a kwanakin nan gaba daya sun lura da Baba Audu baya cikin hayyacinsa dukda be fada musu komai da yake damunsa ba amma ko gidan Mai seya kwana biyu be fito ba aikin Kamfanin ma an dakatar dayi kamar yanda ya fada yana cikin wani dan uzuri ne. Da suka isa gidan a Mota ya bar Musbahu ya qara qofar daya nuna masa a mazaunin ta gidan Malam Hassan. Yayi sallama cikin sa'a Malam din ya fito ya amsa a shirye yake da alama wani gurin zashi, be taba ganin Yakubu ba amma jini da kamannin fuska yasa ya gane dan uwan Audu ne dan haka yayi masa iso cikin gida bayan ya saka Baba Zayya tayi musu shimfida ta kawo masa ruwa a mutunce suka gaisa suna tambayarsa iyali. Cikin nutsuwa da kuma sanin makamar aiki irin nasa ya warwarewa Malam Hassan duk abinda ake ciki be boye masa komai ba hatta da sakin da Audun yayiwa Zubaida da zamanta a gidansa zuwa yanzun data haihu be rage komai a ciki ba. Malam Hassan yayi shiru cikin tsantsar jimami kafin yace "Tabbas nayi zargin wani abu ya faru saboda irin zaryar da dan uwanka ya ringayi a gidan nan kuma alamu na rashin gaskiya sun bayyana tattare dashi sedai na kyautata masa zato na cewar koma menene nasan baze cutar mun da Zubaida ba na saka a raina dai wata matsala ce qila da yake jin nauyin sanar dani. Hatta zuwan da zayya tayi ni na turata domin taje ta ga halin da suke ciki qila mu iya gano bakin zare sedai ya tabbatar mata da cewar ya tura Zubaidan can garinku, tabbas wannan maganar ta tayar mana da hankali hat shaidan yaso yayi wasa da zuciyata ya darsa mun zargin wani al'amari na daban amma na yaqe shi da qarfin addu'a ban kuma gusa ba kullum cikin yinta nakeyi ina roqon ubangiji da koma menene yake faruwa ya bayyana mana ya kuma sauqaqa mana. Na godewa Allah da Jarabawar ta tsaya iyakar haka, na kuma gode maka da kayi mun wannan arziqin na riqe Zubaida a hannunka harta haihu ubangiji ya wanketa daga zargin da dan uwanka yakeyi mata na taje masa gida da Dan da ba nasa ba. Yanzu data haihu a hannunka ze iya tantance kamanceceniyar da take tsakaninsa da abinda aka samu kuma ya iya nutsuwa yayi lissafi na kwarai sabanin idan ana nan ta haihu tunda har ya rigada ya yarda da cewar Boka ko Malamin tsubbu na iya aikata komai la shakka yace itama kamannin dake tsakaninsa da abinda aka haifa qirqirarta akayi". "Hakane Baba ina kuma qara baku haquri akan abinda ya faru In sha Allahu ma komai ze daidaita base har Zubaida ta dawo gida ba daga can gurina zata sake komawa dakinta da yardar Allah kuma abinda yasa nazo na sanar muku da abinda ake ciki saboda ku mahaifantane kuna da haqqi akanta be kamata kuma ace mun rufeku akan babban Al'amari irin wannan ba" Yakubu ya sake fada. Malam Hassan yayi murmushin daya fi kuka ciwo yace "Kayya yaro dena wannan magana kuma ai zancen kome babu shi Aure ya qare sedai muyi fatan ubangiji ya musanyawa kowannensu da Mafi Alkhairi a gareshi. Kamar yanda rayuwar data faru a baya ta shude muka yarda da qaddara wannan ma mun dauka, rabon wadannan bayin Allah yayi sanadiyyar wannan Auran, tsakaninmu da Abdullahi kuma har abada babu abinda zamu ce masa sedai fatan Allah ya dubeshi ya saka masa da Alkhairi kwatankwacin wanda yayi mana. Maidomun da Zubaida gida da yayi ya isheni komai a duniya wlh kuma wannan al'amari daya faru baze goge tarin Alkhairinsa na baya a idona ba, wata Jarabaqar ce daga ubangiji kuma idan munyi haquri zamu cinyeta". Yakubu be ja maganar da nisa ba yayi masa sallama bayan ya roqi Baba Zayya data shirya su tafi Asibiti tare ya kuma sake roqar Malam din da maganar ta zama sirri tsakaninsu. A hanya Baba Zayya ta samu bakin zazzage masa buhun bala'in da bata iyayi gaban Malam Hassan ba kai kace shine Audun, shidai be tanka mata ba domin sunada duk wata dama ta suyi fada dan an bata musu. *MAMAN MARYAM ONLINE BUSSINESS* *Ina kuke Mata Yan kwalisa , Ina nufin isassun Mata ,Wai shin Kuna da labarin shahararren company nan namu na GHT wato good healthtreatments* *Wanda yazo muku da fitattu Kuma* *ingantatattun suppliment ,na dukkan matsalolin ku*❓ *Ina maisan tayi kyau,irin na isassun Mata ya fitar Miki da shef dinki tayi Miki gyara in and out ,nemi royal jelly dinmu na company GHT* *Wanda aka yishi da xuma ,kundai San amfanin Zuma basai na fada miku ba , hajiya ta kixo ki Yi gyara domin ki kerewa sa,a kije taro ko baki da ko sisi kiji Ana rangada Miki hajiya , saboda yanda Zaki Kara kwarjini ,kina walwali acikin mutane , magungunan ght anti agen ne suna maida tsohuwa* *yarinya ,yarinya Kuma ta koma jaririya* *Muna da magunguna iri iri* *NA GYARAN JIKI* *NA GOGE NANKARWA* *NA RAGE QIBA* *NA CIRE TUMBI* *NA QARIN HIPS* *NA GIRMAN BREAST* *NA QARA TSAHON GASHI* *NA QARIN NI'IMA WANDA ZAI SAUKAR MIKI DA NI'IMA YA QARA MIKI DADI DA ZAQI A GURIN OGA* *Muna da hadin bita zai zai ,indai kishiyar ki tana Shan magungunan GHT, tohh lallai sunan ki sorry domin kuwa tazarar dake tsakanin ku kamar tazarar sama ne da kasa* *Muna da Wanda zai matseki ciki da waje Andai na yayin dinki uwargida*, *Sannan company mu na GHTBai tsaya anan ba* *Ya kawo muku maganin dukkan matsalolin ku* *INA MASU HAWAN JINI?* *INA MASU CIWON ZUCIYA?* *INA MASU CIWON QODA?* *INA MASU CIWON HANTA?* *INA MASU SICKLER?* *INA MASU HIV?* *INA MASU CANCER?* *INA MASU NEMAN HAIHUWA?* *Tohh Ku matso GHT taxo muku da magungunan matsalolin ku* *Kuma muna da testimonys da yawa ,na wadanda suka gwada suka da ce* *Munanan a KANO KUNTAU* *Kuma muna tura Kaya ko wanne gari cikin aminci da gaskiya , kuma kayan mu muna badashi ne cikin price Mai rahusa ga kyau ga inganci sannan ga Rahusa* *Kutuntube mu ta wannan number 📞08129249549* *📲07011401314* AUDU Shirye shirye suke tayi saboda a daren ranar suke saka ran tashin su Binta. Gaba baya ta hargitse gidan ta hada faggon jakunkuna tamkar me zuwa yawon bude ido ba Ibadah ba. Addaba masa tayi akan seya qara mata kudi, "Kaga fa a can nake so nayi siyayyar kayan haihuwar nan, dan abinda ka bani me naci a ciki me nayo tsaraba sannan duk ciki kake so nayi siyayyar kayan jaririn?" Binta ta fada tana matse fuska sanda yake jaddada mata sisi baze qara mata ba. Kudade masu kauri ta karba a hannunsa, banda guzurinta ga wanda Babanta ya bata amma a haka take hanqoron se ta sake waftar wasu a hannunsa ya rasa bala'in son kudi irin na Binta kuma ba abin Mamaki bane taje ta dawo daga ita se jakar hannunta dan ya dade da gane Binta bata iya tsinanawa kanta ko waninta da komai a zamansu daga kan sutura zuwa wani abin amfani na gida sabo sedai idan shi ya siyo ko kuma aka mata daga gidansu amma a karan kanta batayi ya kan tuna Bara'atu zamansu duk Azumi zatayi yan kaye kaye ta fitar da tsoffin kayan amfaninta ta maida sababbi banda Bintan. Data ishe shi da surutu shi kuma ya rantse sile baze qara mata ba se kawai ya shirya ya fita, Gidan Mai ya tafi, mamaki ya kamashi yanda yaransa suke ta yi masa barka da Arziqi Allah ya raya bayan sun gaisa haka ya shige ofishinsa ransa fal da mamakin barkar me ake masa. Sallama Musbahu yayi ya bashi izinin shiga bakin nan nasa kamar ze taage saboda fara'a ya gaida Audun kana yace "Yanzu naje na gano yan tagwaye, wlh Baba kamar kayi kaki ka ajiye, duk yaran gidan nan ni banga wanda ma yayi kama da kai kwabo da kwabo kamar su ba". Kallon Musbahun ya ringayi kamar be fahimci abinda yake fadi ba, so yakeyi ya tambayeshi waya haihu amma kuma ya qiyin hakan a maimakon haka seya miqe yana cewa "Muje na gano su" Maganar tasa ta bawa Musbahu mamaki dukda daman yanda ya ganshi tamkar be san da zancen haihuwar ba ya bashi mamaki sannan ya sake shiga duhu akan lamarin, tabbas akwai abinda yake faruwa tun daga daukarsa da Baba Yakubu yayi sukaje can gidan Malam Hassan bayan nan sukaje Asibiti a can din yayi tsammanin tarar da Baba Audun ko matarsa amma yaga akasin haka Inna Balaraba ce kadai se Baba Zayya da suka tafi da ita tare. Shidai bece komai ba har suka isa Asibitin wanda shi yake tuqi yana gaba Audu na biye dashi a baya har suka isa dakin da aka kwantar Zubaidan tana hutawa. Wani tsalle zuciyar Audu ta buga lokacin da idonsa yayi arba da jinjiri a hannun Baba Zayya tana jujjuyashi, idonsa fes akan yaron ya shiga cikin dakin sosai se ganin mutum sukayi sangangan akan su. Balaraba ta buga tsaki kamar zata tsinke harshenta kafin ta miqe tana cewa Baba Zayyan "Bari na zagaya" "Nima bari na biki nasha iska warin magani duk ya cika mun ciki" daga haka ta ajiye jaririn hannunta Musbahu yayi zuruf ya daukeshi suka fice suka barsu a dakin. Idanu Zubaidan ta rufe tana qara gyarawa yaron data gama shayarwa kwanciya a jikinta, Audu na tsaye tamkar wanda aka sarewa guiwoyi ya kasa gaba ya kasa baya jinin jikinsa ya tsinke haka bugun zuciyarsa ya qaru kamar wanda yake kusa dashi ze iya sauraro. Musbahu ya ajiye yaron hannunsa bayan daya gaka jujjuyashi bakin nan yaqi rufuwa ya fita ganin kamar suna da buqatar sirri. Fitar Musbahun ta dan saukar masa da qwarin guiwa har ya qara taku biyu ya isa gaban gadon sosai yana kallonta tareda yaran da kunyarsu tayi masa lullubi. Ko a rufa ido aka shafa fuskarsa aka shafa ta yaran an sana halitta dayace balle a kalle su ido biyu, bayan kamannin fuska qirar jiki da kammani na jini duk sun bayyana tattare dasu, ya kai hannu ze sauki wanda Musbahu ya ajiye a ba zata yaji ta daka masa tsawa tace "Akul ka tabamun yara" ta fada har tana nuna shi da yatsa. Yanda tayi maganar cikin sauti me nuna bacin rai matuqa hakan kuma ya nuna a idanunta tilas ya janye hannunsa daga daukar yaron da ya bude ido yana kallonsa tamkar ya sanshi. A sanyaye kai a qasa tamkar ba Audu uban yan Izza ba ya matsa dab da ita cikin karyayyen sauti yace "Kiyi haquri ki yafe mun, wlh sharrin shaidan ne". "Babu wani shaidan face kai da Annamimiyar matarka, ni yanzu babu wani abu daya rage tsakanina dakai ubangiji ya gama mun komai daya wankeni daga zargin da kake neman laqabamun, ciki dai gashi na haifeshi watanni goma sha daya a gidanka cikin qudura ta ubangiji kuma ya bani Yaya masu kama da kai kaga duk iya sharrinku da kaida matarka baku isa ku barranta wadannan yayan da Ahalinku ba, fatana kar Allah yasa su gado mugun hali irin naka. Wlh nayi dana sanin Auranka Audu, da ace na san haka can cikin zuciyarka yake baqiqqirin da ban amince da kai ba. Ka gwada mun hali me kyau, ka yaudareni da Kyakykyawar Dabi'a. Nayi tsammanin na samu Bangon da zan jingina, jigon da ze tallafi rayuwata ya gyarani ashe kai kayi shirin qarasa tarwatsa rayuwa tane. Rayuwata ta baya ta zama tariyi kai kuma ka niyyati shafamun baqin fentin daya fi na baya muni, shin bakayi tunanin halin da mahaifina ze shiga ba idan yaji wannan mummunan abun daka zargeni dashi? Anya kai ko da zuciya a qirjinka Audu? Me yasa baka tunani da kwakwalwarka ka sakarwa zuciyarka Linzami? To wlh ka farka tun kafin lokaci ya qure maka, wannan rayuwar da ka dauka ta rashin tunani babu inda zata kai ka illah Nadama da dana sani mara amfani. Ita kuma matarka ka gaya mata tabi a sannu, ina tausayawa rayuwar da zatayi a gaba haqqi dabaibaye da ita. Se yanzu na fahimci yanda kuka taru kaka kassara rayuwar Bara'atu kuka laqa mata mata mugun qazafi to wlh haqqinta kadai ya isheku a duniya idan har baku nemi yafiyarta ba ina kuma fatan yanda Ubangiji ya wankeni itama ya wanketa ya bayyana gaskiyar duk wani mugun qulli da kukayi akanta" tana gama fadar haka ta gyara kwanciya ta jera yaranta a gabanta bayan ta bashi baya ta rufe ido zuciyarta na tafarfasa tsanar Audu me tsanani tana hudata. Badan kar tayiwa Allah butulci ba da tace inama ya jinkirta bata wannan gwalalon kyauta a wani gidan inda yafi na Audu Alkhairi? Amma dukda haka ta godewa Allah ta sake gode masa bisa ni'imar da yayi mata. Tamkar wanda lakarsa ta tsiyaye haka ya ringa jefa qafafu harya fice daga Asibitin, ya manta da Musbahu sukaje hakanan beyi tunanin mota ba ya ringa taka qafafunsa bude ido kawai yayi ya ganshi a qofar gidansa tundaga Asibitin Murtala, tafiya yayi wadda rabon da yayi irinta a qafa dai ze iya cewa tun Zamanin yana Audu qolo. Binta na zaune a tsakar gida da jama'arta da suka zo yi mata Sallama makwafta da kuma Turai da Mardiyya Wata sabuwar qawa da tayi babu dadewa. Yanda Audun ya shigo ya saka duk matan binsa da kallo kamar ma be lura dasu ba haka ya tsallaka ta tsakaninsu ya wuce sama, Turai ta kalli Binta kafin tayi mata alama da ta bishi ta miqe tana murmushin yaqe ta sallami maqwaftan ya rage Turai da Mardiyya kafin ta haye sama gurin Audu. Yana zaune akan kujera yayi irin zaman nan na balance ya bude qafafu da hannayensa kana kallonsa kasan da akwai abinda yake damunsa. Cikin salo da kissa ta bude firji ta dakko ruwan sanyi ta matsa gabansa ta tsiyaya masa tana cewa "Lafiya dai ka shigo kamar baka cikin hayyacinka?" Seda ya kwalwale ruwan ya miqa mata kofin kafin ya yunqura ya gyara zamansa yana kallonta dakyau yace "Zubaida ta haihu" "An ganta kenan, a ina? To mema ya shafemu da ita ko haihuwar ta? Halan gurin farkan nata ta je ta haihu acan ko?" Ta yi maganar tana yatsina fuska. Miqewa yayi ya nufi daki yana tafiya a hankali yace "Ta haifi tagwaye duka maza, kamanninsu daya dani" "Me kake nufi?" Ta miqe a zabure qirjinta na dukan dubu dubu kunnenta na mata amsa kuwwar Tagwaye Maza da ya fada, se ya waiwaya ya kalleta yace "Karmu fara wannan maganar ma. Kin cuceni kin rabani da matata, waima meye dalilinki na sheganta mun Yaya Binta? Me yasa kikayi haka?" "Ni na sheganta maka yaya? A yaushe akayi haka? Tsakaninka da Allah ni da kai mun taba magana nace maka cikin Zubaida shegene? Hasashena nayi na fada kai kuma tunda kasan da walakin goro a miya ka tabbatar haka ne to kuma se kazo kace na cuce ka dana maka me? Da kake wannan babatun ma me kake nufi ka karbi cikin kenan ko Yaya?" "Ciki daman nawane" ya bata amsa yana shigewa ciki dan in ya tsaya din be san me zece mata ba. Gaskiya ta fada magana tayi me harshen damo shi kuma ya hau ya zauna daram wato ta tabbata ya zama wawa kamar yanda Yakubu ya fada Bintan ta karanci rashin tunani irin nasa shiyasa tayi amfani da wannan ta cusa masa tunani a kwakwalwarsa harta kaishi ga yanke danyan hukunci yanzu gashi tun ba'aje ko ina ba ya dawo yana dana sani mara amfani dan yasan ya rasa Zubaida ba zata sake yarda ta komo gidansa a matsayin matar aurensa ba. Daren ranar Binta ta wuce Saudiyya cikin tashin hankali bayan sun rakaya dasu Turai sunje Asibiti sun ganewa idanunsu Tagwayen da akace Zubaidan ta haifa. Kuka wiwi ta ringayi kamar wadda kanta ya kwance wai ya za'ayi tazo a bayanta ta haifi tagwaye kuma Maza kenan yanzu ta fita kasafi cikin dukiyar Audu kenan. A Saudiyyan haka tayi Ibadar rabin Addu'arta ta Allah ya sa tayita haifar Yan biyu Maza ne bayiwa kanta wata kwakwkwarar Addu'a ba balle Yayan da take roqon a bata haka aka sauke Hajji ta dawo kamar yanda Audun yayi tunani daga ita se Kayan data tafi dasu yar tsarabar data yiwo bata kai kota kashi goma cikin uban kudin data tafi dasu ba. Bayan dawowarta ta tarar da an kwashe kayan Zubaida wannan ya dan rangwanta mata damuqar data saka kanta a ciki. Daman daga Asibiti Zubaidan gidansu ta wuce kamar yanda Mahaifinta ya buqata Yakubu yayi iyakar roqon da ze iya amma Malam Hassan yace yayi haquri kawai. Ran Yakubun ya sake baci matuqa ya dauka Audun zeyi Nadama ya kuma nemi su sasanta ta koma dakinta amma seyaga akasin haka. Ya dai siyawa Jarirai kayan na Alfarma haka itama Maijegon ya hada da ita da Manya manyan Ragunan suna dana Qauri ranar kwana biyar da Yan Bechi suka zo wanda suma Yakubu ne yaje ya sanar dasu suka kai kayan Barkar. Da aka kwana biyu har ya koma Ikko ya sake dawowa wata daya bayan haihuwar kenan ya sake tarar Audu da zancen ya suke ciki sun daidaita zata dawo idan ta yada wanka ko kuwa kai tsaye babu boye boye yace masa "A gaskiya ni bazan iya zuwa nayi bikon wata mace ba, zan bata lokaci harta huce daga fushin da takeyi, idan ta nuna buqatar cigaba da zama a gidana se mu daidaita". Yakubu ya rasa abin fada ya ringa kallon Audu kawai yana jin kamar ya rufeshi da duka. Ya dade yana ganin marasa hankalin mutane amma Audu leader ne, cikin tsantsar takaici yace "Abinda ya hanaka ka maido da Bara'atu kenan tunda bata furta da bakinta tana so ta dawo ba ko?" "Ka gane ashe, ai Allah ya kallo duk wani abu daya kamata ace nayi da ze nunawa Bara'atu ta dawo dakinta nayi. Kana kallo dawainiyar gidansu kaf har abinda be zama dole na ba yi musu nakeyi, duk wata se nayi mata aiken kudi da kayan abinci kuma idan naje Bechi ina zuwa naga Yaran to me kuma ya rage da zanyi ya nuna mata Biko nakeyi? Sena zubarda girmana na roqeta ta dawo bayan Alfarma zanyi mata naci gaba da zama da ita bayan laifin data aikata mun? Itama Zubaidan ai koda ina da laifi nata yafi yawa a ciki, me yasa bata tsaya tayi mun bayani yanda zan fahimce ta ba amaimakon haka seta ringayin abubuwan da zasu qara tabbatar mun da zargina akanta ni kuma shine ya tunzurani na yanke hukunci. Kuma ai ita har haquri na bata da naje Asibiti tace babu ita babu ni kuma ta hanani taba Yayana shine kake so naje gidansu nace ta dawo salon ta samu damar rainani ko to ni bazan iya wannan aikin zubarda mutunchin ba" Audun ya fada cikin dagawa. Mamaki, takaici hade da baqin ciki sukayiwa Yakubu rubdugu lokaci daya amma ya rasa kalmar da zeyi amfani da ita gurin zagin Audun dan haka ya kada kai kawai ya wuce ya barshi yana jinsa yana masa magana akan ya tsaya mana ina zashi be ko waiwaya ba. Duniya dai akace tafi bagaruwa iya jima, tabbas yana jiyewa dan uwansa randa muguwar Ta'adarsa zata bibiyi rayuwarsa. https://chat.whatsapp.com/I8xKHGurk7EBf5ZqQdxHKG *MATAR MUTUM* *NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER* *FIKRA WRITERS ASSOCIATION* *LITTAFIN KUDI NE* *PAY 500 A ASUSUN* *7061838488* *OPAY DIGITAL SERVICES* *MARYAM FAROUK* OR *0709290797* *ACCESS BANK* *SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488* *IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705* *Kuyi following dina a Arewabooks @Maryamfarouk01 inda zaku karanta wannan littafin tareda sauran littattafaina* *NAGODE* *PAGE 24* Rayuwa ta miqa, kwanan Binta Talatin da bakwai da dawowa daga Aikin Hajji ta haihu ta sake samun Da Namiji da yaci suna Naziru, yafi babu wai Agwai da baqin Da yanayin da ta nuna kenan domin ta gama sakankancewa da Addu'ar data ringa zagaye Ka'aba tanayi akan Allah ya bata yan Biyu Maza ta karbu to dayan ma babu laifi tunda yanzu sunyi kai daya su ukun gaba daya kowacce tana da Yaya Maza Biyu kenan, amma ba ta sare ba za kuma taci gaba da addu'a Allah badi war haka tayi yan uku ma ba biyu ba kuma duka Mazaje dan babu yanda za'ayi wata mace ya fita kaso a cikin Dukiyar da ubantane silar samunta. Ko kaza bata zo mata barka ba daga Bechi balle suna haka sukayi bidirinsu da ita da yan uwanta se qawaye da makwafta shi kansa Audun tun bayan abubuwan da suka faru zamansu ya canza salo dan gaba daya ya daura mata laifin itace silar Rabashi da Zubaida ita kuma ta nuna sam ba haka bane ba. Da fari bayan dawowarta ta biyeshi zaman ya zama babu dadi sedai bayan da suka tattauna da Turai da kuma sabuwar mashawarciyar da suka samu wato Basira se abubuwa suka canza daga bangarenta. Basirar ta qara tunasar da ita cewar muddin fa tana son biyan buqata seta kwantar da kai. Tilas ta maida kanta banza a gurin Audun, tunda har ta fahimci shi mutum ne me matuqar son girma da son a nuna ya isa to tayi amfani da wannan damar gurin kaishi matsayin da Allah be kaishi ba. Ta ringa nuna masa nan duniya babu yashi, duk kuma abinda ze fada karta kuskura ta musa masa ta barshi akan komai yayi daidai ne baya kuskure. "Hajiya sufa Maza kamar qananan yara suke wlh, fahimtarsu kawai zakiyi me suke so menene basa so shikenan ku zauna lafiya. Kuma a yanzu abinda ya kamata ki mayar da kai gurin yi shine ta yanda zaki kafa kanki da Yayanki a gurinsa yanda zakiyiwa duk wata mace da zata shigo rayuwarku Zarra" Basirar ta fada taba durqusar da kai irin na shahararrun munafukai. Binta ta hura hanci tace "Ai ba se kin fada ba, haihuwa dai an haifesu amma naci alwashin muddin ina raye yaya nane zasu zama kan gaba a komai na dukiyar Audu, baze tuna yana da wasu yaya ba bayan nawa, duk wanda yaci Arziqin Audu to ni naso" "Ina yinki qawata fada da cikawa wannan aikinki ne" Turai ta fada tana bata hannu suka tafa. Haka suka yita qulle qulle da shiri na yanda za'ayi yanzu da nan gaba. A haka har lokacin haihuwar tata yazo bayan anyi suna da kwanaki Turai taje ta sameta da zancen rashin zuwan yan Bechi. "Ni se nake gani ko dai babu dadi yaci ace kina sabga dasu, saboda dangin Miji ba qananan Munafukai bane, kinga idan suka kafawa mutum qahon zuqa Allah ne kadai ze kubutar dasu. Kina kallo dai yanda nake zaune da nawa duk sharrin mutum be isa yace na masa mugun abu a fili ba kuma na sani sun sani basa qaunata nima bana qaunarsu amma tunda ban bada qofar da zasu wulaqantani ba kinga qalau muke zaune dan haka kema dole ki gyarota dasu, ki jasu a jiki musamman ma naki da suke Fuqara'u Ahalin tsiya. Kamar kajine kina watsa musu tsaba na tabbata zasu biki ko wannan ma ze qara miki fada idan kika kame yan uwansa kinga koda ace kin samu tangarda dashi ba fata ba yan uwansa zasu zame miki makamin da zaki gyara komai" cewar Turai. Binta ta numfasa tace "Turai baki san yan uwan Audu ba musamman yan dakinsu. Yanda yake da wannan kafaffiyar zuciyarfa iwa ta mutanen farko haka suke. Bana tsammatar kudi ze saka su soni kina kallo ko shi din da yake musu shine jigon komai nasu akan Wannan shegiyar Bara'atun duk suka masa tawaye, yanzu an kuma na biyu sun nuna sunfi qaunar Karuwa akaina shiyasa duk suka qi zuwar mun Barka amma ai na samu labarin su sukazo suka kaikayan suna suna gidansu Zubaidan. Tsinanniyar Bilkin nan tun ranar sunan Dady na farko bata qara tako qafarta gidan nan ba gara Aishar tazo jinya kwanaki can Mazan kuwa tunda suka zo fadar Baqin labarin Auran Karuwa basu dawo ba hatta Baballiya tunda aka Auro ni sau daya ya tako qafarsa gidan nan sedai fa idan naje can Kaduna na ganshi ya samu guri ya baje kamar gidan ubansa yanzu nan Yakubu ne kadai yake zuwa idan cin mutuncibsa ya tashi kuma daman duk ciki Audun ma shi yake shakka shi kadai ne yake tsayawa ya gaya masa magana son ransa kuma ya shanye baze iya mayar masa ba a yanda ya tsaneni kuwa ko duniya da abin cikinta zan bashi baze qaunaceni ba haka Annamimiyar matarsa ni ko kamanninta bazan iya tunawa bama yanzu. Kai na tsani Yakubun nan iyajar raina wlh" ta qarasa tana cizon yatsa tsanar da tace tanawa Yakubu ta nuna qarara akan fuskarta. "Dukda haka dai ance se an tsaga ake ganin jini, daurewa zakiyi ki cusa kanki cikinsu ko basa qaunarki ta hakane fa zaki ringa sanin wasu abubuwa da suka shafi shi kansa Audun, hatta da dukiyar tasa kince duk abinda ya samu acan yake narkata, filaye gonaki duk ya tattara acan to idan kika qwafe a nan kin bar musu komai can ta yaya zaki san me kuke dashi? Irin hakane kina zaune kina lissafin dokin Rano se anzo ranar kasafi kiji abinda ba haka ba ita Bara'atun da take cikinsu tsaya mata zasuyi taja rabo me tsoka ga wannan itama tunda sun nuna tafi musu ke duk mara musu baya zasuyi a barki da lissafi. Amma idan kika shige su ta yanda ba za'a layance miki komai ba kin sani shima kuma ki matseshi ta yanda duk abinda yayi ko zeyi seya gaya miki" "Yana ma gayamun in dai ya siyi abu ze fada mun tunda wannan matsiyaciyar ta fita ne dai kinga yanda abubuwan suka koma" "Se haquri ki kuma cigaba da lallabawa daman ai ba kullum ake kwana a gado ba dole wata rana a samu yanda ake so wata rana kuma aka sin haka sannan ba yanzu muke dubawa ba gaba zamu gina lokacin Jin dadib ai be ma zoba tukunna qawata kedai Allah yayi mana tsahon rai musha shagali" Inji Turai. Binta ta murmusa tace "Ai ni dole ma nayi tsahon rai dan munyi Gadonsa" "Ke karkiyiwa Allah gatsali wlh yanzun kijiki a rami" Turai ta fada tana zare ido, Binta ta rufe baki tace "Uffararan Allah na tuba ba haka zance ba, dangin mu dai sunyi Gadon tsahon rai kinga nima zanyi" ta sake sakin wani shirmen Turai ta miqe tana cewa "Bari kiga nayi nan iskancina be kai shiga hurumin Allah ba, to mutuwa dai ba ruwanta da gadon tsayin rai ko gajartarsa in lokaci yayi dole a tafi" da haka hirar ta watse saboda Binta tace kan me kuma ana hirar arziqi zata sako musu zacen mutuwa. Bayan ta yada wanka ta cewa Audu zataje Bechi ta kwana biyu, wannan yasa ya sassauto daga daure dauren fuskar da yake fama dashi tun rabuwarsa da Zubaida. Ya shirya mata tafiyar Ado sabon Direban daya dauka yake jigila dashi ne ya kaita Bechin niqi niqi da kayan tsarabar data loda dan Hajji Kam taje tayo tsince tsincen su Zam Zam, Dabino Bagaruwa su kallo kallo na yara da sauran tarkacen tsaraba ta tafi. Kadaran kadahan suka karbeta musamman da basu san da zuwanta ba dan haka babu wani tanadi da akayi mata ta bude dakinta ta shiga a ranta tana tsine musu babu wanda ya bita ko suce zasu tayata kimtsa guri sun dai karbi Naziru yana can hannun Sauda Amaryar Aminu. Ta gama kakkabe dakin ta kimtsa abinda zata kimtsa kafin ta bude jakar tsaraba ta shiga kasawa gida gida. Yara ne sukayita shelar zuwanta garin, Aisha ta biya gidan Bilki akan tazo suje yiwa matar Yayan nasu Barka da zuwa amma tace babu inda zataje. Haka ta tafi ita kadai ta tarar da Yaya Mairo da Yaya Amina da matan Yayyensu duk sunzo Goggo Fadi ta aika an gayo musu. Kamar yanda Turai ta fada kuwa duk wadda ta shigo fuska a murtuke dan ba a son ransu suka zo din ba dan dai bazasu tsallake kiran Sirikarsu bane amma data miqa musu qullin tsaraba se kaga sun hau washe baki suna godiya daga nan se a shantake a fara hira kuma wannan tasa Aisha ta tarar da dakin cike da Mata suka gaisa ta karbi yaron da daman shine maqasudin zuwanta bawai ganin Bintan ba tana tambayarta Yayansa tace mata Yana Kaduna tunda suka zo suna suka tafi dashi. Bata jima ba tayi musu sallama tace se gobe zata dawo. Bayan Isha Jamila Uwargidan Hashimu ta sake dawowa da Langa tuwo da miya data sakowa Binta abincin dare. Tana daki bayan ta lallaba Naziru yayi bacci, qullin uban Nama ne a gabanta da damammiyar fura take ci Baballiya ne ya kawo mata bada jimawa ba tayi mamakin ganinsa a Bechi wato ya zo Kano amma koya leqa can gidansu da tayi masa tsiya yace mata ai yaje Kanon amma a Kamfani suka hadu da Yaya Audu dake ba jimawa zeyi ba anyi posting nasa can qasar Kudu yazo yiwa yan gida sallama ne shiyasa be shiga can gidan sun gaisa ba ya ajiye mata saqon ya wuce ta bishi da kallo tana mamakin girman da yayi, idan ba'ayi wasa ba zefi Audu tsaho da qirar qarfi yanzun. "Sangangan kenan sudai sunyo gadon girmaz wai yanzu haka nawa Yayan zasu tashi kenan kamar dakarun yaqi? Allah yasa dai su kwaso hankalin wancan me baqar zuciyar Wan uban nasu dan ta nan ya banbanta da sauran" ita kadai take sambatu tana danna lomar Nama abinta Jamilan tayi sallama. Tsaki taja qasa qasa kafin ta amsa, babu damar ta boye abinda take ci dan ta rigada ta shigo dan haka ta hade fuska dan ba zata sammata ba. "Aa, Hajiya irin wannan rabasha haka kice gashin Haladu aka kawo miki" Jamila ta fada tana kallon ledar kamar ta dumbula hannu yawunta ya tsinke dan qamshin naman ua cika dakin duka. Yaqe kawai Binta tayi ba tareda tace komai ba a ranta tana mamakin meya maido matar nan kuma? Yan cikin gidan ma sun barta ta huta kuma se ita zata kwaso jiki tazo ta isheta a daren nan daga zangar ta dan basu fuska dazu. "Daman Tuwo na kawo miki, yo ahe ke tuni kin makari da babban yanka" Ta sake fada tana bude Langar tuwo da miyar data jere a qasa. Warin daddawa da kuka suka daki Binta a ranta ta danna Ashar tace "Ni zanci wannan baqin tuwon da miya kamar yawun Kaza?" "Zabuwa Babansu yace a yanka a zuba miki a miyar" Jamilar ta sake fada tana karkato mata da kwanon miyar dan taga Namomin da suke ciki wanda qarya takeyi ba Hashimu ne ya bada ba satar mata Zabo tayi tasa aka yanka tasan kuma da zarar labari ya isa kunnensa gobe akwai bala'i dan da tace masa Bintan tazo ma seda ya kora mata ashar yace ina ruwansa da wata Binta. "Allah sarki aiko nagode, bari na ajiye da safe se a dumamamun nayi kari dashi" "Aiko daman yafi dadin ci dumamen" Jamila ta sake fada tana gyara zama. Hira ta shiga sokowa Binta kamo nan kamo can, da taga bata da niyyar tashi dole ta bude naman ta mata bismilla aiko ta dirar masa seka rantse bata ci a gida bayan iyakar qoqari Mazajensu sunayi da wuya ayi miya lami a gida. Seda suka tada naman tas wanda Jamila ce ta cinye Rabi Binta ta janye Furarta gefe dan wannan kam ba zata bata ba. "Uhm bari na tashi dare ya fara nisawa, nace da safe in Allah ya kaimu nazo na rakaki ki gano gidan ummarsu Babangida ko?" Jamila ta fada yana miqewa tsaye da shirin tafiya. "Wace Ummarsu Babangida kuma?" Ta tambayeta cikin rashin fahimtar wa take nufi. *MAMAN MARYAM ONLINE BUSSINESS* *Ina kuke Mata Yan kwalisa , Ina nufin isassun Mata ,Wai shin Kuna da labarin shahararren company nan namu na GHT wato good healthtreatments* *Wanda yazo muku da fitattu Kuma* *ingantatattun suppliment ,na dukkan matsalolin ku*❓ *Ina maisan tayi kyau,irin na isassun Mata ya fitar Miki da shef dinki tayi Miki gyara in and out ,nemi royal jelly dinmu na company GHT* *Wanda aka yishi da xuma ,kundai San amfanin Zuma basai na fada miku ba , hajiya ta kixo ki Yi gyara domin ki kerewa sa,a kije taro ko baki da ko sisi kiji Ana rangada Miki hajiya , saboda yanda Zaki Kara kwarjini ,kina walwali acikin mutane , magungunan ght anti agen ne suna maida tsohuwa* *yarinya ,yarinya Kuma ta koma jaririya* *Muna da magunguna iri iri* *NA GYARAN JIKI* *NA GOGE NANKARWA* *NA RAGE QIBA* *NA CIRE TUMBI* *NA QARIN HIPS* *NA GIRMAN BREAST* *NA QARA TSAHON GASHI* *NA QARIN NI'IMA WANDA ZAI SAUKAR MIKI DA NI'IMA YA QARA MIKI DADI DA ZAQI A GURIN OGA* *Muna da hadin bita zai zai ,indai kishiyar ki tana Shan magungunan GHT, tohh lallai sunan ki sorry domin kuwa tazarar dake tsakanin ku kamar tazarar sama ne da kasa* *Muna da Wanda zai matseki ciki da waje Andai na yayin dinki uwargida*, *Sannan company mu na GHTBai tsaya anan ba* *Ya kawo muku maganin dukkan matsalolin ku* *INA MASU HAWAN JINI?* *INA MASU CIWON ZUCIYA?* *INA MASU CIWON QODA?* *INA MASU CIWON HANTA?* *INA MASU SICKLER?* *INA MASU HIV?* *INA MASU CANCER?* *INA MASU NEMAN HAIHUWA?* *Tohh Ku matso GHT taxo muku da magungunan matsalolin ku* *Kuma muna da testimonys da yawa ,na wadanda suka gwada suka da ce* *Munanan a KANO KUNTAU* *Kuma muna tura Kaya ko wanne gari cikin aminci da gaskiya , kuma kayan mu muna badashi ne cikin price Mai rahusa ga kyau ga inganci sannan ga Rahusa* *Kutuntube mu ta wannan number 📞08129249549* *📲07011401314* "Au, Bara'atu zance miki ko zaki fi ganewa. Juma'a idan tazo mako uku kenan da tarewarsu, kinga gida badai gida ba tamkar naku ba Birni, ai gaskiya Alhaji Audu yayi karamci ya kuma kyauta saboda dangin uban nan nata tasamma ci musu mutunchi sukayi wlh, kinsan basa son uwarta ta fa daman akace. To yana mutuwa suka tada bala'i wai gidan da yake ciki gadonsu ne su goma ya hana a raba ya ke zaune ciki dan haka se su fitar musu a gida a raba sannan su san kasonsu, kinga dan taqin da akace sun cire musu a matsayin rabon baban nasu? Ai badan Alhaji Audu ba a garin nan bamu san Ina Inna Hajara da yayanta zasu tsoma ransu ba shine fa ana gaya masa ya aiko aka far....." "Ya isa haka dan Allah, kije Allah ya kaimu goben se kizo ki rakani" Binta ta dakatar da Jamila daga zubar da takeyi tamkar famfon daya lalace. Jamilar ta fice bayan ta mata sallama tana dariya kamar wata wawiya tana fita Binta ta mayar da qofa ta rufe, wani kalar tashin hankali ke rufzo mata dukda yanayin garin babu zafi amma ita zufa ce take keto mata ta kafofin gashin jikinta. Ta ri ga safa da marwa a dakin tana huce ita kadai tama rasa ta ina zata fara tunani, Audu ya ginawa Bara'atu gida yaushe akayi haka bata sani ba kuma akan me? To kodai sun maida Auransu ne bata sani ba tana can gaho? Ta jefawa kanta tambayar seta zabura a fili tace "Kut**uba kenan ma ai kuwa da anyi yaqi duniya ni za'a yaudara a ninke baibai?" Kukan da Naziru ya sakane ya ankarar da ita hayagagar da takeyi ta daukeshi taci gaba da zaga dakin tana jijjigashi, wato mutanen nan anyi qungurumayen munafukai, ashe da Jamila bata gaya mata ba haka zata gama zamanta ta tafi ba tareda ta samu wannan mugun labarin ba aikuwa zasuga tatura, seta nuna musu ta fisu iya tashanci wato uta zasu hadewa kai? Tabbas Turai tayi gaskita da tace tana can Bihim zasu rabe komai a barta da zare ido gashi kuwa an fara. Daren ranar bacci barawo ne ya saceta dakyar aiko tayishi da mafarkin wai Audu ya mutu an kwashe komai an bawa Yayan Bara'atu da Zubaida ita bata samu ba. Da safe kuwa dakyar ta iya zama jiran Jamila da ace tasan gidanta ma da ba zata iya zaman jira ba gara taje su wuce daga can. Wadanda suka dawo washegari son zuciya ganin yanayinta yasa suka watse dan a dare dayan ciwon qyashi da Hassadar data dorawa kanta ya zabgeta kai ka dauka kwana tayi tana gudawa. Jamila bata zoba se bayan La'asar dalili kuwa Hashimu na gida ranar bayan ya gama Tijarata akan Zabonsa data dauka tayiwa Binta Miyar da ko dandanata batayi ba da safe da Sauda ta kai mata kayan Karin Kumallo tace ta dauke tuwon a bawa Yara. Seda ya fita kafin ta samu ta kammala duk abinda zatayi gudun kar sukai Magriba kafin ta fito. Tinqis tinqis se gasu a sabon gidansu Bara'atu Jamila nata zuba mata dan banzan Surutu ita ko Ruhinta da gangar jikinta suna ga su isa taga gidan da Audu ya ginawa Bara'atu. Tun daga qofar gidan yanda aka lailayeta da fulasta tasha fenti yanayin tsari da taswirar ginin kai ba zakace a cikin Bechi yake ba. Wani abu me daci da maiqo ya taso mata har seda ta dafe qirji tana kallon qofar gidan dake garqame da kwado alamar basa nan. Jamila ta qarasa tana shafa qofar ta juyo ta kalli Binta da taje tunga tace "Kinga basa nan, ko ina suka tafi se Allah amma babu komai gobe ma ranace se mu dawo" tana rufe baki sega Qanin Bara'atu ya shawo kwana ta washe baki tace "To qila ma gasu nan kinga qaninta". Ya qara gurin ya gaishesu a mutunce Jamila tace "Ina mutanen gidan mun tarar qofa a rufe? Ka ganta can ka ganeta ko Matar Alhaji Audu ce tazo muku Allah sanya Alheri". "Ai kuwa kunyi sabani dan basu koyi Minti Ashirin da fita ba sun tafi Rano" ya bata amsa. Ta dafe qirji tace "Rano? Kai sun luluqa da nisa, to kuma yaushe zasu dawo?" "Gaskiya ban sani ba" ya bata amsa cikin qaguwa da maganarta ya fara tafiya ta tareshi tana cewa "Aida ka bude mana to taga gidan tunda kaga ita ba mazauniyar nan bace balle ace ta sake dawowa idan sun dawo, qaraso Hajiya ya bude mana mu Shiga" ta fada tana kallon sashen da Binta ke tsaye sedai wayan bataga kowa a gurin ba. Ta hau waige waige qanin Bara'atu me suna Isah yace "Indai wannan Hajiar ce ai ta dade da tafiya tun sanda nace miki basa nan" daga haka shima ya wuce ya barta tsaye tana cizon yatsa. Bawai da zuciya daya ta sanarwa da Binta wannan maganar ba so tayi ta hada bala'i ta kuma so ace sun tarar da su Bara'atun dan ta tabbatar da Binta bazatayi haquri ba se tayi musu tijara da rashin mutunchi iyakar qarfinta. Cike take da qyashi da hassadar ya za'ayi ace dukda Bara'atu bata tare da Audu kuma taci gaba da kere masu ta kowanne fanni na rayuwa? Shekaru Aru Aru suna zaune gidan qasa lokaci daya Audu yazo ya tadawa Bara'atu da Iyayenta ginin Jan bulo ya danqara musu gida kamar na wani sarki Alhalin su suna fama da jar laka? Shiyasa ta kwazawa Binta maganar tunda ta lura bata sani ba yanzun ko tasan inta koma Birni wacce za'ayi se Allah ita dai fatanta Audun ya kwace gidan kawai tunda dai yana tsoron Binta. Farar safiya Binta ta kammale kayanta tsaf tasa a nemo mata shatar mota zata tafi gida. Goggo Fadi ta ringa tambayarta abinda ya faru data tashi tafiya gagaga haka Alhalin sati guda tace zatayi bata da abin fada mata a matsayin dalilin tafiyarta dan haka kawai ta laqawa Danta ciwo tace shine bashida lafiya gara su tafi ta kaishi Asibiti. A wata mota da Jaki ya fita dadin hawa da saurin tafiya ta kamo hanyar Kano, ita ma din da dakyar aka samo mata ita dan masu motocin daukar kaya tuni kowa ya fita ai kuwa taji jiki kafin taje gida, baya da qafafunta sun fada dan jinjirinta kansa ya gane kurensa a wannan tafiya seda sukayi jinyar gaske ita dashi ga qarin baqin ciki ta tarar Audu baya gari seda taje gidan Turai a kwana na uku bayan taji dama dama sannan ta gaya mata ai sun tafi Legas tareda Ali zasu dakko kayansu. "Karki tareshi da hayaniya kibishi ta siyasa idan kika gano bakin zaren sannan musan abinyi" Turai ta fada mata bayan data shaida mata zancen gidan da Audu ya ginawa su Bara'atu. Haka kuwa akayi, tayi matuqar qoqarin boye tashin hankalinta da damuwa akan Al'amarin harya dawo daga tafiya seda ya kwana biyu ya ware gajiya kafin ta tada masa da zancen ai taga gida akace shiya ginawa su Bara'atu. "Badan Bara'atu na gina musu gida ba nayine saboda Yarana, ya za'ayi ace da raina ban mutu ba a watsarwa da Yayana da uwarsu kayansu a waje bayan ina da halin da zan iya siye garin gaba daya ma ba iyakar gidan da suke ciki ba (kuji fariya). Shiyasa na yanke shawarar yi musu gini na Alfarma irin wanda babu shi a kaf garin da makwafta" ya bata amsa. Binta tayi murmushi a qoqarinta na boye tashin hankalinta tace "Gaskiya hakane amma dai basu kyauta ba suma se kace ba yan uwa ba? Kuma naji ma kamar nace fin qarfi kawai suka gwada musu amma tun Baban nasu yana da rai ya fitar da kowa ya bashi kason kudinsa?" "Oho musu wannan su ta shafa tunda na rigada nayi abinda nayi, gidan ma kuma zan siyeshi na mayarwa dasu Bara'atun se naga ta tsiyarsu ko?" Ya bata amsa, ta zabura se kuma tayi saurin daidaita zama tace "Aiko dai, ka barwa su Bara'atu ko ka barwa su Babangida?" "Ita dasu ai duk dayane kuma duk abinda zanyi mata Alfarmarsu take ci ko iya ruqonsu da takeyi ai tayi qoqari Alhalin ubansu nada rai kuma ina da yanda zanyi" "Uhm hakane, ni da zakayi haquri ma ka yafe abinda ya wuce daka maido su munci gaba da zamanmu kawai hankali kwance. Duk se naji rashin dadi saboda mutane zasuyi ta kallona a matsayin wadda tayi silar raba Yaya da Mahaifinsu" Bintan ta zartar da hukuncin da take ganin shi kadai ne ze datse alaqar Audu da Bara'atu, tunda dai yace saboda yara yake mata komai to gara a kwaso mata yaran suzo suyi ta dabdala a tsakar gida da dai uwarsu tacigaba da morar Audun. Wani kallo ya watsa mata me ma'anoni da yawa fuskarsa ta nuna mamaki qarara yace "Dagaske kike ko wasa? Kina nufin kin yafe mata abinda tayi miki su dawo muci gaba da zama tare?" Seta rausayar da kai ita ala dole gata Allah tace "Abinda ya faru ai ya rigada ya faru na dauki qaddara tunda Allah ya qadarta Yaron bame doguwar rayuwa ko bata silarta ba ze mutu, kuma yara ai basu suka mun laifi ba itan ma kuma na yafe mata Albarkacinsu" "Amma naji dadin wannan magana matuqa in sha Allahu nan bada dadewa ba kuma zan shirya dawowarsu, harkin wankemun baqin cikin abinda ya faru kuma kin qara daraja a zuciyata saboda ba kowa za'ayiwa babban laifi irin wannan ba ya yafe harya cigaba da zama da mutum" Audu ya fada cikin madaukakin farincikin da shi kansa besan dalilinsa ba. Ta maka masa harara a fakaice kafin tace "A kullum burina kenan na faranta maka rai, inda na san wannan ze saka naga farin cikinka haka da tuntuni an aiwatar dashi amma yanzun ma lokaci be qure ba". Daga haka suka tashi daga maganar da kowannensu da kalar manufarsa akan abinda yake fadi. Binta tana maganane akan Babangida da Babannan, su take nufin Audu ya dakko su dawo gidan saboda kar Bara'atu taci gaba da cin arziqinsa ta dalilinsu yayinda shi kuma tasa kwakwalwar ta fassara masa Maganar ta a matsayin ya maido da Bara'atu taci gaba da zama da Yayanta a gidan wannan ne ya sanyashi farin cikin da beyi tsammani ba. Allah ya sani bazeyi qarya ba ba kuma ze iya boye tarin qaunar da yakeyiwa Bara'atun ba saboda ita ya fara so har kawo yau kuma be dena sonta ba Halayen dara tsiro dasu daga baya ne sukayi tasiro gurin ruguza zamansu wanda yake fatan a yanzu ta hankalta ta gane kuskurenta. Abu na biyu daya qara masa jin dadi shine ya san maida Auransa da Bara'atu ze gyara alaqarsu da Yan uwansa data gurgunce musamman Yakubu da Bilki, wannan farin cikin kadai ya hanashi bacci ranar, washe gari kuwa yayiwa Bechi tsinke sedai ya tarar da su Bara'atun har sannan basu komo ba. Izza da girkan kan dai yana nan, ya saka a ransa Mace tayi kadan daya je bikonta, Hayatu Abokinsa ya barwa sallahu akan idan Sun Dawo yaje ya tuntubeta yaji ra'ayinta akan komawa gidansa. "Kai yanzu Audu kana nufin kafi qarfin ka tare ta baki da baki kuyi maganar nan?" Hayatun ya tambayeshi cikin mamaki. "Ga Amsar nan ka bawa kanka ai, ko yanzun saboda Yayana zan mayar da ita bawai dan ta cancanci na maida itan ba" ya bashi amsar da har ransa yasan qarya ya fada. "Ai shi kenan, girman kai dai rawanin tsiya, kuma shi ya halakar da mafiya yawan Magabata" Hayatu ya bashi amsa. https://chat.whatsapp.com/I8xKHGurk7EBf5ZqQdxHKG *MATAR MUTUM* *NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER* *FIKRA WRITERS ASSOCIATION* *LITTAFIN KUDI NE* *PAY 500 A ASUSUN* *7061838488* *OPAY DIGITAL SERVICES* *MARYAM FAROUK* OR *0709290797* *ACCESS BANK* *SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488* *IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705* *Kuyi following dina a Arewabooks @Maryamfarouk01 inda zaku karanta wannan littafin tareda sauran littattafaina* *NAGODE* *PAGE 25* Wasa ya wasa, qaramar Magana ta zama gaske, kamar yanda Audu ya barwa Hayatu sallahu ya isar da saqo dan Bara'atu na dawowa gida ya doma sallama kofar gidansu, ta fita suka gaisa, batayi mamakin ganinsa ba saboda Abokanan Audunna Bechi sukan leqa sa'i da lokaci suga Yaranta. Sukance Audu ya musu rana dan haka bazasu yada yaranshi da suke kusa dasu ba dan idan ka ture halin Audu na Rashin son gaskiya da shegen girman kai yana da kirki, kuma abun hannunsa be rufe masa ido ba daidai gwargwado yana kyautatawa Yan uwa da Abokanansa. Bayan sun gaisa da Hayatun ta tambayeshi jikin matarsa datayi samu da jijjiga lokacin haihu da yake abun a gida ya faru se daga baya aka kaita asibiti abin se yaso ya taba mata kwakwalwa dakyar dai da taimakon Allah aka samu kanta dukda har yanzun dai bata koma yanda take a canbaya ba. Seda suka gama gaishe gaishe kafin ya amayar mata da ainihin abinda ya kawoshi, tayi shiru tana sauraronsa harya gama kafin tace "Shi Audun da kansa ya gaya maka ko kuma aike yayi maka?" "Dakansa yazo lokacin baku gari shineya barmun sallahu akan nazo na tayashi biko da banbaki kafin ya dawo". "Ya yardada gaskiyar ban kashe masa Da ba kenan yanzu?" Ta tambayeshi cikinkar yayyar murya, tausayinta ya kama Hayatun, Bara'atu mace ce me nutsuwa da matuqar haquri, sun taya Abokinsu baqin cikin rasata kuma a cikinsu da akwai wadanda sukayi niyyar neman Auranta se dai sanin waye Audu da tabbacin da suke dashi na cewar be dena sonta ba yasa suka gaza aiwatarda nufinsu saboda Tijarar Audu abar gudu ce tun zamanin yarintama balle a yanzu da karansa ua kai tsaiko. "Bamuyi wannan maganar dashi ba, amma na tabbata a zuwansa baya raba nasaba da warwarewar komai, ta yiwu ya samu gamsuwar cewar baki aikata abinda aka zargeki dashi ba shiyasa ya dawo ku daidaita. Nidai abinda zan iya ce miki kiyi haquri ki mayar da komai ba komai ba ki koma dakinki kodan saboda rayuwar Yaranki. Kowa ya sani Audu be kyauta ba kuma shikeda laifi cikin duk al'amuran da suka faru amma kin sanshi, qi fadinsa baze barshi ya nuna gazawarsa ba sedai na tabbata ko be furta da baki ba zakiga Nadamarsa a aikace dan haka karkiyi wasa sa damar da ubangiji ya baki, kiyi tunani ki yankewa kanki hukunci". Ta koma gida tana ta juya maganganun Hayatu, Inna Hajara bata ce mata komai ba dukda chanjin yanayin da ta ganta ciki se tayi tunanin kodai Hayatun yazo mata da Maganar Aure ne saboda irin zaryar da yakeyi tuntuni tasa tayi tunanin hakan. Har aka kwana biyu da zuwan Hayatu Bara'atu bata sake ba, walwalarta ragu ainun, wani irin cakudadden yanayi take ji na farin ciki, damuwa da kuma zullumi. Farin cikinta Bikonta da Audu yayi domin ba zatayi qarya ba Allah ya sani tana qunar Audu ba kuma ta tsammanin zata iya zama da wani Namiji a duniya ta soshi bayan Audun wannan dalili yana daga abinda yasa zamanta a gida babu marshinshini be wani dameta can ainun ba, Damuwarta kuma tunanin idan ta yarda ta koma wace kalar rayuwa zatayi a gidansa Alhalin Binta tana nan? Zullumin da take ciki kuma shine na tunanin shin Audu ya gane cewar Binta sharri tayi mata ne da har ya nemi ta koma ko yaya? Zata so ta san amsar tambayar nan domin itace zata qara mata qwarin guiwar Amincewa buqatarsa ko akasin haka. Zata so su hadu dashi suyi maganar nan kafin ta kaiga yanke hukunci, "Nikam lafiyarki Bara'atu? Yaro na tsaye kanki yana magana tun dazu kamar me bacci kin masa shiru alhalin idanuwanki a bude suke?" Inna Hajara data leqo daki dalilin maganar Babannan da take jiyowa yana ta maimaita abu daya, Gidan kitso Bara'atun tace yaje ya tambayo mata tunda ya shiga dakin yake fada mata matar tace taje yanzu bataji ba balle ta bashi amsa tayi zurfi cikin tunani har seda Inna Hajar tayi magana da qarfi kafin ta ankare. "Banji shi bane Inna, me kake cewa kai kuma?" Ta fada tana gyara zamanta. Inna Hajara ta shiga cikin dakin da kyau tace "Ai daman ba zakiji shi ba, kai yi tafiyarka wasa, ki fadamun me yake damunki tun randa Hayatu yazo gidan nan na ke lura dake yanayinki ya canza". Barin maganar a ranta baze magance mata komai ba kuma a wannan gabar tabbas tana buqatar Abokin shawara wannan abun yasa ta fuskanci Inna Hajarar ta shiga fada mata yanda sukayi da Hayatun ranar da yazo. Baki ta saki galala tana kallon Inna Hajara wadda ta taqarqare ta rangada guda kafin ta daga hannu sama tana cewa "Allah na gode maka daka sa zanga wannan ranar da raina ban mutu ba, Allah na gode maka daka karbamun Addu'ata. Dama bangaya miki ba? Ba a banza Audu ya jibanci lamuranmu fiye da da ba, tun baroqarki gidansa ban taba yin salla na tashi ba tareda na roqi ubangiji daya bankada sirrin duk wani Azzalimi daya qulla miki wannan mugun shairin ba gashi kuma Allah maji roqon bawansa ya amsa roqon mu. To meye abin damuwar daya kika kasa walwala? Wannan ba abin kiyi rawa kiyi shewa ki godewa Allah ne amma shine kika tsangwami kanki kwana kusan uku bana tsammatar kinyi dariya? Ko kuwa bayan Batun komen akwai wata maganar ne?". "Babu wani abu bayan wannan amma ni abinda ya dameni Inna banida tabbacin cewar Audu ya zabi ya maidani saboda gane gaskiyar abinda ya faru a baya ni nafi kyautata zaton zeyi hakan ne saboda Yayansa. Sannan Inna karki manta har yanzu fa Binta tana cikin gidansa, kina dai ji har ta kori Amaryar da yayi kin kuma ji rade radin da akeyi a gari kan itan ma wata qullalliyar ta qulla mata kenan bata canza zani ba tana nan da halinta babu abinda ya sauya" Bara'atun ta fada a sanyaye cikin karayar zuciya. Inna Hajara ta galla mata harara tace "Ai bari kiji, wlh wannan karon kika kuskura kika tsaya tsoron kishiya yayi tasiri a ranki se kinci ubanki. Ai maciji baya saran mumini a guri daya sau biyu, kin zauna da ita kinsan duk wani salon tuggu da munafuncinta dan haka kema seki shirya irin naki da zaki goga da bata hanyar cuta ko Ha'inci ba. Sannan da kike cewa saboda yayansa ne koma saboda menene dai abu daya ake fata kuma ya tabbata idan baki koma gidansa ba zaki cigaba da zama hakane babu Aure tunda dai kina kallo cikin Garin nan da kewaye labarinki babu inda be ratsa ba wanene ze Aureki? Gidan san dai da kika gogo baqin fentin acan zaki koma ki wankeshi karma ki kuskura naji kin tado da wannan maganar balle har dalilin haka yasa ya janye muradinsa idan ma besan gaskiyar ba. Ko iya komawar da zakiyi ta isa ta karya Alqadarinta saboda ta dauki haqqinki ne saboda tayi silar ki fita daga gidan yanzu kuma Allah ya nufa zaki koma dan haka ma shiri zamu fara, yace da zarar kin amince yana zuwa za'a maida Auranko? To ki aika a kira Hayatun yau ki sanar masa kin Amince, in sha Allahu bazaki rufa qarshen watan nan cikin gidan nan ba zaki koma dakin Mijinki yan hassada da baqin ciki da masuyi mana dariya sedai su mutu Allah yayi abinda basu isa su hana ba". Duk yanda taso fahimtar da Inna Hajara buqatar taja lokaci Audu yazo da kansa su tattauna kafin qulluwar kowacce magana qi tayi, daga qarshe ma takans taje ta samu Qanin Babansu ta sanar masa da cewar Mijin Bara'atu yazo biko bata ko tunanin maganar ta rushe tunda dama ba wani ginuwa tayi ba. Malam Sadi wanda yake cike da wulaqancin da Audu ya musu ya ginawa su Bara'atun sabon gida sannan ya siye gidan da sukaso tozartasu akanshi sedai kuma tsoron Tijarar Audun daya tuna furucinsa na cewar duk seya siye gidajen da suke ciki in suka bata masa rai sanda suka goranta masa cewar meye hadinsa da Bara'atun da har ze siya musu gida? banda Rashin zuciya matar data kashe masa Da ze dawo yana bibiya take ya kora musu gargadi sun kuma san ze aikata domin cefane Bechi yake tayi yana siyan gidaje da filaye tamkar wasu yan tsaki tuna wannan tasa yace babu komai duk sanda suka shirya suzo. Dataga Bara'atu ba zata nemo Hayatu ba dakanta ta tura aka kira mata shi suka qulla magana ba'aja lokaci ba yayi takakkiya yaje ya sanar da Audu abinda ake ciki. "Ashe har yanzu Bara'atu tana sona tana kuma muradin zama dani?" Audun ya fada kamar wani soko sanda Hayatu ya gaya masa yanda ake ciki. Hayatu ya karkace yace "Bana tsammanin haka, domin munyi magana da ita kuma ban fahimci wata alama taso ko muradi a tattare da ita ba se Damuwar data nuna mun ta son sanin ka yarda da ita ko kuwa har yanzu kana mata kallon Mara Imani Azzaluma?" "Bana son maido da wannan maganar tunda har wadda ta zalunta ta yafe mata magana ta qare a gurina" ya bawa Hayatu amsa yana wani dauke kai kamar bashi ya gama shauqi yanzun nan ba, Hayatun ya sake cewa "Kenan har yanzu kana kan bakanka? Dagaske Zuciyarka ta aminta da cewar Bara'atu ta aikata abinda Binta ta zargeka dashi?" Hayatu ya tambayeshi yana tsareshi da ido, seya miqe tsaye yace "Ya za'ayi kazo ka tsitsiyeni kamar wani yaronka kana tambayata? Wannan fa abu ne daya shafeni nida Iyalaina kuma ni nake zaune dasu duk wani wanda ze bayar da shaidar Halin Bara'atu bafa ze kai kamar ni da nayi zaman shekaru sama da biyar da ita ba, ku sanin zahiri kukayi mata ni kuwa na santa har badini dan haka ba ku zaku ringa gayamun abinda zatayi da wanda zatayi ba. Saqo na baka ka isarmun na gode kwarai kuma zan sallameka yanzu In Allah ya yarda cikin zatin da ze kama nima zan shigo garin" ya qarasa yana laluba Aljihunsa ya zaro Rafar Yan goma na Takadda sababbi qal ya irgi dari biyar ya miqawa Hayatun. Girgiza kai yayi cikin tsananin takaicin Audu ya miqe shima yace "Banzo gurinka dan ka bani kudi ba kuma banyi maka abinda nayi shima saboda ka biyani ba nayi ne saboda Allah saboda kuma na daidaita rayuwarka tunda na fuskanci kai baka da alqibla ba kuma kasan ina kakw dosa ba. Abu daya da zance maka shine in har Allah yasa auranka da Bara'atu ya maidu kayi qoqari ka riqeta da kyau dan wlh muddin ka sake yarda Tuggu da makirci yacika ka rabu da ita se kayi nadamar hakan" yana gama fada masa ya fice daga Ofishinsa ya barshi nantsaye da kudi a hannu dan daman a sabon Kamfanin daya bude ya sameshi. *MAMAN MARYAM ONLINE BUSSINESS* *Ina kuke Mata Yan kwalisa , Ina nufin isassun Mata ,Wai shin Kuna da labarin shahararren company nan namu na GHT wato good healthtreatments* *Wanda yazo muku da fitattu Kuma* *ingantatattun suppliment ,na dukkan matsalolin ku*❓ *Ina maisan tayi kyau,irin na isassun Mata ya fitar Miki da shef dinki tayi Miki gyara in and out ,nemi royal jelly dinmu na company GHT* *Wanda aka yishi da xuma ,kundai San amfanin Zuma basai na fada miku ba , hajiya ta kixo ki Yi gyara domin ki kerewa sa,a kije taro ko baki da ko sisi kiji Ana rangada Miki hajiya , saboda yanda Zaki Kara kwarjini ,kina walwali acikin mutane , magungunan ght anti agen ne suna maida tsohuwa* *yarinya ,yarinya Kuma ta koma jaririya* *Muna da magunguna iri iri* *NA GYARAN JIKI* *NA GOGE NANKARWA* *NA RAGE QIBA* *NA CIRE TUMBI* *NA QARIN HIPS* *NA GIRMAN BREAST* *NA QARA TSAHON GASHI* *NA QARIN NI'IMA WANDA ZAI SAUKAR MIKI DA NI'IMA YA QARA MIKI DADI DA ZAQI A GURIN OGA* *Muna da hadin bita zai zai ,indai kishiyar ki tana Shan magungunan GHT, tohh lallai sunan ki sorry domin kuwa tazarar dake tsakanin ku kamar tazarar sama ne da kasa* *Muna da Wanda zai matseki ciki da waje Andai na yayin dinki uwargida*, *Sannan company mu na GHTBai tsaya anan ba* *Ya kawo muku maganin dukkan matsalolin ku* *INA MASU HAWAN JINI?* *INA MASU CIWON ZUCIYA?* *INA MASU CIWON QODA?* *INA MASU CIWON HANTA?* *INA MASU SICKLER?* *INA MASU HIV?* *INA MASU CANCER?* *INA MASU NEMAN HAIHUWA?* *Tohh Ku matso GHT taxo muku da magungunan matsalolin ku* *Kuma muna da testimonys da yawa ,na wadanda suka gwada suka da ce* *Munanan a KANO KUNTAU* *Kuma muna tura Kaya ko wanne gari cikin aminci da gaskiya , kuma kayan mu muna badashi ne cikin price Mai rahusa ga kyau ga inganci sannan ga Rahusa* *Kutuntube mu ta wannan number 📞08129249549* *📲07011401314* Karo na farko da jikinsa yayi sanyi akan bacin ran daya gani qarara kan fuskar Abokinsa koma yace Amininsa. Ya mayar da kudin Aljihu yabi bayan Hayatun da har ya fita farfajiyar gurin ya kwala maaa kira. Dalilin ma'aikata dake kai kawo a gurin ya tsaya, da yawansu duk Yan uwane da qannen Abokanan nasa ya kwaso daga Bechi ya basu aiki se kuma manyan ma'aikata wanda masu kwalayen makaranta ne ya dauka aikin su suke riqe da manyan muqamai a gurin. "Mu koma ciki muyi magana" ya fada sanda ya cimmasa. "Tsayuwar da kaga nayi anan ma Albarkacin wadan nan yaran kaci bazanso su gane cewar kowa kana da Baraka dashi ba" Hayatu ya bashi amsa. Audu ya bata fuska yace "Wai wane irin abu ne wannan? Ni wai a wane kalar mutum kuka daukeni da duk abinda nayi kuskurene kowa ganin baikena yakeyi?" "Ni kuma tsanina da kai ai magana ta qare Alhaji Audu, kayi haquri ma da katsalandan din da na maka bakina da bashida linzami ne ya kasa yin shiru, bari naje kaga Rana da daga zan iya rasa motar komawa gida" Hayatu ya fada daga nan yasa kai ya tafi ya bar Audu a tsaye a gurin. Jiki babu kwari ya koma Ofis ya zauna ya shiga Auna zamansa da Bara'atu da halayenta tareda na Bintan kamar yanda Hayatun ya shawarceshi. Magana ta gaskiya ba tun yanzu ba yayi tunanin abubuwa da yawa da suka faru lokacin zaman Bintan da Bara'atu wanda ya fahimce su dalilin Auran Zubaida. Ya gasgata cewar A bayan idonsa Binta tana cusgunawa Bara'atu tayi amfani da yarintarta da wautarsa tayi wasa da hankalinsa abinda yasa ya fahimci hakan kuwa yanda ta kasa danne Kishinta akan Zubaida kuma har a gabansa bayyanawa takeyi shi kansa dalilin Auran Zubaidan ya fahimci halayenta da yawa da bata bayyana masa su ba a baya se yanzun kuma yaji rashin jin dadin yiwa Bara'atu uzuri a wancan lokacin har ya tsaya ya fahimci gaskiyar abinda yake faruwa ko ya bincika amma maganar mutuwar Zakariyya itace abinda ya gagara tsayar da matsaya akanta. Magana ta Allah shida kansa ya zargi kansa daga baya da yanke danyan hukunci. Ya tuhumi kansa akan kasa bawa Bara'atun kariya koya shaideta saboda ai rainonsa ce, shine mutum na farko daya kamata ya gasgata duk abinda akace tayi ya san kuma tabbas bata da muguwar zuciyar da zata aikata kisan kai amma yanda Al'amura suka kasance a lokacin da yanayin zamansu hade da tasirin maganganun Binta ne suka juyar masa da hankali be kuma tashin gano hakan ba se bayan faruwar al'amarin daya wakana tsakaninsa da Zubaida inda qiri qiri Bintan tayi amfani da Duhun kansa ta ingizashi ruwa wannan ce tasa harya fara tunanin anya kuwa Lamarin Bara'atu ma babu lauje cikin Nadi kuwa? To amma kuma seya tuna Idan sharri Binta tayi mata Ya Za'ayi yan uwanta harda Yaya Sakina su goya mata baya? Gaskiya baya tsammatar ace gaba dayansu sun hada baki akan al'amari irin wannan tilas da akwai qamshin gaskiya a cikin maganar koda ba duka ba. Wannan abin ne har yasa yayarda ze maido da Bara'atun a ganinsa hakan ze wanke laifinsa a gurinta sannan ya daidaita tsakaninsa da yan uwansa qarfin guiwar sa kuma daya samu hadin kan Binta. Kai shi kansa ma ya sake qullewa kuma, Binta ta nuna tana son Bara'atu batayi kishi da ita ba ya auro Zubaida ta kusa haukace masa balahira babu kalar wadda be gani ba sannan yanzu kuma da kanta ta sake cewa ya maido da Bara'atu wai menene hakan ma tukunna? Shine a birkice ko kuwa Binta ce bata da alqibla???? To duk yanda ake ciki madai ya himmatu ze maido Bara'atu, kuma kamar yanda aka saba inya nausa baya jin kira dan haka baya tsammatar akwai abinda zesa ya canza wannan qudurin. Cikin satin ya shirya yaje Bechin, ya tara yan uwansa ya sanar dasu qudirinsa Yakubu da Baballiya ne kadai basa gurin se Hashimu da yace bashida lokacin saurar Soki burutsunsa ba kuma ze yarda dan da aka haifa a gabansa saboda yayi kudi ya zauna yana masa fadanci ba dan haka babu shi akayi zaman Dukkaninsu sunyi matuqar farin ciki da Al'amarin kamar yanda ya tsammata ya san kuma Yakubu se yafi kowa jin dadin maganar har ya qagu yaga farin cikin da zeyi, ya bawa Yaya Baba kudaden daya ware matsayin na sadaki sannan ya sake ware wasu akan a bata tayi shirue shiryen da zatayi. "Aa, wannan ai kai ya kamata ka bata hannu da hannu bamu ba" Yaya Baban ya fada masa amma ya dage akan su hada duka su kai saboda ya shiryawa ransa bazasu hadu ba harse an maida Auransu tukunna saboda gani yake zama ta rainashi idan yaje gurinta yanzu, amma idan yayi haka se abin yayi kamar yan uwansa ne ma suka tursasa dawowartata karma ta gane zumudinsa tazo tace zata rama abinda ya mata. Dasu ka kai kudi kuwa ba'a tashi daga gun ba Mala Sadi yace a shafa fatiha kawai tunda ba sabon Aure bane, a karo na biyu Audu ya sake qullo Aure Binta bata sani ba se bayan daya koma ya fada mata maganar cikin Yaren da ya ke so ta fahimta a sannan cewar "Su Babangida zasu dawo nan da sati biyu". Ta nuna jin dadi da murnarta a fili a zuciyarta kuwa dariyar mugunta takeyi tana shirya yanda zata kwarzabi rayuwarsu a ruwan sanyi kuma ba zata sake bari su koma Bechi ba balle Bara'atu taci Arziqinsa ta silarsu. "Se a gyara musu dakin nan na tsakar gida ko, amma harda Abdullahi zasu dawo dukda dai ya nuna mun ni ba uwarsa bace tunda Bara'atu ta bar gidan nan ko hutu ne sake zuwar mana ba" Bintan ta fadi cikin kissa, Audu yayi murmushi yace "Hardashi duk zasu dawo shi za'a gyara masa dakin tsakar gidan dai tunda yanzu ya zama saurayi su kuma su zauna dakin Mamarsu". Bata kawo komai ba haka bata tambayeshi dawa zasu zauna ba to ina ruwanta? Su zauna dakin su kadai ita bataqi ma wuta ta tashi cikin dare su qone ba kowa ya huta da lissafinsu. Haka aka fara shirye shiryen gyaran tsohon dakin Bara'atu inda kuma Zubaida ta zauna, duk a salon kissa da kisisinar data qaro kwas yasa tayi shiru tana gani ana kankare kankare da liqe liqe har qofofi aka irin wanda aka canza na dakunanta da saman Audun babu jimawa sababbin shigowa na zamani se tayi tsammin ya canza ne saboda gidan duk yayi kala daya. Aka sake fente tsajar gida, ana ya saura kwana uku Bara'atu ta tare su Bilki da wasu yan uwan Bara'atu uku harda Hadiza qanwarta suka zo mata danki na neman magana. Tarkacen kayan jere kadai suka taho dasu dan Audu ya fada musu ze saka mata Gado da Kujeru, Binta na daki tana baccin bayan Azahar suka iso Lantana da Mairo su na tsakar gida, Mairo na kai kawo tsakanin Kitchen da bakin famfo ita kuma Lantana tana daga jikin katanga inda Inuwa ta sauka tana zaro zance wanda duk gulma da tsegumin matan unguwa ne takeyiwa Mairon ita kuwa tafi ki mutu bata ce mata amma hakan be saka tayi shiru ba se zuba takeyi. "Barka barka, baqi mukayi a gidan? Daga ina?" Lantana ta fada tana miqewa sanda su Bara'atu suka shigo da ubannin buhubhuna da suka lodo su kwalla da Samiru. Mairo ma tayi musu sannu da zuwa, ta gane Hadiza a zaman da tayi a gida dukda ta dan qara jiki amma kamanninta basu bace mata ba sannan kuma ga kamannin me gidan a fuskar Bilki hakan ya ankarar da ita cewar daga Bechi suke. "Bismilla ku shiga tana ciki Hajiyar" ta fada musu bayan data gaidasu a mutunce, kafin suyi magana Lantana tayi tsugul tace "Ban gane su shiga ba? Ke haka akeyi kawai daga ganin mutane kice su shigar mata daki kina ganinsu yarkace yarkace da wasu uban buhunhuna kamar yan gudun Hijira qilama mabarata masu neman mafaka ko kinga sun miki kalar qawayen Hajiya balle kice su shiga daki kai tsaye?" "Hayaniyar me akeyi ne haka? Lantana keda su waye?" Binta da subadadin lantana ya farkar da ita ta fada tana leqowa ta tagar uwar dakanta dake cikin tsakar gidan. Tayi sak ganin Bilki wadda suna hada ido ta tamke fuska tam. "Kune tafe cikin ranar nan? Sannunku da zuwa aiko be sanar mun kuna tafe ba ku shigo" ta fada iyakar dauriyarta a qoqarinta na janyo su a jiki da kirki kamar yanda Turai ta bata shawara Bilki kadai ta sani cikinsu ko kuma ta gane tunda tasan Hadiza sedai sanin babu abinda ze kawota gidan yasa bata ma kawo a ranta ta santa ba. Dankwalinta ta shiga nema dan ta fito falo ta jiyo Bilki na cewa "Da yake zuwan namu ba naki bane shi yasa be gaya miki ba, bari mu shiga can mun gode da tayi" daga haka suka ja kayansu zuwa dakin Bara'atun. Bi ta tabi bayansu da harara tareda sakin tsaki kafin ta daure kanta ta fito ranta na suya. Tsabar isa da samun guri ne yasa zasu kwaso jiki rabe rabe suzo mata gida kuma be gaya mata ba ko kuwa shima besan zasu zo ba sannan wadannan uban kwanukan da suke tafe dasu na menene ko daga Kasuwa suke? Take tambayar kanta harta fito tsakar gidan Lantana na tsaye guiwa tayi sanyi saboda yanda taji Hajiyar ta musu magana ya nuna mata sudin ba banza bane kamar yanda ta tsammata. "Ashe baqinki ne Hajiya" ta fada tana sosa kai, Binta ta wuceta tana cewa "Qannen megidan ne" Seko ta dafe qirji ta zare ido, amma data tuna suda banza a gun Binta duk daya se ta dan saki ranta sedai mamaki ya kamata da har Binta tayi musu tayin shiga dakinta, to shiri suka fara haka ko kuwa duk cikin wasan kwaiwayon data fara ne? Binta kitchen din tsakar gidan ta shiga ta tarar da Mairo na kwashe Shinkafar data gama dafawa Miyar na kan wuta tana idasa soyuwa. "Idan kin gama akai musu abinci kafin nan a hada ruwa da lemo idan da Alkaki ki hada musu" ta bata unarni ita kuma ta amsa da "Toh Hajiya". Dakin da suka shigan ta wuce, sun shimfida tabarma cikin kayan da sukazo dasu Mata biyu na zaune Bilki na tsaye taba duban dakin daya qara kyau dalilin sabon fenti da qofofi harda Abun sak kwan lantarki duk aka canza se gurin ya qara haske da kyau. Daga bakin qofar ta tsaya ta aika musu gaisuwa rai babu dadi kamar an mata dole suka amsa banda Bilki data shige daya daga cikin dakunan gurin, Binta tayi kyacci a ranta tana ayyana yanda zataci kan uwarta kafin ta kalli yar dattijuwar da ta fisu shekaru Qanwar Inna Hajara ce tace "Bari a kawo musu ruwa, bamu san da zuwanku ba ai da an muku shiri me kyau" "Ba komai yar nan hakan ma mungode" matar ta fada a ranta tana mamakin rashin kirkin Bintan da ake fada ita dai bata gani ba. "Munafuka" Bilki ta fada bayan ta juya, matar da ake kira da Inna Habi tace "Kai Bilkisu, niko banga abinda kuke fada akan matar nan ba. Yanzu wace macece zata tari dangin kishiya sunzo danki haka?" Mairo ta aje Try data doro su ruwa da Lemo da kayan tabawa, seda ta zabura jin maganar Inna Habin ta kalli Bilki da tayi wata dariyar mugunta tace "Karkiyi saurin yanke hukunci Inna ki dai jira kiga qarshen wasa dan in akayi wasa babu tabbacin ki fita da qafafunki daga cikin gidan nan muddin ta gano wacece ke". Mairo ta hade yawu ta miqe tana gasgata zancen Bilkin tabbas Hajiya bata da wannan baqin Labarin, wato shi Alhaji baya gudun rigima ya ringa zuwa yana daura Aure matarsa bata sani ba dadi daya data ji da taga Alamar Bara'atu ce zata dawo dalilin ganin Hadiza. A can daki kuwa Binta na zaune kan kujera ta harde qafa Lantana na daga qasa suna magana, "Ku tabbatar da basu buqaci komai ba komai suke so a musu, so nakeyi idan sun koma dukda nasan waccen shegiyar ba zata taba fadar Alherina ba amma saura da yau suka fara zuwa dole dai suce na musu Kirki" Bintan ta fadawa Lantana ta miqe cikin rawar jiki tana cewa "An gama Hajiya, kin san dama ni indai Ladabin Kule ne nan na fi kauri laka laka zanwa mutum kamar zan kwanta masa idan ina son abu". Binta ta bita da kallo tana fassara maganarta a zuciyarta kafin taja tsaki a fili tace "Kar nake kallonki ai karki dauka wawiyace ni kice zaki shammaceni". Bajewa su Bilki sukayi suka kwashi Abinci abinsu, Hadiza ta tattaro kwanukan da suka gama dasu ta fito dasu waje gurin wanke wanke ta tarar da Lantana na wanke tukwanen da akayi abincin rana Mairo kuma na qoqarin dora na dare ta aje kwanukan hannunta tana musu sannu suka amsa Lantana ta qureta da ido tana si ta tuna inda ta santa bata tuno dinba Hadizan ta juya ciki. Haka taci gaba da wanke wanken tana ta qoqarin gano inda ta santa haka nan kuma ta tsaya mata a rai harta gama tana maida kwanuka ta kasa haqura ta cewa Mairo "Nikam fuskar matar can batayi miki kalar sani ba?" "Gaskiya Aa, ke kin santa ne?" Ta mayar mata da tambaya se ta tabe baki tace "Oho nidai se na ga kamar nasan me kama da ita, qila kama ce to ko kuma a hidimar gidan nan muka taba haduwa da ita" "Ta yuwu hakan" Mairo ta sake bata amaa tana cigaba da abinda yake gabanta. Daga soro aka rafka sallama, muryar gardi ce Lantana da bata komai taja Gyalenta ta leqa taga Maza biyu da motar kayan katako a qofar gidan. "Yauwa, kiyiwa Hajiyar magana kice ga kaya Alhaji yace a Kawo" wanda da alama shine Direba ya fada mata kafin ta bashi amsa Bilki da ta jiyo sallamar itama ta biyo sahu tana ganin kayan kuma ta gane nasu ne dan haka tace "Ku sauke toh a shigo dasu, ga Almajirai nan su tayaku" "Toh Hajiya" suka amsa mata kafin su fara kiciniyar kwance Belet din da suka zagaye kayan da ita. https://chat.whatsapp.com/I8xKHGurk7EBf5ZqQdxHKG *MATAR MUTUM* *NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER* *FIKRA WRITERS ASSOCIATION* *LITTAFIN KUDI NE* *PAY 500 A ASUSUN* *7061838488* *OPAY DIGITAL SERVICES* *MARYAM FAROUK* OR *0709290797* *ACCESS BANK* *SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488* *IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705* *Kuyi following dina a Arewabooks @Maryamfarouk01 inda zaku karanta wannan littafin tareda sauran littattafaina* *NAGODE* *PAGE 26* "Hajiya wasu Mazane da motar kayan katako, wannan me kama da Alhajin tace su shigo dasu gashi ana kaiwa wancan dakunan" Lantana ta sanarwa da Binta. Mamaki ya kama Bintan, kayan katako kuma na menene? Ta tambayi kanta, to kodai Bilkince zata dawo nan gidan da zama tunda ta samu Labarin a gida take auranta ya mutu? In ko haka ne da anyi tashin hankali da masifa kuwa, ita da gidanta bata san komai ba kawai taga ana shigo mata da kayan gado taqamar tana Qanwar Megida ko? To dashi da itan duk basu isa ba. Fita tayi dan taji ba'asi, a tsakar gidan taci karo da Audu da batasan shigowarsa ba tana ganinsa tace "Yawwa gara da kazo, ban fahimci zuwansu Bilki ba ga kuma wasu kaya da akw shigo dasu na menene?" Fuska a sake ya dubeta bayan daya bawa Direban motar da suka kawo kaya kudi dan har sun gama saukewa yace "Kayan su Babangida ne" "Su Babangida? Su din ne aka siyawa kayan daki se kace na Amarya sababbin Gado da kujeru?" Ta tambayeshi fuskarta na nuna mamakin da take ciki. Tafiya ya farayi zuwa dakin da su Bilkin keta kiciniyar hada kayan yana ce mata "Amarya ce mana, ko bakya so a kwace miki kambunki?" "Audu!" Ta kira sunansa a kausashe tana bin bayansa dan zuwa yanzu kanta ya fara qullewa bata fahimtar maganganunsa. "Ina zuwa, bari mu gaisa dasu Goggo Ramma ki jirani a sama" ya bata amsa daga nan ya shige falon ya barta a tsaye tana saqa da warwara tana jiyoshi da Bilki yana ce mata "Hajiya Bilki Tijjan Bechi" "Kace na qulle jakata bana zan sauke farali" Bilkin ta mayar masa tana ajiye tsumman da take goge goge dashi, yayi murmushi yana tsugunnawa dan gaida Su Goggo Habi ya bata amsa da cewa "Kusan haka, da dai layi za'abi se Yaya Mairo da Amina sunje sannanke amma yanzu kin san ance Albarkacin Kaza qadangare kansha ruwan kasko to kena Albarkacin qawarki bana zaku jera ku tafi tare in Allah ya yarda". Bilki ta rangada gida wadda ta zama kamar saukar guduma a kwakwalwar Binta cikin karadi tace "Nagode dan uwana Allah ya ida nufi, harna hangomu nida Bara'atu muna zagaye Ka'aba ya ubangiji ka nuna mun wannan rana" suka amsa matada Amin gaba daya. A mutunce suka gaisa kafin ya fito ya ganta tsaye a gurin har sannan, "To muje" ya fada mata se kuwa ta bishi kamar raqumi da akala zuwa saman nasa. Zukudi tayi tana kallonsa tareda sauraron abinda yake cewa, "Nasan ko a baya bakida matsala da ita, akasi aka samu akan abinda ya faru wanda da bakinki kika furta kin yafe har kika nemi dana dawo da ita kuma nayi matuqar jin dadin hakan, ina fatan zamanku ya canza salo a wannan karom dan zanja mata kunne sosai akan kar a kuma maimaita abinda ya faru a baya". Murmushi yake yi irin rai fes din nan harya gama maganar, Binta data zama kamar wata hoto se idanu ke motsi suna yawo tsakanin fuskar Audun da bakinsa, so take ta lailayo Ashariya me maiqo sannan ta tambayeshi a gidan kut***r uban wa tace ya maido da Bara'atu sannan dawa yake zaton za'ayi zaman lafiya sedai bakinta ya mata nauyi, bata iya koda motsawa ba seda ya miqe yana mata sallama kan ze koma Kamfani, takun saukarsa daga matakala ne ya farkar da ita daga suman zaunen da tayi ta zabura ta miqe sedai kafin ta kai ga sauka harya fice daga gidan dan tana kaiwa soro taji qarar Motarsa ya bar qofar gidan. Zaman dabaro tayi ta dora hannu biyu a kai ta zunduma ihu kamar wadda aka aikowa da mutuwar Mahaifinta su Lantana da Mairo suka zaburo dan ganin menene, a dakin Bara'atu ma goggonninta biyu sun niyyaci fita banda Hadiza da Bilki da suka san za'a rina Bilkin ce ta dakatar dasu tana dariya ta cewa Goggo Habi "Kinga abinda nake gaya miki ko? To yanzu aka fara, Hadiza rufi mana qofar nan dan ba hankali ne da ita ba se ta fado mana be kuma kamata mu biye mata ba dan ko gaban shari'a akaje mu za'a bawa laifi saboda gidanta muka zo" "Hakane" Hadizan ta fada tana tura qofar ta rufe kamar kuwa sun san nan ta nufo dan zabura tayi kamar zakanya ta durfafi dakin tana kuka tana koro ruwan Ashariya tamkar zararriya ta shiga jijjiqa qofar da niyyar cirera sedai ko Gezau. "Wallahi tallahi na rantse da girman Allah in baku bude qofar nan ba sena babbake ku a ciki, sena nuna muku ki qananan yan iska ne, ni za'ayiwa haka?" Ta fada cikin qaraji tana cigaba da bubbuga qofa. Dattijai biyun suka tsure, Goggo Habi fadi take "Me gado a bude qofar nan karta qona mu kinji abinda take cewa" "Kyaleta Goggo duk kurarin banza ne baki ne da ita babu abinda zata iya a aikace wanda zeyi abu ai baya fada" Hadiza ta bata amsa, Bilki dai bata tanka ba se jera samiru takeyi abinta tana yan waqoqi tamkar ma bata jiyo hauka da Tijarar da Binta takeyi a tsakar gida. Iyakar masifa, bala'i da duk kalar Ashar wata ma a Bakin Bintan goggonnin Bara'atu suka fara jinta yau seda kamar yanda Hadiza ta fada kurarin banza take dan data gaji da buga qofar gefe ta zube tana kuka kamar me tana maganganu da cin Alwashi kala kala. Mairo data ga abin bana qare bane ta koma kan aikinta ranta duk babu dadi da wannan al'amari, ita kuwa Lantana tana nan tsugunne daga gefenta tun bayan data samu tsarabar hambari a qoqarinta na riqeta ta gwabje mata fuska daga nan ta matsa gefe amma taqi tashi daga gurin se fadi take "Kiyi haquri Hajiya, ki tashi mu koma can daki kisha ruwan sanyi" "Se naci "gi***n du***in uwarki Lantana idan kika sake cewa nayi haquri, Allah ya tsinewa haqurin kema Allah ya tsine miki" ta fada dole Lantana taja baki ta kame tana sosa fuska dan inda ta mangaretan har sannan be dena mata zafi ba tsabagen neman gurin zama da iya gulma yasa take zaune a gurin har sannan. Binta na kuka wiwi kamar Jifa se ga Turai ta shigo gidan ita da wata mata, tun daga qofar gida ake jiyo ihu da kururuwar Bintan dan haka cikin sauri suka shigo dan ganin me yake faruwa. "Na shiga uku ni Amina, me ya faru? Waya mutu Binta?" Turai ta fada tana nufar qawar tata da ta ke nan zaune kamar kayan wanke ta miqe qafafu kanta ya tuje dan tun fara Tijarar tata dankwali ya cire. Qoqarin kamata ta shigayi danta miqe amma ta kasa saboda yanda ta saki jiki ita aba ba kadab ba ganin Turan kuma yasa ta sake sakin wani kukan me ban takaici kamar wata yarinyar goye tana fadin "Na shiga uku Turai Audu ya kasheni, wai Bara'atu ya mayar be gaya mun ba" "Har naji sanyi a raina ashe ba mutuwa akayi ba, dan Allah kama jikinki ki miqe, Zainab zoki tayani mu dagata" Turai ta fada jin abinda Binta tace. Dakuar da sidin goshi bayan sun hadu su uku harda Lantana suka kai Binta daki se sannan ma suka tuna da Yaron da suka baro a daki ya fado daga Kujerar data kwantar dashi yana ta tsala kuka gwanin Tausayi. "Dauke shi Dan Allah kuje waje ki rarrashe shi" Turai ta fadawa Lantana, ta dauke Nazirun tayi waje dukda ba haka taso ba, so tayi taji komai dukda ta tsinci kan zancen amma zata so ayi komai a gabanta yanda zata fi jin dadin bata labari idan ta fita. "Yanzu saboda Allah me kikayi haka? Akan wata baquyiyar Bara'atu shine kika kwanta tsakar gida gaban masu aikin ki kina tumami kamar wadda ta kwace daga Turu wani irin abin kunya ne wannan Binta?" Turai ta fada cikin fushi. Binta dake kuka tace "Ki qyaleni, saboda ba'a taba miki kishiyar nan bane shiyasa duk abinda nayi kike daukarsa shirme ke kinsan zafin abin ne balle ki gane yanda nake ji?" "Koma menene, kome kikeji be kai ki zauna kina zubarwa da kanki mutunchi ba a samu abin fada akanki, wannan haukan da kikayi wlh Allah yasan inda ze tsaya dan wannan munafukar me aikin naki kina kallonta kinsan nadar rahoto takeyi. Allah na tuba ba Bara'atu ba ko mata uku Audu yace ya daura aure dasu ya kai ki kwanta kina kuka akai balle Bara'atun da ko kashin jikinki ya fita a gurinki, har meye abin tashin hankali a matar da kika san idan kinga dama ko ruwa ba zaki barta tasha da dadi a cikin gidan nan ba. Kika kara da Zubaida ma kika koreta balle Bara'atu karan kada miya? Dan Allah karki bada ni mana, a gaban Audun kikayi wannan haukar ai kuwa kin kashe kanki kin ruguza duk wani shirinki na baya da wanda ya kamata muyi a gaba wlh murus kin kashe kanko a gurinsa". A hankali ta fara rage kukan da take tana kallon Turai alamar sonjin qarin bayani, ta yaya ta kashe kanta a gurin Audu ta ruguza shirinta ma baya dana yanzu?" "Wai ma tukunna, ta ya akayi har ya maida ta baki sani ba?" Turai ta jefa mata tambayar, taja Dankwalinta da aka tsinto mata a Soro ta face majina kafin ta shiga bawa Turai Labarin yanda sukayi kan zancen maido da yara sa dalilinta nayin hakan har zuwa kan zuwansu Bilki da maganar da sukayi dashi dazun. "Tirqasa, au yanzu suna cikin gidan nan kikayi wannan abin kunyar gaskiya Binta baki haduba kwakwata kin bada ni wlh sauqinta daya be ga wannan qaramin haukan naki ba dan wlh da ace yana nan kikayi shikenan kin gama yawo babu wata fankama da zaki sake yi masa ya yarda" Turan ta sake fada kafin ta muskuta tayi qasa da murya taci gaba da magana. Se bayan sallar Isha'i su Turai suka bar gidan bayan sun tattauna batutuwa da yawa da Bintan tareda matar da suka zo tare, jan kunne tayi mata sosai akan abinda suka tattauna ta fito ta rakosu zuwa sannan zuciyarta ta danyi sanyi kadan. Ta kalli dakin Bara'atun ta ciji yatsa, ta ci Alwashin seta gwammace mutuwarta da dawowa gidan Audu, zaman da sukayi a baya sharar fage ne yanzu ne zata nuna mata Asalin ita din wacece ta shayar da ita ruwan azabar da ko kallon inda Audu yake aka ce ta yi ba zata yarda ba. Tana tsaye tsajar gidan bayan ta rakosu Turai Bilki ta fito sukayi wa juna kallon tara saura ta wuce Abinta bakin famfo ta bar Binta da jan qwafa. Kaf setaci uwarsu wlh a sannu zatayi maganinsu. Se yanzu kam taga baiken kanta data kasa riqe kanta tayi shirmen dazu ai su Bilkin zasu qara rainata su tafi da ita a baki amma ta gode Allah da batayi a idon Audun ba. Tana hawa Barander yayi sallama, ji take kamar ta qunduma ashar a maimakon amsa masa amma ta dake iya dakiya ta amsa sedai bata iya ta tsaya ba balle ta juyi ta masa sannu da zuwa ta shige daki tana jiyo shi suna magana da Bilki kusan minti biyar kafin yabi bayanta. "Uwargida ran gida ko Amarya zance?" Ya tsokaneta yana zama akan kujera tace "Uhm" kawai tana cirewa Naziru Nafkin. "Yau sarautar ta motsa kenan?" Ya sake sako mata wasa ta daure ba tareda ta kalleshi ba tace "To kai ya ka gani?" "Ras" ya fada kafin ya laluba Aljihunsa ya zaro wata Farar Embelop me dan girma ya miqa mata se sannan ta kalle shi ta saka hannu ta karba tana budewa, Awarwaro ne guda hudu a ciki na zinari, ta hadiye yawu Aljanunta na son abin duniya suka motsa. "Tukuici ne, ko ince sadakin fadar kishiya ne" Audun ya fada. Maganar Turai ta dazu ta fado mata da tace "Ki kwantar da hankali kiyi masa laka laka irin yanda kikayi sanda kika shigo gidan, kina kallon dai wahalar da kikasha lokacin daya Auro Zubaida ta isheki ishara kisan tashin hankali ko masifa ba zata biyar da Audu ba sedai lallashi da kwantar da kai ta hakane zaki moreshi sannan ki samu biyan buqatarki to tabbas ta fara ganin gaskiyar hakan. Dake taga abin duniya se gashi harda yi masa murmushi tace ta gode. Ta goye Naziru suka wuce dakinsa tare, ya shiga ciki ya watsa ruwa kafin ya fito ta shirya masa abinci a ranta tana lissafin abubuwan da zata nemi yayi mata yanzu da yake neman shiri da ita. Yana cin abinci yana mata zancen ai jibi Bara'atun zata tare kuma su Bilki zasu zauna nan harse tazo kafin su koma Bechi haka ta ringa daurewa tana yaqe duk a qoqarin ta na amfani da hudubar Turai na karta bari ta canza masa tunani akan wanda yake mata game da Bara'atu ta hakan ne zata sake korata a ruwan sanyi ba tareda ya zargeta ba. Kwanaki ukun da su Bilki sukayi a cikin gidan sun zamar mata kwanaki mafiya baqi da muni a rayuwarta. Idan ta tuna wai Bara'atu ce zata dawo mata gida se taji kamar ta shaqe kanta ta mutu kawai ta huta da takaici, ranar da zata tare din kuwa tun farar safiya yana fita itama ta fice gidan Turai dan bata da sama da ita a Kano wuni guda suna qulle qullen sharri na yanda za'ayi bata komo gida ba se bayan sallar Magriba lokacin ta tabbatar da su Bilki sun tafi idan ma Bara'atun tazo da yan rakiya duk suma sun koma inda suka fito. *MAMAN MARYAM ONLINE BUSSINESS* *Ina kuke Mata Yan kwalisa , Ina nufin isassun Mata ,Wai shin Kuna da labarin shahararren company nan namu na GHT wato good healthtreatments* *Wanda yazo muku da fitattu Kuma* *ingantatattun suppliment ,na dukkan matsalolin ku*❓ *Ina maisan tayi kyau,irin na isassun Mata ya fitar Miki da shef dinki tayi Miki gyara in and out ,nemi royal jelly dinmu na company GHT* *Wanda aka yishi da xuma ,kundai San amfanin Zuma basai na fada miku ba , hajiya ta kixo ki Yi gyara domin ki kerewa sa,a kije taro ko baki da ko sisi kiji Ana rangada Miki hajiya , saboda yanda Zaki Kara kwarjini ,kina walwali acikin mutane , magungunan ght anti agen ne suna maida tsohuwa* *yarinya ,yarinya Kuma ta koma jaririya* *Muna da magunguna iri iri* *NA GYARAN JIKI* *NA GOGE NANKARWA* *NA RAGE QIBA* *NA CIRE TUMBI* *NA QARIN HIPS* *NA GIRMAN BREAST* *NA QARA TSAHON GASHI* *NA QARIN NI'IMA WANDA ZAI SAUKAR MIKI DA NI'IMA YA QARA MIKI DADI DA ZAQI A GURIN OGA* *Muna da hadin bita zai zai ,indai kishiyar ki tana Shan magungunan GHT, tohh lallai sunan ki sorry domin kuwa tazarar dake tsakanin ku kamar tazarar sama ne da kasa* *Muna da Wanda zai matseki ciki da waje Andai na yayin dinki uwargida*, *Sannan company mu na GHTBai tsaya anan ba* *Ya kawo muku maganin dukkan matsalolin ku* *INA MASU HAWAN JINI?* *INA MASU CIWON ZUCIYA?* *INA MASU CIWON QODA?* *INA MASU CIWON HANTA?* *INA MASU SICKLER?* *INA MASU HIV?* *INA MASU CANCER?* *INA MASU NEMAN HAIHUWA?* *Tohh Ku matso GHT taxo muku da magungunan matsalolin ku* *Kuma muna da testimonys da yawa ,na wadanda suka gwada suka da ce* *Munanan a KANO KUNTAU* *Kuma muna tura Kaya ko wanne gari cikin aminci da gaskiya , kuma kayan mu muna badashi ne cikin price Mai rahusa ga kyau ga inganci sannan ga Rahusa* *Kutuntube mu ta wannan number 📞08129249549* *📲07011401314* BARA'ATU Gaba daya komai daya faru ya ringa mata tamkar fim, sanda ta samu labarin an mayar da auranta da Audu daga zuwa kai sadaki rasa tantance me zatayi tayi se kawai ta shiga daki ta kulle ta kwanta kan Katifa tayi shiru ta bar Inna Hajara da yan uwanta dake ta murna a tsakar gida. Ita kadai take hangowa kanta makomar rayuwarta, su murna sukeyi amma ita tasan meta baro a gidan Audu wanda bata fatan ta koma ta tarar. Sannan abinda yake qara sanyaya mata jiki yanda har kawo lokacin bata saka Audu a ido ba dukda ta samu labarin yazo yana garin ta dauka kafin faruwar komai zeje su zanta yaji ra'ayinta taji nashi amma se kawai ta tsinci anmaida mata aure babu jin ta bakinta babu komai abinda ko sanda tana budurwa ba'ayi mata ba anya kuwa Audu ne yake son komen nan ko kuwa yan uwansa ne suka tursasashi maida ita? Tayiwa kanta tambayar. Da yammacin ranar Kawunta ya kai musi kudin sadaki hade danashirue shirye da Audun yace a bata tayi, wannanya qara kassara mata jiki harta kasa daurewa ta fashe da kuka domin ta tabbatar da cewar ba ra'ayinsa bane na mayar da ita dole wani ne ya sakashi idan kuwa hakane ta tabbatar seta gwammace kida da Karatu gashi bakin Alqalami ya bushe ballantana tace a koma baya. A sanyaye take komai ga sati biyun da aka saka na kwanakin tariyarta suna qaratowa har sannan kuma bata saka Audu a ido ba, da tayi maganar wa Yan uwanta Hadiza ce kadai ta fahimceta dan Inna Hajara fada take mata akan waita fiya saka damuwa a rai ai babu yanda za'ayi ace dole aka wa Audu ya mayar da ita tunda shi ba yaro bane ba rashin zuwan sa kuma bata san uzurinsa ba kuma dai duk tsiya gidansa za'a kaita idan taje can koma menene zasu tantance. A wannan gabar ita da kanta seda ta ga baiken Innar tata ta kuma fara yarda da abinda ake fadi a gari na cewar kwadayi ne yake Dawainiya da Innar tata. Idanba kwadayin abin duniya ba kowacce uwa tana qoqarin siyawa yar tamutunci a gurin Miji amma ita wannan be dameta ba fatanta kawai ta koma gidansa duk irin rayuwar da zatayi bata sani ba. Cikin wannan zullumi da Taraddadi ta shiryi dawowa gidan Audu karo na biyu a matsayin matarsa. Tsirarun mutane suka rakota ciki harda yan gidansu Audun basu jima ba kuma saboda motar data kawosu yana tsaye ga kuma wadda zata maida su Bilki dan haka suka rankaya suka koma ana ta tsegumin Ina Binta ta tafi basu ganta ba. Bayan sun tafi gidan ya mata shiru dan ita kadai ta taho yaran ance se ta kwana biyu a kawo su a cewar Hadiza tasha Amarci a tado da tsohuwar zuma tukunna, dariya ma maganar ta bata dan bata hango wannan Amarcin da suke fada muddin Binta na cikin gidan nan. Ta fita tsakar gidan ta tsaya tana qarewa ko Ina kallo, gidan na nan yanda ta barshi se yan canje canje na kwalliya da fenti da aka sakeyi masa yanda ko ina yake shiru cikin Aminci a ranta tayi fatan ina ma gurin ya dawwama a haka? Ina ma rayuwarsu ta baya sanda suke zaune a daki ciki daya a Bechi ta dawo? Har akayi sallar Magriba babu Binta babu Audu, bayan tayi sallah ta gyara kwalliyarta, babu laifi ta qara jiki akan shekarun baya da take gidan dukda ba qiba tayi ta azo a gani ba amma ta murje, yanayin ta dai na Shiru shiru da sanyin jiki yana nan wanda halittace canzashi da kamar wuya, a bangaren wayo ko ace wayewar kai ma babu wani cigaban Azo a gani data samu domin shekaru kusan hudun a Bechi tayi su ta sake komawa duhun kan data baro, mutanen da taci gaba da mu'amala dasu sune dai wanda ta sani tun yarintarta babu wani sabon Ilimi ko wayo data qaro ita ba Makarantar Boko ta shiga ba balle Islamiyya kullum tana zaune a gida kwalliya kanta ba yi takeyi ba Hadiza ce tayi qoqarin ganin ta saitata tayi gyara ciki da waje a dan taqin kwanakin da aka saka na tariyar tata, ita da yake yanzu a cikin Kumbotso take aure babu laifi kanta ya waye fiye da Bara'atun dukda daman tun Asali ba zubinsu daya ba dan da ace Hadiza ce ta samu damarda Bara'atu ta samu ta auran Audu tabbas ba Binta ba kowacce Macece zata iya karawa da ita. Seda aka fara kiraye kirayen sallar Isha'i taji motsin an shigo gidan, ta taga taga wucewar Bintan,gabanta ya yanke ya fadi har seda ta dafe ta shiga karanto Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, fargaba da razanin da ta ke shiga duk sanda ta ganta a baya irinsa takeji a yanzu ta rigada ta tsorata da Bintan Allahya sani. Tana cikin wannan halin aka sake shigowa wannan karon Audu ne shida Musbahu. Faduwar gabanta ta ninku tana jiyoshi suna magana dan bata iya leqawa ma ta ganshi ba harya sallami Musbahun taji alamun tafiyarsa yayi can gurin Binta kafin ta iya sauke numfashi. Tana cikin sallar isha ya shiga dakin, ganin tana sallar yasa ya fita bayan ya fada mata sallahun ta sameshi a falon Bi ta idan ta idar haka ta ringa taraddadin taje ko kar taje bayandata idar da dallar daga qarshe dole ta miqe, babu wani sauran magana ta rigada ta dawo cikin gidan nan abu biyu ne kodai ta tashi ta kwatarwa kanta yanci ko kuma rayuwarta ta qare cikin tsoro da firgicin Miji da kishiya. Tana tafe sallaf salaf a ranta tana kewar Balaraba, qila basu san ma an mayar da Auran nasu ba tasan da tana nan data qara mata qarfin guiwa dan duk sanda sukaje Bechi idan taje gurinta maganar kenan take mata ta tashi ta kwatarwa kanta yanci wannan sanyin Jikin babu inda ze kaita. Da sallama ta shiga falon kanta a qasa bata zauna ba har seda ya bata umarni ta dan dofana kan kujerar data fi kusa da ita. Maganganu yayi musu dan ba za'ace Nasiha ba wanda kusan duka jan kunne ne ga ita Bara'atun akan abubuwan da suka faru a baya da baya so a sake maimaita irinsu ya kuma tabbatar mata da cewar Binta da kanta ta nemi daya maido da ita har yana fada mata a wannan karon itace qasa da Binta dan haka ta bata girmanta na kasancewarta Gaba da ita a aure da kuma shekaru. Yanda ya ringa maganar gaba daya se taji ta muzanta ta kuma gasgata tunaninta na cewarba ra'ayin kansa bane wani ne ya sakashi ya maido da ita amma me yasa duk cikin mutanen se Binta? Meta shirya? Wace kitimurmurar take so ta sake hada mata data nemi a maido da ita iyakar Taskun data sakata a baya be isheta ba kenan? Ya gama maganarsa ya basu damar me magana tayi, Binta da kanta ya gama fasuwa da yanda ya nunawa Bara'atun ita ba komai bace yanzu a gurinsa, taji ina ma haka ta kwantar da kai lokacin daya auro Zubaida tabbas da martaba da qimarta a gurinsa ta zarce ta yanzu amma hakan ma babu laifi zatayi duk iyawarta ta sake kafa kanta. "Nidai babu wani abu daga gurina, Bara'atu daman tun asali yar uwa na dauketa ba kishiya ba ina fatan kuma itama wannan karon zata saki ranta ta zauna dani zuciya daya, sannan kafin a kai ga maganar rabon kwanaki akankwana uku da zakayi mata na qara muku sati kunga kwana Goma kenan saboda kuji dadin Amarci sosai a tuna baya" Bintan ta fada cikin kissa. Wata dariyar Bosawa Audun yayi, Ita dai Bara'atu kanta yana qasa, to me zata ce musu kuma? Tana jinsu suna ta soki burutsunsu shida matarsa kafin aka rufe taro yace taje yana zuwa. Bata tsammaci zuwansa da wuri ba se gashi ko minti goma bata rufa da komawa ba ya shiga da ledar kayan Marmari da kaza. Washe gari haka ta tashi mamaki na neman kasheta, wato Namiji ko, Namiji duk wadda taci laya akansa ta shigenge. Irin yanda Audun ya ringa mata rawar jiki yana fada mata kalamai jinsa kawai ta ringayi, haka da safe be fita ba, Binta da ta kusa hadiye zuciya cikin dare ta mutu saboda baqinciki da kishi amma tun farar Asuba ta tashi ta hau aikin da babu lada domin ba dan Allah tayi shi ba. Lafiyayyen abin kari tayi musu ta kai qofar dakin Bara'atun ta kwankwasa kafin ta ajiye dan ba zata iya shiga ba zata iya manta shiri takeyi ta bazara komai gayyar ta watse. Haka ta ringa musu wannan kabakin arziqi harna kwana uku kafin ta kasa cigaba, yanda Audun ke rawar jiki akan Bara'atun ya tassama haukatata. Ita dashi yake ce mata daya san ze samu wannan kwanciyar hankalin da nutsuwa a gidansa da Bara'atu ya maido a maimakon ya Auri Zubaida har yana tambayarta me yasa bata kishi da Bara'atu amma lokacin Zubaida taqi kwantar da hankalinta? Ta rasa amsar da zata bashi, ba abin ta daddana masa Ashar ba se kawai tace saboda ita Bara'atu a gidan ta tararda kuma Zubaida ba wai kishi da ita takeyi ba kawai Asalinta ne be mata ba da ace itama a gaban Iyayenta ya aurota tamkar Bara'atun da lafiya lau zasu zauna. Ango Audu dai ya ci karensa babu babbaka ya murji soyayya yanda ya kamata shi da kansa ya tabbatar da akwai banbanci tsakanin Abinda zuciyarka ce take sonsa da kuma wanda wani dalili yasa kake tare dashi. Bazeyi qarya ba yana son Bara'atu, haka Zubaida da kansa ya ganta yaji yana sonta har kuma yanzun da da dama ze maidata itama suci gaba da zama yanda yake jin su biyun a zuciyarsa Binta bata kama qafarsu ba amma kuma ya rasa yanda akayi ta fisu tasiri a ransa, yafi girmamawa da daukar maganarta fiye da tasu menene dalilin hakan? Seda ya kwana uku cif yana hutun Angwanci kafinya koma fita aiki a ranar kuma Binta ta sauke hau din data dorawa kanta ta yi mush girki ta bar Mairo taci gaba. Baqin cikin data qunsa a kwanakin Allah yayi yawa dashi tana nan kuma tana jiran ranar ramuwa kwanaki goman nan cif su ta bawa Bara'atun matsayin kwanakin farin cikinta a gidan daga nan kuma wasan ze canza salo. Kamar yanda ta qudurta kuwa haka ce ta kasance kwana goma Audu yayi a dakin Bara'atu wadda zata iya cewa kwanaki goman nan sun zarce shekaru goma na rayuwarta dadi dominbata taba sanin dadin Aure ba a zaman da tayi da Audu kamar na wannan kwanakin. Ya shayar da ita madarar qauna tarairaya da soyayya ba'a magana gaba daya ya goge mata hadda ya kuma goge duk wani shakku da take dashi akansa na cewar ya dena sonta ko yana da wata manufa akan maidota da yayi, walwalarta ta qaru har wani kyau da sheqi ta qara kana ganinta kasan hankalinta a kwance yake Yanda kuma Bintan take sabgogin gabanta bata shige mata irin na wancan karon yasa ta fara tunanin da gaske ta aje makaman yaqinta zasuyi zamane na babu ruwan kowa da kowa wanda zata so hakan. Randa Audun ze bar dakinta zuwa na Binta har kuka ta masa ya ringa rarrashinta akan kwana biyu ne kacal ze dawo sannan a qarshen satin zasuje su dakko su Babangida ma su dawo gida a saka su a makaranta dan Zakariyya ma za'a dawo dashi duka za'a hadasu a kaisu makaranta me kyau wannan yasa ta dan rage damuwa. Lafiya lau yayi kwanaki biyunsa dakin Binta randa ya dawo matasuka tafi Legas wanda tafiyar tazo mata a bazata ce mata kawai yayi ta shirya zasuje wani guri ta dauki kaya kala biyu farko ma ta dauka Bechi zasuje seda ta ganta a filin jirgi ta shiga zare ido, yau gata zata hau jirgi itama bata sake tsinkewa ba seda suka sauka yace mata Legas sukazo ta ringa tsalle kamar yarinya kamar wasa se gasu a gidan su Yakubu. https://chat.whatsapp.com/I8xKHGurk7EBf5ZqQdxHKG *MATAR MUTUM* *NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER* *FIKRA WRITERS ASSOCIATION* *LITTAFIN KUDI NE* *PAY 500 A ASUSUN* *7061838488* *OPAY DIGITAL SERVICES* *MARYAM FAROUK* OR *0709290797* *ACCESS BANK* *SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488* *IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705* *Kuyi following dina a Arewabooks @Maryamfarouk01 inda zaku karanta wannan littafin tareda sauran littattafaina* *NAGODE* *PAGE 27* Da murna tayi musu yawa ita da Balaraban se kawai suka fasa kuka, Yakubu ko bakinsa ya kasa rufuwa, Audun ya shammaceshi dan besan duk abinda ya faru ba wannan abun da yayi kuma ya saka ya wanke duk fushin sa da yake damfare a ransa yaji matuqar dadin ganinsu ko ba'a fada ba kuma yasan hankalin kowannensu a kwance yake. Aka ringa hirar yaushe gamo, A gidan sukayi kwanaki biyunsu dukda Audu yaso su kama Hotel tunda gidan qarami ne dakuna biyu ne daga nasu Yakubun se na yaransu amma Yakubu yace dole su zauna haka baquntar kwana biyu dai haka suka dawo Kano cike da kewa dan kwanaki biyun ba qaramin dadi yayi musu ba sun fita yawo har bakin ruwa sukaje aka musu hotuna Audu be taho ba seda aka wanke musu hotunan suka taho da kwafi dinsu. A kwanaki biyu ba qaramin Ilimi Balarana ta zazzagawa Bara'atu ba da kuma wanda ta gani da idonta ta koyo, sun dawo ta qudiri niyyar tabuka abin kirki a wannan karon itama, zatayi amfani da duk dabarun data koya mata na riqe Miji, zatayi iyakar yinta yanda ba fata takeyi ba koda ace wani abu ya sake faruwa badai a zargeta da sakarci ko rashin sanin ciwon kai ne ya janyo mata ba. Tafiyarsu Legas ta qara rura wutar bala'i a zuciyar Binta, dukda ya gaya mata kafin su tafi abin ya zafeta matuqa harta kasa jurewa ranar da suka dawo a dakinta ya sauka bata iya shanyewa bata amayar masa da abin da yake cikinta tas akaci sa'a be kulata ba domin shima ya qaro karatun zama da mata, ya san da akwai abubuwan da mace zatayi wanda Kishine yake tunzurasu babu yanda kuma zakayi da ita dole kayi haquri. Watanni uku da dawowar Bara'atu, a hankali kyakykyawan zaman daya fara ginuwa tsakanin Ma'auratan ya fara samun tazgado, salon da Binta tayi amfani dashi a zamansu na farko da Bara'atu shita sake maidowa na cusguna mata ta hanyar bautar da ita da kuma zaginta tareda muzantata sedai a wannan karon ta canza salo ta kuma biyo ta hanyar da a qaramin wayo da Dabarar Bara'atu ba zata iya kaucewa Kaidinta ba. Da farko ta dakatar da Lantana da Mairo daga zuwa aikinsu wanda tayiwa Audu qaryar Lantana sata takeyi mata shiyasa ta koreta ita kuma Mairo ta dakatar da ita ne kawai su ringayin girkinsu da kansu be kyautu ace abincin me aiki ze ringa ci ba bayan yana da mata har biyu sauran Ayyukan gidan ma duk bazasu gagaresu, "Da ze yuwu mu zauna da Maman su Baba mu tsara yanda zamu ringa ayyukanmu kawai ba se wani ya taimaka mana ba. A gidan Yaya Aminu naga irin tsarin ya burgeni kuma hakan ya qara shaquwa da fahimta a tsakanin matansa kana gani duk gidanku babu Kishiyoyi masu fahimtar Juna kamar matansa haka yayansa kansu a hade baka ma iya banbance wannan na waye to nima irin zaman da nake so mu gina a gidan nan kenan duk abubuwan da suka faru a baya su zama tarihi mu tun kari gaban mu" abinda Bintan ta tsarawa Audu kenan cikin salo na zallar kissa da iya hada tuggu. Audun yayi na'am da shawararta kuma yaji dadi, tabbas Matan Aminun abin kwatance ne yanda suke zaune tamkar Dadansu da Goggo Fadi kafin rasuwar Malam Tijjani, haka suka tashi gidansu aiki da komai tare su Dadan su keyi kwana a Turakar megida ne kadai ze nuna maka wadda take da Girki a cikinsu shiyasa shawarar tayi masa dadi yasan kuma Bara'atu ma zatayi Na'am da hakan itama. Sanda ya sanarda Bara'atu hukuncin da Bintan ta yanke na sallamar su Lanatana batace komai ba saboda daman ba ita suke yiwa aiki ba, sharar tsakar gida kadai abinda take mora a aikin nasu tunda ba Girki daya sukeyi ba kamar dai farkon zamansu ne me Miji tayi abinci dashi har gara Mairon tana kama mata wasu abubuwan idan tana girki a Kitchen din tsakar gidan Lantana kuwa kallon Arziqi ma baya hadasu balle aje a ga batun tayata aiki shiyasa sallamar masu aikin bata dameta ba. Anyi kwana biyu da maganar ya tarasu falonsa domin tsara yanda zasu raba aikin gidan, Binta ce da girki ranar tana ta kai kawon hada musu abinci su duka gaba daya harda yaran dan sun dawo Abdullahi ma anyi hutun makaranta yana komawa gida ya samu labarin Innarsa ta koma Kano kwanansa biyu shima ya hado kayansa ya taho Audu da Binta suka ringa masa tsiya. Seda aka qare cin abincin suka sallami yaran suka sauka qasa kafin suka nutsu cikin kujera dan yin maganar data tarasu din. "Dan Allah ya kukaji abincin yau? Har wani dadi ya qara na daban saboda mun hadu Ahali gaba daya munci tare, gaskiya haka zamu ringayi daga yanzu saboda ni daman a gidanmu mun saba tare muke cin abinci gaba daya kaima ai ka sani" ta yi maganar tana kallon Audu se shima ya murmusa ya mayar mata da cewa "Kwarai kuwa, ina fatan kuma wannan hadin kan ya dore" "Nikam daga gurina babu wata matsala ai kamar yanda na gaya maka komai daya faru a baya ya wuce itama ina fatan ya zama haka a gurinta dukda har yanzu dai naga ta kasa sakewa se ta ringa darare jikinta kana kallo fa tunda muka zauna yanzu bayan gaisuwa babu abinda ta qara cewa ta barmu muna ta zuba kamar lalatattun Radiyo" Bintan ta soko Bara'atu wadda kanta ke qasa tana kallon lallen da tayi kwanaki biyu da suka wuce sanda ta karbi girki maganar Bintan kuma bata saka ta dago kota amsata ba saboda ita har yanzun ranta yaqi Aminta da wannan takun na Binta ba kuma taso ta saki jiki da ita ta sake shammatarta irin na wancan karon. "Nikam matsalata dake kenan Bara'atu kin fiya qauyanci kiyi abu wani salo salo kamar mara jini a jiki tsakanin nida Bintan waye baqonki da ba zaki sake a cikinmu kiyi sabgoginki ba?" Audu ya fada yana gyara zama. Seta daga kai ta kalle shi, kalmansa sun mata zafi dan har kwalla ce ta tarun mata a ido, bata da dauriyar zuciyar da zata jure cin mutunchi ko tozarci yanzu zata karaya ta fara kuka banda tsabar wukaqanci ita ze kalla yacewa Baqauya to ya suke shida itan? ai babu me gorantawa wani Asali dan tushensu daya koda yake shi daman be iya maganaba. "Haba kai kuwa ya daga magana kuma zaka fara ce mata yar qauye? Koda yake kunfi kusa ai, Qauyawa biyu, yan Qauyen Bechi" Bintan ta zage su duk su biyun a wasance garan kuwa se ya hau dariya yana cewa shi ba baqauye bane ai baqauye wanda bashida wayewa kenan shi kuwa da yake fes ko haihuwar Birnin ba zasu gwada masa wayewa ba ai ita kuwa Bara'atu abun ya sake qular da ita amma ta hadiye bata ce komai ba sedai ta quduri niyyar yi masa maganar muddin suka kebe, zata gaya masa bata so, karya sake wulaqantata a gaban Kishiya (as if zata iya). "Yanzu dai muyi abinda ya taramu dare yanayi" Audun ya dakatar da wasan ganin Bintan na nema ta wuce gona da iri a wasan nata ta fara tabosu tana cewa wai kaf garinsu banda Yakubu waye yayi Karatun zamani dan shi kansa bata yarda yayi sakandiran ba "Ke kuwa nasan dakyar ma idan kin taba shiga Aji" ta sake takalo Bara'atu wanna yasa ya dakatar da ita danshi basa shiri da raini. Bintan ce dai tayi magana akan tsarin da take ganin zasuyi, Me girki ita zata dafa abinci wa gida gaba daya, zasu hade girkin kenan sabanin da da kowa takeyin nata sauran Ayyukan gida kuma shara da wanke wanke wadda bata da girki tayi harda sharar dakunan junansu sedai idan da wani uzuri ko lalura to dayar na iya daukewa dayar aikinta tsarin Binta kenan. Maganar sharar dakunan Junan tayiwa Bara'atu banbarakwai dukda take Baqauyiya mara Ilimin amma tasan ko a karkarar da suka fito Kishiya bata sharewa kishiya daki sedai idan da lalura ina laifin iya tsakar gida? Tana jira taji Audun yace wani abu akai amma shiru sema jaddada hakan yayi da yace sannan ya juya kanta wai yana tambayarta ya mata ko tana da magana? Taga to me zata ce musu? Ta ce be mata ba su samun abun magana daga shi har matar tasa kenan se kawai tayi shiru suka gama abinda zasuyi ta musu sallama ta wuce se bayan data koma dakinta kuma abin yayi ta damunta, Balaraba ta gaya mata karta ringa barin magana a ranta muddin akan abinda ze cutar da itane, koda za'a ce bata kyauta ba gara ta fada a gyara akan ta bar abin a cikinta ta cuci kanta da kanta to amma tana gudun tayi magana kuma su canza mata ma'ana saboda muddin bada zuciya daya Binta tayi wannan abin ba to tarko ta hada mata so take tace wani abu ta ruftata ciki, haka ta kwana tana saqe saqen me zatayi? Ta yarda da wannnan tsarin ko kuwa dai ta gwada sa'arta gurinnusar dashi rashin dacewar hakan? Bata son fitina ba kuma tason abinda ze sake janyo mata matsala da Binta ko Audu, a baya shiga dakinta na qasa da Minti biyar ya janyo har aka laqa mata sharrin kisan kai inaga yanzu taje shara? A bangaren su Audu kuwa Bara'atun Binta ta gyara zama tana tsiyaya masa Zobo a kofi tace "Se naga kamar Bara'atu bataji dadin maganar da akayi ba" "Kinsan ta ai ita ba'a fiya gane ina ta dosa ba tunda kikaji bata ce komai ba hakan ya mata itama kenan" ya bata amsa bayan daya kurbi zobo. Ba haka taso ji ba dan haka ta sake kalailayewa tana cewa "Uhm haka dai kace amma ni yanayin fuskarta na karanci kwata kwata maganar man bata zauna mata ba, idan lura kuma ai tunda kuka dawo daga Legas din nan tsumewarta tafi tada, kafin ku tafi ai tana dan sakin fuska idan mun zauna irin haka amma yanzu fa sedai tayita sunkuyar da kai tana irga yatsunta kodai har yanzu ta riqe abinda ya faru a baya ne a ranta?" "To idan maganar abinda ya faru a baya ne ai ke ya kamata ki qullaceta ba ita ba tunda ke akayiwa laifi ko?" Cewar Audu, se tayi narai narai da fuska tace "Nima dai hala na gani, nida aka cuta na dubi Allahmace na yafe amma kuma tazo tana so tayi zaman gaba dani idan fa ba a gabanka ba ko gaisawa bama yi bana so ina kawo maka maganarta ne kaga kamar wani abun nake so na hada shiyasa amma wlh sam duk yanda nake so na jata mu zauna lafiya taqi sakin jiki kayi mata magana in dai akan abinda ya faru take tunani dataqi sakewa dani wlh na yafe kuma na manta komai ta saki ranta mu zauna lafiya abinmu mu kama ka ram yanda ba zaka sake hango wata ba balle wannan karon ma ka sake kwaso mana Kara da kiyashi". "Allah sarki Zubaida, aiko kin tunamun gobe idan Allah ya kaimu zanje na dubo su Hassan dukda dai nayi musu aike cikin satin nan amma gara naje na ganosu da kaina" Audu ya fada dan maganarta ta qarshe yasan da Zubaidan takeyi aiko abinda ya fada ya doketa har seda ta kware da Zobon da take sha ta ringa tuttula tari yana mata sannu dakyar ya lafa mata ido yayi jajir ta ringa maida nufashi zuciya na tafarfasa. *MAMAN MARYAM ONLINE BUSSINESS* *Ina kuke Mata Yan kwalisa , Ina nufin isassun Mata ,Wai shin Kuna da labarin shahararren company nan namu na GHT wato good healthtreatments* *Wanda yazo muku da fitattu Kuma* *ingantatattun suppliment ,na dukkan matsalolin ku*❓ *Ina maisan tayi kyau,irin na isassun Mata ya fitar Miki da shef dinki tayi Miki gyara in and out ,nemi royal jelly dinmu na company GHT* *Wanda aka yishi da xuma ,kundai San amfanin Zuma basai na fada miku ba , hajiya ta kixo ki Yi gyara domin ki kerewa sa,a kije taro ko baki da ko sisi kiji Ana rangada Miki hajiya , saboda yanda Zaki Kara kwarjini ,kina walwali acikin mutane , magungunan ght anti agen ne suna maida tsohuwa* *yarinya ,yarinya Kuma ta koma jaririya* *Muna da magunguna iri iri* *NA GYARAN JIKI* *NA GOGE NANKARWA* *NA RAGE QIBA* *NA CIRE TUMBI* *NA QARIN HIPS* *NA GIRMAN BREAST* *NA QARA TSAHON GASHI* *NA QARIN NI'IMA WANDA ZAI SAUKAR MIKI DA NI'IMA YA QARA MIKI DADI DA ZAQI A GURIN OGA* *Muna da hadin bita zai zai ,indai kishiyar ki tana Shan magungunan GHT, tohh lallai sunan ki sorry domin kuwa tazarar dake tsakanin ku kamar tazarar sama ne da kasa* *Muna da Wanda zai matseki ciki da waje Andai na yayin dinki uwargida*, *Sannan company mu na GHTBai tsaya anan ba* *Ya kawo muku maganin dukkan matsalolin ku* *INA MASU HAWAN JINI?* *INA MASU CIWON ZUCIYA?* *INA MASU CIWON QODA?* *INA MASU CIWON HANTA?* *INA MASU SICKLER?* *INA MASU HIV?* *INA MASU CANCER?* *INA MASU NEMAN HAIHUWA?* *Tohh Ku matso GHT taxo muku da magungunan matsalolin ku* *Kuma muna da testimonys da yawa ,na wadanda suka gwada suka da ce* *Munanan a KANO KUNTAU* *Kuma muna tura Kaya ko wanne gari cikin aminci da gaskiya , kuma kayan mu muna badashi ne cikin price Mai rahusa ga kyau ga inganci sannan ga Rahusa* *Kutuntube mu ta wannan number 📞08129249549* *📲07011401314* "Sannu bari na shiga ciki nayi wanka kafin ki gama" ya fada mata bayan da tarin ya lafa mata ya shige daki tabi bayansa da harara tamkar idanunta zasu zazzago. Tashi tayi ta hau tattare kwanuka ta sauka dasu zuciyarta fal da tunani, Wannan shi ake kira goma da Ashirin abu na nema ya hade mata biyu bata gama da wannan yar qauyen ba ya maido mata da zancen Zubaida ashe har aike yake musu yana kuma zuwa ya gansu? Koda yake itace sakarya data manta da ita gaba daya matsalar Bara'atu tasha mata kai ta manta da batun tsinannun Tagwayen can data haifa to yanzu ita ina zata kama? Bara'atun zata bari ta koma kan Zubaida? Ko kuwa bari zatayi seta fatattaki Bara'atu sannan ta dira kan Zubaidar? Tana hada abubuwan da zatayi amfani dasu a dakinsa take wannan lissafin a ranta, ta gama ta dauki ledar data zuba kayan, Nazirun na saman har yayi bacci Zakariyya kuma dasu Babangida zasu fita ya bisu yanzu da bata gama yanke yanda zatayi da Bara'atun ba tana bar mata yaron ya kwana da yan uwansa ranakun girkinta dan haka ta rufe qofarta ta koma Saman Audun tana ayyana matsalar Bara'atu zata fara kaudawa, zata bar Zubaidan tukunna dan tata me sauqi ce take ganin. "Wai ni watannin Yan biyun nawa nawane yanzu?" Ta daure ta tambayi Audun bayan sun kwanta, ya danyi lissafi akansa kafin ya kalleta yace "Kamar Goma kenan ko? Ki lissafa tafiyarki Hajji yanzu watan sama kwanansa goma Azumi saura kwana Ashirin ko sha tara kinga a wata na Tara suke sun shiga na goma" "Haka ne" ta fada daga nan ta maida kai ta kwanta tana ayyana dole ma ya karbosu sannan ya nemo me masa hidima dasu yawwa. Haka dai tayi baccin daren babu nutsuwar zuciya, tunanin yanda zata qulla can ta rushe can kawai takeyi, tana jinsa yana jan minshari hawaye ya silalo mata, kamar ta zabga masa mari taji, duk akansa take wannan fadi tashin. BARA'ATU Washe gari da Audu ya fito ze tafi Kamfani ya shiga yi mata sallama bayan sun sake gaisawa bayan wadda sukayi da Asuba, cikin risilama ta maido masa da maganar jiyan saboda tace tana da magana idan ya dawo yace ta fada sannan babu damuwa. "Se naga kamar dakunanmu sirrinmu ne sannan gyaran daki akwai wanda zakaga yafi so yayi da kansa yafi ganin komai yayi masa daidai kamar dai ni, shiyasa zakaga ko dakinka duk sanda nake ciki se na sake gyarawa koda ace Maman Zakariyya tayi gyaran dan bana jin komai ya mun idan ba da kaina nayi ba" Bara'atun ta fada masa da yanayin da take ganin ze fahimta. Ya ringa jjjiga kai irin ya fahimce ta din nan sannan yace ze yiwa Bintan magana. Seda da dare bayan ya dawo ya ya gama cin abinci ya sanarwa da Binta yanda sukayi da Bara'atun, daman tasha kwanan baqin ciki da yinin takaici dan zancen Zubaida da yayanta ya maqale mata a zuciya yaqi wucewa duk haka ta wuni babu walwala qyashi da hassada ya cikata ta ringa hasaso abinda Audun yake kai musu waya sani ko itama gidan ya gina musu irin nasu Bara'atu tunda itama a gidan Laka suke ga Damuna kar yace ze rufto akan Yayansa. Seda ta gama sauraron Audun tsaf kafin ta narke fuska ta samu mafaka abin kuma yazo a daidai yanda take so dan haka tace "Ka ga magana ta ta fito ko? Jiya mena fada maka? Ai nace maganar batayi mata ba tayi shiru me yasa tuna gurin ba zata fadi nata ra'ayin ba se dai ta jaka gefe ta gaya maka, yanzu ai se aga kamar cutarta nakeyi shiyasa ba zata yi magana a gabana ba. Ni ina so muyi zaman lafiya da ita amma kaga abinda ta bullo dashi a taqaice dai tana nufin ni qazama ce banida tsaftar da zan iya yi mata gyaran daki ashe duk wanda nake maka ma in tazo seta sakeyi shikenan tunda haka ta zaba se mu zuba mu gani nida ita aga wanda ze sare in har tashin hankali take neman kai ka sani na iyashi wlh banda ma Allahya doramun qaunarta da son muyi zaman lafiya da ita meye ze hadani da wata Bara'atu ka bata labarin yanda muka gwabza da Gogaggiyar Karuwa ma balle ita karan kada miya" nan ta fara qoqarin tayar masa da Jidalinta. Audu kuwa yaji dadin zaman lafiya baze so abinda ze tarwatsa masa kan gidan daya fara haduwa ba kuma se yaga zancen Binta gaskiya ne Bara'atu bata so ayi zaman lafiya shiyasa zata bullo da wannan maganar inda taso ayi yanda Bintan tace in yaso duk abinda yayi mata badaidai ba ta gyara daga baya baki alaikum. "Yanzu dai kiyi haquri, zanyi mata magana babu wani tashin hankali ko rigima daze bullo a gidan nan zaku cigaba da zamanku lafiya yanda kuka fara" Audun ya tausheta, se ta fara magana kafinta kai qarshe ta saki kuka tana cewa "Ni idan zan fada maka wani abu daya shafeta ai a gabanta nakeyi bana munafunci me yasa ita se a gefe zakuyi magana ta da ita? Allah kadai yasan me take gaya maka akai na shiyasa naga kwanakin nan duk ka canza mun kuma ko rantsuwa nayi bazanyi kaffara ba waccen me kama da Zabiyar ta gidan Yakubu ce ta zugota zuwan da kukayi to nidai tunda naga alamun hade mun kai zakuyi tunda ita yar garinku ce ni kuma bare gara nasan nayi tunda sauran mutunchina kafin ka kunyatani ace qaramar Yarinya ta koreni daga gidan Miji" "Wace irin magana kikeyi haka Binta? Daga zancen shara seki fara sako wani soki burutsu meye wannnan? bana son irin haka kin sani ko? Bari na kirata to tazo ayi maganar a gabanki zan yanke hukunci kuma dole kowa yabi abinda nace" Audun ya fada yana miqewa se ta tareshi da cewa "Hukuncin me zaka yanke? Bayanta zaka bi ko?" "Se ki jira kiji tukunna" ya bata amsa fuuuu ya wuce kiran Bara'atu. Da gudu Binta ta shige bandaki ta wanko fuska tana qyalqyala dariya, ta gama tsanewa ta murza hoda da Gazal kafin ta ware dankwalinta ta gyara daurin tayi fes abinta kamar ba ita ta gama kuka yanzun ba. Bara'atu na zaune da yara Abdullahi ne yace su kwaso Littattafansu a duba saboda an kusa komawa makaranta saura sati daya. Ba sanin abinda sukeyi tayi ba dan haka tana zaune kan Kujera kawai tana kallonsu tana kuma kwabar wanda taga ze bata littafinsa da zane musamman Zakariyya da ya fiya qiriniya se qoqarin batawa Yayyen littafi yakeyi da fensir Audu ya fada dakin sallama ciki ciki yana muzurai. "Ina son magana dake" ya fada ya juya, tabi bayansa da kallo kafin ta miqe a sanyaya tana tunanin to meya faru kuma? Hijabi ta dora kan Baqar doguwar rigar jikinta ta bi bayansa, shi kadai ta tarar a falon se Naziru dake ta rarrafe a qasa ta daukeshi ganin ya nufi qofar da bata rufe dakyau ba ta zauna kan kujera tana masa wasa yana dariya, satar kallon Audun tayi taga ya tamke fuska yana muzurai zatayi magana kenan Binta ta fito daga daki tana masa magana ganinta yasa ta katse tace "Au kece? Yau kinzo hira da kanki kenan ba tare da an kiraki ba" "Uhm" kawai Bara'atu tace kafin ta gaisheta ta amsa tana zaunawa tana sake cewa Audu "Kaga abin mamaki yau Bara'atu tazo hira damu" "Ni na kirata" ya fada fuska a daure qasan ransa yana mamakin yanda tayi kamar bata san yaje kiran Bara'atun ba, "Koda naji, nidai nasan badai Bara'atun dana sani ba" ta sake fada. Audu ya gyara zama yana kallonsu duka yace "Na gayawa Binta saqonki sedai bataji dadin abinda kika fada ba kuma kamar yanda ta fada abinda kika bullo dashi so kikeyi ki ruguza mana zaman lafiyar da muka fara samu a gidan nan dan haka ni a matsayina na wanda ya ajiye ku duka zan yanke hukunci, kamar yanda muka tattauna jiya magana tana nan zaku ringa ayyukanku kan yanda muka tsara babu wani ja inja ba kuma nason na sakejin wata magana daga kowanne bangare". Abin be wani bawa Bara'atu mamaki ba domin tasan za'a rina wai an saci zanin Mahaukaciya wannan ba sabon abu bane a gurinta kuma yanzu ta tabbatar da zarginta na cewar Binta na nan kan halinta babu abinda ya canza kuma nemanta takeyi da sharri shiyasa ta kawo wannan tsari to amma ba zata zauna ta zama sakarya ba a wannan karon ma, dole ta fadi ra'ayinta koda kuwa Audun zeyi masifa bazata yarda taci gaba da zama yar amshin shata a gidan ba. Ta kalli Binta dake murmushi tana lada qafa kafin ta fara magana ba tareda ta kalle shi ba tace "A gaskiya kayi haquri nidai na yafe sharar dakina zan ringayin abata da kaina kuma ina roqar Alfarmar itama ka daukemun ta dakinta, na yarda ta canza mun da wani abun daban da zan ringayi mata amma banda sharar daki" "Yanzu Bara'atu har kinyi kaurin wuyan da zan fadi magana ki musamun ni zan zartar da hukunci a gidana kice ba haka za'ayi ba?" Audu ya fada a fusace cikin tsawa yana kallonta, bata son fada sannan ya za'ayi a tauyeta kuma tayi magana ya nuna ta masa rashin kunya dan ta nemi haqqinta wannan ya karya mata zuciya Kwalla ta taran mata a ido amma ta kasa magana dan tana bufe baki tasan kuka zata saki, Binta da taji kamar ta taka rawar murna ce ta katseshi da cewa "Haba Yallabai, haba ranka ya dade Allah ya huci zuciyarka ungo karbi ruwa kasha" ta miqa masa ruwa be karba se huci yake yana hura hanci ta sake marairaicewa tana cewa "Haba mana Sadauki ni banga abin bacin rai a maganar nan ba kowaccen mu fa tana da damar da zata fadi ra'ayinta shiyasa tun jiya naso ta bude baki ta fadi abinda yake ranta take yanke da bamu zo yanzu ana bacin rai ba amma dukda haka daman maganar nan nina kawota tunda kuma a maimakon samun daidaito tana nema ta haddasa fitina na janye, zan saka a nemo mun wata me aikin kawai taci gaba da taimaka mun itama idan tana so a samo mata in kuma bata so taci gaba da aikinta yanda ta saba shi kenan magana ta wuce kowa yayi haquri". "Bata isa ba wlh ita tayi kadan ta kawo mun tsarin da zanbi a cikin gidana yanda na tsara haka za'ayi" ya sake fada a zabure, Bara'atu ta kalleshi, yanda yake magana tamkar shiya kawo dokar tun Asali kamar ba Shirin Bintan bane ita ta kawo nata tsarin ya hau ya zauna ita kuma da bada sadaki ya aurota ba saboda ana so ayi mata rashin Adalci taqi shine yake wannan kumfar bakin. "To bari na nemi alfarma, tunda tace abar mata sharar dakinta zatayi ni kuma nawa na canza mata da wani aikin ka barmu mu sasanta a tsakaninmu mana" Binta ta sake fada kamar da gaske sasancin take so ayi. Yayi shiru kamar baze tanka mata ba kafin kuma murya a dake kamar ta Boss yace "Ina jinki". "Yauwa Nawan, yau akwai tukuici na daban ladan wannan Alfarmar daka mun" seta juya kan Bara'atu tace Bara'atu da taja Hijabi ta rufe fuska dan ta kasa riqe kukan daya zo mata qasa qasa takeyinsa tana share hawaye wato dai ranakun baqin cikinta basu qare a gidan Audu ba, maidota yayi ya qara sauke mata buhun hunan rashin mutunchin da be ida sauke mata a baya ba, da sauri ta dago kai jin abinda Bintan take cewa "Kin ga ya dage dole mubi tsarin da aka kawo da farko amma tunda kin nemi a canza, idan kin yarda ni a bangarena a maimakon sharar dakina zaki ringa yimun Wankin kayan Yara ke ma seki fadi abinda zan ringayi miki a madadin taki sharar" ta qarasa tana doka murmushi kamar wawiya. Kasa cewa komai tayi, ta kalli Bintan kafin ta kalli Audu tana jiran taji abinda zece se ji tayi yana cewa "Babu maganan ta zabi abinda zaki mata, sharar dakinta ita tace ta yafe kar kiyi na dakinki kuma wannan da ba zatayi ba kika musanya mata" ya juya kan Bara'atu da tayi fakare tana sauraronsu yace "Zaki ringayi mata wankin kayan yaran duk ranar da baki da girki, My decision is final" aka jefo turanci daga nan ya shige daki ya barsu zaune. "Yanzu wasan ya fara yarinya" Binta ta fito mata a sak ta fada kafin ta miqe tana juya Mazaune tabi bayan Audu tana wata shaidaniyar dariya irin ta wanda ya nisa cikin lamarin duniya. https://chat.whatsapp.com/I8xKHGurk7EBf5ZqQdxHKG *MATAR MUTUM* *NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER* *FIKRA WRITERS ASSOCIATION* *LITTAFIN KUDI NE* *PAY 500 A ASUSUN* *7061838488* *OPAY DIGITAL SERVICES* *MARYAM FAROUK* OR *0709290797* *ACCESS BANK* *SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488* *IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705* *Kuyi following dina a Arewabooks @Maryamfarouk01 inda zaku karanta wannan littafin tareda sauran littattafaina* *NAGODE* *PAGE 28* Kwana tayi tana juyi duk motsi abinda ya faru daren jiyan seya fadomata zuciyarta tayi mata nauyi, idanunta banda radadi babu abinda sukeyi dalilin kukan data sha, Ta rasa a wanne matsayi zata ajiye Audu dan bata ta Binta kwata kwata ta gama sallama mata amma shi Audu fa? Son zuciya ko kuwa qin gaskiya ne yake saka shi aikata abubuwan da yakeyi ko yaya? Me yasa duk hukuncinsa yake kasancewa na son zuciya kuma bisa goyon bayan rashin gaskiya?. Rashin baccin da batayi ba cikin dare yasa ta makara, dakyar ta iya tashi tayi sallah kanta na bala'in sara mata ta koma ta sake kwanciya tana jin yaran na qu qunin Yunwa dan Zakariyya harya fara kuka gashi bata jiyo motsin Bintan ba alamarbata sakko ba balle ta dora abin kari, Audun m yau be leqa su da Asuba yaga ko sun tashi ba kamar yanda ya saba haka daya dawo wucewarsa daki yayi tunda fushi yake da ita kuma yau din Lahadi ce baya fita da wuri daman se qarfe sha biyun rana shiyasa Bintan ta qara samun damar tsula tsiyarta. Abdullahi ta kira tace ya share tsakar gida ya wanke saboda hadari ya taso daren jiya ruwa be sauka ba se Iska ta taho da qura ita kuma ta daure ta hada ruwan wanka ta yiwa yaran kafin Hajiyar gidan ta gama qailularta ta basu abin kari. Tana cikin shiryasu ta jiyo hayagagar Binta ta san baze wuce da Abdullahi take ba. Cikin kayan Babannan ta samarwa Zakariyya wanda suka masa tace su zauna nan bari ta kawo musu abin karyawa ta zura Hijabinta tana qoqarinfita ta jiyo sallamar Bintan a qofar dakinta, tayi A'uziyya a zuciyarta domin Binta ta zarce shaidan kaidi, sanin Audu na gida kuma zata yuwu wani bala'in ta sake zuwa ta hada mata dan haka tayi saurin fita kafin ita ta shigo mata cikin dakin. Faran faran tamkar babu wani mugun abu a ranta ta gaida Bara'atun ita dai daga lafiya ta gagara qara ce mata komai saboda zuciyarta gaba daya ma tsinkewa takeyi, ita dai kaf a karkararsu bata taba ji ko ganin Mace irin Binta ba, to ko daman wannan abin shine wayewar da ake fada? Idan kuwa hakane ta godewa Allah da ta kasance bagidajiya akan ta zamo daga cikin munafukai. "Kuyi haquri na barku da yunwa ko? Bacci ne ya kwace mun yau, Bari in maza ko ruwan shayi ne a tafasa se a soya wainar qwai tunda muna da burodi" Binta ta fada tana murmushi. Cikin sanyi Bara'atu tace "Babu komai ai" ta bata amsa a sanyaye daga nan Bintan ta juya tana murmushin da Allah kadai yasan ma'anarsa. Kusan Minti goma tsakani Binta ta sake dawowa da qaton Fulas din ruwan zafi tun wanda Dada ta bata ne lokacin Amarcin da ake zuba musu ruwan zafi a ciki. Yana da girma ga riqe zafi shiyasa take jin dadinsa sosai. "Sannu da aiki" ta fada sanda ta kabi Fulas din, Binta tayi murmushi ta koma kitchen ta sake kawo mata Farantin data Zubo faya fayen wainar qwai. A babban Jug din da take hada musu shayi gaba daya ta zuba Madara da Milo da Sukari kadan kafinta tsiyaya Ruwan zafinta motsa, ta zubanata a kofi ta zubawa Abdullahi se ta qara ruwan sanyi akan sauran ta dan qara musu Madara da Milo sannan ta zubawa sauran Yaran. Yanda suka rarumi Kofunan duk sunbata tausayi musamman Zakariyya da yake qaraminsu a ranta tace "Wato muguntar harda dan cikinta takeyiwa" tana kallo ya kafa kai yana kurbar shayin a yunwace Babannan yace "Umma Burodi da kwai" "Yanzu zan baka ai uban gajen haquri" ta fada tana tura masa farantin data saka masa Burodinsa da kwan akai sauran ma duk ta miqa musu nasu. Abdullahi yakai kofi bakinsa ya kurbi shayi ba zato Bara'atu taji ya fesoshi da qarfi harya batata, a zafafe ta buga masa tsawa tana cewa "Wane irin wulaqanci ne haka ai kasan shayin da zafi zaka kurba ya qonaka ji yanda ka batani duk ka tsalla mana yawu acikin abinci" Abdullahim dake karkada harshe yawu na dilala dakyar yace mata "Umma ba zafi bane, gishirine a ciki kamar ze tsinke mun harshe" "Gishiri?" Ta fada cikin mamaki, Babangida daya matse fuska yace "Nima da akwai a cikin nawa Umma". Robar da sukari yake ciki ta janyo dan ta tantance ko kuskure tayi gurin daukowa sedau sukari ne a ciki, se kuma ta saka cokali ta dibi shayin gabanta dan kadan ta kai baki ai da sauri itama ta fesoshi jin wani azababben gishiri tamkar an jiqe kwano gida ciki ruwan fulas din to meya kawo gishiri ciki? Kofunan hannun Babannan da Zakariyya wanda qiris ya rage ya shanye nasa ta kwace da alama shi be gane banbancin dandanon gishirin bama. Ta hade su a Jug kafinta miqe a sanyaye ta shige kitchen dinta na cikin daki. A Butar tafasa ruwa ta saka nan da nan yayi zafi bata ko Jira ya tafasa ba ta juyo ta sake hada musu wani zuciyarta ta aminta da cewar da gangan Binta ta zuba musu gishiri a ruwan shayi wai me wannan matar take nema da ita fisabillahi. Bayan sun gama ta tattaro kwanuka ta fito dasu danta wanke sedata hado ma cikin kitchen ta zauna ta fara wanke wanke, Shayin dayaqi shayuwa ta tsiyayar a rariya Ta bude Fulas din zata zubar da sauran na ciki kenan ta ji muryar Binta a kanta tana cewa "Aa, Maman Baba meya faru naga kin sheqar da shayi a rariya?" "Shayi kuma?" Audu sa suka fito tareya tambaya yana kallon rariyar da shayin be gama wucewa ba, "Gashi nan kuwa ka gani hadin kauri kuwa wlh, qila sun hada ya musu yawa ne maimakon ki barshi an jima ki dumamawa yara susha kuma se ki zubar ai Almubazzaranci ne wannan" Bintan ta sake fada. Bara'atu bata iya dagowa ba balle tace wani abu dan wannan Bom din kam tilas ya tashi da ita dan tafi kowa sanin Audu baya son wulaqanta abinci tun zamanin tana ita kadai a Bechi kafin su dawo Kano ko abu ya siyo ze gaya mata idanba zata iya amfani dashi duka ba ta fitar ta bayar kar abarshi ya lalace balle yanzu akan Idonsa ta zubar da shayi a rariya tasan ko Binta bata saka baki ba se yayi fada. "Yanzu saboda wulaqanci abinci zaki wulaqanta haka? Da yayi muku yawa me yasa bazaki bawa Abdullahi ya fita ya bawa Almajiri ba?" Audun ya fada cikin fushi. Murya a sanyaye tace "Kayi haquri ba yawa ya mana ba, kuskure aka samu gishiri ne a cikin ruwan da aka dafa se bayan dana hada mana sannan muka ankare kaga baze shawu ba shiyasa ma zubar" "Gishiri a cikin shayin?" Ya tambayeta cikin sigar rainin wayo irin be kama abinda ta fada ba. Fulas din gabanta ta tura masa tana cewa "Dama ba zaka yarda ba amma ga sauran ruwannan ka dandana kaji" "Ikon Allah a garin yaya gishiri ya shiga ruwan shayi? bari muji" Binta ta fada tana dauke fulas din cikin mugunta datayi kama da kuskure ta sakeshi daga tsayen da take ji kake tush ya tarwashe a qasa ruwan ya watse duk ya tsallar musu a qafa harda Audun. "Innalillahi na qone" Bintan daya fi zubar mata ta fada tana daqe qafafu, Audu ya zabga tsaki yana cewa "Wane irin sakarci ne zaki yada fulas se kace bakya gani? Se ki dakko tsintsiya ki tattare gurin ai kafin yara su fito wani ya taka kwalba" yana fadar haka ya baza Babbar rigar da ta zame masa Kayan sawa yanzu ya fice daga gidan. "Ke kin dauka zaki kwanta ki miqe qafa in daga miki abinci? To ba Gishiri ba idan bakiyi sannu ba wata ran shinkafar bera zan zuba miki" ta wuce ciki tana tsaki. Sanadin zaman Bara'atu boyi boyi kenan a gidan, da ranar girkinta da ba nata ba muddin tana so yaranta suci abinci kan lokaci sedai ta tashi tayi, an koma makaranta Abdullahi ya koma makarantar kwana dan haka ita zatayi shara ta hada abin kari ta shirya yan makaranta su tafi sannan tayi wanke wanke ta hado wankin kayan Yaranta dana Bintan da wani sa'ilin harda nata kayan take tulo mata kuma bata isa taqiyi ko tayi magana ba ranar Audu ya ringa surfa mata bala'i akan ta fiya fitina bata qaunar a zauna lafiya. Nana da nan kyan da tayi da cikar jiki suka zagwance Rama ta maye gurbinsu kulawar da take samu gurin Audun ta rasa domin ko sun shirya na dan lokaci Binta zata sake kunna wata wutar da zata wargaza su, a haka Watan Azumi ya kama aiki ya ninkar mata dan bayan abincin gida harda na sadaka sukeyi wanda A baya Mairo da Lantana ke aikin yanzu da babu su itace komai haka zata wuni tsaye kan qafafunta idan dare yayi lokacin da kowa yake Tsaye yana ibada ita kuma gabbanta sun gajiya sedai ta kwanta tayi ta muqususun ciwon jiki ga babu godiya balle kyautatawa daga Megidan a kullum gazawarta yake gani yan uwanta kuma sun gagara gane halin da take ciki idan ka cire Hadiza wadda tasan kan zaman da takeyi. Sallah saura kwanaki Biyar su Yakubu suka zo Kano, a gidansu suka sauka da yake jirgi suka biyo se dab da shan ruwa suka tafi gidan Audu kamar yanda suka tsara da Yakubun sanda ya dakkosu daga Iyafot. Kasa magana Balaraba tayi sanda taga Bara'atu, Yakubu kansa kallo daya yayi mata sannan ya kalli Audu wani abu ya tokare masa maqoshi, farin cikin daya taho dashi ya dishashe nan take yanayinta ya nuna cewar an koma yar gidan jiya kenan Audu tuban muzuru yayi ba dagaske ya gane kuskurensa ba. Shan ruwan haka sukayi shi babu karsashi Binta kadai ke subadadi ita kadai kamar kanta ya qone dan shi kansa Audun tunda yaga canjin fuskar Yayan nasa yasha jinin jikinsa domin yasan baze wuce dalilin ganin Bara'atu ba amma ta yaya zeyiwa Yakubu bayanin halin Bara'atu ya fahimat? Ita din Majicin sari ka noqe ce babu me fahimtar ainihin halinta se wanda ya zauna da ita. Suna gama tsakurar Abincin Yakubu yace ze tafi Balaraba ma ta miqe wannan ya qara tabbatarwa da Audu tabbas Yakubun ya fusata dashi ne. A qofar gida Bara'atu data bi bayansu ta fashe da kuka, tuni Balaraba ta shige mota dan tace ba zata iya magana da Bara'atu ba zuciya tana iya dibanta ta watsa mata mari ko ta daddana mata Ashar haba wannan mutuwar zuciya har ina ta zauna Kishiya da Miji su nemi kasheta da ranta. "Dan girman Allah Yaya Yakubu ka taimakeni kai kadai nake saka ran zaka fahimceni a yanzu, bazan iya yi maka bayanin halin da nake ciki ba amma ina roqonka da kayiwa Allah ka shiga lamarina ka nema mun yanci a gurin Dan uwanka wlh na gaji, ban zata cewar wahalar data fi ta bayace take kirana zuwa gidan nan ba, ban dauka ya maidoni bane saboda ya qara biyamun karatun da be kammala a baya ba, ni dai na haqura ina fatan wahalar dana sha ta zame mun kaffara a rayuwata" ta fada cikin matsanancin kuka daidai nan Audu ya qaraso Soron ya kalleta ya kalli Yakubun daya daga kai sama yana kokawa da bacin ran dake taso masa. "Me kikeyi a nan gurin Dallah wuce ciki" Audu ya fada yana zare mata ido ta juya cikin gidan bayan data sake kallon Yakubu irin kallon ka taimaka mun. "Na zata anan zakuyi sallar Isha in aka idar da Tarawi se na maida ku gidan" Audu ya fada cikin inda inda, Yakubu ya juya ze fita yana cewa "Babu damuwa zamu koma gida kasan muna tare da gajiyar hanya, idan ka samu lokaci kazo ina son magana dakai" daga nan ya sa kai ya fice daga gidan. Masifa da Bala'i Audu ya ringa zazzaga mata bayan daya koma cikin gidan akan seta gaya masa abinda ta fadawa Yakubu dayace yana neman sa amma tayi shiru banda kuka babu abinda takeyi daya gaji ya fita gaba daya ya rikice dan be san me Bara'atun ta fadawa Yakubu ba, maganarta ta qarshe kadai yaji da tace wahalar datasha ta zame mata Kaffara wace wahala? Amma dai ba a gidansa take nufi ba? Ya ringa tambayar kansa. Sallar ranar dai yayita ne kawai ana idarwa kuma ya tafi gidan Yakubu. *MAMAN MARYAM ONLINE BUSSINESS* *Ina kuke Mata Yan kwalisa , Ina nufin isassun Mata ,Wai shin Kuna da labarin shahararren company nan namu na GHT wato good healthtreatments* *Wanda yazo muku da fitattu Kuma* *ingantatattun suppliment ,na dukkan matsalolin ku*❓ *Ina maisan tayi kyau,irin na isassun Mata ya fitar Miki da shef dinki tayi Miki gyara in and out ,nemi royal jelly dinmu na company GHT* *Wanda aka yishi da xuma ,kundai San amfanin Zuma basai na fada miku ba , hajiya ta kixo ki Yi gyara domin ki kerewa sa,a kije taro ko baki da ko sisi kiji Ana rangada Miki hajiya , saboda yanda Zaki Kara kwarjini ,kina walwali acikin mutane , magungunan ght anti agen ne suna maida tsohuwa* *yarinya ,yarinya Kuma ta koma jaririya* *Muna da magunguna iri iri* *NA GYARAN JIKI* *NA GOGE NANKARWA* *NA RAGE QIBA* *NA CIRE TUMBI* *NA QARIN HIPS* *NA GIRMAN BREAST* *NA QARA TSAHON GASHI* *NA QARIN NI'IMA WANDA ZAI SAUKAR MIKI DA NI'IMA YA QARA MIKI DADI DA ZAQI A GURIN OGA* *Muna da hadin bita zai zai ,indai kishiyar ki tana Shan magungunan GHT, tohh lallai sunan ki sorry domin kuwa tazarar dake tsakanin ku kamar tazarar sama ne da kasa* *Muna da Wanda zai matseki ciki da waje Andai na yayin dinki uwargida*, *Sannan company mu na GHTBai tsaya anan ba* *Ya kawo muku maganin dukkan matsalolin ku* *INA MASU HAWAN JINI?* *INA MASU CIWON ZUCIYA?* *INA MASU CIWON QODA?* *INA MASU CIWON HANTA?* *INA MASU SICKLER?* *INA MASU HIV?* *INA MASU CANCER?* *INA MASU NEMAN HAIHUWA?* *Tohh Ku matso GHT taxo muku da magungunan matsalolin ku* *Kuma muna da testimonys da yawa ,na wadanda suka gwada suka da ce* *Munanan a KANO KUNTAU* *Kuma muna tura Kaya ko wanne gari cikin aminci da gaskiya , kuma kayan mu muna badashi ne cikin price Mai rahusa ga kyau ga inganci sannan ga Rahusa* *Kutuntube mu ta wannan number 📞08129249549* *📲07011401314* Audu ya ringa Jijjiga kai yana buga qafafu haka nan zufa take keto masa kamar wanda yake zaune kan Kunama, bakinsa har kumfa yake saboda masifa Yakubu ya zuba masa ido yana kallonsa kawai, shi yanzu tantama yake anya Audu bashida wata matsala akansa kuwa kodai shaye shaye yakeyi be sani ba. Tambayarsa yayi akan me yake faruwa tsakaninsa da Bara'atu ya ringa zana masa maganganu marasa lissafi bare kan gado, a duk abinda ya fada masa babu guri daya dayaji laifin illa tsantsar Zalunci da Azabtarwa da ita suke mata, ya mayar da ita tamkar Baiwar daya siyo da kudi a cikin gidansa shin wai me Bara'atu tayiwa Audu ne a rayuwa dayake daukar fansa akanta yanzu? "To Audu kasan dai Aure anayinsa ne bisa yarjejeniyar Mutum biyu Mace da Namiji, haka nan idan har ya zama da cutarwa kowanne bangare yana iya neman sauqi ta hanyar rabuwa idan har babu wata hanyar samun daidaito bayan wannan din, ni Ina ganin tunda dai zaman ku ya zamana da cutarwa ku rabu hakan ze fi Alkhairi akan kuci gaba da zama daya yana daukar Alhakin daya" cewar Yakubu. Audu ya dago a fusace yace "Wato ce maka tayi kasa na saketa kenan dazun?" "Haka tace, ta gaya mun ta gaji da cutar da ita da kakeyi kaida matarka dan haka tana neman sauqi ka sawwaqe mata auranka taje tayi rayuwarta ta samu wani can ta Aura wanda ze sota tsakani da Allah ya san darajarta kaje kaci gaba da zama da matarka da kake ganin tafi maka kowa" Yakubun shima ya mayar masa cikin daga murya. Se Audu ya miqe yana cewa "Bazan saketan ba, ka gaya mata idan tana da qarfi tazo ta kwaci sakin ko kuma ta saki kanta" "Ai kuwa idan baka saketa ta Arziqi ba zaka saketa ta tsiya dan wallahi maka ka zanyi a kotu qaryar taurin kai kakeyi Audu zan nuna maka jini daya ne yake gudana a jikinmu yanda kake jin ka gado Taurin kai seda na fara gada kafin ka samu ragowa, karka kawo mun takardar sakinta kafin nan da gobe kaga yanda zamu kwashe dakai" daga haka ya shige ciki ya bar Audu a tsaye yana tsuma, Bara'atu tace ya saketa? Ita da kanta ko kuwa wannan matar Yakubun ce ta zugata? Kwanaki uku aka kwashe cikin wani yanayi mara dadi, kwana biyu da Audu yaje gidan Yakubu bayan ya dawo ya samu Bara'atu yayi mata cin mutunchi da tijara ya kuma jaddada mata sedai ta mutu amma baze taba sakinta ba washe gari da safe yana kamfani se ga magatakarda daga Kotun Musulinci an aiko masa da sammaci, ya karba ya duba kiransa akeyi daga kotu matarsa ta shigar dashi qara ya wuto gida Afujajan sedai be tarar da Bara'atu ba tun safe yana fita itama ta fice ta tafi gidan Yakubu tare dashi sukaje Kotun da kanta ta shigar da qarar bayan Yakubu ya sake tambayarta ko zata yi haquri ta bada lokaci su sasanta ta rantse masa akan wallahi ta gama zama da Audu muddin baso suke wata rana a wayi gari zuciyarta ta buga ta mutu ba su qyaleta jin haka yasa yace su tafi Kotun take kuma aka rubuta takadda aka kaiwa Audu. Ranar Jajiberin sallah Bara'atu ta karbi takardar sakin igiya daya data rage tsakaninta da Audu, a ranar ya kamata suyi zaman kotu, tun Asuba daya dawo ya kulle kansa a daki yaqi fitowa, besan yanayin da yake ciki ba wani irin qunci da zafi zuciyarsa takeyi masa. Binta da duk abinda akeyi a kunnenta da idonta amma tayi biris tamkar bata san wainar da suke toyawa ba tana tsakar gida tana aikace aikacenta tana waqoqi Musbahu yazo, bayan sun gaisa yake ce mata gurin Baba yazo ta masa magana qarfe Goma ne zaman kotun nan gashi Tara da rabi tayi, dataje ta gaya masa beko waiwayo ba ya miqa mata farar takarda, duk yanda taso ta daure bayan ta karanta abinda yake ciki ta kasa seda ta rangada guda kamar wadda take saka Amarya a lalle. Tana bawa Musbahu takardar ta hau taka rawa a gabansa se ya rasa abinda zeyi kawai ya tsaya yana kallonta kafin jiki a sanyaye ya juya ya fice daga gidan ya kaiwa Yakubu saqon Audu. Sanda takardar ta shiga hannun Bara'atu ji tayi kamar an mata bushara da gidan Aljanna, da Ajami ya rubuta dan haka ta gane komai abu daya daya dameta a ciki shine cewar da yayi karta tafi masa da Da ko daya, ta yaya zata barwa Binta yaranta? Matar data tsaneta kuma zata iyayin komai akanta da yaranta. "Karki sakawa ranki damuwa akan yara babu abinda ze same su sannan kina nan a matsayinki na mahaifiyarsu babu abinda ze goge hakan komai daren dadewa kuma zasu nemeki. Ki fuskanci rayuwarki ta gaba, ki tashi kinemi ilimi ki tsaya da qafafunki in sha Allahu ubangiji zeyi miki sakayya a gaba da Mafi Alkhairi kinji" Yakubu ya tausheta. A ranar suka tafi Bechi gaba daya dan dama can zasuyi sallah. Shiya kaita har gidansu ya kuma yiwa Inna Hajara bayanin komai, bayan tafiyarsa kuwa wuta ce kadai Inna Hajara bata hura ta jefa Bara'atu a ciki ba, ta kasa hango rayuwar da yarta take ciki da ta sa ta haqura da daular da ita hange, damuwarta kadai mutane zasuyi mata dariya, zasu rasa tallafin da suke samu a gurin Audun tunda ya kwace Yayansa, ita da take saka ran idan Bara'atun ta sauke farali Bana badi kuma a sakata a lissafi shine tayi mata baqin ciki shin Bara'atu wace irin yarinya ce ne? An gaya mata da akwai Auran da ake jin dadi dari bisa dari ne a ciki? Wace Macece zata samu Miji kamar Audu daula iya daula tayi wasa da damarta ai se sakarya irin Bara'atun gashi yanzu Auran ya mutu murus babu damar gyarawa. An cinye watan Shawwal Mahajjata suka fara shirye shiryen tafiya qasa me tsarki, Audu ya rigada ya biyawa Bara'atu, Bilki da Aminu se Balaraba matar Yakubu, a hannun Aminun ya damqa duk wani abu daya kamata na Bara'atun, babu wanda beyi mamaki ba dukda sun san da ita cikin jerin matafiyan amma abinda ya faru yasa suka dauka za'a fasa tafiyar da ita sedai Audun ya basu mamaki. Lokacin tafiya yayi suka shirya sunyi bankwana da yan uwa da Abokanan Arziqi, dalilin su Bilki da Aminu ya saka Audu yi musu rakiya Iyafot dukda qasan ransa badansu yaje ba, haka nan zuciyarsa ta kasa nutsuwa a kwanakin, kullum ya kwanta se yayi mafarkin Bara'atun haka da rana wuni yake da tunaninta a ransa yana jin kamar ta cancanci ya nemi afuwarta koda har yanzun be yarda da cewar ya cutarda ita ba kamar yanda mutane suke fada amma kuma haka nan zuciyarsa take ingizashi ga neman afuwar da besan ta mecece yake da buqata ba. A iyafot Mahajjata sun hau layin karban tikitin shiga jirgi, yana daga tsaye can gefe dan ya sake zama baqo a cikin danginsa tun da ya rabu da Bara'atu ya sake rasa karsashin sakewa musamman a gaban Yakubu yanzun ma ganinsa tsaye suna sallama da matarsa yasa duk ya kasa sakewa gashi yana so yayi magana da Bara'atu amma shegiyar zuciyarsa me masa hudubar tsiya tana gaya masa girmansa ze zube idan aka ga ya mata magana a nan gurin. "Be kamatu na tafi muna riqe da juna a zuciya ba, ina roqon da ka yafe mun idanna maka wani laifi a zaman da mukayi da kai, daga bangarena na yafe maka, iyakar wannan Alkhairin da kayi mun ka zama silar da zan ziyarci ma'aiki ya wanke duk wani laifi naka da yake cikin zuciyata sannan idan ka koma gida ka gayawa Matarka in har taji tsoron Allah ta gaya maka gaskiya ta wankeni daga zargin data saka mutane sukemun na kisan kai na yafe mata idan ba haka ba idan harna mutu ko ita ta rigani mutuwa tabbas shari'armu sedai a qarqareta a gaban Allah dan bazan yafe ba bayan raina a ringa aibata Yayana ana jifansu da abinda ban aikata ba" Bara'atu da be san sanda ta dawo gurin ba ta fada tana kuma gama maganar ta koma cikin Ayari tana daga masa hannu, kamar wanda aka matsawa Remote haka shima ya shiga daga mata hannun, zuciyarsa ta ringa tsinkewa wata faduwar gaba da besan dalilinta ba ta saukar masa haka ya tuqa motarsa ya koma gida yana maimaita zancenta na matarsa ta wanketa daga zargin data dora mata. A karon farko ya tambayi Binta gaskiyar abinda ya faru? Ya akayi tasan Bara'atu ce ta kashe mata Da? Bintan dake cike fam da tafiyar Bara'atun tayi tsaki kawai ta tashi ta bashi guri. Bara'atun nema take ta zame mata qajaga, ta tunkudeta amma ba zata bar zuciyarta ta huta ba kenan? Abu daya ke sanyaya mata rai idan ta tuna aure ya qare tsakaninta da Audu duk Bala'i dole su haqura sannan ga Yayanta nan zube a tsakar gida suna watangaririya iya rabata dasu da tayi tasan zuciyarta ta quntata, jira takeyi Tagwayen Zubaida su shekara biyu suma tasa ya karbo su subi sahun yan uwansu domin tasha Alwashin babu wata mace da zata mori Audu bayan ita, yaya dai da suka haifa sun samu sedai su jira idan ya mutu su yafici abinda suka samu amma badai a yanzu da yake raye ba. An kammala aikin Hajji lafiya Mahajjata nata lissafin kwanakin daya rage musu su dawo gida haka nan yan gida nata shirye shiryen tarbar yan uwansu, kwanaki biyu ya rage Jirgin su Bara'atu ya sauka, a daren ranar da zasu tafi Jidda inda daga can za'a maido su Nigeria suna shirye shirye dan sun gama daure kayansu cikinta ya fara murdawa, kamar wasa tun tana jinsa kadan kadan har ta kai ga ta kasa zama cikin abinda be gaza Minti talatin ba da fara ciwon cikin rai yayi halinsa Bara'atu ta amsa kiran Mahaliccinta. Mutuwarta ta girgiza yan tawagarsu gaba daya bama su Bilki kadai ba. Wata mata ce take fadin "Dazu take cemun tun da muka hau jirgi tayi addu'a idan har ta kammala aikin Hajjinta lafiya kuma ibadarta ta karbu tana fatan ubangiji ya karbi ranta a binneta a qasar Ma'aiki tace tsoro takeji anya kuwa tayi Hajjinta daidai ashe lokaci yana tafe ubangiji ya karbi shahadarki Bara'atu Yarinyar kirki yarinyavme haquri Annabi yasan da zuwanki" haka akayi jana'izar Bara'atu da Asuba a masallacin Harami aka binneta a maqabartar da ba kowa yake samun wannan Alfarma ba se me tsananin rabo shikenan rayuwar ta qare ta tafi ta bar Binta a duniyar da take ganin ba zata qare ba. Dawoqar Mahajjata a maimakon murna se Al'amari ya juye na koke koke da Jimami, duk wanda yaji mutuwar Bara'atu seya girgiza hatta da Binta da da take ganin idan aka bata wuqa zata iya dabawa Bara'atun se gashi sanda labarin mutuwarta ya rsketa zuciyarta seda ta tsinke ta kuma girgiza. Munira qanwar Binta da tazo Kano tun Bayan qaramar sallah dalilin takurar da Mama take mata akan ta fitarda Miji bayan kamar wadda aka sakawa hannu Sauro be taba tsaida ita ba bare yaje gidansu da sunan zance shiyasa ta tattaro ta taho gurin Bintan saboda ta samu sauqi kuma qila ta samu Mijin a nan sanda taji zancen mutuwar Bara'atun kuka ta fasa ta dora hannu tana tumami "Mun shiga uku Yaya Binta matar nan ta mutu bamu nemi yafiyarta ba wlh inaga haqqintane ya kamamu gashi naqi Auruwa Anty Sakina haka siddan aka koreta daga gurin aiki duk irin hanyar Dady da mutanen daya sani ta kasa samun wani aikin ga Mijinta ibtila'in daya fada masa daman da aikin nata suke lallabawa da tallafin da Dady yake bata to ta rasa aikin ita kanta Yaya Salima cikin garari take masifar yau daban ta gobe daban gashi yanzu ta mutu balle mu roqeta ta yafe mana qazafin da muka mata shikenan haka rayuwarmu zata qare a balbalce ni kenan bazan taba yin aure na na shiga uku na lalace wayyo ni Munira kaicona dana biyewa shedan muka laqabawa Baiwar Allah sharrin kisan rai bata ji ba bata gani ba" magana take cikin ihu da kururuwa wanda mutanen da suke tsakar gida Yan Bechi da sukazo tarar su Bilki duk sun Jita, Audu na kan Baranda dan jiri ne yake neman kadashi tun sanda labarin mutuwar ya riskeshi shiyasa ya zauna a gurin ana masa fifita se ga wata sabuwa yana jiyowa daga dakin Binta. *PROMO PROMO PROMO* *Nace kina da Labarin MOMMY MOROCCO ME KAYAN MATA KUWA?* *Ko kuwa dai kina nan zaune baki wangale kina fama da masu niqa Kuka da Citta ko su qulla miki Garin Masara da sunan Magani*? *To ki karkade kunnenki Yar uwa ki kuma maza ki dauraye qafarkin nan da tayi furu furu domin MOMMY MOROCCO Ta diro Nigeria kuma tafe take da Abin Arziqi Niqi Niqi* *Ina mai farin cikin shaida muku Moommy Morocco zatayi BONANZAr kayanta na kwana biyu*. *Tazo muku da zafafan magungun wanda ya taba amfani dasu ne kadai ze baki labari Ingantattun magunguna na gani na fada ajin farko wanda aka hadasu cikin tsari da kula daga Ganyayyaki da kayan abincinmu masu qara lafiyar jiki da saukarwa Mace Ni'imar da take buqata kayanta babu Algus babu abinda ze cutar dake da yardar Allah* *1-Da akwai hadin First ladies exclusive VIP package* *2-Qafarka qafata package* *3-Kankat package* *4-Da kuma Mini package* *Tazo muku da gangariyar maganin SANYI sadidan na Jiki dana Mara wanda In sha Allaahu ba ke ba sanyi kuma za a iya ba wa Yara, Maza ma suna sha* *Bata tsaya iya nan ba tazo da Turarukan ta na ban mamaki se wanda ya gwada ze bada labari, Kedai kada ki bari de wannan damar ta wuceki domin ta zabtare Farashin kayanta har zuwa kaso 50% discount! Kyaso wannan gara basa ta wuce ki kuwa Indai ba Bintan Audu kike ba* 🥴🥴 *A tuntubeta a WhatsApp:09086233009* *Ko kiran waya a 08029988065* *Siyan Nagari Maida kudi gida* *MATAR MUTUM* *NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER* *FIKRA WRITERS ASSOCIATION* *LITTAFIN KUDI NE* *PAY 500 A ASUSUN* *7061838488* *OPAY DIGITAL SERVICES* *MARYAM FAROUK* OR *0709290797* *ACCESS BANK* *SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488* *IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705* *Kuyi following dina a Arewabooks @Maryamfarouk01 inda zaku karanta wannan littafin tareda sauran littattafaina* *NAGODE* *PAGE 29* "Ke Munirah meye haka? Baki da hankaline kike daga murya baki san bamu kadai bane a gidan nan?" Binta ta fada a rikice tana qoqarin toshe mata baki Muniran ta fizge tana cigaba da cewa "Ki barni Yaya Binta abin kukane ya sameni dole nayi, daman Yaya Ummu seda ta fada, tace akwai ranar da zamuyu kuka muyi Nadama, seda tace tun muna da sauran lokaci mu kwance qullin da muka daura a lokacin ban dauki maganarta da muhimmaci ba, haka kawai muna zaman zamanmu muka jazawa kanmu masifa ta hanyar shiga haqqin baiwar Allah da bataji ba bata gani ba muka bata mata suna kuma mukayi silar mutuwar Auranta gashi yanzu ta mututu ta bar mu a duniyarda nauyin haqqinta a kanmu nidai Allah ya isa tsakanina daku kun cuceni wlh" ta sake fada muryarta a sama tana rusa kuka. "Alhamdulillahi! Dadina da gobe saurin zuwa, Allah nagode maka daka matsi bakin Azzaluman bayinka suka tonawa kansu Asuri, kaiconku wlh, kaicon Zuciya me cike da Mugunta da Zalunci irin taku. Yanzu ai ga duniyar nan gaba daya bama gidan Audu ba ta tafi ta bar muku se ku shinfida tabarma ku cigaba da zama kuna kasa abinda kukaga dama a cikin duniyar, amma ku sani wlh cutar da kukayiwa Bara'atu bazata barku ku zauna lafiya ba, yanda kuka saka rayuwarta cikin qunci da takura harta koma ga mahaliccinta da yardar ubangiji haka zaku qare taku" Bilki ta fada idanunta na tsiyayar da hawaye, ta waiwaya ta kalli Audu daya runtse ido kamar yayi bacci a inda yake zaunen tace "Baka da banbanci kaidasu, yanda zasu qare rayuwarsu suna girbar sharrin da suka shuka kaima haka zaka qare taka kana Nadamar zamanka da Bara'atu" "Ke Bilki menene haka? Da wanne kike so yaji dan Allah?" Aminu ya katseta. Bata kulashi ba taci gaba da kukanta. A cikin daki kuwa Munirah na gamsheqar kuka Binta na tsaye akanta ta harde hannye gaba daya kanta ya qulle ta rasa abin da zatayi a lokacin, ji take kamar ta rufeta da duka shegiyar yarinya ta kwance mata zani a Kasuwa yanzu da wace kalma take so ta gyara kwabar da tayi mata? Tana jiyo sanda su Aminu suke fadawa Audu zasu wuce saboda kar suyi dare a hanya. "Ka daure ka shiga daki ka kwanta, rayuwar kenan daman farkonta da qarshenta dan taqin kadan ita dai Bara'atu tata ta qare kuma In sha Allahu munayi mata kyakykyawan zaton tana Babban masauki addu'a kadai zamu cigaba da bibiyarta da ita kafin tamu tafiyar ta riskemu Allah yasa kuma abinda ya faru a baya ya zame mana darasi a rayuwarmu gaba daya" Aminu ya sake fada masa daga nan suka fara haramar wucewa Bechi. Cikin yanayi me ban tausayi Audun ya miqe, dakyar ya iya ce musu Allah ya tsarw hanya ya daddafa ya haye samansa a falo yayi zango ya kwanta rigingine a qasa wani zafi da radadi yake ji daga can cikin zuciyarsa, numfashinsa ya ringa fita da sauri da sauri tamkar wanda yayi gudu a, a sannu ya baiwa Idanunsa damar fitarda abinda suke muradi, hawaye ya gangaro ta gefen idanunsa zuwa cikin kunnuwansa, tamkar me tsoron wani ya jishi ya saki kuka kamar mace, kuka me tafe da abubuwa da yawa a cikinsa. Cikin muryar da bata fita yake cewa "Dana san mutuwa zakiyi Bara'atu da ban rabu dake ba, inama ina da damar maido da baya, dana canza zaman da mukayi zuwa mafarkinki, dana san rayuwarki ba zatayi tsaho ba da...da...." Ya kakare yama rasa abinda ze fada se kawai yaci gaba da kukansa a hankali kewar Bara'atun me nauyi tana dirar masa. Kalamanta na sallamar da tayi masa suka ringa dawo masa kamar sannan take maganar, tace ta yafe masa amma bashida tabbacin Allah baze kamashi da laifin cutar da ita ba wai meya shiga kansa shi? Meyasa ya kasa tantance gaskiya da qarya a zamansa da Bara'atu? Me yasa ya gagara yi mata uzuri ya ringa Muzguna mata yana tozartata? Yanzu gashi ta tafi ta bar masa duniyar dai, tayi masa nisan da baze taba taddota ba. Seda yayi kuka me isarsa kafin ya tashi dalilin kiran sallar Azahar da ake tayi yana layi kamar wanda ya shawu ya dauro Alwala, baze iya sauka ba dan haka a nan yayi sallarsa addu'arsa gaba daya ta nemarwa Bara'atu Rahmar ubangiji ce, yana nan zaune yayi zuru zuru kamar wanda ya kwana zawo, motsin hawowa saman ya jiyo, ya waiwaya ya kalli qofa daidai nan Binta ta shigo da Try a hannunta ta doro kulolin abinci jikinta sanye da Zurmemen Hijabi har qasa fuskarta tayi jaa ta kumbura kamar wadda tasha kuka ta qoshi. A gabansa ta ajiye Try din ta zauna se ji yayi ta fashe da kuka tana hailala da salati, yayi zukudi yana kallonta kawai. "Mun shiga uku mun lalace Ashe Bara'atu mutuwa zatayi daman? Me yasa yarinyar nan bata haqura munyi zaman lafiya anyi rabuwar arziqi ba?" Yeeee ta sake rushewa da wani kukan. "Binta" ya kirata cikin kaushin murya, tayi dif daga kukan munafurcin da takeyi ta kalleshi, cikin sautin daya fi na farko ya sake ce mata "Zan sake tambayarki menene gaskiyar abinda ya faru ranar sunan Zakariyyah?" "Wace gaskiya kuma wai kake buqatar sani bayan abinda nida yan uwana muka shaida maka tun a waccen ranar? Allah ya jiqan Bara'atu kawai ni daman tun tuni ai nace na yafe mata idanma wannan kake tunani" ta bashi amsa ba tareda ta kalli idonsa ba babu tsammani kuwa taji saukar yatsunsa a kuncinta irin marin nan na bazata seda ta wantsala gefe tana zare ido kafin ta taqarqare ta fasa qara tana kiran "Ka mareni" "Na marekin, kuma dukan tsiya zanyi miki yanzu muddin baki bani amsar abinda na tambayeki ba sa'innan na koraki gidanku" ya fada yana miqewa tsaye PPP ll ya razana Bintar bata taba ganin ya birkice haka ba, Bay's play llp ta fara ja ganin yana neme neme da alama abinda ze doketa dashi din yake nema hakan yasa tace "Zan fada maka wlh, nidai na shiga bandaki ina fitowa kawai na tarar da ita ta zauna akan Jaririn" "Har yanzu kina da bakin yimun qarya ko?" Ya fada yana nufota da wayar Radion daya zare, ta yunqura zata gudu Hijabin jikinta ya tadeta ji kake timm ta fadi a qasa be ko bata damar biqin radadin faduwar ba ya shiga zabga mata Bulaliya ta ko ina a jikinta. Dukanta yake kamar ya samu qato dan uwansa yana fadin "ba zaki fadamun gaskiya bako?" Dadai ta tabbatar da gaskiyarta ce zata kwaceta a hannunsa dole ta fada, "Wlh sune, basu fadamun daman ya mutu tuntuni ba se bayan da aka gama mana shari'a wlh ba laifi na bane kayi haquri ka kyaleni". Be barta ba seda hannayensa suka gaji zuwa sannan ko motsin kirki bata iyayi ya mata lilis fatar jikinta duk ta fashe nan ya watsar da bulalar ya shige daki ya barta tana jan numfashin wahala dan kukan ma ta kasa cigaba da yinsa. Wanka yayi ya fito ya tsallajeta yayi waje abinsa, Munira na bakin qofar, tunda ta jiyo ihun yar uwar tata ta taho sedai tsoron karta shiga ya hada da ita yasa taci burki a gurin. "Kar na dawo na tarar daku cikin gidana daga ke har itan" ya fada mata. Ta sauke ajiyar zuciya da be taba lafiyarta ba, seda ya sauka daga qasan kafin ta shiga, yanda taga Bintan ta tsorata ta kamata Binta ta fashe da kuka saboda Azaba ta ko ina jikinta radadi yakeyi mata. Hudu ta gota sanda Munira ta hada musu yan abinda zasu buqata Binta ta coccogala suka fita daga gidan Audu saboda tsoron abinda ze iya biyo bayan zamansu Alhalin yace su tafi. Gidan Turai suka nufa dan babu halin Tafiya Kaduna a wannan lokacin, suka hadu suka ringa jimamin al'amarin. "An auna arziqi dabe furta ya sake ki ba ai, lokaci kawai zaki bashi ya danyi fushinsa ya sakko komai ze daidaita" Turai ta fada. Binta dake kwance magashiyyan Zazzabi na nuqurqusarta a haka ma wai taje Chemis an bata maganin rage radadi dana zazzabin shine taji dama dama. "Yanzu ta mutuma amma tsinanniyar matar nan ba zata barni na zauna lafiya da Mijina ba Allah ya isa tsakanina da Bara'atu" ta fada tana sakin kuka. Munirah tace "Yanzu ashe ba zaki saduda ba Yaya Binta? Wannan abun be isa ya zame miki ishara ba?" "Zanci uwarki idan kika sake saka mun baki a magana" ta fadawa Muniran daga nan tayi shiru tana jinsu da Turai suna maganganu akan matakin daya kamata su dauka, ita dai Allah ya gani tayi nadama kuma tana fatan itama Bintan ta ganr gaskiya tun lokaci be qure mata ba sannan da sun je gida dole ta warwarewa Iyayensu komai daya faru saboda ayiwa tufkar hanci, muddin Binta bata rabu da wannan matar da alamu suka nuna ita take sake dorata a hanyar banza ba ba zata taba komawa ga Allah ba. Washr gari suka tattara suka wuce Kaduna, Binta bata tsammaci abinda ta gani bayan da Munirah ta fasa kwai ba, gigicewar da Salima da Sakina sukayi ba kadan bace Ummu ko fadi take "Kun gani ko? Kunga abinda nake jiye muku ko? Yanzu wa gari ya waya? Gashi nan ta mutu ta bar muku duniyar kuji da dakon haqqinta". Alhaji Zakariyya wanda yake fama da ciwon bugawar zuciya kusan shekara hudu kenan da ciwon ya ta'azzara masa abu kadan yake tayar masa dashi wannan tashin hankali daya riskeshi na abinda Yaran nasa suka aikata ya sake motsa masa ciwon sosai, ita kanta Maman Seda Hawan jininta ya tashi, Allah ya sani daga ita har Mijinta babu me muguwar zuciya da baqin rai irin wanda Yaransu suka gwada. Rashin lafiyar Alhajin tasa basu bi takan Binta ba qoqarin yanda zasu cetoshi kawai sukeyi a sannan. AUDU Tattara yaran yayi ya maidasu Bechi bayan da Binta ta bar gidan harda Zakariyya da bata tafi dashi ba, rayuwa ta masa quncin da be taba zaton ze tsince kansa a makamancinsa ba, komai ya sukurkuce masa, duk ya gigice ya fita a hayyacinsa shi kadai yake rayuwa a gidan abinci sedai ya siya ko yaje gidajen Abokanansa yaci. Be bi takan Binta ba balle yasan me take ciki dukda har yanzun be yanke hukunce dangane da cigaban zama da ita ba ko akasin haka cikin wannan yanayi ya share watanni biyu, Yakubu yazo Kano ya tarar dashi gashi nan shi ba me hankali ba shi ba zararre ba, dukda cewar yana da fushinsa a zuciya amma akace Jini ba wasa ba ya tausayawa Audun. Shi ya ringa tausarsa ya nuna masa cewar kuskure dai ya rigada ya aikata a rayuwarsa yanzu abinda ya rage masa shine ya gyara sannan rabuwa sa Binta ba shine mafita ba a yanzu tunda dai ya fahimci wacece ita ya kuma san tuggu da makircin da take shirya masa a gida seya hankalta ya kuma san me yakeyi, sannan ya bashi shawara da ya hade kan gidansa, yaje ya maido da Zubaida ta raini Yayanta a gidan ubansu yasan kuma ita zata iya riqe Marayun Bara'atu ta hada da nata saboda zancen yace ze maidasu Bechi ma be taso ba ya kuma jaddada masa ya tashi ya koma makaranta ya nemi ilili na boko dana Muhammadiyya saboda Ilimi shine gishirin rayuwaz daga shi har Bintan Jahilci shine jigon abinda yake qara ingizasu ga shirmen da suke aikatawa a rayuwarsu. Karo na farko da Yakubun ya dangantashi da Jahilci kuma ya amsa beji Haushi ba ya kuma tabbatar masa da ze bazama neman Ilimi ze kuma gyara mu'amalarsa, zancen Zubaida kuwa daman ya dade yana saqa hakan a zuciyarsa tun ma kafin Bara'atu ta sake fita daga gidansa dan haka ya roqr Yakubun dayayi masa Jagora suje dan yana kunyar Idon Mahaifinta ya sani be kyautawa Tsohon ba. Yakubu beqi ba suka shirya sukaje, ko a fuska Malam Hassan be nuna musu komai ba ya ringa Maraba dasu ga Yan Biyu sunyi girma sosai sunyi wayo idan ka gansu zaka dauka sun shekara uku ko sama kamanninsu daya sak sedai banbancin halayya inji Malam Hassan ya nuna Hussaini yana cewa "Kaga wannan kaiya biyo sak, rigima a cikin Hussaini harda ta bayarwa sadaka shi kuwa takwarana yanda kasan wannan dan uwan naka salihin bawa babu ruwansa haka Tagwai din zeyita cin zalinsa yayi shiru na zakaji bakinsa ba". Audu ya sunkuyar da kai dan ji yayi kamar zaginsa Malam Hassan yake a fakaice Yakubu kuma yayi murmushi yana cewa "Dama hakane ai duk tagwaye se an samu wannan banbancin dabi'ar daya me sanyi daya me zafi" "Wannan gaskiya ne dan nima nawa Hussainin Allah ya jaddada rahma a gareshi haka muka sha fama tun quruciya har zuwa girma shekarun mu Arba'in da biyar Allah yayi masa rasuwa sedai shi be bar baya ba yaya hudu ya haifa duk kuma sun rigashi mutuwa" Inji Malam Hassan. "Allah ya jaddada rahma a gareshi" Audu da Yakubu suka hada baki gurin fadi. Shiru sukayi nadan lokaci kafin Yakubu ya numfashi ya amayarwa da Malam Hassan abinda yake tafe dasu. "Wai, ashe baka sani ba? Ai yau kwana Ashirin da tara kenan da Zubaida ta daura aure kwana goma sha biyu kuma da tarewarta, nan qasan mu babu nisa take Yaron Aminina Malam Bala ta Aura wannan da kuka taba gaisawa a nan har nake ce maka Daga qasar waje ya dawo yayo karatun Likitanci" Malam Hassan ya fada yana duban Audu Audun kuma ya kalli Yakubu kamar dashi ake maganar, "Tooo ai babu labari Baba, da yake muma din an samu Rashi ne uwargidansa ce ta rasu a Makka sunje aikin Hajji ba'a dawo da ita ba wannan ya tayar masa da hankali har yasa ya dauki lokaci haka be leqo Yaran ba. Ashe kuma haka ubangiji ya qaddaro babu rabon komawarsu da itaz to masha Allahu munyi murna Allah ya sa hakan shine mafi Alkhairi a rayuwarsu baki daya" inji Yakubu. *MAMAN MARYAM ONLINE BUSSINESS* *Ina kuke Mata Yan kwalisa , Ina nufin isassun Mata ,Wai shin Kuna da labarin shahararren company nan namu na GHT wato good healthtreatments* *Wanda yazo muku da fitattu Kuma* *ingantatattun suppliment ,na dukkan matsalolin ku*❓ *Ina maisan tayi kyau,irin na isassun Mata ya fitar Miki da shef dinki tayi Miki gyara in and out ,nemi royal jelly dinmu na company GHT* *Wanda aka yishi da xuma ,kundai San amfanin Zuma basai na fada miku ba , hajiya ta kixo ki Yi gyara domin ki kerewa sa,a kije taro ko baki da ko sisi kiji Ana rangada Miki hajiya , saboda yanda Zaki Kara kwarjini ,kina walwali acikin mutane , magungunan ght anti agen ne suna maida tsohuwa* *yarinya ,yarinya Kuma ta koma jaririya* *Muna da magunguna iri iri* *NA GYARAN JIKI* *NA GOGE NANKARWA* *NA RAGE QIBA* *NA CIRE TUMBI* *NA QARIN HIPS* *NA GIRMAN BREAST* *NA QARA TSAHON GASHI* *NA QARIN NI'IMA WANDA ZAI SAUKAR MIKI DA NI'IMA YA QARA MIKI DADI DA ZAQI A GURIN OGA* *Muna da hadin bita zai zai ,indai kishiyar ki tana Shan magungunan GHT, tohh lallai sunan ki sorry domin kuwa tazarar dake tsakanin ku kamar tazarar sama ne da kasa* *Muna da Wanda zai matseki ciki da waje Andai na yayin dinki uwargida*, *Sannan company mu na GHTBai tsaya anan ba* *Ya kawo muku maganin dukkan matsalolin ku* *INA MASU HAWAN JINI?* *INA MASU CIWON ZUCIYA?* *INA MASU CIWON QODA?* *INA MASU CIWON HANTA?* *INA MASU SICKLER?* *INA MASU HIV?* *INA MASU CANCER?* *INA MASU NEMAN HAIHUWA?* *Tohh Ku matso GHT taxo muku da magungunan matsalolin ku* *Kuma muna da testimonys da yawa ,na wadanda suka gwada suka da ce* *Munanan a KANO KUNTAU* *Kuma muna tura Kaya ko wanne gari cikin aminci da gaskiya , kuma kayan mu muna badashi ne cikin price Mai rahusa ga kyau ga inganci sannan ga Rahusa* *Kutuntube mu ta wannan number 📞08129249549* *📲07011401314* Haka suka tattara suka tashi guiwoyi a sage, har sun shiga Mota Audu ya kalleshi yace "Mu koma mu tafi da yaran" "Idan ka dakko su ina zaka kaisu? Ko kuwa kai zaka haqura da fita nema ka zauna rainon Yara? Koda zaka karbe su ba yanzu ba ka fara bari ka nutsu kasan alqiblar daka kama sannan se kayi batun dakko Yara, yanzu dai gashi yayanka shida Audu Aure uku, ina fatan ya zama na qarshe saboda Aure Aure bashi da dadi, sau da yawa yana kawo rarrabuwar kawuna Ahali musamman a gida irin naka da Shugaban gidan be zama tsayayye ba, kaje ka zauna kayi shawara ka yankewa kanka hukuncin abinda ya kamata kayi a yanzu, kaga dai Bara'atu ta tafi inda babu dawowa, Zubaida Tayi Aure nasan kuma sedai wata qaddara ta ubangiji ce zata fiddota daga gidan auranta Binta kadai ta rage maka uwar Yaya da kake da damar cigaba da zama da ita dan haka ka maidota ta riqe Yayanta kana iya nemo wata Macen daka yarda da tarbiyyarta da zata mayewa wadannan Iyayen da basu tare dasu domin na tabbatar Bintan dana sani bazata riqa maka Yaro ko guda daya tsakani da Allah ba. BAYAN WATANNI UKU Watanni uku suka shude wata biyar kenan tun bayan rasuwar Bara'atu da kuma barin Binta gidan Audu, be waiwayeta ba be kuma je Kadunan ba kamar yanda Suma Iyayenta basu nemi da yaje ba. Mahaifinta yace duk hukuncin da Audun ya yanke akanta dai dai ne kuma shi baze shiga cikin maganar su balle Alfarmarsa tasa ya yanke hukuncin da bashi yaso a zuciyarsa ba. Wannan zama ya quntata Binta matuqa da gaske, babu walwala ko Yancin da take dashi a baya ta zama kamar wata mujiya kowa kyararta yakeyi tsakanin Iyayen abinda yake qara rura wutar Bala'i a zuciyarta kenan ta sake cin Alwashi kala kala akan komawarta gidan Audu. Wulaqancin daya mata baze tafi a banza ba wlh seya gane kurensa. A bangaren Audu kuwa bayan dogon tunani da shawarwari daga yan uwa da Abokanan Arziqi ya yanke shawarar sake Aure, duk wanda ya masa maganar Binta fa se yace yana sane lokaci ze nuna abinda ya kamata yayi da ita da yawa sun dauka ya saketa ne ma ganin an tasarma rabin shekara babu labarinta a gidab. Wannan karon mata biyu ya rakito a lokaci daya, Hadiza data kasance Bazawara auranta biyu na farko Mijin ya rasu sena biyun kuma rabuwa sukayi tana da yarinya daya dashi yar Ƙofar dawanau ce amma tana yawan zuwa Goron dutse gidan Yayarta a nan suka hadu da Audun kamar da wasa yayiwa Mijin Yayarta magana wanda suke gaisuwar mutunci dashi babu bata lokaci ya shige masa gaba magana taje gaban Manya. Ta biyun kuma Aisha, yace ga Sarkin Ƙaraye Maimartaba Alhaji Ahmadu Isah na biyu. Ita din Ƙanwace ga Abokin kasuwancin sa Najibullahi Amadu wanda suka hadu sanadin Noman Rani da Audu yakeyi a gonakinsa da suke Kusalla wani Ƙauye dake ƙarqashin Ƙaramar hukumar ta Ƙaraye Gonakin Audun sunyi iyaka dana Najibullahin wannan tasa suke haɗuwa idan sunje zagayen Gona daga haka kuma zumumci ya Ƙullu harta kai Audun yana zuwa gidan Najibu duk sanda ya shiga qaraye a nan kuma yaga Aisha kamar da wasa yacewa Najibun tayi masa dukda yarinya ce ƙarama shekarunta basu haura sha hudu ba tana cikin ta sha biyar sannan ganinta yana tuna masa da Bara'atu lokacin daya aureta banbancin ita Aisha tana da dan girman Jiki kadan tafi Bara'atu cika ido a lokacin da take da shekarunta. Najibu ya tabbatar masa in har da gaske yake shi ze shige masa gaba akan maganar wannan tasa daya yanke shawarar Ƙarin Auran ya tuntubeshi, babu bata lokaci kuma ya gabatar dashi ga Maimartaba. Shaidar daya samu daga Najibu da sauran Mutanen garin da suke masa aiki tasa har Sarki ya Aminta dashi ya kuma ce yaje ya nemi yardar Aisha dan shi bayayiwa Yaransa Auran dole. Aisha tasan Audu dukda Ƙarqarinsu gaisuwa duk sanda yaje gidan Yayan nata, tana bala'in girmamashi dan ganin babban mutum take masa kwatsam sega maganar Aure tana qoqarin shiga tsakaninsu, ita din yarinya ce me matuqar sanyin hali da biyya ga Manyanta wannan dalili ya saka sanda Yayanta ya sameta da maganar Abokinsa ya ganta yana sonta ya tambayeta ko tana da wani da take so tace masa Aa, shikenan magana ta Ƙullu har anje Tambaya. Yakubu ne ya Tilasta masa cewar dole yaje gidansu Binta, babu yanda za'ayi yaci gaba da jingineta gaban iyayenta tsayin lokaci dan sun masa shiru bayana nufin basu son yarsu bane kawaici kawai sukayi masa kuma da son itama su koya mata darasi ta ganr kuskuren abinda ta aikata dan gaka baze saura sabon aure ba tareda Binta ta san Matsayarta ba. Dole ya shirya zuwa Kaduna, yanda Alhaji Zakariyya ya ringa bashi haƙuri yasa duk yaji wani iri, kamar ze durqusa masa yake roqonsa da yayi haƙuri akan abinda Ƴaƴansa suka aikata masa a madadinsu yana nema musu afuwa, ya Ƙara da cewa "Bana so ka dubeni cikin yanke hukuncin makomarku kaida Mamana, karka cutar da kanka, idan har kana ganin bazaka iya cigaba da zama da ita ba ina goyon bayanka daka sauwaƙe mata domin tayi abinda ta cancanci hakan, amma idan kana ganin zaka iya yafe mata kayi mata uzuri to, ina da yaqinin abinda ya faru a baya baze maimaita kansa ba domin iyakar Fada, Nasiha da Tunatarwar daya kamata muyi mata a matsayin mu na Iyayenta munyi muma kuma fatan taji". Se yaga kamar a fakaice Alhajin roƙonsa yakeyi akan ya mayar da Bintan, kuma bai kamatu ace mutum da yayi masa tarin Alkhairi a rayuwa kamar Akhaji Zakariyya ace shi ya gagara maida masa ba, darajar tasa shi Amincewa yayi bikon Binta, ya kuma sanarwa da Alhaji zancen auran da ze daura da Mata biyu sati biyu masu zuwa Alhajin yayi masa murna da fatan Alkhairi haka ma Mama sannan ya kira Binta a gabansa ya shaida mata muddin ta koma ta sake aikata wani abu da ze tunzura Audun ya sake aikota gida to daga can ta nemi gurin zuwa badai gidansa ba, ya sake ja mata kunne sosai kanta na Ƴasa tana kukan munafunci tamkar taji abinda yake faɗi kuma zatayi amfani dashi. Kwanan sa biyu da zuwa suka juyo tare, zaman dai babu yabo babu fallasa sabgoginsa yake yana ta shirye sgiryen bikinsa. Ta tarar da an sake Ƙalƙale gidan, banda dakinta da yake a kulle hatta da samansa an bare Asalin Tarazo da yake gurin an maida Na zamani kayansa ya sakko dasu dakin da Abdullahi yake ciki nan ya kafa Gadonsa yake kwana yanzun, tsakar gidan ma am Canza Tarazo, kitchen dinsu na waje an gyarashi sosai kamar dai na cikin dakunan su se aka yanki filin tsakar gidan aka sakeyin wani Kitchen din na Langa langa, babu fus bare ta tambayeshi wannan sabon shirin na menene haka a haka taci kwanaki goma da dawowa wanda kuma ya rage saura kwana biyu a daurawa Audu Aure ranar taga ana shigowa da sababbin kayan gado da Kujeru aka haura sama dasu. Daya dawo da daddare ta dauka ranar zasu koma saman tunda an saka kaya harda katifa amma setaga ya bude sabon dakinsa ya shige abinsa se washe gari yake shaida mata gobe Daurin auransa, amma Amarya daya ce zata tare a goben dayar se wani satin. Kamar sabuwar galahanga haka ta bude baki tana kallonsa jin wannan magana, wai Amarya daya, ita dayar se wani satin, "Amaren har su nawane?" Ta jefa masa tambayar, ya wani kalleta sheqeqe kafin yace "Su biyu ne kafin Allah ya kawo cikon ta hudun" "A nan gidan zaka zubamu mu ukun?" Ta sake tambayarsa wannan karon kallonta kawai yayi be amsa mata ba ya juya ya fita. Kuka ta fashe dashi, kishiya har biyu rana daya ita Binta ita za'ayiwa wannan tozarcin? Duk Bara'atu ce ta janyo mata wlhba zata saɓu ba dole ta nemi mafita. Har ta saɓi mayafinta zata fita ta tuno cikin sababbin sharuɗɗan daya gindaya mata harda fita babu izini, ta mayar dan yanzu neman yarda takeyi dole tayi biyayya akan duk abinda aka gindaya mata. Kuka wiwi ta ringayi, Turai take so taje ta gani su shawarta babu halin fita, tayi data sanin ƙin nemo Lantana tunda ta dawo da yanzu ita zata tasa kawai ta aiketa gidan Turan tunda ita ba zata iya zuwa ba. Yanzu haka zata zauna a kawo mata Kishiyar babu ko wanda ze tayata zama ya danne mata Ƙirji? Washe gari kuwa kamar yanda yace tun farar Safiya yasha wanka ya bar gidan, fitarsa babu jimawa sega mota cike da Yan Bechi, su Bilki da wasu daga cikin faccalolinta. Tsohon falon Bara'atu suka baza tabarma suka aje kayayyakinsu. Gaisuwa kadai sukayi da Bintan suka hau haramar dora abincin dan sunzo da cefanensu rankatakaf kafin su shigo Audun ya fada musu inda zasu tsaya su karba danyan abinci kadai suka diba a store dinta suka hau girki. Binta na daki kamar tsohuwar mayya ita da gidanta amma bata iya fitowa su kuwa hidima suke suna raha suna dariya, suka sauke abinci suka ware na Yan Daurin Aure idan dawo da kuma na karbar Amarya sukaci nasu kafin suka hau wanka da shiryawa. Afujajan kamar an jehota Lantana ta diro gidan, taje sau babu Adadi sanda Binta bata nan seda Audu yace ze saka a kulleta idan ta sake zuwar masa gida neman wata Binta kafin ya samu salama ta dena zuwa. Binta na kwance ta dirar mata kamar jifa tana haki harta bata tsoro, "Hajiya, ashe har bayan mutum ya mutu ma yana iya cigaba da kitsa tuggu da munafunci?" Lantanar ta tambayeta, Binta tana gyara zama ta galla mata harara tana cewa "Wane kalar hauka da dabbanci yake damunki Lantana zaki faɗo mun daki haka se kace Asiri? Yaushe na fara sakar miki fuska da zakiyi mun wannan sakarcin?" "Hajiya ki ƙyale wannan maganar tukunna muyi wadda ta kawoni, kinsan wacece Amaryar da Alhaji ya auro miki kuwa?" Lantana ta bagarar da maganar Bintan, itama jin an soso mata inda yake mata Ƙaiƙayi yasa ta zabura tana tambayar wacece. "Ƙanwar Sadiya ce Aminiyar Kishyarki Marigayiya Bara'atu, nidai nace ko a mafarki take zywarwa Sadiyar suka Ƙulla wannan Munafuncin? Ko kuwa daman tun Marigayiyar na raye ita Sadiyar tayi niyyar cin Amanarta ta aurawa Alhaji Ƙanwarta?" "Allah mungode maka daka bamu lafiyar jiki data Ƙwaƙwalwa" Bilki datavshiga tambayar Binta ta bada abinda za'a saka mata abinci ta tsinci zancen nasu me kama dana zararru. "Ban shiga sabgarku ba Bilki karki kuskura kishiga tawa" Binta ta gargadeta, se da tayi irin dariyar nan me cusa takaicin kafin tace "Allah ya huci zuciyar Hajiya Binta uwargidan Dan Uwana Audu, daman kwano nazo ki bada a saka miki abinci, idan kuma kin Ƙoshi shikenan" "Ku kuke yunqar Abinci nida kika ganni kinsan daga gidan wadata na fito abinci ya ishemu shiyasa har muka cida Dan uwan naki Butulu dayaci ya Ƙoshi yake gwada mana halin nas ana butulci, ita kuma annamimiyar da tana Ƙasa a kwance ma ba zata barni na huta ba wlh zamu gamu, Addu'a zan durfafiyi ubangiji ya shiga tsakanina da ita" Binta ta zaburoqa Bilki, seta juya tana dariya tace "Tabbas jahilci yafi hauka ciwo, amma naji dadi da kikace zaki durfafi Addu'a, Allah ya dubeki ya kawo miki sauqi cikin lalular da take damunki Binta" daga nan ta fice Binta ta yunqura zata bita taji ba'asi wai tace mata Jahila kuma mahaukaciya Lantana ta tareta. "Hajiya keda akuyarki tayi kura dan Allah ki nutsu ki Ƙyalesu yanzu matan unguwar nan zasu fara shigowa dan Sadiya babu wanda bata gayyata ba daman surutunki ya gama cika unguwa wasu ma cewa suke Asiri kikayiwa Bara'atu dukda ta fita daga gidan nan seda kika aikata lahira da yawa kinga ba fuskar da zasu shigo miki suka samu ba yanzu ko dalilin bikin nan kowa zata shigo kinayin abu a tafi dake a baki sharri se iya wanda kikaji wlh" da wannan ta tausheta suka zauna jigum jigum babu jimawa kuwa mata suka fara tururuwa a cikin gidan. Ana sallame sallar isha'i aka kawo Amarya gida ya sake cika danƙam da mata, Lantana ce ta fita ta gano mata ina za'a saka Amaryar dan tana ta lissafa inda ze ajiye dayar tubda dai gidansu dakin mata biyu ne ko kuwa can ze gwamutsu kowa ta dauki daki daya su haɗa falo bata san musu ba. Lantana tazo mata da labarin daya sake gigitata, wai sama aka dora Amarya, dama tana ta jiyo dudubniyar mutane ta dauka zazzabi da ciwon kan daya rufetane yasa take jiye jiye ashe da gaske ne, lallai wato da Gaske Audu ya tashi ci mata mutunchi a wannan karon. *PROMO PROMO PROMO* *Nace kina da Labarin MOMMY MOROCCO ME KAYAN MATA KUWA?* *Ko kuwa dai kina nan zaune baki wangale kina fama da masu niqa Kuka da Citta ko su qulla miki Garin Masara da sunan Magani*? *To ki karkade kunnenki Yar uwa ki kuma maza ki dauraye qafarkin nan da tayi furu furu domin MOMMY MOROCCO Ta diro Nigeria kuma tafe take da Abin Arziqi Niqi Niqi* *Ina mai farin cikin shaida muku Moommy Morocco zatayi BONANZAr kayanta na kwana biyu*. *Tazo muku da zafafan magungun wanda ya taba amfani dasu ne kadai ze baki labari Ingantattun magunguna na gani na fada ajin farko wanda aka hadasu cikin tsari da kula daga Ganyayyaki da kayan abincinmu masu qara lafiyar jiki da saukarwa Mace Ni'imar da take buqata kayanta babu Algus babu abinda ze cutar dake da yardar Allah* *1-Da akwai hadin First ladies exclusive VIP package* *2-Qafarka qafata package* *3-Kankat package* *4-Da kuma Mini package* *Tazo muku da gangariyar maganin SANYI sadidan na Jiki dana Mara wanda In sha Allaahu ba ke ba sanyi kuma za a iya ba wa Yara, Maza ma suna sha* *Bata tsaya iya nan ba tazo da Turarukan ta na ban mamaki se wanda ya gwada ze bada labari, Kedai kada ki bari de wannan damar ta wuceki domin ta zabtare Farashin kayanta har zuwa kaso 50% discount! Kyaso wannan gara basa ta wuce ki kuwa Indai ba Bintan Audu kike ba* 🥴🥴 *A tuntubeta a WhatsApp:09086233009* *Ko kiran waya a 08029988065* *Siyan Nagari Maida kudi gida* *MATAR MUTUM* *NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER* *FIKRA WRITERS ASSOCIATION* *LITTAFIN KUDI NE* *PAY 500 A ASUSUN* *7061838488* *OPAY DIGITAL SERVICES* *MARYAM FAROUK* OR *0709290797* *ACCESS BANK* *SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488* *IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705* *Kuyi following dina a Arewabooks @Maryamfarouk01 inda zaku karanta wannan littafin tareda sauran littattafaina* *NAGODE* *PAGE 30* Se gurin sha biyu na dare suka samu sauqin Jamar da suka cika gidan maqil kamar wani sabon yinin biki akeyi,Binta na daki ita da Lantana da yau ta samu guri ga qugunta gana Binta akan Kujera tana bata shawarwari ita dai Binta jinta kawai take badanta fahimta ba, yanayin da take ciki yau din baze misaltu ba, Tashin hankali Kishiya biyu a rana daya. Bata iya runtsawa ba har gidan yayi shiru alamar kowa ya watse, maganganun habaici tasha su a waqe sedai wai yau ita Binta ta gagara yin gaba da gaba da mutanen da sukazo har gidanta suka takaleta da bala'i, yanda yan uwan Hadizan suka zo, dukda basu shigar mata ba waqe waqensu kadai ya sanar mata a shirye suke jira suke ta tanka musu su qaddamar mata dan haka ta kama kanta tana lissafin abinda zatawa Amaruar da zarar an watse domin ta rantse ba'ayi Macen da zata sha gabanta a gurin Audu ba, dole ta fita ta bar mata gida tun gabanin dayar da yake iqirari ta shigo. Tana zaune tana gyangyadi Audu ya shigo, tayi firgigit ta miqe, Lantana dai tuni ta kwanta tana janna Rago taji Laushin Katifa ita ko tuna tana da Miji da yaya batayi ba ta baje a dakin Bintan. "Bakuyi bacci ba ashe? Daman wasu kaya nazo dauka se gobe idan Allah ya kaimu zan shigo gidan" ya fada daga inda yake tsaye kafin kuma tace wani abu ya juya abinsa ya fice. Washe gari ma haka gidan ya tashi da hayaniyar Ƙawayen Hadiza da suka kwana a gidan kamar wanda suka rako budurwa, tana jinsu suna cigaba da Habaice habaicen da suka fara jiya, gidanbe zama nasu ba se bayan la'asar zuwa sannan Yan Bechi sun tafi Ƙawayen Hadizan ma duk sun tafi gida ya rage Binta da Amaryarta dake can sama abinta. Audu be shigo ba se bayan sallar Isha'i, Niƙi Niƙi da ledoji yana daga labulenta ƙamshin gasassun Kaji dana Tsire suka ziyarci hancinta dan ita din ba daga nan ba gurin iya tantance ƙamshi. A tsaitsaye suka gaisa yace mata seda safe ya fita, data rasa abinyi se kawai ta dora hannaye a kai ta rushe da kuka. Washe gari bayan data gama lallashinkanta ta kuma tsara yanda zata ci uban Amarya domin ance ba'a bori da sanyin jiki, Ƙarfe tara tayi wanla tsaf ta sheƙa kwalliya irin wadda ta manta rabon da tayita, ta kashe ɗauri ta fesa Turaren da Mama ta bata sanda zasu taho, fuskarta fes amma da za'a tona ƙasan ranta yafi gawayi duhu. Ta fito saɓe da Naziru, tana fitowa tayi kyakykyawan gani, Amarya Hadiza cikin nata salon gayun ta fito daga tsohon kitchen ɗinsu na tsakar gida hannunta dauke da Fulas na ruwan zafi da kuma na Abinci. Cikin taku me kama da rausaya ta kama matakalar bene ta haye abinta kamar bata lura da tsayuwar Bintan ba. Binta ta bita da idanu tana jin tamkar ta shaƙota amma ta cije, seda ta daidaici Hadizan ta isa saman har yaci ace ta zauna kafin ta yunƙura zata bi bayanta sallamar Lantana ta sake dakatar da ita. "Yawwa, riqemun shi" ta fada tana miƙa mata Naziru ya lafe amma haka ta yakiceshi ta bawa Lantana ya kuwa tsanyara kuka amma bata dakata ba ta haye saman tana fadin "Shegen Yaro me dafar tsiya". Seda ta saisaita kanta ta gwada takun da zata shiga dashi kafin ta tura ƙofar ta shiga kanta tsaye ta durfafi dakin baccin Audu. Hadiza na tsugunne tsakiyar falon tana gyara zaman abin karin data ajiye musu tana kuma dakon fitowar megidan dake ƙarasa shiryawa a ciki tajo an buɗe ƙofa ta daga kai taga Binta ce bata kalli sashen da take ba ta wuce kai tsaye abinta zata shigar mata ɗaki babu shiri ta daka tsalle kafin Binta ta kai ga ƙofar tuni ta cimmata ta tare mata gaba cikin yanayina babu yabo babu fallasa take faɗin "baiwar Allah daga ina?" Binta ta kalleta sheƙeƙe kafin tayi tsaki tace "Ban gane daga ina ba? Kanki daya kike mun wannan tambayar ko kuwa baki san ni wacece ba sannan baki san cewar nan ɗin dakin Mijina bane?" "Ɗakin Mijinki fa? da alamu kece kanki yake da motsi a ciki shiyasa har kika gaza tantance a inda kike, to idan ma ada nan din Ɗakin Mijinki ne a yanzu ba nashi bane mallakina ne, sannan ko ace har yanzu yana mazaunin Ɗakinnasa bakida damar ko shiga tunda ina ciki, kwana nane dole ki jira harse randa na gama uzurina na fita kafin ki shoga ki shimfida naki mulkin" Hadiza ta mayar mata da martani cikin lafazin dake nuna daidai nake dake. Binta ta lafta mata harara tareda da jan dogon tsaki ta kauce mata ta kama mabuɗin ƙofar tana cewa "Idan na shiga se ki fiddo ni waje isashshiya me ɗaki" bata ko gama rife bakinta ba kuwa Hadizan ya fizgota ta maidota bayaz Binta tayi taga taga zata fadi ta kama bango, data tabbatar ta daidaita a ƙasa ta shammaci Hadizan ta wats amata mari. "Bantan uba, kika mareni? Wlh kin jangwalowa kanki masifa da bala'i se kin san ni kika mara" Hadizan ta fada a haukace kafin tayi ƙasa, Binta na jira taga ko ramawa zatayi se ji tayi ta wawashi ƙafafunta kafin tayi wani yunƙuri ta kaita ƙasa. Dambe ne rikica ya sarƙe tsakaninsu, Binta nada garin jiki haka kuma tana da ƙarfi amma naci da dakiyar zuciyar Hadizan tasa take neman cin galaba akan Bintan dan tunda ta fahinci ƙafafunta nan ne Rauninta su take riƙewa ta watsar da ita a ƙasa ta hayeta ta kila idan ta mirgine ita ma ta sakata a Osi ta daka haka suke ta birgima a falon sun yi watsa watsa dashi labulen ƙofar dakin kansa yayo ƙasa sun rikito da ƙarfen. Audu na bandaki ya ringa jiyo kamar hayaniya kamar kuma ana dukan Bango, ya bude ƙofa ya leƙo da kunnensa dan son tantance daga ina hayaniyar take tashi idan ba gizo ba se yaji kanar daga Falo ne, ƙarar fashewar abu dayaji Tusss ta sakashi rarumar Kwangorinsa ya ɗaura din daya jikinsa duk kumfar da be gama ɗaurayewa ba ya fito yana goge ta fuskarsa, yana buɗe ƙofa ya tarar da dambaruwar da ake kwasa a falon, ƙarar dayaji kuma Talabijin dinsa suka rikito da ita ta fashe basu ma lura dashi ba, seda ya buga musu tsawar da ta saka dole suka shiga taitayinsu sannan kowa taja gefe tana sauke numfashi kamar Zakaru. "Wane irin hauka da dabbanci kuke mun a gida? nan ɗin sansanin dambe ne ko yaya? ke Binta me ma ya kawoki nan ma da farko?" Audu ya faɗa cikin tsananin fushi yana kallon Binta dataji jiki dan gar bakinta ya fashe yana zubarda jini. Cikin kuka tace "Bakaga abinda wannn mahaukaciyar daka auro a matsayin mata tayi mun ba se tambayata kakeyi meya kawoni dakin Mijina?" "Wane ɗakin Mijin naki? Ai kinsan banida wani ɗaki a cikin gidan nan yanzu. Banda fitina da son tayar da zaune tsaye meya kawoki? ki maza ki bar nan gurin kuma wannan ya zama kado na ƙarshe da zaki sake tako ƙafarki zuwa saman nan muddin bame dakince ta baki dama ba, fice Malama" Audun ya sake mayar mata da bacin ran dayafi na farko, Binta ta kalleshi ta kalli Hadiza dake sakin murmushin cin nasara wani kuka me tafe da zallar baƙin ciki da takaici ya zo mata seta wuce tana yinsa wiwi dan tasan a yanda ransa yake a ɓacen nan idan ta tsaya zubar da mutunchin seyafi haka Hadiza ta bita da kallo. "Ke kuma akan me zaki kamata da dambe?" ya maida dubansa ga Hadiza se tayi ƙasa da kanta kawai ba tareda tace komai ba, yayi tsaki ya juya yaba ce mata "Ki Gyara gurin kuma ki samarmun wani abun da zanci tunda kun lalata wannan" "Yanzun kuwa in sha Allahu" ta fada tana duƙawa ta fara tattare barnar da sukayi ranta ƙal da beyi mata faɗa kamar yanda yayiwa Bintan ba. Binta kuwa seda taji kanta na barazanar fashewa kafin ta haƙura ta dena kuka. Fuska tayi luhu luhu ga kuka ga Kutufon data sha a hannun Hadiza. Har mamaki takeyi yanda Hadizan da take gani tafi ƙarfi ta lallasata tilas ta canza salo tunda dai a doke ita zata ji jiki to ita ma ta ƙarƙashin ƙasa zata bi mata kamar sauran ta hanyar tuggu da munafunci dan ta rantse ba zata zauna ba ɗayar ba zata shigo ta tarar da ita ba. Ta tafasa ruwa ta gargasa jikinta ta kwanta tana cigaba da ƙulle ƙulle a ranta. Audu kuwa fes suka karya da Amaryarsa suna raha da jin dadi ya mata sallama ya fice ba tareda yako leƙa ya gano halin da Binta take ciki ba. A haka yayiwa Hadiza kwana uku ya koma dakin Binta, a taƙin kwanakin nan kan Binta ta raina kanta domin duk wani tuggu da take jin ta iya Hadizan ta doketa ta shanye a kwana uku seda ta maodata abar tausayi a cikin gidan ta kankane komai ba ga me gidan ba hatta su Mairo se yanda tace dasu dukda daman Mairo bata da Matsala Lantana ce yar kwal uban kuma tun washe garin tarewar Hadizan ta saita mata zama data sakko da kwanuka Lantana na wanke wanake ta ajiye mata seta matsar dasu gefe bata wanke ba, bata kulata ba se da maigidan ya dawo har sannan kuma Lantana bata tafi ba taba daka dan yanzu ta zama ta hannun damar Binta da ita ake shawarta komai tunda basa haɗuwa da Turai suna zaune Audun ya shiga ya cewa Lantana ta fice masa daga gida an sallameta. Binta tayi tsugul zatayi magana ya yarfata yace idan ta sa baki se tabi Lantanar tunda gidansa ne akan me Matarsa zata sakata abu taƙiyi Lantana ta ringa tumami tana roƙon ayi haƙuri dakyar ya barta bayan yaja mata gargaɗi shikenan ta shiga taitayinta. Kamar yanda Audu ya faɗi kwanan Juma'a na zagayowa Iyalan Gidan Sarkin Ƙaraye wanda suka samu rakiyar Ahalin gidan sarkin Kano dan can aka ajiye Amarya masu yi mata danki ne sukayi gaba suka dirarwa gidan Audu. Unguwa tacika maƙil ana ta kallon su masu busa Algaitu natayi. A cikin gida kuwa yai din ba Binta dake neman haukacewa ba su Turai na danneta hatta da Hadiza tasha jinin jikinta ganin wadda ake shirin kawo musu a matsayin ta ukun ta tabbatar wannan duk abinda suke taƙama dashi ta damesu ta shanye, abun da ta sakawa ranta kuma suka shawarta da Yayarta shine ta zauna lafiya da Amaryar, babu ruwanta da shirginta muddin ba ita ta sanyota ciki ba domin fada da saraki babu riba. Se bayan Isha'i Amarya ta iso bisa da rakiyar Gimbiyoyin Kano da Ƙaraye da suka kawota. Dattijai ne na ƙwarai, dukda kasancewarsu sarakai sun san mutunci da darajar Dan Adam, sda suka shiga dakinBinta da kuma na Hadizan suka kai musu Amarya kamar yanda Al'adar Bahaushe take, kafin su iso Kano seda suka kaita Bechi gurin Dangin Audu suka kwana sannan suka dakko hanya washe garin suka iso Kano dan haka babu wanda yazo daga can. Amarya na lullube cikin Alkyabba yar ubansu Ƙwarjinin matan da suka rakota yasa su Turai suka kasa iya daga ido dakyau su kalle su bare su gano ya Amaryar take, Binta dai tana kwance dan ta gagara zama abin dai ba'a cewa komai aka gama musayar gaisuwa da Miƙa Amana suka wuce dakin Hadiza. "Dukda ban ga Amaryar dakyau ba gani nake yarinya ce ma babu wani abu da ze firgitaki akanta Binta" Turai ta faɗa bayan fitarsu. Binta tace "Hmmm" kawai dan baki ya mutu. An bar Amarya da kuyanginta guda biyu ragowar suka musu sallama suka wuce. Turai taso su leƙa Amarya tunda yan rakiyar sun tafi amma Zainab tace Aa, su bari sa dawo takanas su ganta kawai hakan sukawa Binta sallama suka tafi. Ranar Ango be kwana dakin Amarya ba, nan dakin tsakar gidan dai ya shige abinsa ya kwana. Washe gari kafin sha biyu Kuyangin Amarya suka ƙarasa mata gyare gyare sukayi mata sallama kamar yanda ta basu umarni su koma gidan sarki saboda Ango yace ayi masa uzuri base sun zauna ba da akwai masu taimaka musu da ayyuka har biyu anan gidan ya gayawa Yayanta Najibu kuma ya sanar da iyayensu suncr babu komai itama jiyan ya gaya mata shiyasa bayan sun kammala komai tace su wuce kawai. Tun la'asar sakaliya Ango ya shige dakin Amarya wadda bata leƙo tsakar gida ba balle mutan gida su ganta. Hankalin Binta yayi ƙololuwar tashi da jin Al'amarin daya auku, kasa zama tayi ta tafi tagar dakin Amarya ta dasa kujera ason jin me zasu tattauna daya shiga daki tun yanzu tsabar zirgilli se gashi ta jiyo wa kanta abinda yafi ƙarfinta ta ringa kuka a tsakar gida jin Audu yana yiwa Amarya kyaututtuka cikin fitar hayyaci yace har gidan da suke ciki ya bata. Hadiza dake girki ta ringa wa Binta dariya kamar zata kife, faɗi take "Allah ya ƙara, a garin gulma da munafunci zaki jiyo abinda ze toshe miki dodon kunne ki dena ji gaba daya" "Idan baki rufe mun baki ba senayi ƙasa ƙasa dake Hadiza" Bintan ta zaburo mata. Hadiza ta gyara tsayuwa ta dafe kwankwaso tace "Idan baki fasa ba Binta, ai kin san karon mu dake wancan da nayi miki kadan ne wlh yau sace ki zanyi tas dan naga wannan luhu luhun jikin naki yasa kike neman masifar mutane" "Zaki gane kurenki wlh dani kike magana" Binta ta maida mata tana shigewa daki dan ba hauka takeyi ba da zata sake gwabza dambe da Hadizan har yau bata gama jinyar ƙasusuwanta data tasamma karya mata ba. Haka Ango ya yiwa Amarya sati guda, rawar kan da ya ringayi ba Binta ba Hadiza kanta ranta ya sosu amma da yake ita tana da kissar zaman duniya seta shanye bata ko nuna a fuska ba wannan tasa Audun yake ta tata ya kuma hadata da Amarya a cewarsa ta zama ƙanwarta ta ringa kula da ita Binta kuwa data tayar masa da hauka fita yayi a sabgarta ta nemi shiga sabgar yar Amaryarsa da banda gaisuwa da murmushi babu abinda ke hadata da mutanen gidan nan ya nuna mata ya fita hauka. "Wlh ko bisa kuskure naji hannunki ya taba jikinta se kin gane baki da hankali" ya faɗawa Binta sanda tayi niyyar marin Aisha lokacin daya hadasu su ukun. Haka aka ci gaba dagurgura rayuwa, watanni uku Bi ta ta tayarwa da Audu zancen ya kamata a ɗebo yaran Bara'atu da Tagwayen Zubaida su dawo gida kodan saboda makaranta dan a yanzun ta dan rage abubuwa a ƙoƙarinta na son maido da darajarta data zube a idona Audun. Ya kuwa ji dadin maganar harya zanta da Hadiza da kuma Aisha. Hadiza tace zata riƙe su, zata karbe kayansu tunda daki daya ne da ita ba ze yuwu su ringa kwana can ba se su zauna nan dakin da Abdullahi yake amma Binta tayi tsallen Albarka tace ba'a isa ba. Ai ita ta tado da maganar a dakko su kuma ita ta zauna da uwarsu ita suka sani sannan itace babba a gidan dan haka ita zata riƙe Yaran. Daman ita Aisha yar kallo ce a tsakaninsu, idan ba an sako ta ba tafi ku mutu bata ce musu, seta wuni a daki in har ba ita take da girki ba shine zata fito Mairo tanayi tana kallo harta fara karban wasu abubuwan tana tayata dan a gida bata girki kusan yanzu ne ya kamata ace an fara sakata ire iren wadannan ayyukan se kuma Aure yayi mata sammako shi yasa koda suke rigimar waye ze riƙe yaran bata saka musu baki ba ƙarshe da Audun da kansa yace Binta ce zata riƙe yara haka kuwa akayi ya debo su suka dawo gidan, an musu nisa a makaranta wannan tasa aka sake maidasu baya Zakariyya ya wucesu se aka hadasu su biyar harda Naziru aka saka su. Zama yaci gaba matayen uku suka samu ciki kusan lokaci daya, Binta bata lura da cewar sauran biyun duk sun samu ƙaruwa ba domin a duk sallar da zatayi se tayi addu'ar Allah yasa duk su kasance juya basa haihuwa ita kuma Allah yasa duk shekara tayita haihuwar Yara Maza ta cika gidan dasu tana ta kaɗifiri da iyayi wai ita me ciki bata san su biyun ma sun rigata samu ba se randa zataje Asibiti ta fito ta gansu duk su biyun kowa da shirin fita, bata ta Aisha domin tunda ta ganta tace wannan me sauƙi ce Hadiza ce a gabanta dan haka ita ta harara tana cewa "Karma ki kuskura kice yau ma binmu zakiyi, ba zaki tashi fita ba se kinga zan fita da Mijina to se ki taka ƙafarki ko ki fita ki hau Bus" "To ai yau ba ranar girkin ki bace balle ki nuna mun isa da iko, Miji kuma namu zakice dan bake kadai kike dashi ba" Hadiza ta maida mata. Aisha na gefe tana kallonsu bata ce uffan ba sema lafewa datayi jikin katanga tana kallonsu sega Audu ya fito "Uhm Bismillahi zaku fara ba kudai se kace kajin hausa wlh baku da aiki se faɗa ce cacar baki Allah ya sawwaƙa muku" ya faɗa yana baza babbar riga. Binta ta tunzura dan ta tsani wannan wulaƙancin da yake mata a gabansu ya ringa nuna ita ba komai bace daidai suke da ita dan haka tace "Idan ma fita zatayi ka gaya mata ko ta taka ƙafarta ko kuma ta nemi Bus dan ba zata bimu ba" "Tunda motar takice?" Ya mayar mata ba tareda ya kalleta ba, ya juya kan Aisha ya dan saki fuska yace "Bismillah, muje ko?" "Kuje ina? Au itama fitar zatayi?" "Kinga Binta idan baki zuwa ki koma ciki suma duk Asibitin zasuje". Tana cika tana batsewa suka fita wajen tayi wuf zata shige gaba Audu ya dakatar da ita da cewa "Shiga baya, Aisha ce zata zauna gaba" Hadiza ta kwashe da dariya Binta ta sake ƙuluwa ta lailayo Ashar ta watsa mata ita dai ta shige mota tana cigaba da dariyarta. Bayan sun isa Asibiti tana tsammatar taga kowa ta kama gabanta dan a zatonta dubiya su biyun zasuje se gani tayi sun nufi bangare daya na yan Awo dan a waje ya ajiye su yace idan yaje kamfani Musbahu and juyo da motar ya jirasu ya mayar dasu gida. Binta ta ringa binsu tana jira taga abinda ya kawo su gurin Awon ciki sedai daga yanda taga suna gaisawa da Ma'aikatan gurin tasan da sanayya a tsakani suka zauna gurin jira ana bin layi bayan an karbi Katunansu jikinta har rawa ya dauka sanda taga kowa ta zaro kati daga jaka ta miƙa kenan duk cikine dasu bata sani ba? Yaushe akayi? Tana zaman me? Aka ringa kiran Binta Zakariyya ina bata ma jisu ba tayi nisa a duniyar tunani da zullumi karfa suma duk su haifi Maza dan taga kamar Audu bashi da ƙwan haifar ya mace. Matar da take musu awon ta kallera tace "Baiwar Allah tunanin me kikeyi haka duk kin firgice kalli fa har jininki ya ɗaga?" "Kedai kiyi aikinki ki sallameni ina da abinyi" Binta ta gwaɓa mata magana aiko matar ta harziƙo itama tace "Se nice banida aikinyi ko ai bacci kika ga ina yi yanzu ko rawa" "Kiyi haƙuri Sista" Hadiza ta tsoma musu baki aiko Binta tayi kanta da masifa ganin a waje suke yasa ta mata shiru se ma'aikatan ne suka haye itama Bintan kamar sa cinyeta Awon da ba'ayi mata ba kenan ta tattara ta fice ta haye Bus se unguwarsu Turai dan tana buƙatar su tattauna wannan matsala ta yaya za'ayi su biyu suyi ciki. Audu kuwa isarsa kamfani ya tarar da wani mummuman Labari, motoci guda biyar da suka dakko masa Mai daga kudu haka nan wuta ta tashi sun ƙone ƙurmus harda direba guda daya dayayi ƙundunbala saboda motarsa ce ta ƙarsher sun tsaya zasuci abinci Abin ya faru tamkar Tsafi kawai wuta ta kama motar tsakiya kanka kace me sauran sun dauka an hanashi amma ya kafe ya tafi a zatonsa ze iya janye motar kafin wutar ta cimmata se gashi yana shiga ta kama gaba daya se tokarsa aka tattare. Babban abin al'ajabi kamar yanda aka bashi labari ba iyakacin motocinsa bane a gurin mota tafi Ashirin da suka taho tare duk sukayi fakin suna cin abinci amma ibtila'in akan nasa suka sauka basu taba komai ba duk kuma iyakar ƙoƙarinsu na su kashe wutar abu ya gagara. Hankalin Audu ya tashi matuƙa domin ba ƙananan kudade ne suka narke ba sannan ga Rai da aka rasa. Gaba daya suka ɗunguma gidansu Direban daya rasu me suna Lawan sukayi musu Ta'aziyya, ya bawa Iyalansa kudade masu ɗan kauri da kayan abinci yace kafin su yanke abinda ya kamata suyi musu. Wannan damuwar tasa ya manta da matansa na Asibiti a can kuma bayan sun gama har bayan Azahar shiru Musbahun dayace ze zo ya maidasu beje ba Hadiza tace su tafi kawai ta yuwu aiki yasha kansa ya manta. Hakan ko akayi suka kamo hanya suka dawo gida, sun sauka a bakin titi Hadiza tacewa Aisha "Ko zamu ƙarasa gidan Yaya Yakubu dan naji Babansu Baba yace sunzo gari muje muyi Bikon Yaya Balaraba be kamatu ace bama zumunchi da ita ba gaskiya" "Amma bazeyi faɗa ba?" Aisha ta faɗa cikin sanyinta. Hadiza tayi murmushi tace "Haba dai gidan Yaya Yakubu ne fa babu faɗan da zeyi kuma tunda ba girki zamuyi ba kinga bamu da matsala da anyi la'asar se mu wuce gida idan ya dawo se mu sanar masa da munje". Faran faran Balaraba ta tarbesu daman ta dan wayi Hadiza sukan hadu idan tazo gidan Yayarta lokacin da suke can unguwar suma Aisha ce bata sani ba dan bataje gidan ba Yakubun dai yaje yaga Amare da yace suje tace Aa ai bata da sauran dalilin zuwa gidan Audu kuma. Se da sukayi sallar La'asar sannan sukayi haramar tafiya ta hada musu tsaraba cikin abubuwan data zo dasu, Dada da jininsu ya haɗu da Aisha tana ganin sun tashi tacezata bisu "Ki bari muje da ita idan yaso se Baffansu ya maido ta anjima da daddare" inji Aisha suka tafi da ita. Sun riga Binta komawa gida itace da girki kuma, sun tarar da yaran sun dawo daga makaranta Abdullahi ya tafasa musu taliya sunci da sauran miyar da yace ya gani a Kicin, shidin yana gida yanzu sun gama jarabawar fita daga sakandire da Audu yace ze fara zuwa kasuwa se kuma yace ya zauna ya huta dan ƙasar qaje yake da burin turashi idan takardar sa tayi kyau. Binta bata dawo na se guraren biyar da rabi ta shiga gidan tareda Lantana da alama ko ta biya ta gidan tane ta kirata shigarsu babu jimawa Mairo ma tazo ta fara shirin dora abincin dare. Shiru shiru har akayi Isha'i Audu be dawo ba, Binta ta sake cika tayi dam saboda ita keda girki shiyasa yayi zamansa a waje da waccen yar shilarce ai da tuni a gidan ma zeyi Magriba jikinsa na rawa se kace nata Matancin na Gwal ne. Har tara ta buga shiru babu Audu, Hadiza ta leƙa falon Binta dake zaune tana kaɗa ƙafa tana kuma ayyana tijarar da zatayiwa Audu yau idan ya dawo taji muryar Hadizan na tambayarta ko ya shigo. "Ke matarnan ki fita daga sabgata wallahi tallahi idan kika tiƙeni sena miki abinda bakiyi tsammata ba. Wato kunga gurin zama har kun bude mara kun ɗauki ciki to wlh ku kwana da sanin zaku haifesu a gidajen ubanninku kuwa" Binta ta faɗa tana miƙewa tsaye. Hadiza da fuskarta ke cike da damuqa tace "Ni ba tashin hankali ya kawoni gurinki ba, gani nayi ya zarta lokutan daya saba dawowa kuma idan ma zeyi dare irin haka yana sanar mana shiyasa hankalina ya tashi. Mijina na fari daga irin wannan fitar shiru shiru se bugamun ƙofa akayi na buɗe aka shigo da gawarsa" "Keta shafa wannan ni tsakanina da tsohon mijin naki ai Allah ya isa ce da be mutu ba ai da Mijina be kwaso mun ke kinzo kin addabeni ba, ki barmun ƙofar daki kuma Audun ai ba Ji njiri bane da za'ace ya bata" Binta na rufe baki sujai dirar mota mintina kaɗan ya shiga fuskar nan kamar wanda aka aikowa da saƙon mutuwa be kulasu ba ya durfafi sama harya fara hawa meya tuna kuma ya sakko ya wuto Ɗakin Binta. "Au da hankalinka ya gushe can zakayi kenan an maka kiranye ka shigo kamar wanda aka jefo baka ko gani dakyau ai seka tafi can ɗin" Binta ta faɗa tana babbake ƙofarta. Hadiza tayi masa sannu da zuwa ya ɗaga mata hannu yana cewa Bintan "Matsa na shige" "Ai sedai ka koma inda da ka niyyaci zuwa" inji Binta. Tsaki me ƙarfi yaj ya juya ya haye saman Hadiza tabi bayansa Binta ta kwarma Ihu murya a sama tana kiran yau akwai tashin hankali a gidan ashe. A saman kuwa harya fara cire kaya Hadiza ta isa, a tausashe take cewa "Da alama gajiya tasa ka manta ba a nan kake na yau" "Ina sane, sedai in kema korata zakiyi se in tafi" ya bata amsa. "Ba haka bane, rigimar Maman Zakariyya ce bana so kana jiyowa gata can tana masifa bana son tashin hankali ko ƙo dazun a Asibiti seda aka ce mu guji yawan hayaniya" ta sake faɗa cikin taushin lafazi. Audu ya rafka tsaki, da matan nan sun san me yake ciki da sun ɗaga masa ƙafa. Rigarsa ya raruma ya sauka sukayi kiciɓus da Binta na hawowa ya raɓeta ya wuce ɗakin Aisha. Ganinsa ba yanda ta sababa yasa ta masa sannu da zuwa ya shige ɗaki ta bishi da ruwa, tana jiyo hayaniyar Binta dukda bata jin me take faɗi sosai. Abincinta ta kai masa beci ba yana kishingiɗe ya harɗe hannaye ya zurawa guri daya ido, ta ajiye, tana so ta tambayeshi ko lafiya amma ta kasa se kawai ta fita ga Dada da tayiwa mamarta alƙawarin za'a maidota hartayi barci yanayinsa kuma ya nuna ba lafiya ba balle tayimasa maganar. Tana zama Binta ta faɗo kamar jifa, ta mata kallo daya ta maida idonta kan Talabijin yanayin kallon Hadarin kajin da tayi matan ya saka Binta yin shiru dan kwarjini yarinyar ta mata, tabbas Sarauta ba Ƙarya ba. Ɗakin data san zata samu Audu ta tura ta shiga, Aisha bata san ya sukayi ba taga Binta ta fito sumi sumi ta wuce. Data sake leƙawa se taga kamar yayi barci dan haka ta shige dayan dakinta suka kwanta tareda Dada. *PROMO PROMO PROMO* *Nace kina da Labarin MOMMY MOROCCO ME KAYAN MATA KUWA?* *Ko kuwa dai kina nan zaune baki wangale kina fama da masu niqa Kuka da Citta ko su qulla miki Garin Masara da sunan Magani*? *To ki karkade kunnenki Yar uwa ki kuma maza ki dauraye qafarkin nan da tayi furu furu domin MOMMY MOROCCO Ta diro Nigeria kuma tafe take da Abin Arziqi Niqi Niqi* *Ina mai farin cikin shaida muku Moommy Morocco zatayi BONANZAr kayanta na kwana biyu*. *Tazo muku da zafafan magungun wanda ya taba amfani dasu ne kadai ze baki labari Ingantattun magunguna na gani na fada ajin farko wanda aka hadasu cikin tsari da kula daga Ganyayyaki da kayan abincinmu masu qara lafiyar jiki da saukarwa Mace Ni'imar da take buqata kayanta babu Algus babu abinda ze cutar dake da yardar Allah* *1-Da akwai hadin First ladies exclusive VIP package* *2-Qafarka qafata package* *3-Kankat package* *4-Da kuma Mini package* *Tazo muku da gangariyar maganin SANYI sadidan na Jiki dana Mara wanda In sha Allaahu ba ke ba sanyi kuma za a iya ba wa Yara, Maza ma suna sha* *Bata tsaya iya nan ba tazo da Turarukan ta na ban mamaki se wanda ya gwada ze bada labari, Kedai kada ki bari de wannan damar ta wuceki domin ta zabtare Farashin kayanta har zuwa kaso 50% discount! Kyaso wannan gara basa ta wuce ki kuwa Indai ba Bintan Audu kike ba* 🥴🥴 *A tuntubeta a WhatsApp:09086233009* *Ko kiran waya a 08029988065* *Siyan Nagari Maida kudi gida* *MATAR MUTUM* *NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER* *FIKRA WRITERS ASSOCIATION* *LITTAFIN KUDI NE* *PAY 500 A ASUSUN* *7061838488* *OPAY DIGITAL SERVICES* *MARYAM FAROUK* OR *0709290797* *ACCESS BANK* *SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488* *IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705* *Kuyi following dina a Arewabooks @Maryamfarouk01 inda zaku karanta wannan littafin tareda sauran littattafaina* *NAGODE* *PAGE 31* Seda aka kwashi sati daya cikin wani yanayi a gidan, Audu ba magana babu murmushi bare dariya duk kuma wadda tayi kuskuren shiga sabgarsa ta jawa kanta tijara. Basu san me yake faruwa ba se randa zugar Yan Bechi suka zo Bus biyu ranar befita ba kusan kwana biyu ma kenan be fita ba sedai yaransa dake ta zarya a gidan kuma sedai su fita can inda yake ajiye mota suyi magana ko Binta duk iya labenta bata tsinto abinda ake ciki ba har seda yan Bechi sukazo jaje. Ashe bayan motar Mai kwanaki Babbar Gonarsa da yake noman shinkafa ruwa ya shanyeta. Gonata ba yar ƙarama ba. Shinkafar kuma tayi kyau dan har an saka ranar girbi Dam din dake kusa da inda yake Noman yayi ambaliya gana ɗaya ya shafe gonakin dake kan hanya abindai ya munana ba'a cewa komai. Binta ta ringa kyarma jin Maƙudan kuɗaɗen da aka ce sun narke daga kan Mai zuwa shinkafar, "Shikenan, a garin kwashe kwashenka ka kwaso mana me farar ƙafa" ta faɗa hannu biyu aka jiki na tsuma hawaye suna sakko mata. Duk akayi shiru aka zuba mata ido banda Audu dayaja tsaki dan maganar tata ɓacin rai ta ƙara masa ya tuna da wani lokaci can baya sanda suna Yara tun Malam nada rai Goggo Fadi na ce musu yayan me farar ƙafa, a lokacin abinda ya dauka saboda Dada Farace tar duk jikinta abinda take nufi kenan kalar fatar ƙafarta shiyasa be taɓa gayawa Dadan ba se bayan daya girma ya san ma'anar abin sannan ya fahimci zaginsu takeyi shiyasa duk inda yaji an faɗa se ransa ya baci. Binta ta ringa kuka tana maimaita an Auro musu me farar Ƙafa shikenan zasu tagayyare su shiga wani hali yan jaje suka koma wasu na ganin salonta data saba laƙawa matan da yake aurowa sharrine wasu kuma sun yarda da abinda ta fada dan tun bayan Auran Audun abubuwa suka fara canzawa yanayin bunƙasar Arziƙin tayi ƙasa ba'a dai samu wani ibtila'i babba kamar wadannan ba. A hankali rayuwar walwala da jin dadin da akeyi a gidan ta fara juyewa zuwa ƙunci da tashin hankali dan zuciyar megidan a kusa take kullum ƙiris yake jira a taɓashi yayi zazzaga ga mata uku kowacce da ciki haihuwa kusa hatta da yanayin cima ta sauya dan samun ƙasa yakeyi ba sama ba. An kwashi watanni cikin wannan hali, Audu nada shirin mallakar rijiyar Mai tasa ta kasansa a kwankin baya domin har ya fara harhaɗa kudade sun gama tsara yanda za'ayi da Alhaji Zakariyya wanda ze siyar masa da daya daga cikin rijiyoyinsa sedai matsalar daya shiga a yanzu da harta girgiza masa jari ta tilasta masa karbo kudaden daya bayar matsayin kafin Alƙalami ya sakasu cikin harkokinsa na Noma da kiwo wanda anan Ibtila'in yafi sauka, Amfanin gonar da ya noma a shekarar sama da kaso hamsin ƙwari sun lalatashi haka dabbobinsa na gidan gona Kaji sedai a shiga basu abinci a tarar da au fululu a ƙasa sun mutu ko a hangi Sa ya Tirƙeƙen Rago yana kakarin mutuwa sedai a danne a yanka. Abu dai kamar wasa ana saka ran samu sauƙi se ya zamana kullum kamar Tiri ƙaruwa abubuwan sukeyi. Mutane da yawa sukace hannu aka saka masa, Asirine, jifansa akayi ya bazama shine waccen tsangaya ya kai sadaka shine waccen gidansa kuwa kullum cike yake da Gardawa anata saukar Karatun Alƙur'ani idan an gama ayi sadaka amma abin se godiyar Allah kawai. Ana wannan yanayi Hadiza ta tashi da Naƙuda cikin dare, Audu da Aisha ne suka fita kaita Asibiti dan Bibta cewa tayi Allah ya kasheta babu inda zataje da Aishar ta shiga kiranta Audu kuma tace masa Yara, be kamatu a barsu su kadai a gida ba. Haka kawai sun hau Titi suna tafiya mota ta tsaya, ya fita yayi yaj dube dube ya sake kunnata yana ja inji yayi wata ƙara Baammm mota ta cake kuma ko ba'a fada musu ba sun san Injine ya buga, tamkar Audu ya fasa kuka, ya fita nemo taimako Hadiza dai nan cikin mota ta haihu ta santalo danta Namiji ƙato. Wani mutum ne ya taimaka musu ya ƙarasa Asibitin dasu se safiya aka sallamosu bayan an tabbatar da ita da Jaririnta duk lafiyarsu ƙalau motar Audu kuma akaje da Janwe aka dauketa. Binta da taga Hadiza ta dawo gida da Da Namiji ba'a cewa komai, baƙin ciki kamar ta mutu ko zuwa tayi mata barka batayi ba har akayi sunan Aminu Hadizan ta koma gida saboda jikinta dayaƙi mata dadi tun bayan haihuwar Binta faɗi take ta tafi kenan ba zata dawo ba. Haihuwar Hadiza ta sake zuwar musu da sabon sauyin dayafi na farko dan Asara ce take afkuwa kan Asara duk abinda Audun ya taba seya lalace Binta ta samu nayi ta ringa kwakwazo ai damab ta faɗa ya auro me Farar Ƙafa beji ba. Yakubu ya samu Audu yake tambayarsa "Anya kuwa Audu kana fitar da zakka yanda take idan munyi lissafi?" Cikin tsananin damuwa Audu yake ce masa "Allah shine shaidata dukda bani da cikakken sani akan kasafin Zakka shiyasa ma bana fitarwa da kaina nake baka, kuma wlh Duk idan muka fitarda lissafin shekara yanda kace a fitar din nan haka nake cirewa da hannuna nake rabawa dan karma na bawa wani yayi ha'inci ya rage sannan ka san muna fitarda sadaka daban itama haka ake hadawa a rabar nidai na yarda wannan jarabawa ce kawai daga ubangiji ina kuma roƙon daya bani ikon cinyewa" "Hakane, na godewa Allah daya sa ka yarda cewa duk wani tsanani daga shine haka kuma sauƙi ma daga gareshi ne. Kaci gaba da Addu'a muma muna tayaka karka kuskura ka bari wata maganar banza tayi tasiri a ranka ace maka wani ya maka Asiri ko wani abu, ka ƙaddara Allahn daya baka Arziƙin shine ya jarabceka akansa". Kwanan Hadiza Ashirin da bakwai da haihuwa Aisha ma ta haihu ta samu Mace. A gida ta haihu daga ita se Bilki da kuma Unguwar zoman da aka kira dan Audu baya nan kuma babu mota balle a kaita Asibiti kuma Allah ya bata da sauƙi ta samu yarta Kyakykyawa me kama da ita. Binta na daki tana fama da kanta dan itama ta kusa Lantana ta kwaza mata zancen haihuwar, tayi wata dariya harda buga ƙafa tana cewa "Ita kuma da ƙafar hagu ta shigo kowa na farawa da Magaji shine zata haifo mace? Koda yake na godewa Allah, Allah yasa in ma zata cigaba da haihuwar tayita jera irinta" Lantana ta tayata sukayita izgilanci akan Ikon Allah. Da Audu ya dawo ya tarar da haihuwar, farin cikin jin Mace aka haifa ya wanke masa kaso hamsin na damuwar da yake kwana yana tashi a cikinta. Ya fita ya samo mota suka tafi Asibiti, su kadai yasa aka maido shi kuma ya tafi bakin Asibitin Nasarawa inda suke da zuwa Binta siyayyar Haihuwa dan rigar da aka sanyawa Jinjirar bashi ya siya ba be kuma san inda Aisha ta sameta ba halin daya shiga yasa duk ya manta da wai ana da buƙatar wasu abubuwan na haihuwa Hadiza ma se bayan data haihun ya basu kudi suka siyo abinda ya sawwaƙa tunda ta san yanda Al'amuran suke wannan kuwa cewa yayi a hada masa kayan barka na Alfarma, aka ware masa wanda ze tafi dasu lokacin ragowar yace a hade masa su ze turo wanda ze ɗauka ya wuce da sauran. Binta data tsammaci Audu bazeyi murnar samun ƙaruwar Ɗiya mace ba se taga akasin haka, murna sosai ya ringayi, kwanan Aisha uku da haihuwa ta tafi wanka gida wanda daƙyar Audun ya bari gida ya rage Shida Binta se yara. Binta ta shiga zullumi, tunda Aisha ta haihu walwalar Audu ta ƙaru haka bashida wata hira seta yar jaririyar me suna Amina taci sunan Mahaifiyar Najibullahi yayiwa kara, basuyi sati biyu da tafiya ba ya kwashi yaran duka ya kaisu su gano Laila kamar yanda suke kiran yarinyar wannan ya ɗaga mata hankali ta kuma shiga zullumin to kodai itama ta haifi Mace ne saboda bata so ace wani Ɗa yafi nata shiga zuciyar Audu, amma da ta zauna tayi dogon Nazari seta watsar da waccen shawara, ita tana lissafine ne da abinda za'a mutu a bar mata, Yara Maza sune masu Gado duk wannan soyayyar da yakewa Lailan a banza tunda baze ɗauketa ya ɗora akan dukiyarsa ba da wannan ta watsar da tunanin haihuwar Mace taci gaba da lissafin zazzago Yara Maza. Tsiranta da Aisha kwana goma sha tara ta haihu a Asibiti ta samu ya mace kyakykyawa da ita tamkar Laila dan yarinyar na fadowa Nurse din data karbeta ta dagata tana cewa "Masha Allahu zankadi kin samu kyakykyawar yarinya da gani da Mahaifinta tayi kama dan ta fiki kyau" Nurse din ta gaya mata magana dan Binta ta gallabesu se dai idan bataje Awo ba amma tabbas se tayi faɗa da wata daga cikinsu. Zabura Binta tayi ta fizgi ƙafar Yar kamar wadda ta fizgi leda ko wani abu mara rai, tawara ƙafafun tana so ta tabbatar dagaske Mace ta haifa ko kuwa tsokanarta sukeyi data tabbatar din kuwa seta saki yar Nurses da basu gama dawowa daga mamakin fincikar da tayiwa ƙafar yarinyar ba suka dulmiya cikin na sakinta da tayi ba taredadamuwar zata faɗi a ƙasa ba. Kuka ta fashe dashi bayan data koma ta kwanta. Nurse ɗin data cafe yar ta kalleta cikin ɓacin rai tace "Amma kedai anyi yar ku*****ba, banda ke mahaukaciya ce dabba ki fizgi ƙafar Jinjira haka bakya ko tsoron ki ji mata ciwo sannan ki saketa a ƙasa? Wlh badan mu muka karɓi haihuwarki ba da nace sato yarinyar nan kikayi" "To kice mana, idan ma kina sonta ki riƙe na baki kuma karki sake zagina wlh dan na fiki iya tashanci" Binta ta hayayyaƙo mata, matar zata sake magana sauran suka tareta sukace ta barta da alama tana da taɓi a ƙwaƙwalwarta. "Sedai uwarku ce me taɓi a ƙwaƙwalwa bani ba" ta bisu da zagi sanda suka fita taci gaba da kukan ta. Haka suka tattaro suka dawo gida abin dai babu daɗi yanda Binta ta ringayi kamar me taɓin hankali duk saboda ta haifi Mace wannan fincika da tayiwa ƙafar Nazira ita tayi sanadiyyar Nakasarta wanda ba'a gane ba har seda ta kai munzalin tafiya sannan bayan dogon bincike likitoci suka gano wasu ƙananan jijiyoyin dake riƙe Sangalalen ƙafa da tafin ƙafarta ne a tsinke shiya nakastata ya zama ƙafar bata ɗaguwa sedai ta jata a ƙasa. Lokaci daya Hadiza da Aisha suka dawo, tafiyarsu lamuran Asare Asaren da Audu yakeyi ukayi sauƙi, suna dawowa tamkar an watsawa wuta fetur abu ya koma sabo farfaɗowar daya fara aka sake kwanciya rigijin harma abin yafi nada muni. Akace zuciya bata da ƙashi balle kuma irin ta Audu me cike da wasi wasi a hankali se famfon da Binta take masa akan ya auro masu fararen ƙafa ya fara tasiri a zuciyarsa. Ya fara tsangwamar Hadiza da Aisha domin a cikinsu ne yake ganin akwai silar taɓarɓarewar Arziƙinsa, kyara, hantara, wulaƙanci ya fara yawa, Hadiza bata shiru idan ya mata ramawa takeyi daman Binta bata isheta kallo ba dan tasan gamonsu Aisha ce take masa shiru dan haka diban Albarkar tasa yaso yafi yawa akanta musamman da Binta ke yawan cewa daman an fi samun masu farar ƙafar cikin mata masu shiru shiru kuma ai data tafi wankan gida abubuwa sun farfaɗo amma tana dawowa ta dawo da tsiyarta. Abu dai gaba yakeyi kullum ba baya ba, idan yayi kamar yabi ta Binta yaje ayi masa istahara a fayyace masa wwacece silar rugujewar Arziƙinsa se kuma ya tuna nasihar Yakubu dayace jarabawa ce saga Allah idan yayi haƙuri a sannu komai ze zama tarihi seya kanne yaci gaba da Addu'ar neman ɗauki daga ubangiji. Cikin wannan yanayi aka cinye shekara guda wanda a kullum ta Allah abin zama yake jiya tafi yau, Audu da harya fara mance lissafin abubuwan daya mallaka se gashi a hankali ya fara ɗaga kadarorinsa yana siyarwa a ƙoƙarinsa nason farfaɗo da harkar Mansa dake neman durƙushewa baki daya ya saki komai ya mayar da hankali akanta domin itace ƙarfin tattalin Arziƙinsa. Binta ce takai wa mahaifinta rahoton abinda yake faruwa da Audun, shiri tayi ta kwashi kayanta domin tafiyar da tayi bata saka ran zata dawo ba, to ta dawo tayi me? Arziƙin da take zaman gadi yana shirin bin rariya wahala na doko musu sallama ita kam bada ita za'ayi wannan zaman ba. Alhaji Zakariyya ya tashi ɗan aike takanas aka kira masa Audu, sun tattauna amma a duk maganar da sukayi ya kasa gano musabbabin wannan Asara dake hawan Audu kamar wanda akayiwa Baki haka nan be bi takan shirmen Binta ba ya sake daukar Kudade masu kaurin gaske ya bashi yace kuma duk in wata matsala ta tashi karya jinkirta ya je gareshi, wannan karamci na Alhaji Zakariyya ya ƙara samarwa da Binta gurin zama a zuciyarsa domin ya sani Allah ne ya haɗa shi da Alhajin amma Auran Binta na daga abinda ya ƙara dankon zumunta a tsakaninsu kuma duk abinda zeyi masa zeyi dan Allah kuma saboda yana auran yarsa, wannan tasa ya ƙara kulla aniyar riƙe Binta dakyau domin bashida wata hanya da ze sakawa da Alhajin sama da hakan tunda duk sanda zwje gurinsa se yayi masa tanbihin ya kula masa da Binta karya dubi halinta. Wannan kudi da Alhaji Zakariyya ya bawa Audu basuje ko ina ba yana dawowa Kano wani Abokinsa yayi masa tallar Farin wake, a shekarar an samu ƙarancinsa acan wani ƙauye suka samoshi yace su siya da yawa su ajiye zuwa A kwana biyu idan farashi ya hau su fitar su siyar dashi su samu riba. Audu be taɓa yin irin wannan kasuwancin ba dan ko wani yaji ze siyi kaya ya ɓoye zuwa yayi tsada sannan ya siyar se yayi magana ya nuna masa rashin dacewar hakan amma a halin da yake ciki yanzu ta yanda ze farfado da jarinsa kawai yakeyi shiyasa ba tareda dogon tunani ba ya siyo wake aka jibge a suto, ba'a rufe watanni uku ba wake yayi muguwar tsada ya ninka kudinsa sau biyu akan abinda suka siyeshi lafiya lau Alhaji Mala Abokin Audu ya kwashe wakensa ya kai Kasuwa ana bude store din da kayan Audu suke aka tarar da wake dai babu na moro Ƙwari sun masa kaca kaca dayawa har ya fara yin gari tsabar yanda ya lalace kamar wanda ya shekara biyar a ajiye. Hankalin Audu yayi ƙololuwar tashi da wannan Al'amari, Alhaji Mala da Bashir suka sake jaddada masa tabbas idan ba Asiri ba to cikin matansa akwai me Baƙar ƙafa a tasu falsafar. Mala yace ya shirya ze kaishi gurin Malaminsa duk abinda ake ciki ze fayyace masa, yace Malamin yayi tafiya nan da sati ze dawo shima daman zeje dan akwai tafiya da zeyi yana so a bashi sa'a. "Ai Ba'a zama haka Alhaji Audu yanda mutane suka ɓaci da jefw jefe wani ido kawai ze saka maka kaga komai naka ya tasamma lalacewa idan kayi sake magauta se sun kaika ƙas wlh kana kallon dai yanda abubuwa suke tafiyar maka kai base an ce maka da wani abu a ƙasa ba, idan ka biye ta wannan Yayan naka kana ji kana gani sedai ka koma jiran wa wani shago ana sammaka na cefane sunanka ya tashi daga sahun matasan masu kudi ka koma layin yan karayar Arziƙi" Inji Mala. Yana komawa gida ranar Binta ce take da girki, damuwa ta masa yawa yanzun shiyasa abu da yawa ba s an tambayeshi ba yana zaune zeyita rattabo zance kamar wanda kansa ya kwance. "Ina za'a jira har nan da sati ai ka tashi kawai kaje nan gurin Malam Salisu Mijin Lantana, ba tuntuni nake gaya maka ba amma kaƙi jin ta tawa ai yanzu da aka faɗa maka a waje ka yarda. Bari kaga inje in gano maka idan yana nan ai ba'a bori da sanyin jiki wlh gara asan abinda ake ciki" Binta ta faɗa tana saɓar Hijabi. Audu bashida zaɓi a wannan gaɓar ruwan kashe gobara kawai yake buƙata shiyasa be hanata ba, Hadiza na zaune tsakar gida kan tabarma tana cin Abinci garin da dan zafi zafi ga tsohon cikin da take dashi ya ƙara mata jin zafin Binta ta wuceta tana cewa "Maza kici gobe sedai kici a gidan me dattin hula". Can ta samu Lantana suka gama ƙulla yanda za'ayi Lantana ta shiga ta zayyanewa Malam Salisu yace babu damuwa duk yanda tace hakan za'ayi. Seda sawu ya fara daukewa Sha daya saura kafin Audu ya tafi gidan Malam kamar wani munafuki, Malam Salisu ya tambayeshi sunan sa dana Matayen nasa gaba ɗaya ya gama zana ƙasarsa yana jan wani kwandalelen carbi se muzurai yake da ido yana motsa baki yayi zane ya share yafi sau biyar kafin ya kalli Audu yace "Gaskiya Alhaji akwai gagarumar matsala, wai ma ya akayi haka wannan Aure babu bincike?" "Kamar yaya? Anyi bincike mana" Audun ya bashi amsa yana kallonsa a wani ɗage, Malam Salisu ya murmusa yana cigaba da zanen sa yace "Ba binciken halayya ko Asali nake nufi ba, Aa burujin ƙasa. Ya kamata ace in za'ayi Auran Alhaji a ringa bincikawa aga taurari matar ya suke zasuyi daidai da naka ko kuwa? Kamar dai yanzu kaga ita ta farin Fatsuma Binta kace sunanta ko? Wannan mahadin Arziƙi ce. Kaga kai Tauraronka wuta ne, ita kuma Iska ce, ya kaga wuta a lokacin bazara yanda iska take fifitata inta ringaci balbal ai Allah kadai ke iya kasheta to haka ne hadin naku taurarinta suna ingiza Arziƙinka zeyita hauhawa ne to kuma se akayi rashin dace ita Aishatul Humaira taurarinta na Ƙasa ne, wuta kuwa da an yafa mata ƙasa ai mutiwa takeyi to me kankat kuma Hadizatul kubura ita taurarin ruwa ne shiyasa da suka hadu su biyu se ƙarfinsu ya danne na fatsuma suke neman nakastaka kuma in har ba'a dauki mataki ba gaskiya Alhaji abin bazeyi kyau ba dan abinda ƙasar nan take nunamun idan ba'ayi da gaske ba har rigar sawa ka fita seka wayi gari baka da me kyau abinci kuwa wata rana se an kwana ba'a ci ba sannan yawan haihuwarsu yanwan Talaucin da zasu cigaba da saukar maka a gida". Ranar kwana zaune Audu yayi yana ƙullawa da kwancewa, Binta bata tambayeshi yanda sukayi ba domin ita ta tsara komai se dariya take a cikin bargo dan ta saddaƙar gobe daga Hadiza har Aisha kwanan gidajen tsoffinsu zasuyi. Washe gari da duku duku ya mata sallama yace ya tafi Bechi, be ko bi takan sauran matan ba, yara da suke gaidashi ma be iya amsawa ba ya fita burinsa ya isa Bechi ya samu Hashimu domin wannan sabgarsa ce shine yasan takan Malamai. Ya isa Bechi be zarce ko ina ba se gidan Hashimun yayi rashin sa'a baya nan amma inji Jamila ba dadewa zeyi ba dan yace a aje masa abincin rana. A tsakar gidan ya zauna kan Turmi tsabar halin da yake ciki ya gagara shiga turakar Hashimun da tace ta masa shimfiɗa ta aje masa ruwa da fura. Seda akayi Azahar Hashimu ya shigo, an gaya masa anga wucewar Audu amma be yarda ba dan har can gida ya ratsa be ganshi ba se gashi ya tarar dashi a tsakar gida kan Turmi fuskarsa ta gama bayyanar da tashin hankalin da yake ciki. A taƙaice ya masa bayani babu bata lokaci ya goyeshi a mashin suka tafi wani dan ƙauye dake gabansu kadan. Bayanan Malam Salisu sunyi kamanceceniya da juna sedai an saɓa lamba a wasu guraren kamar Taurarin Aisha da Binta dashi bafulatanin yace masa taurarinsu iri daya ne da nasa dan haka babu matsala a hadinsu Hadizan dai itace me matsalar kuma akasin da aka samu Taurarinta nada matuƙar haske shiyasa ta tasiranci duka su ukun suke karbar gashi. Bala'un da Dan fulani ya jere masa je afka idan ne rabu da ita ba sun zarce na Malam Salisu, Hashimu yace "Dama a garin aure aure tun mutum na kwaso Arziƙi harse ya ɗebo tsiya gashi dai ka gani ai se ka san abinyi tunda wuri dan duk abinda Malam Sallau ya faɗa da wuya kaga be faru ba, seda ya hanani Auran Saude naƙi gashi ko ina karbar sakamakona" "Aishi ba Allah bane bare kace duk abinda ya faɗa seya tabbata" Audun ya bashi amsa. Hashimu yayi dariyar rainin hankali yace "Na fika sanin haka, amma tunda muka yarda dashi har muka zo tambaya gabansa ai magana ta ƙare, ya rahe naka ka ɗauki matakin daya dace" a gurin sukayi sallama Audu ya juyo Kano zuciyarsa fal wasi wasi. Ya daukarwa Yakubu Alƙawarin baze sake sakin wata mace ba gashi kuma yanzu dole ta saka zeyi sakin kuma ya san duk ta yanda zeyiwa Yakubu bayani baze taba fahimtarsa ba. Maganar gaskiya kuma baze zauna yanaji yana gani ya rasa komai nasa dalilin wata mace ba. *ALBISHIRINKU MATA YAN UWANA YAN KWALISA NAZO MUKU DA WANI DADDADAN LABARI!!!.* *NASAN KUNDADE KUNA NEMAN FITACCEN GURIN DAZAKUJE AMUKU GYARAN GASHINKU DANA JIKINKU CIKI DA WAJENSA,TO YANXU DAI GA DAMA TA SAMU...* *LABARI NAKE BAKUFA AKAN AFINTY QUEENS SHAHARARREN SHAGONMU NA SALOON DAYA HADA KOMAI DA KOMAI DA KOWACE MACE YAR KWALISA IRINA KE BUKATA,SANNAN MUNADA KWARARRUN MA'AIKATAN DASUKASAN KAN AIKINKINSU,KUZO AFINTY QUEENS KUBIYA KUDI MUKUMA MU BATA LOKACINMU DOMIN TSATSTSAFO DUK WANI KYAWU NA JIKINKU DA ALLAH YAYI MUKU...* *A AFINTY QUEENS MUNA AYYUKA KAMAR HAKA:* *- HAIR SALOON* *-HENNA* *-SPA* *-DUKKAN* *-PEDICURE* *-MANICURE* *-SANNAN MUNA DA TURARUKA IRIN NA AMARE YAN MATA DA KUMA MAI KANKAT DAN UWAR GIDA TA TURARA GIDANTA JIKINTA DAMA KAYAN SAWARTA ITA DA YARANTA,,HARMA ZAWARAWA DUK MUN TANADI KOMAI* *DOMINSU SUMA* *-MUNADA SHOES AND BAGS SBD ISASSUN MATAN DA SUKA AMSA SUNANSU MATA*😊 *- MAKEUP NA BRIDAL ND CASUAL...* *IDAN KINSAN KINAJIN LABARIN SHAGON SALOON NA AFINTY QUEENS AMMA BAKI TABBATAR DA YADDA AIKINSU YAKE BA TO YAR UWA GADAMA TASAMU MEZAKI TSAYA JIRA MAZA KEMA KI ZARGAYO SHAGONMU DAZAN JERA MIKI ADDRESS DINSHI A KASA DOMIN KEMA KI TABBATAR DA KALAR IRIN NAMU KWAZON DA MUKA KWARE AKANSHI GURIN GYARAN JIKIN YAN UWANMU MATA KUMA MUKE GABATAR MUSU DA JAKUNKUNA DA TAKALMA HARMA DA TURARUKAN WUTA DANA SHAFAMA JIKINSU DON NISHADIN ZUCIYARSU DANA MAZAJENSU....* *AFINTY QUEENS DISCOVER BLISS IN BEAUTY 💅💯* *Address 👇👇:* *KU ZIYARCE MU A SHOP NO.9&10 SHEMA PLAZA,BEHIND SHEMA FILLING STATION KASUWAN BACCI KADUNA* *TEL:08133379628.* *MATAR MUTUM* *NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER* *FIKRA WRITERS ASSOCIATION* *LITTAFIN KUDI NE* *PAY 500 A ASUSUN* *7061838488* *OPAY DIGITAL SERVICES* *MARYAM FAROUK* OR *0709290797* *ACCESS BANK* *SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488* *IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705* *Kuyi following dina a Arewabooks @Maryamfarouk01 inda zaku karanta wannan littafin tareda sauran littattafaina* *NAGODE* *PAGE 32* Bayan daya dawo a ɗakin Hadizan ya sauka ta karbi girki, ya ringa kallonta ga Aminu dake da shekara daya da watanni biyu ga ciki da ko yau ko gobe zata iya haifeshi. Tausayinta ya kamashi duk da halin da take ciki amma tana ta kaida kawowa tana hada masa abinci. A zamantakewa Hadiza bata da laifi, mace ce ta gaske dan ze iya cewa a duk matan da ya aura babu tsayayya kamarta. Ta iya kula dashi haka tsakaninta da sauran Matansa tana mu'amalantar kowacce da sigar data zo mata. Duk bala'in Binta ta sarara mata sedai tayi a bayan idonta amma ya zeyi? Shidai baze cigaba da zama da ita ba domin ko ita idan zata masa Adalci inta san itace matsalarsa yaci ta nemi rabuwa dashi da kanta kawai su haƙura da juna ze saketa badan baya sonta ba sedai dan hakan shine maslaharsu baki daya ze kuma cigaba da daukar nauyinta har iyakar rai ze cigaba dayi mata duk abinda ya kamata tamkar tana gidansa. Da daddare harsun kwanta ya tashi zaune, cikin nutsuwar dashi kansa besan yana da ita ba ua shiga yiwa Hadiza bayanin halin da ake ciki. "Kuma ka yarda? Tamkar fa kayi shirka ne Audu ka tara sani da Allah. Ya za'ayi ace maka nice silar Karayar Arziƙinka kuma ka yarda shin Allah baya jarabtar mutum haka nan dole se wani abu ya zama sila?" faɗa hawaye ma zubo mata. Audu ya murtuke fuska, yasan gaskiya ta fada to amma magana ta ƙare tunda har aka gaya masa kuma ya yarda dan haka yace "Kinga muyi haƙuri kawai nidai na rigada na yanke hukunci na sakeki saki biyu, kina da zaɓi na kici gaba da zama a gidan nan ba se lallai mutane sun san na sake ki bama". Kallon kayi hauka tayi masa kafin ta miƙe tana kuka ta shiga haɗa kaya, se yayi fakare kuma yana kallonta duk yaji babu dadi, da ace da wata hanyar da ze magance matsalar sa ba lallai seta rabuqa da Hadiza ba daya bi amma babu yanda ya iya. Washe gari ta bar gidan, Binta ta ringa rawa tana shewa, satin Hadiza ɗaya da tafiya ta haifi Aliyu, tayi maza biyu kenan sunyi kankan kan da Binta wadda keda cikin da na biyar Aisha nada na biyu a sannan. Tun Binta na saka ran Aisha zata bi bayan Hadiza har suka haihu wannan karon ma kusan tare tsiran kwana goma tsakaninsu Binta ta fara haihuwa ta samu Yakubu takwaran Alƙali, seda Babanta ya shiga maganar kafin ta haƙura da wannan takwara da aka mata da babban maƙiyinta Aisha kuma Abdullahi suna kiransa Sarki Al'amuran Audu kuma suka fara daidaita sannu a hankali Arziƙi yaci gaba da bunƙasa harya fi nada. Aisha da Binta sukaci gaba da jera haihuwa, bayan su Yakubu Binta ta haifi Aisha wadda Audu yayiwa ƙanwarsa takwara ta rasu wata daya kafin haihuqar Bintan itama yarinyar watanta hudu ta koma a lokacin kuma Aisha ta haifi Ahmad shekararsa daya cif Binta ta haifi Jafar se suka sake jera haihuwa Binta ce ta fara ta haifi Faisal Aisha kuma Salim, shekara biyu suka sake yin mata duk su biyun Binta ta samu Hafsa suna kiranta Hajiya Ƙarama ita kuma Aisha Khadija. Daga nan Binta haihuwar ta dan tsayawa Binta har seda Aisha ta haifi Maimuna da Aslamiyya sanan Binta ta sake haifar Bashir da Lawal, burinta ya cika, ta tara yaya maza zarata har guda shida tafi kowa Kaso cikin dukiyar Audu. Tsakanin Binta da Aisha zaman dai ba'a cewa komai, Binta bata fasa halinta ba ita kuma Aishar seta zame mata ƙarfen ƙafa domin dukta inda ta buga babu riba tayi tuggun tayi munafurcin amma abun yaƙi yaci. Audun da take taƙamar data san Lagonsa se Aishar ta fita bin yanda yake so domin zama tayi tamkar ruwa a cikinsu, hannu idan an saka mata ba zata ciza ba, duk abinda Binta zatace tayi idan ta titsiyeta ba zata musa ba koda batayin ba zata bashi haƙuri ta kuma baiwa Bintan ta yanda in Binta ta sake tada maganar daga baya a maimakon yaga laifin Aisha se faɗan ya juya kanta yace ta fiya son tada zaune tsaye. Halin Aisha kuma ba Munafurci bane ko Kissa irin ta Binta Aa haka Allah yayita da sanyi, sedai nata sanyi ya zame mata Alkhairi ba irin na Bara'atu na haka ita bata ɗauki wargi ko rainin da har Binta zata bautar da ita ba kallo da ido idan bata ga dama ba zata mata ba idan kuwa zata kwana tana magana setaga dama zata ɗaga kai ta kalleta, da Binta ta buga ta buga taga babu riba seta saki lamarin Aisha ta koma kan Yayan gida wanda ruƙonsu gaba daya ya koma hannunta harda na Hadiza guda biyun ta saka an karbo su tun data yaye Aliyu an watsasu cikin yan uwansu. Riƙo take musu irin na jeka ka mutu, iya babu kwaba, abinci me kyau idan sunci a gidan to ranar girkin Aisha ne wadda iyakarta dasu kenan in ta dafa abinci ta basu. Sanda aka maido dasu Aminu tacewa Audu zata ɗauke su har ta kai kayan yaran ɗakinta Allah kaɗai yasan me suka tattauna da Binta washe gari yace ta mayar dasu cikin yan uwansu saboda baya so kansu ya rabu sannan duk abinda ya shafi wani yaro a gidan muddin ba ɗanta ba babu ruwanta a ciki ƙarƙashin kulawar Binta suke. Ita ɗin bata zurfafawa akan abubuwa dan haka bata tsananta ba ta maidasu kamar yanda yace ayi ba kuma ta shiga sabgar Yaransa muddin ba su suka kai kansu gurinta ba wannan zata musu duk abinda ya kamata sedai idan taga wani abun cutarwa ne take tsoma baki wani sa'ilin yaji ya sa a gyara wani lokacin kuma ya gwasaleta yace ai Yayansa ne ba kuma ta fishi sonsu ba, wannan halin sanyin nata da nuna ko in kula akan wasu abubuwan shiya janyo matsalar gidan bata tsaya iyakar kan Yayan tsakar gida ba ta shafi harda nata. Da Binta taga ta kasa cin galaba akan Aisha seta haƙura ta mayar da hankali gurin ganin ta sake kama Audu a hannu da gidan gaba ɗaya, kamar yanda Turai tace mata ta bar batun Aisha domin ba wata tsiya bace ba kuma wani ji da ita Audun yakeyi sama da ita ba ta mayar da hankali gurin gina gobenta data Yayanta. Abinda yake a gabanta yanzu shine tasan duk ta yanda zatayi ta cusa yayanta a zuciyar Audu ya zamana bashida wani tunani idan bana su ba sannan tayi duk me yuwuwa ta dakusar da ragowar a gurinsa, karta barshi ya shaƙu dasu ta hakane kawai Yaranta zasu zama sune kan gaba a kamai nasa hakan kuwa akayi babu Boka babu Malam seda ta san yanda tayi ta raba tsakaninsa da Yaran dukda daman shiɗinma ba wai yana ta tasu bane sosai domin tunda harkokin Arziƙi suka sake buɗe masa ya zamana bashida isashshen lokacim zama a gida ma balle yayi hira da yaran yasan matsalarsu. Duk wani abu na gidan a hannun Binta yake kama daga abinci, sutura harkar karatu da duk wata buƙata kome ya tashi ita zece a tambaya, Riƙo take musu na mugunta ga Azabtarwa, a gabansa takan nuna ta damu da yaran ta ringa kai masa sukar duk yanda take ƙoƙarin jansu amma basa sakewa da ita irin dai yanda ta ringayiwa iyayensu, yaran Zubaida dana Hadiza da suka tasa se suka fara gudu suna tafiya gurin iyayensu dan itama Hadizar tayi Aure tuni, akan wannan Bintan ta haɗasu da Audu ya musu mugun duka dan tace iyayensu na zugosu duk zuwan da zasuyi se sun dawo da sabuwar ɗabi'a ya kuma kafa musu dokar hanasu zuwan daga ƙarshe ma tasa aka kaisu makarantar kwana banda Nata Yayanso se na Aisha data cw bata yarda ba sunyi ƙanƙanta, idan zasu tafi a Arziƙi irin na ubansu Garin kwaki ne da suga se ƙuli ƙuli provision dinsu idan ya bada kudi yace ayi musu siyayya seta soke ba kuma su isa su faɗa masa ba domin izayar da zasu sha se sun gwammace basu faɗa ba shima ɗin kuma be zama lallai ya yarda ba. Yanayin matsatsi da damuwa da suke a ciki tasa cikin su shidan Hassan ne kaɗai se Aminu suke mayar da kai a karatu daman duk aji daya aka sakasu harda su Babannan da yaci ace sunkammala sakandire a sannan amma aka mayar dasu Aji daya na ƙaramar sakandire gaba daya. Banbancin da ake nuna musu ƙarara a fili tsakaninsu da sauran da iyayensu suke a gidan dukda Yayan Aisha ma ba wai sun tsira bane banbancinsu dasu uwarsu tana a gidan kuma ita bata jiran Audu ko Binta da komai na gida yake hannunta a yanzu duk abinda ya tashi na yaranta zatayi musu wanda sauran basa fahintar hakan gani sukeyi su aka tsana aka ware wannan tasa suka washshi uban da matan uban da sauran yan uwansu gaba daya kowanne ya ƙudire wani abu daban a zuciyarsa. Haka rayuwa taci gaba da wullawa shekaru sun shude a kullum kuma rayuqar gidan Audu lalacewa takeyi a maimakon ta gyaru, ya saki komai a hannun Binta ya fantsama duniyar neman kudi kuma Alhamdulillahi rayuwar tana gara masa. Yanda ya faro tushen Arziƙinsa tareda Yan uwa da yayan yan uwansa wanda ba wani karatu me zurfi sukayi a wancan lokacin ba a sannu zamani yana canzawa sauye sauye suna zuwa a duniyar kasuwanci da akwai buƙatuwa ta mutane masu wata kwarewa ta musamman akan wasu al'amiran dole ya fara shigo da bare yana daukar Ma'aikata masu kwarewa ta musamman. Wannan ya zaburar da Binta, ta watsa yaranta zuwa ga fannonin da take da yaƙinin sune zasu riƙe manyan muƙamai a cikin Empire da Audu yake ginawa ta kuma cigaba da cusa masa su, ya zamana duk abinda zeyi ko kuma duk inda zashi tare dasu ne su su ukun nan Manyan su duniya ta sani a matsayin Magadan AUDU BECHI domin tun kafin Zakariyya ya gama makaranta Audu yake turashi ya wakilceshi a tarurrukan kuma a duk inda yaje ya kan gabatar da kansa ne a matsayin Babban Ɗan Audu Bechi, Yakubu yayi iyakar yinsa gurin ganin Audu ya daidaita amma abin yaci tura dole ya saki ya kuma zubawa sarautar Allah idanu domin a yanzun karan Audun ya aki tsaiko, ya isa, sunansa ya fantsama ya zaga ko ina Burinsa na zamowa ɗaya daga cikin mutanen da duk idan aka ambaci sunansu a faɗin Najeriya babbba da Yaro Mace da Namiji ya sanshi Allah ya cika masa wannan buri nasa. Ga dai zuri'a ta taru amma babu hadin kai, babu shaƙuwa babu jan juna a jiki balle jinƙai a tsakani kowa ya tashi ta kansa kawai yakeyi a gidan. Wadanda babu iyayensu sun girma cikin wani yanayi sannnan sun samu labarurruka na gaskiya dana ƙarya akan yanda zamantakewar Audun da kasancw da iyayensu, ita kanta Aisha da yanzu akw kira da Momy ba dadin zaman takeji ba. Itama ta tafka kuskuren da se a yanzu ta gano qautar da tayi, tayi saken da yaranta suka tashi akan tarbiyyar sauran yaran gidan, babu jitiwa a tsakaninsu kowa sabgar gabansa kawai yakeyi wata irin bahaguwar rayuwa tamkar a garin gwarawa haka ake a gidan Audu babu babba babu ƙarami kowa Tantirin kansa ne, tsakaninta da Binta har yau dai se a hankali dukda dai shekaru sunja kuma Bintan ta watsar da harkar kishi domin ta harba musu makamin da yayi musu illah sama da Hayaniyar zaman kishi, ta tarwatsa musu gida ta cusa muguqar Aƙidar yan ubanci a zuciyoyin Yaran gidan koda yake baza'a kira abinda sukeyi da yan ubanci ba domin ciki dayan ma kowa tasa ta fishsheshi akeyi sedai idan sabga ta haɗo tsakanin ɗan wani ɗaki da wani ba sannan ne sukan nuna haɗin kai kowa ya goyi bayan ɗan uwansa har kuwa Yayan Bintan dan abin yafi muni ma a tsakaninsu son kai da kyashi yayi tasiri a zukatansu. Ahmad da Jafar su kadai suka fita daban. Su biyun sun zama tamkar zakka a cikin Ahalin Audu, halaye da ɗabi'unsu sun fita daban dana sauran. Allah ya haɗa jininsu suna bala'in ƙaunar junanau yanda suke mu'amala ba zaka taɓa ɗauka ba uwa daya ta haifesu ba, Binta tayi masifar tayi Bala'in har Malamai ta shiga akan ta raba Jafar da Ahmad amma abu yaci tura, Jafar din duk cikin yaranta tafi jinsa a cikin zuciyarta, tana da burika masu yawa akansa sedai tun fara tasowarsa ta fuskanci kwata kwata Alƙiblarsa daban da tata yanda kasan an canza mata shi a Asibiti idan badan kamanni da yakeyi da ita ba tsaf zata ce ba ɗanta bane. Duk abinda Jafar zeyi seya shawarci Ahamd haka shima Ahmad ɗin, makwancinsu daya, a makaranta ajinsu daya hatta da kayan sawarsu basu banbantawa guri daya suke ajiyesu. Data rasa yanda zatayi domin tana so taja Jafar ta fara kitsa masa abubuwan da take so ya cimma tun da shekarun ƙuruciya amma abu yaci tura, Turai ce ta bata shawarar ta tura Jafar Makarantar kwana tunda Aisha bata ao bata taɓa tura Yaranta ba tasan bazata bar Ahmad yaje ba a haka zata janye Jafar sedai a banza domin tana tayar da maganar bata ma san anyi ba seda ranar tafiya tazo taga Ahmad ya shirya shima babu yanda ta iya ta barsu suka tafi akan zata sake shiri. Daga sama Allah ya aiko mata da mafita, Jafar yana son kwallo tamkar ransa wanda ita kuma bata so domin tana gabin Kwallon na ɗauke masa hankali ta hanashi karatu Rana tsaka Babban Yayansu ya kirata akam ya samarwa Jafar gurbin karatu a Acadami ta Ƙungiyar Manchester dake Ƙasar Ingila ta sanarwa da Audu idan ya yarda a fara shiri. Da fari taƙi, tana gani za'a cuceta a cutar mata Ɗa ita da take da buri akansa acw ya tafi wata makarantar Ball, amma da Yayanta ya kwatanta mata irin Kuɗin da yan kwallo suke samu take ta amince ta kumayi murna ko banza ta samu hanyar raba Jafar da Ahmad. Wannan tafiya ita ta raba Ahmad da Jafar, Ahmad baya bal Jafar kuma baze iya barin burinsa ba dukda a farko yaso yayi tirjiya akan baze tafi na se sun kammala sakandire idan Yaso Yaya Ahmad kamar yanda yake kiransa ya nemi Jami'a a can su tafi tare amma Ahmad ɗin ya ƙarfafa masa guiwa akan ya tafi basu rabu ba suna tare, hakan ko akayi shekarunsu goma sha uku a lokacin Jafar ya koma Ingila tareda kawunsa ya zama se Ahmad kadai a Najeriya, burin Binta ya cika na rabasu saura kuma na aiwatar da shirinta akan Jafar din domin ba wai kwallon ta kwanta mata bane har a rai Madarar kudin da Yayanta yace mata ana samu ne yasa harta yarda ta barshi ya tafin. Rayuwa taci gaba da gurgurawa abubuwa da yawa sun faru na dadi da akasin haka, anyi rashe rashe yan uwan Audu gaba daya sun kwanta dama ya rage dashi da Yakubu se Bilki data dade da dawowa gidansa da zama tunda suka bar Goron Dutse suka koma Hotoro GRA inda ya tamfatsa gida Gari guda me sassa babu Adadi lokacin ne kuma ya ƙara aure ya auri Rabi'atu yar Malam Haladu Shugaban Maroƙa na wannan shiyya. Malam Haladun shiya tallatawa Ausu auran yarsa a lokacin Audun nada niyyar neman Aure domin yana ganin yaci ace ya ƙara mata dukda ya auri wata Fa'iza a can yawon Ƙasashen duniya suka haɗu da ita amma bata kai ga tarewa ba auran ya watse dalili yace sedai tazo gidansa ta zauna ita kuma tana ganin da uwar kuɗinta da gidanta sedai ya bita har an daura da taƙi tarewa ya sallameta iyalansa basu sani bama se bayan da auran ya mutu wannan tasa ganin Rabi'a tayi daidai da tsarinsa kuma yayi tambaya gun Malaminsa domin tuni shima ya zama dan hannu a sabgar Malamai baya abu da ka kamar yanda suke faɗi aka tabbatar masa Rabi'ar hadinsu yayi daidai shikenan ya Angwance abinsa. Shekararta goma sha biyar kenan, da ace tana da zuciya koda yake acw iyayenta nada zuciya da tuni sun kashe Auran sun huta da gorin Binta. Bala'inta daya kwanta dama ta tattaro ta maido gaba daya ta ɗorawa Rabi'a, gorin safe daban na rana daban na dare daban yar matsiyata yar Maroƙa, tun ba data fara zuba Yaya tayi Namiji na fari daga nan hankalin Binta ya sake tashi, da tayi na biyu tagwaye mata se ta ɗan samu sassauci ana uku ma ta sakeyin Mace sannan ta dakata da haihuwar wannan yasa Binta data koma Hajiya a yanzu ta ɗan ɗaga mata ƙafa kadan daga kwarzabar da take mata ta sake mayar da hankali ga Audu da dukiyarsa da kuma yanda zasu gaje komai ita da Yaranta. Babangida da Aminu su kadai suke aiki a ƙarƙashin Audu wanda suma sun shiga gurin ne bisa tursasawar Yakubu da ya zamewa Binta ciwon ido. Duk sanda wani ya mutu a gidansu Ausu se tace inama Yakubu ne ya mutu, ita dai ya tsare mata abubuwa da dama shi yake rage mata Tasiri yana kuma hanata rawar gaban hantsi. Sanda taso ta watsa duk wani Ahalin yan Bechi da yake aiki a ƙarƙashin Audu ta gama shirya yanda zatayi ta saka ya sallamesu Yakubun ne ya watsa mata shiri. Dukda haka bata saraya ba kuma a ƙalla taci riba domin tayi nasarar ɗora Yaranta a manyan kujeru na jan ragamar kamfanunuwan Audun. Zakariyya shine Manaja na baki ɗayam BECHI GROUP OF COMPANIES, Naziru kuma shine Shugaban sashin Manfetur da sauran Albarkatunsa ɓangaren daya fi kowanne samar da kuɗin shiga, Aminu shi aka dora a matsayin Akanta kujerar data so ace Yakubunta ne akai amma hakan bata samu ba se a yanzu suke saka ran faruwar hakan. A sauran Yaran gidan kuwa, Hassan ya zama Likita harta kai ga bude Asibiti na kansa wanda babu ƙwandakar Audu a ciki, be tambayeshi ba shima kuma beyi yakanar ya taimaka masa da wani abu ba yanda besan ya akayi yayi karatunsa harya kai wannan matsayin ba haka nan besan yanda yayi ginin Asibitinsa ba. Babannan harkar Noma ya kama domin shi dakyar yayi dipiloma ya ajiye boko ya koma Bechi ya cigana da Noma gonar da suka Gada gurin Bara'atu kuma Allah ya saka masa Albarka abun musammanda Babangida shima bangaren Harkar Noman ya karanta shiyasa ma Yakubu ya dage seda aka naɗashi shugaban sashin harkar Noma shi yake taimakawa Babannan ɗin da dabarun Noman zamani da Iri masu kyau dan haka sosai yake samun Alkhairi a sabgar ya siyi gonaki da yawa yana ta Noma abinsa acan Bechi Yayi Aure yake zaune da Iyalansa. Hussani shugaban masu taurin kai da kunne na gidan kenan, da fari yaso ya bi wata hanya ta daban, damuwa tasa yaƙi karatu ya fara bin Abokana banza yana shaye shaye, da Addu'a da Nasiha Zubaida data janye Yayanta da dabara ta samu kansa, be cigaba da Makarantar ba ya kama kasuwanci kuma yana da Nasibi kamar Audun sega harka ta buɗe masa dukda girma ya fara zuwa amma dai ba'a bar Yan bushe bushen duka ba shiyasa idan buyaginsa ta tashi babu me shiga sabgarsa a gidan dan ko Alhajin daidai yake dashi. Aliyu ma dai Injiniyarin ya karanta yana kuma aiki a wani babban Kamfani a Legas shigarsa Kano ma shi se sa'i da lokaci, cigaban da suka samu ya zama duk cikinsu babu wanda ya lalace ko yake aikata wani abu na Ashsha ba ƙaramin cin zuciyar Binta yakeyi ba, taso ace nata ne kadai suka ci gaba a gidan, taso rayuwar sauran ta tagayya ta yanda zasu zamana babu mamora se abinda suka yaga suka basu amma hakan ma babu laifi yanzu rayuwar ta fara. Yakubu ya zama Alƙali har seda ya kai ga zama Mataimakin Shugaban Alƙalan Najeriya kafin yayi Ritaya, rayuwar gidansa kishiyar rayuwar gidan Audu ce, Matarsa Ɗaya tilo har wayau Balaraba suna zaune cikin Amince da Yara Biyar data haifa masa Mata uku duk sunyi Aure se Maza biyu suka rage,Audu ya fishi, kudi, yawan zuri'a da kuma suna a duniya domin sunan Audun ba iyakar Najeria kadai ya tsaya ba a yanzu yana cikin jerin manyan masu Kuɗi a Africa duk wanda ya kwana ya tashi ya san da zaman Mamallakin BECHI GROUP OF COMPANIES wato ALHAJI AUDU BECHI sedai shi kuma yayiwa Audun zarra a gurin samun NUTSUWA DA KWANCIYAR HANKALI TAREDA AHALI ME CIKE DA QAUNA DA KUMA SOYAYYA. END OF BOOK 1 *ALBISHIRINKU MATA YAN UWANA YAN KWALISA NAZO MUKU DA WANI DADDADAN LABARI!!!.* *NASAN KUNDADE KUNA NEMAN FITACCEN GURIN DAZAKUJE AMUKU GYARAN GASHINKU DANA JIKINKU CIKI DA WAJENSA,TO YANXU DAI GA DAMA TA SAMU...* *LABARI NAKE BAKUFA AKAN AFINTY QUEENS SHAHARARREN SHAGONMU NA SALOON DAYA HADA KOMAI DA KOMAI DA KOWACE MACE YAR KWALISA IRINA KE BUKATA,SANNAN MUNADA KWARARRUN MA'AIKATAN DASUKASAN KAN AIKINKINSU,KUZO AFINTY QUEENS KUBIYA KUDI MUKUMA MU BATA LOKACINMU DOMIN TSATSTSAFO DUK WANI KYAWU NA JIKINKU DA ALLAH YAYI MUKU...* *A AFINTY QUEENS MUNA AYYUKA KAMAR HAKA:* *- HAIR SALOON* *-HENNA* *-SPA* *-DUKKAN* *-PEDICURE* *-MANICURE* *-SANNAN MUNA DA TURARUKA IRIN NA AMARE YAN MATA DA KUMA MAI KANKAT DAN UWAR GIDA TA TURARA GIDANTA JIKINTA DAMA KAYAN SAWARTA ITA DA YARANTA,,HARMA ZAWARAWA DUK MUN TANADI KOMAI* *DOMINSU SUMA* *-MUNADA SHOES AND BAGS SBD ISASSUN MATAN DA SUKA AMSA SUNANSU MATA*😊 *- MAKEUP NA BRIDAL ND CASUAL...* *IDAN KINSAN KINAJIN LABARIN SHAGON SALOON NA AFINTY QUEENS AMMA BAKI TABBATAR DA YADDA AIKINSU YAKE BA TO YAR UWA GADAMA TASAMU MEZAKI TSAYA JIRA MAZA KEMA KI ZARGAYO SHAGONMU DAZAN JERA MIKI ADDRESS DINSHI A KASA DOMIN KEMA KI TABBATAR DA KALAR IRIN NAMU KWAZON DA MUKA KWARE AKANSHI GURIN GYARAN JIKIN YAN UWANMU MATA KUMA MUKE GABATAR MUSU DA JAKUNKUNA DA TAKALMA HARMA DA TURARUKAN WUTA DANA SHAFAMA JIKINSU DON NISHADIN ZUCIYARSU DANA MAZAJENSU....* *AFINTY QUEENS DISCOVER BLISS IN BEAUTY 💅💯* *Address 👇👇:* *KU ZIYARCE MU A SHOP NO.9&10 SHEMA PLAZA,BEHIND SHEMA FILLING STATION KASUWAN BACCI KADUNA* *TEL:08133379628.* *MATAR MUTUM* *NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER* *FIKRA WRITERS ASSOCIATION* *LITTAFIN KUDI NE* *PAY 500 A ASUSUN* *7061838488* *OPAY DIGITAL SERVICES* *MARYAM FAROUK* OR *0709290797* *ACCESS BANK* *SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488* *IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705* *Kuyi following dina a Arewabooks @Maryamfarouk01 inda zaku karanta wannan littafin tareda sauran littattafaina* *NAGODE* *BOOK 2* *PAGE 1* "Alhaji! Alhaji!! Alhaji!!!" Taratsi da kwaroroton Binta ya maido shi daga cikin duniyar tunanin daya lula. Ya yunƙura ya zauna da kyau yana cije baki saboda yanda bayansa ya ƙage, baya iya dogon zama tun Hatsarin daya samu shekaru goma da suka wuce a hanyarsa ta zuwa Kaduna Jana'izar Alhaji Zakariyya Mahaifin Binta shikenan yake fama da Baya dukda iyakar bincike ance babu abinda ya samu bayan nasa amma kam yana ji a jikinsa ga kuma shekaru da suka miƙa wannan yana daga abinda yake ƙara ta'azzara masa ciwon. "Alhaji lafiya kuwa? Nakusa minti goma tsaye akanka ina magana kayi shiru badan idonka a buɗe yake bama ai ɗauka zanyi ka mutu" Bintan ta sake faɗa tana zama a gefensa. Ya tsura mata ido, ya rasa dalilin daya saka ranar Allah ba zata fito ta koma ba tareda Binta ta kawo zancen mutuwarsa ba, ya rasa meya tsare mata a duniya da take cike da burin taga ya kau. "Kaci abinci ma kuwa? Koda yake la'asar sakaliya yaci ace kaci abincin rana ai" tayi tambaya kuma ta bawa kanta amsa tana tashi tsaye ta nufi firjin dake cikin Makeken Bedroom ɗinsa me kama da Turakar wani sarki. Ruwan gora ta ɗauko da Kofin tangaran da suke jere a saman firjin ta dawo ta zauna tana tsiyaya masa data gama ta miƙa masa babu musu ya karba dan yana buƙatar ruwan. "Ya kukayi to? An samu kuɗin sun fito?" Ta jefa masa ainihin maganar data shigar da ita gurin nasa. Ya kurɓe ruwan yana gyara zama yace "Ba'a samu ba, yace besan inda suka shiga ba kuma na yarda Aminu baze yimun sata ba dan haka maganar ta ƙare dukma wanda yayi sama da faɗi dasu shida Allah kuma a sannu wata rana asirinsa ze tonu" "Kace me? Miliyan dubu dari biyun harda ɗori kake cewa kabar mutum da Allah akanta Lallai ma Alhaji, tsaya ma, yanzu kai har kana da bakinda zaka shaidi Aminu? Yaushe ka zauna dashi da har kasan halinsa da zakace bazeyi maka sata ba?" Binta tayi maganar a zabure. Alhaji Audu ya kalleta sheƙeƙe yace "Waini nawane kasonki cikin kuɗin nan Binta da duk kika bi kika tashi hankalinki kamar ma kin fini damuwa da abinda ya faru?" "Ni kuwa nake da kaso a ciki, karka manta Yara goma na ƙyanƙyashe maka a gidan nan ga Takwas nan a raye cikinsu kuma Zarata shida duk mazane kaga kuwa ni nake da Kaso a cikin dukiyarka kuma bazan zuba ido ina kallo a ringa damfararmu sannan kayi shiru kace ka bar mutum da Allah ba" ta bashi amsa tana kaɗa jiki tareda juya ido kamar wata ƙaramar yarinya, ya buɗe baki ze bata amsa sallamar Momy ta dakatar dashi seya haɗiye abinda yayi niyyar faɗa ɗin ya amsa sallamar ta ƙaraso ciki hannunta ɗauke da ƙaton Try. Akan Centre table dake tsakiyar ɗakin ba tareda ta nuna tasan da zaman Binta a gurin ba ta kalli Alhajin fuska babu yabo babu fallasa tace "Ai bansan ka dawo ba seda nake nake cewa shiru kace kuma ba daɗewa zakayi ba sannan Baba Bilki tace ai ko taji shigowarka tunɗazun ta zata na sani shiyasa batayi mun magana ba" abincin ta shiga zubawa ta gama jere komai ta sauke kulolin daga kan Teburin sannan ta tura masa shi gabansa yanda zeji dadin cin Abincin. Wani ruwan ta sake dakkowa daga firji ta ajiye masa Binta dai kallonta take tana zare ido a ranta tana tunanin wai ya akayi ta gaza korar wannan sailubar matar har suke dosar shekaru Arba'in tare a matsayin Kishiyoyi? "Bari nayi sallar La'asar se naci abincin" Alhaji Audu ya faɗa kafin ya yunƙura ya shige banɗakin dake manne da ɗakin barcin nasa. Momy ta zauna kan doguwar kujera kwaya ɗaya dake cikin ɗakin Hajiya kuma har sannna tana zaune kan gado tana ƙarewa Momyn kallo kamae wata farin shigar Maita har Audu ya fito ya tada sallah ya idar ya hau kan abincinsa Binta na zaune ita kuma Momy bata ce mata ta fita ba dukda zaman nata ya ɓata mata rai. Har a yanzu da shekaru suka miƙa tsakanin ita ko Rabi babu wadda ta isa ta shiga Turakar Alhajin a ranakun girkin Hajiya Binta amma ita ko a kwance suke tana iya faɗo musu a yanzu ne kuma Alhaji Audun yake son ya gyara wannan barakar har yake ƙoƙarin taka mata burki wasu lokutan sedai a banza domin ta rigada ta raina shi, bashi da wani kwarjini ko Martaba a idonta da zw ce tayi abu tayi ko ya hanata ta hanu har ila yau kuma zancen tayi laifi ya mata faɗa kamar yanda yake musu fa babu shi, ita lamarin Alhaji da Hajiya Binta ma har rasa matsayin da zata ajiye shi takeyi dan ko a labarai bata taɓa cin karo da Macen da take zuba sharafi a gidan Auranta irin Hakiya Bintan ba. "Ina kin gaka abinda ya kawoki?" Muryar Audu ta ratsa kunnuwansu, Momy na danna waya ta ɗago so take ta fahimci dawa yake a cikinsu? Ita me girki ko kuwa Binta data zo ta tasasu gaba? Hamshaƙiyar kuwa ƙara gyara zama tayo dan a tsammaninta da Aishar yake seda ya sake maimaita maganar yana kallon idonta kafin ta ankare, ta buɗe baki zata faɗa masa ba dadi se kuma ta gimtse data tuna tanada shirin da take so ta cimma seta miƙe tsaye tana murmushi tace "Ai to bari naje, duk na shafa'a ne wlh se naga kamar a Ɗakina nake". Tana dafda fita daga ɗakin wayar Momy tayi ƙara alamar shigowar kira, Hajiya ta fice amma ta coge a bakin ƙofa ta kasa kunne, abin ya rigada ya zame mata Ɗabi'a ko ace ciwo, gulma da Laɓe, tsabar yanda ta ɗorawa kanta bala'i ko a hanya take tafe taji wasu na ƙusƙus seta dakata ta kasa kunne ko ba zataji ko ta fahimci abinda suke faɗi ba, ga zargi da tsarguwa ko yayan cikinta taga suna magana seta tsargu da ita suke ko wani abun suke shiryawa. A cikin ɗakin kuwa a speaker Momy ta saka wayar saboda kunnenta dake mata ciwo kwana biyu bata kara wata a kunnen muryar Ahmad ta ratso wayar yana cewa "Momy, kin masa maganar kuwa?" "Tukunna dai, wai idan sauri kakeyi haka ka tareshi da kanka kayi masa maganar mana seni zaka mayar yar aikenka" ta bashi amsa. Daga waje Binta ta sake manna kunne a jikin ƙofa tunda taji muryar Ahmad da kuma cewar anyi magana wace maganace? Abinda take so kunnuwanta su zuƙo mata kenan. Ahmad ya sake marairaicewa Momy yana cewa "Haba sweet mother, haba rabin raina kinsan dai bazan iya tunkararsa ba kuma na gaya miki Jafar ya masa magana yace he will get back to us yanzun kusan one month kenan bamuji komai daga gareshi ba and time is really against me Momy, idan baze samu ta hanyar sa ba na sani na nemi wani Alternative ɗin kinji Mamana? Ya ƙarasa maganar kamar ze saka mata kuka yana idarwa kuma tari ya sarƙe shi" "Bakaje Asibitin da nace kaje ba kenan?" Ta jefa masa tambaya ba tareda tabi ta kan maganar da suka fara ba, Ahmad da tarin ya tsagaita masa yace "Naje wlh Momy an rubutamun magani na ma farasha, kiyi masa maganar yanzu dan Allah kinji" "Zanyi" ta faɗa a taƙaice daga nan ta kashe wayar. Alh Audu na cin abincinsa kuma yana sauraron duk wayar da sukeyi tuni kuma ya fahimci zancen da tunin da Ahmad ɗin yake magiyar tayi masa. Ruwa yasha yana kallonta yace "Shi baze iya zuwa ya sameni muyi magana ba se ya ringa turomun yan aike?" "Wane shi? Wannan ai se Yayan gida Yayan So" ta bashi amsa hankalinta na kan wayarta se yayi shiru yana kallonta, a yan shekarun nan Aishar ta fara canzawa, idan tayi wani abun se yaga kamar ta fara gajiyawa dashi ne kamar me neman wani dalili da ze janyo saɓani a tsakaninsu. Ajiyar rai yayi yace "Ai shikenan, kice masa gobe ya sameni a gidan Gona na Kwanar Dawaki se mu tattauna maganar kuma yazo da takaddun" "Baka da lambar wayarsa kaima kenan?" Ta faɗa tana tsareshi da ido, tamke fuska yayi be kuma bata amsa ba ya shige banɗaki wanko hannu. Tayi tsaki a ranta wani abu me ɗaci yana taso mata seta miƙe ta shiga tattara kwanukan daya gama dasu ta ɗora akan Try ɗin data kawo su ta fita. A bakin ƙofa sukayi kiciɓus da Hajiya dake dakon jiran a faɗi gundarin abinda take so taji buƙatar da Ahmad ɗin yake nema a gurin Alhajin da har yace ya sameshi a gidan Gona. Kardai fa tufka take ta baya tana warwarewa tana nan tana haƙilon ganin sun danne komai Aisha ta ringa mata zagon ƙasa suna wawasa ita da Yayanta? Dole ta Ƙara saka idanu kenan akan harkar shige da ficen gidan da duk abinda yake faruwa wannan maganar ma da ba'a ƙarasa ba seta bi diddiginta tunda sunan Jafar ya fito a ciki shi zata tambaya dukda dai shegen Yaro ne ba lallai ya faɗa mata ba tunda sirrin ubansa Ahmad ne. Tana ganin Momyn ta ɗan diririce se kuma ta waske ta tura ƙofar irin dawowa ta sakeyi zata shiga. Momyn ta kaɗa kai kawai ta wuce, ba yau Hajiyar ta sababa Laɓe ya zame mata ɗabi'a. Hajiya na ganin Momy ta sauka ta juyo itama ta fice dan akwai abinda yake a gabanta yanzu kafin ta juya takan zancen Ahmad ɗin, ɗakinta ta wuce ta tarar da YAKUBU na cin abinci, Hajiya ƙarama na tsaye gaban console mirror dake falon tana gyara ɗaurin kallabinta. Ganinta yasaka Binta sakin fuska ta washe haƙwaranta duka, guda biyu data sakawa Haƙorin Makka na zinari sunata ƙyalli, Umarar Bara da sukaje ta cire Asalin guda daya na bakinta daya cinye aka saka mata biyun. "Kinyi kyau uwar masu gida, yau zuciyar mahassada sedai ta buga dan baƙin ciki" Hajiyar ta faɗa tana ƙarasawa kusa da ita. Hajiya ƙarama ta saki murmushi kafin ta shiga juyawa dan ta nunawa Hajiyar kwalliyarta dakyau, Fitted gown ce ta wani cotton London Brocade a jikinta dark blue me zanen flower sea green da fari a jiki, kudinsa ya tasamma dubu sittin, Jafar ne ya aikowa da Hajiyar su sun kai guda goma yace a ɗinka mata dogayen riguna saboda laushinsa yasan zeyi dadin sakawa shine Hajiya ƙaramar ta kwashe uku dan tasan ba ɗinkawa Hajiyar zatayi ba ta kai aka mata lalatattun dinkuna a ciki wannan fitted gown din itace me ɗan dama dama dan ta rufe mata jiki gaba daya illarta kawai shape dinta daya bayyana ƙarara. "Kin fa gama haɗewa Yar nan babu makusa" Hajiyar ta sake faɗa tana bata hannu suka kashe daidai nan wayarta tayi ƙara, sunan Abba Tee ya bayyana akan screen ɗin. Tsanar dadi harda wani maƙale hannaye Hajiya tayi sama kamar Kangaroo bakin nan ko har maƙogaronta ana hangowa, Hajiya ƙarama ta amsa wayar cikin muryar shagwaɓa kamar zata fashe da kuka tace "Harka iso" "Yes Babe, ina waje" ya bata amsa daga cikin wayar, ta sake narkewa tana cewa "Baka shigo ciki ba? Issa baya nan ne? Kayi horn ze buɗe maka Get ya shogar dakai palour kafin na fito" "He isn't here, oh kamar gashi nan wani Buzu ko? ya buɗe Get ɗin bari na shigo" " Saurayin ya sake Faɗa kafin ya katse wayar. Hajiya ta sake bata hannu suka kashe tana cewa "Wai, Allah ya taimakemu, maza kije ki ƙara turare, duba ɗakina akwai wannan Disaina da kike nacin na baki na gurin Yayanki ki ɗauka, bari na duba abincin idan sun kammala" "An gama kumai har na shirya a Try kaowa kawai za'ayi" Inji Hajiya ƙarama "Yauwa yar gari, jeki to kar yayita zama Allah ya bada sa'a" cewar Binta. Hajiya ƙarama ta wuce ɗaki ta ƙaro turare kamar yanda Binta tace ta fito tana takun yauƙi Albarkatun jikinta na motsawa danma kayan jikin nata sun matseta kam hakan ya rage musu samun damar rangaji yanda ya kamata. Yanda Yaran Alhaji Audu Maza suke Dogaye ginannu idan ka cire Ahmad daya ɗauki Jikin Aisha bashida ƙiba sam haka beyi irin tsahonsu ba to Matan ma duk haka suke dogaye masu cikakken jiki, Allah ya taimake su da ƙira mai kyau ta jiki data fuska musamman da dukansu se akayi katari suka ɗauko fuskar Dada, Farare tas ɗin cikinsu Amina, Aslmaiyya da Hajiya ƙarama da yan Biyun Hajiya Rabi Baba Bilki takance kamanninsu kwabo da kwabo da Dadarsu. "Yauwa, saura kuma ki sake maimaita abinda kikayi wancan karon kika saka yayi fushi, kina kallo dai har dubuta dari Turai ta damfareni, koda yake kwalliya ta biya kuɗin sabulu tunda an janyoshi yazo, soyayyar nan ta zamani ke sekace ba wayayya ba da ita ake kama samarin nan, banda abinki waye ze kwasheki haka siɗan ba tareda ya tabbatar kin iya kalar soyayyar da yake da buƙata ba, yar rungumar nan da kis ne dai Allah na tuba ai ba wani abu bane, ban dai ce kije ki buɗe kafa ba ki saka mu shiga uku kuma kuyi a hankali Alhaji ma sama ze iya saukowa kowan...." "Hajiya!" YAKUBU da ke cin abincinsa tun shigarta be tanka maganar da sukeyi ba ya kira sunanta cikin ɗaga murya me kama da tsawa dan a firgice daga ita har Hajiya ƙaramar suka kalleta kowacce na tsammanin da ita yake. Farantin gabansa ya ture ya miƙe tsaye fuskar sa tamkar zatayi aman bacin ran daya turnuƙeshi lokaci daya. Ya nuna Hafsatu da yatsa yana cewa "Ashe abinda ake faɗa akanki gaskiya ne? Iskancin da aka ce kinayi dagaskene saboda kin shahara yanzu har cikin gidan ubanki kika kawo saurayi zakuyi iskanci?" Kai ta shiga girgiza masa tanaja baya domin Yakubu bashida daɗi, ba su ba uwar data haifeshi ma shakkarsa takeyi dan Lamarinsa me girma ne. Hajiya Binta ta dake tana hararar sa tace "Kai bana son ɗiban Albarka, a gidan uwar masu faɗar aka ganta tana iskancin? Koda uban wani tayi a cikinsu da har suke bayar da shaida? Bakaji me nake faɗa bane? Ce mata nake fa ta saki jiki dashi ita ai gida huma ce duk samarin da kake gani suna zuwa suna tafiya ai ƙin basu fuska takeyi shi yake korarsu. Shifa wannan ɗin in gaya maka, Yaron Alhaji Mudi Tanko ne tsohon Senet piresiden kuma yanzu haka takarar gwamna yake a Garinsu, can kwanaki bana muku zancen sa ba har yazo sau ɗaya shine ya tafi be sake dawowa ba? Ai in gaya maka wannan shashashar yarinyar ce ta kusa kwafsa mana, wai fa ɗaukarta yayi sukaje Otal ya kama Ɗaki, daga cewa su shiga ciki shikenan ta gudo wai har da ce masa ita ba yar iska bace se kace yace mata wata tsiyar ze mata idan suka shiga. Shiko yayi fushi ya tafi, dakyar fa yanzu seda na baiwa Turai dubu ɗari ta kaiwa Malaminta akayi aiki akansa shine fa ya zo yanzu, faɗan da nake mata kenan kar a maimaita ta wnacan karon a samu a kamashi a hannu ya fito ayi zancen Auren nan masu yi mun dariya su sha kunya suji da ƙaryar sarauta suzo suga Arziƙi a inda yake dan duk na samu labarim gidansu ba ƙaramar wadaƙa ubansu yakeyi idan ya tashi Aurar da Yara ba". Yanda take maganar hankali kwance tamkar me faɗar wani abin Arziƙi, Yakubu yayi sakato yana kallonta a ransa kuwa kokwanto yakeyi akan Hajiyar ce ta haifi Hafsatu ko kuwa Riƙonta takeyi? Anya uwa zata yiwa yarta irin wannan huɗubar kuwa? "Zatayi mana, mussamman uwa irin taku da take bautawa duniya da abinda yake cikinta" zuciyarsa ta bashi amsa. Seya ja numfashi ya furzar kafin ya zabura ya nufi ƙofa, cikin Hajiya ƙarama ya kaɗa, Hajiya kuwa yatsine fuska tayi tace "Ke da Allah rabu dashi, ance masa bansan duk abinda sukeyi bane su? Duk fa haka suke lallatse yammatan suma suna basu kuɗi balle ke da Aurenki ma zeyi jeki abinki manta dashi kar kuma ko manta uar soyayyar nan da ake nunawa a fim irinta zaki masa kinji ki hargitsa masa tunani yayi maza maza ya turo azo ayi magana kar zancen Auran Aslamiyya ya riga naki tashi". A saluɓe Hafsan ta fita duk karsashin da take dashi ya barta. A ƙofar fita daga ainahin cikin gidan taci karo da Ali Daya daga cikin Ma'aikatan gidan me kula da shuke shuke, da gudu ya taho badan ta matsa masa ba da tuni yayi tafiyar gari da ita. "Yawwa Hajiya kiyi sauri, ga Alhaji Yakubu can yana dukan baƙonki" ya faɗa yana haki. Ƙirji ta dafe tana zaro ido daga inda take kuma tana iya jiyo ihun kukan data tabbatar na Abba Tee ne da kuma hargowar Yakubu yana faɗin "Daga yau ka sake zuwa wani gida ka yi iskanci da ƙanwar wasu". Da gudu ta juya ciki tana kuka tana kiran Hajiya. Binta nacan tana gyara zaman kofunan da za'a kaiwa Baƙon tana kwararaqa me aikinta Ashar akan wai bata goge su dakyau ba so take yace musu ƙazamai sega Hafsa na kuka jage jage, bata ko iya sauraronta gaba daya ba tayi waje cikin tashin hankali tana kiran Yakubu. Yakubu kuwa dukan Ɗa da Uba yakeyiwa saurayin Hafsatu ya fasa masa baki da hanci ga hauri yana kai masa a ƙafafu yana kiran seya karya su yaga da wanda ze ringa yawon iskancin Hajiya ta iso ta cakumeshi tana zaginsa se kuma ta saka kuka tana cewa "Shikenan kaima an taɓa ka, nidai yanda naga ka fito ido a jirkice daman kamar wanda iska ta shafa nasan da walakin, ni aka tozarta a gidan nan ko? Anga Asirin da akayiwa Yata yaƙici kullum sababbin Manema take samu shine aka biyo ta wannan hanyar ko? To wlh mu zuba mu gani, bana Boka bana Malam amma ko wanene ya taɓani seyaji a jikinsa" se kuka wiwiwiwi. Ma'aikatan gidan gaba daya sukayi dafifi suna kallon ikon Allah, Drama a gidan dai ba sabon abu bace ta safe daban ta rana daban ba kuma sa gundira da tirka tirkan gidan domin kullum sabon abu suke gani. Audu da hayaniyar ta fito dashi ya isa gurin cikin dakakkiyar murya yake tambayar abinda ya faru se sannan kuma Abba Tee ya samu ya miƙe ya nuna Yakubu yace zasu gamu seya san shiya taɓa, Yakubu ya zabura ze sake damƙarsa ya taka ya gurin motarsa da sauri ya shige yana cigaba da faɗin "We shall meet in court, zaka san ni ka daka se ka gane baka da wayo". Cikin tsawa Audu ya bawa ma'aikatan umarnin su watse kowa ya juya gurin aikinsa. Ya kalli Hajiya dake kuka har sannan Hafsatu ta runguketa itama tana kukan kafin ya mayar da hankalinsa kan Yakubu yana tambayarsa meya faru? Waye wancan ɗin kuma meya haɗa u harta kai ga duka? Kafin ya bashi sa Hajiya tayi zuruf tace "Me kuwa ya haɗasu? Magautane sukayi masa turen Aljani haka kawai ya rufeshi da duka saurayin Hafsa ne fa, anga Allah ya fito mata da Miji na nunawa Sa'a shine aka bi yanda akayi shima aka koreshi kuma wlh ba'a taɓa banza ba ko wacece a cikin matanka tayi abin nan ta kwana da shirin zubin Adashi tayi ɗauka kuma dole, ka wuce kai kuma ka kwanta kana tsaye kana wa mutane muzurai ko Aljani ƙarƙuzu ne wlh sekaci ubanka sannan ka koma kan wadda ta aiko ka" ta faɗa tana aikawa da Yakubu wata harara me tafe da gargaɗi. Juyawar yayi kamar yanda tace ya fice daga gidan gaba ɗaya ita ma suka koma ciki da Hafsa dake kuka har sannan. Alhaji Audu ya sauke ajiyar zuciya me ƙarfi yana kallon Ma'aikatan gidan da duk suka maida hankali kamar masuyin wani abun ya tabbatar kuma kunnuwa da hankulansu har sannan yana kansu, an gama na ɗazu ga wata an sakeyi kuma, idan ba'ayi sa'a ba kafin kwanciyar bacci se an kuma kafta wata Drama. A sanyaye ya ringa taku ya fita ya shiga Masallacin dake manne da gidan tunda Magriba ta kawo kai saura mintina kaɗan a kira. Carbi yake ja amma ya lula cikin tunanin daya aureshi, bashi da damar yayi shiru haka nan ko yayi tunanin abu me daɗi kullum se damuwa se ɓacin rai daga wannan se wannan. Wayar sa dake gaban Aljihu ta ɗauki Ƙara ya zarota, Alƙali Yakubu ne, miƙewa yayi ya fice daga cikin masallacin ya tsaya daga gefe lokacin wayar ta katse dan haka yabi bayan kiran. A taƙaice suka gaisa, Yakubun ya tambayeshi yanda Zaman su ya ƙare da matsaya akan zancen kuɗin. "Mun rigada mun gama magana yayi rantsuwa akan bashi ya ɗauka ba kuma na yarda amma na sauke shi daga kujerar Takwaranka ze riƙe na lokacin kafin musan abinyi" Audun ya faɗa masa. Daga ɗaya ɓangaren Yakubu yace "Idan har ka yarda dashi menene dalilin daya saka ka dakatar dashi daga aiki kuma?" "Haka dokar take a rubuce, duk wanda aka kama da laifin cin hanci ko yiwa Kamfani zamba hukuncinsa korace sannan ze maido da duk abinda aka rasa, bamu baƙaci ya mayar da komai ba amma an dakatar dashi saboda idan banyi haka ba kamar na buɗe Ƙofa ne ga sauran kowa ze iya wasarere da dukiyar Kamfani saboda yasan babu matakin da za'a ɗauka akansa, kuma dalilin daya saka bamu buƙaci ya maido da kuɗin ba saboda Bincike ya tabbatar da basu shiga account ba, a rubuce ne kawai akwai su kuma idan aka tattara lissafi ya kamata ace suna ciki sedai am rasa ta inda suka maƙale". Dariya jawabin Audun ya bawa Yakubu ya dara kafin yace "Ai shikenan, tunda har ka gano da kanka inda matsalar take ina ganin babu laifin Aminu kamata yayi ka tattara shuwagabannin kowanne ɓangate su gabatar maka da lissafinsu da kansu sannan ka haɗa dashi wamda suka bashi daga nan za'a tantance me laifi da me gaskiya, most especially guraren da kuke generating kuɗi sosai Oil da sauran Mineral su ya kamata ka tsananta bincike akai na tabbata daga nan matsalar take" Yakubun ya bashi shawara daga nan suka ɗan tattauna wasu batutuwan kafin sukayi sallama dalilin sallah da aka kira. A cikin gida kuwa a tsakar gida Hakiya ta kafa kujera tana zazzaga bala'i, daga Momy Har Anty babu wadda ta leƙo ballantana ta tanka mata daman da Baba Bilki tana nan ne itace zata kulata to tana gidan Sarki matarsa ta haihu ita take zauna mata. Har aka kira sallar Magriba batayi shiru ba bakinta har kumfa yake yawu na sarƙeta amma taƙi haƙura ita kanta Hajiya ƙaramar datayi iyakar yinta akan Hajiyar tayi shiru taƙi ɗaki ta shige tana cigaba da kukan Asarar da Yaya Yakubu ya janyo mata, ita ai bata ce masa zata biye ta zancen Hajiya ba domin da tana hawa layin data ke ɗorata da tuni ta daɗe da zama riƙaƙƙiyar karuwa a cikin gida domin abinda Hajiyar take nuna mata kullum shine tayi komai ba komai bane muddinba bude ƙafa zatayi ba. Ta rasa irin tunani da son zuciyar Hajiya, bata duba mutunchinta ko zunubin da zasu ɗauka da ita me aikatawar da ita data turata burinta kawai ta cafko musu Dan Attajiri wanda ya kere Mijim Anna dana Khadija da kuma saurayin da yake neman Aslamiyya tunda bata samu yanda take so akan Nazira data janyowa Nakasar data so ta hanata Auruwa daga ƙarshe Audun ya haɗata da wani Yaronsa babu laifi yana da abin hannunsa daidai Misali shima kuma yana sonta. Ita Anna Ɗan Sarkin Zazzau ta aura Khadija kuma Wani Matashin Ɗan Kasuwa me jida Yayan Banki duk su biyun suna cikin daula da jin daɗin rayuwa ita Khadija ma zamansu rabi da rabi ne a Nigeria sunfi zama a Dubai wannan Daula da Yayan Momy suke ciki ta tsolewa Hajiyar Ido, sannan ga Auren da Sarki yayi ya Auro wata halfcast Ambariyya, Mamarya ce Bahaushiya yar Nigeria Babanta kuma Balaraben Qatar ne Hamshaƙin me Arziƙi Bikin Sarkin da yanda Uban Amaryar yayi wasan kuɗi ya gigita Hajiyar, ada tana hura hanci akan Matar Zakariyya da Matar Naziru yan manyan gidaje ne tana habaicin kaf Yayan gidan babu wanda ya auro Ya daga gida kamar nasu se gashi Sarki ya goge mata hadda ya auro Balarabiya wannan yasa ta sake cin buri akan Hafsa seta auri Mijin daya doke nasu Khadija sannan Jafar shi ze wanke mata takaicin Sarki ya samo wata tsaleliyar Baturiya ko Indiya shida yake sananne a Duniya ma ai Matar da ze Aura se an ganta kawai yanzun hankalinta yafi karkata akan Hafsa tayi Aure se kuma ta mayar da hankali kan Autarta Sarah. *ALBISHIRINKU MATA YAN UWANA YAN KWALISA NAZO MUKU DA WANI DADDADAN LABARI!!!.* *NASAN KUNDADE KUNA NEMAN FITACCEN GURIN DAZAKUJE AMUKU GYARAN GASHINKU DANA JIKINKU CIKI DA WAJENSA,TO YANXU DAI GA DAMA TA SAMU...* *LABARI NAKE BAKUFA AKAN AFINTY QUEENS SHAHARARREN SHAGONMU NA SALOON DAYA HADA KOMAI DA KOMAI DA KOWACE MACE YAR KWALISA IRINA KE BUKATA,SANNAN MUNADA KWARARRUN MA'AIKATAN DASUKASAN KAN AIKINKINSU,KUZO AFINTY QUEENS KUBIYA KUDI MUKUMA MU BATA LOKACINMU DOMIN TSATSTSAFO DUK WANI KYAWU NA JIKINKU DA ALLAH YAYI MUKU...* *A AFINTY QUEENS MUNA AYYUKA KAMAR HAKA:* *- HAIR SALOON* *-HENNA* *-SPA* *-DUKKAN* *-PEDICURE* *-MANICURE* *-SANNAN MUNA DA TURARUKA IRIN NA AMARE YAN MATA DA KUMA MAI KANKAT DAN UWAR GIDA TA TURARA GIDANTA JIKINTA DAMA KAYAN SAWARTA ITA DA YARANTA,,HARMA ZAWARAWA DUK MUN TANADI KOMAI* *DOMINSU SUMA* *-MUNADA SHOES AND BAGS SBD ISASSUN MATAN DA SUKA AMSA SUNANSU MATA*😊 *- MAKEUP NA BRIDAL ND CASUAL...* *IDAN KINSAN KINAJIN LABARIN SHAGON SALOON NA AFINTY QUEENS AMMA BAKI TABBATAR DA YADDA AIKINSU YAKE BA TO YAR UWA GADAMA TASAMU MEZAKI TSAYA JIRA MAZA KEMA KI ZARGAYO SHAGONMU DAZAN JERA MIKI ADDRESS DINSHI A KASA DOMIN KEMA KI TABBATAR DA KALAR IRIN NAMU KWAZON DA MUKA KWARE AKANSHI GURIN GYARAN JIKIN YAN UWANMU MATA KUMA MUKE GABATAR MUSU DA JAKUNKUNA DA TAKALMA HARMA DA TURARUKAN WUTA DANA SHAFAMA JIKINSU DON NISHADIN ZUCIYARSU DANA MAZAJENSU....* *AFINTY QUEENS DISCOVER BLISS IN BEAUTY 💅💯* *Address 👇👇:* *KU ZIYARCE MU A SHOP NO.9&10 SHEMA PLAZA,BEHIND SHEMA FILLING STATION KASUWAN BACCI KADUNA* *TEL:08133379628.* *MATAR MUTUM* *NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER* *FIKRA WRITERS ASSOCIATION* *LITTAFIN KUDI NE* *PAY 500 A ASUSUN* *7061838488* *OPAY DIGITAL SERVICES* *MARYAM FAROUK* OR *0709290797* *ACCESS BANK* *SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488* *IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705* *Kuyi following dina a Arewabooks @Maryamfarouk01 inda zaku karanta wannan littafin tareda sauran littattafaina* *NAGODE* *BOOK 2* *PAGE 2* Kiran sallar Magriba ne ya tasheta badan ta gaji da zazzagar da takeyi ba ba kuma ta gama ba zata cigaba. Ta bubbuga sallarta domin babu nutsuwa tattare da ita ko kaɗan tana idarwa ko salati bata iya tsayawa tayiwa Annabi ba taja waya ta shiga kiran Tirau. "Yaushe zaki dawo? Akwai matsala" ta faɗa ba tareda ta tsaya sun gaisa ba. "Jibi in Allah ya yarda, jirgi muka rasa yau shiyasa ma bamu taho ba se jibin muna Jidd ma, wlh ansha dake, da uwa kuɗinki matar nan ki biya mu tafi abi mu kikaƙi, tafiyar nan tayi daɗi yanda baki zato keni ban taɓa umarah me daɗin wannan ba yanzu ma muka dawo daga kanti munyo siyayya naga wasu riguna har zan kiraki idan kinaso a siyo miki na tuna da dai kyautace zaki karba koda yake ko kyautar ce babu lallai ki saka ma sedai ki Ajiye har su daddage su zama gari" Turai ta bata amsa cikin dariyar shaƙiyanci. Binta taja tsaki tace "Ai shikenan se kun dawo ɗin, idan kuma naga bazan iya jira ba zanje gurin Hajiya Halima kawai muyi maganar ai tasan gidan Malamin nan naki ko?" "Daɗina dake rashin saiti wani sa'ilin wlh Binta, ce miki nayi ina haɗen Malami da ƙawaye? To ai ko ke abinda yasa kikaga ina kai matsalarki gurin Malamina saboda nasan ba layinki bane dole tasa kike leƙawa kuma ba zakimun yankan baya ba. Ki kuskura ki kaiwa Halima matsalarki zaki gane baki da wayo wlh ke baki san da yawa neman hanyar ganin bayan mu akeyi bako? To idanbata kaiki inda za'ayi miki magani ba ta kaiki inda za'a ƙara dagula miki lissafi ai. Maganar Hafsatun ce ko yaya? Ba jiya kince mun yau yaron zezo ba? Be zo bane ko yaya? Amma abin da kamar wuya ace be zo ba dan kiranyen da Malam ya masa idan kinga be zo ba to a kabari yake dan wlh aikin da aka masa irinsa akeyiwa Riƙaƙƙun masu laifo kiji ance sun gudu daga Magarƙama to Aljanu ake turawa su ɗauko su, yauwa ya wancan zancen kuɗin komai ya tafi daidai ko? Dan ko ɗazu seda Malam ya mun tunin kasonsa nace masa ban dawo ba bamu zauna naji yanda ake ciki ba tukunna". "Uhm kedai Turai Allah ya kaimu jibin ku dawo ma zanta, maganganun da yawa ni na rasa ma abinda zanyi wlh" Bintan ta faɗa kamar abar tausayi, Tirai ta sheƙe da dariya tace "Ai Binta lamuranki kamar me bakin uwa, kiga abu rumi rumi an ƙullashi se yayi kamar yaci komai ya watse gaskiya ki tashi tsaye magauta sunga gadon barcinki lokacin daya kamata ki huta yazo, Yayanki sun kawo ƙarfi amma kuma kwanciyar hankali taƙi samuwa? Allah ya kaimu jibin to mu dawo zuwa gata seki shigo muji yanda ake ciki" daga nan sukayi sallama ta rafka tagumi tana tunani. Masifar gidan da kullum gaba takeyi ba baya ba ta sakata fara abinda bata da ra'ayi akai kwata kwata wato Bin Malamai, tun Kissar tana ci a sannu ta dena tasiri saboda an kai gaɓar da wata kwarkwasa ko kisisina ta dena tasiri akan Audun, sabgar Kasuwancinsa kawai ya saka a gaba, shekarun baya lokacin da yake ta tiri tiri da ƙoƙarin ganin BECHI GROUP OF COMPANIES ya tsaya da ƙafarsa lokacinsu ma wahala yake masa, ga tafiye tafiye ko yana ƙasar ma se su kwana su wuni basu sakashi a ido ba a wannan lokacin ne kuma tayi Arziƙi domin itace akan komai, Ashana idan babu a gidan gurinta za'a nema cefane se abinda taga dama za'a kawo ta ringa tara kuɗi tana siyar Kadarori, Filaye, gidaje ta zuba yan haya da kuma sarƙoƙin gwal wanda ba sakawa take ba suna nan narke a drawer wani Design dinma wanda suka ƙirkireshi sun manta da Kalarsa. Da su Zakariyya suka gama makaranta kuma dukda daman tun suna ciki take cusa su akan harkokin Audun kullum tana nuna masa ya kamata ace ya sakasu domin sune magadansa tun yanzu ya kamatu su san komai da yanda ake gudanar dashi ba wai se rana tsaka ne zasu kama abin ba, tun baya sakar musu har yazo dakansa ya yarda yana da buƙatar su horu akan sabgar kasuwancin nasa domin Bare ze iya ha'intarsa wata rana kamar yanda yake gani ga Abokanan kasuwancinsa da suka tashi tare da yawa sun durƙushe kuma idan aka bi kadi daga ƙarshe yakan kasance wasu daga cikin ma'aikatan gurin ne da suka fitar da sirrunsu ga abokanan Hamayya har hakan ya janyo durƙushewar gurin amma se tunanin sa be kawo masa cewar ba su kaɗaine yayansa ba ko kuma ba su kaɗai ne magadan nasa ba kamar yanda take faɗa, burinta ya cika suka samu gurin zama dukda da farko sun fara ne a ƙanana ma'aikata tafi tafi suna haɗa tuggu da manaƙisa irin wadda suka sha a Nono har suka saka aka tunɓuke asalin waɗanda suka da muƙamansu na yanzu suka maye gurbinsu. Aminu da Alhaji Babannan Alƙali Yakubu ne ya cusa su a gurin da kansa, duk kuma bala'inta haka tayi ta haƙura wannan tasa ta matsa Yakubu ƙarami sukayi yanda sukayi har suka ciccibashi ya kai matsayin mataimakin Accountant General wato mataimakin Aminu a birinsu na ganin a sannu sun tunɓuke Aminun se Yakubun ya maye gurbinsa ta haka suka shirya wannan ƙulla ƙullar suka zabtare lissafi wanda daman aikinsu kenan yawan kuɗaɗen da suka zabtare ne yasaka har ta tashi aka gane aka kuma ɗora laifi kacokan akan Aminu dukda daman kuɗin babu su, lissafi ne kan lissafi tsoho da sabo suka harhaɗa ya bada wannan Adadi amma Asalin abinda suka kwasa Naira Biliyan daya ce kuma tana kwance cikin boyayyen Asusun Crypto wanda Naziru ya buɗe musu, Asusu ne irin wanda ba'a iya tracing koda an tura kuɗi ba za'a iya bibiyar su aga inda suka tafi ba can suke tura duk wata Albarkar office da suka samu kafin su zauna su ukun, ita Hajiyar, Zakariyya da Nazirun ayi kasafi kowa a tura masa nasa dan hatta da su ɗin ba wai ta yarda data bar kuɗinta a hannunsu bane, wani sa'ilin ma Ruwan Cash take karɓowa ta zube a ɗaki abinta tayi ta shafasu tana jin daɗi. To wani sa'ilin kuma idan Al'amura sun cukurkuɗe mata ta rasa mafita se Turai tace suje gurin Malam, tun akan Muƙamin Yakubun da Audu yaso yayi mata buyagi yaƙi yarda Turai tace ta kawo kuɗi, har yarjejeniya sukayi akan odan aiki beci ba zata maido mata kuɗinta se gashi tana zaune Audun ya kira Yakubun wannan tasa ta fara amanna da sabgar dukda ko buƙatar ta taso ba ita take zuwa ba, Turai take bawa kuɗi aje a mata abinda ya dace tunda sabgarta ce, ta daɗe dayin amannan da Bin Malamai harda Bokaye zuwa gurinsu takeyi shiyasa har kawo yanzu Ta kanainaye Ali, shekaru an tasamma Hamsin amma se yanda tayi dashi ƙarin Aure da yake da burin yi tunda jajayen sahu ta hana haka yake ta gurgura rayuwa ga kuɗi ya tara mata ita da yayanta suna wadaƙa Yau tana waccen ƙasar gobe tana wannan kayan Alatu kuwa kullum cikin siya takeyi dan ita ba irin Binta bace tana cin kuɗinta Binta kuwa har yau har gobe abin naira goma sabo idan ka ganta dashi to Yaranta suka siya mata shi ko ma ace Jafar dan shine duk abinda ya gani na kwalliyar jiki a gurin hamshaƙan mata ze siyawa Hajiyar abin takaici kuma ba zata saka ba musamman idan taji kuɗin kayan, suturu da sauran kayan Ado da kuɗi kam ta tarasu babu Adadi har tsokanarta Faisal yake yana cewa "Hajiya idan kika mutu zamu ja kaya da yawa dan wlh inaga kason abinda zamu samu na gadonki se yafi na Alhaji" duk ranar da yayi mata wannan maganar kuwa Ashar da tsinuwa babu wadda baya sha tace sedai ubansa ya mutu tamkar ita ɗin zata zauna gadin duniya ne. Bayan sun gama waya da Turai ta miƙe tayi sallar Ishar da aka idar tuni, tana zaune a gurin takaicin duniya ya isheta, jibgin kayan snacks da Kaji da akayiwa Abba Tee take tunawa ya zatayi dasu harda irin shinkafar Larabawan nan da ake dafawa da naman Rago yayi ligib aka masa yanzu duk sun tashi a banza ta saka ran ze cakewa Hafsatu kuɗin da zasu maida wanda aka kashe harda riba se gashi wancan Dan is** yaron ya janyo mata Asara. Tsaki ta rafka yanda kasan wata riƙaƙƙiyar tsaka, ita kaɗai taci gaba da bala'i daga zaunen da take tana dannanwa Yakubu Ashar. Faisal ya shiga kamar an jefoshi, ya kalli Hajiyar ya kalli cikin falon ganin ita kaɗaice zaune kuma tana ta faman sababi yasa ya matsa gabanta yana cewa "Hajjaju, kinƙi yarda Jayy ya kaiki Asibitin da yace, lamarin nan naki fa kullum ƙara gaba yakeyi gara a tari abin tun beyi nisa ba" "Dan ubanka Faisal kaima mahaukaciyar kake so kace mun?" Ta faɗa tana miƙewa tsaye, Faisal yayi wata dariyar shaƙiyanci yaja ja da baya dan ya san tana iya kai masa duka yace "Ni ba haka nake nufi ba, bafa ciwon hauka bane Ciwon damuwa akace kamar yana damunki kuma idan yayi yawa ne yake komawa haukan kinga ba zamu so haka ta kasance ba gara ki daure aje Asibitin nan asan abinda za'ayi dan wlh daga mutum yana zama shi kaɗai yana maganganu kodai wata rana aganshi warwas a ƙasa ya mutu ko kuma aga ya zura da gudu saitinsa ya kwance.." Be dire maganarsa ba ta fashe da kuka tana cewa "Sedai kaga hauka ko mutuwa a kanka dan iska kawai, fice mun daga ɗaki kafin nayi maka baki" "Allah huci zuciyarki ni ban faɗa dan kiyi kuka ba, ɗaki kuma sedai kiyi haƙuri amma yau a nan zan kwana bazan shiga can ba akwai tamu da Salim" yana gama faɗa mata ya shige kitchen da lafcecen takalmin Salim daya sace. Abincin daya gani a gyare ya ɗebi iyakar abinda ze isheshi ya shaƙo plate ya fito har sannan Hajiya na kuka da faɗe faɗen maganganu marasa daɗi akan Yakubu daya fara jangwalota da kuma Faisal ɗin daya ɗora nasa wanda kuma be kyautu ace uwace take danganta Yaranta da irin kalamanba. Kan kujera ya haye abinsa bayan ya kunna Tv ya ƙure volume abinda ya fito da Hafsatu ya hau cin abincinsa ya gama ya gyara zama yana kallo, duk Tijarar da Hajiyar take zuba masa be tanka ba harta gaji dan kanta ta wuce ɗaki ta barshi anan bacci ya kwasheshi dan ko giyar wake yasha bazeje ɗakinsu ya tarar da Salim ba tsaf seya masa dukan mutuwar da yace ze masa. Washe gari da safe zuwan Alhaji Zakatiyya ne ya wankewa Hajiya Binta baƙin cikin data kwana dashi jiyan, dukda sun fara maganar a waya tunjiya amma da yazo yayi mata bayani dalla dalla na yanda komai ya faru se ranta ya sakeyin fari ƙal. "Ai ni wani tunani nakeyi, anya wannan shegen yaron ma ze bamu haɗin kai idan ya hau kujerar? Jiyan nan fa kar kaga tijarar daya mun a gidan nan ya zubar mun da mutunchi a gaban maƙiya" nan ta bashi labarin yanda sukayi da Yakubu jiya, Zakariyya ya jijjiga kai yace "Haba kema Hajiya wani sa'ilin se ki ringa abunda be kamata ba, yanzu saboda Allah wannan tarbiyyace? Ko yar wani kikaga zatayi abinda be kamata ba ai hanawa zakiyi amma kike ingiza yarki ta aikata wannan ba daidai bane sam wlh kuma koni da ace na tarar da yaron sena ballashi wlh itaka kuma se naci uwarta dama ana yawan kawo mun zancen bataji na zata hassadace kawai akeyi mata ashe da gaskene to dan ubanta kawai zamu nemo koma waye mu aurar da ita mu huta kafin ta janyo mana abin kunya a gari". Baki sake Binta ta ringa kallonsa har ya kai aya kamar zatace wani abu kuma seta haɗiye ta bar maganar tace "Ai shikenan, zancen ya wuce, yanzu dai a aikamun da kasona a akawun kai a kawomun kash kawai na ringa ganinsu inajin ɗuminsu kusa dani" "Miliyan dari ukun za'a kawo miki cash Hajiya?" Zakariyya faɗa cikin mamaki, ta harareshi tace "Bangane dari uku ba? Wai nawane kuɗinma da kake kiran wata dari uku za'a bani?" Cikin ɗaga murya tayi maganar yayi saurin yi mata alama da tayi shiru saboda motsin taɓa ƙofa dayaji, Yakubu Bechine ya shiga fuskar nan a turɓune kamar ta Audu, Binta ta lafta tsaki tace "Dallah rabu dani yaji mana, nama zata wani barene ze shigo" "Barka da safiya Hajiya, Zakariyya Sannu" ya gaishe su daga tsayen da yake. Hajiyar ta harareshi bata amsa ba dan a cike dashi akan abinda yayi jiya Alhaji Zakariyya kuwa wani banbarakwai yaji daya kirashi Zakariyya gatsal kamar wani sa'ansa, yanzun shigowarsa ya haɗu da Ahmad ze fita shi kuma, seda ya kusa kaiwa ƙasa kafin ya gaishe shi kuma da Yaya ya kirashi ya amsa masa a wani wulaƙance yana shan ƙamshi kamar wanda yazo masa maula kuma yaron ko a jikinsa ya wuce abinsa har yana masa fatan fitowa lafiya daga gidan se yanzu Yakubu ƙaninsa ciki ɗaya ze masa wannan gaisuwar se kace wasu Abokanai? Koda yake ai Yakubun ma ya mutuntashi tunda Faisal da ido kawai ya kalleshi sanda ya shigo ita kanta Hajiyar be tsammaci ya gaisheta ba ya fita dan da ganinsa lokacin ya tashi ma daga barci. "Tambayarka nake nawane kuɗin?" ta sake nanata masa seya sauke ajiyar zuciya yace "To nidai abinda yace mun kenan kuma baze yuwu a saka kuɗin lokaci ɗaya ba saboda kinga yanzu EFCC ta tsaurara da binciken shige da ficen kuɗaɗe a Account ɗin mutane kar mu jefa kanmu a matsala gara a ringa sakawa da goma da biyar har ayi balancing" "Zezo ya sameni kuwa, a gidan ubanwa kasafin ya zama dari uku? Nida nake lissafin kusan dari bakwai shine zaku cemun wata dari uku? Nifa shiyasa naƙi jinin haɗa sabgar kuɗi da Naziru dan macuci ne, tsayin lokaci kullum yace ana juya kuɗin za'a turo ina nan galahanga kenan kuna can kuna sharafinku se yanzu zaku ɗan yafutamun abinda kuka ga dama shiyasa naji ance ka siyawa Matarka motar Miliyan Ashirin shi kuma yana rabon kujerun Umarah ko ni dana hada pulan ɗin ban san komai ba kun ninkeni a baibai" murya a sama take maganar babu ɗar ko shakkar wani ya jita Zakariyya kuwa daga inda yake zaune har zufa ta fara keto masa ta tsoron kar wannan fallasar ta Hajiya ta janyo musu tonon Asiri tun ba'aje ko ina ba, muakutawa yayi cikin rage sauti yace mata "Yanzu dai kiyi haƙuri na gaya miki yace ze zo kuyi magana tafiyar gaggawa yayi zuwa Legos amma Litinin ze dawo ba jimawa zeyi acan ba" "Ai ko bezo ba ni zanje har gida na sameshi, yo hauka akeyi mu damfari ubanku sannan ku zagayo nima ku cuceni" ta sake sakin wata maganar "Dan Allah Hajiya kiyi ƙasa da muryarki kar a jiyo me muke ciki" Alhaji Zakariyya ya sake faɗa, Yakubu daya haɗo shayi yana daga kan Dining yana jiyosu ya kuma fahimci tsaf inda suka dosa a maganar tasu, daman ya zargi saka hannun yan uwan nasa a manaƙisar da akayiwa Aminun amma be kawo dagaske an ɗebi kuɗin ba ya zata lissafi kawai suka ƙara masa. Kwankwaɗe shayinsa yayi ya taso yana cewa "A fitar dani ko wallahi na fasa ƙwai" "Dan uwarka ka yanka Kaza ƙarewar fasa ƙwai, kai baka san a cike nake dakai ba ko? Ka bari mu haɗe seka gane baka da wayo wlh" Be kalleta ba, Alhaji Zakariyyan yake kallo yace "Ko a tabbatar dani AG ko wlh na fasa tayi wari kowa ya rasa dan naji ƙishin ƙishin idan Aminu ya tafi wani bare ake shirin kawowa". Zabura Binta tayi da jin wata sabuwar lukutar Masifar kuma dake shirin danno kai, wani kuma? Wa za'a kawo? Kodai Ahmad ne? Kenan maganar da akeyiwa Alhaji tuni akanta kenan yace ya sameshi yau a gidan gona? Lallai bataga ta zama ba wai an saci zanin mahaukaciya. Wayarta ta raruma, Jafar zata kira tunda dashi aka ƙulla komai, ta kira sau uku bata shiga su Yakubu duk suka tsaya suna kallonta ganin yanda ta ruɗe se kokawa take da waya "Wai wa zaki kira? Badai Alhaji ba?" Yakubu ya tambayeta, seta miƙa masa wayarta tana cewa "Kunno mun Jafar na gaza samunsa yasan komai akan maganar nan dashi ake ƙullata". "Aikuwa ba zaki same shi a waya yanzu ba dan suna da wasa ƙarfe sha daya, lah lokaci yayima an fara ina tsaye bari kawai na kalla a nan" Yakubun ya bata amsa bayan ya dire mata wayarta a gabanta ya matsa gaban Cinema Tv bango guda wadda Jafar ya sakawa Hajiyar saboda tace wai bata ganinsa dakyau a tsohuwar tata. Tv na daidaita kuwa kamar me daukar hoton wasan Kwallon da ake yasani ya haskowa Hajiya Binta fuskar JAFAR BECHI tarr kamar ze fito ta cikin gilashin Tv. Zabgegen saurayi irin ƙirar Yayan AUDU BECHI, dogone sosai jikinsa nada ɗan kauri dukda ba za'a sakashi a layin masu ƙiba ba amma a murɗe yake koda gani ba se an gaya maka yana motsa jiki dakyau ba. Fatarsa nada haske sosai dukda ba fari bane sedai hutu da zaman Turai ya bashi wata kala me kyau kuma me wuyar samu a cikin mutane, ba wani shahararren kyan fuska yake dashi ba Aa daidai Misali ne irin na Maza gayu da yanayin muhalli da wankan da yakeyi ne yasa har Mata suke iya sakashi a jerin Maza masu kyau wanda ake gwarama kai akansu , ga duk wanda yasan Hajiya Binta Musamman a zamanin ƙuruciya kai tsaye ze tabbatar da JAFAR din jininta ne dan zubin fuskarsu daya idan ka cire Idanun Gidan BECHI daya samu se labbansa wanda Binta tace irin na Alhajinsune, duk tana jika dai da itan yake kama kenan. Jafar ɗin na tsaye a coner ya take kwallo da ƙafarsa ta hagu idanunsa kuma na kan saitin inda yake so ya bugata. JC ce a jikinsa Jaa me ratsin fari ta club din Arsenal wadda ke dauke da Number 7, a bayan rigar an Rubuta JAAY, wani murmushi yake saki daidai sanda Referee ya busa whistle gaba ɗaya yan ƙwallo suka shiga tara tara kowa na jiran ya jefo ta inda yake ya kama, baya yaja kaɗan ya buga ball ɗin daga inda yake ta ringa kurɗaɗawa ta tsakakanin ƙafafuwan yan wasan aka rasa wanda ze taketa har seda ta dangana da cikin raga shikansa Goalkeeper kamar an riƙe masa hannu da ƙafafuwa ya kasa tareta har ta shige, ihun yan kallo na cikin Tv tarefa na ZAKARIYYA BECHI da YAKUBU BECHI ya cika falon, Hajiyavkanta da take cikin ruɗu fuska a ɗaure bata san sanda ta saki dariya ba tana cewa "Ai na sani, sedai idan ba Jafaru na ba be taba kama kwallo ya saka ba tareda ya kaita raga ba, kai Allah dai yacigaba da tuntuɗo maka Albarka ɗan nan Allah ya cigaba da tsole idon maƙiya" Ɗa guda tilo kenan cikin rayayyu tara da take dasu wanda take ɗaga hannu ta roƙar masa nasara a gurin Allah ta kumayi masa addu'ar fatan nasara tareda saka Albarka, yana kuma ganin hasken hakan domin Uwa duk yanda take Uwa ce kuma tasirin harshenta nada girma. Jafar ɗin me shekaru Ashirin da bakwai a duniya yanzu ya kai matsayi mai girma a duniyar kwallon ƙafa. Matashin Dan wasa ne da ake ji dashi a faɗin duniya wanda kowanne Club suke zawarcinsa, idan ka cire Messi da Ronaldo JAAY shi yake take musu baya a duniyar kwallon ƙafa a yanzun. Ubangiji ya hore masa baiwar sarrafa kwallo, duk rintsi duk tsanani idan JAAY ya karbi kwallo seya kaita ga inda ya hara kafin ya haƙura, juriyarsa da Nacinsa da kuma ƙoƙarinsa na haɗakan Yan Team ɗinsa Abokanan taka ledars shiyake ƙara masa ƙima a idon duniya domin kowa ya shaida wannan jajircewar tasa ce ƙashin bayan cigaba da Nasarorin da duk wani club dayake taka leda a ciki yake samu. Cikin farin ciki suka haɗu suna kallon Wasan, harda Hafsatu da Sarah dake bacci ihun su Yakubun ya taso su ko karyawa basuyi ba suka haɗu aka cigana da kallon. BECHI FARM Kamar yanda Alhaji Audu yace Ahmad ya sameshi a gidan gona haka ce ta kasance, Alhajin ya riga Ahmad isa saboda baƙi da yayi ze gana dasu acan wanda shine musabbabin daya saka yace Ahmad ya tarar dashi a can ɗin, sanda ya isa Alhajin na tsakiyar tattaunawa dan haka yayiwa kansa masauki a daya daga cikin falukan da suke gidan gonar idan kaga tsaruwarsu zaka ɗauka a cikin gida kake ba wai gidan gona ba. Yana zaune cikin zullumi rungume da takaddun tsarin abinda yake so ya gudanar, zuciyarsa fal wasi wasin yarda ko akasin haka daga gurin Alhaji, idan Alhajin be yarda da buƙatarsa ba a ina ze samu gurin da ze aiwatar da aikinsa tamkar wanda yake nema a gurin Alhajin? Gajiya yayi da zama da tunani ya tashi ya fita yana zagaya gidan gonar, sashen tsuntsaye ya tafi, acan ya shantake yana kallon Halittun ubangiji, tsuntsaye gasu nan kala kalanda Alhajin yake kiwo danginsu Dawisu, Aku, Kanari da sauran tsuntsaye masu tashi kala kala a keji nan su ga kuma tattabaru nan irin ƙasashe daban daban Jikinsu kaɗai abin sha'awa. Kukan tsuntsayen da surutun masu kula da gurin ne ya ɗebe masa kewa har besan lokacin daya ɗauka ba seda wani daga cikin yaran Alhajin yayi kiransa. Masaukin daya tarar da Alhajin yafi kowanne haɗuwa a gidan gonar, yana zaune kan Luntsumemiyar Rolar chair two sitter irin zaman da yayi da suturar da take jikinsa kamar wani basarake seya cike kujerar gaba daya kwarjininsa ya cika falon. Tamkar beran da ruwa yayiwa duka haka Ahmad ya raɓe daga gefen kujera yana gaida Alhaji. "Ka tashi ka zauna a sama, meye haka kakeyi kamar wanda yazo Maula?" Alhajin ya faɗa cikin muryarsa me razana Maza. Ahmad ya sake yin ƙasa dakai cikin tsantsar ladabi yace "Aa Alhaji nan ma yayi, be kamata kana zaune akan kujera nima na zauna ba" "Umarni na baka ba shawara ba" ya sake faɗa a dake, wani sashi na zuciyarsa kuma yana tsinkewa, Ladabin Ahmad daban ne kaf a cikin Yayansa 28 yayi zarra wanda yake take masa baya kuma Jafar ne wanda zama da Ahmad ɗin ya washsheshi shima ya rabautu da kyawawan ɗabi'u. Kamar wanda ya zauna akan wuta haka Ahmad ya ɗosana mazaunansa akan kujerar jininsa yana sake tsinkewa, falon yayi shiru, motsin ƙofa da aka buɗe ya saka Ahmad ɗin zabura kamar mara gaskiya ganin Kuku ne ya shigo yana tura abinda ake ɗoro abinci akai yasa ya maida kansa ya sauke Ajiyar zuciya a hankali. A nan tsakiyar falon kan Ledar da Kukun ya shimfiɗa ya jera abincin daya shigo dasu. Seda ya gama ajiye komai daya kamata kafin ya juya ya fita bayan ya sanarwa da Alhaji komai ya kammala. Alhajin ya sauka ya zauna a ƙasan ya tokare hannunsa ɗaya da Tum Tum ya shiga serving kansa abincin Ahmad yayi sauri ya sauka ya karɓa. Ganin duk ire iren abincin da Alhajin yake ci yanzun ne dangin Alkama dasu Acca se kayan ganye sakamakon Sugar daya gamu dashi ya saka masa komai madaidaici yanda ze iya ci kafin ya koma ze zauna Kukun ya sake shigowa da madaidaicin Tray ya ajiye a gaban Ahmad ɗin ya sake fita. "Ga irin naku nan" Alhaji dake cin Funkaso da akayi da garin Alkama da wata miyar tantaƙwashi ga shayin Goruba yana kurɓa ya faɗa. Ya buɗe baki da niyyar yace ya ƙoshi amma kallon da Alhajin yayi masa ya saka ya buɗe abincin. Soyayyar jollof din Basmati ce se kaza guda gasashshiya da kuma coslow. Favorite ɗin Ahmad kenan shinkafa balle ga Kaza mutuniyarsa a gefe daman be karya ba ya fito dan haka tuni ya manta da surukutarsa da Alhajin ya hau zuba loka. Seda suka ƙoshi ƙat, Kuku ya sake zuwa ya kwashe komai ya dire musu kayan marmari da tataccen ruwan Inibi me sanyi, Alhaji nata satar kallon Ahmad kamar yanda shima yake satar kallon Alhajin. Dukda wata magana bata shiga tsakaninsu ba har suka gama cin abincin amma duk su biyun yanayin ya musu daɗi domin wannan shine karo na farko da suka taɓa haɗa muhallin cin abinci tun tasowar Ahmad ɗin sedai su hangeshi sunaci da Hajiya tareda Yayanta, sanda suna yara idan ta kira Jafar yazo suci abinci suka tafi tareda Ahmad ɗin haka zatayi ta zaginsa ta koreshi shi kuma Jafar ya saka kuka yabi bayansa wata rana haka da duka zata tisa Jafar ɗin seya zauna dukda bazeci abincin ba domin basa raba kwano da Ahmad da suka fara girma kuma da lokacin cin abincin wanda sukafiyi da dare ya kusa ze ja Ahmad su bar gidan ma doke ta haƙura ta barshi kuma duk abinda akeyi Alhajin be taɓa magana akai ba, ashe haka cin abinci tareda Mahaifi yake da daɗi? Ya raya a ransa. "Ina sauraronka, menene abinda yake tafe da kai?" Alhajin ya soko ainin abinda ya tarasu. Ahmad ya zaro takaddun daya zo dasu. Filla filla yayi musu a gaban Alhajin zane ne a jiki da guntayen rubutu yayi ta maza ya shiga yi masa bayanin abinda yake shirinyi. Tsarin taswira ne na katafaren Shopping Mall dayake da ƙudirin buɗewa, burinsa ne tun yana yaro provision store yake bashi sha'awa. Sanda suna Goron Dutse kafin su taso har Tireda ya kafa a ƙofar gidansu yake siyar da alawowi harda su Maggi da Omo, sau Biyi Audu yana sakawa a jijjigeta amma idan aka cire Yau in Allah ya yarda kwana biyu yayi yawa zega sabuwa a karo na uku harya niyyata ze cire ranar a kan Idon Ahmad ɗin yace masa "Dan Allah Alhaji karka ciremun, idan ma kuɗin haya kake so na ringa biya zan baka idan na tara kuɗi jarina yayi yawa, so nakeyi idan na girma na gina babban Shop da za'a ringa siyar da komai da komai" wannan maganar ta sanyaya masa jiki tasa ya fasa abinda ya niyyata wanda a sannan ma Binta ce tace masa Aisha ta saka Ahmad ya buɗe tiredar saboda aga gazawarsa ace ya kasa daukar ɗawainiyarsu, maganganun Yaron kuma se suka tuna masa da sanda ya daura ɗambar cika nasa burin sanda yake yaro yanzu da Ahmad ɗin yake nuna masa abinda yake so yayi se abinda ya faru kusan shekara Ashirin kenan ya dawo masa. A nutse ya ringa kallon komai yana kuma sauraron bayaninsa, ya fasalta masa guri da girman filin dayake da buƙata danyin ginin. "Shin kana da kuɗin da zaka gabatar da duk wannan aikin daka ɗauko?" Alhajin ya tambayeshi, Ahmad ya haɗe yawu kafin yace "Da akwai tanadin da nakeyi dukda nasan baze isheni nayi koda rabin abinda nake da buri ba a yanzu, amma a hankali ina sha Allah ina saka ran zan samu" "Ok, to me kake so nayi maka kenan?" Alhajin ya jefa masa tambayar me kama da rainin wayo, jikinsa yayi sanyi dan be hango alamar samun nasara ba amma ya daure yace "Wannan filin na cikin gari inda ake ajiye manyan Motoci da nake so idan da Hali a bani Aro tunda an dena amfani dashi". "Aro?" Alhajin ya tambayeshi kamar da mamaki, kansa na ƙasa ya ɗaga masa shi da tabbatarwa seya gyara zama yace "Se kum me?" Muryarsa na rawa kamar a tsorace ya sake cewa "Sannan idan da hali a gina mun, se muyi lissafi a yankemun abinda zan ringa biya duk shekara har na mallakeshi ya zama nawa". Shiru ya ratsa tsakaninsu fin tsahon minti goma sha biyar har Ahmad ya yanke ƙauna daga samun Amsa me daɗi Alhajin kuwa kallonsa yakeyi yana nanata kalmar Aro da yace ya bashi na guri sannan ya yanka masa abinda ze ringa biya kuɗin hayar daya ambata tun yana yaro kenan ze ringa biyansa, kenan a matsayinsa na Mahaifinsa baze iya roƙarsa ya mallaka masa gurin kyauta ba ko kuma ya gina masa irin yanda sauran Yaransa Yayan Binta sukeyi ko su ɗauki abinsa ma suyi amfani dashi ba tareda saninsa ba? "Idan ya tambayekan zaka yi masa hakan ne?" Zuciyarsa ta tambayeshi se ya rasa amsar da ze bawa kansa dan haka yaja numfashi yace "Shikenan, ina fatan kana da Lawyer? Ka haɗa duk wata takadda data kamata ka kaiwa Barr, kuyi magana dashi daga nan ka samu Mr Lee ku tsara yanda construction ɗin ze kasance da abinda za'a kashe daga nan se a tattara lissafin, darajar filin dai shekara goma baya an taya Miliyan dari ban siyar ba, nasan yanzu ya ninka haka sau goma ko fiye da haka tunda kasan inda yake kaima kwaɗayin kyawun location ɗin ne yaja hankalinka dan haka zan bar maka shi a Dari biyu, ka gayawa Barr, sannan ka fara haɗo kuɗin filin tukunna koda rabine sannan zan yarda na fara gina maka". Wani sanyi ya ratsa zuciyar Ahmad, ya shiga zuba masa godiya, seda ya gama kuma kwakwalwarsa ta shiga aiki na gaske, Miliyan dari biyu da Alhaji ya ambata kuɗin fili seya biya sannan za'a fara gini a ina ze nemota? Tanadinsa ƙarƙaf idan ya haɗa baze fidda kuɗin filin ba, amma ya yarda a ransa Allah zeyi masa ze kawo masa hanyar da ze samu abinda ze cika burinsa. *ALBISHIRINKU MATA YAN UWANA YAN KWALISA NAZO MUKU DA WANI DADDADAN LABARI!!!.* *NASAN KUNDADE KUNA NEMAN FITACCEN GURIN DAZAKUJE AMUKU GYARAN GASHINKU DANA JIKINKU CIKI DA WAJENSA,TO YANXU DAI GA DAMA TA SAMU...* *LABARI NAKE BAKUFA AKAN AFINTY QUEENS SHAHARARREN SHAGONMU NA SALOON DAYA HADA KOMAI DA KOMAI DA KOWACE MACE YAR KWALISA IRINA KE BUKATA,SANNAN MUNADA KWARARRUN MA'AIKATAN DASUKASAN KAN AIKINKINSU,KUZO AFINTY QUEENS KUBIYA KUDI MUKUMA MU BATA LOKACINMU DOMIN TSATSTSAFO DUK WANI KYAWU NA JIKINKU DA ALLAH YAYI MUKU...* *A AFINTY QUEENS MUNA AYYUKA KAMAR HAKA:* *- HAIR SALOON* *-HENNA* *-SPA* *-DUKKAN* *-PEDICURE* *-MANICURE* *-SANNAN MUNA DA TURARUKA IRIN NA AMARE YAN MATA DA KUMA MAI KANKAT DAN UWAR GIDA TA TURARA GIDANTA JIKINTA DAMA KAYAN SAWARTA ITA DA YARANTA,,HARMA ZAWARAWA DUK MUN TANADI KOMAI* *DOMINSU SUMA* *-MUNADA SHOES AND BAGS SBD ISASSUN MATAN DA SUKA AMSA SUNANSU MATA*😊 *- MAKEUP NA BRIDAL ND CASUAL...* *IDAN KINSAN KINAJIN LABARIN SHAGON SALOON NA AFINTY QUEENS AMMA BAKI TABBATAR DA YADDA AIKINSU YAKE BA TO YAR UWA GADAMA TASAMU MEZAKI TSAYA JIRA MAZA KEMA KI ZARGAYO SHAGONMU DAZAN JERA MIKI ADDRESS DINSHI A KASA DOMIN KEMA KI TABBATAR DA KALAR IRIN NAMU KWAZON DA MUKA KWARE AKANSHI GURIN GYARAN JIKIN YAN UWANMU MATA KUMA MUKE GABATAR MUSU DA JAKUNKUNA DA TAKALMA HARMA DA TURARUKAN WUTA DANA SHAFAMA JIKINSU DON NISHADIN ZUCIYARSU DANA MAZAJENSU....* *AFINTY QUEENS DISCOVER BLISS IN BEAUTY 💅💯* *Address 👇👇:* *KU ZIYARCE MU A SHOP NO.9&10 SHEMA PLAZA,BEHIND SHEMA FILLING STATION KASUWAN BACCI KADUNA* *TEL:08133379628.* *MATAR MUTUM* *NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER* *FIKRA WRITERS ASSOCIATION* *LITTAFIN KUDI NE* *PAY 500 A ASUSUN* *7061838488* *OPAY DIGITAL SERVICES* *MARYAM FAROUK* OR *0709290797* *ACCESS BANK* *SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488* *IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705* *Kuyi following dina a Arewabooks @Maryamfarouk01 inda zaku karanta wannan littafin tareda sauran littattafaina* *NAGODE* *BOOK 2* *PAGE 3* Daga gidan gona kai tsaye gidan Anty Manfusa Inda ya ajiyw Momy dan tare suka fito. Yayi masu bayanin yanda sukayi da Alhajin dan Anty Manfusan na cikin waɗanda zasu saka hannun jari idan Allah yayi buɗewar shopping mall ɗin. "Wato uban nan naku lamarin sa yana matuƙar bani mamaki, yanzu ba'a rufa wata guda ba Yayansu Nihal (Dan Mijinta ne) yake cemun Anyi musu ƙarin kuɗin hayar shaguna a plaza, da aka kawo musu takaddu yaga an canza sunan da yake jiki wai yanzu ta zama ta NAZIRU BECHI, a yanda akace wai siya yayi gurin Alhajin wasu kuma sunce bashi yayi, nima yana faɗa nace wlh ƙaryane bashi yayi saboda rashin tsoron Allah duk girman plazar nan ace ya bawa Naziru shikaɗai shagunan ciki fa sunyi hamsin? nifa da nice a matsayinki wlh da tuni gayyar ta watse dan bazan zauna ana wannnan kutumar ubancin inyi shiru ba" "To banda abinki Manfusa Naziru ai Ɗansa ne yana da damar mallaka masa duk abinda yayi niyya" Momy ta bata amsa. Manfusa ta harzuƙa tace "Shi Ahmad ɗin ai Agola kikaje masa dashi shi yasa ze kasa bashi kyaitar fili, tsabar zalunci kuma ya lafta kuɗi har Miliyan ɗari biyu ce masa akayi Ahmad ɗin barawo ne irin sauran Yayansa da ze mallakin waɗannan kuɗin a shekarunsa? Ko kuwa saboda yana rayuwarsa cikin rufin Asiri bai taɓa neman wani abu a hannunsa ba?" "Hakan ma da yayi nagode Anty dan wlh idan a gurin wani ne darajar filin nan ta zarce haka ko a haya za'a bani a gine dai a shekara Miliyan Hamsin sen bayar da ita wlh kinfa san location kafin ni nasan manyan Organization da suka nema ya hanasu har Gwamnati seda taso ta kwace gurin Baba Alƙali ne ya tsaya masa Allah ya taimaka aka bar masa in sha Allahu in har muka samu abinda muke so shekara biyar tayi yawa zamu mallakeshi ya zama namu kawai dai kuyi ta tayamu da Addu'a" Ahmad ya yayyafawa wutar masifar data fara ruwa, dole tayi shiru tunda uwa da Ɗan da take haƙilo akansu abinma.be damesu ba. A hanyar komawa gida Momy take ce masa "Nifa ubana ina tsoron mutanen gidanku akan maganar gurin nan, ban manta ba Yayanku Zakariyya ya taɓa nemar ya bashi ya gina Hotel yaƙi, baka tsoron idan sunji suyi maka lamɓo se ka saka kuɗinka su zugashi ya kwace?" "Momy, dan Allah ki kyautata zato akan abin nan ki cire duk wani wasi wasi daga ranki. Nida ke duk mun sani Alhaji kaifi ɗayane, idan da beyi niyyar bani ba koda ace duniya zata taru akansa wlh baze bayar ba haka nan yanzu daya ce ze bada bana tsammanin da akwai abinda ze canza masa ra'ayi akan hakan, ki kwantar da hankalinki" "Ai shikenan, Allah yasa tabbatar da Alkhairi" "Amin Momy, abinda ya kamata ki faɗa kenan" daga nan suka shiga wasu hirarrakin harya sauketa gida ya juya yana so yaje yaga Barr Ansaruddeen Kalam, Childhood friend ɗinsa ne kuma shiya Aminta dashi da zama Lawyersa, a gidan Barr yayi Magriba da isha suna tattauna yanda za'ayi da takardun daya kamata su haɗa kafin su zauna da Lawyer Alhajin. Cikin hukuncin Allah yarjejeniya ta ƙullu tsakanin Alhaji Audu Bechi da Ahmad Bechi, kowanne bangare ya gamsu da tsarin da akayi har kuma BECHI CONSTRUCTIONS sun aza harsashin gini bisa Jagorancin Mr Lee, Injiniyan da yake shugabantar bangaren gine gine da ƙere ƙere na BECHI GROUP OF COMPANIES kujerar da Hajiya Binta take hari domin kuwa tuni ta matsantawa Faisal tafiya bangaren Engineering ɗin yanzu haka yana shekara ta biyu ne a Civil Engineering, burinta daya gama kuma a tunɓuke Mr Lee ya koma ƙasarsu Faisal Bechi ya maye gurbinsa. Ubangiji ya sirrinta Al'amarin ta yanda har gini yakai Linta Hajiya da Yayanta basu san abinda ake ciki ba, koda yake Yakubu Bechi ya sani saboda buƙatar fitar da kuɗin da aka kai kan Teburinsa dan tuni ya maye gurbin Aminu Bechi. Yakubun be fiya shiga sabgar da bata shafeshi ba, a barshi dai da son kansa dan haka muddin Abu ba wai ya shafi personal Interest nasa bane baze ce komai a kai yanzun ma haka ce ta faru yayi shiru ya saka hannu kawai kamar yanda aka buƙata be kuma tattauna maganar da kowa ba. Yanda akayi Labari ya isarwa Hajiya Binta kuwa hanya ce ta bida ita ta gurin da filin yake zataje gaisuwar Lantana wadda Allah yayiwa Rasuwa, Hajiyar bata yada Lantana ba a wannan bangaren kam tayi Alƙawari dan Lantanar tsautsayi ta gamu dashi a shegen yawonta mota ta kaɗeta shikenan ta gamu da Ƙafa, shekararta goma a zaune kafin Ajali ya sauka Bintan na leƙata lokaci lokaci duk kuma sanda ta wuce seta kalli wannan fili tana wassafa burinta akansa. A Zoo road yake, zuciyar Kasuwanci, kanta takeyiwa tanadi zata gina plaza ta zuba shaguna wanda ko iyakarsu me kadararta tasan ba ƙananan kuɗaɗe zata ringa shaƙa duk shekara ba. Jiki na rawa ta samu Alhaji Zakariyya da zancen waya tada gini a wannan filin? "Badai siyar dashi yayi bamu sani ba? Ka nema ya hanaka ina fakonsa shine ze siyar? To duk wanda ya siya ma kuwa ya siyi Asara dan ciniki be yuwu ba" Inji Hajiya Binta. Alhaji Zakariyya da har ya fita shiga ruɗu domin a halin da ake ciki a yanzun ya karɓi kuɗi a hannun Lebanese da suke son gurin zasu gina Hotel dan bashi zeyi ginin ba kuma ya musu Alƙawarin kafin watan da ake ciki ya ƙare zasu fara aikinsu se kuma yake Jin wata magana daban. Bangaren Land and properties ya tafi ya samu Alhaji Musbahu, basa shiri saboda duk sanda suka tashi cefanar da wani abun muddin basu kai masa takadda ta gaske me ɗauke da signature Chairman ba baya basu Approval, Zakariyyan kuma baya duba Girma ko Shakarun Alhaji Musbahun haka ze zageshi a gabansa yace ai bashida gadon ubansu balle ya ringa hanasu Taɓa dukiyarsu, yau ɗin se gashi harda risinawa ya gaidashi kafin ya tambayeshi suwa aka bawa Filin da har suka fara gini" "Ban sani ba, kaje ka samu uban naka kaitsaye, ku masu jiran Gado ma kuke ɗauka kuyi yanda kuka so da guri balle me abun daya tara da guminsa?" Amsar da Alhaji Musbahu ya bashi kenan shima kuma ita ya mayarwa da Hajiya. Ranar akayi dacen itace da Girki dukda Alhaji Audu baya gari ya tafi Umara amma a daren ranar ake saka ran dawowarsu shida Hajiya Rabi da Yammatan gidan duka suka tafi Umara wanda Albarkacin Tafiyar da za'ayi da Hajiya ƙarama da Sarah, wanda ze buga musu Visa da karanbaninsa ya haɗa da duka sauran Yara Matan da suke a gidan se kuwa gashi Alhajin bece komai ba akai. Amma fa seda akayi uwarka ubanka da Hajiya Binta kafin tafiyar ta yuwu harda Allah ya isa yanda kasan kuɗinta aka ɗiba akayi tafiyar dasu. Babu shirin da tayi na cewar yau Megidan ze dawo tunda ya tafi ma sau biyu sukayi waya Albarkacin zata bashi sautin Dogayen Rigunan Gumama wanda take bulalawa a tsakar gida tayita yawo kamar Maroƙiya, idan tacewa Hafsatu ko Sarah su siyo mata cewa zasuyi ta tura da kuɗi shiyasa ta aikawa da Alhajin hotunan kalarsu kamar wani Yaronta tace guda biyar za'a siyo, da taji shiru be duba saƙon ba shine ta kirashi, na biyun ma tinin an siya tayi masa yace Eh Alhalin ko downloading yaga me ta tura beyi bama. Ƙarfe goma na dare jirginsu ya sauka kafin a gama dakko musu kayansu su tafi gida sha biyu saura shi Alhajin dama VIP lounge na Arrival ya shige abinsa yace idan sun gama a sanar masa dan baze tafi ya barsu su duka mata ba ga dare, Ahmad ne kaɗai ya tsaya Tarbarsu a samarin gidan, a cikin gida kuma Momy ta musu ɗan abin taɓawa dukda dawowar darece amma tasan Alhajin baya cin abincin jirgi ko China zeje sedai yasha ruwa ko shayi shiyasa ta tanadar masa abinda zeci dukda ba girkinta bane sedai ganin Yau Hajiyar ko Hanyar kitchen bata kalla ba yasa tayi, kamar ma dai bata da lafiya ne dan karaɗin da take isarsu dashi a gidan ma yau shiru kunnuwansu sun samu sa'ida. A Ɗakinsa Momyn ta shirya masa komai ta bari tayi masa sannu da zuwa daga bakin ƙofa ta wuce Ɗakinta da Yammatanta da suka ruƙunƙumeta suna faɗin sunyi kewarta. Dukda darene haka ma'aikatan gidan Maza suka ringa shiga Babban Falo suna masa sannu da zuwa, Hamshaƙai kuwa, Yakubu, Faisal da Salim harda Mu'allim suna Ɗakunansu babu kuma wanda yake bacci a cikinsu daga masu chatting se masu waya da Yammata gara Mu'allim ɗin ya fita ya tarbi uwarsa ya rakata cikin gida kafin ya koma yaci gaba da Chatting, Tashen Balaga yake akayi rashin sa'a kuma Yayyensa da suke kewaye dashi babu wani gwani da ze kwafi abin Arziƙi a gurinsa shiyasa shima yake nema ya tashi da Ɗabi'u irin na gidansu da ya zame musu Gado wato halin ko in kula. Hajiya Binta bata saurara ko Babbar Riga Alhajin ya cire ba yana sallamar Masu aiki ya hau sama ta dirar masa a Ɗaki, ransa a jagule da rashin ganin sauran Yaran dake cikin gidan tamkar yanda Ahmad yazo ya tsaya kuma yaga motar kowannensu a ajiye dan ya kafa dokar hana yawon dare ƙarfe goma ake rufe masa Get ba shiga sedai fita duk kuma wanda ya kwana a waje shi yasan ta yanda yake hukuntasu kuma sun biyu suna bin dokar. "Yawwa Alhaji sannunku da sauka, nace ɗazu naje Goron dutse se nabi ta Zoo road zan karbi saƙo, base naga gini tsiriri a filin kaba? Ni na gaza fahimtar ma me ake ginawa yo bulune ta ko ina an tayar da katangu inaga hawa uku ma aka ɗora bene a gurin" Hajiya ta faɗa tana zama idanunta kuma akan kwanukan da Momy ta ajiye. Alhaji ya shiga kacaniyar zare kayan jikinsa, sati biyun nan yaji dadinsu ya samu lokaci da Amaryarsa dan har wani ɗan kumari yayi yanzu ya dawo zata fara ƙwarzabarsa, ita bata tarairayeshi ba sannan ta addabi masu tarairayarsa ta hana musu sukuni. Seda ya cire rigarsa ta rage singlet da Wandon dakakkiyar Gedzenar jikinsa kafin ya janyo teble ya bude Casserole ɗin da Momyn ta ajiye, Irin dankalin nan na yan gayu da ake soyawa sama sama sannan a gasa yaji Albasa da Koren tattasai da Yellow da zafinsa alamar yanzu aka gama ko akayi Microwaving ƙamshi na tashi. Ya tsiyaya Shayin dake cikin yar buta yayi bismillah ya faraci ba tareda ya bata amsa ba. A daren take son jin yanda ake ciki dan haka tayi shiru ta tuno da tsohuwar kissa ta matsa tana cewa "Yi haƙuri duk na sha'afa banma ce maka ga abinci ba, Allah sa be huce ba dan na daɗe da gamawa". "Da dai harshena ya dena tantance ɗanɗano sena yarda, sannan yaushe kika fara siyan irin kwanukan nan? Ina cewa kikayi na yara ne sedai a siyawa su Dada ko kuma kin canza shawara kinbi sahun su Aisha tsofai tsofai daku kuna Asarar kuɗi a siyan kayan kitchen?" Alhajin ya mayar mata da martani yana murmushin rainin hankali. Tayi tsam, har yar kunya ce ta kamata wato yasan ba ita ta ajiye ba kenan? Amma seta waske tajira harya cinye tas ya shiga banɗaki ya kuskuro baki ya zauna a bakin gado yana duba wayarsa. Maganar ta sakw soka masa hankalinsa naga saƙonnin da yake dubawa yace mata "Ahmad ne ze bude kanti a gurin". Ruwa take sha babu shiri ta ƙware nan ta shiga tuttula tari kamar zata amayo kayan cikinta Alhajin na jera mata sannu. Seda ya lafa mata ido da fuska sunyi jajir se sauke numfashi takeyi dan ta shaƙu amma bata daddara ba ta kalli Alhajin tana zaro ido tace "Ban fahimci Ahmad ne ze buɗe kanti ba? Ka gane inda nake maka zance kuwa? Filin Mota fa nake magana bawai wani guri daban ba" "Nan ɗin nima nake miki zance ai, ba kince kinga ana ta gini ba? Shopping Mall ze buɗe a gurin" ya sake bata amsa. Yanzun ta tabbatar da ya gane inda take nufin kuma gaskiyar zancen yake gaya mata. A fusace tace "Ahmad ze buɗe shopping Mall ko zaka buɗe masa? Ni zaka ninke a baibai wannan filin zakace ka bawa Ahmad ya bude kanti a ciki ina nan da Me sunan Alhaji yace yana son gurin cewa kayi da tanadin da kakeyi akai ashe Ɗan gidan Aisha kakeyiwa tanadi zaka buɗe masa kanti?" Hankali kwance dan seda ya kishingida kafin ya bata amsa yace "Ko kaɗan yanda dai kikaji nace miki shi ze buɗe to hakan ne nidai na bashi fili mun kumayi Agreement harya biyani wani kaso zan gina masa gurin a hankali idan kasuwa ta kafu ze ringa biyana har mu warware" Data rasa abin ce masa se kawai tace "Ai shikenan" ta fice daga ɗakin. Da Asubar Allah ta tattago Naziru da Zakariyya ta shaida musu abinda akw ciki, suka ƙule a ɗaki suna ta ƙulleƙullen yanda za'ayi a rusa maganar amma sun gaza samo hanya domin a yanda Alhajin ya iya bata amsa jiya tasan ba wata magana da zata faɗa yanzu ta samu shiga a gurinsa. Idan ya murɗe barinsa takeyi domin a garin tace seta latsa dole se ayi rashin sa'a kwaɓarta tayi ruwa shiyasa yanzun ma kamar zatayi kuka tace "Kubar komai a hannuna zan barshi dai yanzu tunda naga kansa yana hayaƙi amma zan maidashi hankalinsa ne kuma wlh ba Ɗan Aisha ba ko ubanta ne yayi kaɗan daya mallaki gurin nan se an karɓeshi". NAZIRU da yayi shiru yana ta tunani ya gyara zama yace "Wani tunani nayi, tunda kince yace miki ba kyauta ya bashi gurin ba na tabbatar kuma dagaske ba kyautar bane, me ze hana mu bi abin a siyasance? Nasan dai a shekara goma Ahmad indai ba Naman mutane ze ringa siyarwa ba a gurin nan baze haɗa kuɗin filin nan da ginin da za'ayi masa ba..." "Kai na rabaka, ka dena ganin yaron nan yana yawo tsalo tsalo dashi wlh neman kuɗine ya hanashi ƙiba, yanda kasan wannan tsohon haka yake babu sana'ar da baya gwadawa" Alhaji Zakariyya ya tare Nazirun. Seya ja tsaki yace "Ka dakata Malam kaji point ɗina, i know what I'm saying, kai kasan nawa ake taya filin nan Tsohon nan yaƙi siyarwa? Kuma kaidai kasan riba kawai ya sani babu batun faɗuwa ko mu da yake mana Gwanjon kayansa ai saboda uwarmu ta iya ƙasarta ne, ni shirin dana hasaso yanzu as i was saying a shekara goma Ahmad baze biya kuɗin gurin nan ba shi kuma Tsohon nan nasan duk Nacinsa shekara biyar gaba ma yaci ace ya dunguri ƙasa dukda ma naga Sugar nasa da hawan jinin wani sanɗa sukeyi sunƙi su rarakeshi yanda ya kamata ya buɗa mu samu muja kaya. Yawwa maganata a nan a bar maganar akwace guri ko wani abu, da zarar Alhaji ya sheƙa lokacin kuma Ahmad ya gama wahala da gurin ya rayashi kawai zamu tayar da rigima muce guri na Alhaji ne, babu ruwanmu da ko nawa sukayi yarjejeniya ya biyashi bamu san anyi ba dan haka guri yana cikin lissafinmu". "Ji banza, kai matsalata dakai wani lokacin se ka ringa magana kamar wani ɗan ƙwaya wlh, da kake cewa idan Alhaji ya wulla semu tada rigima ana maganar yanda za'ayi guri ya zama mallakinmu kana kawo shirme ko kuwa ka manta bamu kaɗai Alhajin ya haifa ba idan anzo rabon kowa se an fitar masa da kasonsa dai dai da namu?" Naziru yaja hanci irin yanda masu zuƙar hoda sukeyi ya wani karkace yana hararar Zakariyya yace "Kai ai kanka baya kawo wuta ne kwata kwata, kaji da Kuɗin mutane daka karba nasan sune matsalarka yanzu, zancen Gado kuma ai me sauƙi ne. Karka manta Yaya Tara ne a Ɗakin nan namu mu shida Maza a ciki munfi yan kowanne ɗaki yawa sannan mu muke da ruwa da tsaki a duk wasu sabgogin megidan nan, karka manta Kadarorin da uwar kuɗin kansu se abinda muka ga dama muka fito dashi za'a raba kuma ba wanda ya isa ya ɗaga mana yatsa" "Wannan gaskiyane" Hajiya da tunda ya fara maganar batace komai ba ta faɗa tana gyara zama dakyau dan tafi jin dadin wannan Haɗi na Naziru. "To idan suka haɗe mana kai fa? Kasan dai in suka haɗu sun nunka mu a yawa Mazansu da Matansu" Alhaji Zakariyya da yake jin shawarar Naziru bata kwanta masa ba ya sake faɗa, ta yaya za'ayi a zauna lissafin jiran Alhaji ya mutu? Cewa yayi yau ko gobe ze mutu? "Kai kana bani ciwon kai wlh, a gidan nan kake zancen haɗin kai? Ko mu da muke Abokanan cin mushe muke cin dunduniyar junanmu ballantana kake maganar waɗanda a cikinsu akwai wanda suka fi shekara basu ga fuskar junansu ba, ni kana haɗuwa da Hussaini kuwa? Kasan zuwana Legos na ƙarshe kawai Mr Oniye ya ambato mun sunansa, wlh na manta a gidan nan munda wani Hussaini se lokacin wai yaron nan lasisin fitar da Mai ya taceshi yake nema bama ya siya a nan ba" A tare Hajiya da Zakariyya suka zabura suna haɗa baki gurin cewa "Hussainin?" "Wlh fa, i was shocked irin kamar na faɗa tsakiyar transformer, kai nifa abun nan ma ya fara rikitamun lissafi ta yaya za'ayi ne mu mukeda kuɗi da iko from no where yaran nan su ringa fasowa suna mana over taking?" Nazirun ya sake faɗa, Zakariyya ya dunƙule hannaue yana kaɗa ƙafafu kamar mejin fitsari Hajiya kuwa kasa haɗiye kyashi, hassada da baƙin cikinta tayi kawai ta fashe da kuka tana cewa "Nidai Binta ina ganin ta kaina a gidannan, na gama da Hadiza dakyar bangama da matsalar Aisha ba gata Zubaida tana neman ɓullo mun niko me nayiwa wani da wannan bala'u suke rikirkitomun haka wani bin wani?" Haka taro ya watse dalilin wata sabuwa data bullo. (Ai daman duk wanda yace tukunyar wani ba zata tafasa ba to fa tasa ko ɗumi ba zatayi ba). A bangaren Aminu Bechi tsohon AG kuwa cikin hukunci irin na ubangiji barinsa BECHI GROUPS ba'a ko cike sati ba yana zaune ya fara samun gayyata daga kamfanonin da suke hamayya da BECHI GROUPS din, wasu sun so jansa ne domin su samu damar da zasu karya BECHI GROUPS saboda sunsan dole yasan sirrinsu ciki da waje kuma korar sa da akayi tana iya saka yayi fushi ya nemi ɗaukar fansa a kansu sedai Aminunba haka yake ba, koda cewar beji daɗin abinda ya faru dashi ba kuma yana da wani Rauni daban a zuciyarsa gameda Chairman ɗin BECHI GROUPS wannan bazata saka ya ha'ince su ba domin karya Alhaji Audu daidai yake da karya kansa dan ko babu komai Uba yake a gurinsa shiyayi silar zuwansa duniya wanna ta saka ya karbi aiki a wani ƙaramin Kamfani dan be kai sauran da suke farautarsa ba, Albashinsa be kai wanda ake biyansa a baya ba amma a hakanma ya godewa Allah tunda ya ishe shi yacigaba da biyan buƙatunsa na yau da kullum dan shi bashida burin ya tara kuɗi daman shiyasa tanadinsa ƙalilan ne, jin daɗi makura yana bawa Iyalansa a duk sanda dama ta zo kuma ya tabbatar ko be mutu ya bar musu komai ba wannan farin cikin da ya sanyasu sanda yana raue zasu ringa tunawa suna masa Add'u, abinda ya rasa daga nasa Mahaifin. Rayuwa taci gaba da tafiya, wanda yake binta a sannu tazo masa da sauƙi, wanda suka ɗauketa da girma tana cigaba da kwallo dasu bugu ta kowanne bangare har ana rasa na inda za'a tare se fatan ubangiji ya kawo sauƙi. A cikin shekara daya da wasu watanni ginin katafaren Shopping Mall ɗin Ahmad ya kammala. Gini ne akayi shi badai ya gini ba, tsari da taswirar gurin kaɗai ta isa ta sakaka ka shiga kayi siyayya ko badan kana ra'ayin hakan ba. An fitar da komai a tsare, bangare bangare daga na kayan Abinci na dafawa dana kwalama dangin su Alawa su Biscuit, kayan sakawa na manya da yara, kayan amfanin gida daga kan sumunti har zuwa ƙarshen abinda ake buƙata domingida ya amsa sunansa na gida da akwai a gurin, kai babu ce kawai Ahmad ne zuba a gurin ba, kuma wani abin jin dadi yanda ya faɗaɗa komai ya bawa Yan uwa da Abokanan Arziƙi damar shiga su saka hannun jari, bashida kuɗin da ze raya gurin shi kaɗai dan haka yayiwo gayya. Yan uwansa na gidansu kaf babu wanda be samu akan maganar ba ya kuma tallata masa idan akwai abinda yake so ya zuba ya kawo amma kaɗan daga ciki suka amsa tayin. Takanas yaje har Bechi ya samu Alhaji Babannan wanda seya shekara biyar be taka ƙafarsa a gidansu ba seda babban dalili koda yake waɗanda suke cikin Kanon ma ba zuwa suke ba se su ɗin dai da iyayensu suke cikin gidan su kadai suke dabdalarsu idan kaga wani a cikin sauran tofa ba ƙaramin abu ya faru ba tunda Alhajin yayi musu Aure shikenan kowa ya sallami kansa. Ahmad ya samu Alhaji Babannan akan zancen Shinkafa wadda yakeyinta sosai kuma yana jin yanda ake yabon irin da yake amfani dashi ana siyan shinkafar sosai dan kamfanunuwa ne suke kwasheta da yayi girbi dan hatta da BECHI RICE suna siyan shinkafar Babannan ɗin saboda ingancinta. "Ina ganin Yaya me ze hana kaima ka samu Alhaji kuyi yarjejeniya kamar yanda mukayi dashi, a maimakon ka ringa siyar da shinkafar daka Noma ya gina mala kamfani ka ringa sarrafata da kanka ana packaging kai tsaye kana siyarwa zakafi ganin ribar abinda kakeyi sosai kaga se a ringa ajiyewa a gurinmu masu siyan ɗaɗɗaya yan sari kuma suzo kamfani gurinka" shawarar da Ahmad ɗin ya bashi kenan. Alhaji Babannan ya murmusa kawai, shiɗin bashida yawan magana tamkar marigayiya Bara'atu amma kuma dafin da yake cikin zuciyarsa yasa maganganun bakinsa basu da daɗi sam. "Kaine mara zuciya da har abin hannunsa ya tsole masa ido ka iya neman Alfarma a gurinsa, yanda beyimun abinda ya zama wajibi na haƙƙina akansa ba bana fatan Allah ya kawo wani abu da ze sakani neman Alfarma a hannunsa komai ƙanƙantarta, abinda nake samu ya isheni rufin Asiri a duniya dan haka ka tashi ka tafi" amsar da Ahmad ya dawo da ita kenan tana masa nauyi a cikin zuciya ya kuma kasa amayar da ita ga kowa domin shi ubangiji ya hore masa ƙarfin zuciyar iya sirri komai girmansa komai ƙanƙantarsa. Be daddara ba ya samu Ali ɗan uwan Aminu, bayan aikin kamfani yana siyan gyada ya kai kamfani a fitar masa da Mai yayi packaging ya siyar, a cikin waɗanda suke uba daya banda Jafar da baya cikin lissafinsu Alin na da saukin Hali se Hassan su biyun daman yasan da wuya suƙi tayin nasa Alin ya yarda yayi murna sosaima har yake cewa daman ya gaji ya fara tunanin haƙura da harkar saboda yanda yake shan wahala da mutane idan suka karɓi kayan kafin kuɗinsa ya fito. Hassan kuwa Magunguna yace ze zuba a bangaren Pharmacy da aka ware yace kuma ze tuntuɓi Hussaininsa wanda ko Lambar wayarsa Ahmad ɗin yace baya samu zeyi masa magana ko kuɗine se su haɗa su buɗe Pharmacy ɗin. "Amma Ahmad idan ban shiga abinda be shafeni ba da se nace me yasa kayi register Kamfaninka da BECHI AND SONS sannan kayi Naming Mall ɗinka BECHI SHOPPING MALL? why not AHMAD BECHI SHOPPING MALL If you must include the Bechi a cikin sunan? Ni kaina dana buɗe Clinic ɗina da BECHI HOSPITAL I'm regretting kuma ina shirye shiryen chanza masa suna soon" Dr Hassan ya faɗa, Ahmad ya ɗanyi shiru yana mamakin dalilin wannan maganar lura da hakan yasa Dr Hassan yi masa ƙarin bayani yace "Magana tazo mun cewar yan gidanku sun cewa duk mu gama wahalarmu a ƙarshe komai da muka tara ya zama nasu mun sauƙaƙa musu ma da mukayi naming property namu da na Alhaji, dukda ni nasan ko sarautar hauka suke taƙama da ita babu wanda ya isa yazo anywhere near my property yayi claiming cewar nasa ne saboda uban nasu ma besan sanda na gina abuna ba balle su" Dr Hassan ya faɗa cikin zafin rai. "Kayi haƙuri Yaya ka tausasa kalaminka akansa ko babu komai mahaifinmu ne Allah kuma babu ruwansa da wani abu da yake tsakaninka dashi wannan kyautatawa da bayar da girman dole kayi masa" Ahmad ɗin ya tareshi cikin ɗar ɗar domin dama damarsa ya gani akan Alhaji Babannan da har ya iya yi masa togaciyar. Ajiyar zuciya Dr ya sauke kafin yace "Hakane, thaks for reminding me, amma kamar yanda nake gaya maka kai kana tsakiya, you still didn't own the property hundred percent, and you know that Man, he can be cunning, ina tsoron ya maka shigo shigo babu zurfi yayi ta kwace maka kuɗi daga ƙarshe ya barka da rigima da Yayansa ko kuwa ya baka papaers ɗin guri komai is in your name now?" Ahmad ya girgiza kai a hankali alamar Aa, zuciyarsa naso ta kama zancen Dr Hassan sedai amintacciyar na jaddada masa babu yanda za'ayi Alhaji yayi haka, yama za'ayi hakan ta faru? Ya tabbatar suffar da suke ɗorawa Alhajin bashida ita haba da kuwa ya cika ƙarshen Azzalumi a duniya ace ya rasa wa ze damfara se Ɗan cikinsa kai wannan abin ko a labari be taɓa jin anyi irinsa bama. A sanyaye yace masa "Bai bani papers ba amma komai da mukayi a rubuce ne akwai copy a gurina da Lawyer na shima haka, sannan Baba Alƙali ya sani, Baba Abdullahi ma ya sani Barr Aminu ma ya sani da Baba Musbahu duk suna cikin shaidu" "Cikin yaran gidan fa ya sanarwa da wani?" Dr Hassanya sake tambayarsa. Duk se Ahmad ya nemi daya hargitse da tambayoyin Hassan ɗin shaiɗan ya nemi daya fara rawar disco a zuciyarsa yana kawo masa wasi wasi. Kamar maraya yace "Aa bansani ba ko ya gaya musu dai Amma Yaya Yakubu ya sani Jafar kuma tare muke shirya komai" "Jaay, dazun na gama kallon maimaicin wasansu he is really making us proud, kaga a gidan Alhaji Audu, ku biyun nan ne kaɗai abinda zance yamun na kirki daya haifeku ko babu komai My two half brothers are something to write about" Inji Dr Hassan, se Ahmad ya fara tattare takaddunsa cikin alamar haramar tafiya amma Dr ya hanashi yace se yayi Dinner tukunna. Tare sukaje sallar Magriba da Isha'i sukaci abinci sunyi hira sosai sun kuma samu fahimtar juna daya tashi tafiya ya rabawa yaran Dr kuɗi dan yau be fito da Chocolate ba ko a mota bashida sannan ya kama hanyar gida yana tafe yana tunanin irin Daɗin da rayuwar gidansu zatayi da ace guri ɗaya suke zaune gaba ɗaya, se ya ringa ganin kaman samun daidaito a gidansu ze zama abu me sauƙi amma duk sanda ya zauna da wani a cikin yayyensu seya fuskanci abun ya shallakewa tunaninsa, tabbas Allah ya azurta Alhajinsu da zuri'a sedai ya watsata, haɗuwarta kuma se ikon Allah. A yan ɗakin Hajiya Yakubu ya amsa tayinsa ya zuba zunzurutun kuɗi ba kayaba an kumayi komai a rubuce ta yanda za'a ringa bashi ribar abinda aka samu, shikaɗai ya zuba jari se Jafar wanda daman dashi ake tafiyar, yayi supporting Ahmad ɗin da duk abinda ze iya shima kuma ya zuba kayan ƙwallo da kayan motsa jiki a yanzun shima yana kan tsarin buɗe Academy ta Ball ne under his NGO wanda ze ƙaddamar idan yazo Bikin buɗe shopping Mall ɗin Yaya Ahmad da yace ko za'a bashi query se yazo be kuma sanar da kowa zuwansa ba banda Ahmad ɗin domin muddin Hajiya taji seta hana. Abinda ya matuƙar bashi takaici duk bayan daya gama zagaya sauran yan uwa ya dawo kan yan cikin ɗakinsu da yake tsammanin bashida matsala dasu se gashi sunyi disappointing nashi. Kaitsaye Sarki yace he should count him out akan duk wani abu me kama da joint business shi kuma Salim da yake yazo ya ringa zama a gurin ranar da bashida lectures a makaranta se cewa yayi sedai idan shi za'ayiwa Manager to ya yarda amma bazeyi yaron shago ba. "Kai baka san kasuwanci ba, se kaje ka haɗo dame ƙashin tsiya komai ya rushe a barka a ciki bazanyi wannan abunba I'm going to send you something ka ƙara jari ni yanzu hankalina ba'akan Business yake ba because I'm going in to politics" zancen Sarki kenan, Ahmad besan sanda yace "Saboda shirme kabar Business ka koma siyasa? Ka kwashe kuɗinka fa kenan kaje ka zuba a cacar da baka da tabbacin samun nasara who does that? " "Kai zaka gayamun abunda zanyi kenan?" Sarkin ya faɗa yana tsareshi da ido, Ahmad yayi shiru, basa faɗa irin na sako da sako amma fa basa ga Maciji sam, ba sarki kaɗai ba harda Salim kullum cikin faɗa suke Sarki na ganin Ahmad ya rainashi yana shigar masa rayuwa a son ya nuna masa daidai ko rashin daidai shi kuma Salim yace Ahmad ya takura masa ya tsaneshi komai yayi abin faɗane a gurinsa bayan kuma Ahmad ɗin duk ya fisu gaskiya shi Sarki tunda Abokai suka masa famfo suka ce ya shiga siyasa shikenan lissafinsa ya kwance Salim kuma da Faisal basu da saiti sam shiyasa yake matsanta musu yanzu shi a ɗakinsu Momy da yan uwansa mata ne abokanan hirarsa da shawara Mazan kowa kansa hayaƙi yakeyi. Cikin nasara akayi bikin buɗe BECHI SHOPPING MALL, da yawan mutane kam sun ɗauka mallakin Alhaji Audu Bechi ne dukda sunan AHMAD BECHI dake matsayin CEO dayawan mutane ma se sannan sukasanshi a matsayin ɗan Alhaji Audun, wani abun mamaki duk tarin Yayan Audu ba kowa ya sansu ba idan ka cire waɗanda suke cikin kamfani. Abinda ze baka mamaki shine hatta JAAY da yake sananne kuma shahararre a duniya mutane basu san Ɗan Audu Bechi bane saboda da yawa suna ɗaukar Alhaji Muhammad Babban Yayansu Binta wanda ya tafi dashi UK a matsayin shine mahaifinsa dan yawan ganin hotonsu da akeyi tare acan, ganinsa da akayi a Taron buɗe Mall ɗin Ahmad da yawa sun bashi expression na cewar Abokin Ahmad ne, ko kuma wani abu na daban ya kawo shi gurin. Au na manta ban faɗa muku bala'in da aka kwasa da Hajiya akan zuwan Jaayy ba, ayi shiru kawai amma Ahmad ya kwashi tsinuwa saboda ta dalilinsa Jaayy ze rasa Miliyoyin da akace mata kullum ana bashi. MATAR MUTUM* *NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER* *FIKRA WRITERS ASSOCIATION* *LITTAFIN KUDI NE* *PAY 500 A ASUSUN* *7061838488* *OPAY DIGITAL SERVICES* *MARYAM FAROUK* OR *0709290797* *ACCESS BANK* *SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488* *IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705* *Kuyi following dina a Arewabooks @Maryamfarouk01 inda zaku karanta wannan littafin tareda sauran littattafaina* *NAGODE* *BOOK 2* *PAGE 4* BAYAN WANI LOKACI. Ahmad Bechi na tsaye a sashen siyar da kayan yara na BECHI SHOPPING MALL daga inda jerin kayan jarirai na sakawa dana amfaninsu, riguna yake dubawa da hannu ɗaya ya dafe wayar dake kunnensa da ɗayan hannun da suke magana da Jafar. Yaja tsaki a karo na uku tunda ya fara duba kayan, daga cikin wayar Jafar yace "Yah Ahmad what is wrong with you? Tun ɗazun kake sasi?" "Don't tell me u still can't pronounce Tsa Jafar?" Ahmad ya faɗa cikin muryar raha, daga can Jafar ya ƙume, bece masa komai ba dan yasan yanzu ze fara tsokanarsa. Tun suna yara harshensa bashi da Tsa, tun ana zaton yarintace dan shi be fara magana irin sosai da wuri ba har yakai shekarun daya kamata ace ya iya furta kowacce kalma amma baya iya faɗin Tsa, sedai kaji yana Fisari, Samiya, Sugunna da sauransu abunna bashi haushi idanana kwaikwayon maganarsa shiyasa yayi shiru dan yasan yanzu Ahmad ze fara jansa ne. "Bari nayi switching to face time call please ka tayani differentiating kayan Baby Boys dana girls, ni duk iri ɗaya suke mun, tace pink for girls blue for boys kuma I'm seeing both colors a kowanne sample na kaya" Ahmad ya kawar da shirun jafar ɗin, "To kai kenan ma da kake ganinsu, ka ɗauka duk wanda ya maka kyau kawai ko ka tambaya wani a kusa da kai, ina yaran da suke tsawaya a counter?" Jafar ya bashi amsa, "Kasan na manta dasu wlh, barina kira Majid kawai ya haɗamun kayan daman aikinsa ne" "And u are there stressing ur self, Yah Ahmad ka fara tsufa fa, ya kamata kayi yunƙuri ka samo mana mata mu sha biki dan Allah" Jafar ya faɗa teasingly, Ahmad yayi murmushi yace "Za'a samu soho a sakaninmu..." "Stop it" Jafar ya tareshi Ahmad ya fashe da dariya yana waiwayen inda ze gano Majid karaf idanun sa suka sauka kan wata Budurwa dake nan tsaye ta jingina da bango ta harɗe hannayenta a ƙirji, kallonsa tayi da alama dariyarsa ce ta janyo hankalinta suna haɗa ido ta juya bayan data masa wani kallo me kama da harara wanda yaji dirarsa har tsakiyar zuciyar sa. "I will call u back, Jafar" ya faɗa be jira amsarsa ba ya kashe wayar ya jefata a Aljihu daidai nan kuma Majid ya iso gurin yana bawa wata Mace me ciki haƙuri akan daɗewarsa, Kwalin Gadon Jarirai ne a hannunsa da alama a store ya ɗakko, daga nan yaci gaba da haɗa mata kayayyaki tana nuna wanda take so yana ɗaukowa. "Kalli wannan Sunyi kyau?" Matar ta nunawa Budurwar dake tsaye ba zaka taɓa cewa tafiyarsu ɗaya ba saboda yanda ta kame gefe tana ta muzurai kamar wadda akayiwa wani abun, "Sunyi kyau Anty, dan Allah ki barsu haka mu tafi ma sake dawowa wani lokacin duk na gaji" ta bata amsa. "Aiko babu inda zanje sena gama siyan komao dan ba lallai na sake samundamar fitowa ba shiyasa ma nace kai tsaye mu taho nan dan nasan komai da nake so zamu samu in kuma ban ƙarasa ba waye ze zo ya siya mun?" Matar ta faɗa tana cigaba da duba kayayyakinta, Budurwar ta narke fuska kamar zatayi kuka tace "Wlh zanzo na siya Miki amma ki barsu haka yanzu mu tafi dan Allah" "Ai se kiyi, in kinga na bar nan to na gama abinda ya kawoni ne ahto" Me cikin ta sake faɗa tana yin gaba abinta da alama wasu kayan ma zata tafi nema, ta kusada Ahmad ta gifta, fuskarta a sake ganin yana ta kallonta yasa tace masa "Sannu" se ya shiga sosa kai, besan sanda ta iso inda yake ba kuma bawai da niyya yake kallonta ba, wani abu yake so ya tantance, idan ba idanunsa ne suke gizo ba gani yayi kamar mutum ɗaya da kaloli biyu a gabansa. Ita da budurwar kamar an tsaga kara, hatta da muryoyinsu, banbancinsu Budurwar fara ce tas ita kuma tana da duhu dan bama za'a kirata wankan Tarwaɗa ba, Baƙace amma kyakykyawa ce tagaske Tabarakalla dan hartafi farar kyau sanda tazo kusa dashi sosai kuma ya fahimci ta girmewa waccan sosai, ba ita ba shikansa da alama zata iya girmarsa dukda da tana da kyan jiki. "Kamar ku ɗaya" ya faɗa mata kamar wani yaro yana nuna ƙanwar tata data zabga tsaki har inda suke tsaye sun jiyota. Matar ta sake faɗaɗa murmushinta tace "Haka ake faɗa, amma na fita kyau ai" ta matsa gaban kayan da yake ta juyawa duk Unisex ne, suna waya da Jay yana jagwalgwala kayan. Nazira ce ta haihu yake so yaje yaga baby shine yake so ya zaɓi kayan da ze kai mata ya kira Aslamiyya tace masa Anything pink is for girls blue na maza shine fa duk ya rikice ya rasa me ze ɗauka kusan minti sha biyar yana abu ɗaya. Ganin ta ciro wasu tana dubawa ya saka yace mata "Yawwa dan Allah Anty wanne ne na mata wanne na Maza?". Tayi murmushi har haƙoranta suka fito kafin tace "Wannan duk unisex ne, ana iya sakawa kowa kawai dai kasan Pink da blue color an fi sakawa Mace ko Namiji amma bayan su kana iya ɗaukan ko wacce kala zeyi, haihuwa akayi maka?" Kai ya girgiza mata yana murmushi yace "Aa, ai banida Mata. Yayata ce ta haihu baby girl nake so naje na ganta shine zan kai mata gift, ko zaki tayani zaɓa toh idan ban takuraki ba?" "Allah ya raya, ya kawo mata ta gari babu damuwa guda nawa kake so kuma kamar na wane kuɗi?" "Haba Anty Sauda jiranki fa nakeyi shine zaki shiga wata sabgar kuma da bakizo ba waye ze zaɓar masa kayan? Duk ma'aikatan gurin nan ke kaɗai ya gani da zece ki tayashi ɗaukar kaya ko kuwai neman gurin zama?" Ƙanwar tata ta faɗa cikin bacin rai. A fili Ahmad yace "Ikon Allah" yana kallonta yayarta me suna Sauda ta lafta mata harara kafin tace "Wai ni dole na miki da ki biyoni ne ko yaya? Idan ba zaki iya jira nagama abinda nake ba FATIMA ga hanya yi tafiyarki mana" Majid da se lokacin ya lura da Ahmad ne a gurin ya saki abinda yakeyi da sauri ya isa cikin ladabi yana cewa "Ranka ya daɗe wani abun kake buƙata?" "No, cigaba da aikinka kawai babu matsala ga Anty zata tayani zaɓa" ya sallameshi. Bata tafin ba se ƙara lafewa bango da tafi tana cika tana batsewa kamar fulawar dataji yeast. Anty Sauda kuwa ta cigaba da ɗaga kaya tana zaɓar nata dana Ahmad da yace kala biyar yake so. "Nagode sosai, Allah ya saka da Alkhairi" yayi mata godiya, Majid ya karɓi kayan yayi masa gaba dasu shi kuma ya kalli Fatima dake dabda fashewa yace "Ki zauna kar ƙafarki ta gaji bari a kawo miki ruwa me sanyi kisha". Sanin idan ta buɗe baki ba zata bashi amsa me daɗi ba tasa tayi ƙwafa kawai ta sake tsumewa. Seda Antynta ta gama jan ranta iyaka kafin aka tattara mata kayan da ta siya aka kai gurin biyan kuɗi lokacin tuni Ahmad ya biya nasa an kai masa mota yana ƙarasa wani abu kafin ya fita, ko tsinke ya ɗauka a gurin seya saka kuɗin balle ma wani yayi tunanin zuwa yace ze ɗibi bati kamar yanda Salim yaso ya fara masa sanda yake zuwa seya kwaso Abokanansa su ɗebi abu ayita rigima dasu a gun biyan kuɗi yace shiya basu ba zasu biya ba securities su hanasu fita, seda Ahmad ɗin yayi masa kaca kaca a gurin sannan ya samu salama dalilin kuma daya saka Salim ɗin ya bar aiki a gun wanda daman Momy tayi masa dole. Suna tsaye a bakin titi suna jiran abin hawa, Fatima nata zabga Mita Anty Sauda kuwa ta mata shiru kamar bada ita take ba, iyakar zafin ranar dake ratsasu ya isa sunfi Awa guda cikin sanyin Raɓa kuma sanda suka shiga rana bata take kamar haka ba seda suka fito suka ganta ƙwal da alamun hadari ze iya haɗuwa zuwa jimawa. Wani abin takaici kamar an hana masu Adaidaitan hanyarsu zuwa duk wanda suka tare da sunce MARMARA zece ba nan yayi ba, wanda zasuje kuma da mutum a ciki su kuma ga kaya drop ma yaƙi samuwa kamar wanda akawa baki. Suna nan tsaye kamar Fatima zata fashe ga rana ga babban abinda ya dameta ita, yanayin da take ji a jikinta ta tabbatar period ze iya zuwar mata a kowanne lokaci dukda gobe take saka ran zuwansa shiyasa ma bata fito a shirye ba amma suna shiga gurin nan taji jikinta ya fara sauyawa irin yanayin da takeji idan jinin ze zuba dan bata wani laulayi ko ciwon Mara sedai taji jikinta na mata wani Yamm kamar tana jin sanyi dataji haka tasan any moment ze iya zubowa to wannan yanayin takeji shiyasa duk ta takura tun shigarsu gurin Miskilanci kuma ya hana tayiwa Anty Saudan bayani se baƙin rai takeyi tana tsaki. Wata dalleliyar mota Ford fara tas ta giftasu se gata ta dawo da baya a hankali ta tsaya a gabansu, Ahmad ya sauke glass, fuskarsa me ɗauke da murmushin yan Aljanna ta bayyana ya kalli Fatima suka haɗa ido yanda tayi seda ya kusa bushewa da dariya amma ya kanne ya maida dubansa ga Anty Sauda. "Bari na rage muku hanya to nima cikin garin na nufa" Ya faɗa bayan da Anty Sauda ta masa bayanin sun rasa abin hawan hanyarsu ne, Fatima ta zabura tace "Yi tafiyarka zamu samu" Anty Sauda ta galla mata harara ƙasa ƙasa tace "Duk saboda ke yake wannan abun kiyi dagaske harya fusata ya tafi" "Allah ya kiyaye ni beyi mun ba" abinda Fatiman ta faɗa ya isa kuma har kunnen Ahmad dake ƙoƙarin saka musu kaya a booth securities biyu da suka hangoshi suka taho da sauri suna tayashi. Murmushi yayi da jin furucin Fatiman, sam kuma ransa be ɓaci ba illa ma burgeshi data ƙarayi domin ta nuna ita ɗin Macece me ra'ayi wani abu da ta gani tattare dashi be ruɗeta ba dukda yasan basu da masaniyar shine mamallakin gurin da sukayi siyayyar. Akan shiga motar ma seda akayi daga da ita Anty Sauda ta balbaleta da masifa Ahmad ya shiga tsakani yana bata haƙuri tareda lallashin Fatiman kan ta shiga su tafi, shikam Ajinta burgeshi yakeyi saɓanin sauran Matan da suke zuwa gurin kaga Mace har Mace amma babu Aji, wasu takanas suke zuwa ganin CEO saboda an san kusan koyaushe yana zaune a office ɗinsa indai yana Kano, wasu ma zuwa suke da ƙaryar kaya zasu kawo, ba kuma zasuyi magana da Sales Manager ba seda CEO kai tsaye da Ma'aikatan suka gane me yake kawo su se suka fara hanasu suce basa karban kaya a hakan wasu zasu zauna a waje jiransa muddin anga motarsa a Parking lot kiran waya kuwa seda ya maida layinsa private idan beyi saving Number ba kira baze shiga ba sannan ya samu Sa'ida, kuskurensa saka Main Line ɗinsa akan Banner su. Suna tafe suna yar hira da Anty Sauda har suka isa bakin titi inda ze ajiyesu dan Mota bata shiga har cikin layinsu, Anty Sauda ta fita ta kira yara suka fara kwashe mata kayanta, seda suka gama tas ta kalli Ahmad tace "Mungode sosai, Allah ya saka da Alkhairi" "Amin Anty, Allah kuma ya raba lafiya, gashi banga gidan ba balle nazo cin naman suna" "Seka karbi number waccen, idan na haihu seta sanar maka ko?" Cewar Anty Saudan. Ya juya ya kalli Fatima yana cewa "Kodai ki bani da kanki, kalli fa yanda ta haɗa fuska Allah sa ba tunanin yanda zata shaƙeni takeyi ba , daman idan kin haihu karki bari ta fara ɗaukan Babyn kar yayo gadon rashin fara'arta ". Fatiman na zaune tana kuma jinsu kamar an dasata a gaban motar, tasan me afkuwa ta afku shiyasa ta kasa motsawa daga inda take. Abinda ta guda da hawa lift ɗin kenan, idan da Napep suka hawo bakinta alaikum se samu hanyar kurɗawa ya kaisu har ƙofar gida data sauka ta afka kuma ba lallai kujerarsa ta nuna ba sabanin ta Ahmad da take fara tas ita kam yau ina zata kai wannan abin kunyar staining a motar jama'a daga Rage hanya? Ya miƙawa Anty Sauda wayarsa ta sanya masa number Fatima wadda tare suka siyi layin banbancin lambobin ƙarshene kawai da tata shiyasa ta riƙe kafin ta sake masa godiya ta shige layi ba tareda tabi takan Fatima ba. "Ko ba tare kuke ba?" Ahmad ya faɗa yana karantar fuskarta, dukda be santa ba amma wannan fuskar tata da akwai abinda yake damunta ba iyakar Miskilanci bane". Fatima ta yunƙura domin babu amfanin zaman da takeyi a cikin motar. Ta kalli kan layinsu dukda tsakiyar ranace ƙwal amma munafukai yan saka'ido na nan suna bin inuwar gefen Titi a haka zata ratsasu ta wuce? Jakarta ta buɗe da dabarar kiran Anty Sauda ta bada Hijabi A Miƙo mata tazo mata, da zasu fita harta saka Hijabinta haka nan ta canza kaya ta saka Abaya Light blue ashe rabon abin kunya ya jata da Hijabi ne Asirinta a rufe kota bata masa kujera shamiƙewa zatayi ta tafi dan ba sake haɗuwa zasuyi ba balle taji kunya. Takaicinta ya ƙaru sanda ta zaro wayar taganta a mace, ita dai yau bata fito da sa'a ba. Ta kalli Ahmad fuska a marairaice, so take tace ya bata aron wayarsa amma ina hali irin nata na shegen Miskilanci ya hanata se kawai ta rungume jakarta jin ya yiwa motar key da alamun ya gaji da jiranta ne ze tafi da ita ko yaya ta kama murfin motar ta buɗe, tana zura ƙafafunta waje Ahmad dake lura da duk motsinta yaga abinda take boyewa, da saurin gaske ya dakatar da ita ta hanyar kiran sunanta da ƙarfi. Ta dakata ɗin tareda kallonsa yace mata "Me yasa tun a Mall bakiyi magana an baki pad kin gyara jikinki ba? Da a haka zaki keta titi ki wuce waɗannan Mutanen?" Mutanen daya faɗa ta kalla. Suna nan tun tsayuwarsu a motar suka baza idanuwa suna naɗar rahoton gulma da munafunci wanda sukafi ƙwarewa akai. Fita yayi daga motar ya buɗw booth, tana tunanin Pad ɗin ze ɗauko mata ko me? Koda yake a yanzu ai pad bata da amfani a gurinta ta samu abinda zata rufa ta isa gida kawai take da buƙata kuma wayar tasa dai itace mafitarta. Tana saƙa abinda zatayi ya dawo da leda a hannunsa ya miƙa matata karɓa ganin kamar yadin Hijabi ko Abaya. Hijabi ta gani data warwarshi har bata sanda ajiyar zuciya me Nauyi ta kwace mata ba, ta zura a jikinta kafin ta saci kallonsa kamar mara gaskiya tace "Nagode" "Babu damuwa, but next time idan kina cikin yanayin buƙatar taimako kiyi magana bakiyi ɓacin rai kina kumburi ba" "Toh" kawai tace masa kafin ta fita tana waiwayen inda ta zauna ya baci sosai kuwa kamar ma da gayya Jinin yazo da yawa dan ya kunyatata. Murmushi Ahmad ya rakata dashi harta ƙulewa ganinsa, harya tada motar se kuma wani tunani ya saka ya gyara parking ya sauka yabi cikin Layin da sukayi. Beyi nisa da yawa ba ya tambayi wasu yara gidansu Fatima sukace basu santa. Ya riƙe ƙugu yana kallon Lokon da ya tabbatar idan ya ƙureshi ze tsinci kansa ne a wata unguwar daban ba wadda yake ciki ba, hagu da dama kuma layukan duk basa ɓulla ya tabbatar gidansu na daga cikinsu, harya haƙura ze juya tunda ya samu number wayarta sega wani saurayi ya fito daga wani gida da bokitin Markaɗe ya tareshi yana tambayarsa gidansu Fatima. "Farace sosai?" Yaron ya tambayeshi ya gyaɗa masa kai alamar itace, yaron ya ƙwalawa ɗaya daga cikin yaran dake wasa kira yace "Ka rakashi gidan Malam bakanike" "Bansan gidan ba" yaron ya faɗa yana zabura ze koma gun wasansa wanda ya kirashin ya talle masa ƙeya yace "Gidan su Jafarun ne zakace baka sani ba banza gidansu yar Fara fa" "To ai haka zaka ce mun ba yanzu Anty yar Faran ta wuce ba da Antynsu me Mota sun taho da kaya da yawa mu muka kai mata gidan ma ta bamu Cakulat" yaron ya sake faɗa kafin yayi gaba yana tsalle, Ahmad ya zaro dari biyar a aljihunsa ya bawa babban yaron kafin yabi bayan wancan. Da yar tafiya daga Titi zuwa gidansu a can cikin Lokon suke har sun kusa shiga Alfindiki ma daɗin da sukaji lokon gaba ɗaya lailaye yake da Interlock ga Fitulun Solar da alamu basu da matsalar haske har tsakar gida sun huta da kunna fiti. A ƙofar wani gida yaron ya tsaya. Daga yanayin ginin zaka fahimci gidan masu ƙaramin ƙarfi ne, ya sallami Yaron da alawoyin dake cikin Aljihunsa sannan ya juya ya tafi daman gurin kawai yake so ya gani. Babu ƙyama ya saka Ruwa daya zubawa Omo da freshner ya goge kujerar tsaf, ya maimaita gogewar har sau uku kafin ya saka clean ruwa ya goge sannan ya sake fesa Freshner akai sa'annan ya ya tayar da mota ya bar gurin. Yana tuƙi yana tunanota, yanda take haɗa fuska tana motsa ƙaramin bakinta ba ƙaramin kyau tayi masa ba. Ya tuna idanuwanta sanda ta rasa mafita ya bata Hijabi, muryarta a karaye da tace masa ta gode har zuwa tafiyarta a sanyaye kamar wadda batada laka. Zuciyarsa ta ringa ayyano masa gidan data fito, yanayi na suffa da tsarin halitta daga ita har Yayarta be taɓa hango daga irin wannan unguwar suka fito bama balle wannan gidan, seya tuna da wani abokinsa Munir da ya taɓa ce musu Mata da suka amsa sunan Mata na cikin Lungu. "Kunga unguwannin nan da muke gani as no go, wlh mata nacan, kaga yarinya kamar ita tayi kanta gashi sun ƙoshi da tarbiyya kawai dai basu kai wayewar da muke kwaɗayi ba amma ni dai idan na tashi aure Lungu zanje na samo mata wadda zan ringa Faɗawa magana taji da ɗan kuɗina ƙalilan Alaji a hankali na wayar da ita yanda nake so" inji Munir ɗin to yau ya gasgata zancensa domin Fatima dai kodaga Villa ta fito ta isa Mace kuma za'a nunata a ko ina ba tare da anji kunya ba, shikam yaga Mata dukda tace be mata ba, ze tabbatar da se yayi matan dan baze bari ta wuceshi ba, ita ɗin tayi daidai da tsari da ra'ayinsa. Yama manta da zeje gidan Nazira seda ya ganshi a ƙofar gidansu tukunna ya tuna, kwakwalwa duk tunanin Fatima har ya fara loosing focus. Gidan ya shige akan se da dare idan ya fita seya kai mata kawai. Haka ya ƙarasa yinin ranar har gizo take masa muryarta na masa amsa kuwwa. Ahmad be taɓayin budurwa da yaji ta shiga zuciyarsa farat ɗaya a ganin farko ya sakawa ransa ya samu mata ba se akan Fatiman. Mutum ne shi da idan abu ya shiga ransa tofa se Allah, Fatiman kuma abin nata yazo masa da gaske, daga haɗuwa yini ɗaya harya fara tsara rayuwar da zasuyi tare, har tunani yakeyi idan da gaske tace beyi mata ba wani kalar garari rayuwarsa zata shiga dan ya rigada ya kwallafa rai a kanta, shi kuma duk abinda ya saka rai da samu baya taɓa saduda har seya mallaki wannan abun. Yaya zeyi idan ya gaza cin galabar zuciyar Fatima ta Aminta dashi. Seda yayi sallar Isha'i ya tafi gidan Nazira, ya tarar da Matan Naziru Uwargidan Anty Mardiyya da Amaryar da yayi kwanannan Yusra wato Yuseebaby Shahararriyar yar rawar Nanayece a Sabuwar Manhajar Tiktok, su suka fara yankewa bin waƙa ana rawa a tiktok ɗin cibi. Allah kaɗai yasan inda Nazirun ya yayibota kuma da yake me uwa a bakin murhune duk sukar da abokanan Alhaji suka ringa kawo masa akan Yarinyar wadda kowa ya bada shaidar bata jin magana cewa yayi tunda me Auranta yaji ya gani ai shikenan, Karuwa ma idan ta tuba ana auranta balle ita da babu wanda ze kawo shaidar cewa tana Alfasha, Yarinyar da har video take iyayi da undies ta ɗora a Tiktok amma Alhajin ya murje ido yace babu komai ya aureta, koda yake umarnin Hajiya domin ita yarinyar tayi mata, yanda tayi suna tayi shura tana da followers bila Adadin a duniya baki ɗaya ba iyakar Nigeria ba ga uwarta tana da kuɗi suna da ƙaton gida wanda akace ire iren Alhazan da take hulɗa dasu ne wani ya gina musu gidan, hatta Kawunta daya bawa Nazirun Auranta se bayan anyi Baba Alƙali ya binciko cewar ƙaryane ashe ba ɗan uwanta bane tsohon saurayinta ne. Mahaifinta kuma yana raye sukace ya rasu, mutumin Sokoto ne, gajiya yayi da halin uwarta ya saketa tun Yusran na yar yarinya ta taho da ita Kano ta tashi a sakalce yanda dai take yanzu, to Me aure da iyayensa sunce sunji sun gani duk wani me abin faɗa dole ya kama bakinsa. Sanda Ahmad ɗin ya shiga falon Nazirar ma tarar da ita yayi ta jera Yayan Nazirar Su uku yammata babbar ta riƙe yar Babyn ta kunna waƙa tana musu Video suna rawa Nazirar da Mardiyya da wata da be sani ba suna zaune suna hira daga gefe, ransa ya baci, tun batafi wata da shiga gidansu ba ta fara koyawa Yaran gidan wannan iskancin raye rayen ana video, seda ya kwace wayar Maimuna data Sarah, ita Aslamiyya tumda ya mata gargaɗi ta dena. Wayar Sarah ko awa batayi a hannunsa ba Hajiya tazo ta fara Tijara Momy tace ya basu wayarsu. Maimuna ma taurin kai tayi masa taci gaba dayi wai a Draft take saving randa ya ɗauki wayarta ya gani shikenan ya kasheta ya ajiye seda tayi wata uku taji jiki kafin ya bata to basu Kaɗai ba Babbar Yar Alhaji Zakariyya ma tana nan ance ta fara zama sananniya a Tiktok ɗin dukda dai ubanta yace wai tallan kaya takeyiwa Mamanta dake tana siyar da Dogayen riguna da sauran kayan kwalliyar Mata, amma fa rawa take tiƙa abinta kuma duk wani trend daya fito sune akan gaba gurin yi abin dai se a hankali. Bayan sun gaisa ya Naziran yace mata "Amma Anty kina kallo take ɗaukan video yaranki harda Baby zata saka a Tikto, baki san duk a nan yara suke kwaso baki kowa idan ya gani da me faɗar Alkhairi dame bakin sharri wani ma yabawa zeyi amma idan bakinsa bame kyau bane se kiga wani abu ya faru, ya kamata dai ku ringa kiyayewa, ko su wanda suka kawo Tiktok ɗin wayanda suka san abinda sukeyi a cikinsu basa exposing yaransu ƙanana ko zasu musu video basa nuna fuskarsu amma kalli yanzu dan Allah Nur ai ta wuce shekarun da zata ringa daukar hoto babu kallabi bare har a ɗorata a Tiktok". Mardiyya tace "uhm" domin abune dayafi ƙarfinta tayi magana su koma gida ta haɗa mata tuggu gurin Mijinsu se ɗayar matar ce tace "Nima dai na faɗa, Malamai ma nata wa'azi akan wannan shagalar data zo mana wlh, gaba ɗaya yara sun lalace, tun suna ƙanana an cire musu kunya ana sakasu suyi ta raye raye ana ɗorasu a duniya haka zasu tashi basajin nauyi ko kunyar yin rawa a ko ina ko a gaban wa kuma ta bakinka dame baki mai kyau da mara kyau kowa ya tanka Allah dai ya kiyaye. Kaganni ni ko saka hoton jinjiri a status na kiyaya wlh, nan wata ƙawata ta haihu, bakuga yaron ba Tabarakallah Masha Allah kyakykyawa kamar ɗan larabawa. Ta ringa turashi group group na makaranta, na kasuwanci, na Novel ne groups ɗinta na WhatsApp babu inda bata tura hoton Yaron nan ba kowa kaya kaya anata yabawa wasu na cewa basu taɓa ganin Jinjiri me kyansa ba, in taƙaita muku wlh Yaron nan kamar wasa ya fara rashin lafiya, Asibiti har Saudiyya suka kaishi anyi gwaje gwaje ance komai lafoya ba'asan abinda yake damunsa ba yaron nan be samu lafiya ba har seda ta Allah ta kasance shekarar sa Ɗaya ya mutu kuma bata daddara ba yana Jinyar tana sake tura hotonsa wai a tayasu da Addu'a Allah ya bashi lafiya, shin idan ka haihu ba zaka iya faɗa haka kawai ba dolene se ka tura hoton Yaro ko Yarinya a group? Kasan iya inda ze tsaya mutane da Aljanu masu ido biyu da masu huɗu duk suyi ta kalle maka Yaya to yi ta kanki dai ki karɓe jinjinniyarki idan ma su manyan ba zaki hanasu ba ita dai bata san komai ba kar a fara ɗura mata sheɗanci a kwakwalwa". Yusra fa ta shaƙa tayi fam musamman da Nazira tace ta goge Video dan idan Babansu ma ya gani tasan se yayi faɗa ai ta zata a WhatsApp status zata ɗora shiyasa ma batayi magana ba. Ta ringa hararar Ahmad domin shiya zo da wannan sanaben, shidai ko kallonta beyi ba dan ko gaisawa basuyi ba ya gama abinda ya kaishi gidan ya tafi. Yana cin abinci a falon Momy yana bata labarin zuwansa gidan Nazirar Jay ya kirashi, a speaker yasa wayar yana ci suna magana har zasu kashe Jay ɗin yace "Yah Ahmad waye ka gani ɗazu that you hanged my call?" Ahmad ya saki wani murmushi, shauƙi ya kwasheshi harya manta a inda yake. Wani baya yayi ya tallafe ƙeyarsa da hannu biyu yace masa "Addu'arka ce ta karɓu, muna wayar nan naga wata tsaleliyar budurwa ta sace mun zuciya, I'm telling you my brother na samu matar Aure" Ihu Jay ya fasa, a kwance yake akan tamfatsetsen gadonsa cikin apartment ɗinsa a birnin London amma haka ya tashi yana ihu yana tsalle kamar wani ƙaramin yaro. Ahmad kuwa besan katoɓarar da yayi ba seda ya ɗaga kai suka haɗa ido da Momy, a sittin ya fice daga falon seda suka kwana biyu suna wasan ɓuya dakyar tayi Bikonsa amma dukda haka sun zama kamar surukai baya iya haɗa ido da ita. *ALBISHIRINKU MATA YAN UWANA YAN KWALISA NAZO MUKU DA WANI DADDADAN LABARI!!!.* *NASAN KUNDADE KUNA NEMAN FITACCEN GURIN DAZAKUJE AMUKU GYARAN GASHINKU DANA JIKINKU CIKI DA WAJENSA,TO YANXU DAI GA DAMA TA SAMU...* *LABARI NAKE BAKUFA AKAN AFINTY QUEENS SHAHARARREN SHAGONMU NA SALOON DAYA HADA KOMAI DA KOMAI DA KOWACE MACE YAR KWALISA IRINA KE BUKATA,SANNAN MUNADA KWARARRUN MA'AIKATAN DASUKASAN KAN AIKINKINSU,KUZO AFINTY QUEENS KUBIYA KUDI MUKUMA MU BATA LOKACINMU DOMIN TSATSTSAFO DUK WANI KYAWU NA JIKINKU DA ALLAH YAYI MUKU...* *A AFINTY QUEENS MUNA AYYUKA KAMAR HAKA:* *- HAIR SALOON* *-HENNA* *-SPA* *-DUKKAN* *-PEDICURE* *-MANICURE* *-SANNAN MUNA DA TURARUKA IRIN NA AMARE YAN MATA DA KUMA MAI KANKAT DAN UWAR GIDA TA TURARA GIDANTA JIKINTA DAMA KAYAN SAWARTA ITA DA YARANTA,,HARMA ZAWARAWA DUK MUN TANADI KOMAI* *DOMINSU SUMA* *-MUNADA SHOES AND BAGS SBD ISASSUN MATAN DA SUKA AMSA SUNANSU MATA*😊 *- MAKEUP NA BRIDAL ND CASUAL...* *IDAN KINSAN KINAJIN LABARIN SHAGON SALOON NA AFINTY QUEENS AMMA BAKI TABBATAR DA YADDA AIKINSU YAKE BA TO YAR UWA GADAMA TASAMU MEZAKI TSAYA JIRA MAZA KEMA KI ZARGAYO SHAGONMU DAZAN JERA MIKI ADDRESS DINSHI A KASA DOMIN KEMA KI TABBATAR DA KALAR IRIN NAMU KWAZON DA MUKA KWARE AKANSHI GURIN GYARAN JIKIN YAN UWANMU MATA KUMA MUKE GABATAR MUSU DA JAKUNKUNA DA TAKALMA HARMA DA TURARUKAN WUTA DANA SHAFAMA JIKINSU DON NISHADIN ZUCIYARSU DANA MAZAJENSU....* *AFINTY QUEENS DISCOVER BLISS IN BEAUTY 💅💯* *Address 👇👇:* *KU ZIYARCE MU A SHOP NO.9&10 SHEMA PLAZA,BEHIND SHEMA FILLING STATION KASUWAN BACCI KADUNA* *TEL:08133379628.* *MATAR MUTUM* *NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER* *FIKRA WRITERS ASSOCIATION* *LITTAFIN KUDI NE* *PAY 500 A ASUSUN* *7061838488* *OPAY DIGITAL SERVICES* *MARYAM FAROUK* OR *0709290797* *ACCESS BANK* *SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488* *IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705* *Kuyi following dina a Arewabooks @Maryamfarouk01 inda zaku karanta wannan littafin tareda sauran littattafaina* *NAGODE* *BOOK 2* *PAGE 5* MARMARA GIDAN MALAM HAFIZU BAKANIKE Jiki a sanyaye kamar kazar da ruwan sama ya buga ta shiga gidan bakinta ɗauke da ƙaramar sallama. Anty Sauda na tsaye bakin fanfo tana wanke hannu bayan ta gama jajjefa ɗan waken da Ummansu tayi abincin rana, giftawar Fatiman kawai ta gani ta shige ɗaki dan bataji sallamar ba, bata daɗe a ɗakin hannunta riƙeda Kwandon kayan wankanta se zani da ledar pad har sannan tana sanye da Hijab ɗin daya mata kyau matuƙa ta raɓe Anty Saudan zata shige banɗaki "Ina kika samo Hijabi kuma?" Antyn ta tambayeta ta shige ba tareda ta bata amsa ba. Taci Sa'a ruwan fanfo yazo ta tara bokiti dukda bata son wanka da ruwan sanyi kwata kwata komai zafi dole haka ta watsa dan babu lokacin da zata tsaya ɗumama ruwa yanzu. Bayan ta gama ta wanke rigar ta da kayan cikin da suka ɓaci, faɗin irin yanayin da take ciki kan wannan abin kunya daya sameta ɓata lokacine, tunani takeyi wa ze gyara kujerar da ta ɓata? Da kansa ze goge ko car wash ze kai? Ita kam yau taga ta kanta Period ya kwafsa mata wai ma Allah yasa ba idon sani bane babu lallai su sake haɗuwa yanzu da be bata Hijabin nan ba ya zatayi? "Ko ina ya samu Hijab ma oho" ta faɗa a fili tana shanya kayanta akan igiya. Anty Saude tayi rashe rashe cikin barander ga Zobo me sanyin gaske gabanta tana sha tana kallon Fatiman ta sake shigewa ɗaki, seda ta kimtsa kanta sosai kafin ta fito har sannan ranta babu daɗi ta zauna kan Tabarmar kusada Anty Sauda. "Wai wane isakanci ne yake damunki AFEEYA ina ta miki magana kina mun banza, wani sabon raini ne yake neman shiga tsakaninmu ko yaya?" Anty Saudan ta faɗa a ɗan fusace. Idanun Fatima sukayi rau rau har muryarta na rawa tace "Toni me zance miki? Duk bake kika jawo mun ba ina tace miki mu taho gida kikaƙi har seda kikaja na ɓata jikina shima na ɓata masa mota" Anty Sauda ta buɗe baki da mamaki tana kallonta kafin tace "Lallai yarinyar nan, duba nakeyi da zansan matsakarki ko kuwa ɗinke miki baki akayi da bazaki gayamin abinda kike ciki ba? Yanzu staining kika masa a mota? Innalillahi Afeeya kin tafka abin kunya staining a motar saurayi haɗuwar farko gaskiya abu beyi daɗi ba ka kujerunsa farare tab" bata gama rufe baki ba se ga hawaye sha sun fara zubowa Afeeya kamar an kunna fanfo abin ma se ya bawa Anty Sauda Dariya ta cigaba da Tirata tana faɗin ta kwafsa "To waya baki Hijabi kuma?" Ta tambayeta cikin kukan Afeeya tace "Shiya bani mana, harda cewa wai meyasa tun a can gurin ban tambaya an bani pad ba?" Anty Sauda cikin jimami kamar gaske tace "Ai gaskiya ne, kinga ranar Gayu ai gobe ma idan kina Al'ada ki sake saka kaya masu haske ki fita babu Hijabi, ni wannan daya bakin ma ɗinkin yamun kyau, idan ya kiraki ki tambayarmun shi inda ya siya". Kuka AFEEYA ta dage tanayi kamar yarinya tsa tsani raini yanzu ga ƙarshen raini can wani Namiji yaga jinin Al'adarta ita kuma Anty Sauda harda cewa wai ya kirata, ai wlh koya kira blocking zatayi babu ma zancen ko gaisawa suyi balle ya tuno abin kunyar da tayi a motarsa. Sallamar Ummansu ce tasa ta tsagaita kukan da takeyi, bata ma san bata gidan ba se yanzun data shigo. Umman ta zare Hijabin jikinta ta saƙale jikin igiya tana kallom Afeeyan tace "Uwannan lafiya? Meya faru kike kuka? Ina kuma kika tsaya Yayarki ta rigaki shigowa gida?" Se maganar Umman ta sake tunzurata kukan ya ƙara ƙarfi, ta gaya mata bata son wannan sunan wai Uwannan amma Umman taƙi bari kamar da gayya ma take kiranta haka dukda Baffa da kansa yace ta dena amma taƙiji. Anty Sauda ce tayi mata bayani, Umman ta haɗiye dariyarta tace "To kuma shine abin kuka? Lalura ce shima ai ya sani. Kima godewa Allah daya sa yana da abinda ze baki ki suturta kanki, kina kukan dan shi kaɗai ya gani to da kuma kin keto Titi da abin ashe ba zaki sake fita ko ƙofar gida ba saboda kunyar yan unguwa" maganar Umman Gaskiya ce wannna tasa ta haɗiye kukanta ta zubo abimci tana ci tana sauraron hirar Umman da Anty Sauda. Har dare ta kasa sakewa duk motsi seta tuno Ahmad da yanda ya ringa kallon gurin data ɓata Allah kaɗai yasan tunanin da yakeyi a ransa. Da Mijin Anty Sauda yazo zasu tafi haka suka sake kinkimar kayan da suka siyo ɗazun aka kai Mota, Afeeya nata mitar mema yasa ta kawo su gidan da se ta barsu acan su mata Delivery kai tsaye ba seta wahalar da mutane anyi ɗauka biyu ba. Har Anty Saudan ta zauna a motar ta yafito Afeeya tana cewa "Ya kiraki kuwa?" "Wa?" Ta tambayeta kamar bata gane wanda take nufi ba. Anty Sauda ta lafta mata harara tace "Saura ki masa wulaƙancin da kika saba yiwa samari" "Ai daman na gaya miki beyi mun ba" amsar data bata tana tura baki ta koma gida. Dagaske take har ranta Ahmad beyi mata ba a matsayin saurayi. Bashida makusa a halitta domin kyakykyawane daidai misali amma magana ta domin Allah yayi mata ƙarami shi ba wani tsayi can ba kuma bashida jiki sannan da ganinsa sanyi ƙalau ne se yanda mace tayi dashi kuma ya fiya Fara'a gaba ɗaya be kama hanyar Mijin da take buri ba. AHMAD Yar matsala suka samu ta rikicewar lissafi a Shago wannan ya ɗauke masa hankali haryasa be samu damar kiran Fatima ba har akayi sati guda da haɗuwarsu badan ya manta da ita ba ko bata ransa Aa sedan yana da buƙatar nutsuwa gurin warware abinda yake a gabansa. Seda ya samu komai ya koma kan layi kafin ya dawo lissafin Fatiman har yayi niyyar kiranta sedai kamar Almara ya nemi number da yayi saving da hannunsa sama ko ƙasa ya rasa. Yayi mamakin yanda akayi ta goge amma ya godewa Allah daya sa yayi basirar bincikar gidansu tun waccen ranar. Da Magriba ranar Juma'a bayan ya dawo daga sallah ya niyyatu zuwa gidan idan yaso ya sakw karɓo number dan dagaske yakeyi yaga fure kuma bazeyi saken da zata kufce masa ba. Fuskar daya gani a gurin Yayarta ta tabbatar masa Fatiman a kasuwa take, ma'ana wani bai rigashi ba ko ba'ayi mata baiko da wani ba domin yanayinsu basuyi kama da wanda zasuyi kwashe kwashen samari ba. Tsaf ya shirya cikin Manyan kaya ya kafa hula shida kansa yasan yayi kyau ya ringa murmushi yan fesa turare yana hasaso fuskarta ya zata karɓeshi? Da tace beyi mata ba dagaske takeyi har ranta ko kuwa dai irin abin nan na yammata ne? Wayarsa dake ajiye ce ta ɗauki ƙara ya janyota ya duba Momy cw take kira dan haka ya ɗaga da sauri yana sallama. "Yaya Ahmad wai ni ina saƙona daka karɓomun kai baka ce mun gasu ba nima na sha'afa fin sati se yanzu da nake so nayi amfani dasu na tuna" Momy ta faɗa bayan data amsa sallamarsa. Tana cewa saƙo ya gane wanda take nufi, Hijaban daya karɓo mata ne a gidan *UMMU-MAHEER ME HIJABS ƊIN YAN GAYU* wanda harya ɗaukarwa Fatima a ciki. "Yanzu zan kawo miki Momy na mantane wlh" ya faɗa da sauri kuma ya ɗauki muƙullin motarsa ya fita daga ɗakin suka kusa yin karo da Lawan, Autan Hajiya Binta a Maza ya taho hannu biyu riƙe da Tab yana buga game kamar wani yaro ƙarami yayi diri diri shi bai kauce ba be kuma matsa bayaba. Haushi ya ƙume Ahmad, ga sauri yanayi a fusace yace masa "Ni zan kauce maka ka wuce kenan?" Lawan ɗin yayi muimui da baki kafin ya raɓe gefe, Ahmad yayi ƙwafa ya wuceshi dan yana da abinyi yanzu amma tabbas se koma ta kansa wannan rainin da yaron ya ɗauko baze zuba Ido ya barshi ya tashi a haka ba kamar sauran Yaran gidan idanba haka fa Zayyad da yake ƙarami a gidan duka shima haka ze taso da Tarbiyyarsu, Matan tasu rashin kunyar da sauƙi da wuya suyiwa Mazan sedai a tsakaninsu amma su waɗannan da suke tashi yanzu shida Mu'allim jin kansu suke daidai dai da uban kowa daman Salim Da Faisal sun rigada sun ƙafura tuntuni. Ledar Hijaban ya ɗauka, guda goma ne ya bawa Fatima ɗaya ya wuce ciki a tsakar gida suka ci karo da Hajiya idanuwanta akan Ledar hannunsa tamkar zata huda tashiga taga abinda yake ciki haka take kallon Ledar ko gaisuwar da yake mata bataji ba balle ta amsa dan haka yayi gaba shina ya kusa shiga ɗakin Momy ya jiyota tana cewa "Au Amadu, kana kallona ka wuce ko gaisheni ba zakayi ba" "Ya fa gaisheki Hajiya kinata kallon Ledar hannunsa" Sarah ta bata amsa aiko ta kai mata duka ta kauce nan ta shiga sababi tana cewa "Dan uwarki dake nake? Ko kin koma Amadu bansani ba shegiya me shegen shishshigi a abinda ba'a sakata ba kuma da idon ubanki kika ga ina kallon kayan hannunsa?" Hajiya Rabi na daga cikin falonta inda ta idar da sallah tana lazumi hayagagar Hajiyar ya na neman ya raba mata hankali dan ta jikin window ta take tsaye, rabon ayi yasa ta leƙa kaɗan tacewa Hajiyar tayi haƙuri tayi shiru nan ta juya kanta ta dirar mata cin mutunchi da gorin da bata gajiya dayi mata. "Itama Rabi banda neman magana waya kaita tanka mata? Yau Allah ya taimakemu tun safe kunnuwanmu shiru rabon dai se an mana na dare" Momy ta faɗa sanda Ahmad ya dire ledar hannunsa a ƙasa ta jata gabanta tana fito da kayan ciki. Hijabai tara ta gani, ta fara ciresu daga ledojinsu tana duba yadin, fuskarta a washe tace "Kaji laushin yadin nan ga kyau a ido waye zece ba Ɗan Egypt ɗin bane?" Ahmad ya ja guda yana dubawa yace "Wai daman ba order kikayo ba?" "Inafa order? Yadin gidane wlh a gurin Hajiya Hauwa nake ganin ire irensu harta bani guda biyu naji daɗin ɗinkin sosai yanda yake zama a jiki be matse ba kuma baya bin Jikin mutum ga matured style na hannaye nima na ɗauka na wajene tace mun wata Matace takeyinsu sunanta *MARYAM FAROUK amma anfi saninta da UMMU-MAHEER (07061838488) indai Hijabi ake magana daga Normal Hijab me Hannu ko Mara hannu, Jilbab, ko two pieces Gown da V hijab to idan ka sameta an rufe magana, ga yadikan da take amfani dasu ka gansu nan dai ga kyau ko ba'a faɗa ba zasuyi quality sannan ga sauƙi shiyasa nace ta bani number ta kawai na siya na huta da jigilar siyowa daga Egypt ɗin nan kuma babu lallai mutum ya samu yanda yake so". "Gaskiya sunyi kyau sosai nima idan zan siyi Hijabs zaki bani number ta" yayi suɓutar baki, Momyn tayi dariya tace "Wato kowacece wannan bata kama da sauƙi ba, to Allah ya nuna mana lokaci dama ai ita zan bawa order Hijaban Lefenka da Jafar, ni guda tara ma na gani inaga tayi kuskuren lissafi ne" Ahmad ya shafa kansa cikin kunya yace "Aa Momy ni na ɗauka ɗayan" "To seka turamun kuɗina kuwa, ina zakaje haka naga kasha kwalliya da daren nan ko gurin yar tawa zakaje?" Ta sake faɗa tana kallonsa daga sama zuwa ƙasa ganin harda hula ya kafa, seya juya ya nufi ƙofa yana cewa "Kai Momy, nidai sena dawo kiyimun addu'a" "Allah ya tsare ya dawo dakai lafiya" "Amin Momyna" ya amsa daga nan ya fice da sauri yana jin Hajiya na kwala masa kira yaƙi tsayawa dan ɓata masa lokaci kawai zatayi ya sani. Daidai inda ya saukesu waccen ranar yayi parking, akwai wutar Nepa ga kuma fitilun Solar a cikin layukan dan haka hankali kwance ya ringa kutsawa harya isa ƙofar gidansu. A kan Dakali dake ƙofar gidan ya zauna ganin gurin fes yake babu datti kamar yanda Dandamalin Ƙofar gidan yake har zuwa cikin soron da shima yake shafe da sumunti da fasassun Tiles ko ina tas. Hangen yaron daze tura yayi masa sallama da ita yakeyi sega wani Saurayi da zasu iyayin Sa'anni koya girme masa da kaɗan ya fito daga gidan yana ganinsa ya fahimci ɗan gidannan kamarsu ɗaya dasu sedai shima be kaita haske ba amma yafi waccen Yayar tasu haske. Ya miƙawa saurin daya dakata hannu sukayi musabaha. "Baffa za'ayi maka sallama dashi?" Saurayin ya faɗa dan dukda ya ganshi Matashi be kawo gurin Afeeya yazo ba tunda yasan samarinta a waya suke kiranta da wuya a aiko yaro sallama kuma ya dade a cikin gida harya fito beji tayi waya ko tayi zancen zatayi baƙo ba. Ahmad kuwa ji yayi kamar ya masa wata tunasarwa daya manta. Tabbas da mahaifinta ya kamata ya fara magana ya nemi izinin nemanta kamar yanda Shari'a ta tanadar dan haka yayi murmushi yace masa Eh. Saurayin ya juya, a bayan rigar Jessy dake jikinsa yaga an rubuta JAY amma bata Arsenal bace ta club ɗin unguwa ce amma ya tabbatar sunan daya gani baya rasa ace Fan ɗin Jafar ɗinsa ne. Saurayin ya fito ya sanar masa da Baffan yana zuwa daga nan ya wuce inda zashi, babu jimawa Sega wani Dattijon ya fito a ƙalla zeyi shekaru sittin da ɗoriya yana da matsakaicin jiki tamkar dai Ahmad ɗin, babu wata shahararriyar kama tsakaninsa dasu Fatiman seta jini da kuma fatarsa me duhu da Anty Sauda da saurayin da yaji ya ambata da Jafaru suka ɗauka. "Samari kaine Jafaru yace kanaa sallama dani?" Baffan ya faɗa. Ahmad ya zube a ƙasa kamar ze kwanta ya shiga gaisheshi Baffa se cewa yake ya tashi karya ɓata kayansa amma ya ƙi tashin. Bayan gaisuwar shiru ya biyo baya, Baffa na kallonsa da sauraron jin me yake tafe dashi Ahmad kuma nauyin Dattijon da kunya irin tasa yasa ya kasa magana seda Baffan yace "Inajinka samari lafiya dai ko? Fuskar taka ta kwantamun gaskiya ko maganar gyaran Mota ce?" "Aa Baffa, bamu taɓa haɗuwa bama. Daman wata yarinya na gani kuma akace a nan gidan take, shine nake so nayi tambaya naji ko da maganar wani a ciki" ya tattara ƙarfin guiwa ya faɗa. Baffa yayi murmushi Ahmad ɗin kuma ya burgeshi domin ya nuna shi ɗin mai tarbiyyane kuma yasan shari'a. Gyara tsayuwa Baffa yayi yana kallonsa yace "Madallah, naji daɗi kwarai da kayi abinda ya kamata kuma ina mai sanar dakai Yarinya tana da manema amma har yanzu dai babu wanda magana me ƙarfi ta ƙullu tsakaninsu dan haka kana da dama ka gwada taka sa'ar idan da rabo se Allah yasa a dace, amma Yaya sunaka? Kuma kai ɗin ɗan garin nan ne ko Ina?" Daɗi ya kama Ahmad jin amsar Baffa ya sake sunkuyar da kai yana murmushi yace "Eh, ni ɗan garin nan ne. Mahaifina sunansa Alhaji Audu Bechi sunana Ahmad" "Alhaji Audu Bechi dai dana ke jin sunansa?" Baffa ya faɗa cikin mamaki, Ahmad ya gyaɗa kai cikin tabbatarwa yace "Eh shi, ni Ɗansa ne". "Toh, toh masha Allah, amma yaro ita Mamana ka gani ko kuwa wata ce tazo gurinta kaga ta shiga nan gidan?" Baffa ya sake tambayarsa dason tabbatarwa domin sunan Mahaifinsa daya kira ya sakashi kokonton Anya wanda ya fito daga babban gida kamar wannan ze biyi yar Talaka irinsa yace yana sonta da aure? "Sunanta dai Fatimaz tareda yayarta Anty Sauda na gansu" Ahmad ya bashi amsa wannan ya tabbatar masa dagaskw ita Fatiman dai ya gani. Numfashi yaja kafin ya fara magana yana cewa "Tabbas Yatace wacce ka gani, sedai kuma a matsayi da irin gidan daka fito bana tsammanin zaka zo gida kamar nawa kace kaga yarinya kana so ba kuma da aure, dan haka ina roƙonka da kayi haƙuri idan wata sharholiya ce ta kawoka gurinta ka tafi domin nasan maganar Aure ba zata taɓa yuwuwa a tsakaninku ba saboda banbanci matsayi da kuke dashi, a zamanin nan da Masu kuɗi suke kyamatar talakawa bana zatom koda har zuciyarka da gaske kake son Fatima Iyayenka zasu goyi bayan daka Aureta kadai ga gidansu ka kuma ganni nine mahaifinta ni ba kowa bane sana'ar gyaran Mota nakeyi da ita nake cida Iyalina na shayar dasu kar wani kyau ko zubin Halittarta ya ruɗeka, ni bana son tashin hankali da abinda ze janyo Kace nace, a Ƙasar nan babu wanda besan sunan Mahaifinka ba bana tsammatar mutum kamar shi ze yarda ya haɗa zuri'a da Talaka kamata". Cikin mutuwar jikin da maganganun Malam Hafizu Ahmad ya buɗe baki dakyar yace "Amma Baffa banji daɗin da kayi mun zaton wani abu na daban ya kawoni gurin Fatima ba aure ba, dukda kaima kana da naka uzurin amma Baffa da Mai kuɗi da talaka duk Allah yayisu babu wanda yafi wani a gurinsa se wanda yafi tsoronsa da kiyaye dokokin Allah. Sannan babu wata Aya ko Hadisi ko shari'a data haramta Aure tsakanin Mai kuɗi da Talaka, kuma Baffa Mahaifina baya daga cikin irin waɗannan mutanen da suke kyamatar wani saboda banbancin matsayin abun duniya ko Mulki, a auratayya bayan Ingancin Asali da Tarbiyyar gidan da aka nemo Auran muddin Ma'aurin yana so bashida damuwa baze hana ba. Nine Ɗa na goma sha ɗaya a jerin Maza, yayyena Tara sunyi aure ɗayane beyi ba a cikinsu kuma harda me mata uku sannan kowa da irin gidan da yayo aure babu kuma wanda Alhajinmu ya taɓa hanawa ya auri Matar da yake so ba na tabbatar kuma ba za'a fara a kaina ba In sha Allahu". Malam Hafizu ya sakw jan numfashi yace "Karka fahimceni a baibai Yaro, tabbas ba kowanne me kuɗi bane yake da hali na ƙin Talaka amma kuma kuma masu irin waccen Ɗabi'ar su sukafi yawa. Abinda yasa kuma nake maka togaciya saboda bana so azo a maimaita abinda ya faru akan Yayarta, Mijin da ya aureta yayiwa Iyayensa ƙarya akan Asalinta saboda ya samu su barshi ya aureta ba tareda qata tangarɗa ba, aure kuma ba'a ɓoye ɓoye domin komai daren daɗewa se gaskiya ta bayyana dan haka abu ɗaya da nake so kaje ka nemi Yardar Iyayenka ka gaya musu yar wa kake nema kake kuma so ka aura kar kayi musu ƙarya idan har ka samu Amincewarsu ni banida matsala ya rage tsakaninka da yarinya kus samu daidaito namu mu rakaku da Addu'a" Daga haka Baffan yayi masa sallama ya koma gida Ahmad guiwoyi a sage ya koma gida gashi bega Fatima ba be kuma samu number tata ba balle ya kirata. Yasan bashida matsala ko kaɗan da Momy, Besan ya ze tunkari Alhaji da zancen aure ba yanzu dukda yasan abu me me wahala ace Alhaji ze hanashi Auran koma wacece ya kawo tunda ya bari an auri me rangwamen Asali ma ai baze hanashi Auran Fatima ba. Ranar kwana yayi yana saƙa ta inda ze fara, ze gayawa Momy sannan ze nemi shawarar Jafar su biyun sune manyan Abokanansa kuma duk shawarar da suka bashi yasan zata bulle masa. Sha biyun dare ta haura amma haka ya dannawa Jafar kira, Macece ta ɗauki wayar cikin harshen turanci ta sanar masa Jafar ɗin yana wanka amma karyewar harshenta ya tabbatar da ba Asalin Baturiya bace tana da wani yaren daya fi zama a harahenta sosai, yana jiyo tsawar da Jafar ɗin ya buga mata akan me yasa zata amsa masa waya. "I'm sorry Yah Ahmad and wlh ba abinda kake tunani bane, she is only a friend tayi visiting ɗinane and she is leaving now" Jafar ya faɗa bayan daya karɓi wayar a hannunta. Ahmad ya sauke numfashi irin na disappointment kafin yace "Nidai bazan gaji da tuna maka kaji tsoron Allah ba, karka bari ɗaukaka ta saka ka manta wanda yayi maka komai ka kuma saka masa ta hanyar saɓa masa da aikata abubuwan da yayi hani dasu sannnan Jafar ka sani Zina bashi ce, muna da ƙanne Mata, zamuyi aure mu haifi Yaya karkayi abinda zaka janyowa Yaranmu da basuji ba basu gani ba su biya bashin da basu suka aikata ba, i called you to discuss something important but since you are busy may be we takl about it some other time" yana gama faɗar haka be jira ta bakin Jafar ɗin ba ya kashe wayarsa ransa duk babu daɗi. Ya sani a ƙadamin da Jafar yake ko be nemi Mata ba Mata zasu nemeshi, koshi da be kaishi Ɗaukaka da samun suna ba a yanzu fama yake da Mata masu binsa ƙafa da ƙafa da sunan so wasu kai tsaye suke faɗin ko ba aurensu zeyi na su ƙulla Alaƙa kawai, balle Jafar dake tsakiyar Mata kala kala na kowacce yare da ƙabila wanda kowa ze so ace yana da Alaƙa dashi. ya rasa irin lalacewar da zamani yayi yanzu Maza sun dena neman Mata da fasiƙanci Matan ne suke kai kansu da kansu wasu dan neman abin duniya wasu kuma ka rasa ma me suke nema domin idan kuɗi ne suna dashi kai Allah yasa mu dace kawai. Yanajin wayarsa tana ƙara, Jafar ne haƙuri kuma ze bashi to amma idan ya aikata abinda yake guje masan ai bashi ze bawa haƙuri ba Allahn sa daya batawa ze nemi gafararsa. Jafar daya gaji da kira ya turo masa Text message yana cewa "Wallahi Allah Yah Ahmad i have never cross any girls boundary, only kiss and some fore play, shima zan dena in sha Allahu". "Oh zaka dena bama ka dena bako? Duk zina sunanta Zina babba ko ƙarama, Jafar live your life as you want it ban hanaka na ina sauke haƙƙi ne a matsayina na ɗan uwanka shi yasa nake tunatar dakai abinda yake daidai da ba daidai ba" ya turawa Jafar ɗin. Jafar ya karanta saƙon duk hankalinsa ya tashi bama komai yake ganewa ba kuma iyakar Gaskiyarsa yake faɗawa Ahmad ɗin, yana ƙoƙari gurin kama kansa shiyasa ko Budurwa bayayi just friends dan karma shauƙin soyayya yasa ya manta Morals nasa ba irin tarkon da Mata basa haɗa masa yasan Allah ne yake kareshi har cewa akeyi ko Gay ne shi saboda baua harkar Mata wannan tasa a shirmensa saboda ya kori sharrin da ake nema a laƙa masa ya fara ɗan biyewa Matan suna dan Romance shima bada kowacce ba saboda he is very selective when it comes to Mace, yana da ƙyama kuma sosai dan haka bada kowa ze iya haɗa jiki ba balle wani abu ya shiga tsakaninsu. Duk rantse rantse da magiyar Ahamd ya ɗaga waya beci galaba ba haka ya haƙura shi kuma Ahmad ya masa hakane saboda ya ƙara nisantar abinda bashi da kyau saboda yasan baya son fushinsa, idan ka cire Hajiya Ahmad ne mutum na biyu da yake jin maganarsa ya kumayi abinda yace masa with out second thought dan yama fi jin Maganar Ahmad ɗin akan ta Hajiyar dan ita sakin layinta yayi yawa wani abun idan ta gaya masa sedai kawai yace mata toh amma bazeyi ba saboda ba abu bane me kyau. Washe gari ya samu Momy da maganar, tayi murna sosai ta kuma yi Addu'ar Allah ya tabbatar da Alkhairi. "Banda abin Mahaifinta Talauci se yasa ka kasa auran yarsa se kace kai ɗin ƙaeuna ne ya haifeka? Wannan ba wata matsala bace ka samu Alhajin ka gaya masa" "Momy aike zaki gaya masa" ya faɗa yana langwaɓe mata, ta harare shi tace "Har se yaushe zaka fara tun karar mahaifinka kana magana dashi? Sanda ka sameshi kan maganar Fili cizonka yayi ko duka? Aure fa zakayi idan baka shirya ba ai shikenan karka gaya masa". Duk magiyarsa Momyn tayi rantsuwa akan ba zata gayawa Alhaji ba ya sameshi da kansa. Ba samun Alhajin ne baze iya ba domin akan Fatima ya shirya tunkarar kowa sedai tsoro da taraddadin amsar da Alhajin zw bashi wadda ba lallai tayi daidai da muradinsa ba shi yasa yake shakkar samunsa. Da kunnensa wata rana bayan Mahaifin Hajiya Rabi yazo Masa Maular daya saba zuwa da farar safiya ya sallameshi ya tafi, yana tsaye daga bayan Alhajin ya jiyoshi yana magana shi kaɗai yana cewa Da ace yana da damar maida hannun Agogo baya da be auri yar wannan mutumin ba, me za'ayi da Auren Talaka? Baze bari wani cikin yayansa ya maimaita kuskuren da yayi ba to amma tsakanin Mahaifin Hajiya Rabi dana Fatima ai akwai banbanci. Mahaifin Fatima nada Sa'arsa kuma ya tabbatar ko bashida ita kamalarsa ta wuce ace ya ringa zuwa gidan Siriki Maula amma Mahaifin Anty Rabi fa? Dama ai Alhajin ya sanshi yasan sana'arsa ce roƙo kuma da biyu ya masa tayin auran yarsa shi ma ya kasa haɗiye kwaɗayinsa ya aura gashi yanzun ya addabeshi Farar Asuba idan ta raya masa ze wanko ƙafa yazo gidan yau yace sun tashi basu da abinda zasu ci gobe yace wani cikin Yaransa bashida lafiya yana neman na kaishi Asibiti da siyan magani bayan duk watan duniya ko bezo ba Alhajin zeyi masa aiken kuɗi dana Kayan abinci, ita kanta Hajiya Rabin duk a ƙoƙarin kare mutuncin kanta dana Iyayen nata kome ta samu kai musu takeyi amma dukda haka bata tsira ba zuciyar Mahaifin nata ta rigada ta mutu da roƙo da banbaɗanci idan beyi ba baya taɓa jin daɗi. *ALBISHIRINKU MATA YAN UWANA YAN KWALISA NAZO MUKU DA WANI DADDADAN LABARI!!!.* *NASAN KUNDADE KUNA NEMAN FITACCEN GURIN DAZAKUJE AMUKU GYARAN GASHINKU DANA JIKINKU CIKI DA WAJENSA,TO YANXU DAI GA DAMA TA SAMU...* *LABARI NAKE BAKUFA AKAN AFINTY QUEENS SHAHARARREN SHAGONMU NA SALOON DAYA HADA KOMAI DA KOMAI DA KOWACE MACE YAR KWALISA IRINA KE BUKATA,SANNAN MUNADA KWARARRUN MA'AIKATAN DASUKASAN KAN AIKINKINSU,KUZO AFINTY QUEENS KUBIYA KUDI MUKUMA MU BATA LOKACINMU DOMIN TSATSTSAFO DUK WANI KYAWU NA JIKINKU DA ALLAH YAYI MUKU...* *A AFINTY QUEENS MUNA AYYUKA KAMAR HAKA:* *- HAIR SALOON* *-HENNA* *-SPA* *-DUKKAN* *-PEDICURE* *-MANICURE* *-SANNAN MUNA DA TURARUKA IRIN NA AMARE YAN MATA DA KUMA MAI KANKAT DAN UWAR GIDA TA TURARA GIDANTA JIKINTA DAMA KAYAN SAWARTA ITA DA YARANTA,,HARMA ZAWARAWA DUK MUN TANADI KOMAI* *DOMINSU SUMA* *-MUNADA SHOES AND BAGS SBD ISASSUN MATAN DA SUKA AMSA SUNANSU MATA*😊 *- MAKEUP NA BRIDAL ND CASUAL...* *IDAN KINSAN KINAJIN LABARIN SHAGON SALOON NA AFINTY QUEENS AMMA BAKI TABBATAR DA YADDA AIKINSU YAKE BA TO YAR UWA GADAMA TASAMU MEZAKI TSAYA JIRA MAZA KEMA KI ZARGAYO SHAGONMU DAZAN JERA MIKI ADDRESS DINSHI A KASA DOMIN KEMA KI TABBATAR DA KALAR IRIN NAMU KWAZON DA MUKA KWARE AKANSHI GURIN GYARAN JIKIN YAN UWANMU MATA KUMA MUKE GABATAR MUSU DA JAKUNKUNA DA TAKALMA HARMA DA TURARUKAN WUTA DANA SHAFAMA JIKINSU DON NISHADIN ZUCIYARSU DANA MAZAJENSU....* *AFINTY QUEENS DISCOVER BLISS IN BEAUTY 💅💯* *Address 👇👇:* *KU ZIYARCE MU A SHOP NO.9&10 SHEMA PLAZA,BEHIND SHEMA FILLING STATION KASUWAN BACCI KADUNA* *TEL:08133379628.* *MATAR MUTUM* *NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER* *FIKRA WRITERS ASSOCIATION* *LITTAFIN KUDI NE* *PAY 500 A ASUSUN* *7061838488* *OPAY DIGITAL SERVICES* *MARYAM FAROUK* OR *0709290797* *ACCESS BANK* *SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488* *IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705* *Kuyi following dina a Arewabooks @Maryamfarouk01 inda zaku karanta wannan littafin tareda sauran littattafaina* *NAGODE* *BOOK 2* *PAGE 6* Duk Ahmad ya rasa me zeyi, Jafar ne last hope ɗinsa shi kuma kwana biyu yana fushi da shi, seda aka kwana uku da wancan abun kafin ya sakko ya kulashi bayan ya tabbatar masa ya sallami yarinyar da yace daga Spain taje gurinsa, wai Model ce kuma Actress sonshi takeyi kamar me zuwan tama be sani ba Abokinsa ne yayi setting komai kawai dawowa yayi daga field ya ganta a apartment ɗinsa, baya so ya wulaƙantata shiyasa ya barta tayi kwana biyu ya sallameta amma haka ba zata sake faruwa ba. Shima Ahmad ya gaya masa maganar Fatima data Mahaifinta Jafar ɗin yace "Amma Yah Ahmad duk matan da suke Kano ka rasa wa zaka so se Daughter Mechanic? Yar Talaka For heaven sake me take dashi? Sannan har Babanta ya zauna ya gaya maka wasu magana haka se kace ze baka Gold, duk ina Babes ɗin da suke nacin sonka? Ina su Najiba Shaka, Ina Khulsum Galadima yarinyar nan loves you dearly kuma dai duk abinda zaka nema gurin matar Aure tana dashi hankali har yayi mata yawa plus akwai zumunchi tsakaninku and if ba ita ba why not Zahidah Ab..." 'Jafar! Fatima nake so ba wata ba kuma a gurina tafi duk waɗannan da kake jerowa yanzun. What is wrong with her father been a Mechanic? Kanikanci ba sana'a bane? Talauci Fasadi ne? Karka shiga layin da bansanka akai ba kaima ka shiga sahun irin waɗanda suke kyamar wani Abokin Halitta saboda fifikon Arziƙi, idan na samu matsala daga kai i will loose hope dan nasan sauran ma babu me goyamun baya so please Jafar mu ajiye maganar Matsayi ko sana'ar Mahaifinta mu fuskanci ta yanda zan samu amincewar Alhaji akan maganar nan" Ahmad ya dakatar da Jafar. Daga can ɓangaren Jafar ya fesar da iska daga bakinsa he can't believe simplicity irin na Yaya Ahmad har ya kaishi ga faɗawa soyayya da yar me gyaran Mota, Mechanic fa Yah Ilahi wace irin yarinya ce har haka da ta saka Ahmad ya manta waye shi ya manta gidan daya fito zece ita yake so?" "Kayi shiru ko baka da abinda zaka faɗa mun?" Ahmad ya sake magana jin bece komai ba se sannan Jafar ɗin yace "Gaskiya Yah Ahmad nidai idan shawara kake nema a gurina i will say just late that girl go, karka saka kanka matsala itama ka sakata. Iyakar problem ɗin gidanmu ya isa, kana kallon Maman Mu'allim ban sani ko yanzu ba amma sanda nake gida nasan rana daɗɗayane batayin kuka saboda abinda take gani a cikin gidan nan and sauƙinta ma is because Alhaji yana sonta I'm sure shiyasa takai yanzu a gidan nan. Look at Anty Mardiyya ko cikin Co Inlaws ba kowanne taro take iya zuwa ba because of the humiliation she faced, haka kake so itama matarka ta tashi ana wareta kullum ana zaginta?" "I'm different from Alhaji And Yaya Naziru, babu wanda ya isa ya wulaƙanta matar Aure na na ɗaga masa ƙafa suma su suka bada damar da ake raina matansu kuma ni ba zan zama irin su ba" "Zakayita faɗa da yan uwanka kenan saboda matarka?" "Bazanyi faɗa da kowa ba kuma bazan bayar da hanyar da kowa ze taka matata ba, look Jafar duk ba wannan ta saka na kiraka ba, I have already made my mind so no going back. Nayi magana da Momy ta saka mun Albarka akan maganar i wanted her to talk to Alhaji about it amma tace ba zatayi ba nina sameshi na masa magana kuma ni bansan ta inda zan fara ba, idan yace Aa bansan ta yaya zan roƙeshi ba shiyasa nake so kai kayi masa maganar Dan Allah" Ahmad ya faɗa cikin sigar roƙo. Yanzu fa kake cewa ka shirya facing kowanne challenge amma kace ba zaka iya yiwa Alhaji Maganarta ba kaga kenan kaida kanka kasan maganar bame yuwuwa bace Alhaji baze karɓeta ba, kuma ni yanzu da kake so nayi masa magana idan nayi and it turns out Negative response nasan ni zaka ɗorawa laifi saboda na nuna maganar batayi mun ba, kayi haƙuri for the fist time bazan iya maka abinda kake so ba, kamar yanda Momy tace ka sameshi da kanka, Yah Ahmad is high time you stand for your self. Alhaji fa ba Dodo bane bare ka ce tsoronsa kake ji, go meet him ka gaya masa buƙatarka but it should be you and him alone, karka bari maganar nan ta fita asan wa kake nema, Allah ya bada sa'a but i will pray you change your mind kafin ka sameshi because magana ta Allah banji yarinyar tayi mun ba" matsayar Jafar akan zancen Fatima kenan. A karon farko Ahmad yayiwa wani mutum ƙarya, ya kasa samun Alhajinsu da maganar se kawai ya yanke komawa gidansu Fatima ya kuma tabbatarwa da Mahaifinta yayi magana da nasa Iyayen kuma sun yarje masa daya nemi auranta. A zuciyarsa ya tabbatar Allah baze bashi kunya ba tunda Aure yake so yayi ba wani mugun abu ba, kafin sanda zasu buƙaci ya turo ze san yanda zeyi da Alhaji, idan ma bashi ba Baba Alƙali ze kaiwa maganar Auransa kawai. "Amma da akwai magana guda, Mamana Karatu takeyi, ta ƙare shekarar farko zasu shiga ta biyu yanzu suna hutu ne saura yan kwanaki su koma A can Jami'ar Zaria take Karatun" Malam Hafizu ya faɗa masa. Ahmad dake durƙushe yana faman sunne kai yace "Babu komai Baffa, gidanmu gidan Karatu ne. Idan Allah ya nufa zamuyi aure Fatima tana cikin makaranta bbau damuwa zanyi duk abinda ya kamata gurin ganin bata takura ba ko Karatunta be samu matsala ba, sannan idan ta zaɓi har seta kammala kafin muyi Aure zan iya haƙuri na jira lokacin, fatana kawai na samu Amincewarta da taku" "Allah ya shige mana gaba ya sa a ƙulla Alkhairi, bari na shiga ciki na turo maka ita" cewar Malam Hafizu daga nan ya shige gida. Tun zuwan Ahmad na farko Malam ɗin ya sanarda ita daya wassafa mata kamaninsa ta ganeshi tunda ba sanin sunansa tayi ba. A lokacin ji tayi kamar tacewa Baffan nata ya sallameshi kawai yace ya mata Miji, tsakani da Allah be mata ba, kuma ita da wanne ido ma zata sake kallonsa bayan wancan abinda ya faru shi ma ya zeyi mata haka ya dawo? Dataji shiru be kirata a waya ba ta zata ya janza shawarane ashe shi me gaba ɗaya ya shirya mata biyowa ta hannun Baffa. Tana jin yanda Baffan yake ta yabon Kamalarsa da hankalinsa sannan ya gayawa Umma yanda sukayi da abinda yace masa, Jiki a sanyaye ta fita, Dogon Hijabin datayi sallah dashi ne a jikinta, bata tsaya gyara fuska ba balle akai ga fesa turare ko sauran Al'adu da yammata sukeyi idan zasu fita hira haka ziƙau ɗinta ta fita abinka kuma da jiki kalar Madara a hakan ma tayi kyau abinta. A cikin gida kuwa bayan fitar Fatima Umma tayi jugum kafin ta kalli Malam tace "Ban tsammaci yaron nan ze dawo ba, Anya kuwa Malam ba'a yi ɗage da yawa ba? Ɗan gidan Alhaji Audu Bechi yazo neman Auran Afeeya, wannan fa ba irin Mijin Yayarsu bane idan ma ana maganar masu Arziƙi irinsu Alhaji Audu a ƙasar nan Sirikin Saudatu inaga ai ko gurin baze leƙa ba, gaskiya ni koda da sahalewar Iyayensa ba zanso wannan Auran ba, Malam kafa san irin zamanin da muke ciki yanda Aure ya zama ƙwarya tabi ƙwarya duk kuma wadda tayi kuskuren faɗawa gurbin da ba nata ba zata fusakanci ƙalubale" Ki kyautata zato ki kumayi Addu'a Allah ya zaɓa mata binda yafi zama Alkhairi, sannan ki tuna shi yaga Afeeya yace yana sonta bawai tura masa ita akayi ba, Nutsuwa da Kamalar yaron ta burgeni idan har Allah ya zaɓa matashi a matsayin miji zanyi mata murna kwarai dan daga ganinsa mutumin kirki ne" inji Baffa. Umma ta nisa tace "Toh, Allah ya zaɓa mafi Alkhairi amma dai Alhaji Audu Bechi fa.." "Ai kingama magana tunda kika miƙawa Allah zaɓi sedai mu zuba ido muci gaba da Addu'a kawai" Baffan ya sake tareta. Seda Fatima tafi minti biyar tsaye a soro kafin ta hada courage ta fita, wata irin kunya da nauyin sake haɗa ido dashi takeji tasan yana ganinta wancan abun ne zero faɗo masa a rai, da dai taga babu sarki se Allah yasa ta fitan, Ahmad na jingine jikin katanga ta raɓe gefensa tana yar siririyar sallama kai a ƙasa tamkar wadda ya kama tana gulmarsa. Murmushinsa me kyau yayi ya amsa mata sallamar kafin ya tsaya dakyau yana fuskantarta, har sannan kanta a ƙasa murya a sanyaye ta gaidashi "Hajiya Fatima, se yanzu sarautar ta sakeki kenan har ina shirin na ƙaraso soron na taroki ai" ya faɗa cikin raha. Bata tanka ba haka nan bata ɗago kanta ba, ya waiwaya ya kalli Dakalin gurin kafin ya kalli mutanen da suke wucewa kamar an basu gadi duk wanda yazo seya zura musu ido sannan ya wuce se ya kalleta yace "Mu zauna a nan ko mu tsaya cikin soron?" "Bari na kawo maka abin zama" ta faɗa kafin ta juya cikin gidan ranta babu daɗi, shi gurin zama ma yake nema, ita data fita da niyyar su ƙarƙare kuma yana neman yaja maganar da tsayi. Kujerun roba ta kawo guda biyu ta saka a Soron ta koma ta dauko pure water da Zobon da Ummansu take siyarwa ta haɗo masa da ƙaramin kofi dukda bata da tabbacin zesha. Seda ta aje komai kafin tace ya shigo, yana ta doka murmushi kamar sabon Ango ya zauna, kallonta kaɗai nishaɗi yake bashi musamman yanda take sunne kai yasan meye dalilinta naƙin haɗa ido dashi amma a ganinsa wannan ai ua wuce, banda abinta idan Allah yayi wata rana na jikinta ma ai wanke mata zeyi balle gurin da ta ɓata. A taƙaice yayi mata bayanin kansa da dalilinsa na zuwa gurinta. "Kema se ki bani taƙaitaccen bayani akanki" ya faɗa yana ƙarewa fuskarta kallo. Kyakykyawace Masha Allah komai na fuskarta ɗan daidai hasken fatarta kuma ya ƙara ƙawata kyan nata, tana da tsayi dan ko ze fita da kaɗan ne sannan ba ramammiya bace kuma bata da ƙiba, baze iya ƙiyasta shekarunta ba saboda suffarta irin wadda bata nuna shekaru ce, se kayi wa mutum kallon yaron idan kaji ainihin shekarunsa kuma kayi mamaki. Yanayin zubin jiki da fuskarta yafi kama dana Jajayen Buzayen Niger ko kuma Fulanin Mambila, sannan daga yanayin goshinta ya fahimci tana da kufar gashi, kuma irin me Laushin nan dan gashin goshin nata a kwance yake luf kamar na Jariri sabuwar haihuwa gashi baƙi siɗik. "To ai kasan sunana Fatima kuma nan ne gidanmu" maganarta ta maido shi daga tunanin daya tafi. Ya saki murmushi, jan Ajin nata ya fara yawa, ya zata kuma tunda har yaga mahaifinta kuma zata ɗan sake masa tasan dai bada wasa yake yi ba. Ya gyara zama yace "Nasan sunanki Fatima kuma naga gidanku amma ai ni ba iyakar abinda na faɗa miki a kaina ba kenan, na gaya miki mena karanta, aikina har adadin yan gidanmu da wanda nafi so seda na gaya miki fa" Tayi shiru tana jinsa, idanun daya zuba mata su sukafi damunta da alamu kuma idan ba magana tayi ba baze dena kallonta kamar ze hango yan cikinta ba dan haka tace "To ai ni banida wani abu da zan gaya maka ne, amma dai kamar yanda nace maka nan ne gidanmu, mu uku ne ai kaga Anty Sauda itace babbarmu se Yah Malam.." "Jafar? wanda yayi mun sallama da Baffa?" Ya katseta, kai ta ɗaga masa kafin taci gaba da cewa "Shi nake bimawa, ni kuma banida ƙani ko ƙanwa, ina makaranta a Zaria Level two zan shiga ina karantar English Literature, bayan Baffa da Umma dasu Anty Sauda Ina da Best Friend Badar i think iyakar abinda kake buƙatar sani akaina kenan" ta ƙarasa tana yamutsa baki. "Masha Allah ku uku kacal a gidanku kenan, ashe ke ɗin Autace shiyasa shagwaɓarki tayi yawa, shekarar ki nawa toh" "20" ta bashi amsa a gajarce tana ci gaba da murza zoben hannunta. Sukayi jugum shi yana kallonta ita kuma tana faman juya Zobe, wayarsa dake Aljihuce ta katse musu shirun ya cirota ya duba, Jafar ne yake kiransa, ya nuna mata screen ɗin wayar yana cewa "Jafar ne yake kirana". Tankar wadda take zaune akan ƙaya ta miƙe da sauri tace "Ka amsa toh, bari naje ciki kafin ka gama". Kallonta yayi kaɗan ya kasa fassara yanayinta amma dai kamar she is not comfortable with him, ya mata uzurin haɗuwar farko ne dan haka ya miƙe shima yana laluba Aljihubsa yace "Ai inaga zan wuce kawai idan naje gida se na kirashi wayarmu bata yankewa da wuri ga dare ma ya farayi karna zaunar dake a waje" Kuɗi ya zaro masu yawa daga Aljihun nasa ya miƙa mata yana cewa "Kinsan farin shigan zuwa hira ne ni, bansan me akw tafiya dashi zance ba kiyi haƙuri ga wanan kisha Sweet kafin na sake zuwa" "Nagode" ta faɗa ba tareda ta karbi kuɗin ba se wani kallo da ta musu ta ɗauke kai kamar taga wani abunda bata so. Wayarsa ya sake miƙa mata uace ta saka masa Number ta wancan ta goge, nan ma seda taji jum sannan ta karba, ta saka number ta mayar masa. Akan kujerar data tashi ya ajiye mata kuɗin ya juya yana cewa "Zan kiraki idan na isa gida se kiyi saving number ta. Ki gaida Umma, se na sake dawowa" Ganin ta tsaya kamar wata sokuwa kawai tana kallonsa yasa yayi murmushi ya fice daga soron yanajin wayarsa nata ƙara yasan Jafar ne bala'in wutar ciki ne dashi yanzu idan ba ɗauka yayi ba ya ringa kira kenan ga Mita kamar Mace. Jiki babu ƙwari ta haɗe kujerun ta ɗauke farantin ruwan da be ko taɓa ba daman tasan ba sha zeyi ba Umma ce tace ta kai masa. Iyayen nata na yar hirarsu ta shiga. Seda ta ajiye kujerun a mazauninsu kafin ta isa gaban Baffa ta Zube kuɗin da Ahmad ya bata. "Wannan fa?" Baffan ya tambayeta yana kallon kuɗin, a sanyaye tace "Shi ya bani wai bezo da komai ba danaƙi karɓa shine ya ajiye akan Kujera ya tafi" "Toh madallah amma idan ya sake dawowa ki gaya masa na hana karki Ƙara karɓan kuɗinsa" Baffan ya faɗa ta amsa da "Toh Baffa" kafin ta miƙe tsaye zata wuvmce yace mata "Kwashe kije dasu ai ke aka bawa" "Ni babu abinda zanyi dasu Baffa" ta bashi amsa tana juyawa. "Zo nan Mamana, me yake damunki? Ko wani abu yayi miki?" Baffan ya sake dakatar da ita saboda lura da yanayinta sam ba daidai take ba, murmushi ta ƙaƙalo tace "Babu komai Baffa kaina ne yake sarawa zanje na ƙarasa shirya kayana sena kwanta" "Toh Allah ya sawwaƙa ki samu magani kisha kafin ki kwanta ɗin idan be dena ba da safe se kije Asibiti, sannu ko" Baffa ya faɗa cikin tausayawa. Seda ta shige sannan Umma ta gaya masa abinda take zaton shine sikar tsumewar Fatima. Yayi murmushi yace "Ina ruwan Mamana, wato kunya ce duk ta dabaibayeta, to ya za'ayi abu ya rigada ya faru ta yuwu ma ya manta idan kuma ya ganota ya samu abin tsokanarta ai" tana jiyo Baffan daga ɗakiz harta hasaso Ahmad ya dawo da zancen ai lumewa zatayi a ƙasa kawai ta huta. Harta bacci ya fara fizgarta wayarta ta tayar da ita, Data ta a buɗe yake dan haka taga sunan Ahmad Bechi a truecaller, kamar ba zata ɗauka ba se kuma zuciyarta ta kwabeta kan wulaƙanci babu kyau. "Allah yasa ban tasheki a barci ba" ya faɗa bayan data amsa wayar, cikin muryar da bacci ya fara tasiri a cikinta tace masa "Aa". Ahmad ya gyara kwanciya akan Gadonsa, tunda ya shiga gida suke waya da Jafar daya kai masa ƙarar Hajiya wai ta kirashi akan seya Rantawa Faisal Kuɗi ze fara harkar Crypto kuɗaɗe kuma ba Ƙanana ba take cewa ya bashi ita lissafin Ribar da Faisal ɗin yace mata kawai za'a samu takeyi bata hango Risk da yake tattare da sabgar ba kuma wai rance bama kyauta take nufi harda bashi zuwa lokacin da ze turo kuɗin shine ya kawowa Ahmad ƙararta ita da Faisal ɗin se kace ze iya masa wani abu akai be samu sun gama maganar ba se yanzun yana ta Allah Allah kar tayi bacci ba suyi magana ba. "Kara zakiyi mun amma muryarki ta fallasaki, kiyi baccinki toh in Allah ya kaimu da safe sena kiraki ƙarfe nawa kike tashi daga bacci?" "Ko yaushe ma" ta bashi amsa cikin ƙaguwa, ya fiya tambaya take ayyanawa a ranta. Ahmad naso suyi hira dan so yake ta sake dashi da sauri amma kuma bayaso ya shiga haƙƙinta dan haka ya mata sallama akan ze kira da safe dukda bata gaya masa sanda take tashi ba ya kuma jaddada mata kan tayi saving number sa. Tsaki tayi bayan ta kashe wayar baccin data fara ya gudu se ta shige WhatsApp tana duba saƙonni kafin baccin ya dawo. Dm na samari gasu nan babu Adadi unread messages ɗinta sunfi dari duk ta tsallake ta wuce kan number Badar dataga ta mata magana da ita suke hira daman baccin ya kwasheta. "Al'amin yace inya kiraki wayar bata shiga, a WhatsApp kuma baki buɗe chat ɗinsa me yasa?" "Blocking ɗinsa nayi" ta bawa Badar ɗin amsa ganin tana online. Tana turawa kuwa ta buɗe ta shiga yi mata voice. "Kina kuwa yanda ya gigice Afee zuwansa fa gidan nan biyu yau wlh se in kira masa ke a wayata na kira kuma bata shigo ba lokacin wai me ya haɗaku ne? Dan Allah ki tausayawa guy ɗin nan wlh Al'amin yana sonki sosai fa" cewar Badar. "Uhm duk ya gama haukansa can ya nemi daidai shi a gaba, wai ni Badar shikenan Namiji baze so ni saboda Allah ba se dan wata buƙata ta daban? Ki faɗamun tsakaninki da Allah ko da akwai wani abu da nakeyi mara kyau da yake Attracting yan iskan Maza zuwa gareni? Ni kenan duk wanda zece yana sona seya nemeni da lakata me nakeyi daya sa suke mun kallon Mara kamun kai Badar?" Fatiman ta mayar mata da Voice note muryarta na rawa kamar zata fashe da kuka saboda zafin abinda take ji a ranta. Allah ya mata farin jini bana wasa ba, bata taɓa fita ta dawo gida Namiji be tsaidata ko an biyota gida ba amma duk wanda ta kula take ganin kamar zasu samu daidaito da tafiya ta fara nisa se ya kauce layi ya shigo mata da wani zancen na daban. Tun abin baya damunta har yazo ya fara bata tsoro ta yaya za'ayi ace duk wanda yazo yana sonta seya nemi ya taɓa jikinta se kace ita kaɗaice Mace a duniya ko kuwa duk suma sauran Matan haka ake musu?? "Na gaya miki Afee wannan matsalar fa bake kaɗai ta shafa ba, abinda yasa kuke mun kallon Masifaffiya kenan na kasa tsaida saurayi ko ɗaya saboda ni bana iya shiru, mutum na zuwar mun da shirme a take nake tsigaleshi gara nayita zama single dina har Allah ya kawomun Mijin Aure na na gaske, ke kuma duk wanda yazo miki da suffar Salihai seki saki jiki se mutum ya nuna miki true color kizo kina ciwon rai kenan shima Al'amin ɗin shegene da gemunsa kamar Na Allah ai da kin gayamun da wuri wlh da daya zo ɗazun sena wulaƙantashi dan iska shege me ci da buguzun da fuskar Salihai" Badar ta hau spark daga nan suka cigaba da tattauna abinda yake damunsu ya kuma zama ruwan dare a zamanin nan. Samari sun zama abinda suka zama kawai, sun maida mata tamkar wasu Takalma da zasu ce se sun gwada sun samu wanda yayi musu daidai kafin su siya a irin haka waɗansu da ƙadda take hawa da wanda suke kasa jure jarabawar ubangiji yayi musu suga kamar idan Saurayin ya gudu ba zasu samu wani ba se su bayar da kai bori ua hau wanda daman samarin yan latsine da sun samu abinda ya kawosu su fece shikenan se a shiga lahaula da Innalillahi Allah ya rufa asiri. Soyayya ta ƙullu tsakanin Fatima da Ahmad ko ace farashin soyayya nata hauhawa a zuciyar Ahmad domin abinda yakeyi yafi kama da One sided Love sedai ya kasa fahimtar hakan. Kwana uku tsakanin zuwansa na farko ya sake komawa daga nan kuma ya mayar da zuwan nasa sau biyu a sati bayan nan kuma kullum a ƙalla ze kirata waya sau uku yaji ya take, kulawa da tattali duk irin wadda yasan zata farauto masa da zuciyarta yana mata amma ko a jikinta shan ƙamshin nan ma ƙaruwa yake ko a waya idan suna magana yanayin da take amsawa tamkar bata so amsarta bata wuce Eh ko Aa shi zeyita zuba surutu inya gaji yace tana jinsa tace Wh bata da abin cewa ne shi yasa tayi shiru hakan kuma yake jurewa baya fushi yana cigaba da lallaɓata. A cikin haka suka koma makaranta wanda taji daɗin hakan sosai saboda ko babu komai zata huta da zuwan da yakeyi sannan zata samu uzurin da zata ringa gujewa wayarsa yanzu dan a gida Idan ya kira Umma data fahimci Ahmad ɗin be samu karɓuwa gurin Fatiman ba ita take takura mata tayi ta mata faɗa idan ta bar wayar tana ƙara ko yazo ta tsaya nuƙu nuƙu taƙi fita. Ta kance mata wulaƙanci babu kyau, bata san abinda Allah ya tsara ba kuma ita bataga makusarsa ba da zatace beyi mata ba dan a zuwansa na biyu ya shiga har ciki ya gaidata itama data ganshi ta fahimci nutsuwa da Kamalar da Malam yace yana da ita. Yaro ne amma Allah ya hore masa nutsuwa da dattako daya zarce shekarunsa kuma duk wasu iyaye na kwarai tabbas zasuyiwa Yarsu sha'awar samun Miji me kulawa tamkar Ahmad ɗin. Bayan sun koma makaranta haka zeyita kiranta ba zata ɗaga ba, tun su Badar basu sanda Ahmad ba dan bata gaya musu ba har suka gane dalili wata raba ya kirata tana sallah Badar ta amsa wayar suka gaisa ya kama sunanta shikenan hira ta ɓarke, Fatima bata so ba domin muddin Ahmad yayiwa Badar tasan ta shiga uku, takura kam ko ruwa me daɗi ba zata barta tasha a dalilin Ahmad ba shiyasa take ta ɓoyewa gashi yanzu Badar ɗin ta ganoshi. "Dukda banga guy ɗin nan ba tun daga voice ɗinsa nasan ya haɗu, wato Afee kin iya catching Big Boys matsalar duk yan iska ne in disguise Allah yasa dai wannan na Allah ne dan wlh daga magana a waya harya burgeni yana da nutsuwa ga kirki, waye shi? A ina kuka haɗu" Badar ta tambayeta bayan ta gama waya da Ahmad ta bashi uzurin abinci zataci shi kuma ya shaida mata ze fita Jafar ne yazo ze ɗauko shi daga Airport. "Ya samu hutu ne shine yazo Gaisuwar Rasuwar Brigadier General Baballiya Bechi, ƙanin Alhajinmu sa sukayi Hatsarin jirgi last two weeks ai kinji labari ko?" Abinda ya gaya mata da duk ya saka taji kunya kenan. Sanda akayi rasuwar ta gani a SM, kuma anyita surutun a gari kan set up ne akayi musu ba wai Accident bane ba ance akwai wani sirri da suke shirin bankaɗawa na wata badaƙala data faru shine kafin nan masu laifin suka kawar dasu, tunda taga Bechin a ranta ta kawo yana da alaƙa da Ahmad kuma ta gani ya saka a Status harya tura mata cewar an masa rasuwa kunyar data ji yanzu irin gaisuwar da tayi masa ta "Allah ya jiƙan rai" kawai tace, babu wani sympathy babu nuna concern na cewar Kawunsa ne na kusa ya rasu tana ganin shiyasa yanzu yake gaya mata Jafar yazo dan tasan Mutuwar me muhimmanci ce a gurinsu tunda har na wata ƙasar ya taho ita kuwa ba wanda ta gayawa a gidansu ma balle ko a waya su masa gaisuwa. Hoton Ahmad kawai ta nemo ta miƙawa Badar data addabeta da waya, cikin Mamaki take kallonsa tace "Ahmad Bechi? Wlh Afee kinyi Miji kinsan kirkin mutumin nan kuwa?" "A ina kika sanshi?" Ta tambaya tana tsare Badar ɗin da ido wani abu da bata taɓa tsammatar zata jishi akan Ahmad ɗinba ya taso mata wato kishi. "A IG mana, ai ina following ɗinsa" b Badar ta bata amsa. Seta tsume fuska tace "Shine har kika san kirkinsa daga ganinsa a IG kuma" "Ai mutumin kirki baya ɓuya, kuma idan da kinsan yanda mutane suke yabonsa da bakiyi mamakin dan nace yana da kirki ba, kin san yanda yake taimako kuwa? Ke dai Allah yana sonki Afee, kinga ya canza miki da abinda yafi duk shegun da kika rasa Alkhairi wlh ki gode masa" "Allah ya saka mu a danshinku Afee, ke kam Allah ya taimakeki da jinin manyan mutane, Bechi Family fa?" Ilham roommate ɗinsu ta faɗa nan suka shiga hirar caaa caaa kowa na tofa Albarkacin bakinsa. Ahmad Ƙarfe biyu ya fita ɗakko Jay wanda suka samu delay na jirgi daga Abuja zuwa Kano, tun daren jiya ya sauka daga London, ya biyo jirgin Abj to Kn na sha biyu da rabi na rana basu taso ba se biyu da wasu mintina uku saura suka sauka a Kanon. Beyi mamaki daya kira Yah Ahmad yace masa already yana cikin Airport ɗin ba. Be taɓa barin sa yayi jira muddin yana gari shi ze zo ya ɗaukeshi kafin Jirginsu yayi Landing Ahmad ya isa Airport wani sa'ilin har Abujan yake zuwa ya taro shi su taho Kanon Tare. Cikin tsananin murna da ɗokin ganin juna suka rungume juna kowanne yana jin soyayyar ɗan uwansa na sake ratsa Jini da jijiyarsa. "Kullum ƙara girma kakeyi da fresh, look at you, idan muka jera za'ace kai Yayana ne na uku ma" Ahmad ya faɗa cikin zolaya yana kallon Jay daya ɓata fuska irin na sangartattun yara wai yace masa tsoho. Kuma da gaskiyar Ahmad ɗin, A tsaye Jay yake gansansan kamar ya haɗa jini da samudawa koda yake jinin Binta da Audu fa kowanne ba baya bane a garin jiki. Suna tafe suna hira gwanin sha'awa har suka isa gida. Hajiya na tsaka da shiri domin wannan karon ta rantse gayya zasuyi suje taro Jay ɗin se Kano gaba ɗaya ta san da ya dawo. Idan zezo gida babu wanda yake sani, ko a jirgi badda kama yakeyi saboda ya tsani irin taro da hargowar da mutane sukeyi duk sanda suka ganshi a cika guri ayita ihu ana ɗaukar hotuna dashi ayi blocking masu uzurirrika shiyasa kusan shekara biyar kenan ya canza salon zuwansa Nigeria, hatta da manager sa na nan wrong schedule yake bashi dan shi yake sanarwar Jay ɗin na tafe ya haɗa masa mutane shiyasa ya zaɓi boye zuwansa, Ahmad kaɗai yake gayawa se idan ya dawo a kwashi tsiya da tsiyataku da Hajjaju dan idan zezo Yau ce mata yakeyi se Jibi sedai ta ganshi kamar dirar kirsimeti. Zuwansa na ƙarshe waccen shekarar na buɗe Shagon Ahmad daman bata san da zancen ba ganinsa kawai tayi, ta zabga tijara ta kuma ce Alhaji yayi mata tsakani da Ahmad ya fita a sabgar Ɗanta, ta yaya za'ayi idan ba mugunta ba ya saka ya baro gurin sana'arsa dan yayi Asarar miliyoyin da ake biyansa? Ta kuma ce zancen Ahmad shi kaɗai ya ɗauko shi daga iyafot ya kau, duk in ze sake zuwa zuga za'ayi dangi da Abokanan arziƙi aje a taroshi jama'a su san yana da gata ba wai ace kamar shi sananne a duniya idan zezo gida ya ringa shigowa kamar Ɗan fashin da ake fako a kama. Shine dalilin daya saka ta haɗo Jama'a kenan dangi da Abokanan Arziƙi, jira takeyi ayi La'asar su ɗebi motoci a tafi Iyafot ɗauko Jafaru, yau ɗin har kwalliya taci, ta saka Sabuwar Atamfarta Super Sheraton, kusan shekarar ta uku a ɗinke, da siyanta kuma zatayi biyar ko Shida ta sallah ce da Alhaji yayi musu sauran da yuwuwa sun dade da bayar da tasu amma ita se Yau Allah ya nufa zata saka shima da fari wani Lace ta saka, sabone amma ajiya tasa ɗinkin ya fita a yayi, tun ana style me Umbrella da hannu me ɗorin Kafaɗa, ga wata uwar boader Lace da aka tattara a wuya da bakin Hannu, da ace Zallar Lace ɗin aka ɗinka mata ko ya shekara goma zata saka abinta dan babbane, Design ɗin Lace kuma baya tsufa sedai ɗinkin jikinsa ya nuna shekarunsa. Turai ce ta kalleta sanda ta fito ala dole ta ƙure gayu ga Sarƙar Zinare irin design ɗin Saudiyya damɓasheshiya ta sauka har kan ƙirjinta, jan hannunta Turai tayi da sauri suka koma ɗaki tana cewa "Haba Binta, yanzu saboda Allah da wannan shigar zaki tafi tarar Jafar ɗin se kace wadda ta fito daga riga? So kike ki ja masa abin magana a ɗauke ku hoto a yaɗa a a duniya duk suturunki keko ki rasa wanda zaki saka se wannan Matsiyacin Lace ɗin dan girman Allah ina zaki kai ubannin suturun da kike dasu ne?" Hajiya ta yamutsa fuska tana kallon Turai tace "Karki gaya mun mara daɗi mana, me Leshi na yayi? Ina a gurinki na siyeshi ko a lokacin ai ya haura ɗari balle yanzu indai ba cutata kikayi ba kuma" "Shekararki nawa da siyansa? Ni wlh har na manta da nayi irin Leshin nan bana zaton wadda na bawa ma har yanzu yana nan be zama tsumma ba, yanzu dai duk ba wannan surutun ba su Hajiya Rafi'a da Hajiya Zuwaira duk suna falo yanzu suka iso se kin raina kanki idan kikaga kwalliyarsu, yayayenau kansu da sukazo dasu bakiga yanda suka sha kwalliya ba se ke da ake taron saboda ke ce zaki fita a haka kamar mara kan gado dan Allah wuce ki sauya Kaya, ki nemo na mutunchi wannan rakwacam ɗin sarƙarma kiyiwa girman Allah ki tattarosu muje gurin Alhaji Mansur a narkasu, a maida miki ƙirar zamani". Badan taso ba shine ta canza da Atamfar dukda itan ma Turai tace ba tayi ba, gafa kayan nan a jibge amma ta bari ta zaɓa mata ma tace Aa, da babu gara babu daɗi Atamfar Ɗinkin doguwar rigane an mata Bead work a wuya da bakin hannun, Sarƙar ce dai tace ba zata cire ba, tilas Turai ta barta, a neman mayafi kuma aka tafka abin kunya dan Hajiya dai bata da Mayafin fita Taro, ƙarshe se a gurin Momy Turai taje da kanta ta Aro mata Jaka da Takalmi kuma aka samu a gurin Hajiya ƙarama. "Wlh Binta ki canza hali, wannan tsumulmula har ina? Kuɗi kina dasu kamar su kasheki amma ace ko jikinki ba zaki iya kashewa ba wannan wace irin rayuwa ce? Yanzu tsabagen zubar da ƙima Gyalen da zaki saka ki fita kunyar Ɗanki ma baki dashi se an aro a gurin kishiya wannan abin takaici har ina?" Turai ta dasa mata mita, Binta dake kiciniyar Rataya Jaka a hammata ta buɗe baki zata bata amsa suka jiyo ihun Yara ana oyoyo Uncle Jay, Hajiya ta zabura tayi waje dan ta tabbatar da abinda take jiyowa, Jafar ɗin da ta gama haɗa jama'a da motoci zasu tafi tarowa ko kuwa wani daban suke nufi???? *ALBISHIRINKU MATA YAN UWANA YAN KWALISA NAZO MUKU DA WANI DADDADAN LABARI!!!.* *NASAN KUNDADE KUNA NEMAN FITACCEN GURIN DAZAKUJE AMUKU GYARAN GASHINKU DANA JIKINKU CIKI DA WAJENSA,TO YANXU DAI GA DAMA TA SAMU...* *LABARI NAKE BAKUFA AKAN AFINTY QUEENS SHAHARARREN SHAGONMU NA SALOON DAYA HADA KOMAI DA KOMAI DA KOWACE MACE YAR KWALISA IRINA KE BUKATA,SANNAN MUNADA KWARARRUN MA'AIKATAN DASUKASAN KAN AIKINKINSU,KUZO AFINTY QUEENS KUBIYA KUDI MUKUMA MU BATA LOKACINMU DOMIN TSATSTSAFO DUK WANI KYAWU NA JIKINKU DA ALLAH YAYI MUKU...* *A AFINTY QUEENS MUNA AYYUKA KAMAR HAKA:* *- HAIR SALOON* *-HENNA* *-SPA* *-DUKKAN* *-PEDICURE* *-MANICURE* *-SANNAN MUNA DA TURARUKA IRIN NA AMARE YAN MATA DA KUMA MAI KANKAT DAN UWAR GIDA TA TURARA GIDANTA JIKINTA DAMA KAYAN SAWARTA ITA DA YARANTA,,HARMA ZAWARAWA DUK MUN TANADI KOMAI* *DOMINSU SUMA* *-MUNADA SHOES AND BAGS SBD ISASSUN MATAN DA SUKA AMSA SUNANSU MATA*😊 *- MAKEUP NA BRIDAL ND CASUAL...* *IDAN KINSAN KINAJIN LABARIN SHAGON SALOON NA AFINTY QUEENS AMMA BAKI TABBATAR DA YADDA AIKINSU YAKE BA TO YAR UWA GADAMA TASAMU MEZAKI TSAYA JIRA MAZA KEMA KI ZARGAYO SHAGONMU DAZAN JERA MIKI ADDRESS DINSHI A KASA DOMIN KEMA KI TABBATAR DA KALAR IRIN NAMU KWAZON DA MUKA KWARE AKANSHI GURIN GYARAN JIKIN YAN UWANMU MATA KUMA MUKE GABATAR MUSU DA JAKUNKUNA DA TAKALMA HARMA DA TURARUKAN WUTA DANA SHAFAMA JIKINSU DON NISHADIN ZUCIYARSU DANA MAZAJENSU....* *AFINTY QUEENS DISCOVER BLISS IN BEAUTY 💅💯* *Address 👇👇:* *KU ZIYARCE MU A SHOP NO.9&10 SHEMA PLAZA,BEHIND SHEMA FILLING STATION KASUWAN BACCI KADUNA* *TEL:08133379628.* *MATAR MUTUM* *NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER* *FIKRA WRITERS ASSOCIATION* *LITTAFIN KUDI NE* *PAY 500 A ASUSUN* *7061838488* *OPAY DIGITAL SERVICES* *MARYAM FAROUK* OR *0709290797* *ACCESS BANK* *SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488* *IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705* *Kuyi following dina a Arewabooks @Maryamfarouk01 inda zaku karanta wannan littafin tareda sauran littattafaina* *NAGODE* *BOOK 2* *PAGE 7* "Jafaru, ni uwarka ka yaudara wannan karon ma kace mun biyar na yamma jirginku ze sauka seda na gama tattara jama'a zamu tafi taronka mu nunawa Duniya gatanka shine zaka tozartani Ko La'asar bata rufa ba ka diro a gidannan wato ka sanar da Amadu shi da yake ƙanin ubanka yaje ya dauko ka ko?" Hajiya ta faɗa tana zarewa Jafar idanu. Sakin Yaran Yayyensa da suka ruƙunƙumeshi suna masa oyoyo yayi ya nufeta fuska ɗauke da murmushi cikin shagwaɓa yana cewa "Haba Hajiyata, dawowana lafiya ai shine komai yanzu, maimakon ki tareni da warm hug se ki farayi mun faɗa kuma?" "Ka matsoni sena kwasheka da mari wlh, kai kuma me kama da dido dido, sau nawa zan faɗa maka ka fita daga sabgar Jafaru? Shin wai Aisha ta haifamin shine ko Yaya? Nace ka fita daga sabgata data Yayana Amadu amma kaƙi kaji shin ana dolene? To kaji da kunnenka duk bala'i da tuggunku sedai ya ƙare muku amma babu tsafi ko Asirin da zeci Jafaru wlh balle har kuga ya samu nakasu. Ɗaukaka da cigaba a rayuwa yanzu ya fara ganinta duk nasan shirinku da liƙe masan da kakeyi ba wai ban sani ba Asirin da kayi ka lashe masa zuciya ma ina kan karyashi kuma idan na juyo takanka ba zaka ji da daɗi ba" "Haba Binta wannan wane irin abune kikeyi dan girman Allah? Meye amfanin wannan faɗe faɗen da kikeyi? Jafar dai gashi ya dawo lafiya me kuma kike da buƙata?" Turai ta katse Hajiya daga Hauragiyar da takeyi se kuwa ta zabga mata harara tace "Babu ruwanki Turai, idan ba zaki tayani ba to kija bakinki kiyi shiru" "Allah ya sawwaƙa miki, Sannu da zuwa kaji Jafar yi wucewarka can Ɗakinku, idan kuma zaka fara shiga ku gaisa da iyayenka da suka zo tarbarka toh, sannu da hanya" Hajiya Turai da bataji kashedo ba ta faɗa tana nunawa Jafar Palour Binta wanda jama'ar ciki sukayi shiru suna saurar abinda yake faruwa a wajen, Mutan gidan kuwa daman sun san za'a rina dan haka abin bezo musu a bazata ba. Jafar ya kalli Hajiya dake tsaye kamar sojanniya se numfarfashi take tana dannanwa Ahmad da yayi ƙasa da kansa harara, cikin sigar rarrashi Jafar ɗin yace mata "Please mana Hajiyata, ki saki fuskarki, change of schedule muka samu na flight and na manta ban sanar miki ba. Believe me Yah Ahmad ma be sani ba seda na sauka Kano. You Know i Miss you so much shiyasa ba zan iya jira ba kuzo da yawa ba shiyasa kawai na kirasa nace yazo ya ɗauko ni amma ba laifinsa bane Allah nike da laifi amma kiyi haƙuri bari na koma Abuja kawai gobe sena dawo kizo keda jama'arki ku taroni" ya faɗa bayan daya isa dab da ita. Hararar da takewa Ahmad ta mayar kansa kafin tace "Billahillazi karka ɗauka kaci banza baka isa ka tozartani a banza Ƙawayena su tafi suna gulmata ba sannan na ƙyakela muje cikin" "Ai wanan unnecessary drama taki ce zata saka a tafi ana gulmar taki, sabida Allah meye abin tashin hankali a nan? Daman banda ɗaurawa kai ke kika saba taroshi ko yaya? Wlh Yaya Binta bakya gudun abin magana da abin sakawa kai ciwon kai a duniyar nan, duk inda zaman lafiya yake kin ɓauɗe masa" Munira ƙanwarta da batayi niyyar magana ba sedai ganin Abin na Yayartata na neman zarce misali yasa ta fito tana mata maganar. Fuuuu Hajiya ta shige ɗaki Jafar ya kalli Ahmad yace "I'm sorry Yah Ahmad ni na jawo maka" "Kaidai jeka kafin Hajiya ta canza maka wannan fuskar taka babu ruwana bari naje wani guri bazan jima ba zan dawo" Ahmad ya bashi amsa yana juyawa ya fice daga gidan. Dukda yayi ƙoƙarin danne ɓacin ransa Amma Jafar ɗin seda ya fahimta, ya sani dole kalaman Hajiyar su sosa masa rai shi kansa beji daɗi ba amma yasan idanyace wani abu baya ga kalmar lallaɓi da banbaki a yanzu ƙara tunzurata zeyi tayi musu zazzafar Tijara a gaban mutane. Jiki a sanyaye ya bi bayan Hajiyar, Yaƙe kawai ya ringayi yana gaisawa da tarin matan dake zaune falon Hajiyar, ya so ya gane wasu amma ya manta sunayensu wasu kuma sababbin fuskane a wajensa dan Hajiya badai tara ƙawaye ba ga Yayayensu da suka kwaso sekace Biki keyi yanzu da tana nufin waɗannan jama'ar zata kwasa su tafi Ɗaukoshi daga Airport ɗin?. Abinda ya sake ɓata masa rai yanda Yayan Ƙawayen Hajiyar suketa wani abu kamar masu shafar Jinnu, se ɗaukar hotuna suke da video ana sakoshi a ciki wasu ma yaga kamar Live sukeyi a IG suna faɗin gasu a gidansu Jay sunzo taron shi. Ƙasa Ƙasa yake jan tsaki yana durƙushe tsakiyar Mata kowacce da kalar soki burutsun hirar da take jefa masa da tambayoyi kamar sun aikeshi ya dawo, ba Hajiyar ba ba Ƙawayen nata ba babu wadda tayi tunanin a gajiye yake ko yana da buƙatar yaje ya huta seda Hajiya Turai ta fito daga Kitchen taje tana shirya abincin da za'a rabawa Jama'ar da Hajiya ta tara abin Allah arziƙin Jay yau ba Ƙaramin Better tasa aka shirya a gidan ba harda Rago aka gasa. "Kana tsugunne Jafar ai se Ƙafafunka su gaji tashi kaje ka huta kaida ka shawo tafiya" Turai ta faɗa, ya saci kallon Hajjaju da ta zauna ta haɗe fuska tana juya ƙafa da gani lissafa yanda zataci ubansu daga shi Har Ahmad ɗin daya rusa mata shiri takeyi. "Tashi kaje mana kake kallona da wasu idonka irin na Ubanku" ta faɗa tana zaburo masa. Ya miƙe yana shafa kai, daidai nan Faisal Bechi ya shigo yana kwalawa Hajiya kira yana cewa "An fa gama saita komai har Photographer ya iso Allah dai yasa ma a barku ku shiga Airport ɗin irin wannan gayya se kace masu taro Governor.." Se kuma ya dakata saboda ganin Jay a gabansa, ya buga tsalle kamar yaro ya ɗaneshi yana ihu. "Get off me my friend, kai baka zaka girma da shirme ba ko?" Jafar ya faɗa yana tureshi. Bakin Faisal kamar ze yage yace "Welcome brother, ni na sani sedai ba Jafar Bechi ba wlh se kayi disappointing Hajiya amma fa ka kwafsa kai kasan irin Grand welcome da aka shirya maka kuwa yau?" "Matsa na wuce" Jafar ya tureshi jin yana neman ɓallo masa sabon ruwa Faisal yabi bayansa yana kyalkyala dariyar mugunta yana gaya masa irin shirin da Hajiya tayi. Ɗakin Momy ya wuce, tana zaune kan kujera da waya a hannunta tana dannawa Khadija, Aslamiyya da Maimuna duk suna falon suna kallon Tv duk Drama da aka kwasa suna zaune basu fita ba balle su tanka Jafar ya shiga da sallama suka amsa masa a tare kowannensu fuskarsa na faɗaɗa da murmushi. Gaban Momy ya wuce ya zauna dab da Ƙafafunta yana kallon Step sisters ɗinsa fuska ɗauke da murmushi. "Barka da dawowa Sheikh Jafar" Momy ta faɗa cikin raha. "Mun same ku lafiya Momy?" Ya mayar mata ta amsa da "Lafiya lau, ya ka baro abokanan sana'arka da gurinsu Yaya Muhammadu?" "Duk suna lafiya suna gaisheku" "Madallah sannu da zuwa" ta sake faɗa kafin ta miƙe ta shiga kitchen, bata jima ba ta fito me aikinta Amira na biye da ita da babban Try ta ajiye a gaban Jay kafin ta gaishe shi ta koma. Ya miƙawa Nu'ayma Babyn Khadija hannu ta tafi kamar zata faɗi dan tafiyar tata batayi kwari ba, Khadija, Maimuna da Aslamiyya suka haɗa baki gurin yi masa sannu da zuwa ya amsa musu kafin yace da Khadija "Yaya Khadija ya yara? Ina Alhaji?" "Yana Islamiyya se sun tashi idan an ɗauko shi zasu biyo ta nan mu wuce". "Kasha ruwa, ga mutuminka nan Coconut Juice" Momy ta faɗa ganin yana ta wasa da Nu'ayma be taɓa abinda aka ajiye masa ba. "Yah Jay sha kaji dan Allah ni nayi fa" Maimuna ta faɗa cikin zumuɗi ta sauka ƙasan ta tsiyaya masa a Cup ta bude kwanon da aka zuba kayan maƙwalashe tana cewa "Har small chops ɗin ma ni nayi fa" "Kice kin zama Chef babu labari? Me ya samu wayarki na dena ganinki Online?" Ya faɗa yana karɓan Cup ɗin da ta zuba masa Lemon, seta kalli Momy, Momyn tace "Kya kalleni? Ki gaya masa abinda kikayi Ahmad ya kwace wayar mana" "Ai base ta faɗa ba ma Momy tunda kikace Yah Ahmad ne nasan tayi abu mara kyau ne, Any Juice ɗin yayi daɗi sosai, and this too" ya nuna Chocolate cake dake hannunsa. "Thank u, shine Yah Aslamiyya yace ba zakaci ba wai beyi daɗi ba" "Zanci mana har Token zan baki ma for the good job". Gwalo tayiwa Aslamiyya Momy da Khadija na musu dariya Faɗan sako da sako sukeyi kamar kaji. A cikin zuciyar Jafar kuwa abinda ya sabaji a duk sanda yake cikin ɗakin Yauma yaki, ina ma ace shima ɗan ɗakin ne? Duk sanda ya zo Nigeria irin wannan tarbat yake samu a gurin Momy. Ita zatayi masa maraba ta bashi abinci Hajiya kuwa se Hayagaga ta cikashi da tambayoyi da ƙorafe ƙorafe, ruwa seya tambaya kafin zata tuna ya kamata a bashi babu ruwanta da duba daga wani guri me nisa yazo yana da buƙatar hutu da kulawa Aa matsalolinta kawai sune a gabanta. "Bari naje nayi sallah an kira La'asar" ya faɗa yana miƙewa tsaye, Momy tace "Tam, zasu Miƙo maka abinci Gas ne yayi mana tsiya amma an gama ƙarashene kawai" "Nagode, Yah Khadija kafin ki tafi kimun magana" daga haka ya fice daga falon. Seda ya leƙa Hajiya Rabi, a mutunce suka gaisa se sannan Yaranta suka samu sukunin yi masa sannu da zuwa suma, ya kama hannun Zayyad suka fita tare zuwa masallaci. "Idan kina Ƙaunar Allah Binta ki zauna, mene haka? Waike bakya kunyar idon mutane ki ringa abu kamar wata zararriya?" Turai ta faɗa tana tare Ƙofar uwar ɗakin Hajiya dake shirin fita ta raba hali, Jafar na fita tacewa Aidah, Jikarta Babbar Yar Nazira ta bishi taga inda zashi ilai kuwa tace mata ya shiga ɗakin Momy ta zabura zata fita Turai ta hanata shine ta turata ɗaki suketa tata burza tun dazun lokacin daya ɗauka a ɗakin be fito ba shi ya saka Harzuƙata, ta window taga fitowarsa da shigarsa Gurin Hajiya Rabi shine ta zabura zata tareshi ta tsigaleshi taji tsakanin Aisha da Rabi ko da akwai wadda ta tayata ɗaukar cikinsa ko ɗawainiyar rainonsa ne bata sani ba dayafi mutuntasu da girmama su akanta? "Turai kirabu dani, ni ban iya haɗiye baƙin ciki ba sena Amayar dashi, ke ni fita ki sallami kowa ma ta wuce gidanta zaman me kuma za'a mun tunda wanda ake taron danshi ya watsa mun ƙasa a ido, sallami kowa dan Allah na samu sararin huce fushina yanda ya kamata" Hajiya ta faɗa a fusace tana fuzgewa daga riƙon da Turai tayi mata. "Kamar ya in sallamesu ni na tara miki su ko yaya? Sannan Ai kya jira su gana cin abinci ko ba'ace su tafi ba kowa kama gabanta zatayi tunda ba yinin Biki bane balle ace se rana ta faɗi idan kuma zaki fita ki korasu daman ba baƙon abu bane a gurinki ai siyar da hali" Turai ta mayar mata itama a fusace kowa ta kalli Bango tana hura hanci. Jafar kuwa daƙyar ya ƙwato ya fito daga Masallaci, ɗakinsu shida Ahmad ya wuce. Ya saki murmushi ganin yanda aka canza tsarin ɗakin daga zuwansa na last year ya canza musu Gado da Labulaye da Carpet harda penti aka sake sabo ga kyawawan Food warmers da Jug a ajiye yasan aiken Momy ne. Seda ya sakawa Ƙofa Key kafin shiga wanka. A cikin kayan Ahmad ya nemi marasa nauyi Three quater Kaki da Armless shirt ya saka ya dirarwa Abincin. Tuwo ne da Miyar Agusi, taji Wasulla na ruwa dana ƙasa wato Momyn kamar tana shiga zuciyarsa duk zuwa seta tareshi da abinda yake da burin ci idan yazo gida. Sosai yaci tuwon ya sha Juice ta ture kayan gefe ya kishingiɗa jikin gado yana jin jikinsa ya cika da yawa, shida abinci me nauyi kamar tuwo se yazo Nigeria shina baya ci da yawa saboda Diet ɗinsa. Wayar Ahmad ya kira, "Ina Get" Ahmad ya faɗa bayan daya amsa wayar dan idan be ɗaga ba Jay kira zeyi tayi baze barshi ba. Ragowar Abincin daya rage Ahmad yaci suna hira Salim ma ya shigo se Lawal da Mu'allim da suka shiga suka gaida shi suma suka kuma gaya masa mutane na jiransa a ƙofar gida. "Ka ce musu na fita" Inji Jafar. Ahnad na siɗe hannu yace "Sun fika sanin whereabouts ɗinka ai, garama ka tashi kaje kafin Alhaji ya dawo ya tarar da taro a Ƙofar gidansa ya dirar maka daga dawowa" "Yana nan da halinsa kenan be canza ba? Is high time da muma ya kamata mu mallaki gidan kanmu haka a dena zuba mana Iko, small thing ze fara badai a gidana za'ayi this ba? A gidana kuke mun that?" Jafar ya faɗa yana mimicking muryar Alhaji Audu. Ahmad dasu Salim sukayi dariya, dole ya fita ya sallami Fans ɗakyar kafin ya koma ciki Matan da Hajiya ta tara nata fitowa kowa na kama gabanta ya ɗauke kai kamar be gansu ba yanajin Yannatan na kiran sunansa amma ya share. Shi ko ƙawar hira be hango a cikinsu ba balle Alaƙar da iyayensu suke son ƙullawa dashi. Bayan Magriba suka shirya shida Ahmad sukaje gidan Late Brigadier General Baballiya Bechi yayiwa Matarsa da yaransa Ta'aziyya, daga can Ahmad yace su biya gidan Baba Alƙali sukayi rashin Sa'a baya nan yana Abuja se washe gari ze dawo inji Mama Balaraba, dukda basu tarar dashi ba amma suka zauna har kusan 11 suna can dan idan sukaje gidan nan basa iya fita da wuri daman musamman da suka tarar da Fadlan ya fara caccakar Jay akan Premier League wai suna kwan gaba kwan baya, se sunyi sama se su diro ƙasa sun kasa yin abin kirki. Drama Jay da Fadlan daman bata ƙarewa tunawa da dokar Alhaji Audu ta hana kaiwa dare a waje yasa suka tafi a 11 ɗin. "So we go cross fence today" Jay ya faɗa sanda suka tarar da Kantamemen Get ɗin gidan a garƙame, Ahmad yace "Da rabon kayi kwanan Cell kuwa, gidan Alhajin Bechin zaka haura? To sauka nayi tacan farkon Layi karma yace tare muke" suka fashe da dariya suna tuna wani lokaci zamanin yarinta Jafar da yarbanzar ƙiriniya Hajiya bata nan ta kukke ɗakinta ya shiga ta window wai ze ɗakko Uniform ɗin Islamiyya ya shiga amma fitowa ta gagara a zatonsa bata saka key ba a Ƙofar ze buɗe ta ciki ashe ta murza Key abinta haka ya zauna ɗaki har Magriba akayi sa'a Alhajin ya riga Hajiya dawowa akace ga Jafar can ya haura ɗaki ya kasa fitowa Alhaji ya tubure se an kirawo yan sanda kafin a buɗe ƙofa se su tuhumi Jafar dalilin daya saka ya haura masa gida dakyar fa Aka bashi baki ya ɗauko spare key ya buɗe shi amma yaci duka a gurinsa ranar. Horn Ahmad ya danna, Issa ya leƙo ganin motar Ahnad ya buɗe Ƙofar, "Da alama Alhaji baya gari" Ahmad ya faɗa bayan da ya ajiye mota. Issa yace "Aa, mun faɗa masa kunje gidan Alhaji Soja kuma kunayin dare acan shine yace idan kune a buɗe, idan ba ku bane kowaye ya kwana ga waje, kuma Alhajji Yaƙubu bayaga gida? Ko bashi a Kano baki ɗayane?" Ya tambayesu. "Ohna manta ko banga Yah Yakub ba, ko baya nan?" Jafar ya faɗa Ahmad yace "I'm not sure da safe dai mun haɗu, ta yuwu yayi tafiya ko kuma Gidansa ze kwana kasan Yah Yakub ya zama jan wuya Alhaji ya saka masa ido kawai" "Kodai Hajiya ta tsaya masa ba?" Inji Jafar daga nan suka wuce ɗaki, yana so yaje gurin Hajiyar amma yasan tashin hankali ze siyo da se ta hana kowa bacci a tsanake gara ya bari ayishi ido na ganin Ido. Ƙofar falon Alhaji da suka gani a buɗe tasa suka fahimci yana ƙasan dan haka suka shiga sedai suna saka kai duk su biyun sukayi dana sanin shiga a lokacin, Hajiya na zaune da akama su take jira, Jay ya juya ze koma Ahmad ya rufa masa baya ta tashi da hanzari ƙiris ya rage ta hantsila tana cewa "Gasu nan, ka gani ko ya janyeshi sunfita ze fara koya masa yawon Iskancinda yakeyi, wlh tallahi kayi mun tsakani da Aisha da zuri'arta ta fita a sabgata idan ba haka ba ta bari na waiwaya kanta wlh na lahira se ya fita jin daɗi. Banda tsabagen an juyar masa da hankali Jafaru ne zezo ƙasar nan ya shiga sabgoginsa tamkar na mutu baya tunawa dani? Kalleshi fa, kai da gani kasan ba a hayyacinsa yake ba to na rantse da Allah duk abinda mutum yake taƙama dashi na dameshi na shanye kuma se na nuna muku ku baku san komai ba ƙananan yan banza ne ku, dallah wuce ka bawa mutane guri kana wani sunkuyar da kai kamar na Allah kai kuma shigo nan" ta dakawa Ahmad tsawa. Daman neman hanyar tsira yake dan haka da sauri ya wuce ya bat Jafar a gurin. A gurguje yayi shirin bacci yana sake gwada kiran Fatima. Tun da rana da sukayi magana yace mata ze ɗauko Jafar ya sake kiranta kusan sau huɗu bata amsa ba, sanda suka fita tareda Jafar ya kirata tace she will call him back tana abune amma shiru yanzu kuma neman abinda ze hana maganganun Hajiya tasiri a zuciyarsa yakeyi shiyasa ya kasa jirn ta kirashi kamar yanda tace yake sake kiranta. Ko dazun ma da rana sanda ya ɗauko Jafar fita kawai yayi daga gidan ya tafi can bakin titi daya gwada wayar Fatima be samu ba ya zauna yana ƙirga motocin da suke wucewa har zuciyarsa tayi sanyi shine ya dawo gidan. Yaja tsaki yana cilli da wayarsa akan gado dalilin kiranta daya sakeyi sau biyu bata ɗauka ba, wlh da ze iya cire sonta daya masa kamun kazar kuku daga zuciyarsa daya haƙura da yarinyar. Duk wasu alamu na nuna rashin karbuwarsa a gurinta ta gwada masa, ya rasa Aibunsa daya saka Fatima ba zata so shi ba, shiɗin da Mata suke bi kamar ƙuda da Alawa shi Mace take wulaƙantawa gaskiya So baya kyautawa sam. "Lafiya kake tsaki Yah Ahmad ga wayanka kuma a ƙasa?" Jafar daya shige fuska tayi jaa ya faɗa, Ahmad ya kalli ƙasan dayace, ashe wayar can tayi tsalle ba kan Gadon ta tsaya ba. Ya sake yin tsaki ya ɗauka, Screen ɗin ya tsage, sabuwar wayace Dal Samsung ƙirar shekarar Kwanansa huɗu da bareta, guda biyu ya siya ze bata ɗaya idan sun dawo hutu ko yaje Zarian ko screen guard be saka mata ba gashi takaicin Fatiman ya saka ya fasata. Dannawa yayi ya tabbatar iyakar Screen ne faɗuwar ta taɓa be shafi Sensor ba dayaga lafiya lau take ya ɗorata kan Bedside ya kwanta. Jafar daya gama shan Rap a gurin Hajiya abin takaici Alhaji na zaune yanajin yanda take aibata Ahmad tana ɗora masa Alhkin wai son ya rabata da ɗanta amma ya gagara cewa komai harta gaji ta barshi ya taho. Wanka yayi ko ze samu sauƙin bacin ran da yake cikiz Ahmad daya kasa bacci abin tausayi ya sake ɗaukar waya yana gwada number Fatima tana ta ƙara amma bata ɗaga ba. Tashi yayi ya shige banɗakin da Jafar ya fito. Jay ya zauna a bakin gado ya ɗauki wayar Ahmad. Tunda suka fita ya lura da yana ta trying qata number idanbata shiga ba yayi tsaki ya ajiye waya har a gidan Baba Alƙali hankalinsa rabi baya tare dasu shida Fadlan ya barsu sunata surutu. Call log ya shiga sunan FATIMA ya fara cin karo dashi da wata Red heart a gaba. Yaja tsaki a fili yace "She must be that Mechanic daughter, har take da guts ɗin wulaƙanta Yah Ahmad". Haka kawai ya sake danna kiran number zuciyarsa na tafarfasa addu'a yake Allah ya bashi sa'a ta ɗaga, cikin ikon Allah kuwa ringing uku yaji an ɗaga, Fatima tsaye a gefen Tukubar Sambo me Mac Dee tana jiran a sallami Badar. Test garesu har biyu a gobe dan haka tunda yamma suka fita karatu. A silent ta saka wayarta shiyasa bata ji kiran Ahmad na farko ba, da sukaje sallar Magriba kuma taga missed calls, fa sukaje sallar isha ma ya sake kira tace she will call back amma ta manta bata kirashi ba kamar yanda Badar tace saboda baya gabanta shiyasa har take mantawa da abinda ya shafeshi. Kiran da yake tayi mata na yanzu kuma ta na gani dan wayar na hannunta da ita take karatu ƙyuyar ta tashi ta fita daga class ɗin ta amsa wayar ya saka taƙi dagawa ganin yanata kira yasa tayi rounding off suka fito dan daman Badar tace ta gaji bacci takeji, suna tafe seda suka wuce FSLT Badar tace wai yunwa takeji zataci Mac Dee shine suka zarce gurin Sambo a gaban Social Centre tana ta Allah Allah a sallamesu ta shiga hostel ta kirashi sega kira ya sake shigowa wannan dalilin yasa ta ɗauka muraya a sanyaye cike da gajiya da bacci tayi masa sallama. "Dallah riƙe sallamarki Malama, who the hell do you think you are da har zaki ringa wulaƙanta mutum kamar Ahmad? Do you even deserve to date someone like him? Koda yake daman haka kuke Yayan Talakawa yayan Matsiyata ku ba kowan kowa ba se shegen girman kai da isa kamar wasu sarakai. Imagine Yar Mechanic, bawai me Gyaran Mercedes Benz ko wata Lambo or Tesla ba just a common mechanic may be ma Motorcycle yake gyarawa not even cars shine kika samu damar raina Ahmad Bechi saboda he stop so low yace yana sonki. I even began to think anya ba Asiri kikayi masa ba? Ke koma dai Mayyace ke because they way Ahmad is behaving yafi kama da someone that is possed. "What ever you have done to him bear it in your mind bazaki Aureshi ba, in har ina raye i will make sure that ko Inuwar Ahmad baki tsaya tareda ita ba balle har kiyi tunanin Auransa. Look for your mate ki kuma sakar masa Soul idan kuma ba haka ba zanyi maganinki, ni Jafar Bechi i will be the end of you akan Ahmad zan iya sacrificing life ɗina kuma bazan saka ido ina kallo yayi wasting rayuwarsa on worthless thing like you ba ku....." "Jafar..." Ahmad daya fito daga wanka ya kira sunansa cikin ƙaraji kafin ya kwace wayarsa. Ya duba screen tabbas da Fatima yake magana ita yake faɗa wannan kausasan maganganun daya taraddashi yana faɗa. Na ƙarshen ma yaji Allah kaɗai yasan me yace mata daga farko. "Fatima, i will call you please. Karki bari maganarsa ko guda tayi tasiri a zuciyarki ina ganin shaye shaye ya fara, let me deal with him first zan kiraki kiyi haƙuri dan girman Allah kinji?" Ahmad ya faɗa, be jira amsarta ba saboda yand aya rikice ko kashe wayar beyi ya ajiyeta ya fuskanci Jafar da idanunsa suke ci da wutar Bala'i. "Why Jafar? Me yasa zakayi mun haka? Kasan wacece ita? Kasan matsayinta a gurina?" Ya faɗa yana kallo Jafar, a fusace Jafar yace "Koma wacece ita ta wuceni a gurinka ne? Ni Yah Ahmad kake tunanin shaye shaye nakeyi saboda na gayawa waccen bastard ɗin gaskiya ta shiga hankalinta? Do you think i can withstand seeing you being disrespected by that local champ? No kuma kaima you must come back to ur senses wlh ba zaka auri waccen yarinyar ba da bata san mutunchinka ba. Duk matan duniya kowace kake so ka nemo i will stand with you but not her not Fatima or what ever her name is" "I will slap you wlh ka sake zaginta Jafar, Fatima is my Life, matar da nake burin na aura ce in har kana so na dole ka sota duk yanda take and you must respect her as much as you respect me. Tsaya Jafar yaushe ka zama haka? Yaushe ka fara kyamatar Talaka? Juat tell me the truth, Do you hate Fatima for not been from prestigious family like yours ko kuma saboda bata sona?" "Akan Mace zaka Mareni Yah Ahmad, macen da bata san mutunchinka ba?" Jafar ya faɗa yana nuna kansa mamaki sosai a muryarsa. "Answer me Jafar akan me ka tsaneta kafin nan zan tabbatar maka da ka cancanci Marin ko kuma ba haka ba" Ahmad ya mayar masa tasa muyar cike da tabbatarwa. Kawai se Jafar ya jijjiga kai ya nufi ƙofa yana cewa "Wlh ko kowa ya yarda ka aureta bazan bari ba, bata isa ta shigo ta lalata abinda Allah haɗa ba, babu matar da zata lalata zumunchin da yake tsakanina dakai kuma Mayyace Ta kama maka Soul, first thing tomorrow morning Bechi zan tafiz ai da muna Yara ance da akwai Sarkin Mayi acan, I'm going to report her to him duk ma inda ta kai Kurwanka seta dawo dashi I promise". Fatima ko tayi tsaye da waya a kunne tana sauraron Jafar, ta ma kasa fahimtar kalamansa da inda suka dosa, ta fahimci ba muryar Ahmad bace abinda take tambayar kanta waye wannan??? Zagin Mahaifinta da yayi shi ya karya mata zuciya har bata san hawaye ya fara saukar mata ba seda Badar ta taɓata akan su tafi taga tana kuka da waya a kunna wannan yasa da sauri ta zare wayar ta saka a speaker don a zatonta ko wani Bad news ake gaya mata daga gida nan ta tsinci faɗan Jafar da Ahmad dan lokacin ya gama zazzaga mata tijara Ahmad ya kwace wayar. "Atleast he stood for you, shi kuma ko wanene wannan da yake iƙirarin indai yana raye ba zaki Auri Ahmad ba Bi'iznillahi da ransa yanaji yana gani zaki Aureshi sedai baƙin ciki ya sa ya haɗiye zuciya ya mutu. Ke kuma banza kin tsaya kina kuka, me yasa baki cuccusawa uwarsa Ashar ba? Dallah muje ni kar kisa na huce haushi na akanki kin wani tsaya kina kuka wlh na ɗauka mutuwa aka kira a gaya miki daga gida, daman idan baki nemo mana number sa munci Kutumar ubansa ba to naki zanci Soloɓiyon banza kawai". Badar ta ringa masifa iyakar Ƙarfin ta har suka isa Ɗaki ita kuma Fatima tana kuka. Yar Matsiyata, mayya daya kirata yafi komai yi mata ciwo a rai, shi be san ba son Yayan nasa takeyi ba bare har yaci mata mutunchi akansa? Koda ace tana son Ahmad wannan dalilin ya saka ko zata mutu seta rabu dashi wlh. Wayarta ta ɗauka take tayi blocking ta kumayi deleting number Ahmad, an gama chapter sa domin ba ayi wasu Ahali fa zasu wulaƙanta mata Baffanta ba kuma ko Ahmad ne Autan Maza sedai ta mutu batayi Aure ba. MATAR MUTUM* *NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER* *FIKRA WRITERS ASSOCIATION* *LITTAFIN KUDI NE* *PAY 500 A ASUSUN* *7061838488* *OPAY DIGITAL SERVICES* *MARYAM FAROUK* OR *0709290797* *ACCESS BANK* *SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488* *IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705* *Kuyi following dina a Arewabooks @Maryamfarouk01 inda zaku karanta wannan littafin tareda sauran littattafaina* *NAGODE* *BOOK 2* *PAGE 8* Sosai Ahmad ya ɗauki fushi da Jafar akan abinda yayiwa Fatima, dukda shi Jafar ɗin ya sauke kai ya bashi haƙuri inda suka sake fafatota da yace se ya kira Fatima ya bata haƙuri ai ita yayiwa laifi nan fa Jafar ɗin yace muddin ba Momy bace bazeyi ba, sedai idan sanadin haka yasa Ahmad yace shi ba jininsa bane amma wlh baze bata haƙuri ba, da niyyar sati uku yazo Nigeria dalili wannan ɓarakar yasa kwana goma yayi a daddafe ya tafi kuma duk gida seda aka gane akwai matsala tsakanin Jay da Yah Ahmad ɗin nasa dan muddin yana gari duk inda zaka gansu tare suke amma wannan karon kowa sabgarsa yakeyi. Momy ta tambayi kowannensu akan meya faru amma sukace mata babu komai, ta haɗasu tayi musu Nasiha akan karsu bari shaiɗan yayi tasiri a cikin zukatansu, su ɗin sun kasance abin misali cikin zuri'ar Audu Bechi karsu yarda seda girma ya fara zuwa kuma su kama wata hanya ta daban. "Na san abu biyu shaiɗan yake saurin samun gakaba akan mutum ta dalilinsu, Mace da Kuɗi, karku bari ɗaya daga ciki ya haɗaku kuyi Ƙoƙari ku sasanta kanku" tace musu duk suka amsa mata da "In sha Allah" amma suna fita kowa ya kama gabansa. Ahmad yanda ya kasa samun Fatima a waya shiya sake dugunzuma hankalinsa har yake ƙara tasirin fushin Jafar a zuciyarsa, Allah ya sani yana sonta, so me tsanani da yake jin tamkar idan be sameta ba ze iya rasa ransa. Daya kasa samun wayarta tilas ya shirya ya tafi Zaria abinda ya Ƙara tunzura Jafar shi kuma tsanar Fatiman ta ninku a zuciyarsa tunda har ta zama silar ruguza Alaƙar sa da Ahmad yayi rantsuwa ba zata shiga zuri'arsu ba domin Allah kaɗai yasan abinda zata haifar musu. Shirin komawa ya shigayi duk da kwanakin daya niyyata basu cika ba kawai gara ya tafi dan baze jure abinda Yah Ahmad yake masa akan Mace ba, Macen ma wadda bata kai matsayin ace Ahmad ɗin ya haukace haka akanta ba. Har hasaso kamanninta yakeyi Ƙila wata baƙace mummuna da fuskarta kamar ta shafa Baƙin Man da Babanta yake ta'ammali dashi, kai Yarinyar nan ma dole asiri tayiwa Ahmad kuma tilas ya karyashi. Hajiya kuwa ranta ƙal tamkar zata taka rawa data fahimci yanda abu yayi zafi tsakanin Jafar da Ahmad. Dubunta Hansin ta bawa Turai taje mata gun Malam akan ayiwa musu Farraƙu domin taga alamun Amadun yana neman yasa kwaɓarta tayi ruwa kuma aiki yaci. Duk wani buri da tanadi da take dashi akan Jafar in har yana tareda Ahmad ba zata samu cikar burinta ba Jafar kuma shine makamin ƙare danginta a yanzu. Tana da shiri da kuma tsarin ganin ya zama makwafin Alhaji. Da akwai matattarar sirrin Alhajin inda duk wani abu mai muhimmanci daya shafi rayuwarsa yake da wanda su suka sani harma da wanda basu sani ba takaddun Kadarorinsa na gida dana Ƙasashen waje duk a nan ya ajiyesu. Wata Safe box ce a cikin Wardrobe ɗinsa ta kaya. Safe ce da akayita da wani irin matakan tsaro ta yanda duk tsiya da bala'i muddin ba wanda ya kulleta ba shi kaɗai ze iya buɗewa babu ta yanda za'ayi lalata tsaronta kuma ba zata fasu ba. Tasha ta saita Kemarar wayarta ta yanda zata ɗauko mata Ɗalamisan da Alhajin yake buɗe gurin dasu amma abu ya faskara kamar ma ba wani abu da yake dannawa se daga baya ta fahimci kwayar idonsa ce mabuɗin gurin, kenan babu ta yanda za'ayi ta buɗu indai ba shine da kansa ba. Hankalinta yana Ƙololuwar tashi idan tayi tunanin yanzu ace ya faɗi ya mutu ta yaya zasu buɗe gurin su kwashe wasu abubuwan da bazasu so ace sun fito a rabon gado ba sedai ita da Yayanta su handame? Da fari taso ta tattauna maganar da Zakariyya da Naziru taji ko suna da Mafita, sedai ta fasa hakan saboda ta sani a yanzu ita dasu shegen Sama ne uake dukan na ƙasa, kowanne ƙoƙarin ya gina kansa yakeyi idan kuma ya samu dama ya tattare komai shi kaɗai shoyasa ta fasa sakasu a cikin shirinta. Jafar kaɗai ta aminta da sakashi gaba akan cimma wannan ƙudurin nata, shi take so ya zama magajin Alhaji domin tayi ammanna duk cikin Yayansa babu wanda ya aminta dashi har zuwa yanzu ya sanar dashi ta yanda za'a buɗe ma'ajiyar bayan ransa. So takeyi ta sake cusa Jafar ɗin jikin Alhaji ta fili data baɗini ta yanda ze Amince dashi ya damƙa wannan Amanar a hannunsa ya zama shine Magajinsa, ita kuma da wannan damar ta samu Jafar ɗin ya gama sanin komai game da Alhajin shikenan burinta ya cika domin se yanda tayi da Jafar ɗin da kuma dukiyar Alhaji sedai wannan muradi nata baze cika ba muddin Jafar yana tare da Ahmad, shi yasa bataji komai ba da Turai tace ta bada kuɗi zata je mata inda suka kai sunan Abba T saurayin Hajiya Ƙarama domin dukda dukan daya sha a hannun Yakubu be haƙura ba, ya dawo amma a can gidan Haj Turai sukeyin Hira ko kuma su fita yawo gari maganar da ake yanzu ma Bayan sallar Azumi yace Iyayensa zasu zo tambayar masa Auranta. Babu wanda ya san zancen a gidan kosu Naziru Hajiyar bata gayawa ba tace sedai aji komai katsahan tunda har a yayan cikinta akwai masuyiwa Hafsatun baƙin ciki. Ahmad na Zaria Jafar ya tafi dan tarewa yayi a Hotel kullum haka ze je Samaru ya wuni a Faculty of Art yana bibiyar ta inda ze gamu da Fatima amma taƙi yarda su haɗu se ranar daya kwana uku ne ya samu nasarar ganinta sammako ya buga tun bakwai yaje ya zauna a bakin Class ɗin da zasuyi Lecture, a gurin wani Guy ya samu Time table ɗinsu bayan daya nuna masa hotonta ya tabbatar masa ya santa bata zuwa Class kwana biyu amma na goben ya tabbatar zata zo indai tana Makaranta dan Malamin baya wasa Individual Attendance yake ɗauka and is automatic carry over idan mutum yayi missing wannan tasa ya tafi da wuri, 8 zasu shiga amma 7 bata gama rufawa bama ya kafa ya tsare a bakin Ƙofa. Yana tsaye a gurin suka zo ita da Badar da wasu yammata biyu, bata ganshi ba se Badar ce ta nuna mata shi tana cewa "Kinga Ahmad" "Ahmad?" Ta maimaita da mamaki tana kallon inda take nuna mata se gashi kuwa a tsaye ya zuba hannaye a Aljihu yana binta da kallo suna hada ido maganganun Jafar suka fara dawo mata tamkar a lokacin yake faɗarsu wannan tasa tayi saurin ɗauke kanta ta doshi class ɗin da sauri dan ba zata bari ya tareta ba amma kafin ta shiga yasha gabanta. "Ka matsamun na wuce" ta faɗa ba tareda ta bari sun haɗa ido ba saboda yanayinsa da yake neman karya mata lago ya samu galaba akanta. "Zan jiraki a waje ku gama" ya faɗa a sanyaye yanajin tamakar ya rungumeta saboda So, taja baya saboda kusancinsu yayi yawa tana cewa "Karka jirani dan ko ka zauna bazan saurareka ba" "Shikenan, zan shigo Ajin na roƙi Lecturer ya bani dama a gaban kowa nayi magana dake hakan ya miki?" Yanda yayi maganar ta fahimci ze aikata abinda yake nufi dan haka tace "Karka shigo, ka jirani a waje" "Good girl" ya faɗa yana mata murmushin ƙarfin Hali, kansa ciwo yake masa be taɓa zaton haka so yake dagaske ba. Fatima ta wuce, Badar ta matso fuskarta ɗauke da fara'a, she is lively ko yaushe fuskarta a washe take kamar ta Ahmad ɗin muddin ba an tsokalota bane. "Hi" ta faɗa tana waving masa, "Hello Badar" ya mayar mata yana ɗaga mata hannun shima bakinta har kunne jin ya ambaci sunanta, ashe dai Fatima ta bashi labarinta. "Karka damu, just give me your number, kaje ka samu comfortable guri ka zauna i will bring her to you damun gama Class" ta faɗa tana bashi wayanta. Ya karɓa ya shigar da Digits ɗinsa kafin ya mayar mata yace "Nagode Badar, i will be in Shinkafi Elite, zan jiraku a can" "Ayt, se munzo" ta sake ɗaga mishi hannu kafin ta shiga Ajin ta zauna kusada Fatima dake leƙensu ta window, duk a kan Idonta Badar ta bashi wayarta tana ganin yanda suke ta wani Murmushi duk seta tsargu. Badar batace mata komai ba har akayi Lecture aka gama suka fito, tana lura da yanda take satar kallon gurin da alama Ahmad yake nema amma bata ganshi ba A zuci Badar tace "Munafuka kawai tana so tana kaiwa Kasuwa". Suna tafe duk Fatima bata da laka, tunani takeyi ko ya tafi? ƙila ya haƙura da itan kawai tunda har ya karɓi number Badar. A hanya Badar tace su biya ta Shinkafi su siya Chips tace ta ƙoshi amma Badar ta nace se sunje in yaso ta siya ita kaɗai. "Kije can ki zauna kinga akwai layi kafin azo kanmu" ta nuna mata Table ɗin dake kusa dasu, Fatima tayi tsaki, can ƙarshe ta wuce seda ta zauna kafin ta lura da Ahmad ne a gurin. Zabura tayi zata miƙe ya dafe hannunta, karo na farko da hakan ta faru tsakaninsa da wata Mace da ba Muharramarsa ba. Cikin sauri ya saki hannun nata se kuma ya miƙe tsaye ganin tana shirin barin waje yace "Kwana na uku ina yawo cikin makarantar nan, na kasa samunki a waya, idan na canza layi na kira ki da kinji muryata seki kashe daga ƙarshe kindena Amsa duk wata number dana kira da ita why Fatima? So kikeyi zuciyata ta buga na mutu kowa ya huta? Dame kike so naji? Da Matsalarki koda rigimar Jafar? Wlh ko ki tsaya muyi magana yanzu ko kuma ba biki har cikin Hostel, Bet me I'm fuc***g serious zaki sha mamakina yau". Kuka Fatima ta fasashe masa da shi kawai ta zauna tareda kwantar da kanta akan Table ta shiga rera shi. Ahmad ya zauna ya harɗe hannaye yana kallonta ba tareda ya hanata ba. Badar kuwa saya karɓi order ta tafiya tayi Hostel. Seda Fatima tayi kuka me isarta Ahmad na zaune ya na kallonta kafin ta tsagaita ta fara zazzage masa abinda yake ranta wanda Jafar Bechi yaci ace ta gayawa sanda yake zaginta amma ta huce akan Ahmad ɗin. "Kiyi haƙuri dan Allah kuma ki manta duk wani abu daya faɗa shima cikin fushine and he regretted everything he said, zan haɗaku a waya ze baki haƙuri komai ya wuce" Ahmad ya faɗa kamar zeyi mata kuka. "Ni na haƙura sannan kaima na haƙura dakai, Brother ka ya gaya mun what i need to know about your Family, na sani daman ba zasu soni ba saboda ni Talaka ce amma ka sani ka kuma gaya masa tabbas mahaifina Talaka ne amma ba Matsiyaci bane domin yana da wadatar zuciya kuma sana'ar sa da yake zagi Halal yake nema Haram ba sannan ba yawon Maula yake gurin wasu mutane ba balle ya samu damar zaginsa ya Ƙasƙantar dashi. Nasan mutunchin Iyayena dan gaka bazan bari wani ya taka darajarsu ba, ko beyi rantsuwar bazan Aureka ba na rigada na yankewa kaina wannan shawarar sannan ka gaya masa Maita daya dangantamu da ita, nasan ko nayi shari'a dashi a duniya ba za'a bi mun haƙƙina ba saboda shi ɗan masu kuɗi ne amma zamuyi shari'a a Katun da ba'a bada cin hanci" ta faɗa sababbin hawaye na sauko mata. Duk yanda Ahmad ya zata abin ze zo masa da sauƙi ya zarce haka, taurin kaine da ita kamar mutanen farko ta riƙe maganganun Jafar Bechi se maimaitasu takeyi. "Amma Fatima ko Allah daya halicce mu baya kama wani mutum akan laifin da wani daban ya aikata muddin ba sunyi tarayya a cikin aikata laifin ba. In har akan Abinda Jafar yayi miki ne na baki haƙuri kuma in har zakiyi mun Adalci kin san bani na sakashi ba, ki faɗi kanki tsaye cewar bakya sona, ba kya Ƙaunata kawai dan rajin kanki ba saboda abinda Jafar yayi miki ba. Na dade da fahimtar haka, amma na kasa cire rai dake bansan me yasa zuciyata ta kasa haƙura dake ba, ina Addu'a akan Allah ya zaɓa mun mafi Alkhairi a kullum kuma ji nakeyi tamkar ana Ƙaramin sonki, duk yanda nakeji akanki wlh zan jure kuma zan roƙi Allah ya yayemun muddin kika furta da bakinki bakya Sona ba kuma zaki aureni ba nayi miki Alƙawarin daga nan gurin ba zaki sake gani na ba zan kuma fita daga rayuwarki koda Sonki ze zama Ajalina zan haƙura dake Fatima". ************* A YEAR LATER Gudu gudu sauri sauri take tafiya saboda ta kusa makaraz fata takeyi Allah dai ya rufa mun asiri ta samu ta shiga Ajin nan kafin Dr Abolude ya rufe, ba rasa ajinsa ba wannan banzan halin nasa na marking note se kace a primary ko secondary school shine abinda yake bawa kowa haushi dashi balle ita yau da rubutun ya zamar mata biyu, ga nata gana Badar dole taje da wuri ta samu sit a gaba, layin wanka ne ya bata mata lokaci saboda Monday ce kusan kowa na block dinsu nada Ajin safe. Qiris ya rage ta hantsila daidai Basket ball court saboda wani mutum da tun fitowarta daga Amina Hall ya zura mata ido kamar me shirin ganin yayan hanjinta, taja tsaki ta dauki Jakarta data zame ta fadi a ranta tana mitar wannan kallo haka taci gaba da zabga sauri a karo na biyu ta sake yin gaba tana shirin gangarawa daidai Senate building saboda mutumin dazu data gani tsaye gabanta kamar Aljani. Batasan sanda ya biyota ba harya tare mata hanya, zuciya ta harziqomata amma bata tankashi ba ta sake rabeshi ta wuce a kato na biyu se ji tayi daga bayanta ance "Sihh, jimana yammata". Raita ya ninka da baci, a duniya idan akwai abinda ta tsana be wuce irin wannan kiran wulaqancin da maza sukeyiwa yammata ba, se kace wata mota ko Mashin a ringa maka wani Sihh wasu tantiranma har fito suke kamar masu kiran kare. Taci gaba da tafiyarta kamar zata tashi sama ga haushin mutumin ga na bata mata lokaci da yake tayi dan ta tabbata yanzun kam ta makara sedai ta maqale a bakin window idan batayi sa'a ba. Karo na uku ya sako fadowa gabanta, wannan baƙar ɗabi'a ta mutumin da abin takaici take baya ko tunanin zata iya faɗuwa tunda batasan da shi ba ya ringa diro mata kawai kamar wani jifa. "Dan Allah ki saya" ya faɗa yana kallonta se a sannan ita ma ta kalleshi fuskarta babu alamar rahama amma can ƙasan ranta seda ƙirjinta ya buga saboda se yanzu ta kalleshi da kyau. Wani zabgegen mutum me ƙirar ƙarfi jiki a murɗe dan a yanzu da yake tsaye gabanta shigarsa ta nuna motsa jiki yakeyi, rigace Armless jikinsa da wandonta wanda da kaɗan ya zarce guiwa kayan suka qara bayyana surar ƙarfinsa, bata tantance fuskarsa ba dan bata kalleta sau biyu ba, yanda ya kankane mata hanya yasa ta raina kanta da tsahon da take taƙama dashi dan wata yar firit ta ganta a gabansa. "Afuwan, Assalamu alaikum" ya sake faɗa da sautinsa daya sa ta gaza tantance wane yare ne shi, sake daga kanta tayi ta sake kallon fuskarsa, a zubi za'a kirashi Bahaushe ko kuma Hausa Fulani amma a zubin jiki dai yafi kama da Irin zabga zabgan Igbiran nan ko Inyamurai haka fatar jikinsa da take da haske dukda ba fari bane amma a goge take tar yanda kasan ya hada jini da fararan fata. Tsaki ta zabga data kalli sumar kansa da tasha gyara irin na Yan Ball din nan itako yana daga irin abinda ta tsana dan duk girman mutum idan ta ganshi da irin Askunan nan kallon wanda be san kansa take masa ba. Tuna abinda yake gabanta yasa ta kauce ya sake tareta yana cewa "Nayi sallama kin bini da tsaki ki amsa mana Ammata" ya faɗa da wata cukurkudaddiyar hausa yanda kasan wani Yare yake. Tsakin ta sake masa tayi baya a tsiwace tace "Ka matsa Malam ni ina da abinyi" "Zan masa amma se kin mun abu uku, firstly ki amsa sallamata dan wannan dolene a musulunci kinsani then you tell me your name, lastly you give me your digits" ya ƙarasa yana irgawa da yatsunsa. Harara ta galla masa amma yanda ya bake hanyar tasan ko tureshi tace zatayi ko gezau bayi zeyi ba kuma duk inda tayi binta yake wannan yasa ta amsa masa sallamar a ƙufule tana cewa "Se ka matsamun na wuce Malam tunda na amsa maka sallamar ai" "Ai baki cika sauran sharuddan ba" ya sake faɗa se tayi saurin tareshi da cewa "Nayi wanda zan iya" "Baki isa ba, na miki rangwame cikin biyu you choose one, either you tell me ur name or you give me your contact, barshima, bari sunan, bani number kawai" ya faɗa yana miƙa mata wata tsadaddiyar waya da bata taɓa ganin irinta ba. Ta harareshi taa harari wayar tana cewa "Ashema kai zaka zabarmun abinda zanyi? To sunana Afeeya, dan girman Allah ka matsa ka bani hanya dan ka rigada ka makarar dani" "Kince Allah wuce Afeeyah, suna me kyau kamar yanda kike da kyau" ya faɗa fuskarsa ɗauke da murmushi ya harɗe hannaye a Ƙirji yana jifanta da wani kallo. Tuni tayi masa nisa, a jikinta taji har sannan yana biye da ita bata waiga ba har ta shiga Department dinsu ta sauke numfashi ganin yan Ajinsu a waje suna hirarraki alamar Malamin bezo ba, ba tareda ta tsaya ba ta shige ciki abunta dan zuciyarta wani bugu take kamar wadda tayi tseren gudu. Ta wutsiyar ido ta kalli window inda taji alamar idanun mutum akainta, yana nan tsaye kuwa ya harɗe hannayensa a Ƙirji damatsansa sun ƙara fitowa kamar an aje duwatsu se tayi sauri maida kainta kan desk tana jin yanda zuciyarta take tsere, bata dade da zama ba Malamin ya ƙaraso, ya ringa zabga dictation suna rubutawa ajin awa biyu ne amma tsabar mugunta ya roqi next Lecturer da ze shigar musu ya ara masa lokacinsa tun takwas da wasu mintina bamu muka samu kanmu a hannun Dr Abolude be barsu ba se sha biyun rana zuwa sannan hannun kowa ya sage nata kam har sun kumbura gefen inda take riƙe da biro sunja ruwa daman haka yake mata duk sanda tayi dogon rubutu tofa se tayi jinyar hannu abinka da Jiki duk Madara inji Qawayenta. Taimakon da Allah yayi musu da yace ba lokacin ze karbi note din ba Class rep ya hada ranar Wednesday ya kai masa kuma shine CA dinsu, tayi hamdala a fili dan rubutun nasu rabi da rabi tayi, idan tayi nata se ta kama na Badar duk a tsoron kar a tashi karɓa ta rasa gara ko yayane dai ta rubuta mata wani abu. A mugun gajiye ta wuce Geography mosque dan Azahar ta kawo kai gara ta tsaya tayi sallah kafin ta koma Hostel ta ɗan kwanta zuwa La'asar suna da wani Ajin. Seda tayi alwala ta shiga cikin masallacin tayi Nafila raka'a biyu kafinta nemi guri saitin fanka ta kishingiɗa tana jin kamar tayi bacci saboda gajiya ga bashin na daren jiya da batayi dakyau ba. Wayarta ta shiga Vibrating ta janyota daga cikin jaka, gaba ɗaya ta sha'afa da ita. Tun gurin ƙarfe Tara an kikkirata dukda bata duba ba tasan baze wuce Ahmad bane me kiran yanzun ma tana cirota kiran nasa na tsinkewa a nan taga missed calls ɗin daya mata guda biyar se Message da yake tambayar lafiya yana ta kiranta bata amsa ba idan tagani ta kirashi. Tayi ƙaramin tsaki da batasan dalilin yinsa ba kafin ta danna kiran layin nasa ringing biyu tayi ya katse se gashi ya biyo baya dukda uban katin wayar da yake loda mata duk satin duniya amma idan ta kirashi baya ɗauka, ire iren halayensa na kyautatawa da suke son tursasa zuciyata sonsa kenan badan ta aminta dashi ba har ƙasan rainta. Cikin muryarsa me sanyi amma ba kamarta mata bafa Aa irin ta Mazajen da hayaniya bata dame su ba yayi mata sallama, ta amsa kafin ta gaishe shi wannan tarbiyyar Ummansu ce gaisuwa ga duk wanda ya girme su ta kuma rigada ta zame mata jiki. "Fatima! Lafiya ina ta kiran wayarki tun da safe baki ɗauka ba?" Ya faɗa bayan daya amsa mata gaisuwar. Taja numfashi saboda Fatiman daya kirata, bata so amma ta rasa ta yanda zata gayawa Ahmad ya dena. Sunan Innar Baffansu ce kuma sunan Kakarsu data haifi Ummansu sannan Babbar Yayar Baffansu wadda ita ta riƙeshi itama sunanta Fatiman. A hannunta ya girma bayan rasuwar Iyayensu, su uku kacal suka haifa daga Ita se shi se ƙaramar ƙanwarsu Umma Halima ita Umma Faɗima wadda ta riƙe Baffa ta girme musu sosai dan shekaru bakwai ta bawa Baffansu shi kuma ya bawa Umma Halima shekaru biyar, wannan tudu ukun da naci na sunana FATIMA yasa kowa yake jin nauyin faɗarsa se AFEEYAH Laƙabin da Baffa ya bata ko a makaranta a rigister kaɗai ake kiranta da Fatima amma kowa da AFEEYA ya santa banda Ahmad da bata tsammanin ma yasan ana Kiranta da Afeeyah. "Kinyi shiru, kina jina kuwa?" Ya sake faɗa abinda ya maidota daga tunanin data tafi ta sauke numfashi kafin tace "Ina jinka, ina Class tun 8 bamu jima da fitowa ba na shigo masallaci kenan daman yanzu nake so na kiraka" tayi masa ƙarya badan tana da niyyar kiran nasa ba. A tausashe ya sake ce mata "Ayya sorry love, gaskiya Malaman nan suna wahalarmun dake da yawa amma kun gama gaba ɗaya yau koh?" "Aa fa ina da wani Ajin 4-6 ma" tabashi amsa, cikin jimami ya sake cewa "Toh Allah ya bada sa'a, in sha Allah kamar yau ne zaki ga kun gama ai sedai ki ringa tuna baya kina kewa. Nima daman ɗazun na shigo Zaria na ɗauki Jafar yanzu haka ma muna hanya zan kaishi Abuja ze koma London. Naso mu haɗu amma babu komai in Allah ya kaimu se Wednesday zan juyo ko Thursday zan tsaya kafin na wuce Kano na ganki. "Allah ya tsare hanya ya maido da kai Lafiya" ta faɗa, cikin tsokana yace "Shifa Jafar, baki yi masa Addu'a ba? Ko na bashi wayar ku gaisa harda ma fa saboda shi naso mu haɗu yau dai Abokanan faɗa suga juna" Cikin sauri tace "Allah ya kiyaye ko Inuwarsa bana fatan Allah ya nunamun ballantana wai mu gaisa dashi, idan so kakeyi na sake faɗa maka na tsaneshi fiye da yanda yake tunanin shi baya sona" cikin tsiwa take maganar tareda fushi tana tuna kalaman Jafar ƙanin Ahmad, shekara guda kenan amma ta kasa manta abinda yayi mata. Murmushi Ahmad yayi haka kuma ta jiyo wani dogon tsaki daga cikin wayar wanda ta tabbatar da Jafar ɗin ne yayi ai ko a fusace ta ɗaga murya tace "Allah ya tsinewa tsaka ma ballan tana kai abin banza" "Fatima" Ahmad ya kira sunanta se tayi shiru amma bata amsa masa ba yaci gaba da cewa "Ni nake Driving, idan na isa zan kiraki Ok?" "Allah ya tsare ka kula mun da kanka kaji" ta fada bawai har ranta ba sedan tabbatarwa da tayi wayar a speaker take kenan tunda yace shi yake tuƙi Jafar yana jin duk maganar ta keyi shi take so ta bawa haushi". "I will, you take care too I love you" Ahmad ya sake faɗa tana jiyo Jafar ɗin cikin fushi yana cewa "Wlh Yah Ahmad either you cut this call ko kayi dropping nawa a nan, da wata muryarta ta Villagers ko Turanci bata iya ba" "Tunda ba karatun fatiha na kasayi ba ai da sauƙi, kaida Turancin yake yaran Babarka ai se kayi tayi" ta faɗa bata jira amsarsu ba ta kashe wayarta tana jan tsaki daidai nan kuma aka fara kiran sallah. Fita tayi ta ɗaurayo bakinta ta dawo ranta na suya, Bata taba haɗuwa da mutumin dayaci mutuncinta yaci na iyayenta irinsa ba ita kuwa bata da babban maƙiyi daya wuce wanda yace ze keta Alfarmar iyayenta a duniyar nan, za'a iya takata ta shanye amma fa kar a taɓa mata Iyaye Jafar kuma ya keta wannan Alfarmar ya zagesu shiyasa bashi da sauran mutunchi a idonta balle ta raga masa. Shi kansa Ahmad ɗin Alfarmar Baffanta yaci da har taci gaba da kulashi dan yace ba laifin Ahmad bane ba ba kuma shi ya saka Jafar yayi abinda yayi ba dan haka ko a gurin Allah laifin wani baya shafar wani ta haƙura taci gaba da saurararsa amma wannan dalili yasa karɓuwar daya fara samu a gurinta a baua ta wargaje kuma har zuwa yanzu tsayin shekara daya da faruwar abun ta kasa mantawa haka zuciyarta ta gagara yarda da Ahmad ɗari bisa ɗari har yanzu. Tana tare dashi ne kawai saboda karamcinsa amma a kullum cikin addu'ar Allah ya fiddo mata da Miji daidai da ita takeyi ba zatayi ɗage ba ta kai kanta inda bata isa ba domin daga abinda Jafar yayi mata ta saka a rant tana tareda babban Ƙalubale idan ta shiga zuri'ar su Ahmad domin ba ƙarya Jafar yayi ba ya faɗi gaskiya ita ɗin dasu akwai banbanci, tazarar dake tsakanin su tamkar ta sama da ƙasa ce ta fito daga gidan Talakawa amma masu wadatar zuciya, Babanta Bakanike ne Ummata kuma Tela ce basu da wani gata sena ubangiji saɓanin su Ahmad da suka fito daga babban Ahali tana nufin gidan da aka tara Arziƙi na Kuɗi dana Zuri'a, Mahaifinsu Babban Attajiri wanda duk mutumin daya kwana ya tashi a Nigeria baki ɗaya yasan sunansa. *ALBISHIRINKU MATA YAN UWANA YAN KWALISA NAZO MUKU DA WANI DADDADAN LABARI!!!.* *NASAN KUNDADE KUNA NEMAN FITACCEN GURIN DAZAKUJE AMUKU GYARAN GASHINKU DANA JIKINKU CIKI DA WAJENSA,TO YANXU DAI GA DAMA TA SAMU...* *LABARI NAKE BAKUFA AKAN AFINTY QUEENS SHAHARARREN SHAGONMU NA SALOON DAYA HADA KOMAI DA KOMAI DA KOWACE MACE YAR KWALISA IRINA KE BUKATA,SANNAN MUNADA KWARARRUN MA'AIKATAN DASUKASAN KAN AIKINKINSU,KUZO AFINTY QUEENS KUBIYA KUDI MUKUMA MU BATA LOKACINMU DOMIN TSATSTSAFO DUK WANI KYAWU NA JIKINKU DA ALLAH YAYI MUKU...* *A AFINTY QUEENS MUNA AYYUKA KAMAR HAKA:* *- HAIR SALOON* *-HENNA* *-SPA* *-DUKKAN* *-PEDICURE* *-MANICURE* *-SANNAN MUNA DA TURARUKA IRIN NA AMARE YAN MATA DA KUMA MAI KANKAT DAN UWAR GIDA TA TURARA GIDANTA JIKINTA DAMA KAYAN SAWARTA ITA DA YARANTA,,HARMA ZAWARAWA DUK MUN TANADI KOMAI* *DOMINSU SUMA* *-MUNADA SHOES AND BAGS SBD ISASSUN MATAN DA SUKA AMSA SUNANSU MATA*😊 *- MAKEUP NA BRIDAL ND CASUAL...* *IDAN KINSAN KINAJIN LABARIN SHAGON SALOON NA AFINTY QUEENS AMMA BAKI TABBATAR DA YADDA AIKINSU YAKE BA TO YAR UWA GADAMA TASAMU MEZAKI TSAYA JIRA MAZA KEMA KI ZARGAYO SHAGONMU DAZAN JERA MIKI ADDRESS DINSHI A KASA DOMIN KEMA KI TABBATAR DA KALAR IRIN NAMU KWAZON DA MUKA KWARE AKANSHI GURIN GYARAN JIKIN YAN UWANMU MATA KUMA MUKE GABATAR MUSU DA JAKUNKUNA DA TAKALMA HARMA DA TURARUKAN WUTA DANA SHAFAMA JIKINSU DON NISHADIN ZUCIYARSU DANA MAZAJENSU....* *AFINTY QUEENS DISCOVER BLISS IN BEAUTY 💅💯* *Address 👇👇:* *KU ZIYARCE MU A SHOP NO.9&10 SHEMA PLAZA,BEHIND SHEMA FILLING STATION KASUWAN BACCI KADUNA* *TEL:08133379628.* *MATAR MUTUM* *NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER* *FIKRA WRITERS ASSOCIATION* *LITTAFIN KUDI NE* *PAY 500 A ASUSUN* *7061838488* *OPAY DIGITAL SERVICES* *MARYAM FAROUK* OR *0709290797* *ACCESS BANK* *SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488* *IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705* *Kuyi following dina a Arewabooks @Maryamfarouk01 inda zaku karanta wannan littafin tareda sauran littattafaina* *NAGODE* *BOOK 2* *PAGE 9* Bayan ta idar da sallah tayi addu'a tana shirin tashi Maman Minal ta shigo masallacin, Roommate ɗinta ce dan haka ta dakata ta jirata tayi sallar itama kafin suka rankaya Hostel. Tana hango Senate Building Gayen ɗazu daya tareta ya faɗo mata a rai, taɓe baki a fili tace "Wani sangangan dashi kamar basamude, kai wannan duk yanda akayi ya hada jina ma dasu" "Suwa?" Maman Minal ta tambayeta seta tsuke baki tana cewa "Ai yau gamo nayi da safen nan in gaya miki" ta kwashe da dariya tace "Gamo Afee, na Aljani kona soyayya?" "Mutum Aljan dai, wani fa sangamemen mutum in gaya miki, wlh gani na nayi a gabansa kamar nida Ruth, kofa fuskarsa bana iya gani sosai saboda yanda yayi sama da yawa". Tsabar dariya seda Maman Minal ta kware ta dage Niƙab din fuskarta dan tasha iska sosai idonta cike da hawaye tace "Kinga kin sakani irin dariyar da babu kyau meye kuma Mutum Aljan ana zaune lafiya? Inaga irin yan Basketball ɗin nan kika gani sune zabga zabga ni jiya da daddare da naga wani Yaro seda gabana ya faɗi, kinga tsayi? gashi siriri kamar ze tsinke". "Wannan ba siriri bane gaskiya yana da yar ƙiba badai sosai ba amma fa dogone yanda kika san jinjirin samudawa" ta sake faɗa tana hakaito Jay a zuciyarta. "Allah ya shiryaki dai Afeeyah a ina ke kika taɓa ganin jinjirin samudawan toh da har kike kiran wannan haka?" "To dai yau na ganshi, Allah yasa mu sake haɗuwa zan muku video sa ku gani" ta sake faɗa tana Ƙoƙarin zaro Id card suka shiga hostel. Sururat na maida shinkafar data tace cikin tukunya sukayi sallama, ta amsa tareda watsawa Afeeyah hararar wasa setaa ajiye jakarta akan gadotna tana cewa "Whats up my love?" "My dear, if u like call me Shahrukan but you must wash this plates" muka kwashe da dariya harda ita da tayi maganar Maman Minal tace "Ƙarshen love kenan ba, amma dai a mata haƙuri ta huta yanzu, kinga duk ta rigamu fita da safe" "Wlh Anty Zarah na you dey spoil dis girl, haba yarinya se gaye cinguli work she cannot do" Sururat ta cigaba da Mita, Afee ta rungumeta ta gefe tana dariya tace "Haba sisi na kinsan fa zan wanke yanzun haka wlh kaina ciwo yakeyi, we had a boring class and i still have one more to go" mtsw tayi ƙaramin tsaki danda gaske kan nata ciwo yake mata. Fuskarta Sururat ta nuna tausayawa kafin tace "Eyya, let me finish cooking then you eat and get some sleep you will fell better, sannu kinji". Afee ta wuce gaban gadona ita kuma taci gaba da hada Salad ɗin da takeyi, kayan jikita ta cire ta daura Zani harta zauna kuma kawai ta ɗauki Hijabi da Jakar kayan wankata da Bucket daya ta sauka ƙasa. A bathroom ɗin down floor tayi wanka ta ciko bucket da ruwa ta koma lokacin har Sururat ta gama abincinta zuba musu a babban Try kamar yanda suke ci yawanci idan kowa yana ɗakin yau su uku Badar na Kaduna tasan dai tana hanyar dawowa Ummi kuma se Five zata gama Lecture, Ruth tana kan gadonta duk yanda suke janta a jiki da nuna mata an zama ɗaya takan kama kanta musamman irin lokutan da suke cin abinci sedai ta ɗibi nata a plate daban amma ba zataci dasu ba. Tsaf suka cinye abincin data saka musu suna santi dan Sururat ba daga nan ba gurin iya girki, ta wuce wanka da sauri dan tana da aji ƙarfe biyu ita kuma Afee ta tattare gurin ta haɗe kwanukan dattin duka a bokiti ta sauka dasu ƙasa. Wata Mama da take kai munu ruwa da wanke wanken wasu lokutan n Ta bawa kwanukan na koma ɗaki. Maman Minal tace mata "Afee bari naje dakinsu Nnenna mu Ƙarasa Assignment ɗin nan" "Sannu Eng girls" ta faɗa tana hayewa gado. Tana ganin Ƙoƙarin Maman Minal wato Anty Zahra, Mechanical Engineering take aji biyar. Matar aure ce harda yaranta uku kuma da auran nata ta fara karatun lokacin tana da cikin fari gashi a shekara hudu tayi yaya uku kuma cikin luɗufin ubangiji bata taɓa samun carry over ba Allah ya taimaketa ya bata Miji me fahimta da son tayi karatun duk dashi ba dan boko bane hasalima iyakarsa secondary school amma be tauyeta ba kuma iyayensa sun bata gudummawa Yaranta uku duk a hannun uwar Mijin suke yanzu da sun shekara zata ce ta yaye su taji da karatunta suna can Kaduna ita kuma ya kama mata daki a Off K tun Level one ba kuma ya gajiya da kawo mata ziyara A final year din nan ne ta dawo cikin makaranta gaba daya da zama kuma a nan suka haɗu ɗaki ɗaya da ita sedai idan Mijin zezo ne zata buɗe ɗakinta na Off K ko idan matsalar rashin ruwa ko wuta ta faru a cikin makaranta zasu tafi can duka. Ita ce ta zama Kamar Babbar Yayarsu duk abinda taga zasuyi mara kyau zata tsawatar musu tsakani da Allah take zaune dasu shiyasa suke bata girma sosai. Bata san tayi bacci ba seda Ƙarar Alarm data saita ta manta wayar a saitin kanta ya tayar da ita, a firgice ƙiris ya rage ta faɗo daga gado. Ta ringa tsaki kamar wani ya aje mata wayar, ganin tsakin baze kai ta ba ta miqe. Duk sun fita se ita kaɗai ashe, a gurguje ta sake watsa ruwa saboda yanayin garin da akwai zafi tayi Alwala, Riga mara nauyi me spagetti hannu ta saka ta zame ribbon ɗin kanta, tafi kwana uku bata taje kan ba sedai ta saka hannu ta warwareshi dan bata son jan gashin ta koda kanta ne balle wani yaja mata shiyasa bata kitso ta kwantar sa gaban da bruah kafin ta saka Chantilly cap ta zura Jilbab kalar Maroon me duhu tun wanda Ahmad ya bata haɗuwarsu ta farko, Son Hijabin take kamar rai, dukda ya sake siya mata wasu har Number matar da takeyi wato *UMMU MAHEER 07061838488* Ta karɓa a gurinsa saboda duk wanda ya gani se yace yadin masa kyau a ina ta siya shine kawai Ahmad ya bata shawarar ta fara siyarwaq sosai kuma take cinikin Hijaban a cikin Campus. Ta kalli kanta a Mudubi, gani tayi tayi haske fau da yawa kamar wata Zabiya yau hakan yasa tayi saurin cire Hijabin ta lalubo wani Fari ta saka, Badar ta tsani Hijabin, na Anty Sauda ne da tayi Umarar Azumi dashi ta karbo duk sanda ta saka se Badar tayi tsaki tace "se kace fatalwa" ita kuma son Hijabin takeyi. A gurguje ta fita, tana shirin kulle Ƙofa Badar ta hawo saman da ubannin ledoji tana nishi, ta banka wa Afeeyah Harara ita kuma ta fashe da dariya saboda yanda ta rungumo kaya kamar irin haɗamammun Yaro boys da ba zasu bari wani ya samu ba mayafin tama a Ƙugu tayi ɗamara dashi. "Dole kiyi dariya mana tsabar rashin mutunchi ashe kina nayi kiran wayarki yafi sau nawa baki amsa ba" ta fada tana zube kayan a bakin ƙofar. Ta buɗe mata ƙofa tace "Wlh banji ba ina ta sauri karna makara me yasa baki ƙwalo mun kira daga ƙasa ba to se nazo na tayaki" "Na gama shan wahala tun daga Bakin Hostel se na tsaya wani jiran ki dallah gafara na wuce" ta faɗa tana tureta, Badar rigima, ta matsa mata ta shige ita kuma ta ajiye jakarta ta fara shigar mata da ledojin tana cewa "Sannu da hanya, da naji shiru na zata ma se gobe zaki dawo". Kayanta ta shiga cirewa tana cewa "Neman magana dai, kwana biyun ma kamar Momy zata cinyeni kinsan da yanda ta barni na kawo yau da cewa tayi jiya komai dare se na taho ai" "Allah sa ba tayi fushi ba da banje ba?" Afeeyah ta faɗa tana aje ledar ƙarshe se Badar ta zare ido tace "Ai gara da bakije ba, inaga da muna shiga zata ce mu juyo, ƙarshe ma gori na jawa kaina tana cewa ita so tayi ta haɗa mu dukka ta huta shegen baqin jinina yasa seta sake kashe kuɗin kama gurin biki daban harda fa cewa ƙawayenta wai idan sunji wani na neman mata gani". Afeeya ta dinga kyalkyala dariya har seda taazauna, wato Momyn su Badar character ce me zaman kanta matar nan ga kirki ga zafi babu abinda ya shalleta tas zata maka akan gaskiyarta. Seda ta gama dariyar ta miƙe tana ce mata "Toh na Jira ki ko na tafi?" "Ai ko HOD ne zeyi Aji yanzu dai ba zani ba wlh gara ma ki tafi kya samu ki mana Attendance" ta bata amsa tana zuba ruwa a bokiti Afeeya ta fita a ranta tana mamakin Yau batayi mata Ba'ar Farin Hijab ba ilai huwa se ji tayi tace "In kika mutu a hanya an huta nemo likafani kaiki kawai za'ayi". Minti Arba'in Lecturer yayi ya sallame su saboda duk kusan sunyi covering komai sati biyu ya rage musu su fara Exam. Surayya Mas'ud ta jata Ribadu Hall dan taga Babynta, ta haihu sati uku kenan yau ta fara shigowa Lecture ta bar yaron gurin sister ta acan suka shantake har akayi Magriba kafin suka fito tare Mijinta yazo daukarta ita kuma ta shiga Amina. Tun daga staircase ake jiyo kayaniyarsu Sururat da Badar haka suke kullum basa gajiya da magana kamar Aku ta shiga da sallama ashe video kayan Lefen Anty Yusra Yayar Badar suke kallo, dalilin zuwanta Kaduna kenan ta cire Hijabita ta ninke itama ta shiga kallon, Anty Yusra tasha kaya, ko da yake abu ne irin nasu na kwarya tabi Kwarya, Babansu Badar Ex Senator, zaben da ya gabata ya sauka Baban Angon ya karɓa. Suna kallon suna cin abunda Badar tazo musu dashi da suka gama ta koma kan gadonta ta kira Baffanta. Cikin shaƙuwar dake tsakaninsu suka gaisa, yace mata "Mamana ya makatanta ya karatun? Babu dai wata matsa ko?" Safe da yamma idan sukayi waya seya tambayeta haka, Yanda Baffanta yake sonta yasa take jin zata iya sadaukar da komai sabida shi. "Komai Lafiya Baffa, baka koma gida bane har yanzu naji ƙarar babura?" "Ban koma ba yanzu dai nake shirin tafiyar, kinga Yayanki ya turo miki kuɗi ko? Kiyi haquri da abinda ya samu abinda nake ta jira a biya ni ne har yanzu shiru lamarin ƙasar se Addu'a kuɗi sunyi wuya a hannun mutane ga Yayan naki shima komawarsa Makaranta ya tashi shiyasa nace ya raba wannan ya tura miki idan yaso in Allah ya yarda wasu suka samu se a sake aiko muku" "Babu komai Baffa sefa da nace maka ma ka barshi ina da komai kudin ma akwai canji a hannuna zasu isheni har zuwa sati hudun amma kaƙi yarda da ka barwa Yah Jafar ɗin duka yafini buƙata" ta faɗa cikin muryar shagwaɓa. Baffa yayi murmushi yace "Ba wani nan na sani ko baki da komai ba zaki faɗa ba ni kuma haƙƙi nane dole nayi miki fatana dai kiyi karatu dukda bani da haufi akanki amma ina sake jan kunnenki da ki tsare kanki ki kuma tsaya iya inda Allah ya ajiyeki karki ringa hangen wasu da suka fiki ko kiyi sha'awar abinda suke dashi rayuwa mataki ce wata rana idan da rabo se kiga kin kamo su". Ta haddace wannan kalamanna Baffa, shekara uku ke nan tunda taa shiga Jami'a kullum sukayi waya se yayi mata takararsu. A sanyaye tace "In sha Allahu Baffa ina kiyayewa kuma zanci gaba da kiyayewa" "Yauwa Mamana Allah yayi miki Albarka, ina Badariyya yau ban jiyo karaɗinta ba" Baffan ya sake fada nayi murmushi nace "Gata nan Baffa bata dade da dawowa daga Kaduna bama an kawo Lefen Yayarta jiya ɗazu ta dawo ta kawo mana kayan dadi" "Aiko naji zancen gurin Ummanku tace nan da wata biyu ne auranko? To Allah ya sanya Alkhairi yasa zamu ga lokaci in sha Allahu idan na samu dama nima zanje musu ɗaurin aure saboda kirkin mutanen da yanda suka riƙeki ba wanda zaka yanke zumunchi dasu bane kice ina gaisheta ina mata ya hanya" Kafin ma Afeeya tayi maganar Badar ta wafci wayar dan tunda ta kira sunanta ta miƙe. Ta gaisheshi ta ringa washe baki tana cewa Amin kafin ta miƙa mata wayar har sannan bakinta a buɗe, sukayi sallama yace ta gaida sauran yan ɗakinsu. "Muguwa da zaki mun buƙulun gwalagwalan addu'oin Baffa" ta faɗa bayan data kashe wayar. Zata bata amsa Anty Sauda ta kirata dan haka ta dakata ta ɗaga da sallama kafin ta shiga tsokanarta tana cewa "Amarya uwargidan Alhaji Ali, kin tare gaba kin tare baya" "Faɗi ki ƙara dagani babu wata" ta baya amsa ta tabbata tana can tana fari da ido irin yanda take duk sanda tayi mata kirarin. Dariya sukayi kafin na gaisheta ta amsa tana tambayata makaranta. "Ina Mutumina Mahfuz? Banji Gwarancinsa ba yau?" "Suna gida, nazo Marmara ne, bikin Ƙanwar Baban Aziza za'ayi wannan satin dan wulaƙanci basu kawo mun Anko ba se ɗazu shine na kawowa Umma kuma ranar Laraba za'a saka" "Tofa, seta zarga miki ko Bubu ce ai ina Umman har yanzu ba'a gyara wayarta ta bane?" "Me gyaran yace ya gama kuma Jafar ya koma makaranta ɗazu be karɓo mata ba, ina Badar?" Anty Sauda ta faɗa seta bawa Umma wayar tayi sallama da Hausarta da yau bata saisaita ba, Buzanci ya cinye harshen nata sama da shekaru Talatin da Baffan ya aurota ya kawota Nigeria amma Hausa ta gagara kama harshenta dakyau. Bayan sun gaisa da Umma itama ta sake mata jan kunne akan ta kula da kanta kafin tace na gaida Badar da sauran Roommates ta maidawa da Anty Sauda wayar. "Naji Umma tace kince se kunyi hutu zaki dawo, bikin Zuhran Umma Halima fa saura sati biyu, ba zaki zo ba?" cewar Anty Sauda. Afeeyah ta gyara kwanciya ta ce "Saura sati biyu mu fara Exam kinga satin bikin kenan zan mata addu'a daga nan Allah sanya Alkhairi" "Kedai dan bakwa shiri ne kawai amma nasan da Zainab ce ko jarabawar kike sekin zo ai" "Zainab kikace ai, Yah Zuhra kuwa ko ina Kano be zama lallai naje bikinta ba wlh" "Allah ya shiryeki da ruƙo Afeeya ke abu baya taɓa wucewa a gurinki ne wai?" Cewar Anty Sauda. Afeeya ta tunzura baki kamar tana gabanta tace "Ai wlh duk wanda ya ci mutunchin iyayena ko bayan shekara dubu bazan yafe masa ba balle mu'amalar arziƙi ta haɗani dashi" ta faɗa cikin jin zafin abinda Itama Zuhran tayi mata, faɗe ya haɗo su ta zageta tace mata dangin Sadaka Yallah, kuma ai ba ita ta zaga ba da Ummansu take tunda itace Buzuwa daman kuma kullum idan tsiyar Babarta Umma Halima ta tashi da haka take zagin Umman tasu dan basa shiri, tunda aka aurota bata sonta a yanda sukaji wai da Aminiyarta Baffa yake so tunda ya tafi fatauci Nijar can ya hadu da Ummansu a hannun Mahaifinta ya zauna shikenan daya dawo yace ya fasa auran Ƙawar Umma Halima wannan ya Ƙulla gaba tsakaninta da Ummansu har yau kuma dukda abin yayi sauƙi saboda girma da shekaru amma bata fasa rashin idan rashin mutunchinta ya motsa seta mata gorin cewar tunda aka aurota maimakon Baffa yayi gaba tsiyacewa yake wai yanda take fara tazo musu da farar Ƙafa. Sallama sukayi tana cire wayar daga kunnenta kiran Ahmad ya sake shigowa. Tun tana wayar takejin alamar wani kiran, ta yatsina fuska kafin ta ɗaga ita wlh ta manta ma shaf tace zata kirashi ɗazu. Kamar ko yaushe cikin taushi yayi mata sallama ta amsa tareda gaisheshi sannan tayi shiru. "Baki kirani kinji ya na sauka ba" ya faɗa a sanyaye, ta sauke ajiyar zuciya tana jin babu daɗi a ranta tace "Kayi haquri, bacci nayi, ina tashi kuma kasan na gaya maka ina da class ɗin yamma na dawo kuma ina ta zuci zucin na kiraka na manta wlh" "Kullum dai uzuri Fatima, Allah ya nunamun lokacin da zanyi matsayi a zuciyarki da zaki dena mantawa da al'amurana. To ya makarantar? Ya lecturer? Badar ta dawo?" Kunya ta kamata jin abinda yace kuma beyi fushi ba, tace "Lafiya lau, Badar gata nan ta dawo tun da yamma". "That's great, my regards to her, ki gaya mata idan dawo tare zamuzo da Bukar Babagana, friend ɗina da nake gaya miki surutunsu ɗaya". Ta guntse dariya tana kallon Badar kamar yanda ta tattara hankalinta akanta itama yanda kasan an bata ajiyarta in har auna waya da Ahmad ta ringa matsarta kenan seta tabbatar da batayi wani abun rashin kyautawa ba, ko bata faɗa masa maganar soyayya me daɗi ba dai to ba zata bari ta faɗi wadda zata bata masa rai ba. "Zan gaya mata, kace na tanadi earpiece Aku biyu zasu haɗu ranar bazamuji kunne ba" ta faɗa tana fashewa da dariyar dan ta kasa ruƙuwa. "Nidai babu ruwana bani na faɗa ba" cewar Ahmad shima yana dariya kafin ya sake cewa "Baki tambayeni Jafar ba, jirginsu ya tashi babu jimawa yanzun nan ma na koma Hotel room" "Ayya" ta faɗa a fili a zuciyarta kuwa tace "Da shi kaɗaine a jirgin Addu'a zanji ya kife kowa ya huta da baƙin halinsa ai" Ahmad yace "Ayya kawai zakice? Ba zaki masa fatan sauka lafiya ba jini nane fa Fatima". Kafinna tashi amsa wayar tayi din din alamar shigowar wani kiran, na cire daga kunnenta ta duba sunan Bestie ne yake yawo se ta maida ita kunne tana cewa "Amm, Umma tana kirana bari na amsa idan na gama zan kiraka" "Muyi sallama kawai dan nasan da wuya ki kira, in kuma Allah ya dorani akanki yau kin kira i will be more than happy dan ina so nayi magana dake sosai, i really missed you Fatimaa" yaja sunan nata. Ƙirjinta ya buga, bata so ya ringa wani langwabewa yana mata magana hakan ze saka ta iya narkewa na fara sonsa dan ita ɗin son soyayyane da ita kamar wata India. Yanda take hasaso Mijin da zasu zuba madarar ƙauna ne Sam Ahmad bezo da cikakkiyar suffar ba. Tana lissafin Namiji dogo me ƙirar ƙarfi a matsayin Sharukhan ɗinta, wanda ya iya tarairaya da kalaman soyayya masu saka jinin jiki ya tsaya, irin mazan nan da kallonsu kaɗai ze saka kaji zuciyarka ta motsa ko bashida sisi zata zauna dashi zata masa komai indai ze ringa kasheta da ƙauna yana dagata sama kamar yanda akeyi a India, ya ringa saɓarta kamar jaririya yana goyata Mafarkinta kenan na Abokin rayuwa. Ahmad nada dukka suffofin datake so ta bangaren iya soyayya da tarairaya uwa uba akwai canji a hannunsa burin yammatan zamani Yaro da kuɗi sedai a gurinta ya rasa wani kaso me muhimmanci wanda take nema. Ƙaramin ruwa gareshi, dukda ba gajere bane dan idan suka jera ya kereta dukda tana da tsaho amma rashin ƙibarsa yasa sam bashida kwarjini idan ka ganshi zaka zata befi irin shekara Ashirin da uku zuwa da biyar ba a hakan wai talatin yake. Da ace yana da Dan Jiki koda tsahonsa be kai yanda take so ba zata iya Manaji dashi ko dan tarin kirkinsa. Jinjirin samudawan da tayi gamo dashi yau ya faɗo mata a rai, seta zaro ido a ranta tace "Aa ba kamar wannan ba, ai idan ya samu mace ballata zeyi tas a rasa me ɗorata yayi girma da yawa". "Fatima" Ahmad ya kira sunanta da ƙarfi daya maidota daga duniyar wasiƙar jakin data tafi. "Inata magana kinyi shiru, lafiya kuwa?" Ya tambayeta seta diririce nace "Yi haquri network ɗin ne ya ɗauke banajinka" "To na jiraki ko nayi bacci?" Ya sake faɗa a sanyaye, kiran da Nurain yake ta dokowa kamar Wanda yazo karbar bashi yasa tayi saurin ce masa "Ka kwanta to zan tasheka to idan na gama dan akwai Assignment ɗin ma da zanyi idan na gama wayar" se yayi dan murmushi yace "Shikenan toh, ki gaida Badar" "Zataji" ta bashi amsa tana zare wayar daga kunnenta taji ya jefo mata da I lobiyu harda wani kiss me ƙara daya sa tsigar jikinta zuba, da sauri ta katse kiran tana sauke numfashi wayar Nurain ta sake shigowa ta daga a tsiwace tana cewa "Ni wai Nuraini bashin ko tara da kake faman kirana se kace zan gudu?" Yar banzar dariyarsa me kama data yara yayi kafin yace "Hey hey relax, dawa kike ta waya ma dai da farko na miki over ten missed calls kika ƙi dagawa?" "Toh ubana Hafizu Mu'azu" ta faɗa, ya sakeyin dariyar dake ƙular da ita yace "You are my ward, dole nasan duk wasu whereabouts dinki dan haka just tell me dawa kike waya ko yanzu na kira Baffa na gaya masa kina waya da daddare while ur mates are there in class reading" "Kai ai tutorial kakeyi a nan inda kake ko? Dan Allah barni haka meye kake ta kirana ma?" Ta dakatar da jan maganar sa dan se a kwana anayi. "I'm missing you ne kawai nace bari nazo naga Bestie na, har na shiga Geography na fito na manta yau kince ba zaki fita karatu" Nurain ya faɗa seta duro daga gado tana cewa "Awwn, dagaske kayi missing ɗina?" "Kinsan ba wasa nake ba, saboda ke na shigo school. Ina mutuniyata i missed her also ina white sit ku fito muyi hira mana". Kusada Badar ta zauna ta tureta tana jan tsaki tace "A nan kike rawar kai da ƙafa kan ƙananan yara da ba'a dena basu pocket money ba, saboda Nurain kika kashewa Ahmad waya, ji yanda kike wani lanƙwasa murya kina wani cewa you missed him but you can't talk to ur responsible boyfriend with affection Allah yasa ki gane idan kina da rabo tun kafin lokaci ya ƙure miki". Indai Mitar Badar ce sun haddace akan Ahmad, sonsa take kamar Ƙanin Momy koshi baya jin zafin abinda Fatima take masa kamar yanda Badar takeji. "Bata wayar" Nurain yace mata. Ta san ba zata karɓa ba dan haka ta sakata a speaker "Badar my love" ya faɗa ta harari wayar tana cewa "Don't call me that" "Haba my heart, kin san fa ina sonki kece dai kike mun wulaƙanci ni yanzu ma ke nake son gani nasan na kiraki zagina zakiyi shiyasa na kira wayar Bestie, taimaka ki fito naga chocolate face din nan taki ko na samu karatu ya zauna a kwakwalwata ga saƙonki ma na fito dashi yau". "Hummm, sedai ka yaudari wata badai ni ba marowacin kawai, aron baci ba ka bani abu amma ka hana" "Allah dagaske nake gashi nan yau na kawo miki" ya sake faɗa yana dariya, Badar tayi Ƙwafa kafin tace "Wlh idan ƙarya kake gaban Amina yayi mana kaɗan sedai a kaimu security office dan tsalle zanyi na falla maka mari" "Gara da kikace se kinyi tsalle, my love yi maza kizo zuciyata harta fara narkewa, i can't wait ta see you" ya sake faɗa ze kashewar tace "K dena murna se ka siya mana Mac dee da" "Ko Sambo kike so yanzu zan saka a gasa miki shi ur Highness, ai kinfi ƙarfin haka ya sake faɗa yana dariya itama dariyar tayi kafin ta kashe wayar tana cewa "Wanda besan Nurain ba ya cuceshi, shiyasa yammata suke neman kashe kansu akansa daɗin baki kamar me" Fatima na saka Brassiere dan na rigada tayi shirin kwanciya tace "Ai dan kinƙi ne amma kun dace da Nurain wlh kai da bansan ya zanyi ranar auranku ba my two besties oh my G" "Allah ya isa na, sa'an nawa? amma Afee kin rainani, koda yake baqin jinane ya jamun ta bakin Momy da ba zaki ce na auri Nurain ba" gaba daya suka kwashe da dariya Maman Minal tace "Kefa kike raina Nurain Badar amma ba yaro bane yanda kike tunani he is 28 i think dan naga Birth date dinsa ranar nan da muna cike wata takadda kuma fa ya fara karatu a waje kinsan rashin lafiyarsa tasa ya bari ya dawo gida and he started all over again sannan yanzu kina level 3 yana 5, sanda zaki gama yayi service harya kama aiki saboda kinsan ku Yayan manya aikine yake jiranku ku gama school ba ku zaku nemeshi ba. Kuma haɗinku zeyi daidai, naga kice Babanshi ma Abokin Dadynku ne to dan Allah me kuma kike jira tunda dai ya nuna dagaske yana sonki?Allah da zaki bashi chance he is a good guy zaki ji dadi". "Gaya mata dai Anty" Afeeyah ta faɗa tana mata gwalo ta harareta tace "Munafuka kyama faɗi gaskiya Maman Minal Ƙarya fa yake saboda mu fita ne dan yasan zan hanata shine fa yake mun wannan daɗin bakin ba har zuciyarsa yake faɗa ba". Sururat tace "Haa Mama Minal, that Nurain na good player oo, i know three of his babes a department namu and babu Wanda tasan yana kula wata fa can you Imagine?" "Thank you my sister ke kinsan gaskiya ai" Badar ta sake faɗa tana ficewa bata saurari Maman Minal dake cewa "Amma wlh ni munyi magana yace mun dagaske yana son Badar, kawai dai yasan ta rainashi shiyasa yake mayar da abin wasa". Fatima tabi bayanta tana cewa "Bakiji Anty Zahra na magana ba?" "Zan zageki Afee kuma na koma wlh" "Allah baki haƙuri ta zunnu" Afeeyan ta sake faɗa cikin tsokana. Nurain na ganin su ya taso ya nufi Badar kamar zeyu hugging nata yana cewa"Oyoyo my love" ta galla masa harara ya saka dariya yana cewa "Kai Badar kinci sunanki aradu, yanda aka fafata a yaƙin nan haka kike fata fata da mutane" seda ta murmusa. Suka zauna Abdul shiru shirun Abokinsa yace musu yana waving, sukayi waving back. Badar da take kar a fita se gashi sun shantake suna zuba zance akan movie daya sako mata a flash drive suka bar Afeeya da Abdul da idan ya fadi magana guda se yayi minti takwas be sake cewa komai ba sedai murmushi, irin marasa maganar nan ne har mamakin Abotar su akeyi da Nurain da ko bacci daƙyar idan bakinsa yana shiru, seda goma ta buga Afeeyah tace bacci takeji kafin suka tafi gurin Sambo karbo Macdee. Guda shida Badar ta ce a musu yan 300, Nurain ya buga tsallen albarka yace baze biya ba, ita kadai ze siyawa taya zataci Macdee shida? Sanin za'a kwata hakan yasa Afeeya fita da ATM ɗinta dan tasan hali tsaf se an gama saka musu ze iya guduwa ya barsu a gun gashi kuwa sunzo suna drama yace sedai ta aje huɗu kuɗin biyu ze biya ita dai ta bawa Sambo ya cire kuɗinsa yana dariyar lamarin Badar da Nurain, sedai basuje gurin ba amma kullum se sun siyar da hali. "Wadannan yan uwan naki kullum kukazo se sunyi Drama" Sambo ya faɗa, Afeeyah tayi dariya tace "saurayine me Mammaƙo da Budurwa me kwaɗayi" "Allah ya isa amma kin cucemu" suka haɗa baki gurin faɗa ita dai ta tsallake ta barsu, bata san ya suka ƙare ba dan har ta kwanta Badar ta shigo harda Ƙarin Kaza guda ɗaya da Can Exotic guda shida se L&Z one liter. Suka baje suna ci taji ƙarar text ta duba taga Alert 5k from Usman Bashir Yabo ta nunawa Badar tace "Saurayinki ne, kinsan dadin rantawa Bestie kuɗi harda extra ze biyaka" "Dan rainin hankali,, kawai shi se anyi surutu hankalinsa ze kwanta, da kuɗin fa a jikinsa har cash ya bani bari ma na tura masa kiga karna manta amma shine ze yarfamu akan Macdeen 1800 kuma ki biya ya wani maido miki da kuɗin yaron nan se a hankali". "Sonki yake shiyasa yake neman fitinarki" Maman Minal data dage akan zancen ta ta sake faɗa, Afeeyah tace "Allah ka nunamun wannan rana Nurain da Badar, bangon gidanku Adon Fire extinguisher zan muku saboda tsaro" duk suka saka dariya harda ita da suke tsokana. *MATAR MUTUM* *NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER* *FIKRA WRITERS ASSOCIATION* *LITTAFIN KUDI NE* *PAY 500 A ASUSUN* *7061838488* *OPAY DIGITAL SERVICES* *MARYAM FAROUK* OR *0709290797* *ACCESS BANK* *SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488* *IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705* *Kuyi following dina a Arewabooks @Maryamfarouk01 inda zaku karanta wannan littafin tareda sauran littattafaina* *NAGODE* *BOOK 2* *PAGE 10* Da wata irin kasala ta farka da Asuba sakamakon mafarkin data kwana tana yi. Ta kalli Badar dake masifar tun ɗazu take tashita amma ta mata banza. "Haba Badar ki barta mana" Maman Minal ta faɗa kafin taci gaba da cewa "Kin san dai Afeeya tana riga kowa tashi ko bata sallah se ta farka ta tashemu tunda kikaga yau ta makara se ki mata uzuri". Badar tayi tsaki tace "Idonta biyu fa tsabar iskancine idan ba zatayi sallar ba seta faɗa ai a barta" fuu taci gaba da juye ruwan zafin da take a bokiti. A kasalance Afeeyah ta yunƙura ta tashi zaune tana cewa "Zanyi mana", gabanta ya faɗi saboda yanda tajini a jiƙe, mafarkin da tayi ya shiga dawomata seta kalli Badar data zuba mata ido itama, kamar zatayi kuka amma ta kasa cewa komai. "Kar dai fa Aljanin darene yazo mata? Mutumin data haɗu dashi jiya kwana tayi tana mafarki dashi kuma ta tashi cikin wannan yanayin karfa da gaske Aljanine? kai Innalillahi taga ta kanta ita Afeeya ina ta kwaso Aljanu ta shiga uku" ta raya a zuciyata kafin ta sake yunƙurawa tana tattare rigarta a ranta ta Ƙudurce tana yin sallah zata kira Ummanta ta faɗa mata tun wuri, bata taɓa irin mafarkin ba se yau gara ta faɗa mata koma menene a tareshi tun kafin ya aureta ta shiga uku. Seda na sauka daga gadon ta kalli shimfiɗar stain ɗin jini da ta gani ya sakata sakin ƙaffaffar ajiyar zuciya saboda ganin wani abu daban ba yanda tayi tunani ba. Towel ta ɗauka ta wuce wanka da Ruwan Badar tana jin tana zaginta amma ban tanka ba. Seda ta kintsa kainta kafin ta cire bedsheet din ta kama inda ya baci ta wanke a baza daman yau zasu haɗa wanki, takwas saura suka fita class bayan sun karya har sannan kuma jikinta a sanyaye yake idan na tuna mafarkin jiyan se taji Zuciyarta ta buga kuma wani abun mamaki sukayi waya da Umma da Baffa amma ta kasa faɗa mata kamar yanda tayi niyya, abin ne da nauyi kawai Anty Sauda zata kira to ta faɗa mata. A Ajin ma bata da wani kuzari da kuzari Malamin da kansa seda ya tambayeta lafiya take tace kanta ne yake ciwo. Malamin na fita Class Rep ɗinsu ya tsallaka sit ɗin da suke, ta kwantar da kanta a kan Desk suka gaisa da Badar da Yusuf ta harari Sahid dan basa shiri kafin ya kalleta yace "Whitey (haka yan class ɗin suke kiranta ko Afee whitey saboda haskenta) I have been looking for you since yesterday" Ba tare data ɗago ba tace masa "Ya akayi?" Dan Sahid akwai dan banzan surutu shima da gulmar tsiya "Wani mutumi ne, I mean one guy asked me about you yesterday and i told him every detail i know har layinki na bashi, Afee you don do good catch i swear, from his looks gayen nan is Rich, his face looks familiar to me but i couldn't figure out inda na sanshi" Sahid ya fada. Badar ta harareshi tace "Haka ka iya kai dai ka zama kamar wani kawali kullum cikin haɗa yammata da Samari", hausar bata bawai yana jinta dakyau bane Banufe ne dan haka ya kalli Yusuf da suke tare yace "What is Kalali? Because i know Badariyya, when ever she speak big big Hausa word she is up to no good" dukda yanda nake jina amma seda nayi dariyar maganarsa Yusuf yace "Tana nufin you are a good match maker" "Ehen" Sahid din ya sake fada da alamar be yadda da abinda ya fada ba amma se ya maida hankali kaina yana cewa "He gave 100$" "Kaji daɗi" Afeeya ta faɗa tana miƙewa saboda cikinta daya hautsina, tsallakesu tayi ta fita da sauri can gurin fanfo tana zuwa ta shiga sheƙa Amai masu wucewa suna binta da sannu. Kamar ta kunno ciwo tana gama aman marata ta riƙe ita da bata Mp se gashi ta gagara tashi tsaye daga gurin seda Badar tazo ta ɗagata. "Muje Hostel kawai daman baki da lafiya amma kika fito?" ta faɗa suna tafiya a hankali. Yusuf ne ya kaisu har gaban Amina a motarsa kafin suje ta galabaita juye juye kawai take a cikin motar na azaba dakyar ta iya fita ai kuwa nan gurin Security ta kwanta tana kuka shaɓe shaɓe kamar wadda zata haihu, abinda bata sababa, bata taɓa experiencing ciwon Mara ba se lokacin shiyasa take jinsa wani sabon abu kamar zata maɗe. aka daka saboda ciwo. "Sannu Afeeya me yake damunta?" Anty Amina daya daga cikin matan security da mmsuke mutunchi dasu ta tambayi Badar, "Inaga zazzaɓi ne" Badar ta bata amsa Afeeya ta nuna musu mararta da hannu, cikin tausayawa Anty Aminan tace "Wayyo sannu, daure ku ƙara ciki se kisha ruwan zafi da pain relief, Allah ya kawo Afuwa" "Kuje kuyi aure yara kun zauna kuna fama da ciwo" Ɗaya matar ta ɓaro maganar, Badar ta Anty Amina suka kamata ganin an fara taruwa akana kallonta wasu na cewa Aljanu takeyi. A common room suka ajiyeta ta kasa zama kan kujera se a ƙasa ta kwanta tana cigaba da murƙususu, ashe haka Matan suke ji amma ta ringa cewa Bafar raguwa idan tana ciwon Mara yau gashi Allah ya kamata itama kamar fa an hura mata wuta takeji a gurin wannan abu da akwai Azaba. Ta fi awa a gurin kafin ciwon ya lafa mata lokacin har gashin kanta seda ya hargitse kamar wadda tayi naƙuda. A duddƙe ta ringa tafiya har sukaje ɗaki, duk wanda Badar ta gayawa abinda yake damunta se yayi dariya kafin ya mata sannu dan haka take musu. Sururat ta haɗa mata ruwa me zafi takai mun banɗaki kafin ta fito Badar ta haɗa mata shayi me kauri ta gyara mata gado, kamar wata sarauniya haka suke lelenta suna mata iskanci kuma, tasha Paracetamol ta kwanta bacci ya kwasheta wata Jalalar Mutumin ya sake diro mata a mafarki amma ba irin na daren jiya ba. Na daɗe sosai tana bacci har gurin qarfe biyun rana kafin ta farka ta ji daɗin jikinta se abinda ba'a rasa ba. Kamar me ciki ta seda ta sakeyin Amai kafin tayi tsarki da ruwa me dumi sosai ta canza pad ta koma ɗaki tana tafiya salaf salaf kamar waddata fito daga Labour room. "Abin nema ya samu" Ummi ta faɗa ta harareta kafin ta zauna kan Gadon Maman Minal tana cewa "Tun jiya Ummi daga zuwa Lecture baki kwana a nan ba?" "Bayan na fito daga lectures ne na hadu da Surayya shine kawai na bita City tunda yau banida lecture, yanzu ma motar bati na samu shiyasa na taho da wuri" Ummin ta bata amsa kan tabi Cousin ɗinta city gidan Antynta. Afeeya ta kalleta badan ta yarda Zaria City tasan baze wuce yawonta na banza ta tafi ba. Ummi bataji ko kadan, ta santa tare sue a English da zasu shiga Level 3 ɗin nan ta bari ta koma Library science saboda rashin mayar da hankali ana nema a koreta, party da clubbing a Zaria babu inda bata sani ba yanzun a hakan ma ta rage ne zama dasu suna matseta dole ta rage wasu abubuwan da wuya ta fita ta kwana a waje duk yawonta zata dawo Hostel. "Wlh gidan su Surayya naje idan ma baki yarda na kirata yanzu kiji da kunnenki" ta katsewa Afeeya shirun da tayi dason wanke kanta. Wayar Afeeya ta fara ringing akan gado ta ɗakkota tana cewa "To me kikaji nace Ummi? Duk ma abinda mutum yayi ai dan kansa me kyau ko mara kyau zaka tarar da sakamakonka me sonka ne yake damuwa da abinda kakeyi har yake so ka hau hanyar daidai". Ahmad ne yake kiran kafin ta answer ta ktase se lokacin taga missed call daya mata kafin wannan kiran. Wani kiran ya sake shigowa, ta ɗaga yana narke murya dan bata so wayar tayi nisa. "Fatima kin tashi? Ya jikin?" Ya faɗa cikin kulawa, ta kwanta tana cewa "Da sauƙi, ka kira aka ce ina bacci ne?" "No, dana kira baki ɗaga ba i called Badar ita ta gaya mun bakya jin dadi ta barki kina bacci i hope you are feeling better now? Kodai zakuje hospital ne kira Ilyas ya kaiku?" Ya sake tambayata a tausashe, a maimakon taji daɗin kulawar tasa ma haushi yake bata ya fiya sanyi da yawa ta muskuta tana cewa "Nafa samu sauƙi kuma nasha magani, Ilyas na zata ya bar Zaria ai" "No yana nan be samu sun canza masa din ba so kuma ma saura two months ya gama shiyasa ya haƙura" (cousin ɗinsa ne yaron sister Momy da yake Internship a Shika Asibiti). "Ayya Allah ya bada sa'a, ya kake? Abujan? Yaushe zaka dawo?" "Are you missing me?" Ya faɗa yana sakin murmushi najin daɗi yau Fatima ta tambayeshi wani abu daya shafeshi, kunya ta kamata tayi murmushin ita ma amma bata ce komai ba yaci gaba da cewa "Se Thursday In sha Allah, kina zumuɗin ki ganni ne?" "Uhm" kawai tace, cikin tsokana yace mata "Da gobe fa zan taho, sena haɗu da wata yar farar Yarinya me irin zubinki, ita take so ta riƙeni na kasa tahowa". Ba wani son sa take ba ba amma se da zuciyarta ta sosu da abinda ya faɗa kishi ya taso mata, a ƙufule tace "Kace kayi budurwa yar Abuja yar gidan masu kuɗi" yanda tayi maganar ita kantaseda ta idar ta fahimci muryar da tayi amfani da ita tayi kauri da yawa ta kuma bayyana kishin daya taso mata ƙarara. Dariya sosai Ahmad yayi tayi shiru kunya da takaicin kanta suka rufeta, seda yayi me isarsa kafin yace "Ashe dai Fatima na kishina haka? Gaskiya naji daɗi". Bata sake ce masa komai ba ya gama surutansa tana ji ganin ta ƙi bashi amsa yasa ya canza akalar maganar da cewa "Haka kawai Tuwo nake sha'awar ci da Miyar Kuka, kamar na tafi Kano yau ma nake ji" "Ikon Allah Tuwo kuma ka rasa wacce miya seta kuka?" Ta faɗa cikin mamaki dan zata iya cewa a matasa dai shine mutum na farko data taɓajin yana son Miyar kuka, Yah Malam dinsu cewa yayi ganyen bishiyar Aljanu ne tsaɓar hatsabibanci irin na mata suka mayar dashi abinci shiyasa duk me yawan cinsa kwakwalwarsa toshewa take saboda sharri. "Kuka dai da kika sani, ni ai idan kina so ki burgeni to ki bani abincin gargajiya amma fa with a touch of modernity bawai kuma ayi abu babu sha'awa ba, irinsu dambu, Akubus, Fate, Ɗanwake babu wanda bana ci kuma a kowanne lokaci zan iya ci be it safe, rana dare duk zan iya cinsu musamman idan an shiryashi ya dace da lokacin". Kai ta ɗaga kamar yana ganinta tace "Na gane" "Yawwa idan ma baki iya ba se ki koya dan ni babu ruwana da wasu continental dishes da kika ganni shiyasa ma kikaga nake daidaitan se Umma ta sauke abincin dare nake zuwa gidanku dan ba Ƙaramin daɗin girkinta nake ji ba kuma na ci na Anty Sauda ma naji yayi kalar na Umma Allah yasa kema haka kika iya girki" "Ina koya" ta bashi amsa a taƙaice tana janye wayar daga kunnenta, minti goma sha daya suna magana zan iya cewa basu taɓa kaiwa haka suna waya ba idan ma sunyi to befi sau a ƙirga ba. Kamar ya shiga ranta taji shima yana cewa "This is our longest phone call so far, bari na shigar dashi a Diary yau ɗin ta shiga tarihi". Ta yatsina fuska kamar yana ganinta kafin tayi magana cikin sauri taji yace "Ki huta Fatima, i will call you later Jafar yana kiran ɗaya wayana". Wani tuƙuƙin baƙin ciki ya taso mata dajin sunan wanda ya ambata. Ta tsani Jafar ɗin nan tsana me tsanani da bata san iyakarta ba. Bata ko amsa masa ba ta kashe wayar tqna jan mugun tsaki. Maman Minal da bataji shigowarta ba ta ce "Lafiya kike tsaki haka?" "Babu komai" ta bata amsa tana miƙewa saboda yunwa data faraji. Ta zuba taliyar data gani a tukunya ta hau ci ranta duk a dagule, ta kusan cinyewa Badar ta shigo da alama ta kwaso yunwa dan hannu kawai ta wanke ta dirarwa abincin da Afeeyan take ci seta tsame hannu ta bar mata dan daman ta ƙoshi gudun kar su mata masifar da suka saba idan ta rage abinci yasa take turawa daƙyar. "Jibi tuwo zamuci a ɗakin nan" Maman Minal data idar da sallah ta faɗa, Afeeya ta kalleta, Badar tace "Ai kuwa mun kwana biyu bamuyi tuwo ba. Bari rana ta lafa se muje cefane miyar me za'ayi?" "Kamar Kuka naji kince ko Afee?" Ta jefawa Afeeyah tambayar, zare manyan idonunta tayi tana kallonta da rashin fahimta dan bata gane inda maganarta ta dosa ba, ita yaushe sukayi zancen tuwo? Maman Minal Ta miƙe tana ninke sallaya tace "Zancen tuwo naji sunayi da Ahmad shine naji sha'awarsa nima kinga se ta mana Jibi idan zezo" "Kai Anty Zahra daga jin muna magana bafa cewa yayi yana so ba labari ne kawai ya kawo maganar ba cewa yayi na masa ba" tayi saurin defending kanta kafin su ƙallaba mata abinda bazata iya ba. Badar dake side hannu ta cafe tana cewa "Aiko yin tuwo Lazim idan ba so yake ba meze saka ya miki zancensa kawai dai be fito kai tsaye bane ke kuma in kinada lissafi ai kinsan me yake nufi Allah ya kaimu jibin dama bamu da Lectures kuma na shinkafa zaki mana Aradu ki tuƙeshi da kyau yasa malmala mu kwashi gara abinmu" "Aiko zaki ɗige indai ni zan tuƙa miki tuwo, shima ya nemi inda zeci tun dare be masa ba wlh" Cewar Afeeya, Badar ta hayayyaƙo mata tana cewa "Wlh se kinyi, ko mu ba zaki dafa mana ba se kin wa Ahmad banza wadda bata san Abin kirki ba. Ahmad ɗin nan kwanta miki kaɗai ya rage ya farayi amma hakan be saka yaci darajar mutunchi kema ki ringa mutuntashi ba kici gaba ubangiji ya miki ni'ima amma kina nema ki butulce masa in bakiyi wasa ba kika watsar da damarki ba fata na miki ba gaba se kinyi kuka da dana sanin rasa shi dan wlh a zamanin nan samun kamar Ahmad Namiji kyakykyawa, me kuɗi ga Ilimi da nutsuwa ga hankali kuma ya soki tsakani da Allah bawai da lalataba se an tona ai mazan dai gasu nan ke zaki bada labari dan babu kalar saurayin da bakiyi ba kowa kuma yazo iskanci yake kawoshi koda wanda ya tsaya bayan Ahmad din" Badar ta faɗa a hasale bacin ran ya nuna har kan fuskarta. Kallonta Afeeya tayi bayan data zauna akan gadonta, bata tanka mata ba ta maida kai kan wayarta tana duba number data kirata yanzu kafinkuma ta answer ta katse, ganin ta waje ce yasa ta ajiye wayar ta yuwu Kamfanine ko sacammer. Tana jin Badar na maganganu tayi mata banza dan idan ta tanka se ran kowa ya ɓaci. Badar tana yawan faɗa mata maganganun da bata jin daɗinsu akan Ahmad amma tanayi mata uzuri saboda tasan bada wata manufa take faɗarsu ba a ganinta damuwa da lamarinta nema har yasa take tada jijiyar wuya akan abinda ya shafeta amma kuma idan aka kalli maganar tata ta wata sigar tana nuna kamr Alfarma Ahmad yayi mata da har yake sonta wanda wannan yana daga cikin abubuwan da yasa bata sonsa. Bazata auri Mijin da ya zarce matsayinta ba wanda kowa ze ringa mata kallon cusa kanta tayi ko kuma Alfarma yayi mata daya aureta bata kai Ajinsa ba kamar yanda Ɗan uwansa ya faɗa mata. "Badar na gaya miki ba sau ɗaya ba ba sau biyu ba idan kina son Ahmad na bar miki shi kuma zanyi duk iyawata gurin ganin kin same shi. Na sani ba tsarana bane, ire irenki ne m daidai dashi, matsayi da Arziqin iyayenku yayi kamanceceniya kinga babu me ganin cewar Alfarma yayi miki idan yayi tarayya dake" Afeeya ta faɗa zafafe tana barin ɗakin saboda gajiya da maganganun Badar dukda yanda Maman Minal da Ummi suke mata magana akan tayi shiru amma taƙi, dagaske neman fitinarta takeyi yau amma ba zata biye mata ba gara ta fita. "Saboda ina sonki na damu dake ina miki burin ki auri Mijin da yake sonki kiji daɗi shine kike gaya mun haka ko Afeeya?" Ta faɗa tana Ƙanƙancr ido. Fes Afeeyan ta kalleta tace "Kinji abinda na faɗa ai, Ahmad ne bana sonsa bazan aure shi ba kuma fatan da kike mun baze kamani ba Allah ze kawo mun Miji Talaka daidaini na aura wanda babu me saka mana ido ballantana a ringa fassara duk wani motsina akan sa da sunan na butulcewa ni'imar ubangiji". "Meye haka Afeeya?" Maman Minal ta dakatar da ita, ta kalleta da idonta da suka fara canza kala tace "To akan me Anty Zahra? Duk sanda magana zata haɗo akan Ahamd se Badar ta yimun gori a fakaice tace yafi ƙarfi na? ni na janyo shi nace ya soni ko yaya? Da yana da zuciya ma ai da bamu kai haka tare ba saboda na nuna masa bana muradinsa ta duk hanyar data dace amma ya nace ya kafe so takeyi na aureshi Alhalin danginsa basa ƙaunata? Ba'a a kunnenta ƙaninsa yayi mun cin mutunchi ya zagi iyayena sannan ta dage sena cusa kaina inda Allah be kaini ba saboda kwadayin abin duniya? Toni kudinsa ko wani matsayi nasa ba zasu rufe mun ido ba su sa na jefa rayuwata cikin ƙunci na rayu da mutanen da basa so na, idan tana sonsa gashi nan na bar mata ta aureshi itace daidaishi" ta ƙarasa tana Ƙoƙarin riƙe kukan daya taho mata amma ta kasa dole ta sakeshi ta doshi Ƙofa zata fita amma mutanen da suka tsatstsaya munafunci yasa ta fasa fitar ta shige bayan Ummi da ke zaune ta kasa cewa komai ta kwanta tana kuka. Maman Minal ta kulle Ƙofar jiki a sanyaye kafin ta zauna tana cewa "Daga zancen tuwo shikenan se tashin hankali? da alama sheɗan ya shigo ya laɓe a ɗakin nan shiya haɗa komai kuma bazeyi nasara ba in sha Allah". Badar da jikinta yayi sanyi laƙwas ta zauna daga tsayuwar da tayi ta kasa cigaba da masifar tata. Har ga Allah ita batayi magana da manufar da Afeeya ta ɗauka ba, ta riƙi Afeeyar a matsayin yar uwa shiyasa har take son cigabanta take kuma son ta da Ahmad ganin cewar mutumin kirkine ya na da duk wasu qualities da mace zata so a gurin Namiji gashi yana sonta baya ga haka wlh ita bata da wata manufa ta daban akan maganar. Dakin ya ɗauki shiru se shasheƙar kukan Afeeya, kowa da tunanin da take a ranta wayarta ta sake ɗaukar ƙara lambar dazun ce bacin ran da take ciki yasa ta kashe wayar gaba ɗaya ba tareda na amsa kiran ba. Ranar har dare dukkansu basu da walwala shiru ɗakin kamar anyi mutuwa, tsakaninta da Badar kuwa se kallo seda Baffa ya kira wayarta akan be samu ta Afeeyan ba sannan nema ta tuna data kashe wayar tata, data miƙa mata bata kar ɓa ba, ta kunna tata ta kirashi. Sururat ce ta saka su shirin dole cikin daren bayan ta dawo Ummi da Maman Minal suka tsara mata abinda ya faru ta ringa masifa ta kuma ɗorawa Afeeya laifi kacokan wannan yasa suma sauran suka buɗe baki tare da nuna cewar ita ce bata kyauta ba su da kyakykyawar niyya suke tare da ita kuma wannan tasa har suke son abinda suke ganin ze zamar mata Alkhairi ba wani abu ba. Bata so aja maganar da tsaho dan haka nace taji ta kuma bawa Badar haƙuri kamar yanda Sururat tayi insisting. "Wlh Afeeya ina jinki kamar Yah Yusra, idan har zan iya aure ko soyayya da Mijinta to zanyi da Ahmad. Son da yake miki da kamalarsa tasa har nake miki sha'awar auransa dan nasan irinsa basu da yawa a duniyar yanzu amma tunda har zuciyarki tana raya miki wani abu daban akan niyyata in sha Allahu zan kama kaina, bazan sake yi miki wata magana data shafeshi ko ma akan saurayi ba gaba ɗaya. Zanci gaba dayi miki Addu'a Allah ya zaɓa miki abinda yafi Alkhairi" Badar din ta faɗa bayan da Afeeya ta bata haƙurin, jikinta yayi sanyi ganin yanda idonta ke zubar kwalla sanda take maganar, ta tabbata har ranta gaskiya take faɗa kuma Badar na sonta kamar yanda ita ma take sonta amma abune yazo da rashin fahimta dukkan su kowa tana da dalilanta na so ko Ƙin tarayyata da Ahmad amma ta haɗiye nata za kuma ta cigaba da addu'a Allah ya fiddo mata da Mijinta daidai ita ya fiye mata sauƙi. Saboda ta tabbatar musu maganar ta wuce yasa washe gari suna gama Lectures tacewa Badar suje kasuwa ayi cefanen, ta kuwa ji daɗi sosai dan da sunta share juna amma daga zuwa kasuwar komai ya wuce aka dawo daidai Harda kayan zoɓo suka siyo, sesaga baya kuma Badar tace su siya Kunun Ayar Shinkafi kawai ba se anyi Zoɓon ba. "Bari na kira Salima Nasir ta zo manada snacks gobe se a hada masa ko?" Badar ta sake faɗa. Dole Afeeya ta amsa gudun karta ƙara laifi a gurin Badar data saki ranta dalilin za'ayiwa Ƙanin Dadynta girki. Sunyi markaɗen stwe a Kasuwa dan haka suna komawa suka ɗora girki suna hira kamar ba abinda ya faru jiya. Washe gari haka Afeeya ta tuƙa tuwon rabin kwano tayi miyar kukar da Ƙamshinta ya karaɗe duka block ɗinsu ya buwayi hancin kowa. A Set din food flask da suka ɗakko da safe a gidan Maman Minal ta saka masa tuwon Miyar aka barta a tukunya akan seya zo se a sake dumamawa a zuba a flask din. Kayan da zan saka ko Badar ta turarasu ya kai sau uku, jikinta har rawa yake idan Ahmad zezo musamman wannan karon, sunyi waya da Afeeya ya gaya mata be taso da wuri na ze kai zuwa uku kafin ya sauka dan haka zuwa biyu ta gama komai tayi wanka suka zauna suna ta labarai. Biyu da rabi ya kirata akan ya shigo zaria. "Na gaji da yawa ni nayi driving zan wuce nayi Lodging hotel idan na huta da Magriba sena shigo kuma bani kaɗai bane tare muke da mutumin Badar" ya faɗa mata. Har zatace masa toh ta tuna da Tuwon data gama shan wahalar tuƙawa hannayenta duk sun sage tafin se radadi yake mata Allah ma yasa kar nayi kanta. Da shagwabar da bata san tayi ba tace masa "Toh Abincin fa? Shima se da magribar zaka ci?" "Wane Abinci?" Ya tambayeta cikin rashin fahimta se sannan ta tuna da bata gaya masa tayi masa tuwon ba dan haka tace "Girki mukayi shine na ɗibar maka ko bazaka ciba?" "Nidin banza, gani nan yanzu kuwa zanzo na karba kamar kinsan yunwa nakeji ko breakfast banyi dakyau ba saboda dokin son ganinki" Guntun murmushi tayi kafin suka aje waya. Miyar aka sake ɗumamawa Maman Minal tayi masa zubi me kyau duk ta kwashe Albarkatun cikin miyar ta bar musu saura. Hijabi ta ɗakko cikin na *UMMU-MAHEER 07061838488)* wankakke gogagge ta ɗora akan doguwar rigar jikinta Badar ta kwaso Ashar ta watsamata ta haɗiye dan daman ta san se sunyi. "Tsabar iskanci in gama shan wahalar turara miki kaya ki wani kwashi Hijabi kamar me takaba ki saka" ta faɗa a fusace tana neman fizge hijabin. Maman Minal tace "Ki barta ai ze dawo anjima se tayi kwalliyar sannan". "Masifaffiyar banza kawai" Afeeya ta faɗa Ƙasa ƙasa. Sururat ce ta tayata ɗaukan Basket da suka zuba abincin. Kallon da bata so ya kafeta dashi tun daga corridor harta fita wajen hakan da yayi yasa hankulan mutane da yawa yayiwo kanta har suka Ƙarasa gabansa yana ta sakin murmushi kamar wani wawa. Kallonsa tayi taga ya sake zama wani dan tsurut musamman daya saka ƙananan kaya se taga ma har tsakiyar kansa tana kallo tsanar sharri, murmushi tayi itama ta shiga gaishe su shida Abokinsa da kana ganinsa kaga Kanuri. Wani Baƙi dashi hausar ma se a hankali se surutu kamar ya ƙone a kai. "Gaskiya Amaryarmu ba kalar rana bace, dan haka kodai ka nemi inuwa ku zauna ko kuma ka barta ta koma ciki an jima idan gari yayi sanyi seka dawo. Ni ganin basket ɗin nan ma gaba ɗaya ya sake tadomun da yunwa" Bukar ya faɗa ga surutu ga saurin baki. Kanta na ƙasa tana wasa da zoben hannunta duk kallon da Ahmda ya kafeta dashi ya takurata, "Bari muje Fatima anjima se na dawo bayan La'asar ko?" Ya faɗa cikin sigar tambaya ta ɗaga masa kai ta ce "Toh". Abokin ne ya karɓi basket ya saka a mota Ahmad ya bishi ya ɗakko wata leda me tambarin super market dinsa BECHI STORES ya miƙa mata ta karɓa ta ɗan rusuna tace "Nagode" "Tsarabarki ce, tukuicin girki kuma se naci naji Ɗanɗanon sa tukunna" Murmushi tayi, ya langwaɓe kai ya jingina da mota yace "Kamar karna tafi, kinyi kyau sosai Fatima Hijab suna miki kyau" Yaƙe kawai takeyi Abokinsa ya leƙo daga mota yace "Kodai na zuba na fara ci ne in ba yanzu zamu tafi ba?" "Kaga kun kwaso gajiya, kodan saboda dashi kuje Anjiman se ku dawo" ta faɗa, seya gyara tsayuwarsa yana cewa "Naga hannunki" Ƙirjinta ya buga, me ze gani a hannunta kuma? Amma haka ta daure ta miƙa masa hannun da daga wrist zuwa fingers ɗin ne a buɗe, "Masha Allah ya faɗa" kafin ya juya yana ɗaga mata hannu da cewar Se ta dawo ita ma ta ɗaga masa. Ta tsallaka ta shige hostel tana ta mamakin dalilin son ganin hannunta da yayi. Tuwo ta tarar suna ci ta wanke hannu ta zauna, tunda ta gama taso taci jarabar Badar ta hanata wai bakinta zeyi warin daddawa se kace idan ta wanke baze fita ba. Seda suka qoshi Ƙat kafin a zazzage ledar tsarabar. Wata Arniyar Turkish gown ce Material me sharashara Amma tana da landing Dark blue ce da flowers Yellow da fari da dan yarfin ja kadan. Irin design da ake sakawa roba a waist ta matse ta sama ƙasan kuma ya buɗe ce se mayafai Medium guda biyu plain da kana ganinsu kasan suma daga Turkey suke saboda samfurin jikinsu, takalmi loafers dark blue qafa daya se Wani kwali ƙarami na turarene babu suna a jiki hakan ya tabbatar mata da sabone basu luncher shi ba testing ya kawo mata kamar yanda ya saba tunda suka haɗu, Ahmad yanayin Designer perfumes kuma duk sanda sukayi sabon Turare kafin a fitar dashi seya kawo mata. Company haɗin guiwa ne da wasu Abokanansa da sukayi karatu tare a Paris Asalin kamfanin yake amma a Dubai suke operating. Tarkacen Chocolate na yan gayu birjik su su Badar suka ɗiba ragowar kayan ta watsa su a kan gado. Ahnad baya gajiyawa kullum cikin hidimta mata yake. Idan ya tashi siya mata kaya tamkar besan zafin kuɗi ba daidai da Slippers yanda yake saka Designer haka yake siya mata tun Baffa da Umma na faɗa har suka haƙura suka zuba masa ido kyautar Kuɗi ce dai Baffa ya dakatar shine yace idan an hanata karɓan kuɗi ai ba za'a hanata kaya ba dukda haka kuma idan zata koma school seya tura mata kuɗi masu nauyi sedai taji dirim. Shida saura Ahmad ya kirata akan sun fito suna hanyar Samaru, bisa takurawar Badar Ummi tayi mata light make up ta cakare cikin Atamfa dinkin fitted straight Bubu, bata kamata tsam ba haka bata yi buhu ba tabi shape dinta ko ina ya fita masha Allah abinka da dogowar Mace na ta juya Anty Zahra tace "Afee kinyi kyau, komai kika saka kyau yake miki". Badar ce tayi mata ɗauri me kyau daya dace da kwalliyarta Seda aka idar da sallar magriba kafin ta fita dan bayan ya isa kirata yace ze shiga central mosque yayi sallah tukunna. Bata cika fita babu Hijabi ba infai ba Abaya ta saka ko irin Bubu plain Gown ba a hakan babu kwalliya gajiya takeyi da idanun mutane balle yau datayi shigar Atamfa harda kwalliya a fuskarta ga ɗaurin gaban goshi wani irin kyau tayi me sanyi da ƙayatarwa ba Maza ba hatta matan dake kaikawo a waje Hostel binta suka ringayi da kallo duk seta jita a takure shoyasa tafi gane ta suturta kanta da Hijabi Ko Abaya. Yanda Ahmad ya saki baki yana yabon kyan da tayi ko har seda abin ya bata kunya ta sunkuyar dakai tana murmushi. Shi kaɗai ya dawo Abokin nasa wai ya shiga City, a nan Basket ball court suka zauna suna hirar duniya dan a itane take sakewa dashi suyi magana ko zancen Business dan tanada sha'awar kasuwanci sosai abinda ma zata ce ya a birgeta da Ahmad kenan Business mind set, a tsaye yake da ƙafafunsa kuma kullum cikin nuna mata amfanin neman na kai yakeyi. Yakan ce mata "Ina so naga matata tana sana'a badan bazan wadata ta da komai na rayuwa ba Aa sedan ni na yarda da ko wani zeyi mun abu ya zamana nima inada abuna wanda zan kalla nace da gumi na na sameshi". Seda aka kira yace ta kira su Badar su fita wannan daman constant ne duk sanda yazo seya fita dams yawo sun sha iska sunyi ciye ciye, tana kiranta minti goma suka fito duk a shirye harda Ruth suka zauna su huɗu a baya ita a gaba banda Maman Minal suka tafi Zaria Suya kamar yanda Badar tace can za'aje sunata hira da Ahmad har suka isa. Sunci kifi sun sha shayi sunyi take away kaza da Suya amma banda Afeeya da idanun da Ahmad ya kafeta dasu suka hanata sakat. Yau se take ganin kamar tasan wani bayan shi me irin idon, amma ta gaza tuna waye. https://chat.whatsapp.com/FKsWield4wPKepHDZwtPUP *ASSALAMU ALAIKUM WARAHMATULLAH* *MUNA GABATAR MUKU DA UMMU-MAHEER COLLECTION Ita din dai kuka sani taku ta gargajiya da take kawo muku kayayyaki irin na yangayu daga kan ATAMFA, BUYERS BATIK, COTONOU BATIK, SWISS LACES, LAGOS LACES, MAYAFAI, KAYAN KWALLIYAR YARA DA SAURANSU. TA SAKE SHIRYOWA TSAF DA COLLECTION NA HIJABAI IRIN NA AFEEN JAYY FA AMMA BANA HAJJAJU BINTA GUMAMA BA* *YI MAZA KU GARZAYO DOMIN KUYI SIYAYYAR KAYAN SALLARKU A GURINTA CIKIN RANGWAMEN FARASHI GA BIYAN BUQATA* *DA AKWAI NORMAL HIJAB ME HANNU, MARA HANNU, POCKET HAND SE WANDA KIKA ZABA KALA KAWAI ZAKI BADA AYI MIKI AIKIN, JILBAB DINMU TAMKAR SAUKAKKE DAGA EGYPT, WANDA SUKA SIYA ZASU BAKI TABBACIN INGANCIN YADINMU. DA AKWAI NORMAL YARD, AKWAI LONDON CREP IYAKAR KUDINKI IYA SHAGALINKI* TWO PIECES GOWN DA V HIJAB NA YARA DA MANYA HARDA MA ABUBUWAN DA BAN FADO BA ZAKI SAMUSU GURIN UMMU-MAHIR DA YARDAR ALLAH. *SANQAMA MATA KIRA KO CHATTING AKAN 08142548705/07061838488 KO KUMA KIYI JOINING GROUP DINTA KAI TSAYE DOMIN SAMUN LATEST DESIGN AND AVAILABLE KAYA DA SUKE A QASA* *MADALLAH DA MASU SO FISABILILLAHI IRIN NA AHMAD BECHI* *MATAR MUTUM* *NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER* *FIKRA WRITERS ASSOCIATION* *LITTAFIN KUDI NE* *PAY 500 A ASUSUN* *7061838488* *OPAY DIGITAL SERVICES* *MARYAM FAROUK* OR *0709290797* *ACCESS BANK* *SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488* *IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705* *Kuyi following dina a Arewabooks @Maryamfarouk01 inda zaku karanta wannan littafin tareda sauran littattafaina* *NAGODE* *BOOK 2* *PAGE 11* "Saura sati nawa kuyi hutu?" Ya tambayeta yana sake narkar da idanunsa a kanta. Ta lissafa a zuciyarta kafin tace "Four weeks i think" "Fatima" ya kira sunanta da sautin dake nuna muhimmancin maganar da zasuyi, ta gyara zamanta ta saci kallonsa yaci gaba da cewa "Shekara biyu kenan since i meat you. Banyi zaton zan ƙara wata shida ba daga ranar dana haɗu dake ba tare da kin zama matata ba amma se gashi har an tafi shekaru which kece kika jawo hakan, please Fatima, i will ask you again ki aureni, last week na je na samu Baffa akan ina so na turo magabatana yace na nemi Amincewarki tukunna, idan kin yarda ko yaushe na shirya na tura ayi magana. Bansan me kike jira ba, Fatima Aure baze hanaki ƙarasa karatunki ba tunda shine maganarki kullum ke kinfi so ki gama makaranta ni bazan hanaki karatu ba idan kin gama wannan kina so kici gaba wallahi ko a Nigera ko wata ƙasa ni zan tsaya miki har se ke da kanki kince karatun ya ishe ki tukunna kawai ki Amince mun ki bani dama na tura Iyayena ayi maganar auran mu saboda wlh Haƙuri na ya fara ƙarewa Aure nake so Fatima" Shiru tayi masa kuma kunyar kalamansa na ƙarshe ne ya assasa shirun wai Aure yake so, matso da kujerar sa yayi kusa da tata kamar ze haɗe su yana cewa "Talk to me Fatima bana son shirun nan naki menene matsalarki bayan maganar karatu? Idan da akwai wani abu daban let me know please" Kamar tace masa "shi ɗin ne bata ra'ayin aure se kuma ta canza maganar dan ko babu komai kirkin Ahmad ya wuce tayi masa irin wannan cin fuskar. Kora da hali dai ba wadda bata masa baa baya amma ya ƙifahimta to ya yake so tayi dan Allah? Gyara zama tayi ta dan ja baya saboda kusancin nasu yayi yawa kafin tace. "Nidai Ahmad nafi so na kammala karatuna tukunna in so samu harma nayi NYSC kafin nayi aure, sannan kana cewa muyi aure naci gaba da karatu na tayaya hakan zata faru bayan Matan gidanku bas karatu?" Buɗe ido yayi irin na mamaki ya kalleta kafin yace"Waya gaya miki haka?" "Haka naji a gari" ta bashi amsa tana sauke ido ta saboda yanda ya saka mata nasa, cikin taushi yace "Fatima abin harda sharri? A wane gatin kikaji? Waya ce miki matan gidanmu basa karatu? Matan Yayyena harda me Phd Matar Dr Hassan tana aiki Lecturer ce, inaga a cikin sauran babu wadda batada Degree, idan kuka Ƙannena kike nufi Aslamiyya da Hajiya Ƙarama Level 2 suke kowacce kuma Next two month aka saka ranar Auransu kowacce zata gama Karatun a gidan Mijinta ya za'ayi kice ba'a karatu a gidanmu kodan kinga Alhajin mu ba Ɗan Boko bane?" "Ni bance haka ba, to inaga qadda ta gaya munce bata ji daidai ba" ta faɗa cikin kare kai shaci faɗi kawai tayi seta daki garwa. Ya saki murmushi yace "You know nothing about my family kar kuma kice zakiyi judging da abinda kike ji a bakin mutane. Babu wata mace da aka taɓa aurowa a gidanmu akace ba zatayi karatu ko aiki ba, duk wadda kikaga bata aiki bata da ra'ayi ne, amma dai ni in particular bazan yi miki ƙarya ba tun yanzu ki sani idan har Allah ya sa ka munyi aure babu maganar aiki ba zakiyi ba. Ba zan yarda Matata ta ringa yawo a gari da sunan aiki a Ƙarƙashin wasu ƙatti ba. Business dai wannan idan zakiyi zan baki jari daga naira ɗya har zuwa Miliyan ɗari ya danganta da abinda zaki siyar amma ban miki ƙaryar zakiyi aiki ba" ya faɗa da iyakar gaskiyarsa. Duk yanda yaso ya sha kanta akan ta bashi dama ya tura, ya yarda aje ayi magana idan yaso a saka rana sanda zata gama Makarantar idan haka ne burinta amma ta tubure ita ba haka ba. Cikin yanayin dayake nuna ransa ya ɓaci da rashin samun amincewar tata ya maidasu Makaranta, be tsaya ba yace mata Bukar ze maido mata da Flask gobe be taho dasu ba shi Asubanci zeyi ya wuce Kano. "Idan yazo Badar ce zata karɓo ba keba" ya faɗa da sigar umarni. Cikin wasa Badar ta ɓata fuska tace "Wato ni mara galihu tunda bani da tsayaye ko" "Kika sani ko ya zama tsayayyen?" Ya tsokaneta. Bundle ɗin 1k ya bawa Badar yace "Tukuicin Tuwo, yayi daɗi da alama ke kikayi" "Afeeya ce wlh" ta faɗa bayan data dafe kuɗin, ya juya mota yana cewa "Idan ta amine da muradi ma zan haɗa na bata tukuicin a tare" yaja ya tafi babu wata profer sallama da suka sabayi. "Alamu sun nuna kin kwafsa Afeeyah,wai dan girman Allah se yaushe Ahnad zezo Zaria ya koma da farin cikinki ne?" Badar ta faɗa suna shiga Hostel. "Hmmm" ta bata amsa dan ita da kanta taji rashin daɗin yanayin daya tafi, duk shanye fushinsa yau seda fuskarsa ta nuna, amma ya zatayi toh? A rabon Maman Minal ta yafita mata Kaza taci dan da Badar rantsewa tayi ba zataci ba tunda bata da mutunchi. Harta kwanta wayarta ta fara Ƙara, International number ce, kwana uku kenan ana kiranta da ita kullum kuma ko ta tsinke kafin ta ansa ko kuma taga miss call ita kuma ta san bata da wani a Ƙasar waje da ze kirata shi yasa bata taɓa bin baya ba ta yuwu ma scammers ne. Ta amsa wayar ta saka a kunne ba tareda tayi magana ba, kusan minti guda ita shiru haka wanda ya kira shima beyi magana ba daga can ƙasa dai tana jiyo maganganu alamar yana kusada inda ake hayaniya. Suka ci minti uku, harta yanke shawarar kashe qayar dan ba zata fara magana ba ta yuwu wand aaka ce suna tsotse jinin mutane ta waya ne suna jira tayi magana su gama da ita, harta zareta daga kunne taji wani sauti daya saka zuciyarta tsayaqa na wasu seconds kafin taci gaba da aiki "AFEEEYAAAAHHH!" Yaja sunanta, bata iya amsawa ba se sunayen Allah da take maimaitawa a ranta Ƙirjinta na lugude. "Afeeya!" Me kiran ya sake maimaitawa, bugun Ƙirjinta ya tsananta zufa ta fara tsassafo mata haka numfashinta ya shiga yi kamar ze tsaya tamkar wadda take cikin matsanancin tsoro kuma kamar wadda aka kafe ta kasa cire wayar daga kunnenta se kokawa take da numfashinta dake barazanar tafiya hutu saboda tasirin da muryar wanda batasan ko waye ba yayi a kanta. Bata taɓa katari da Bakin daya iya furta sunanta, ya bawa kowanne harafi haƙƙinsa kamar me waƙa. "Afuwan, Assalamu alaikum" ya sake faɗa cikin wani sauti me haɗe da irin ƙaramar dariyar nan, take ta kware da yawun bakinta ta shiga tari tul tul Ummi data fi kusa da ita ta miƙa mata ruwa tasha tana maida numfashi har sannan kuma be kashe wayar ba, kwakwalwata ta ayyano mata me wannan muryar, sallamar da yanayin da yayinta ya tuna mata da jinjirin Samudawan da tayi gamo dashi ranar Monday. "Sannu, badai loman abinci kikeyi ya Ƙwarar dake ba?" Ya sake tambayeta se kawai taji bakinta ya saki tsaki kafin ta zare wayar ta kasheta tareda ajiwa batama lura da yanda yan ɗakin sukayi shiru tareda zuba mata ido ba se sannan. "Afeeya meya faru? Kinga fuskarki kuwa se kace wadda Fulanin Daji suka kira?" Maman Minal ta faɗa, ta shafa fuskar da hannu, Badar tace "Meya tsorataki? Kin kara waya a kunne kusan minti goma bamuji kince komai ba lafiya ko wani abun ne ya faru?" "Uhm" kawai tace ta miƙe tareda ɗaukar ɗankwalinta ta fita ba tareda ta amsa tambayar ba har sannan kuma zuciyarta bata bar bugawa ba kamar yanda jikinta yake rawa. Last floor ta haye ta tsaya tana kallon 90s mutane nata karaina surutu duk ya cika gurin, tunani takeyi shi ɗin ne ko ba shi ba? Idan shine a ina ya samu number ta sannan kiran me yake mata? Zancen Sahid dayace ya bawa wani number ta ya faɗo mata to ko shi yake nufi a gurinsa ya samu number wayata tunda ta faɗa mata sunanta daman? "Afeee" aka Ƙwala mata kira daga Ƙasa, tayi firgigit daga tunanin da take ta kalli inda taji sautin na tasowa tsabar wulaƙanci Nurain ne yake kwala mata kira daga cikin 90s, bata amsa ba ta harareshi ya ɗago mata Kwalin popcorn yana cewa "Kinyi kyau, zaki ci popcorn?" Still da Ƙarfi yayi maganar abinda ya janyo hankulan waɗanda ke kusa dashi suka kalli gurin dan ganin dawa yake tana ganin haka tayi saurin sauka ta koma Floor ɗinsu dukda haka tana hango su se shegiyar dariyarsa yakeyi tana shiga Badar tace "Cin kan Bestin naki ya motsa yau" "Ke kuma sweetynki ba" tabata amsa tana Ƙoƙarin cire rigar jikinta wayarta ta shiga ringing, data Badar a tare ta ɗaga ganin Ahmad ke kira bayan ta haye kan gado, hira suka shigayi ya saki kamar bashi ya tafi fuska babu walwala ba, Bashi da ruƙo, yana daga cikin kyawawan halayensa se santin kwalliyarta yakeyi har yana cewa saura ƙiris yayi abin kunya next time karta sake saka Red Lipstick idan zata masa kwalliya har se ta zama matarsa. Sedata kashe wayar ta kura Badar ta fita Ruth tace mata sun fita da Ummi Nurain ne ya kirata "Gulma, ana so ana kaiwa kasuwa" ta faɗa,daga nan ta gyara kwanciyarta ta bhau WhatsApp. Lambar Basamude ta gani a farko yayi mata magana "Why did you hang my call and you hissed at me? Not even in your dream you try that again" Ta maimaita saƙonbabu Adadi Mamaki ya kasheta, a fili tace "Ikon Allah, ji wata magana kamar wani uban mutane, wannan yana da lafiya kuwa?" a maimakon ta amsa se ta shiga profile ɗinsa, Hoton Jessy ne akai ta Yan Ball kalar Red da white no 9 an rubuta *JAY* a jiki, batasan ko ta wanne club bace ba abinda ta sani dangane da yan Ball. Tayi tsaki na fita daga chat ɗin tana jinjina Ƙarfin halinsa, status ta fara kallo kira ya shigo video call tayi rejecting wannan mutum ko maye ne ai se haka wannan Naci har ina? Be haƙura ba ya sake kiranta voice call ta sake rejecting, seda ya kira sau uku ana huɗun ta amsa tun kafin tayi magana yace "Wallahi Afeeya, if reject my call again I'm going to deal with you" "Malam kanka guda kuwa? Who are you? Are you suppose to tell me what to do or what?" Ta bashi amsa a haslae jin abin nasa ze zarce ganga da makaɗi. Tana ji yaja numfashi kafin ya sassauta murya yace "Baki san abinda nake ji a zuciyana bane, 3 days i have been calling but you are not answering, na sameki yau and you hanged on me haba Afee bakida tausayi ne?" "Don't call me that again" ta faɗa jinyanda Afee daya kirata ya saka tsikar jikinta zuba, Tanaji yayi wani mayaudarin murmushi yace "*AFEEYAH* God i love the name, gaskiya Dadynki ya kyauta daya saka miki suna me daɗi da Ma'ana, idan munyi aure nima zaki haifarmun tawa Little Cute Afeeya like you ko?" "Qit" takashe wayar,, koda wanda ta sani bata wannan zancen shirmen ballantana da stranger wanda bata san mutum bane ko Aljan. Seda ta kashe Data ta saka wayar a Silent kamar yanda takeyi idan zata kwanta kafin tayi addu'a ta rufe idonta amma bacci yace be san zance ba, dakyar da taimakon Allah ya saceata. Kwana tayi tana mafarkin mutumin wai suna tafiya akan Gajimaren suna tsinkar furen soyayya. Da Asuba ta samu tsarki tayi wanka tana Azkar Ahmad ya kirata suka gaisa ya gaya mata yanzu ze tafi Kano. "Da wurwuri haka?" Ta tambayeshi, tana ji yana warming mota yace "Alhaji ne ya kirani zan takashi Hadeja Ɗaurin Aure kinga dole na tafi da wurwuri karna ɓata masa lokaci" "Haka ne, Allah ya tsare hanya ya kaika lafiya" tayi masa Addu'a ya amsa da "Amin" kafin sukayi sallama ta kashe wayar ta juya da niyyar maida kai taui bacci aka sake kiranta. "Jarabar duniya" ta furta a fili ganin me kiran da farar Asubar nan se kace wanda yake binta bashi ze fara kira wannan wane irin mutum ne mara lissafi ta shiga mita a ranta amma hakan besa taƙi amsa wayar ba dan harga Allah can ƙasan ranta har wani daɗi taji daya kira. Cikin dakakkiyar muryarsa ta Maza irin wadda zakaji kamar har echo tke yi yayi mata sallama ta amsa tana jin wani sabon yanayi yana mamayarta. "Jiya kika kashe waya kuma bayan nace bana so, kuma nayita kira baki amsa ba why?" ya faɗa a tausashe kamar bacci be gama sakin muryarsa ba hakan ya sa muryar tayi wani amo na daban me tsinka jini, numfashi taja ta fesar amma batace komai ba yaci gaba da magana yana cewa "Bana so, don't you ever hang on me again gara ki gayamun ni na kashe wayana da kaina if you don't want to talk to me, raini ne wannan kuma bana so". Ta shagala da sauraron Muryarsa se kuna ta zabura tace "Wai kai a matsayinka nawa ne da zaka ringa kafa mun sharaɗi?" "Ina son tsiwa, amma bana son rashin kunya, idan kika ci gaba sena fasa miki baki, then i will keep kissing it har se ciwon ya warke" ya bata amsa seta hangame baki ta kasa cewa komai, baccin da take tattalawa ya kama gabansa. "Afeeyah, i hate it when someone hisses at me, karki sake" ya sake cewa "Waye kai?" Ta samu kanta da tambaya dan wannan gadarar tasa ta shallake ta masu hankali kuma, "I will call you by 10am, kina free?" Be bata amsar tata tambayar ba ya jefa mata tasa Ta wurga ido kamar yana gabanta kafin tace "No, i have class by that time" "2pm?" Ya sake faɗa se ta karkace tace "That will be my resting time" "In the evening?" Be haƙura ba ya sake tambaya ba kai tsaye tace masa "Kasan me, ina da lokaci amma ba naka bane so you better respect your self and stop calling me talk less of Bossing around kana wani gayawa mutum abunda zeyi da wanda ba zeyi ba" "Idan na kira karki daga kinji" ya faɗa yanda kasan wani Baffanta kafin kuma tace wani abu ya kashe wayarsa ya barta da baki a gantale. "Afee don do new catch" Sururat ta faɗa teasingly, takaicin daya cikata ya sa bata tanka mata ba tana jin Badar na cewa "Tun jiya take wata waya kamar ta munafukai koma wanene yayi ta kansa wlh dan ina gani babu wanda ya isa yayiwa Ahmad over taking". Kwanciya tayi cike da jin haushin kanta da biyewa mutumin har ya samu damar raina mata hankali. "Amma ya haɗu, haka take son tsayayyen namiji, ta tabbayar da Ahmad ne sedai yayita lallaɓata yana cewa tayi haƙuri". AHMAD Ƙrfe Tara da mintina ya isa Kano dalilin Hold up daya samu a Kwanar Ɗangora wata babbar Mota ta faɗi a tsakiyar Titi wannan ya kawo cin koson ababen hawa a titin dan se zagaye suka ringayi suka kaucewa inda hanyar ta rufe ma. A Ƙofar Katafaren Get ɗin gidan Alhaji Audu Bechi ya tsaya yana danna Horn, Issa ya tsallako da gudu daga gidan dake kallon nasu inda suke zaune da sauran masu gadin gidajen layin ciki. girmamawa yake masa sannu da zuwa "Yi sauri Issa, na makara Alhaji yana jirana" ya faɗa ganin Issan ya tsaya ɓata masa lokaci da gaisuwa da sannu da zuwa hakan yasa ya wangale masa Get ya shiga. Cikin Rumfunan da aka tanada domin Ajiye mota yayi parking, motoci ne birjik a gurin yanda kasan kamfanin saidasu, cike da murna ma'aikatan dake kaikawo a Kantamemen compound ɗin suka nufeshi suna masa maraba, duk saurin da yake haka ya tsaya yana basu hannu, babu kyama balle nuna banbancin kasancewar Barorin gidansu ne su yake mu'amalantarsu wannan Ɗabi'a tasa ta karrama Ɗan Adam yasa yake da farin jini matuƙa gurin mutane. Junaidu daya daga cikin masu kula da shara ya ɗaukar masa Ƙaramar Akwatin da kayansa suke ciki, har ya nufi bangarensu na Mazan gidan yayi burki ya juya zuwa ainihin cikin gidan. Da sallama ya shiga tsakar gidan shiru babu kowa kai tsaye ya doshi Falon Momy, ya kai tsakiya ya tsinkayi muryar Hajiya a bayansa tana cewa "Aa, su uban Bilki an dawo kenan?" (Baba Bilki tana kiransa Babanta saboda Tace Asalin sunan Tijjani Amadu ne dan haka da Babangida da Ahmad duk sunan Malam Babansu sukaci shine Hajiya ta samu idan iskancinta ya tashi take ce masa Uban Bilki) Jiya Ɗan uwanka yake cewa kace masa zaka daɗe a Habujan se gaka kuma da Sassafe lafiya dai ko?" Birki yaci yana cije lebensa, ya tsani sunan nan data ke kiransa kuma a duk sanda tayi hakan tana nufin zagin Baba Bilki ne ta yuwu sunyi hatsaniya shine zata fake da haka ta zageta da alama kuma yau da ɓurɓushin mutunchi tunda har ta kira Jafar da Ɗan uwansa Seda ya daidaita fuskarsa kafin ya waiwaya ya kalleta, babu yabo babu fallasa ya durƙusahar ƙasa kamar yanda yake gaida Mahaifiyarsa yace "Hajiya Ina kwana?" Tana ƙara matsowa ta amsa masa da lafiya tana sake maimaita tambayar dalilin dawowarsa da safiyar nan da be bata amsa ba. Ƙatuwar Robar hannunta ya kalla ya girgiza kai, Nama ne shaƙe a ciki yau Juma'a da alama tayi halin, zuwa take ta zaftare naman Abincin sadaka da akeyi duk ranar Juma'ar, tun suna yara haka Hajiyan takeyi ko ran girkinta ko ba nata ba se taje ta kwashe Naman kuma babu wanda ya isa yace dan me hatta kuwa da me bada kuɗin Naman wato Alhajin gidan. Gaba yayi yana ce mata "Wlh Alhaji ne yayi mun kiran gaggawa zan rakashi Hadeja, yanzu ma sauri nakeyi nasan ya shirya ni yake jira". Ya lura da yanda murmushin kan fuskarta ya ɓace ɓat kamar ɗaukewar wutar Nepa hakan kuma nada nasabada jin cewar Alhaji ne ya kirashi. Wucewa yayi ya barta nan a tsaye, Da sallama ya shiga falon Mony wanda ya tarar da Ƙofar a buɗe, Momy na zaune a ƙasa tareda ƙanwarta Anty Maimuna da bata fi minti Goma sha biyar itama da shigowa Kanon ba daga Katsina inda take aure suna karyawa Ahmad ya shiga. Seda ya cire takalminsa sau ciki a baqin wajen kafin ya shiga yana sake nanata sallamarsa Momy da Anty Maimuna suka ɗago a tare kowacce fuskarta washe suna amsa masa ya zube a gabansu yana kallon Antyn nasa dake masa oyoyo kamar wani ɗan yaro yayi dariya yace "Anty saukar yanzu ko nan kika kwana? Koda yake munyi waya da Momy dazun bata ce mun kina nan ba kenan yanzu kika zo". "Zuwana " kenan Amadi ban daɗe ba, kayan lefe nazo haɗawa ƙnin Baban Sayyid nayi waya da shagon da zan siyi kayan basu fito ba shiyasa nayo nan na karya tukunna" ta bashi amsa seya ƙara washe baki yana gaisheta tareda tambayar Yaranta tace duk suna gida suna gaishesu kafin ya juya ya fuskanci Momy da murmushin kan fuskarta ya gagara gushewa saboda farin cikin ganinsa. Cikeda tsantsar ladabi ya gaisheta ta amsa tana tura masa plate din gabanta tace "Nasan baka karya ba" "Kai Momy, so kike Alhaji yamun faɗa kenan ƙarfe tara fa yace zamu tafi gashi yanzu goma ake magana" ya faɗa yana miƙewa tsaye, Momy ta goge hannunta da tissue tana cewa "Dana ji shiru ma na zata har ka shigo kun tafi dan tun ɗazun dana kai masa abin kari naji kuna waya yace ka kusa gida da ai da Takwaran Alƙali zasu je ban san ya akayi tafiyar ta juyo kanka ba" "Haba dai, kina da rai na taho daga wani gari na shigo har cikin gidan nan na fita ba tareda nazo na ganki kin saka mun Albarka ba ai ko bakida rai na shigo na kalli ɗakinki nayi miki Addu'a Momy" Ahmad ya faɗa, wani murmushi me nuna irin Alfaharin da Momyn keyi da kasancewar sa ɗanta tayi kafin ta miƙe tana cewa "Ka hanzarta dan nasan yaji shigowarka karka ja yayi maka suruti" seya rusuna a gabanta yana cewa "Zan fita" "To Ɗan Albarka, Allah ya kaiku lafiya ya dawo daku lafiya Allah kuma ya tsare ku daga sharrin ƙarfe" Momyn ta faɗa tana dafa kansa kamar ƙaramin yaro ya miƙe yana murmushi yacewa Anty Maimunan ya tafi itama tayi masa Addu'a kafin ya zura takalmin sa rabi ya fita da sauri jin agogo yana buga goma. Anty Maimuna ta rakashi da murmushi kafin ta kalli Momy tace "Allah kenan, idan ya baka dubu masu bata maka se ya baka ɗaya da ze wanke maka takaicin duka dubun nan. Yanzu ki gani har qofar dakin nan Salim yazo keda kika haifeshi baki isa ya leƙo yace ya kika tashi ba balleni baƙuwa zuwan yanzu kuma ba kunya ya karɓi abinci yayi tafiyarsa. Momy ta kai zaune tana cewa "Ai Maimuna Al'amarin Salim a kullum maimakon yayi sauƙi ƙara ta'azzara yakeyi. Ba Salim kadai ba ni yanzu Yayansu shi yafi damuna, ace mutum beyi shashanci ba da ƙuruciya se yanzu daya fara tara iyali? Kuma wannan ƙallababbiyar sabgar siyasar da ya shiga ita take neman canza masa alƙibla, daman ni sam abin be kwanta mun ba. Tunda ya fara yake sakani magana, kullum matarsa na hanyar kawo ƙararsa. Yanzu shekaran Jiya seda sukazo sulhu da saboda tsabar wulaƙanci Yaron nan wai wancan satin ya kawo mata wasu ɗirka ɗirkan yayan Ƙabilu gida wai Yawon Campaign suka zo basu da masauki duk Hotel da suke Kano bega inda ze kama musu ba se gidansa yace ahine ta zo nan take gaya mun na kirashi nayi masa tatas ya sallamesu be daddaraba shekaran jiyan sega wata ya sake kaiwa wai sati ma zatayi a gidan shi zasu tafi Abuja dan haka zata zauna a gidan har ya dawo data kira waya ta gaya mun na sanarwa ubansa bece komai ba, se Alƙali na kira na gaya masa shi kuma ya kirashi sukaje can aka kashe maganar to Allah yasa dai yaji, Haba Yanda kika san su kaɗai ne Yaya a gidan nan kullum cikin sakani magana da ɗakko mun zance suke Salim da Babana na rasa yanda zanyi dasu". "Hmmm, Anty Aisha kenan, ai bazangaji da gaya miki ba kin tafka kuskure a baya kuma sakamakon sa kike girba a yanzu. Sufa Yaya kiwo ne Allah ya bamu, ba kuma iyakar wanda ka haifa daga cikinka sune naka ba, Malamai fa suna cewa ranar Lahira hatta akan gidan auranmu da zamantakewar mu se anyi mana Hisabi kinga kenan dole mu yi iyakar iyawarmu gurin ganin mun sauke duk wasu nauyi daya rataya akanmu shine kuma ya haɗa da kula da tarbiyyar yayanmu da duk wand suke zagaye damu. Kinga waɗannan yaran da kika ringa zuba ido ana cutarwa? Rayuwarsu ta ringa gantafalfala alhalin kinada halin taimaka musu ki kwatar musu yancinsu ta yanda koda basu samu dukkan gata ba zasu samu rangwamen halin da suke ciki amma kika naɗe hannu da sunan ba ruwanki baki shiga abinda ba'a sanyaki ba wlh ko kaffara bazanyi ba harda haƙƙinsu cikin abinda ya saka kika gaza ganin daidai a cikin taki zuri'ar. Kuma irin tarbiyyar da kika bari aka ginasu akanta ita naki yayan da suka tashi suka ɗauka, abinda da yawa muke kasa ganewa kenan a duk sanda kaga Ɗan wani musamman na kishiya yana abinda be kamata ba kar kace babu ruwanka ko bazaka tsawatar masa ba domin ze cuɗanya da naki Yayan, duk bakin tarbiyyar da kika haƙiƙance kina yi musu kuwa kina can ba zaki san lokacin da zasu ɗauki halaye marasa kyau ɗin da kika bari suka ci gaba ba. Kinzo gidan nan kin tarar da yara da yawa, da ace ke me dabara ce a sannan jan su zakiyi a jiki kiyi musu irin tarbiyyar da Kike fatan yayanki su tashi akanta, haka mata masu wayo sukeyi suja yayan kishiya a jiki su kula dasu da tarbiyyarsu karki taɓa duba halin uwarsu ko abinda zata miki domin taki gaban kike gyarawa, yanzu wa gari ya waya? Banda Ahmad da Matan da kika samu Allah ya duba miki ya sassauta abin akansu dukda suma ɗin da nasu, gaba ɗaya yayan gidan nan babu wata shaƙuwa ko soyayya a tsakaninsu, kowa kansa ya sani wlh ina jiye muku ranar da mutuwa zata fara ɗauki ɗai ɗai tsakanin Iyaye ko yayayen, kar a wayi gari a ce cikin Rayayyun yan uwa a rasa masu duba bayan abinda Ɗan uwansu ya bari. Wlh ki farka ki dage da Addu'a ki kuma sa a miki Allah ya haɗa miki kan zuri'arki dan wlh cikin waɗannan Yayan naki Ahmad kaɗai nake da tabbacin yau idan wani cikin sauran ya faɗi ya mutu baze bar zuri'arsa tayi kukan maraici ba, amma kinga wannan Uban namu da Salim? Allah ya rufa asiri kawai kawunansu kawai suka sani sedai Allah ya duba ya shiga cikin Lamarin". Jikin Momy yayi laƙwas kamar an zubawa Salak gishiri, maganganin Maimuna sun shigeta kuma ta sani gaskiya ta faɗa a yanzu ne take nadamar rayuwar baya data zama kamar hoto bata taɓuka komai gurin gyaranmakauniyar tafiyar da akeyi a cikin gidan ba, a lissafinta idan taja nata yayan sun isa suyi rayuwarsu sedai kuma ta tafka kuskure gashi kuma yanzu tana girbar abinta saboda wannan hanyar da Yayayen nata suka ɗauka ta kowa kansa ya sani ta samo Asali daga abinda suka tashi suka gani anayi a gidan nasu ne. Maimuna na kurbar shayi tace "Gara dai ki yi ta kanki kina kallo ita Harbutsatstsiyar gidan naku duk da rashin kan gadonta batayi saken da kan yayanta ya rabu ba kuma komai da ita suke shawara bakinsu ɗaya ke kuwa fa? Banda Ahmad wa yake zuwa ya durƙusa gabanki ya faɗa miki halin da yake ciki ko ga wani abu da zeyi?" "Allah ya rufa asiri dai Maimuna, gama cin abincin mu fita rana ta farayi kuma yai Juma'a ki samu ki gama da wuri" da haka suka bar zancen. Ahmad kuwa bayan fitarsa Kusan karo sukaci da Hajiya dake fitowa daga ɗakinta da tabarma a hannunta da alama shimfiɗa zatayi ta zaunasana'ar tata ta sakawa masu shiga da fice idanu. "Aa, Amadu har ka fito kenan" ta faɗa fuska a washe ba kamar ɗazu dayace .ata Zasuyi tafiya tareda Alhaji ba. Cikeda gajiya da tambayoyinta yace "Na fito Hajiya, na gaya miki Alhaji yana jirana tafiya zamuyi" "Ayyo to, da ai da Yakubu zasuje,sedaga baya Yakubun yace yana da aiki nace ma suje da Faisal shi kuma wai tes zeyi a makaranta ashe kai ya kira banda Alhaji seya tattagoka tun daga Abuja base ya ɗauki Direba yayi tafiyarsa ba? Shikenan dai, ya akayi yau naga ka shigo mana gida hannu na dukan cinya babu yar tsarabar daka saba riƙowa ne?" Ahmad yai zuguɗi yana kallonta se kuma ya zabura daya tuna abi da yake gabansa ya tafi yana cewa "Idan mun dawo zan kawo muku" ya wuce da mamakin Hajiyar, tsarabar da kullum ya kawo haka zata amshe tana aibata shi tana masa shaguben Allah sa da kuɗin Halal ya siyo shine yau tambayar bata gani ba?. Hajiya ta bishi da kallon tsana ƙarara tana jan ƙwafa, ta tsani Yaron ya kuma zamar mata ciwon ido dan ta rasa ya zatayi dashi. Yanzu da Alaƙa take ƙara Ƙarfi tsakaninsa da Alhajin ya sake dagula mata lissafi ba kuna zata lamunta ba duk yanda zatayi setabi gurin datseta tun kafin tayi ƙarfi. Ko yanzu da gayya take ta jansa da magana saboda ya ɓata lokaci har Alhajin ya fito yayi masa tijara burinta kenan ba wani abu ba. A gurguje ya shirya, wata dakakkiyar shadda kalar sararin samaniya ya saka ta haska Fatarsa dake da duhu bacan ba ɗinkin babbar riga ne, be sakata ba ya riƙe a hannu da hular da ze saka da Agogo, Takalmi da Azurfa, cikin sauri ya fesa turare ya fita da silifas a Ƙafarsa. Alhaji na tsaye bakin motar da zasu tafi a ciki an kawo masa ita daidai Barabder yana waya da alama Ahmad alamu sun nuna Ahmad kawai yake jira kenan. Cikin tsantsar ladabi jikinsa har rawa yake ya durƙusa yana gaida Alhajin, wata Kafirar Shaddace data sha aiki na Alfarma a jikin Alhajin, yanayin ƙirarsa ga shigar da yayi ta ƙasaita yasa kwarjininsa nunkuwa tamkar wani Basarake. Ba yabi ba fallasa ya amsawa Ahmad gaisuwar kafin yace masa "Ya haka zaka fito kamar wanda aka koro?" "Babu komai Alhaji, daman so nake sena shiga mota sena ida shiryawa". Harara Alhajin ya maka masa, yasan abinda yake nufi dan haka sum sum ya shige falon ya shiga ƙarasa shirinsa. Tsaf ya fito bayan ya kafa hula Babbar rigar ce dai be saka ba saboda karta yamutse kuma takura masa ma zatayi, data son ransa ne ma Normal Kaftan ze saka na yadi ba shadda ba sedai sanin halin Alhajin tsaf idan yayi shigar da bata gamsheshi ba dizgashi zeyi gaban jama'a babu ruwansa. Shi Mamaki yayi ma da Alhajin ya nemi ya rakashi wata unguwa me muhimmanci irin wannan domin be taɓa ba, Yanzu da sabgogi sukawa Su Zakariyya yawa Yakubu ne abokin rakiyarsa ko Faisal, wani Sa'ilin har Lawan ɗauka yakeyi ya rakashi be san dalilin daya saka Alhajin nemansa ba. A kunne motar take dan haka yayi bismillah ya shiga, Alhaji ya gama sallamar Balarabe me ban ruwan Fulawa kafin ya buɗr gidan gaba kusada Ahmad ya zauna yana hailala, wannan kuma haline klda su Naziru ze fita a gaba yake zama. A ɗarare Ahmad daya gama karanto Addu'ar hawa abin hawa ya taka motar suka tafi, a tare suka ringa ɗagawa masu aiki dake musu Allah ya tsare hannu, Alhajin me halin tsiya dana kirki kenan, a ɓangaren mu'amala da mutanen waje bashida matsala. Duk qanqantar mutum in har musulmi ne yazo giftashi zeyi masa sallama har ya bashi hannu suyi musabiha barshi dai da halinsa idan ya motsa wannan kam kowa ma yi masa yakeyi. Tafiya sukeyi babu me cewa komai in banda karatun Alƙur'ani da Ahmad ya kunna can ƙasa yana bi a hankali. Jefi jefi Alhajin yake amsa waya, wata ta kasuwanci wata kuma Abokanansa ne masu tambayar ko ze samu halartar ɗaurin auran bikin ɗan Abokinsa ne da sukayi makarantar sakandire tare. Sun miƙe hanya sosai kamar daga sama Ahmad yaji Alhajin yace *Masu qorafi akan kun gaji da jin labarin Fatima, kuyi haquri kubi komai a sannu idan kuma baku iya jurewa ku tsallake 🥹🥹 duk wanda yake bibiyar rubuta kunsan yanda nake, nakan fitar da komai dallah dallah ta yanda me karatu ze ringa ji tamkar film yake kallo ko kuma a gabansa akeyi. Wanda salon yayi musu a hakan sunfi masu qorafin yawa amma dole nayi addressing issue din na haqurtar da wanda suke son ayi sharp sharp kuyi haquri ku bi a sannu in sha Allahu ba zakuyi nadamar bin tafiyar nan ba 🙏🙏🙏* *Innar Mahiru* https://chat.whatsapp.com/FKsWield4wPKepHDZwtPUP *ASSALAMU ALAIKUM WARAHMATULLAH* *MUNA GABATAR MUKU DA UMMU-MAHEER COLLECTION Ita din dai kuka sani taku ta gargajiya da take kawo muku kayayyaki irin na yangayu daga kan ATAMFA, BUYERS BATIK, COTONOU BATIK, SWISS LACES, LAGOS LACES, MAYAFAI, KAYAN KWALLIYAR YARA DA SAURANSU. TA SAKE SHIRYOWA TSAF DA COLLECTION NA HIJABAI IRIN NA AFEEN JAYY FA AMMA BANA HAJJAJU BINTA GUMAMA BA* *YI MAZA KU GARZAYO DOMIN KUYI SIYAYYAR KAYAN SALLARKU A GURINTA CIKIN RANGWAMEN FARASHI GA BIYAN BUQATA* *DA AKWAI NORMAL HIJAB ME HANNU, MARA HANNU, POCKET HAND SE WANDA KIKA ZABA KALA KAWAI ZAKI BADA AYI MIKI AIKIN, JILBAB DINMU TAMKAR SAUKAKKE DAGA EGYPT, WANDA SUKA SIYA ZASU BAKI TABBACIN INGANCIN YADINMU. DA AKWAI NORMAL YARD, AKWAI LONDON CREP IYAKAR KUDINKI IYA SHAGALINKI* TWO PIECES GOWN DA V HIJAB NA YARA DA MANYA HARDA MA ABUBUWAN DA BAN FADO BA ZAKI SAMUSU GURIN UMMU-MAHIR DA YARDAR ALLAH. *SANQAMA MATA KIRA KO CHATTING AKAN 08142548705/07061838488 KO KUMA KIYI JOINING GROUP DINTA KAI TSAYE DOMIN SAMUN LATEST DESIGN AND AVAILABLE KAYA DA SUKE A QASA* *MADALLAH DA MASU SO FISABILILLAHI IRIN NA AHMAD BECHI* *MATAR MUTUM* *NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER* *FIKRA WRITERS ASSOCIATION* *LITTAFIN KUDI NE* *PAY 500 A ASUSUN* *7061838488* *OPAY DIGITAL SERVICES* *MARYAM FAROUK* OR *0709290797* *ACCESS BANK* *SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488* *IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705* *Kuyi following dina a Arewabooks @Maryamfarouk01 inda zaku karanta wannan littafin tareda sauran littattafaina* *NAGODE* *BOOK 2* *PAGE 12* "Rayuwa kenan, duk waɗannan da kaji muna magana dasu a sanda mukayi makaranta ƙyamatarmu sukeyi saboda su lokacin a gaban Iyayensu suke mu kuwa Almajiranci aka kawo mu Kano, naci da dagiya tasa muka Shiga Bokon amma yanzu dubi ka gani kowanne cikinsu so yakeyi yayi alaƙa damu, bakaga roƙon da Alhaji Mustapha ya ringayiwa Babanku Alƙali akan ya ɗaga tafiyarsa Umarah yaje masa ɗaurin aurannan ba, Allah kenan wato shiyasa duk yanda mutum yake karka rainashi dan baka san me ze zama a gaba ba, a lokacin suna ganin su yan gatane se gashi a yanzu da Yan Bokon cikin su da Yan Kasuwar babu wanda ya zarce nida Ɗan uwana" Alhajin ya faɗa cikin Alfaharin abun. Murmushi Ahmad yayi, be tanka ba dan Alhajin yakanyi magana shi kaɗai wani sa'ilin, ya tabbatar idan so yakeyi ya bashi amsa kai tsaye ze ambato sunansa a cikin maganar, to mema zece masa shi? Yana wannan tunani kuwa yaji Alhajin ya sake cewa "Ya aikin Super market ɗin kuwa? Jiya Asiwaju ya kirani yana ta zuzuta gurin yace har yafi na Kano girma da tsari ko?" "Ina ga dai kallon tsoro yayiwa gurin gaskiya amma befi rabin na nan Kano ba, kawai dai yanda aka fitar da taswirar ginin ne yasa ya ɗauki hankalinsa, an kusan kammala komai dan har an fara zuba kaya ma, yace so yakeyi a buɗe ranar Bikin haihuwar Yarsa, daman na bari sena dawo ne se muyi maganar" Ahmad din ya bashi amsa yana shafa kai domin ko Legos ɗin baje baniyyarsa daga Zariya idan ya dawo Kano seya bi jirgi. Ginin sabon Shopping Mall sukeyi wanda wani Aminin Alhajin Asiwaju Bayerabe Attajirine a birnin Ikkoh ganin yanda Bechi Mall ya samu karɓuwa a Kano yasa yace Ahmad yaje ze bada fili suyi haɗin guiwa ya sake gina Bechi Mall a Lagos ɗin gashi har an kusa kammala komai se abinda baza'a rasa bane ya rahe a gurin. "Ai tun daga plan daman da gani kasan ginin ze bada ma'ana, Allah ya sanya Albarka yasa a buɗe a sa'a. Maganar kayayyakin mu kuma idan kuna ka samu Idi kuyi yanda kuka saba". "In sha Allah" Ahmad ya faɗa daga wannan seda suka sake shafe kusan minti talatin suna sharara gudu a titi kafin Alhajin ya sake cewa "Ɗan uwanka fa? ya tafi ne ko yana nan har yanzu?" "Aa ya wuce tun ranar Litinin, be kira waya bane?" ya faɗa yana satar kallon Alhajin. Shiru yayi harya fitar da ran ze amsa masa kafin yaji yace "Kai kafi kowa kusanci dashi ka ringa masa faɗa kana nuna masa rayuwa shi yaro ne har yanzu baze gane abinda ake son nuna masa ba. Saboda nayi masa faɗa nasan uwarsa ce ta zugashi tace ya dena kirana ko? To ka jaddada masa wallahi, muddin na sake samun labari makamancin wanda ya faru sena a nan ze gane ni ba abokin wasansa bane, kuma daga ranar ya bar buga Ball". "In sha Allah zan sanar masa, hakan ba zata sake faruwa ba" Ahmad ya amsa masa dan a yanda Alhajin yake magana ya hasala in kuma yace ze fahimtar da shi ya wanke Jafar daga laifin dayake zargin ya aikata yasan rufta kansa zeyi duk su hadu suyi laifi a gurinsa amma banda haka a bune a buɗe kawai dan shi Alhaji besan me duniya take ciki ba shiyasa ya ɗauki abin da zafi. Rape Allegation ai ya rigada ya zama ruwan dare akan Celebrities, Matan sun maida wannan harkar samun kuɗi a shekara Ɗaiɗaidaikun Manyan Celebrities ne suke tsallake sharrin Mata ba tareda kaji ance anyi ƙararsu akan sunyi Molesting wata ba abinda ya faru da Jafar kenan wata yarinya tayi Ƙoƙarin ɓata masa suna akan yayi Raping nata shi Alhaji har se bayan ma anyi case an gama yarinyar ta Ƙaryata kanta har kotu ta yanke mata hukunci kafin can ya gano tsohon labarin a Jarida. Shine dalilin tattago Jafar yazo gida babu shiri, sunga Tijara daidai gwargwado wanda hakan yayiwa da yawa daga cikin Ahalin gidan daɗi dan Alhaji kulle ido yayi ya wanke Hajiya tass ita da ɗan gaban goshinta. Cewa tayi ita bataga laifi ba idan ma Jafar ya aikata abinda kace yayi, ubanwa ya kai yarinyar gurinsa?/ ko janta yayi ta ƙarfi? Basu suke bibiyarsa kamar jela yana yakice su ba banda ma rainin hankali Maza nawa ta buɗewa ƙafa se shi data raina take bibiya da sharri zatace ya mata Fyaɗe shine fa Alhaji ya zazzage mata tijara a tsakar gida yace ba zata saka yaje ya zubar masa da mutunchi a duniya ba. Abu ɗaya yasaka ya sassauta masa be tsaurara mataki akansa ba saboda sunan Bechi da be jona a sabgar ƙwallonsa ba, ba kowa nema ya san Ɗansa bane banda Close Family and Friends da yawa Muhammad Yayanta sukewa kallon Babansa dan dashi ake ganinsa ko Biography ɗinsa kayi searching it only shows Abdullahi Tijjani As his Father's name Nationality kuma Nigerian from Kano shikenan. Daƙyar Alƙali ya kashe maganar Jafar ya koma ashe Alhajin be haƙura ba. Sun isa Haɗeja Lafiya kai tsaye fadar sarkin Haɗeja sukayiwa tsinke inda a can za'a ɗaura auran. Alhaji Mustapha Babandede yayi matuƙar jin daɗin ganin Alhaji Alhaji Audu Bechi, suka riƙe hannun juna ana gaisawa yanda Alhajin ya sake da tsofaffin Abokanansa ana gaisawa cikin barkwanci ya bawa Ahmad mamaki, koda yake daman hakane, duk girma da wani matsayi da mutum ya kai a rayuqa idan ya shiga cikin waɗanda sukayi gwagwarmayar Karatu tare se kaga duk an koma yara ana tuna baya. To tare akaci daɗi aka sha wuya, lokacin da kowa be gama fahimtar tanadin da ubangiji ya masa a rayuwa ba. Yakubu ya taɓasu labarin daya kai Alhajin taron Tsofaffin ɗalibai a ranar har rawa yayi, wai hana yin video akayi shiyasa be ɗakko musu ba abun ya basu mamaki suka ringa hakaito Alhaji yana rawa wane irin farin ciki ne haka ze sakashi ya taka se gashi yau Ahmad yaga makamancinsa a fuskarsa dan Dariyar da Alhajin yakeyi harda ƙyaƙyatawa abin ya tashin kansa ya kuma sake tabbatar da Abotar makaranta tana da wani ƙarfi da tasiri na daban sama da sauran Abota, an girma shekaru sun taru amma idan aka haɗu se a ringa ji kamar an koma bayane. Se bayan da aka ɗaura auren a gurin Reception ya haɗu da yayayen Abokanan Alhajin waɗanda suka kawo iyayensu. Wasu ya sansu suna hulɗa wasu kuma ranar ya fara ganinsu, Basu bar Haɗeja ba se ƙarfe huɗu bayan sunyi sallar La'asar kafin kowa ya kama gabansa. A hanyar dawowa Alhaji ya ware yana masa labari irinsu "kaga wane? Lokacin da muna makaranta fa kaza da kaza amma yanzu kalli kaza ya faru" Ahmad ya lura Alhajin na cike da shauƙin ganin tsofaffin Abokanai shiyasa yau harya maidashi abokin hira. "Ya kamata ku motsa ku fito da mata kuma tunda ƙannenku mata sun tsaya shiririta. Kasan ban fiya mayar da hankali gurin gayyato tsofaffin Abokanai na na ƙuruciya sabgar auren yayana ba amma ina ganin wannan karon har Gala Nigh zan shirya mana ta yanda zasu zo su kwana musha hira kafin ranar ɗaurin aure" Alhaji ya fada. Ahmad ya shafa ƙeya da hannu ɗaya yana murmushi me kama da dariya, wato su Alhaji har Gala Night za'ayi lallai abin nayi ne, shi kuwa Alhaji yanayin nasa se yasa yayi zaton kunya yaji da yace su fito da Mata tunda yau a giya tara yake yan mutunchin na kusa se yace masa "Toakwai ta a ƙasa kenan irin wannan murmushi da kake bugawa, Yar gidan wacece?" "Ƙuuu" cikin Ahmad ya kaɗa, maganar tazo masa a bazata, ba tanan ya shirya tasota ba. Ya rigada ya gama tsara takan Baba Alƙali zebi shi ze kaiwa maganar auransa kai tsaye tunda dai shima Alhajin idan maganar ta tashi shi ze wakilta amma yanayin nasa neman auran yasa gara ya fara samunsa dan ya tayashi gyarota idanma matsala ta shirya afkuwa yanzu kuma Alhaji na nema ya titsiyeshi, be kuma san ya ze ɗauki maganar ba idan ya sanar masa da wadda yake nema musamman da yaji ya tambayeshi Yar wacece kenan yana tsammanin ze samo yar wani Attajiri ko ƙusar gomnati wanda yana faɗar sunansa ze gano wanenene? "Kayi shiru, ko babu ne?" Alhaji ya sake faɗa yana kallonsa. Harda rage gudu Ahmad yayi kafin ya saci kallon Alhajin yaga shi yake kallo shima sannan ya haɗiye yawu yace "Wata yarinya ce Fatima, a Marmara gidansu yake amma cikin lungune se anyi tafiya kamar za'a shiga Alfindiki, Mahaifinta Bakanikene yana gyaran mota da babur Amma kafin ma na fara zuwa gurinta seda nayi bincike wlh mutumin kirki ne kwarai da gaske haka ma ita yarinyar tana...." "Ban tambayeka halinta kona mahaifinta ba ko kuwa kai ne zaka mun binciken halin waɗanda zan haɗa surukuta dasu?" Alhajin ya dakatar dashi muryarsa dai kadaran kada han babu farin cikin da yake ciki dazu haka babu zafin da kai tsaye Ahmad ze zarce cewa be aminta da abinda yazo dashi ba. Tamkar Ahnad yace "Ai naga kamar su Yaya Naziru su sukayi binciken Matan da zasu aura shiyasa baka hanasu ba" se kuma yayi azamar kwabar zuciyar dake neman kwanto masa ruwa ya shiga taitayinsa, Ya sauke ajiyar zuciya tareda yin shiru Alhajin ya sake jefa masa wata tambayar yace "A ina kuka hadu da ita?" "A Shago, sunzo siyayya tare da Yayarta" ya bashi amsa a sanyaye Alhaji ya sakeyin shiru kafin ya kuma cewa "Ita yayar tata budurwa ce ko matar aure?" Se Ahmad yayi saurin cewa "Matar aurece, Dan gidan Balarabe Faranshi take aure ma yaranta uku yanzu" ya shaidawa Alhajin harda sunan uban Mijin Anty Sauda domin ya sanshi, dukda ya rasu amma har yanzu akwai manyan Yayansa da suke huldar kasuwanci dasu, dabararsa hakan zesa Alhaji ya fahimci ba a gidan banza ya nemo mata ba. Alhaji ya muskuta yace "Marmara? Ina ganin Musbahu ne kamar naje Ɗaurin auransa a nan masallacin sarki idan ban manta ba shekaru bakwai kenan yanzu dan tsiran auran da shekara ɗaya Alhaji Balaraben ya rasu. Amma yarinyar daya aura shi ai kamar Baƙar buzuwa ce dan ban manta ba na halaci Dinner da Alhaji Balaraben ya haɗa musu" Rai fes Ahmad yace "Itace, mahaifiyarsu ce Buzuwa amma mahaifinsu haifaffen nan Marmaran ne duk yan uwansa anan tsukun suke yaran ne dai sukayi kama da Mahaifiyar tasu shi yasa idan aka gansu se a dauka Buzaye ne" "Wato farar fatar ce da dogon gashi suka ruɗeka ko?" Alhajin ya faɗa fuska babu wasa yana tsare Ahmad da ido nan ya diririce murnar da yake ta koma ciki, cikin in ina yace "Aa wlh Alhaji kawai dai.." "Kawai dai me? Da ba Suhaima yar gurin Alhaji Lamin kake nema ba?" Alhajin ya dakatar dashi. Tamkar ze fasa masa kuka yace "Ni daman ita ta ke sona, kuma daga baya tace ita ba zata zauna a Nigeria ba tunda yan gidansu sun koma US sedai na bita can nima abinda ya rabamu kenan" "Eh anyi haka, naji yayyenta biyu ma duk auransu ya mutu da sukace zasu bi uban su koma can da zama, Lamin,Lamin ban san kalar kwayar da yake sha ba. Haka kawai ya tattara wai shi ya bar Nigeria banda shirme waɗanda suke a wajenma idan girma ya riskesu dawowa gida suke su mutu cikin Ahalinsu se shi ze tattara ya koma can, to ita kuma Safiyyah yar wajen Goggonka Salaha fa?" Alhajin yayi kiɗansa ya taka rawarsa lokaci ɗaya. Ahmad da gaba ɗaya ya gama shigewa ruɗani, da fari abu kamar ze zo a sauƙaƙe amma kuma yana neman yayi wahala Alhajin se wani kale kalen magana yakeyi, ta maza yayi dan duk ji yake kamar ya fashe da kuka ko Alhajin ze barshi da zaɓinsa yace "Ai ita Abbanta yace yayi mata Miji, Momy bata gaya maka ba auran ma saura wata biyu yanzun ma Anty Maimuna tazo siyan kayan Lefe Ɗan Mijinta ne wanda Safiyyan zata aura" "Wato sun hanaka zasu bawa Ɗan Mijin Maimuna, kai dashi waya fi kusanci dasu?" Alhaji yayi maganar cikin faɗa Ahmad besan sanda ya ɗage kai da hannu biyu ya saki sitiyari ba yana cewa "Wallahi tallahi ba hanani sukayi ba, gajiya Abban yayi da jiran kuje ayi magana kuma daman ya rigani fara nemanta seda ma Anty Salahan tace a fasa dashi Mony ce tace Aa ba za'ayi haka ba tunda dai ya riga a bashi" "Baka da hankali zaka saki mota?" Alhajin ya buga masa tsawa se ya nemi gefw ya faka, Allah yasa babu mota dake biye dasu gab kuma ba gudu yake sosai ba shiyasa daya sakwta bata watsasu wani gurin ba. To fisabilillahi kamar wanda aka ritsa a Kotu Alhaji se zabga masa tambayoyi yakeyi yana muzurai ba dole ya manta abinda yakeyi ba? Shiru ne ya biyo baya, babu kalar addu'ar da Ahmad beyi a ransa ba akan Allah ya sassauto zuciyar Alhaji ya amince da buƙatarsa babu ja in ja. "Tada motar muje gida, zamu ƙarasa maganar a can" Alhajin ya faɗa bayan daya mula. Jiki ba laka Ahmad yaci gaba da tuƙi, har wani zazzaɓi yake ji yana shirin saukar masa domin yanayin Alhajin ya nuna koda ace ze yarda da batunsa tofa se an kai ruwa rana. Sun shiga Kano anyi magriba, a kusada wata Majalisa yace ya tsaya ganin suna hada jam'i da alama makararru ne nan suka yi alwala suka bisu. Bayan sun idar ganin Alhaji na lazumi Ahmad ya tsallaka inda yaga wani me gasa Nama yayi sa'a akwai wanda sukayi nan da nan yasa aka shiga yanka masa kashi kashi aka gama tsaf ya basu kuɗinsu yara suka kai masa mota ya sake jido fruits ya ƙara daidai nan Alhaji ya shafa Addu'arsa ya taso suka cigaba da tafiya. Har bakin falonsa inda ya ɗauke shi ya tsaya da motar Alhajin ya sauka yana Hamdala, filin gidan tarwai da haske tamkar idan allurarka ta fadi zaka ganta. Sarah ce ta fito da Dogon Hijabi da alama aikenta akayi tana ganin Ahmad ta fasa ihun murna ta ɗaleshi, Alhaji ya zabga mata harara kafin ta sauka da gudu ta koma cikin gida se ga gayyar Maimuna da Yan biyun Anty da Mariya tareda Zayyad ta kirasu suka dabaibayeshi suna sowa da murna ga Yah Ahmad ga Yah Ahmad bakinsa ya gaza rufuwa ya ringa ɗaga wadanda ze iya yana saukewa kafin ya buɗe Boot ya shiga fito da ledojin ciki tun a gurin yasa aka ware dan haka ya danƙawa kowa ta ɗakinsu Hatta su Issa dake nan tsaye yayo musu kashinsu suka karba suna murna dayi masa Addu'a, ya gama rabon tsaf ya rage ledoji biyu a hannunsa, Alhaji na tsaye har sannan be shiga ciki ba yana kallon Ahmad. A cikin Yaransa Ashirin da takwas ya fita daban kyautatawarsa ba kadan bace baga su iyayensa ba ga kowa daya rabeshi se yayi sambarka da halinsa, se yake ganinsa kamar shi a zamanin ƙuruciyarsa. "Ina nawa Naman toh? Tun ɗazu nake haɗiyar yawu a mota" Alhajin ya tambaya fuska a tamke kuma, Ahmad ya ƙarasa gabansa ya rusuna yana miƙa masa Leda yace "Fruits ɗin idan an gyara se a kawo tunda kafi so a matse" "Allah yayi Albarka" Alhajin ya faɗa bayan daya karɓi ledar, cikeda farinciki Ahmad ya amsa da "Amin" domin yasan alfanun Addu'ar iyaye, ita take dabaibaye dashi yake ganin haske a rayuwarsa. Tasowarda yayi kamar hadari yayiwa jama'a da yawa rumfa a matsayinsa na matashin Ɗan kasuwa, buɗe shopping mall ɗinsa ya saka kasuwar wasu da yawa tayi ƙasa badan tasirin addu'ar iyayen ba ai da yanzu maƙiya sun kaishi ƙasa. Da kansa ya kaiwa Momy tata ledar kafin ya wuce ɗaki yayi wanka yayi sallar Isha'a dan an rigada anyi a masallaci. Ya ɗan jima a zaune yana azkar da be samu yayi ba a hanya kafin ya sake shiga cikin gidan yana tafe yana kiran layin Fatima wadda tun suna Haɗeja ya kirata basu wani yi magana me tsayi ba se yanzun yake sake so yaji ya take ya kuma ce ta tura masa da Kwalliyar Juma'ar da duk sati seya roƙa kafin ta bashi. Busy yaji layin nata a ransa yayi tunani ƙila da yan gidansu take waya shi kansa badan tafiyar da yayi ba yau ya kamata ya leƙa ya gaida Baffa dan kusan duk sati indai yana Kano ko Fatima bata nan se yaje ya gaishe su, yanzun babban abinda yake a ransa jiran jin amincewar Alhaji game da maganar auransu wanda kuma a jikinsa yana ji in Allah ya yarda ba za'a samu matsala ba fatansa daya Allah yasa kar Alhajin yayi zancen da Hajiya har ya gaya mata yar wa yake nema ita kaɗaice a cikin gidan yake da tabbacin zatayi Adawa da auransa da Fatima domin ta tsani TALAUCI da TALAKA, ya tabbatar kuwa muddin ta sani se inda ƙarfinta ya ƙare gurin ganin haƙansa be cimma ruwa ba na auran Fatima, ko ba dan komai ba ta samu hanyar rama tsaya mata a maƙwogwaro da yayi ya hanata rawar gaban hantsi, ya tabbatar zata shiga ta fita gurin ganin be samu abin da yake so ba amma Allah ya fita. A haka ya shiga cikin gidan Hajiya Rabi na tsakar gidan tana bawa Baba Mairo sallahun abinda zata taho mata dashi wani satin idan zata zo, Baba Mairo dai me girkin gidan tun zamanin Hajiya na Amarya duk haifarsu akayi suka ganta a gidan bayan sun dawo nan Hotoro GRA kusan shekaru Ashirin kenan, wannan tazarar tasa bata biyo su ba saboda har yanzun Mijinta yana raye yana kwance yana Jinya se ya zama se sati sati take zuwa tana girkin Sadaka ana biyanta dukda girma ya kamata yanzun amma macece me lafiya da kazar kazar sannan aikin na rufa mata asiri shiyasa bata saki duka ta daina ba. "Yaya Ahmad, an dawo" Antyn ta faɗa kamar yanda yaran gidan suke kiransa tana murmushi, ya sunkuyar da kansa shima yana murmushin yace "Tun dazu Anty, har nayi wanka naje sallah ina wuni" ya gaisheta bayan daya idasa kaiwa tsugunne ya sake kallon Baba Mairo da bakinta yaƙi rufuwa da ganinsa yace "Iya, ina wuni? Ya jikin Baba?" "Lafiya lau Alhaji, Malam jiki da sauƙi Alhamdulillahi ko da zan fito seda yace na gaishe ka na kuma ƙarayi maka godiya. Na dai barwa Hajiyar tsakiya sallahu da aka ce baka nan amma naji daɗisosai dana ganka mun gode Alhaji Allah ya saka da Alkhairi yaci gaba da yalwata arziƙi ya kuma rabaka da Alhaji Babba da Hajiya lafiya". Anty ce ta amsa da Amin fuskarta a washe ta tabbata halin nasa yayi musu na Alkhairi, kyautar Ahmad irin wadda Annabi yace ayi ce, ka bayar da hannun dama ba tareda Hagunka ma ta gani ba, ya miƙe yana sake cewa Anty "Ina Aboki? Dana dawo da safe banshi ba ina sauri shiyasa ban shigi na dubashi ba" "Ai bama nan ma da wuri na fita ma kaishi Allura seda muka dawo Momy tace ka shigo amma kun fita da Alhaji, yana ciki rigima yake tayi tunda akayi allurar bari Hasna ta kawo maka shi ko zaka shiga?" "Bari na leƙashi to ance idan anyi allurar ba'aso ana jagwalgwalasu ko ƙila zafi take masa" ya faɗa yana nufar ɗakinta. Tun daga wajen falon kuwa yake jiyo kukan Abdallah Autan gidan a yanzu me watanni uku kuma shine Ɗa na shida da Antyn ta haifa. Babban Ɗanta Musa da suke kira Mu'allim nada shekara goma sha takwas yanzu, se yan biyu mata Husna da Hasna masu shekaru sha biyar sannan Mariya me goma Zayyad me shekaru takwas sai kuma Abdallah data haifa watanni uku baya. Fadar tashin hankalin da akasha da Hajiya akan cikin nan bata baki ne dan tabbas Allah ya hakunta zuwan sa badan haka ba iyakar baƙin cikin da takaicin da Anty ta ringa sha na Hajiya da gori da cin mutunci akan tazo tana ta zuba yaya saboda taci gado yar matsiyata yaci ace cikin ya bare kota haifi yaron da lalura se gashi Allah ya bata lafiyayyan Ɗa kuma Namiji abinda ya sake gigita Hajiyar ta ringa abu kamar wadda ta zauce, Allah kaɗai yasan da yanda tasha kan Alhaji haka ya saka Antyn a gaba taje Asibiti aka juyar mata da mahaifa wai da shekarunsa rututu ga manyan yaya abin kunya ne ace har yanzu ana haihuwa a gidansa yana haifar Ƙannen Jikokinsa badan Manyan Yayan Alhaji Babannan da Babangida duk Mazane ba da yanzu ma ya fara aurar da jikoki itama Antyn tace daman ko bece ba ta gama haihuwar. Karɓan Abdallan yayi daga hannun Mariya dake jijjigashi yana cewa "Ya haka, me yasa yake kuka kuma?" "Wlh Yaya Hasna ce ta ja masa ƙafar da akayi masa allura wai zata fi saurin saki shine fa yake ta kukan nan". Ahmad ya harari wadda aka kira da Hasna ta sunkuyar dakai kafin yace "Banda cin zali ya za'ayi kija masa ƙafa? idan ke kikaji ciwo aka taɓa miki ya kikeji hum?" "Kayi haƙuri Yaya" ta faɗa tana sadda kai ƙasa, yayi tsaki kafin ya juya da yaron ya fita Husna Usainarta tace "Wlh Naso Yah Faisal ne ko Yah Salim da kinji a jikinki banza muguwa kawai. A falon Momy da Ahmad ya shiga ta karɓi Abdallah tana cewa "Meya samu babana tun ɗazu nake jiyo kukansa kuma dai shi baya kukan banza?" "Wai Allura akayi masa" ya bata amsa bayan daya sake gaiaheta. "Wayyo, Babana yau ansha ƙarfe, yi shiru kaji kar suyi mana dariya ace tsohona rago ne, Allah ya taimaka bata saukar masa da zazzabi bama zuwa safiya in sha Allahu ze ware" ta faɗa tana zare masa dogon wandon dake jikinsa ta cire masa Diaper da aka matse masa cinya tana sake cewa "Da gani wannan aikin Hasna ne uwar raino yau kam ai a ɗaga masa ƙafa da wata Diaper a barshi yaji da sagaggiyar cinya" tana cirewa kuwa ya dena kukan ya shiga wulla ƙafa, Ahmad yayi murmushi yace "Babu baki, ƙila ma duk abinda ya takurashi kenan yake ta kukan haka su kuma basu sani ba, ina Anty Muna badai ta wuce ba?" "Ka ganni Amadi sallah nayi kai nake jira ka shigo musha hirar yaushe gamo" Anty Maimunan ta faɗa tana fitowa saga Bedroom ɗin Momy. A nan yaci abincin dare tareda Salim da tunda garin Allah ya waye se sannan ya shiga falon ya zauna da Momyn suka gaisa kuma yana gidan wuni sur sallar Juma'a kawai ya fita ya dawo wai bashida lecture a makaranta shine ya wuni bacci. Har gurin sha daya kafin Ahmad yayi musu sallama ya tafi makwanci ransa cike da mamakin abinda ya samu wayar Fatima yana zaunen ya kira yafi sau goma amma still busy ake gaya masa, abin ya bashi mamaki dan layinta akan tsarin call waiting yake in dai wayace da zasu gaya masa sedai idan a DND ta saka wayar ko kuma a kashe take sharrin Network yake ce masa busy, haka ya kwanta duk yanajin babu daɗi ga kewar muryarta duk ta cikashi danya saba koda ba wata hirar soyayya suke ba amma yana jin daɗin magana da ita a haka bacci yayi awon gaba dashi. FATIMA Ƙarfe ɗaya harda mintuna suka gama Ajin ranar dan Lecturan nacewa yayi akan se yayi covering abinda ya rage mana sannan yayi fixing musu test ranar Monday saboda Next week ake saka ran fara First Semester exam. Sanda suka fita har an fara tafiya Masallaci, tayi murmushi tana kallon yanda Mazan Makarantar suke tafiya a sahu cikin shiga me kyau a fili tace "Allah mun gode maka da kayi mu musulmai, dan Allah Badar kalle su, ina son Juma'a a school ɗin nan ranar ne wanda ma baka taba zaton musulmi bane zaki ganshi da Kaftan ya tafi masallaci". Haka suka ringa hira suna ratsa mutane har suka isa Hostel. A gurguje suka yi Alwala, cikim postgraduate Hostel suka fita zuwa masallacin yau basu samu ciki ba saboda sun makara dan haka a waje sukayi sallar kafin suka koma ɗaki. Ta kira yan gidansu suka gaisa a wayar Baffa dan har sannan ba'a gyara wayar Ummansu ba, yaran Anty Sauda na gidan ta ɓata lokaci sosai suna magana dasu harda Autar Goggonsu Faɗima da taje gidan hutun makaranta. Tana gama wayar kiran JAY ya shiga, tayi ƙaramin tsaki kafin ta sauka daga kan gado saboda hayaniyar mutanen ɗakin sunyi baƙi Jama'ar Sururat kunsan mutanen Yarabawa badai ɗaga murya ba idan suna magana. Guri ta samu me kyau ta zauna kafin ta duba wayar yayi mata two missed calls, kusan Minti goma tana jira ya sake kira dan tace ita ba Asararriya bace da zata kira layin waje da Katin Ahmad, harta fidda ran ze kira se ga wayar ta shiga Ringing bata ko tsaya dubawa ba saboda yanda zuciyarta take azalzalarta da son jin wannan muryar tasa ta kai wayar kunnenta sedai Muryar Ahmad tayi mata sallama ba wadda tayi tsammanin ji ba. A taƙaice sukayi magana dan rabta babu daɗi dalilin ta tsammaci JAY ne, ya gaya mata yana Haɗeja ya kai Alhajinsu Biki dalilin tafiyarsa da sassafe kenan maganar batayi tsaho ba sukayi sallama yana kashewa kiran da take ta zaman jira ya sake shigowa. Ajiyar zuciya ta sauke me ƙarfi har ranta taji daɗin da ta kasa tantance na menene amma dukda haka seda taja aji wayar na dabda katsewa kafin ta daga "Hello Baby" ya faɗa da muryarsa me tsinka daskararren jini kota daskarar da tsinkakken to itama dai daskarar da nata jinin yayi dan hatta bakinta ji tayi ya mata nauyi ta gaza furta komai seda ya sake cewa "I'm sorry, Assalamu alaikum". A hankali taja numfashi kafin ta amsa masa daga nan ta sakeyin shiru. Jay dake tsaye gaban Mirror cikin katafaren Bedroom ɗinsa yana taje Quater Million Sajen dake kan fuskarsa yayi ƙaramin murmushi kafin yace "How are you my love?", zare ido tayi kamar tana gabanshi kafin cikin tsiwa nace "when did i become your love? Don't call me that again" "The first time i set my eyes on you, i know you are my lost but found true love" Jay ya faɗa yana ɗaura agogo, fita zeyi, kiran da ya mata bata ɗauka ba shine ya shiga wanka yanzu ya fito yana shiryawa ya sake kiranta. Baki ta tura amma kalamansa sun mata daɗi, wato da confidence yake komai nasa babu wani ɗari ɗarin irin na Ahmad shi gaba gaɗi yake faɗar abinda yake a zuciyarsa. "Hey sweet, are you there?" "Uhm" ta iya furtawa kawai dan ta rasa bakin magana. Ta kasa gane kanta da wannan stranger ɗin, bala'in jin daɗin magana dashi take kusan zata iyacewa a class hankalinta duk yana kan wayar da sukayi da Asuba, bata sanshi ba bata san waye shiba ba amma har cikin ranta ji take kamar sun shekara dubu tare. "I'm going out, dama na kira ne naji muryarki nayi miki barka da Juma'a, i might be late out though, will you wait for me ba zakiyi bacci ba har na dawo muyi magana?" Jay ya faɗa tamkar me barwa matarsa sallahun ze fita wani guri, mamaki ya sake kasheta amma cikin tsiwa kuma ta miƙe tsaye tana kakkaɓe jikinta tace "To ni meye haɗina dakai kuma da zanƙi bacci na jiraka?" "Abinda nake so muyi magana akai kenan, ina so kisan meya haɗaki dani yau" ya bata amsa a tsume jin zata fara masa rashin kunya, wai kuma se shakkarsa ta shigeta harta gyara harshenta tace "Karma ka kirani dan bacci na zanyi koma zan kashe wayar kawai tunda kai idan ka fara kiran mutane se kace sunci bashinka baka haƙura se an amsa" "Wait for me please" ya faɗa da taushin daya saka ta ɗaukewa na sakanni, yayi miskilin murmushi, ya gama gane lagonta ba ita kaɗai ba yammata da yawa muryarsa na cikin abinda yake saurin kassarasu shiyasa ya laƙanci salo salo da yake amfani dasu gurin ladaftar da masu kunnen Ƙashi irinta. "Will you?" Ya sake faɗa da sautin dayafi na farko taushi, tsikar jikinta ta hau zuba, kai ta ringa ɗagawa kamar Ƙadangaruwa kawai kafin dakyar tace masa "Toh, amma kar yayi dare da yawa" "Till i call, bye, I love you" ya sakar mata maganganun kafin ya kashe wayarsa. Taji I lobiyu tabi kashi Miliyan amma bata taba jin wadda ta gamsar da ita irin wannna da bata da tabbacin da gaske yake ko ƙarya ya sharara ba. Da yamma ta suka fita karatu sai bayan Magriba suka dawo rabi da rabin hankalinta nakan Jay dayace ze kirata, dukda yace se dare amma fata take ya sake kira da yammar. Suna hanya Nurain ya kirata akan ya shigo Makarantar. "Ina my Badar? Wayarta baya shiga?" Ya tambayeta. Ta saci kallon Badar data ƙurawa hanya ido kamar me neman wani abu kafin tace "Gata muna tare, ka jiramu a white sit mun kusa isowa" "Alright Bestie" ya kashe wayar. A nan gurinsa suka lalace suna hira har gurin tara dukda hankalin Afeeya rabi da rabi ne a gurin Badar ce suke kurɓar madarar soyayya da Habibin nata ayi faɗi. Tara da rabi tace ita zata shige ciki yunwa takeji Nurain yace suje su siya abinci a Baescope. "Wlh ba zamuje ka sake yarfamu irin na ranar nan yau ban fito da kuɗi ba" Afeeyah ta faɗa yayi dariya yace "Haba da kenan, yanzu ko wani na gani ze yanƙwana Baby na Badar ai se inda ƙarfi na ya ƙare balle nida kaina. Suka tafi a motarsa, a can sukaci ya siya musu Ice cream suka dawo. "Bestie meya faru ne? Fuskarki ta nuna kamar kina cikin damuwa?" Nurain ya tambayi Afeeyah ganin duk walwalarta ta gushe. Tunda suka je gurin yake lura da yanda ta tsume abincinma tsakurarsa tayi bayan ita tace tana jin yunwa jefi jefi kuma tana duba waya tana tsaki. "Babu komai Bestie I'm just too tired, bari na baku guri dan nasan Badar tsuntsun soyayya baze barta ta gaji ba" ta wuce Badar na zaginta. Harta gama shiri ta hau gado badan tana jin bacci ba sedan ranta babu daɗi Jay be kira ba kamar yanda yace. Ta rufe idonta tana jin kamar ta fasa kuka, su Ummi suka tambayeta lafiya tace kanta ne yake ciwo kowa ya mata sannu suka barta. A zabure ta miƙe jin wayarta ta fara ringing, a jikinta taji cewar shine, ta dire daga kan gado tana neman hular da zata saka takalmi ma wari da wari ta zura ta fita har suna karo da Badariyyah. "Wai Afeeya wane salon munafunci kika samu na ba zakiyi waya a ɗaki ba?" Badar ta faɗa tana riƙe Ƙugu, Afeeyan ta harareta tace "Yo aike ke tashen munafunci yanzu, ki gama cika baki Allah ya sawwaƙa me zaki ci da Bestie na ashe mu kika mayar shashashu kuna can kuna tsinke furen ƙauna" "Ya ranki?" Cewar Badar tana fari da ido, Afeeya ta girgiza kai kawai ta fice. Dukda dare ga uban sauro haka ta samu wani saƙo ta lafe ta bi kiran Jay daya katse, be amsa ba ya kashe ya kirata back "Irin Ahmad ta raya a ranta" muryarta na amsa kuwwa a kunnenta ta manta da wani batun Amadi bawan Allah ta fuskanci Jafaru. *MATAR MUTUM* *NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER* *FIKRA WRITERS ASSOCIATION* *LITTAFIN KUDI NE* *PAY 500 A ASUSUN* *7061838488* *OPAY DIGITAL SERVICES* *MARYAM FAROUK* OR *0709290797* *ACCESS BANK* *SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488* *IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705* *Kuyi following dina a Arewabooks @Maryamfarouk01 inda zaku karanta wannan littafin tareda sauran littattafaina* *NAGODE* *BOOK 2* *PAGE 13* "Assalamu alaiki" ya faɗa cikin murya me sauƙi kamar wanda yake cikin nishaɗi sosai. Ta amsa can ƙasa, yayi murmushin daya saka kunnenta fara Ƙaiƙayi kafin yace "Na kiraki morethan ten times baki amsa ba, you are lucky ina cikin farin ciki yau amma da sena hukuntaki" "Toh" tace masa, "Oh toh ma zakice kawai? U are not apologing, Any way how is my sweet baby doing? Ya Juma'a?" Ta karkace ta gyara zama kafin tace "Komi lafiya" "That's great" ya bata amsa se sukayi shiru na kusan minti biyu kafin ya sake cewa "Afeeya, i hope you remeber me?" "Nidai idan zakayi magana ka dena kiran sunana and i don't remember you i don't think we have ever met" ta faɗa da shagwabar da batasan tayi ba saboda yanda yake kiran Afeeyan gaba ɗaya wani yanayi yake sakata. "Babe karki Kashewa Hajiya ni da wannan shagwaɓar taki" ya faɗa, yanda yaja Babe ɗin ya sakata jin wani sanyi yana ratsa mata ɓargo har seda ta haɗe jikinta tanayin kamar kanta na hayaƙin shauƙi. Allah ya sani Ahmad na iyakar yinsa gurin riritata yana faɗa mata kalaman soyayya amma batajinsu kamar na wannan mutumin. "We met on Monday, kina sauri zaki tafi class i followed you to your department a gurin Class Rep naku na samu number ki so you are this popular ina cewa Afeeyah yace ya sanki, i hope you are known for the good not for the other way?". Shiru tayi masa dan idan yana magana bata so ya dena, sautin muryarsa is killing her, "Afeeyah" ya kira sunanta ta amsa da "Uhm". Shiru yayi kafin yaja numfashi yace "Kafin muyi nisa Afeeya let me make this clear to you, ina da saurin fushi like the smallest thing you couldn't imagine can trigger my temper. Na tsani na yiwa mutum magana yayi shiru ko ya amsa mun da uhm ko body language, I prefer kayi mun magana ko zagina zakayi and bana son nuƙu nuƙu da boye boye na tsani ƙarya da munafunci, i love bold and straight forward person in dai kika kiyaye wannan zamu zauna lafiya, lastly I'm a lover boy, i love to be loved and be pampered, kinga idan kina riritani kina shayar dani madarar love na rantse har Ƙafarki zan ringa lasa tsabar biyayya". Bata san sanda ta tuntsure da dariya ba saboda maganarsa ta ƙarshe wai lashe ƙafa kamar wani maye kai wannan mutum da abin dariya yake ma wlh. Tayi dariya sosai shi kuma yayi shiru yana sauraronta seda ta gama dan kanta tace "You are so funny wlh" "Some times" ya bata amsa kafin ya sake cewa "I should make a proper introduction of my self now. Sunana JAFAR but the world knows me as JAY, Bahaushe ne ni haifaffen Kano amma rainon Turai, na bar Nigeria when i was 13 na tafi Manchester nayi joining Football Academy. I'm a professional footballer, shekarana 11 ina taka leda yanzu professionally, I'm currently playing with Arsenal, ina buga number 7 or 9". I'm from a polygamous family, inada siblings da yawa sosai i think that's all that you might want to know now about me for now, may be with time zaki ƙarasa sanin komai a kaina". A duk bayanin nasa babu abinda yayi catching attention ɗinta kamar sunansa da kuma profession dinsa, JAFAR kuma FOOTBALLER? Samun kanta tayi dace masa "Kai kaɗaine Jafar musulmi kuma dan Nigeria da yake buga kwallo a Turai?" "No bani kaɗai bane, akwai Jaybee a Tottenham se Jay Jay a Leinster, but they are all half Nigerians me yasa kika tambaya?" Ya maido mata seta sauke wata ƙarfaffar ajiyar zuciya yanda kasan wadda aka ritsa da bindiga ta samu ceto koda yake da tunanin da yake zuciyarta ai har gara ace bindigar ce, indai ba mantawa tayi ba Jafar ƙanin Ahmad ma ƙwallo yake yi a turai idan ya zama shine Jay da take magana dashi ai sheƙe kanta kawai zatayi ta mutu, zuciyarta ta aminta da cewar Jafar ɗin Ahmad yana cikin ɗayan biyun waɗancan daya faɗa ko Jaybee ko Jay Jay tunda bata san mamanshi ba, ta yuwu halfcast ce kamar yanda yace suɗin half Nigerians ne amma ba wannan JAY ɗin bane ba, babu yanda za'ayi ya zama JAY ma. A yanzun haka suna da aikin da sukayi sharing da Jafar ɗin yasa kaso Arba'in na zumuɗin da takeji akansa ya disashe, zuciyarta har wani harziƙowa tayi da tunanin abokin faɗan nata, Jay da yaji shirunta yayi yawa yayi gyaran murya yace a sanyaye kamar bashi ba yace "Afeeya lafiya kikayi shiru ko da akwai wani abu ne" "Babu komai, kawai sunanka da profession dinka sunyi kama da na wani abokin rigimata" ta bashi amsa, muryarsa har ƙara sauti tayi kamar a fusace yake tambayarta "Wanene shi? Meye ya haɗaki rigima da Namiji?" "Cousin ɗina ne" ta samu kanta da yanko wannan Jibgegiyar ƙarya da seda ta faɗa sannan takaicin kanta ya kamata to saboda me zatayi masa ƙarya? Haka kawai taji bazata iya ce masa ƙanin saurayinta bane ba, daga can Jay ya sauke numfashi yana cewa "Your cousin is a footballer too, wane club yake?" "Nima ban sani ba, amma kamar a Arab countries ɗin nan yake" ta faɗa saboda last tima kamar daga Qatar taji Ahmad yace yazo shiyasa ta bayar kawai tacan Arab countries yake ƙwallon. Bata taɓa ganinsa a fili ko a hoto ba balle ta kwatanta masa shi, a waya suka taɓa magana sau ɗaya wadda yaci mata mutunchi se jefi jefi idan yana gari ta kan jiyoshi tareda Ahmad har ya gasa maganganu itana ta rama. Har sannan murya babu walwala Jay ya sake ce mata "Oh i see, i hope there is nothing between you two? Bama shi ba da farko if you know you are committed to relationship wanda iyayenki suka shiga tell me?" "Babu" ta bashi amsa a sanyaye kamar me tsoron yace ya fasa kulata. "Amma dai Mace kamarki ba zata taɓa rasa suitors ba, ina da kishi beyond your imagination. Bana so nayi sharing abinda nake so da wani, that is why i hate someone saboda the person stole the most precious thing to me" ya faɗa cikin jin haushin Fatiman Yah Ahmad kafin yaci gaba da cewa If you know you are in to any relationship just call it to end saboda me guri yazo kowa ya tafi kawai" "Late comer ya kwace maka budurwa ko?" Ta tambayeshi kishi na neman kamata itama. "Forget it, kawai kiji abinda na gaya miki. Allah i will not accept sharing you with anyone. I love you fisabilillah and i want Marry you Afeeyah. I want to settle down hopely by the end of this year kuma dake nake so nayi aure will you do me the honor and be my beloved wife?" Ji tayi kamar an watsa mata ruwan sanyi, kalamansa sun shigeta har tsajiyar zuciyarta wani yamm takeji a jikinta. Cikin nutsuwa irinta wanda ya san kan soyayya da yanda ze farauci zuciyar mace a karon farko ya ringa tsarata. Tayi shiru tana sauraronsa, tayi nisa cikin hakaito kamanninsa, se ta ringa ji kamar kafin haɗuwarsu a makaranta. Sana'arsa data sani a yanzu ta bata satar amsa tabbas tana ganin fuskarsa a wasu guraren kamar posters, jikin Baburan Adaidaita sahu da sauran gurare. Ta tuna Sani Abokin Yayanta Jay ake masa dalilin son da yakeyiwa Ɗan ƙwallo Jay, amma ya akayi bata ganeshi ba? Koda yake ba wai kallon Ball takeyi ba shima shahararsa ce da kuma yanda su Yah Malam kullum basu da aikinyi se magana akansa tasa ta riƙe sunansa da fuskarsa amma kuma data ganshi a fili ya canza mata. Be rabu da ita ba seda ya tabbatar ya isa duk inda ya kamata a cikin zuciyarta kafin yace taje ta kwanta dare yayi. Be tambayeta komai akanta ba, ta ringa jin wani iri, ta sani surah da kyan fuskar da Allah yayi mata ne ya ruɗi Jay zuwa gareta idan har yasan ainihin ita wacece tabbas ze gujeta, Sanannen mutum a duniya kamarshi bazeyi tarayya da yar Talaka kamarta ba balle har suje ga batun aure. Yanda ya ringa nanata mata Hajiyarsa tana sonsa ya tabbatar mata da Mama's boy ne, yace a gidansu sunfi su Talatin, daga kuma few things daya faɗa mata akan familynsa ta fahimci suma suna da ire iren matsalolin da da yawan Manyan gidajen masu hannu da shuni wanda suka tara Iyalai da yawa suke fuskanta, wasu har a social media zakaga suna raba hali. Yanda ta fahimta suna da matsala irin ta yan ubanci a gidansu, ta tuna Ahmad shima gidansu suna da yawa amma kuma bata taɓajin ya gaya mata wata ɓaraka a tsakaninsa da yan uwansa ba, sudai Allah ya taimakesu toh. Kwana tayi tana juya maganarsa da yake ce mata "Amma kinsan san dana ganki banyi zaton zanji kinyi hausa ba because you look Asian, da akwai wata girlfriend da nayi Zoya she is from Korea amma Dad ɗinta ne Korean mum ɗinta is Arab from Iran so she has that Iranian look and Korean skin, oh my God you need to see her, i have never seen someone as beautiful as she is se ke dana ganinki kunyi kama sosai wlh tsayi kawai zata fiki". "Ikon Allah" ta fada a zuciyata bangare daya kuma haushin wai girlfriend ɗinsa da taji ya ce ya kamata har bata san sanda bakinta ya furta "Oh saboda nayi kama da Ex Girlfriend ɗinka yasa ka kulani kenan?" "Ko ɗaya, sanda nake tare da ita ma she was the one pushing the relationship and i supported her just because she was nice, Zoya was the most beautiful soul i have ever met in my life tana da kirki na ƙarshe ta so ni she really wanted to marry me kuma ko ni i lokacin idan da zanyi aure it will be her but unfortunately she lost her life in a plane crash ta tafi ganin Mamanta a Iran from London bata da lafiya tafiyan da bata dawo na kenan sukayi hatsari shekara biyu kenan and since then i remain single". Ita da kanta ta yarda akwai mutanen da kirkinsu yake sakawa dole kayi mu'amala dasu kamar Ahmad, ta kwatanta a ranta ace shi ya mutu, irin yanda taji yasa tayi saurin kawar da tunanin daga raita Washe gari dakyar ta iya tashi baccin da bata samu isashshe ba, sun daɗe suna magana da Jay a waya sannan data kwanta ta kasa bacci tayita bitar hirar da sukayi. Shida da rabi ta idar da sallah tana Azkar ya sake kiranta ta ɗaga fuskarta da murmushin da batasan ma tanayi ba suka gaisa. "Zan fita ne nace bari na fara kiran Baby na naji ya ta tashi, or you are still in bed?" Ya faɗa salonsa dake kassarata. A shagwaɓe tace "Aa na tashi nayi sallah Azkar nakeyi yanzu". "Kinyi mana addu'a ko?" Ya tambayeta ta ɗaga kai kamar tana gabansa se ya sake cewa "Zan fita Training ki kula da kanki i will call you when I'm back ok?" "Allah ya kaimu" ta bashi amsa a sanyaye dan se taji bata so ya ajiye wayar. Be sake magana ba ya kashe tana ajiyeta kiran Ahmad ya shigo seda ta harari wayar kafin ta ansa. AHMAD Yana zaune a gefen gadonsa, shigowarsa kenan daga masallaci tun Asuba kwana yayi da tunaninta, tunda ya farka da Asubar yaso ya kirata amma ya daure ya bari gari yayi haske. "Fatima, meya samu wayarki jiya taƙi shiga na kira yafi sau goma?" Ya faɗa bayan data ɗaga wayar. Muryarta a kumbure kamar me bacci alhalin haushine ya cikata tace "Bacci nayi da wuri, kuma ban sani ba ta shiga DND se yanzun dana tashi na cire". "Haba nayi mamaki duk hankali na kuma ya tashi amma yanzu na samu nutsuwa tunda lafiya kike, ya school ɗin toh?" Ya faɗa har yana sauke ajiyar zuciya se kuma tausayinsa ya kamata wato So Jarabtace wanda Allah ya dorawa kaɗai yasan wahalarsa gashi itama idan batayi da gaske ba tana neman afkawa komar wanda ze wahalar da ita. Ta miƙe tana ninke sallaya tace masa "Lafiya lau nake, ya hanya? Kun koma Kano ko can kuka kwana?" "A cikin Kano mukayi sallar Magriba ma" ya bata amsa ta haye gadonta tana cewa "Masha Allah kunyi sauri gaskiya toh sannunka" "Yawwa kema sannunki" daga nan suka ɗanyi shiru se ya sake cewa "Bari na barki zaki koma bacci ko yau weekend nima cikin gidan zan shiga na gaida Momy se na dawo na kwanta an jima idan Allah ya kaimu zanje gurin Baffa kina da saƙo ne?" "Aa, babu" ta bashi amsa se yace "Toh shikenan ki kwanta we talk later" "Bye" daga haka ta kashe wayar taja bargo dan bacci be isheta ba Badar ta fincike tana cewa "Gidan uwar wa kika tafi jiya har sha biyu wayarki kuma bata shiga?" "Not this early Badar bacci nakeji" Afeeyah ta faɗa tana sake jan bargon da taga zata takurata ta sakar mata ta janyo Hijabin data cire ta ƙudunduna duk kuma tsiyar Badar bata kula taba dan ita idan taso bacci babu abinda yake hanatayi dan mutum yaga dama ya dakko police band ya kaɗa baccinta zatayi sanin haka itama yasa ta barnta ta koma nata gadon tana cigaba da mita kafin tayi shiru tayi bacci. Se bayan Azahar da tayi wanka tana shiryawa ta lura da aika aikar da sauro yayi mata zaman da tayi a waje jiya jikinta yayi Jaa duk inda ya ciza ya tashi, Maman Minal tace "Yauma cikin flowers kika je yin waya ko? Waini Afeeya wa kika samu da ba zakiyi magana dashi a ɗakin nan ba se kinje cikin sauro?" "Bari na dawo ke kaɗai zan bawa labari Anty Zahra tunda mutane yanzu kowa boye sirrinsa yake" ta faɗa tana hararar Badar ta gefen ido, ta aje turaren hannunta da take fesawa ta kwaɓe fuska tace "Nasan idan kuka sani sena tsani kaina saboda tsokanarku duk na gama cika baki wlh So be kyauta mun ba wlh". Suna class Jay ya kirata lokacin wayar na hannun Badar ta shiga Ig tana duba styles na ɗinkin da zasuyi da bikin Anty Yusra. Ta miƙa mata wayar ta ɗaga ƙasa ƙasa tace masa "I'm in class zan kiraka in mun fita" ta kashe. "Waye kuma Jay kika samu?" Badar ta tambayeta bayan ta maida mata wayar, tayi fari da ido nace "New catch, a big fish" "Yaushe kika zama Money monger Afee?" Ta faɗa tana kallonta, Afeeyah ta zare ido tace "Daga cewa Big Fish? To na janye ni ba abinda nake nufi kenan ba matsayinsa nake kwatanta miki, Professional footballer ne a Arsenal yake wasa ma" Seta kalleta da sauri tace "You mean JAY? No you must be kidding, Afeeyaj a ina ma ze ganki yana UK kina Nigeria? bama wannan ba JAY fa Afee, yes i know you are Beautiful, kin kai a soki but JAY noooo. A yanda nake jin labarinsa he can't date Nigerian girl Hausa for that matter. Shifa ko yammatan da ake ganinsa dasu se kin kallesu kin sake, irin models din nan ne da zakiga kamar su suka yi kansu sedai idan wani ne yake so ya yaudareki da sunansa dan ko a IG kika duba accounts masu sunansa sunfi dubu ma". Kasaƙe tayi tana kallonta, koda ba laifinta bane gaskiya duk wanda tacewa JAY dai na Arsenal take waya dashi kallon batasan me take cewa ba zeyi mata amma dukda haka se tace mata "Toh Badar ina shi Bahaushene me yasa za'ayi mamaki idan yaso Bahaushiya kuma lower class irina?" "Yes Bahaushene Dan Kano nema aka ce amma abinda nake so ki duba shifa babban Celebrity ne, koda yake ke ba sabgar Ball kika sani ba amma da keda kanki idan aka ce miki shine sekin ƙaryata. Kamar fa kice min Messi ya kiraki ne ko Ronaldo". Maganar Badar ɗin ta sakata tunani domin abinda ta faɗi yakan iya zama gaskiya tunda dai ita ba sanin wancan Jay na gaskiya tayi ba haka kuma wannan sau ɗaya ta ganshi sedai tabbas akwai kamanceceniya a tsakaninsu to amma menene ribarsa idan yayi mata ƙarya da sunan wanda ba shine ba? "Dubo mun picture ɗinsa na gani indai shine zan gane" ta faɗawa Badar, seta kalleta kafin tayi dariya da alama cewar da tayi idan ta ganshi zata gane ne ya saka Badar dariyar.i "Ashe kun haɗu face to face ma? ko hoto ya turo miki?" Tayi mata tambayar da sigar rainin hankaki ita kuma Innocently tace mata "A school ɗin nan fa muka haɗu Badar ranar Monday da ace kina nan kema da kin ganshi na fito zan tafi class da safe ya tareni kuma shine wanda Sahid yace ya bawa number ranar da muna tare dake". Data fara dariya har seda hankalin Lecturer ya dawo kansu duk aka juya ana kallonsu babu ɓata lokaci kuwa ya korasu waje kuma har sannan ba wai ta bar dariyar bane guri ma ta samu ta zauna tana ci gaba da abarta dan harga Allah abin na Afeeyah mugun bata dariya yayi, Jay Afeeyah zatace ta gani a cikin ABU Zaria? Jay ne ze shigo Zaria ba tareda garin ya girgiza ba? Da ace Afeeyah na kallon Ball ko ta taɓa nuna ra'ayi akan Jay Footballer da se tace tsabar yanda ta kwallafa rai akansa ne har yasa ya fara mata gizo amma yanzu ta tabbatar wani ne yake so yayi mata wasa da hankali amma ya akayi har Afeeyah tayi falling wa cheap trick kamar wannan da sauri haka? "Bana son iskanci Badar me kika daukeni ne?" Afeeyah ta faɗa a fusace se Badar ta nuna ta tace "Da alama zaman da kikayi a waje kwana biyu kinyi gamo dan wannan maganar da kike batayi kama data me cikakken hankali ba". Ran Afeeyah ya ɓaci ta hayayyaƙo mata tace "Wato kin gama akan Ahmad yanzu kuma kin samu sabo ko? Wani Badar me kika ɗaukeni ne? Alfarma maza sukeyi mun su soni ko kuwa ban kai macen da za'a ce ana so ba?". Kafin ta bata amsa Sahid ya kwaso da gudu kamar wani ƙaramin yaro har yana ture waɗanda suke fitowa daga class ɗin alamar an gama lecture ya tsaya a gabansu yana haki yace "Afeeya i have been looking for you all round the school, na yesterday i remember where i know that Guy's face from, he is JAY Afeeya the great JAY of Gunners was in front of me but i couldn't recognised him God i was so stupid, definetly my village people are behind this misfortune but still I'm lucky and I'm happy that i gave him your number i hope he called? If yes please Afeeya do me this favour of introducing me to him as his ride or die fan wallahi....." "Sahid haba mana ya isa" ta dakatar gashi ganin maganar bata da alamar ƙarewa s zuba yake kamar wanda kanda ya ƙone, a fusace ta sake maida kallonta kan Badar dan ta ƙarasa zazzaga mata abinda ke ranta rungunar da tayi mata tareda fasa ihu kamar zata toshe mata kunne bata ko damu da a waje suke ba ta shiga tsalle tama kasa magana kamar wata wawiya se ihu takeyi. "Innalillahi Badar kinyi haukane ko yaya sakeni dan Allah karki kayar dani" Afeeyah ta faɗa tana Ƙoƙarin yakice Badar amma taƙi sakinta cewa takeyi "Da gaske JAY ne yake son Afeeta innalillahi daɗi kasheni" ta sake fasa wani ihu Sahid na tayata yana mata rantse rantsen wlh shine, yau da safe ya kalli Recap na wasansu kawai ya ganshi shine ya tuna "Amma taya akayi ya shigo harya fita babu wanda ya ganeshi se ku biyu?" Badar data tsagaita da ihub ta tambayeta, Afeetah tayi tsaki tana tafiya tace "Seki nemo shi ai ki tambayesa, ni taya zanyi na sani?" a gurin ta barta saboda haushi ta tafi Hostel tana tafe ranta na suya akan abinda Badar tayi mata so takeyi dagaske ta yarda izgilanci yasa take mata irin waɗannan abubuwan amma zuciyata ta gaza karbar hakan. Da gudu ta bi bayanta dan tayi nisa sosai, ta rungumeta har suna shirin faduwa tace "Haba mana Afee wai fushi kuma kimayi?" wai dan Allah dagaske kin hadu da JAY? Kedai kina da sa'a Afeeyah ga Ahmad yanzu kuma ga Jay kin samu, na daɗe ina crushing akan JAY amma nasan nisan dake tsakanina dashi kamar nisan sama da ƙasa ne shiyasa na sahalewa kaina Afeeya ke me sa'a ce kina zaune yazo har inda kike ya tarar dake na miki murna Allah ya sakamu a danshinku Miji kam se kin zaɓa kin darje" ta faɗa idonta suna kawo hawayen da batasan na menene ba. Wani iri taji, can kuma haushin cewar da tayi Jay crush ɗinta ne shi yasa ta tureta tana cewa "Ni dalla cikani, me kika gama cewa? ban kai kalar matan da yake kulawa ba wani ne yake mun ƙarya dashi" "Afee ki fahimce ni, wlh ruɗewa nayi. Kamar fa nace miki Shahrukhan ya kirani yana sona dan Allah zaki yarda kai tsaye?" ta faɗa da iyakar gaskiyarta, Afeeyah ta fincike hannunta tana cewa "Ai ni ba shahrukhan nace miki ba, Jafar nace Bahaushe kamata dan Kano kinga kuwa ko sarkin ingila ya zama ba abun mamaki bane dan ya so wadda suke da tushe daya. Sannan naji kamar kince crush ɗinki ne ko? Gara da kika faɗamun tunda wuri ba se anyi nisa kizo kina mun ihu da hayaniya a gaban mutane a kansa ba saboda kishi. Zan gaya masa kina sonsa Allah yasa ki masa tunda yanzu na gane ko Nurain da kike mun masifa kina hanani haɗuwa dashi ashe son sa kikeyi". "Karki gaya mun maganar banza Afeeya saboda ma kinga ina lallabaki shine zaki ringa botsarewa bafa ke kadai kika iya tijara ba" Badar ta faɗa tana ja baya yanda fuskarta ta nuna lallai taji zafin abunda Afeeyah ta faɗa mata. Itama seta riƙe ƙugu tana kallonta ta sake cewa "Na faɗa ɗin ko ba haka bane? Duk sanda Nurain ze kirani kin ringa baƙin rai kenan kina bin bini se kinji me muke cewa ba zaki taɓa barina na fita gurinsa ni kaɗai ba haka Ahmad a koda yaushe cikin gasa mun magana kike kina nuna ban kai ba Alfarma yamun daya soni haka kullum cikin yaba kirkinsa kike da nuna da zaki samu kamarsa ba zaki tsaya sokonci iri na ba and now Jafar kai tsaye kin gaya mun he is your crush duk hakan me yake nufi Badariyya?" "Meye haka Afeeyah lafiya kuke taaye kuna hayaniya akan hanya? Abdurrazaƙ course mate ɗinsu daya ƙaraso gurin ya faɗa. Badar data kasa cewa komai tunda Afeeyah ta fara magana ta tsaya kawai tana kallonta ta sauke ajiyar zuciya kafin jiki babu kwari ta fara tafiya ta barsu a tsaye. "Yanzu Afeeya saboda abun kunya keda Badar za'a gani kuna faɗa a kan hanya? Ai koma me ya haɗaku kamata yayi kuje ɗaki ku sasanta amma ba anan ba gaskiya kun bani kunya kuma da alama kece bakida gaskiya dan naji wasu daga cikin maganganun da kikeyi" Abdurrazaƙ ɗin ya sake faɗa. Ajiyar zuciya ita ma ta sauke, bata ce masa komai ba ta juya itama ta tafi, Ribadu Hall ta shiga gurin Islam, ƙawartace tsohuwar Roommate dinsu kuma. Ta kwanta akan gadonta duk tana jin babu daɗ kuma akan abinda ya faru amma ta rasa abinda yasa ta kasa controlling kanta duk abinda ya tunzurata kuma cewar da Badar tayi Jay crush ɗinta ne sosai takejin zafin abin a ranta har sannan akan me zata faɗi haka bayan da tasan suna waya kuma hakan yana nufin maganar So ta shiga tsakaninsu? Islam ta dafa Indomie ta juye a plate kafin ta hau gadon tana cewa "Tashi muci, in Badariyyah na ganki ke kaɗai? Koda yake nasan faɗa kukayi. "Naqoshi, kuma wayace miki faɗa mukayi?" "Ai tunda na ganki ke kaɗai kinzo kin kwanta kamar Manja daman nasan da walakin indai ba bata school ba to faɗa ne kawai zesa ba'a ganku tare ba kuma kece da laifi wato har yanzu dai ba zaku canza hali ba kamar kaji kullum se kun raba hali? Da ana ganin kamar kece abar tausayi Badar ce rigimammiya se wanda ya zauna daku ne ze gane halinki tsaf Afeeyah baki da daɗin sha'ani idan baki so ba" Ƙaramin tsaki tayi tace "You know how Badar can be annoying, rainin wayonta ya fara yawa wlh shiyasa nake kasa yin shiru yanzu" "Yes i know, amma Afeeya kin fita zafin kai maganar ta gaskiya. Na san Badar da faɗa amma da wuya tayi akan rashin gaskiya ke kuwa kina sane kike fitittikewa kiyi abu duk kuma yanda mutum ze nuna miki kuskurenki se kinga dama zaki yarda" Islam ta faɗa calmly. Afeeyah tayi shiru dan tasan gaskiya ta faɗa ko a gida haka Ummansu take cewa tanada rikicin gangan kamar yanzun dai in dai gaskiya ne be kamata maganar Badar ta batamata rai ba amma bata san me yasa take hasala ba duk sanda irin hakan ta hado su dukda cewar koda da gaske tana goranta matan ne batayi ƙrya ba, bata kai matsayin da Maza masu Aji kamar Ahmad da Jafar zasu ringa karakaina akanta ba. Ko a layin ƙawance tsakaninta da Badar ɗin kanta akwai tazara matsayinta na yar Ex Sanetor ita kuma ɗiyar me gyaran mota. "Ke kika takaleta ko?" Islam ta sake tambayarta, a taƙaice ta faɗa mata yanda sukayi da abinda ya haddasa faɗan, "Ke ɗince ai baki iya magana ba Afeeyah ga rashin fahimta kuma da gangan kikeyi" "Yanzu ko wani ne yace miki Badar zata so saurayinki Afeeyah seki yarda balle harke da kanki ki ringa wannan tunanin? Gaskiya kin bani kunya lamarinki kuma ya fara shallake hankali. Tabyaya kina zaune da ita for good three years amma ace babu trust a tsakaninku? kin taɓa kamata da laifin cin Amanarki ko me da zaki ringa wannan tunanin akanta?" Islam ta faɗa cikin fushi kamar wata Mamanta. Ta girgiza mata kai alamar Aa kafin tace "To amma Islam aikin san yanda kullum take mun akan Ahmad, ke kanki shaida ce tasha faɗar da ita ta sameshi da tuni wata maganar akeyi yanzu ba wannan ba" "To ai ko ni zan faɗa miki wlh dani Ahmad yake so Afeeyah da yanzu na haihu ma a gidansa, dan bazamu rufa six months da haɗuwa ba zamuyi aure. Ke kinsan yanda samun Nagartaccen Mijin aure yayi wuya kuwa? Ki ajiye maganar wasata samun me nutsuwa wanda idan ya aureka ze mutuntaka ya mutunta iyayenka ma kaɗai sunyi wuya balle harda Bonus na Tsabar dukiya ga kyau ke kuwa me kike nema a duniyar nna da baki samu ba kike ta bulayi? Let me be prank with you Afeeyah, ki ga wannan Jay kikace ko waye da kika samo yes babban mutum ne world class Celebrity, you can flight with him and get popularity amma zancen aure tsakaninku Afeeyah karki fara saka shi a ranki. Tabbas Allah yakan haɗa soyayya tsakanin duk mutanen da yaso matsayi ko wata nasaba ba zata zama togaciya ba amma kece kike yawan faɗin kin fi so ki auri Miji daidai ke wanda babu me miki kallon kwaɗayi ya saka kika aureshi ko kuma a ringa ganin yafi ƙarfinki, idan ban manta ba kince mun dalilin daya saka baki bawa Ahnad dama ba saboda kina ganin tazarar dake tsakanin Families ɗinku kamar idan maganar aurenku ta tashi za'a iya samun matsala shine yanzu kike so ki saka kanki a soyayyar wanda criticism na fan kaɗai ya isheki kafin aje ga nasa Familyn da baki san waɗanne iri bane ba? Think twice, Afeeyah, kiyiwa kanki Hisabi kafin ki fara abinda zakizo daga baya kina dakin sani. Samun Ahmad da yardar Ahalinsa seya fi miki sauƙi akan wannan sabon mutumin da naga alamun kinyi nisa a cikin soyayyarsa. Kinsan Ahmad kin San duk abinda yakeyi, yana mutuwar sonki idan kika aureshi wlh kin gama dacewa dan kin samu mijin kerewa sa'a amma wannan ɗan ball da kike hasashe kinsan yaya ɗabi'unsa suke? Shin yana da hali me kyau ko kuwa? ace duk kin tabbatar da wannan kin ma kin aureshi wlh yanda kike da bala'in kishin nan iyakar matan da zasu ringa bibiyarsa kaɗai se sunsa kinyi mutuwar tsaye. Soyayyar da kike kwaɗayi ba zaki sameta ba kuma baki isa kiyi ƙorafi ba yana da damar yin duk abinda yaga dama. Ya rage naki kiwa kanki karatun ta nutsu tunda wuri, sannan tun wuri idan kin tabbatar ba auran Ahmad zakiyi ba to ki bar mana filin mu gwada sa'armu tunda ke kanki baya kawo wuta dakyau, lissafinki a gaba a baya kikeyinsa". Ido Afeeya ta zubawa Islam tana auna duk wata magana da take fada amma da kyakykyawan ma'auni bata bari zuciyarta ta kawo mata shirmen data saba ba dan idan haka kawai ne tsaf zata fassarata akan kawai tana so ta rabata da Jafar ne maganar ta ta ƙarshe ta saka ta zabura jin wai ta barsu su gwada sa'arsu akan Ahmad. Tayi rau rau kamar zata saka kuka tace "Duk ku ba zaku gane ba" "Daman ba zamu gane ba mana se ke da kika sakawa kanki abinda yafi ƙarfinki kece zaki gane ai" Islam ta faɗa. Afeeyah tayi shiru me tsayi tana saƙa da warwara. Tabbas auran Ahmad ze fi zama abu me sauƙi fiye dana sabon masoyinta. Amma Jafar take so, ta yarda zuciyarta ta mace akansa Ahmad kuwa koda ta aureshi sedai ta zauna dashi tukuicin kyautatawarsa gareta da iyayenta. Cikin rauni tacewa Islam "Amma yana sona, shifa ya tareni kuma ya nemi number na ya kirani yace yana sona aurena zeyi" "Shi wa?" "Jafar" "Afeeyah kenan, daman zece yana sonki mana, kuma zata yuwu da gaske yakeyi amma kuma ba iyakar son ba kiyi tunanin me soyayyar zata haifar miki? Amma tayaya za'ayi mutumin daga haɗuwa lessthan sati guda ki kamu da soyayyarsa har haka? Ko daman kin sanshi ne?" Islam ta tambayeta. Ta rintse ido fuskar Jafar nayi mata gizo kafin ta buɗe tace *Assalamu alaikum* *Ina matan suke, Manyan mata yan kwalisa da suka amsa sunansu na Mata ba muna mata ba Kawayen Binta gumama?* *SODAH GENERAL ENTERPRISES ce tazo da kanta ba aike ba tana kuma shaida mutu da cewar zafafan kaya sun sauka, kamar yanda kuka sani tana kawo muku suturu na sakawa kama daga kan Atamfa, Laces da dangoginsu* *Wannan karon ta sake taho muku da tsarabar Supplements ingantattu wato Original bawai copy ba. Ku sani bayan abinci jiki yana da buqatar qarin wasu sinadarai da zasu taimakawa ginuwar jikin da lafiyar kowanne bangare na jikin, SODAH ENTERPRISES tana da General Supplements ma'ana wanda suke tattare da Vitamins da dukkan jiki yake buqata sannan tana da special supplements wanda HQ wato gidan mutunchi yake buqata domin sake tsare qima.* *Ina wadda take fama da skin nata yaqi dadin azanci? Fata ta bushe tayi dabbara dabbara ta shafa mai duk a banza se qara lalacewa tayi? To maza ki leqa gurin SODAH ENTERPRISES domin tana da sabulu me kyau da inganci me gyara fata tayi kyau ta goge tayi sulbi baya saka Fari asalin kalarki ze sake fiddo miki ya kuna goge duk wasu tabo ko rashes da suke hanaki walwala, sabulunta babu chemical ba kuma na bleaching bane yawwa karki tsammaci da zakiyi haske Aa sedai glowing kalarki ta ainihi ze fitarda.* *A tuntubeta kai tsaye akan 08137145294* *Ko ki danna wannan link kai tsaye domin magana da ita* https://wa.link/wwvjr3 *Location Kano, tana Nation wide delivery* *MATAR MUTUM* *NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER* *FIKRA WRITERS ASSOCIATION* *LITTAFIN KUDI NE* *PAY 500 A ASUSUN* *7061838488* *OPAY DIGITAL SERVICES* *MARYAM FAROUK* OR *0709290797* *ACCESS BANK* *SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488* *IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705* *Kuyi following dina a Arewabooks @Maryamfarouk01 inda zaku karanta wannan littafin tareda sauran littattafaina* *NAGODE* *BOOK 2* *PAGE 14* "Ban san shi ba ban kuma taɓa ganinsa ba se ranar. Ni kaina Islam bansan ya akayi ba na kamu da sonsa har haka ba. Ta yuwu kodan yayi daidai da tsari da kuma mafarki na akan Abokin rayuwa shiyasa" "Kiyi addu'a idan da Alkhairi a tsakaninku Allahya tabbatar amma ki cire son rai a yayin da zaki nemi zaɓi a gurin Allah kuma ki dena wannan halin na zargin wata zata kwace miki abinda kike so sannan ki lallaɓa Badar wlh Afeeyah samun mutum da ze soki tsakani da Allah kamar ita a yanzu yana da wahala" "To ni yanzu taya zan bata haƙuri kinsan dai Badar sanda kake lallaɓata sannan zata botsare ta fara rashin mutunchi ni kuma ba zan jure ba sena tanka mata" "Tunda kece baki da gaskiya kuwa haka zaki yi shiru ko zaginki zatayi, yanzu ki kirata tazo nan ku sasanta tun wuri ma ba se kun koma ɗaki ku sake raba hali ba a ringa yawo daku a baki" Islam ta sake faɗa ta kalleta da son jin ƙarin bayani ta yamutsa fuska tace "Eh mana, ce miki akayi duk wanda kake dariya dashi me sonka ne tsakani da Allah? A aji ranar ina jin Ummi na hirar kuna ce mata tana yawo bayan kuma abinda kukeyi kenan ko kuwa samarin da suke kashe muku kuɗi ƙannen babanki ne da zasu ringa muku bauta ba tareda suna benefiting komai a gurinku ba" Take ta sake hasala tace "Ita Ummin take cewa haka?" "Bana faɗa miki bane saboda kije kiyi tashin hankali, ke matsalarki kenan bakya cin ribar zance da an faɗi abu kamar wuta fuu zaki tashi se daga baya kizo kina regretting action naki I'm only telling you so that kusan zaman da kukeyi da kowa kuma ba komai zakuci gaba da sakin baki duk sirrinku kuyi ta faɗa a ɗaki ba, ai dai tun muna tare nake muku wannan faɗan daga ke har Badar kun fiya saurin yarda da mutane baku da sirri". Tilas ta kira Badar dan ta yarda da gaske bata kyauta ba ta ringa bata haƙuri bayan tazo, Badar bata da ruƙo, sha yanzu magani yanzu ce dan haka take ta zazzage mata abinda yaje ranta maganar ta wuce. Ta dai gaya mata wlh koda wasa ta sake maimaita mata abinda tayi zata nuna mata bawai bata da zuciya bane ko kuma ita kaɗaice me baƙin rai, zata fita a harkarta dan bazata cigaba da zama da ita Alhalin zuciyarta bata aminta da ita ba. Gurin Islam suka wuni, Badar bata iya boye abinda yake a ranta tayiwa Afeeyah murna akan Soyayyarta da Jay amma tace "Afee karki sakashi a ranki sosai saboda gudun abinda zeje ya dawo. Muyita addu'a idan shine Alkhairinki Allah ya tabbatar amma magana ta Allah nafi sonki da Ahmad sedai idan kuma za'abi ta suna Jay ɗin nan fa ze ɗaga mana aji, ganinmu za'a ringayi muna cafkewa da world class Celebrities, Allah kenan sega Badar zata haɗu da JAY a ɓagas, kinga su MESSI duk zasu zama Abokanmu wayyo Allah na" suka ringa dariya, Afeeyah jinsu takeyi ta tabbatar gaskiya suke faɗa mata amma kuma zuciyarta ta rigada ta afka ga koginda fitowarta se anyi da gaske. ****************** "Naziru kalleni dakyau nayi kama kama da wawiya da zaka zauna kana tsarawa wannan zancen na kama? Ni ba surutun banza da iska nake so naji ba, kuɗina zaka bani maza ka zuba munsu anan" ta warware ƙaramar Ghana Must Go dataje da ita kafin taci gaba da cewa "Maza maza kana ɓatamun lokaci daga nan janguza zanje an yanka wasu filaye zanje na siye na ajiye abuna tunda lamarin ƙannenku babu Allah yan iskan yaya sun zama ɓarayi, yaron nan Faisal da Jafaru yaƙi bashi kuɗin shine yabi dare yayi mun sata, ni banma san nawa ya ɗauka ba dan lissafi ya kwace mun tunda naga haka nace toh ba yanzu ya saba ba, daman na daɗe ina ganin kuɗin nayin ƙasa se in ɗauka ajiya ce ta saka sikayi laushi. Kuma fa kwana suke cikin sanyi yanda kace, kaji ɗakin kuwa kamar dusar Ƙanƙara zata zubo....." "Haba Hajiya, ki tsahirta mana karki ƙware" Naziru ya dakatar da hajiyar dake ta zuba kamar nunanniyar kanya kafin yaci gaba da cewa "Na gaya miki Hajiya yawan shige da ficen da kuɗi sukeyi a personal account ɗina yana neman ya jawo mun matsala. Kinsan dai yanda EFCC yanzu suke saka idanu kan duk wani motsin manyan kuɗi a ƙasar nan, na gaya miki ba'a account ɗin company suke ba kuma ko a nan ne ke account ɗinki idan aka tura kuɗaɗen nan wlh suna iya rufeshi azo bincike ki saka kanki a matsala. Haƙuri zakiyi kamar yanda nace zan ringa ciresu a hankali ana juyawa se a ringa tura miki da kaɗan ko Miliyan ɗaya ce duk wata". "Ai shiyasa nazo da jaka tashi zakayi mu tafi bankin ka ciremun kuɗina na gaji da wannan ƙarairayin naka kullum bayan Alhaji Zakariyya ya gaya mun ya karɓi nasa ni kake so ka cuta kenan ka cinye mun kuɗi to baka isa ba" Hajiyar ta faɗa cikin ɗaga murya. Naziru ya dafe kai, ya rasa bayanin da zeyiwa Hajiya ta fahimceshi, saboda Allah tayaya ze tura mata Miliyan ɗari uku ko kuma ya cirosu ya zuba mata a Ghana Must Go a wannan halin da EFCC ta matsa ko da account ɗin kamfani cikin takatsan tsan suke abubuwa balle aga kuɗi irin haka suka fita daga personal account ɗinsa ai tona masa asiri zatayi. "Hajiya shima kayan kuɗi ya karɓa ba zallarsu ba kuma kiyi haƙuri ki dena ɗaga murya mutanen gidan sunajinki" ya faɗa a tausashe. Ta zabga masa harara tace "Ni kuɗi na nake so, waima kayan uban wane kuɗi kuke magana akai kamar wasu marasa gaskiya haka yace mun wai kaya ya karɓa su kayan basu da suna ne bayan Mai akwai abinda ka fara siyarwa ban sani bane da ake samun kuɗi saboda mugunta baka gaya mun ba balle na gwada nima?" "Zinare ya karɓa na gaya miki na fara haƙar zinare a Zamfara ai" "Dan ubanka da akace dutse yana ruftowa mutane so kake ka mutu saboda rashin godiyar Allah zaka zurƙuma cikin rami wai haƙar zinare Naziru?" Hajiya ta faɗa tana zare ido kamar ance mata dutsen ya rufta dashi. Ya kalleta, da ace watace daban daya tambayeta a duniya waya kaita son zuciya amma uwarsa ce duk iskancinsa baze kwatanta haka ba se yayi murmushi yace "Bafa da kaina nake shiga ba Hajiya kamfani ne suke haƙan da injina kuma jari kawai na saka ina karɓan ɗanyan gold se na fitar a sarrafashi" "To nima ina so a saka kuɗin, amma ni idan an haƙo gida za'a kawomun abuna in ajiye se yayi tsada sannan na fitar na siyar sarƙoƙina ma zan kwashe su idan zan tafi Umarah Turai tace sunfi daraja yanzu acan zan siyar se in baka kuɗin a ƙara jarin yanda za'a ringa samu da yawa. Wallahi fa ance kuɗi akeyi sosai da harkar nan, kaga yaro bashi da ko taro amma dayaje ya shiga rami ya dawo kaga ya zama Miloniya wannan tubda da Inji nema za'a haƙo sedai muna zaune muyita karɓar kaya toh haka za'ayi, amma bani ko Goma ce yanzu na tafi da ita dan na saka rai zan siyi filayen nan har nace a dubamun na bakin Titi zasu fi daraja idan an kwana biyu". Naziru ya sauke ajiyar zuciya jin ya tsarata kuma ta hau kafin ta sake botsarewa ze san abinyi. Dole ya shirya suka fita Banki ya cire 10M aka saka mata a Ghanarta ko tsoro bataji ta haye Napep wai ta tafi Janguza, dayace ze kaita cewa tayi Aa, a dabararta karyaje yaga inda Filayen suke. Yakubu sau biyu yana sace mata Takardun Manyab Fikaye yaje ya siyar, dake bata mantawa da komai nata har gewaya take zuwa taga lafiyar kadarorinta ɗaya taje taga an yi gini har An saka Amarya ɗayan kuma Plaza akayi tayi masifar tayi bala'in ƙarshe tayi Allah ya isa dan Yakubun taurin kaine dashi kamar me kuma hauragiyarta ba tsorata shi take ba, sa'idar data samu yanzu matsayinsa daya ƙaru a Kamfani, sedai shegen Yaron kamar yanda take faɗa kansa kawai yake Azurtawa. Ko sun so ayi cuwa cuwar da aka saba ya kankane komai ya hana ta tabbatar idan suka matsa kuma kamar yanda yake cewa tsaf ze fasa ƙwai, rabuwa dashi tayi yanzu amma tana nan zatayi maganinsa yanzu maganar auran Hajiya ƙarama data taso ce a gabanta daia Abba Tee har iyayensa sunzo anyi tambaya shima Yakubun Aure zeyi. AFEEYAH Sannu a hankali soyayya da shaƙuwa me ƙarfi ta shiga tsakaninta da Jay, wani irin so take masa da bata san iyakarsa ba, kodan ya dace da duk wani mafarki nata akan Mijin da take so t aura ne oho? Ahmad da kansa ya gane cewar akwai wani al'amari a gabanta wanda ya sake karkatar da hankalinta daga kansa saboda yar hirar da yake samun dama sunayi ma yanzu gagara takeyi, duk sanda ze kirata uzuri zata bashi na tana wani abun musamman da suka fara Second semester exam daga tace masa karatu takeyu se ta gaji zata huta alhalin lokacinta karankaf yanzun na Jay ne, karatun kansa ba wani mayar da hankali takeyi kamar da ba da idan akace zasu fara exam da sati ɗaya ma ta dena hawa Social media tattara hankalinta take tsaf har se sun gama sannan to wannan karon kuwa se a hankali, idan tana waya da Jay manta kowa da komai takeyi bata ma son abinda ze katseta se su raba dare suna magana har se da kansa yace ta kwanta tayi bacci dan bata faɗa masa ma mun fara exam ba seda sukayi guda huɗu ya rage uku su gama sannan ranar kuwa tasha fada ta kuma ƙara tabbatar da Jay baya ɗaukar nonsense dagaske kamar yanda yake cewa. Har yajin kiranta yayi na wuni guda aikuwa taji a jikinta dan ya mata mugun sabo da soyayyarsa me tsayawa a rai. Jay ya iya soyayya, ya iya saka mace ta manta kanta duk taurin zuciyar Mace idan ta shiga hannun Jay tilas ta sallama dan yasan duk wani lago na mace da ze karya ta dashi, ita da kanta ta kance salon Jay da Ahmad yana kama. Tabbas da ta bawa Ahmad dama ta buɗe masa zuciyarta ze mallaketa tsaf ta yanda wani baze samu matsuguni ba amma ta rasa abinda ya hanata yin hakan, ta yuwu dalilin zuwan Jay ne, wani lokacin se taji muryoyinsu har kamanceceniya yake mata kawai dai ta Jay tafi ta Ahmad tashi, haka idanunsu iri ɗayane, seda tayiwa hoton Jay kallo na tsanaki ta fahimci haka idanunsu iri ɗayane, shape ɗinsu, kalar kwayar idon da komai Badar tace mata wai Sexy Eyes kenan masu irin idanun sun iya soyayya kuma dasu suke cafke zukatan Yammata ta yarda da hakan dan bata iya haɗa ido da Ahmad se taji gabanta na faɗuwa duk sanda ta kalli idonsa ji take kamar ta sallama masa amma taurin kai irin nata ya sa har aka kawo i yanzu. Saura kwana biyu su gama Exam ranar Ahmad ya kirata, kwana biyu ya bata space tunda tace masa Exam sukeyi idan ya kira bata ɗaga ba kota amsa ta bashi uzuri sosai ransa yake sosuwa shiyasa ya zaɓi daya barta ta gama exam ɗin idan har da gaske itace uzurin daya saka baya samun lokacinta. Tana kwance duk batajin daɗin dalilin yajin kiran wayar da Jay ta daka mata, tunda ya fahimci Exam suke kuma take wasa da karatunta tana biye masa shine yayi fushi. Ya gaya mata baya son mutumin da bashida focus, yana sonta amma baze taɓa haɗa lokacinta da Aikinsa ba me yasa ita zatayi wasa da Karatunta saboda shi? Yace baze sake kiranta ba se sun gama kuma ta tura masa da Time table sannan idan ma ta kirashi baze amsa baz kullum da safe ze mata text haka da rana da dare amma babu phone call saboda magana dashi yasa takeji kamar wata mashashshara ce ta kamata duk ta rasa gane kanta. Tana ganin wayarta na ringing ganin Ahmad ne kamar ba zata amsa ba se kuma ta ɗaga dalilin tunanin da tayi a ranta, tabbas Alhakin Ahmad ne tun ba'a je ko ina ba Allah ya jarabceta da Jay. A sanyaye suka gaisa daga ita harshi babu wani me karsashi, "Yaya Exam ɗin? Saura guda nawa ku gama?" Ya kauda shirun da sukayi bayan gaisuwa ta bashi amsa a taƙaice da "Lafiya lau, saura biyu" "Masha Allah, Allah ya bada sa'a" daga nan suka sakeyin wani shirun. Ya sani idan zasu kwana a haka ba lallai ta sake cewa komai, wlh daze iya da ya rabu da yarinyar nan dan duk wata hanya da mace zata nuna bata ra'ayin mutum ta nuna masa amma zuciyarsa ta kasa haƙura da ita. A kullum cikin Addu'a yake akan idan babu Alkhairi a tarayyarsu Allah ya cire masa ita daga zuciyarsa ya musanya masa da wadda ta fita amma abun kamar ana rura wuta ƙaruwa yakeyi. Idan Jafar yana bashi labarin sabuwar soyayyar daya gamu da ita se yace shi kam bashida sa'a ne a soyayya da Alama. Bega Yarinyar da Jay yake so ba, amma yanda har Jay yake labarinta ya sani ba ƙaramin sonta yakeyi ba itama kuma tana riritashi, ze iya cewa be taɓa ganin Jafar a yanayi na soyayyar gaskiya irin wannan ba, yace masa auran yarinyar zeyi, Bahaushiyace yar Nigeria a Zaria suka haɗu. Yaƙi ko gaya masa sunanta dayace ya tura masa hotonta ya nunawa Fatima ko ta santa nan ya fitittike ya ringa zuba masa Tijara yace kuma baze tura ba se ya dawo zasuje ya ganta face to face ko sunanta baze gaya masa ba balle ya faɗawa Fatiman. "Tana da Friends haɗaɗɗu irinta zan samo maka guda ɗaya ka fita daga sabgar waccen Ajawon Fatiman da take wahalar da kai Yaya Ahmad" abinda Jay ya gaya masa. Ahmad yaja numfashi, kusan minti bakwai daga shi har Fatima babu wanda yace wani abu. A sanyaye yace "Fatima, idan wani laifi nayi miki kiyiwa girman Allah ki sanar mun na baki haƙuri, na gaji da azabatar da zuciyata da kikeyi kusan sati uku kenan kin hanani zaman lafiya nace zanzo kince Aa, idanna kiraki a waya koda yaushe cikin bani Excuse kike me nayi miki? Idan maganar kai gaisuwa da nayi ce kince Aa kuma na haƙura bayan wannan wane laifi nayi miki da kike hukuntani ta hanyar azabtar da zuciyata haka?" A maimakon ta sassauta se maganganunsa suka sake ƙukar da ita, ta tsani Namiji da bashida ra'ayin kansa se abinda mace tace yayi wannan yana daga abinda bata so da Ahmad yanda yake mata wani lako lako kamar ita ce Namijin shine macen, to tun yanzu baya iya taɓuka komai daga abu ya haɗa m Su ya fara kamar zeyi kuka yana lallaɓata idan sunyi auren kenan baze ringa tsawatar mata ba idan tayi masa laifi. Haɗuwarta da Jay tasa ta ƙara fahimtar banbancin Namiji da muna Maza, duk yanda yake nuna So ta yake riritata idan tayi masa abinda be gamshe shi ba murɗewa yakeyi ita ce zatayi ta lallashinsa da ban baki kafin ya sakko kamar dai yanzu daya yi fushi saboda bata maida hankali akan Exam ɗinta ba ta tabbata da Ahmad ne tsayawa zeyi yana lallashinta akan tayi kaza ko kartayi. "Dan Allah Fatima ki tausaya mun. Na sani bakya sona Alfarma kike mun ina roƙon da ki daure kici gaba, ki dubi kalar jarabawar da nake ciki ta Sonki ki tausaya mun. Wlh Fatima da zan iya da tuni na cireki daga raina na rabu dake, koda baki taba buɗe baki kin gaya mun ba nida kaina nasan bakya sona kina kulani ne kawai saboda wulaƙnta ɗan Adam ba tarbiyyarki bace kuma na gode da hakan. Bazan gaji da roƙonki na akan ki bani dama, ki bude mun zuciyarki ko yaya ne in Allah ya yarda ba zakiyi nadamar tarayya dani ba" Ahmad ya sake faɗa a sanyaye. Zuciyarta tayi rauni da jin abinda ya ke cewa, wato shi da kansa yasan bata sonsa amma ya gaza haƙura da ita tashi jarabawar Sonta ita kuma tata Son Jay Allah kenan. Ajiyar zuciya ta sauke na shaking tace "Nifa Ahmad ba haka bane ba, na gaya maka exam mukeyi ina buƙatar isashshen lokaci saboda nayi karatu shiyasa duk wani waya da wani chat na ajiye su amma mun kusa gamawa nan da Three days In sha Allah". Yayi murmushi da jin abinda tace shima yace "Ranar Thursday kenan zaku gama?" Ta yatsina fuska kamar yana kallonta tace eh, se ya sake cewa a sanyaye "To yaushe zaki dawo Kano?" "Paper safe ce, in har na gama komai kafin 12 ma zan taho a ranar in Allah ya yarda" "To nazo na ɗakko ki?" Ya faɗa da sigar roƙo kamar wani me magana da ogarsa a gurin aiki, bata san sanda tsaki ya subuce mata ba tace "Zan dawo da kaina, kasan Baffa ya hana ai ka ringa barin aikinka kana tahowa hidimata". "Dan Allah Fatima karkice Aa kar kuma ki jingina maganar nan da Baffa sedai idan bakya sone kawai sena haƙura" ya sake faɗa gwanin ban haushi kuma ban tausayi kamar ze mata kuka, babu yanda ta iya haka ta yarda akan yazo ya ɗauketa, ita kanta zata ji daɗin hakan saboda hutun Session ne zata tafi da duka kayanta. Ya ringa zabga mata godiya kamar wanda tayiwa kyauta daga ƙarshe sukayi sallama bayan ya sake roƙarta akan dan Allah ko sau ɗaya ne a rana idan ya kirani ta ringa amsawa gaisawa kaiwai zasuyi baze ja mata lokaci ba tace Toh. "Allah sarki Ahmad, wlh yana bani tausayi na daɗe banga soyayya me zafi irin wadda yakeyi miki ba Afeeyah,dan Allah ki tausayawa mutumin nan yaci Albarkacin so wlh na tabbatar ba zaki yi nadamar auransa ba saboda yana sonki" Badar ta faɗa, Afeeyah ta hararaeta tace "Kyaji da fuska biyunki anjima idan Jay ya kira waya jikinki na rawa zakiyita karaɗi kina bashi assurance na ze sameni ke ga campaign coordinator kuma se na gaya masa abinda kike cewa yanzu" "Amma Thruth to be told Afeeya wlh Ahmad yafi sonki, ki gani fa shekara biyu yana binki kina jansa a ƙasa na tabbata Jay baze ɗauki haka ba Mace ta ringa wasa dashi kamar wani Toy, da yanzu ya daɗe da sallama ki" Badar ta sake faɗa. Afeeyah ta tashi zaune daga kwanciyar da take tace "To ai banbancinsu kenan shi yasan mutunchin kansa baze zauna a ringa wulaƙantashi akan abinda yafi ƙarfi ba shi kuwa Ahmad kamar mara zuciya ke nifa ba zan auri Mijin da zan ringa juyawa ba ga yan uwansa basa sona naje ana wulaƙantani baze iya tsayawa ya kwatar mun yanci ba". Badar tayi kasaƙe tana kallonta amma ta haɗiye abinda tayi niyyar cewa ta canza maganar da wata tace "Yawwa, nikam kinsan Familyn Jay ne?" kai ta girgiza mata tana cewa "Aa, me yasa kika tambayeni?" Tayi ajiyar zuciya zata yi magana kenan Ummi tayi sallama ta shigo, ciki ciki ta amsa fuska a ɗaure Badar ce ta tambayeta ya Exam ita kuwa ta zari Bucket ta fita dan tun daga ranar da Islam tace mata tana faɗar maganganu akansu ta washsheta, bata son munafukin mutum, idan ta yarda dakai kayi breaking trust ɗinta shikenan kuma. A gurguje tayi wanka ta shirya dan har Badar ta shirya zata fita Library tace ta jirata suje tare. Maganar da suka fara ɗazu na rantaso take taji dalilin daya saka Badar ta tambayeta ko tasan Familyn Jay dan yanayin da tayi maganar ya nuna akwai wata a ƙasa. A Frizlers sukayi Lunch, tana kallon Badar dake ƙarasa cin abinta tace "Ɗazu kina tambayata akan Familyn Jay?" tasha ruwa ta goge bakinta kafin tace "Oh yah nace kin san wani abu akansu kuwa?" "Nace miki ai ban sani ba, wani abu ne ya faru kuma?" Ta tambayeta tana yatsina fuska, Badar ta gyara zama tace Ranar Monday da naje office din Yah Sani (Abokin Yayantane ta ne da yake Lecturing anan) kinsan na gaya miki na taɓa ganinsa sunyi hoto da Jay sanda yaje Masters Uk hoton na office ɗinsa shine ina zuwa da na gani maganarku ta faɗo mun a rai nave masa two weeks ago Jay yazo school ɗin nan, he was suprised yace mun wai ya akayi na sani, then i told him about your encounter kinga mamakin da yayi kuwa? Ashe Mamansa da Maman Jay cousins ne shima suna bala'in shiri sosai gurinsa ma yazo nan Zaria kwanan sa ɗaya ya wuce babu wanda ya san yazo dan da daddare ya shigo kuma a gidansa ya sauka da safen daya fito ma be san inda yaje ba kuma harya tafi babu wanda yace masa ya ganshi then he asked me wai waye Dad dinki a Nigeria da har Jay yace yana sonki?" "Ban gane ba?" Afeeyah ta katseta fuskar ta na nuna alamar confusion, Badar taci gaba da cewa "Nima abinda nace masa kenan, to cut the story short Afeeyah abinda na fahimta Mamarsa yar Jari hujja ce, Yah Sani ya gaya mun Jay personally bashi da matsala, and tunda yace yana sonki dagaske yake yi amma inda matslar take mawuyacin abune Mahaifiyarsa ta yarda ya aureki saboda a duniya idan da akwai abinda ta tsana be wuce Talaka ba. Yaranta auran Jari take musu kuma babu wanda ta ɗora buri akansa Irin Jay saboda tafi sonsa duk cikinsu matsayin da yakai yasa ta tattara duk wani burinta na duniya akan matar da ze auro, ita a sonta cikin turawa ko larabawa zeyi aure ai kinsan Shahida Anchau ko?" Ta jefo mata tambaya, ruɗu da tashin hankalin da ta shiga yasa dakyar ta ɗaga mata kanta da yayi nauyi Badar taci gaba da cewa "To Mamansu babu yanda batayi akan a haɗa auransu da Shahida ba kinga dai Abbansu kafin ya rasu yayi kuɗi kamar me kuma har yanzu Mamansu kanta tana da kuɗi amma wai Maman Jay taƙi, ba Shahida kaɗai ba yace a Familynsu babu daga gidan da ba'ayi masa tayin aure ba amma taƙi bari ya karɓa. Ki ga dai Familyn ANCHAU duk Kaduna babu wanda be sansu ba saboda tsofaffin kuɗine, arziƙinsu tun duniya na kwance har jikokinsu ba lallai suyi talauchi ba amma Mahaifiyar Jay ta raina su tace bataga yar da ta dace da shi a ciki ba. Ni wlh mantawa nayi ma tunranar ban gaya miki ba se yau abin ya faɗo mun a rai nace masa ma zamuje tare ya faɗa miki da kansa kafin ki ce hassada nake miki ko ƙarya na shirya saboda na rabaki dashi". Ƙasa Afeeyah tayi da kanta tanajin wani abu nayi mata yawo tsakanin ƙirjinta da maƙoshi yaƙi wucewa yayi ƙasa kuma yaƙi haurowa ya fito. Wato kallon yar masu ƙumbar susa Jay yayi mata saboda ya ganta fara ƙal kalar madara ya shaƙi ƙamshin designer turare a jikinta ga Hijabin Crep yard da Ummu-Maheer tayi mata ze tsammaci irin yan Turkey ɗinnan ne ko Egyptian shiyasa yake sonta? Kenan wannan ne dalilin da ya saka yake yawan kawo mata labaran ƙasashen duniya idan ta nuna bata sani ba yace wasa takeyi masa? Bata manta ba ranar nan suna maganar kallon Ball da tace masa Badar na kalla a waya yace me yasa ita bazata kalla ba tace masa kawai, se yace ta roƙi Dadynta wannan Holiday ɗin suje Muje London ta kalli wasan sa Live har take ce masa ita Baffa ne da ita ba Dady ba kuma wace London ita da ko Aiport bata taɓa zuwa ba ya ringa dariya yana cewa ta raina masa hankali kenan kallon yar Masu kuɗi yake mata irin wadda Mahaifiyarsa take da burin ya aura lallai kuwa an yanka ta tashi. "Afeeya your body is shaking, ki nutsu dan Allah ba fa na faɗa miki maganar nan saboda ki saka kanki a damuwa bane ba...." "Na fahimta Badar na gane wlh dama kuma nima ina yawan wannan tunanin a raina, Ahmad da be kaishi matsayi da suna a duniya ba Yan uwansa suna ganin ban dace dashi ba ina ga JAY wanda ba yan uwa ba na tabbata mutanen duniya kansu se sunyi mocking ɗinsa idan suka san yar wa ya aura, damuwata kawai Badar me yasa yasan da wannan tsarin na mahaifiyarsa ze zo gurina? Tun haɗuwata dashi ban boye masa komai a kaina ba, na gaya masa Mahaifina ba kowa bane me neman na kansa ne amma se yayi dariya kawai yaga kamar wasa nakeyi, kuma banyi wani abu na ƙarya da ze saka yayi tunanin na fito daga wani babban Ahali ba ko kawai kenan Surata ce ta rudeshi yayi mun kallon daidai da matsayinsa? Kenan a gidan Masu kudi kadai ake samun Yara masu Kyau da sura irina ba'a haifarsu a gidajen Talakawa?" se tayi shiru tana jin kuka yana taso mata, bata iya riƙe shi ba kuwa ta fara Badar ta miƙe hankali a tashe ta dawo kusada ita ta riƙe hannuna tana cewa "Dan Allah ki dena kuka kinga ana kallonmu" "Badar ina son Jay, idan na rasa shi bansan ya rayuwata zata kaya ba. Na sani ban kai koda matsayin me aikinsa ba amma zuciyata ta yi ɗage ta kai kanta inda be kamata taje ba kuma shine sila, shi ya kwaɗaitamun soyayyarsa irin wadda na daɗe ina nema me yasa be dubi matsayi da tazarar dake tsakani mu ba ya shiga rayuwata da alƙawarurrukan ƙarya da ya san baze cikamun su ba ya san mahaifiyarsa nada zaɓi kullum yake cemun duk abinda yake so shi take so ba zata taɓa hanashi auran wata mace ba muddin yace ita yake da muradi?" "To ai Afeeyah kinga shima Yah Sani ya faɗi abinda ya sani ne kawai akan Mamanshi, zata yuwu ta canza ko kuma kamar yanda ya gaya miki ba zata hanashi auran duk macen da yace yana so ba tunda ta fi sonshi cikin yayanta doke taso farin cikinsa. Ni dalilina na faɗa miki maganar nan saboda karki sake jiki kuma daga ƙarshe ba fata ba ki zama disappointed, amma kamar yanda kika ce shi yasan wacece ke kuma a hakan yace yaji ya gani yana sonki ki kwantar da hankali all shall be well in sha Allah" Badar ta faɗa cikin lallashi. Afeeyah ta kife kai kan Table taci gaba da rera kuka tamkar har ranar rabuwarsu da Jay tazo, she can't imagine loosing Jay, is like loosing her whole life dan bata tsammanin zata sake moruwa, soyayyar sati uku jinta takeyi tamkar ta shekara ɗari uku, daƙyar ta haƙurtar da kanta ta kuma ɗauki shawarar Badar da tace tayi confronting Jay domin tasan makomar relationship ɗinsu tunda wuri tunda dai shi zuciyarta tayi amannan da. Tabbas tana da buƙatar hakan, zata so ya furta mata da bakinsa tunanin da yakeyi akan Ahalin da ta fito sannan zata kawo maaa maganar Mahaifiyarsa taji view ɗinsa akai. *Assalamu alaikum* *Ina matan suke, Manyan mata yan kwalisa da suka amsa sunansu na Mata ba muna mata ba Kawayen Binta gumama?* *SODAH GENERAL ENTERPRISES ce tazo da kanta ba aike ba tana kuma shaida mutu da cewar zafafan kaya sun sauka, kamar yanda kuka sani tana kawo muku suturu na sakawa kama daga kan Atamfa, Laces da dangoginsu* *Wannan karon ta sake taho muku da tsarabar Supplements ingantattu wato Original bawai copy ba. Ku sani bayan abinci jiki yana da buqatar qarin wasu sinadarai da zasu taimakawa ginuwar jikin da lafiyar kowanne bangare na jikin, SODAH ENTERPRISES tana da General Supplements ma'ana wanda suke tattare da Vitamins da dukkan jiki yake buqata sannan tana da special supplements wanda HQ wato gidan mutunchi yake buqata domin sake tsare qima.* *Ina wadda take fama da skin nata yaqi dadin azanci? Fata ta bushe tayi dabbara dabbara ta shafa mai duk a banza se qara lalacewa tayi? To maza ki leqa gurin SODAH ENTERPRISES domin tana da sabulu me kyau da inganci me gyara fata tayi kyau ta goge tayi sulbi baya saka Fari asalin kalarki ze sake fiddo miki ya kuna goge duk wasu tabo ko rashes da suke hanaki walwala, sabulunta babu chemical ba kuma na bleaching bane yawwa karki tsammaci da zakiyi haske Aa sedai glowing kalarki ta ainihi ze fitarda.* *A tuntubeta kai tsaye akan 08137145294* *Ko ki danna wannan link kai tsaye domin magana da ita* https://wa.link/wwvjr3 *Location Kano, tana Nation wide delivery* *MATAR MUTUM* *NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER* *FIKRA WRITERS ASSOCIATION* *LITTAFIN KUDI NE* *PAY 500 A ASUSUN* *7061838488* *OPAY DIGITAL SERVICES* *MARYAM FAROUK* OR *0709290797* *ACCESS BANK* *SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488* *IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705* *Kuyi following dina a Arewabooks @Maryamfarouk01 inda zaku karanta wannan littafin tareda sauran littattafaina* *NAGODE* *BOOK 2* *PAGE 15* A daddafe suka ƙarasa exams idan kaga Afeeyah se ka ɗauka jinya takeyi saboda yanda ta fita a hayyacin ta. Tun daga ranar da Badar ta bata taƙaitaccen labarin Mahaifiyar Jay ta shiga wani yanayi na tunani da lissafin yanda makomarta zata kasance. Ƙarin tashin hankalinta kwanki huɗu kenan basuyi waya da Jay ba, zeyi mata text safe rana dare ya tambayeta ya take amma a ƙarshe ze sake jaddada mata karta kuskura tace zata kirashi har se ta kammala Exam ta san koda ta kira kuma baze amsa ba ita kuma taso suyi magana, ya warware mata abinda ya addabeta a zuciyarta ko ta samu nutsuwa. Ranar Thursday suka kammala, ƙarfe bakwai da rabi suna shirin fita Ahmad ya kirata wai ya shigo Zaria yana Dogarawa lokacin, tayi kasaƙe da waya tana mamaki dan gaba ɗaya ma ta manta da batun ze zo ɗaukarta yau, ita bata ma shirya kayanta ba dan lissafinta kawai se gobe Juma'a zata wuce gidan amma tunda yazo babu damar tace ya koma hakan dai dole zata shirya ta bishi su tafi dan haka suna fitowa daga Exam basu tsaya komai ba suka wuce Hostel. Ahmad ya sake kiranta akan idan babu damuwa zeje Kd yanzu ya amso wani saƙo kafin ta gama shiryawa ya dawo "Idan ba sauri kakeyi ba ka jira kawai mu tafi tare se mu kai Badar gida" ta faɗa masa, Badar ta ƙwalalo ido tana kallonta tace "Ni nace miki yau zan tafi?" "Nima ai ba yau nayi niyyar tafiyar ba saboda ya rigada yazo yasa dole zan tafi, ki tashi dan Allah karmu tsayar dashi" Afeeyah ta gaya mata. Dole Suka kashi kaya dan shirin da basu ƙarasa ba kaɗan ne, Badar nata mitar batayi sallama da Sweetynta Nurain ba kuma sunyi yau ze kaita yawo yanzu tasakata tafiya gida ita dai ta toshe kunne har suka kama hanya. Badar da Ahmad keta hirar su ba tareda sun damu da Afeeyah ba dan daman sun saba muddin tafiya ztacehaɗa irin haka shiru takeyi tabarsu idan ma daga shi se itane sedai ya gaji da magana ya kunna Radio. A gidan Hajiya Ummu Yayar Hajiya Binta ya karɓi saƙon Laces ne ya siyawa Momy, a mota ya barsu ya shiga shi kaɗai da ze fito Hajiya Ummu da itama zata fita daman shi take jira ta biyo shi suka fito tare. "Au daman tare kake sa baƙi shine ka barsu a Mota Ahmad? Rowar yar tawa kakeyi mun ko kuma baka riƙeni uwa ba shiyasa ka hanasu shigowa?" Hajiya Ummu ta faɗa. Ahmad ya duburburce, sam be kawo zata fito ba kuma shi be ƙiyi musu tayin shiga ba sedan baya so su ɓata lokaci dan yasan Antyn Ummun cewa zatayi se sun zauna sunci abinci dan shi kansa daƙyar ta barshi ya fito shaf shaf ɗin gashi kuma yanzu yayi complicating abun. "Wlh Mama ba haka bane, ita wannan gida zamu sauketa Fatima kuma mu wuce Kano tare. Naga rana tayine bana so mu ɓata lokaci amma kiyi haƙuri bari su shigo". Yanda duk ya rikice yana mata bayani yasa tayi murmushi tace "Karkayi kuka na yarda ba da niyya kayi ba". Ahmad yayi dariya, Badar da Fatima suka fito suka gaisheta ta amsa da fara'a tana tambayarsa wacece Surukar tata a cikinsu. "Ki zaɓa Mama" ya faɗa yana shafa kai, tace "Kowaccece a ciki Allah ya tabbatar da Alkhairi, saura ɗan uwanka ya kamata shima ya bar ruwan ido haka ya fitarda mata" ta koma cikin gida bayan tace su jira tana zuwa. Hijabai ta ɗebo ta basu sukayita godiya. Badar data karɓi ledar bayan sun shiga mota kafin Ahmad ya shiga tacewa Fatima "Ke Hijaban Ummu-Maheer (07061838488) ne, kinga ledarta". "Ai sun zaga duk inda bakya zato Kyau iya kyau, kasha gayunka da kuɗi ƙalilan a ringa zaton tafiyayye kika saka dole ki ganshi a gurin manyan mata irinsu Hajiyar nan". Suna yan hirarrakin Ahmad ya dawo suka kama hanya. Tilas seda sukaci abinci sukayi Azahar kafin Momynsu Badar ta barsu suka tafi. A hanya Ahmad nata mata santin kirkin Maman Badar. "Ai Momy badaga nan ba gurin kirki, ita Badar ta gado" amsar data bashi kenan ta kame baki ya gaji da jan maganar shima ya kunna musu karatun Alƙur'ani ƙasa ƙasa suka cigaba da tafiya. Lokaci lokaci yake kallonta yana ganin yanda ta mayar da hankali kan wayarta kome takeyi se Allah idan ta nisa kuma taja tsaki ita kaɗai tayi tagumi ta kalli window. Yana so ya tambayeta me yake damunta amma ya kanne, so yake ya fara jurewa yana danne sonta ko ze samu ta fara dubansa da kimar da yake so. Bukar ya gaya masa ya bata iska, bawai barta ba tunda yana sonta amma ya koyi kamewa shima ya dena nuna mata cewar idan babu ita baze iya rayuwa ba. Wayarta tayi ƙara, yana ganin yanda ta zabura ta duba in beyi ƙarya ba har sautin ajiyar zuciyar da tayi ya jiyo. Suka haɗa ido sanda ta saci kallonsa kafin ta ɗaga wayar. Zuciyarsa ta harba, daga yanayinta da yanda take magana a wayar dukda bajin me take cewa yakeyi ba tsabar yanda tayi ƙasa da murya ya gane da Namiji take maganar. Kansa ya ɗauki zafi, har wani sara masa yakeyi idanuwansa sukayi jajir lokaci ɗaya saboda wutar kishin data tashi ta fara ci balbal a zuciyarsa. Be san ta gama wayar ba seda yaga tana Ƙoƙarin saka cajin wayar ta ajikin cajar motar. Murya a kausashe da irin sautin da bata taɓa jinsa dashi ba ya kira sunanta kafinyace "Ni ba shashashan Namiji bane da kina zaune tareda ni wani ze kiraki a waya ki ɗauka, this should be the last time da zaki kwatanta wani abu kamar haka. Wlh kika sake sena fasa wayar idan yaso naga da abinda zaki cimun fuska kiyi magana da wani Namiji". Tsabar yanda maganarsa ta shigeta har karkarwa jikinta ya ɗauka, tunani takeyi daman Ahmad ya iya faɗa irin haka? Yanda ya juye mata lokaci ɗaya ya firgitata ga speed daya ƙarawa motar yanda kasan zasu tashi sama. "Kayi haƙuri" ta faɗa bakinta na rawa. Har suka isa Kano kuma be sake ce mata komai ba, a bakin layinsu da suka isa ya faka be kulata ba ya fita ya samu yara ya buɗe booth suka kwashe mata kayanta. Be bata fuskar da zata sake masa wata magana ba, a wajen motar ma ya tsaya har seda ta sauka kafin yaja yayi tafiyarsa ya barta da bin bayansa da kallo. A sanyaye ta isa gida kafin ta shiga dai tayi ƙoƙarin daidaita nutsuwarta saboda gudun tambayar meya sameta. Ta tarar da Anty Sauda da yaranta, ganinsu yasa ta sake sakin ranta musamman kuma da sahibul Ƙalbinta ya kirata ya mata fatan sa'a akan Jarabawar da suka gama yace zasuyi magana idan ta isa gida. Wannan birkicewar ta Ahmad ce ta jirkitata amma tana shiga gida ta manta da babinsa ta shiga sabogogi sedai lokaci lokaci yakan faɗo mata, yanda ya fututtuke se taji kamar Jay yana sababi, daman ance masu haƙuri basu iya fushi ba yau kuwa gashi ta tabbatar. Ahmad kuwa seda yayi dagaske kafin ya danne abinda ya ringa cin zuciyarsa, yana da kishi matuƙa musamman akan abinda yake so kamar Fatima. Koda yake binta yana lallaɓata dan yasan kawai ra'ayinsa ne batayi bawai wani saurayi ne da ita daban da yasa take ƙinsa saboda shi ba. Yasan bata double dating, shiyasa ya nace yake ta roƙon Allah yana kuma ƙara cusa kansa gurinta amma yanzu ya fahinci ta samu wani saurayin da take ra'ayi shiyasa harta iya ci masa fuska ta ringa waya dashi a gabansa shi ga sakarai wato bazeji komai a ransa ba. Seda aka kwana biyu da ɗakkota da yayi be sake kiranta ba, dan ya yanke dole ya koyawa zuciyarsa haƙuri da ita tunda har ya fahimci da wani bayan shi yanzu komai yana iya faruwa kenan. Da safe ranar Asabar kwana biyu kenan da dawowar tata yana kwance a ɗakinsa se gashi ta kirashi. Ya ringa kallon wayar kamar wanda yayi loosing memory saboda ya kasa yarda Fatima ce take kiransa da karan kanta yau. Rejecting yayi kafin yabi bayan kiran duk da zuciyarsa nace masa karya amsa ya bar wayar tayi ringing ta gama harta sake kira dan ya tabbatar da gaske shi take kira ba tuntuɓen number tayi ba. "Ina kwana?" Ta faɗa a sanyaye bayan da yayi mata sallama ta amsa. Ya amsa gaisuwar yana jin tamkar ya taka rawar murna, dahgaske kenan idan mutum yaja aji za'a mutuntashi tunda gashi fushin kwana biyu ya juyo masa da hankalin Fatima. "Kayi haƙuri akan abinda ya faru ranar nan banyi da wata niyya ba" ta sake faɗa a sanyaye. Daɗi ya sake kamashi, har tasan ta kirashi kenan ta bashi haƙuri ai kuwa akwai haske a cikin tafiyar. Ya wani mula yace "Babu komai kawai dai na gaya miki idan kika sake sena fasa wayar tunda bazan iya fasa miki baki ba" "Ai dai nace kayi haƙuri" ta sake nanatawa yace "Na haƙura na kuma yafe miki Alhakina da kika ɗauka kika sa nayi fushi dake". "Uhm" kawai tace, suka ɗan taɓa hira kafin sukayi sallama bayan yace mata zeje da yamma tace tana gidan Anty Sauda ya sameta a can dan kwana zatayi. "Toh ko kefa? Nifa harga Allah zancen wani Ɗan Ball be kwantamun a rai ba. Haka kawai zaki kwasarwa kanki abinda ze saka miki ciwon rai idan ya aureki ɗin ma kenan. A matsayinki nawa Afeeyah zakice zaki auri world class Celebrity? Ai ɗagen yayi yawa, irin waɗannan ai ba kowacce mace ba, kuma duk ma ba wannan ba na tabbatar wlh fuskarki ce kawai ta ruɗeshi, babu tabbacin idan yasan wacece ke ya yarda ya aureki a haka gara miki Ahmad ɗin. Mutumin nan ga Hankali, nutsuwa, mutunchi, karamchi uwa uba yana matuƙar sonki kuma ya sanki ciki da bai yasan Mahaifanki a hakan kuma yace yaji ya gani yana sonki ze aureki na rasa wace masifa ce tasa bakya son Bawan Allahn nan Afeeyah wlh in guje miki kiyi nadanar da ba zata amfana miki komai ba a gaba" Anty Sauda wadda ita ta tursasata kiran Ahmad bayan data shaida mata abinda ya faru tsakaninsu ta faɗa. Afeeyah ta zumɓura baki, kafin tayi magana wayarta ta shiga ƙara, ringing tune data sakawa Jay ne dan haka ta miƙe da sauri da wayar a hannunta ta shige ɗaki Anty Sauda ta rakata da ido tana cewa "Idan kina da rabo Allah ya ganar dake amma wlh nasan wannan Jay yake kowa yaudararki yakeyi ba auranki zeyi ba gara tun kina da sauran dama kiyi amfani da ita amma ba takanki zanbi ba, Baffa zan samu tun wuri asan abinyi baze yuwu shekara biyu ki gama yaudare bawan Allah kizo kice ba zaki aure shi ba" taja wayarta ta shiga kiran Baffansu sedai wayarsa a kashe. Tayi ƙwafa a fili ta sake cewa "Har gidan zanje, gara ko auran dole ne miki tunda baki da hankali" ita dai Afeeyah na kan gado tana malele kuwa Jay na kasheta da kalaman Love, tunda suka shirya ta manta komai. Hatta maganar dake ta azalzalar zuciyarta ta mahaifiyarsa bata tayar ba tama manta da batun ta sake zama daram akan Alƙawarurrukan madarar ƙaunar da yace ze shayar da ita idan sukayi aure. Ya mata Alƙawari nan da watanni shida zezo Nigeria musamman saboda ita, ya kuma ce mata zuwan da zeyi zeje ya gaida Mahaifinta daga nan iyayensa suzo dan ya rigada ma harya gayawa Yayansa maganarta shima shirin Aure yakeyi tare za'a haɗa da nashi dan haka ta fara duk wani shirinta da idan yazo tana iya yuwuwa daga tambaya taji an ɗaura musu aure kawai sedai taji ana fito kibi Mijinki. Ranar tayi dariyar maganarsa yace tasaka wasa zata gani da gaske yakeyi, Alhajinsu bashida wasa ko yau yace masa zeyi aure muddin ya yarda da inda ya nemo auran magana ta ƙare tambaya kawai za'aje ayo. Wannan tasa ta yanke shawarar sanar da maganarsa a gida tunda wuri ba wai se rana tsaka ba, ta fara takan Anty Sauda domin itace tsanin da ze kaita gasu Baffa. Muddin tayi na'am da abin tasan komai ze zo da sauƙi sedai daga yanda ta karɓi maganar tasan ko zata yarda se an yi ƙwaibai da ita dan tamkar Badar itama Ahmad ya lashe mata zuciya sonsa suke nasa son abinda ze taɓa shi. Daga ce mata sunyi faɗa tace seta kirashi ta bashi haƙuri idan ba haka ba ta gayawa Baffa ta samu wani saurayi yana hure mata kunne harta kori Ahmad ta masa wulaƙanci shiyasa ta kirashi. **************** Hajiya Binta zaune kan carpet tana zubawa Alhaji Audu faten Accar da tayi masa saboda tana da buƙatu yau da kanta ta tsaya ta masa girki me kyau ta kashe gayu da wata kamfalarta shadda ta saka daham, lallen bikin da aka mata tun yau litinin yayi raɗau a hannayenta da Ƙafa dukda na Salatif ne me yankan Siga amma da yake fatar da sauran Armashinta ya mata kyau. Humrar da akayiwa Amarya Hafsatu ta bulbula abinta ƙamshin har hawa kai yakeyi dan seda Alhajinya kunna fanka bayan Ac dake falon saboda Atishawar da turaren nata ya saka ya fara jerawa. Hira take masa wadda duk labarin irin tsaruwar gidan Hajiya ƙaramar take zayyana masa. Jiya su Turai suka dawo daga jere, dakyar da roƙon Allah ma ta yarda ta zauna dan cewa tayi da da ita za'aje. "Wannan wane irin abune babu kunya kawai Binta ki bimu se a ganki tsalam ace ga uwar Amarya a ina kima taɓa ganin anyi haka? Ita Aisha data aurar da Yaya biyu gata uku wanne kika gani a ciki tajewa jere baku ne kuke zuwa ba se kece zakice se kinje salon ki zubarwa da yarinya ƙima tun bata kai ga shiga cikinsu ba? Abujar ce baki taɓa zuwa ba ko kuwa ance za'a rufe shigarta ne idan bakije yanzu ba?" Turai ta ringa zazzaga mata bala'i dan lamarin Ƙawar tata ya fara kaita bango. Fafur tace Anty Rabi da Momy ba zasuje mata jere ba, Baba Bilki ma da tace ba za'a da ita ba dake har yau na sanyi tayi ba tace ai uban Binta ma yayi kaɗan balle ita ta hanata zuwa gano gidan Yar Audu. Saboda neman suna tace wai Hajiya Balaraba tazo aje da ita tace Aa saje kai Amarya daga ƙarshe dai bisa tursasawar Turai suka tafi da ita da Momy wadda bata so zuwa ba se Hajiya Zainab da Munirah ƙanwar Binta wadda har yau sama da shekaru hamsin kenan tana zaune bata samu Mijin aure ba bayan rasuwar Mamansu ne ta dawo nan Kano da ta fara zama gidan Binta zama yaƙi daɗi se kawai ta siyi gida take zaune abunta tana kasuwancinta tana cigaba da roƙon Allah daya yanke mata dukda ta san cewar ba komai ya janyo mata shiga halin da take ciki ba se haƙƙin baiwar Allah da bataji ba bata gani ba suka laƙa mata sharrin da harta mutu wasu na kallonta dashi. Suka hanata zaman lafiya a gidan auranta harta koma ga Allah. A can Kaduna suka haɗe da sauran yan uwan Binta akaje akayi jeren wanda babu wani abin arziƙi data siya. Kayan Gado dai a BECHI FURNITURES yace aje a ɗaukar mata duk abinda uba yakeyi saɓanin su Khadija dayake ƙayyade Adadin kuɗi yace a ɗauki kaya na kaza. Su Turai ne sukaje suka zaɓa suka darje kaya na ƙarshen mutunchi a shagon, da Alhaji yaga Invoice ya ringa surfa masifar da bata da Amfani domin dai shiya nada dama kuma sun rigada sun ɗauka har an jera dan a Branch ɗinsa na Abuja suka kwasa ƙarshe abin ya ƙare akan Aslamiyyah yace Gado biyu kujera biyu za'a ɗaukar mata saɓanin Hajiya ƙarama da aka sakawa huɗu, ɗaki biyar ne a gidan da faluka biyu manya se ƙarami ɗaya wanda yake haɗe da Master Bedroom a sama shine na Megidan iyayensa sun gyara masa dan haka hatta ɗakin da me aiki zata zauna Royal aka saka saboda samun guri da nuna akwai. Kayan Kitchen dai daman yace musu a Al'adar Hausawa uwa ce takeyi to yana kan wannan magana har akan Hajiya be saketa ba dan haka ita tayi kayan kitchen tarkacen banza da wofi wasu matsiyatan kuloli da fulasai ta bakin Turai. Yanda ta ringa zuzuta ta gama siyan komai dan ƙin yarda suje siyayyar tare tayi, haka ta nuna mata kayan taƙi se randa zasu tafi Jere da za'a ɗiba aka tattara kaya ko cika buhu biyu basuyi ba amma faɗi take "Kinga kaya ko Turai? Dama na gaya miki sena baki mamaki ai bikin Nazira shammatata akayi amma wannan na shirya" "Billahillazi Binta idan baki fitar da kuɗinki kinci kin morawa kanki ba se kin mutu kina kwance a ƙasa zakiga yayanki na wadaƙa dasu, yanzu wannan kayan kike zuzutu akai? Abinda ko Talaka me zuciya se yayi ninkin abinda kikayi wannan abin kike so akai ace daga gidan Bechi suka fito? Turai ta ringa masifa kamar zata ari baki tana kafa mata hujja da kanta yanda takeyi idan zata aurar da Yayanta da sauran ƙawayensu, ta kawo mata Misalin Momy, auran Khadija da Annah ita da kanta tace har seda suka maido da wasu abubuwan gida dan seda aka kai sukaga an siya an ƙara siya tasan kuma yanzu ma na Aslamiyyah haka zata fitar da kanta kunay. Duk wanda yaga kayan gadonta da kujeru yasan ubanta ne yayi mata ke za'a zaga ace uwarta bata da zuciya dan wlh ko yar riƙo a gidan nanta wuci akaita da wannan tarkacen. Ƙarshe se Alhaji Zakariyya da Alhaji Naziru harda Yakubu Turan ta kira tace kowa yazo ya bada abinda ya samu, ta tattara ta bazama kasuwa tayo mata siyayyar kayan kichen na fita kunya suka kai ta barwa Binta tsiyarta da tace ta ajiyewa Auta Saratu ta huta ita tasan ba zata raina wannan ɗin ba toh fa tunda suka dawo aka kawo mata Video shikenan ta kasa nutsuwa labari data kai aya zata maimaito tun Alhajin yana ji harya gaji yace mata "Binta yanda kike nanata mun labarin gidan nan ko zuwa nayi yanzu bazan ɓata ba danna gama gane kowanne lungu da saƙo na gidan, ki bani abincin naci kafin ya huce dan Allah do nakeyi na fita zamu haɗu da Alƙali mu tattauna yanda taro ze kasance kinga lokaci yana ƙaratowa yau Litinin saura kwana huɗu ɗaurin aure". "Ai toh yi haƙuri wlh santin gidan ne yaƙi ya barni, ai Hajiya dai tayi gida Allah ya tsole idon maƙiya yasa mutu ka raba" ta faɗa tana bashi. Shida ya shiga cin abincin yana jinta dan batayi shiru ba. Ta gyara zama tace "Dama Alhaji zancen gurin Kamu ne an gama magana da mutanen nan yanzu sun dawo sunce wai kuɗi yayi kaɗan se an ƙara kuma ni nayi ƙarƙaf dubu Ashirin yanzu se nayi da gaske zan fito da ita ai bikin nan dai ya talautani da gaske". Ya kalleta ta gefen ido a ransa yana mamakinta, wai ta kashe kuɗi kome ta yi se Allah bayan duk abinda ake ciki yana da labari. Zakariyya ya gaya masa su suka bada kuɗin kayan kitchen bayan ta ɗiora musu Alhakin abinda za'aci a gurin Mother's eve data shirya shi kuma nan be san Buhu nawa da galan na mai nawa da sauran kayan abinci data kwashe masa a Store tace za'ayi abincin biki ba. Kaji ɗari biyu ya saka aka bata ita kaɗai banda Sa da za'a yanka na abincin yini. Tunda aka fara zancen bikin nan Aisha bata ce ma ya bata sisin kobo ba, Bilki ce ta nusashsheshi har ya batan dukda be kai ko kwatan abinda Binta ta Ƙwamusa a hannunsa ba. Kayan gado kansu ya banbanta Hajiya Ƙarama cewa yayi su ɗauki wanda ya musu Aslamiyya kuwa dalilin ɓarnar da su Turai suka masa shiya faɗi kalar wanda za'a ɗaukar masa an gaya masa Ahmad da Sarki ne sukayi cikon Kuɗaɗe masu nauyi suka ɗaukar mata irin na Hafsatun kuma duk abinda ya kamata ace yayi wanda Aisha bata tambayeshi ba su sukayi yana kallo aka ringa sauke ruwa da lemo besan katan nawa bane inji Ahmad Jafar kuma shi ya siya Musu Cinema Tv su biyun nan cikin Yaya bila'adadin daya haifa ne suke da zuciyar bashi gudummawar auran ƙannensu dukda sun san yana dashi ba babu ba amma yaji abinhar cikin zuciyarsa. "Alhaji kayi shiru" Hamshaƙiyar ta girgizashi. Ya aje farantin hannunsa ya miƙe tsaye yana cewa "Ki karɓo kuɗinki kizo kuyi a nan cikin gidan kamar yanda su Aisha zasuyi ni banida wasu kuɗi da zan sake baki kuma a yanzu nayi iya abinda zan iya" "Ai shikenan, kana ji Jafaru wai baze zo bikin bako? Gaskiya ka kirashi kayi masa magana ta yaya za'ayi ace baze halarci ɗaurin auran ba? Ta ya mutane wai zasu san Ɗanka ne yafi so ayi ta kallonsa a ba kowa ba ai idanya fito kowa ya san Ɗanka ne darajar sa seta sake linkuwa a ƙasar nan ko ya kace?" Ta sake soko masa wata maganar, ya miƙe yana shiga ɗaki yace "Duk yanda kika ce Binta, bari na shirya na fita dai na baki guri" ya barta tana cizon yatsa. Daman ba Even centre data kama, tunda taji a gida Momy zatayi Kamunta zata kira masu Decoration taje kakarta ta yanke saƙa bari zatayi ta gama shirya komai se ranar tayi ta kankane ita da mutanenta dan ba zata iya zare Miliyan nawa ta kaiwa masu gurin biki ba, abinci ma da Turai tasa ta kashi kuɗaɗe ta bayar ciwon rai takeyi, so tayi ta bawa masu aikinsu ayi shi nan a cikin gida amma tace gun yan gayu zasu kai, so tayi ya bata kuɗin ta rage asarar wanda tabayar shine yace bashida su yanzu duk kwalliyar nan da tayi ta tashi a banza kenan ai shikenan. Alhaji ya fito a shirye yana waya, bata san da waye ba abinda taji kawai ya fizgi hankalinta shine "Babu damuwa nagode, bari mu gama da hayaniyar wannan bikin zanyi magana dashi. Idan son samune ya haƙura da yarinyar ya nemi wata dan sam banji abin ya kwanta mun a rai ba amma bama so na hanashi abinda yake so saboda yaron nada biyayya nasan muddin nace Aa tilas ze haƙura koda ace hakan ze cutar dashi amma yanzu zan samu Alƙali shima da maganar yanda mukayi zakaji". "Toh fa wane yaro kuma ake magana akai?" Tayi tsalam ta tambaya bayanya kashe wayar. Yana tafiya ze sauka ƙasa tabi bayansa yace "Ahmad ne, ya samu yarinyar da ze aura. Kiyiwa wancan yaron magana shima ya dakata da shashancin da yakeyi ya fitar da mata dan tare zan haɗu bana son Biki a rarraben nan" "Yo naji kana cewa yarinyar bata maka ba? Halan kwashe kwashe yayo ko? Ni daman nasan za'a rina Allah yasa dai ba gidan matsiyata ya kwaso auran ba mu shiga uku su ƙara yawa bamu gama data gidan nan ba ya kwaso mana wata" Hajiya ta faɗa shidai be bata amsa ba ya fice daga falon dan Malam Sadi Driver sa yana tsaye harya kunna mota. Ta wuce ciki inda ta baro ƙawayenta da sukazo ana ta tsara yanda biki ze kasance, Kamu dai rigar na Momy zasu shiga dukda ba haka su Hajiya Zainab suka so ba Turai kuma tace haka ne daidai tunda dai Yaran nan ubansu ɗaya toh ayi Kamun nan a tare idan yaso tunda kowacce gidan Mijinta sun shirya Dinner se suyi abarsu daban ga sauran events da kowacce Amarya zatayi da Ƙawayenta. "Yanzu kawai sedai mu zama yan kallo mun raɓe raɓe kenan?" Hajiya Sha'awa ta faɗa, Binta ta karkace tace "Inji wa? Ai biki namune wahala kawai zasu mana su shirya komai. Da kunji ance ina uwar Amarya ku rufa mun baya mu shige, duk wani kira da za'ayi ku shike kuyi kinini karku basu wata ƙofa a gurin" akayi shewa aka tafa. Se ranar Laraba Ahmad ya kaiwa Fatima Ɗinkakkun kaya, Atamfa me kyau da akayiwa ɗinkin zamani amma Modest ɗinki se wani shegen Lace da Anty Sauda tace ya haura dubu ɗari biyu. Kowanne kaya da mahaɗinsa, Takalmi, mayafi, jaka harda Sarƙa da agogo. Zobunan gold guda biyu ya saka mata a ciki ganinsu ya tuna mata da ranar da yace ta nuna masa hannunta kenan measurement ɗin hannun ya ɗauka. Yace mata Atamfar ta Ankon Kamun ce dan ya gaya mata zasuyi biki har Iv ya tura mata Lace kuma kawai ɗinka mata yayi na Dinner. Tace ba zataje ba Umma ta goya mata baya a cewarta babu tsayayyar magana a tsakaninsu da har zata saka taje musu biki, idan kuma zuwan nata ya janyo wani abu da ba za'a so ba fa? Gara dai da ace anyi magana yan uwansa sun san da zamanta da sauƙi ko cikin yan uwa tana iya samun wata suje tare su dawo. Baffa ma da aka gaya masa cewa yayi Aa. Da kansa ya kira Ahmad yace ba zataje ba, yayi kuma faɗan zobuna har biyu da Umma tace masa zinare ne yace in yazo ya karɓe su ya ajiye idanAllahyasa taje gidansa ya bata ya dai amsa da Toh amma koshi Baffan yasan baze karɓa ba dan yasha ya kawo mata abu yace a mayar yaƙi karɓa sedai ya kalallameshi da magana yace ko babu soyayya tsakaninsu Baffa Babansa ne zeyi mata komai saboda shi. Wannan ya rushe batun zuwanta Biki wanda daman ko da an barta a karan kanta ba zata so taje ba, to wai se taje a matsayinta nawa??? An dai yi biki a gidan Alhajin Bechi lafiya duk kalen bala'in Hajia da yan korarta dole suka kama kansu domin Yan uwan Momy da ƙawayenta wannan karon basu zo da wasa ba. Yanda Hajiyar ta saba musu idan ana biki ba yarta ba amma komai yana hannu ta se abinda tace se yanda ta tsara za'ayi wannan karon basu bari ba. Basu saurari Alhajin ba kansa Ahmad da Sarki sun share mata hawayen komai domin duk halinsa shima wannan karon Ahmad ya shawo kansa sun fitarda mahaifiyarsu kunya ba tareda sunyi jiran kowa ba. Anyi biki lafiya Amare sun tare Hafsatu an tafi Abuja Aslamiyyah na nan Kano se Amaryar Yakubu shima da Allah yayi bana yayi auran tsalle tsalle ya ƙare dukda seda Alhajin yayi masa barazana da ze saukeshi daga Acting Account General dan har yanzu ba'ayi confirming nasa ba kafin ya kawo matar akayi Bikin. Afeeyah kuwa Rikicewa ta ringayi harta fara zaton WhatsApp ɗinta ya samu matsala saboda status ɗin Ahmad da Jay da suka zama iri ɗaya tunda aka fara bikin har aka gama seta yi tunanin repeating sukeyi taga kamar ana Jay dan komai ma gizon sunansa yake mata yanzu. Ko kusa bata kawo cewar Jay ze iya haɗa wata alaƙa da Ahamd ba shiyasa ma bata tsawaita tunani ko bincike ba ganin kuma komai ya koma normal shikenan ta manta. Ada bata fiya wani duba status ba amma haɗuwarta da Jay kusan kullum seta duba update ɗinsa wanda duk akanta yakeyi. Yace mata yaso yazo Nigeria abinda ya hanashi zuwa contract ɗinsa da Arsenal taje ƙarshe, Clubs da yawa suna zawarcinsa har yanzu kuma beyi finalizing inda ze koma ba yana so se yayi sealing deal ɗin kafin yaje wani guri. Ya tura maata da sabon Field name ɗinsa, a maimakon JAY its going to be AJAY. Yace A for AFEEYAH and JAY remain for the JAFAR bata yarda da gaske yake ba har se ranar da yayi sealing deal da PSG sabuwar rigarsa da AJAY aka bugata. Ta ringa murmushi kamar wawiya sanda take kallon Interview ɗinsa, an tambayeshi me yasa ya canza suna kuma me A take nufi yace it remains secret lokacin da ze bayyana yana zuwa. Tana jin Yah Malam ɗinsu da Abokinsa Sani da tsabar yanda yake son Jay sunansa ya koma Jay ranar sunata magana. Ance Initial ɗin budurwarsa ne, wasu sunce Initial ɗin Yayansa ne da yake bala'in so kowa dai da abinda yake faɗi. Kamar taje ta gaya musu gaskiya se kuma ta kama bakinta. Anty Sauda tayiwa Umma zancen itama bata bada goyon baya na cewa ma tayi karsu bari Baffa yaji dan ranta ne ze ɓaci. Ya za'ayi tsayin lokacin nan ta dawo tace wani daban ba Ahmad ba itama tasan wasa takeyi. A ranta ko babu gudu babu ja da baya tasan kuma Baffa baze taɓa bin ta tasu ba ya aura mata abinda bata so. Ai da bakinta bata taɓa cewa wani tana son Ahmad ba ko zata aureshi su suke kiɗansu suna rawarsu dan haka babu wata hujja da za'a kafa da zata rabata da wanda take so, badai yace ya kusa zuwa Nigeria ba yana zuwa zata kaishi gidan ayita ta ƙare da haka suka cinye hutun session daya ritsa da Strike kusan watansu uku a gidan kafin suka koma School First semester Four hundred level. *Assalamu alaikum* *Ina matan suke, Manyan mata yan kwalisa da suka amsa sunansu na Mata ba muna mata ba Kawayen Binta gumama?* *SODAH GENERAL ENTERPRISES ce tazo da kanta ba aike ba tana kuma shaida mutu da cewar zafafan kaya sun sauka, kamar yanda kuka sani tana kawo muku suturu na sakawa kama daga kan Atamfa, Laces da dangoginsu* *Wannan karon ta sake taho muku da tsarabar Supplements ingantattu wato Original bawai copy ba. Ku sani bayan abinci jiki yana da buqatar qarin wasu sinadarai da zasu taimakawa ginuwar jikin da lafiyar kowanne bangare na jikin, SODAH ENTERPRISES tana da General Supplements ma'ana wanda suke tattare da Vitamins da dukkan jiki yake buqata sannan tana da special supplements wanda HQ wato gidan mutunchi yake buqata domin sake tsare qima.* *Ina wadda take fama da skin nata yaqi dadin azanci? Fata ta bushe tayi dabbara dabbara ta shafa mai duk a banza se qara lalacewa tayi? To maza ki leqa gurin SODAH ENTERPRISES domin tana da sabulu me kyau da inganci me gyara fata tayi kyau ta goge tayi sulbi baya saka Fari asalin kalarki ze sake fiddo miki ya kuna goge duk wasu tabo ko rashes da suke hanaki walwala, sabulunta babu chemical ba kuma na bleaching bane yawwa karki tsammaci da zakiyi haske Aa sedai glowing kalarki ta ainihi ze fitarda.* *A tuntubeta kai tsaye akan 08137145294* *Ko ki danna wannan link kai tsaye domin magana da ita* https://wa.link/wwvjr3 *Location Kano, tana Nation wide delivery* *MATAR MUTUM* *NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER* *FIKRA WRITERS ASSOCIATION* *LITTAFIN KUDI NE* *PAY 500 A ASUSUN* *7061838488* *OPAY DIGITAL SERVICES* *MARYAM FAROUK* OR *0709290797* *ACCESS BANK* *SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488* *IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705* *Kuyi following dina a Arewabooks @Maryamfarouk01 inda zaku karanta wannan littafin tareda sauran littattafaina* *NAGODE* *BOOK 2* *PAGE 16* Rayuwa ta shuɗa, soyayyar Afeeyah da Jay tana ƙara ƙarfi inda al'amarinta tsakaninta da Ahmad yake sake taɓaɓarewa. Zywa yanzu ya gama tabbatarwa Fatima bata ta tashi da gaske wani ya masa shigar sauri kuma ya sure Imaninta. Ya sake tsananta Addu'a akan Al'amarin amma mainakon rangwame se sake jinta yakeyi a zuciyarsa kamar ture. Damuwar da yake ciki da ayyuka da suka masa yawa yasa duk ya sake figewa ya fita a hayyacinsa. Kowa a gidan yaro da babba ya shaida Ahmad yana da damuwa hatta Hajiya kuwa seda ranar ta tsare shi tace "Kai Amadu anya magauta basu danneka ba? Wannan uwar rama haka kamar wanda ake ɗiba ayi miya kullum? Koda yake jarabar neman kuɗi daka saka a ranka ai dole kaƙi abin kirki, ni na rasa ma me kake nema ko kuwa so kake se ka yi gasa da ƙaninka ne? Shidai kasan yan guje guje kawai zeyi a fili ya dirim Miliyoyi sun shiga akawun, shiyasa yake mulla ƙibarsa kai kuwa kana ta fama da dogon wuya kamar tsohon raƙumi takwaran ubanka". A Ƙofar ɗakinta take maganar ga Hajiya bata rage Volume dan haka hatta Momy dake cikin falonta suna magana da Baba Bilki sun jiyota. Baba Bilki ta girgiza kai tace "Yau rashin mutunchin Binta ya motsa kenan, daɗina da ita bata bar kowa ba, kinji Mijinku ne takwaran tsohon raƙumi. Amma fa maganar gaskiya ki matsa Babana ya gaya miki me yake damunsa da gaske wannan ramar tasa tayi yawa, ni dana tambayesa yace wai aiki ne amma kuma wane aiki ne haka damuwarsa zata nuna har a fuskar mutum? Amadi da ko yaushe fuskarsa take a washe ga barkwanci amma yanzu se a wuni baka ga murmushinsa ba gaskiya ya kamata kiji damuwar yaron nan idan kuma naje Bechi daman zan karɓo masa taimako dan dole mahassada suyi masa caaa irin wannan buɗi da ubangiji yayi masa kiga komai yaro ya taɓa se ya zama kuɗi". Tana rufe baki ya shiga falon da sallama ƙasa ƙasa, suka bishi da kallo harya zauna kusada ƙafafun Momyn. Murmushin yaƙe yayi ganin yanda suka zuba masa ido yace "Lafiya dai Innata da Momy kuke kallona haka kamar kunga baƙo?" Inna yake kiran Baba Bilkin Jafar ma ya kama saɓanin sauran da Manyan suce mata Hajiya ragowar Baba. "Ai dole mu kalleka Ahmad, kana duban kanka a Mirror kuwa? Wannan ƙasumbar da gashin daka tara a kanka na magani da menene?" Momy ta tambaya tana dafa kan nasa. Ya shafa gashin shima yace "Lokaci ne ban samu naje aski ba amma yanzu idan na fita zanyi" "Gara dai kayi ko ka koma hayyacinka amma fuska gashi biya biya kuma ba'a kintse ba ai babu kyau" Baba Bilki data miƙe ta sake faɗa yayi murmushi yana tambayarta fita zatayi tace masa Bechi zata tafi kwana biyu bataje ba sati zatayi kafin ta dawo. "Da bana komai ai da na kaiki" "Aa yi zamanka, tare zamu tafi da Yaya Yakubu ai can gidan nasa ma zan tafi yanzu" "Toh Allah ya kiyaye hanya ki gaidasu" sukayi mata bankwana. Bayan fitarta Momy ta fuskance shi dakyau tace "Karka boyemun komai ka faɗamun gaskiyar abinda yake damunka Ahmad". Ya nisa kamar bazeyi magana ba se kuma yace "Momy Fatima ce na kasa gane kanta" "Matsala kuka samu?" Ta tambayeshi tana nazartarsa. Ya karkace kamar zeyi mata kuka yace "Ni dai babu abinda nayi mata Momy itace dai bansan ko na mata wani abu ba. Gaba ɗaya ta canza duk na kasa gane kanta". "Ahmad kama Addu'a kuwa akan lamarin yarinyar nan?" Ta tambayeshi, yaja rantsuwa yace "Wlh ina yi Momy, ko jiya kwana nayi ina sallah ina addu'ar neman zaɓin Allah amma wlh kamar an ƙaramun sonta a maimakon ya ragu a zuciyata" "Kuma ba addu'ar son rai kakeyi ba? Kana cewa kana neman zaɓin Allah amma kuma ranka ba haka bane ka rigada ka zaɓarwa kanka abinda kake so?" Momy ta sake faɗa tana dubansa yace "Momy shekara uku fa kenan, na san ba nacina ko dagiyata ce zata bani abinda nale so ba amma kuma Allah na barwa zaɓina ina ganin da inada wani haske daban bayan ita da yanzu na ganshi amma Momy ita ɗin dai ita na gani nake kuma ji a jikina itace matata". "Toh addu'ar dai ita zamu cigaba dayi akan koma menene Allah ya warware sannan damuwar daka saka a ranka ba zata amfana maka komai ba kayi Ƙoƙari ka cireta, duk abinda Allahya saka cewar rabon bawa ne a duniya seya same shi idan kuma ba rabonka bane duk wuya haka zaka haƙura domin ba zaka sameshi ba. Sannan kuma ni ina ganin cewar harda halinka yasa yarinyar nan take maka koma menene" Ya zabura yace "Halina kuma Momy? Me nakeyi?" Momy tace "Shekara uku kace da bakinka yanzu, wace irin soyayya ce haka har yanzu da za'ace ba za'ayi aure ba? Kaida bakinka kace mun mahaifinta yace maka ko tana cikin makaranta idan ka shirya aurar da ita zeyi to me kake jira har yanzu? Kana tsammanin zata cigaba da zaunawa tana ɓata lokaci dakai ne Alhalin ƙila tana da wasu masoyan da suka fika himma?" Yayi shiru dan besan bayanin da zeyiwa Momy ta fahimta ba. Baya so ya ɓata Fatima a idonta ta hanyar sanar mata cewar itace har yanzu batayi na'am dashi ba kuma ita taƙi bashi damar ya tura ayi maganar auransu idan kuma yayi shiru Momy zata cigaba da bashi laifi na cewa shi yake ɓatawa Fatiman lokaci wannan yasa ta karkata hankalinta ga wani daya fishi himma kamar yanda tace. "To ai Momy yanzu tana Level 4 har sun gama First semester da bari nayi tunda son zo ƙarshe kawai ta ƙarasa daganan se aje ayi magana" "Oh so kakeyi harta gama makarantar tazo ta zauna sa'annan ka gama shiriritarka se aje ayi maganar aure ko? Lallai kuwa kana zaune nan zakaji wani ya aureta. Waima sanyar me kakeyi ne? Ina kace tun tuni ka sanar da Alhaji maganar nan me kake jira da ba zaka sake tayar masa da ita ba tunda ka nace lallai se shi zaka kaiwa maganar auranka?" "Aa Momy ba haka bane ba, naga ai Alhaji ne Ahaƙƙu da na sanarwa da zancen aurena idan yaso shi kuma ya iya saka wakili ya shige mun gaba" ya bata amsa kai a ƙasa. Momy ta harareshi tace "Sannu uban fitar da Ƙoƙon Asali, dama dai yanda kake da ƙulafucin uban nan shima haka yake ta taka amma na tabbata yanzu ya manta ma da kunyi wata magana data shafi zancen auranka dashi. Se kaje ka sake samunsa ai ka tuna masa, idan kuma yace Aa kaga aiseka fara sabon lissafi tunda ga tudun dafawar da duk yanda aka ciza ze tsaya maka kace baka san zance ba ba zakaje ta wurinsa ba". "Ni Momy bana so a sakeyin irinta Yaya Sarki kina kallo dai Alhaji swda yayi ta faɗa akan ya zameshi daga maganar auransa shiyasa amma ba wani abu ba kuma nasan ai dai ko shi na gayawa dole dai Baba Alƙalin ze wakilta" ya sake faɗa Momy tace "Ai shikenan, amma dai mafita guda ce in har da gaske kake son yarinyar nan manya su shiga maganarku, kaje ka samu ubanka ka fayyace masa komai ya tura a nema maka auranta in kuma zaka zauna nuƙu nuƙun ne kuma shikenan" "Toh Momy zanje" daga nan suka bar maganar suka shiga wata. Bayan fitarsa ya ringa shiryawa yana warware ta yanda ze sake tunkarar Alhaji da zancen aurensa da Fatima. Amma ta yaya ma ze taso magana alhalin ita wadda za'a aura ɗin bata yarje masa ba? Ya samu jikin katanga ya lafe ya shiga kiran layinta, yanzu abin ya sake ta'azzara har rejecting take in bata ga damar amsawa ba kuma ya dameta, So hana ganin laifi haka yake jurewa domin ya yarda ƙaddarar sa ce Son Fatima. A kira na biyu ta amsa muryarta ta shaida masa bacci takeyi dan haka yace "Kiyi haƙuri na tasheki a bacci" "Babu komai ina zaune ne nima ban san baccin ya kwasheni ba, ina wuni?" Ta gaidashi. Tana da kirki, tana da tarbiyya, Mahaifanta mutane ne kai tana da duk wani quality da yake nema a gurin matar auransa baya zaton idan ya barta ze damu full option abinda yake nema a gurin mace tamkar nata ya ayyana a ransa. "Kina free yau da dare zanzo?" "Eh" ta bashi amsa a taƙaice, shikenan ya mata sallama akan se bayan Magriba zeje haka kuwa akayi yaje yayi aski ya ɗan shiga saiti ana sallar Magriba ya sha kwalliya ya tafi gidansu. A can yayi sallar Isha a masallacinsu Baffa kafin suka ƙarasa gidan tare. A ƙofar gida Baffa ya dubeshi yace "Malam Ahmad na bawa Mamana Saƙo kusan sati nawa amma banji amsa ba". Da rashin fahimta ya dubi Baffan kafin cikin girmamawa yace "Ina ganin ta sha'afa ne Baffa ko kuma nine na manta da ta gayamun amma wace magana ce?" Baffa yayi murmushi yace "Dama maganar zuwan magabatanka ne nace lokaci yayi daya kamata ace manya sun shiga cikin maganar nan, ni badan ka buye ta tata ba kace a barta ta gama karatun kamar yanda take so ai da tuni kuma ka huta da biyo dare kana maƙalewa jikin katanga" Baffa yayi masa barkwanci. Yayi yar dariya yana sosa Ƙeya, Baffa ya sake cewa "To ina sake maimaita maka tunda da alama ta sha'afa kamar yanda kace, a sanar musu saboda a san abinda ake ciki" "In sha Allahu Baffa zan sanar musu" ya faɗa kai a ƙasa, Baffa ya wuce ciki yana masa Addu'a da fatan Alkhairi. Shiya turo masa Fatima wadda ta manta da batun zuwan Ahmad ɗinma seda Baffa yace mata yana waje. Dogon Hijab ta saka, bata shafa ko hoda ba ta fito tana bulbula ƙamshin designer perfumes ɗin da yake kai mata akai akai. Ta gaishe shi ya ringa kallonta kullum ya ganta ƙara sonta yakeyi, jinta yakeyi har tsakiyar ransa shi be taɓa sanin haka So yake ba seda ya afkawa kogin ƙaunar Fatima. "Yanzu Baffa yake cemun ya baki saƙo amma baki gaya mun ba" ya faɗa yana kallonta. Ta juya ido abinda ya sake kashe shi kafin tace "Wane saƙo kenan?" "Ya wuce ai tunda ya faɗa mun da kansa. Magana ce akan turo magabata na ayi maganar auranmu, na so na gaya masa har yanzu bamu samu fahimtar juna nida ke ba amma kuma na kasa". Ta ringa kallonsa babu ƙyaftawa harya kai aya kafin ta sauke kanta jikinta nayin sanyi kamar wadda rana ta daka, Ahmad ya harɗe hannu a ƙirji yana kallo ta ya sake cewa "Baffa da kansa ya mun magana na turo neman auranki, kar kisa ya ɗaukeni a mutumin banza idan na gaza cika umarninsa. Fatima me kike da buƙata? Ki gaya mun dan Allah me nene dalilin daya saka ba zaki bani dama na shiga rayuwarki ba?" A maimakon tayi masa magana kawai se gani yayi hawaye ya fara mata tsere dan da hasken Nepa tar a ƙofar gidan, ya buɗe baki yana kallonta da mamaki kafin yayi magana ta juya da sauri ta shige gida tana cigaba da kukan. Yayi kasaƙe a gurin, shi ba abin ya bita ciki ba mamakin dalilin kukanta ya rufeshi. Yana tsaye Baffa ya fito be ankate ba seda ya kira sunansa. "Malam Ahmad lafiya kuwa naga ta shiga gida tana kuka ko wani abu ne ya faru?" Baffan ya tambayeshi. To shi me zece masa yanzu? Gaskiya ze faɗa masa ko kuwa yayi shiru Baffan ya zargi wani abun yayiwa yarsa? "Wlh Baffa babu abinda ya faru, tambayarta kawai nayi ta amince na turo iyayena shine ta fara kuka ko magana batayi bama ta wuce ciki" ya faɗa cikin rawar murya. Baffa yayi ajiyar zuciya yace "Kayi tafiyarka kayi abinda nace maka in har da gaske kake son aurenta ka turo magabatanka" "Nagode Baffa in sha Allahu zaka jini bada daɗewa ba" daga nan yayiwa Baffa Sallama ya wuce, farin cikin daya samu dalilin ganinta ya gushe, har wani ciwon kai yaji yana neman kamashi kukan Fatima ya tabbatar masa da gaske bata sonsa tilas ya haƙura da wannan yarinyar muddin ba rabuwa da ita ne Ajalinta ba. A can gidansu Fatima kuwa bayan Baffa ya koma ciki tarar da ita yayi tana sharɓar kuka Umma na tsaye kanta tana faɗa kamar zata rufeta da duka. "Ya isa Zara'u rabu da ita" Baffa ya faɗawa Umman, ta zauna tana tsaki, ji take kamar ta rufe Afeeyar da duka ko zata maidata cikin hayyacinta. "Duk menene dalilin wannan abun? Me ya sakaki kuka daga yace ze turo magabatansa dama bakya sonsa ne ko kuwa ra'ayi kika canza?" Baffa ya tambayeta. Bata amsashi ba se kuka da takeyi ƙasa ƙasa. Umma ta jefeta da takalmi tana cewa "Ba magana ake miki ba kinaji kinyi shiru?" "Nace ki barta Zara'u ko?" Baffa ya faɗa a ɗan fusace. Umma tayi ƙwafa ta wuce ɗakinta. Baffa ya sake duban Afeeyah, yanda taji muryarsa ta tabbata ransa a ɓace yake ta san kuma fushi ba ɗabi'arsa bace tabbas ta kaishi bango ne dan haka yana sake maimaita mata tambayar jiki na rawa taja baya daga kusa dashi kafin tace "Ni daman Baffa ban taɓa cewa ina sonsa ba kawai bazan iya wulaƙantashi bane amma duk wata alama da ya kamata na nuna masa nayi amma yaƙi ya haƙura". Baffa ya ringa kallonta har tayi shiru, yafi minti goma kafin ya iya cewa "Kina nufin tsayin shekara uku da yaron nan yake bibiyarki yana wahalta miki duk ya tashi a banza yanzu zakice ba sonsa kikeyi ba?" "Wlh Baffa ni ban taɓa cewa yayi mun abu ba, kuma ai ko kai kana hanashi amma se ya dage se yayi kuma ni ina gaya masa ya dena kawai shine baya ji" Umma ta leƙo a fusace tace "Dan ubanko dole yanzu kice bakya sonsa mana kuma bake kika saka ya ringa miki wahala ba, Kare ne shi da ze shekara uku saboda rashin zuciya yana tare dake kina nuna masa rashin So kuma yaci gaba da zama dake? Kin gama yaudarar sa kin ɓata masa lokaci saboda baki da mutunchi yanzu zakice bakya Son sa me yasa tun farko baki faɗawa Malam ɗin ba shi da kansa ya kirashi ya sallame shi se yanzu da koɗaɗɗiyar fuskarki zakicewa mutane ke daman bakya son sa to wlh baki isa ba" Umma ta shiga sababi harta manta darene ta muryarta a sama. Baffa daya kasa magana tuntuni ya kalli Fatima yace ta wuce ɗaki, sum sum ta shige tana jin kamar an sauke mata wani nauyi daga kanta tunda har ta iya furtawa Baffa bata ra'ayin Ahmad tasan magana ta ƙare. A ɗaki Umma ta warwarewa Baffa komai game da zancen Yaron da Afeeyah take so wato Jay ɗan Ƙwallo. "A ina suka haɗu?" Ya tambayi Umman, ta watsa hannu kafin tace "Wai acan makarantarsu, Malam ka sanarwa Yaron nan kawai ya turo Iyayensa suzo a ɗaura musu aure kawai idan yaso ta mutu ƙarshen rashin Son Sa". "Ba za'ayi haka ba, za'a bi komai a hankali, magita zata samu da yardar Allah" inji Baffa. Daren raba shi yayi yana sallah da addu'oi, ya kasance me yawan tsayuwar dare amma yau Umma tasan sallar tasa harda ta neman ɗauki gurin Allah kan wannan abin daya tunkaro shi. Baffa na Son Afeeyah, amma abu ɗaya da tayi imani dashi shine baze bi Son rai ya zubar da ƙimar sa ba shiyasa ya maida lamarin ga buwayin sarki gagara Misali wanda duk hukuncin daya yanke babu wanda ya isa yayi inkari akai. Kwanaki uku Baffa ya jera yana Istikara cikin tareda tsananta Addu'a da roƙon ubangiji akan Al'amarin, Afeeyah kuwa rai fes dan Ahmad be sake kiranta ba tunda ya tafi kuma ta furta abinda yake ranta dan tasan Umma ta gayawa Baffa zancen Jay babban abinda ya sakat nishaɗi da farin ciki kuma shaida mata da Jay yayi yana tafe Nigeria nan da sati biyu masu zuwa. Saura kwana biyar su koma makaranta semester ƙarshe ce babu Lectures da yawa se aikin project da abinda baza'a rasa ba dan haka ta yanke ba zata koma bahar se yazo tukunna abinda bata taɓayi ba ƙarin hutu tunda ta fara University. Ta gayawa Badar Jay yana tafe, Badar nason Jay da Afeeyah amma ba kamar yanda take sonta da Ahmad ba kamar yanda take ce mata Ahmad Mijin Aurene Jay kuma na rage lokaci da neman suna domin ita dai bataji a jikinta Jay auran Afeeyah zeyi har yanzu ba duk kuwa da tarin ƙaunar da yake nuna mata akan haka har faɗa suka sakeyi ta dai rabu da ita tana kuma yi mata addu'a a matsayinta na ƙawarta. Takanas taje gidan Anty Sauda tace mata nan zata fara kawo Jay kafin Umma ta sauka daga fushin da takeyi da ita tukunna se ta kaishi gidan. "Yanzu kina ganin abinda kika zaɓawa kanki daidai ne Afeeyah?" Anty Sauda wadda Umma ta gaya mata duk abinda ya faru ta tambayeta. "Haba Anty dan Allah wai ana aure dole ne? Naga kema zaɓi aka baki kika kawo wanda kike so me yasa ni ake nema a tauye mun haƙƙi?" Ta jefawa Anty Saudan tambaya. Seta girgiza kai kawai tace mata Allah ya kawo Jafar ɗin lafiya, bata wani jima ba ta koma gida dukda zaman gidan ba wani daɗi yake mata ba yanzu saboda yanda Umma ta canza mata. Daga ita har Baffa babu wanda ya mata zancen ganinbata koma makaranta bama se Yah Malam daya zo hutu ne yace ya ya ganta a gida tace se wani satin zata koma. Baffabe canza mata kamar Umma ba dan ze amsa gaisuwarta har ya sakata aikace aikace kamar yanda ya saba amma Umma ko gaiseta tayi da harara take amsa mata tti duk yanda zatayi Umman ta sakko amma abu yaci tura tasan dai fushin Umma akan Ahmad ne addu'a takeyi Allahya kawo Jafar wanda yace zuwa ɗaya zeyi kafin yayi na biyu za'a tambaya masa auranta dan ya matsu. "Yah Ahmad ka dena sona wlh, yanzu ace zanzo gida amma babu wani murna ko ɗokin gani na daka sabayi kawai Allah ya kaimu shikenan abinda zaka ce?" Jafar ya dasawa Ahmad mita akan beyi murna daya ce masa zezo gida ba. Ahmad daya kwanta zazzaɓin malaria kamar yanda yayiwa Momy ƙarya amma gaskiyar abinda yake damunsa Love sickness ne. Tun ranar daya baro gidansu Fatiman damuwa ta saukar masa da ciwon kai da zazzaɓi me zafi amma haka yake bankar Anti Malaria da Momy tasa dole yaje asibiti aka rubuto masa. "I told you bani da lafiya Jafar amma kana ta so se ka sakani magana" "Ni ai bazanyi maka sannu ba saboda wannan ciwon kai ka ɗorawa kanka, let me ask you please, is this Fatima made of Gold or some sort of precious stone da tayi deserving wannan soyayyar da kakeyi mata? Yah Ahmad me yake damunka? For heaven sake kana nema ka kashe kanka akan wata banzar mace? Is she the only living woman on earth? Ko dai asiri tayi maka? Oh na manta mayyace believe me ta cinye maka zuciya kuma wlh bata isa ba. Ko waye ubanta she must leave you, seta fita a rayuwanka let me come back first I'm going to deal with her personally, se ta gane bata da hankali wlh" ya ringa sababi kamar ze aro baki daman kuskure Ahmad yayi daya taso masa da maganar gashi yana neman ya sake ƙara masa ciwo. "I love her, kuma banajin zan iya dena sonta idan da abinda zakayi kasa ta soni i will appreciate it more zaginta da kakeyi dan baka san abinda nake ji bane ba nidai idan kana sona da gaske just help me fight na samu Fatima" Ahmad ya faɗa. Jafar yayi shiruj irin wanda takaici ya gama tiƙewa kafin yace "Indai haka ne ze sa ka yarda Ina sonka then I don't love you Yah Ahmad and i will never love you indai se naso wannan yarinyar ne ka cireni a jerin ƙannenka, i hate her, i hate her with all my life kuma ko Allah yasa ka aureta bazan taɓa shiga gidanka ba" yana gama magana ya kashe wayansa yanda Ahmad ya jishi yasan ba ƙaramin zafi ya ɗauka ba. Yayi murmushi, yasan rigimar Jafar na lokaci ne zuwa anjima ze sake kiransa kawai dai wannan ƙiyayyar da yakeyi mata me zafi ce ya rasa dalilinta, saboda shine kuma yanzu so yakeyi ya haƙura da ita ba shikenan ba. **************** "Alhaji, ni tun kwanaki naji kana zancen Amadu ya samu mata ko? Ashe ma ya taɓa kaiwa Ummu ita, se jiya da muke magana Jafaru yace daya zo za'aje masa neman aure shine tace mun zancen ai taga budurwar Amadun ma ya ɗaukota daga makaranta suka biya gidanta wai ya karɓowa Aisha Leshi, wai a Zaria take makaranta, nace Yayan masu kuɗi suna zuwa wannan makarantar kuwa?" Alhaji Audu na kurɓar baƙin shayi daya sha spices, Girkin Hajiya Rabi ne ita ta dafa masa tana kawowa Hajiya Bintan tazo ta kankane gurin dole ta fita ta bata guri dan har ta fara sakar mata maganganu tana ci mata zarafi shi kuma Gwankin na zaune shirim bece komai ba. Ya gama sauraron Hajiyar kafin yace "Oh ya samu mata kenan da yake ke zaki nemo masa auran shiyasa ya fara sanar dake?" "Shi wa? Ummu nace maka ni a suwa Amadu ze faɗamun ya samu Matar Aure Aisha ce ni kowa?" Ta faɗa tana wani taɓe baki. Alhaji ya sake zuba shayinsa yana sha yace "Shi Ɗan naki nake magana" "Wai Jafaru? Dama idan be gaya mun ba toh wa kake so yaje ya fara sanarwa ko yana da wata uwar ne bayan ni a duniya?" "Aa bance ba, shi Ahmad ɗin dake ya ɗaukeni uba ai tun fara neman yarinyar da yakeyi ya sanar dani, kawai inda ya nemo auran ne be gama kwanta mun a rai ba shiyasa ma kika ga an kawo yanzu maganar bata tashi ba amma yafi shekara da sanar dani". Har wani zullo tayi kamar zata kwanta a gabansa tace "Ashe maganar ta daɗe? Daman Ummu tace anfi wata shida da zuwan nasu tun kafin lokacin bikin su Hafsatu to ashema ka sani toh naji kace gidan daya nemo auran ne beyi maka ba, da akwai matsala kenan?" Da zuciya ɗaya yace mata "Yar wani Bakanike ce yarinyar Malam Hafizu akace sunansa a Alfindiki yake, a binciken da na saka akayimun dai Mahaifin yarinyar nace bashi da matsala mutumin kirki ne toh amma ita yarinyarce surutu yayi yawa akan yanda Samari suke zuwa gurinta wannan yazo wannan ya tafi gashi a matsayin mahaifinta irin rayuwar da akace tanayi ta wadata ya zarce ace shi yakeyi mata, kinsan yaran yanzu, zakiga Iyaye suna iyakacin ƙoƙarinsu gurin tarbiyya amma idan sun fita se abinda hali yayi musamman masu tafiya karatu wasu garuruwan ba gaban Iyayen nasu ba to wannan yasa na dakata kuma shima Ahmad ɗin tun maganar farko da mukayi be sake tayar mun da zancen ba dukda dai ina da labarin suna tare haryanzu kuma ita kaɗai yake kulawa ta yuwu yana jira ta kammala makaranta ne tunda ance shekarar ƙarshe take". Tamkar me ɗaukar karatu haka Hajiya ta naba'a tana sauraron Alhaji se gyaɗa kai takeyi har ya kai aya kafin cikin Jimami tace "Ikon Allah, shi kuma Amadu inda ya tafi kenan? Nida nake ta sauraro naji ya samo yar gidan Ɗangwate ko BUA tunda suke abokanan goga kafaɗarka a ƙasar nan seya ɓige da yar gidan Bakanike? Toh Allah ya rufa asiri, ita dai ta Jafaru ance Balarabiya ce dan ya turawa da Munirah hotonta wai irin wanda ake kalla sau ɗaya ne shiyasa bata kwafa ba ta ajiye mana. Todai daya zo koma ya ake ciki zamuji, seka fara shirya wa'inda zasu nemo masa auran inajin dai baze wuce a Saudi Arebia ba ko Dubai" Alhaji yace mata "Toh, Allah ya kawo shi lafiya" "Toh amma Alhaji ina da wata magana idan babu damuwa kuma ka bani dama in faɗa" yanda tayi maganar yasa ya tattara hankalinsa akanta dan yaji me zatace. Hajiya ta gyara zama kamar gaske kai a ƙasa tace "Dama Alhaji akan mu'amalarka da yaran gidan nan ne naga ya kamata a gyara wasu abubuwan, ina nufin su Alhaji Babangida da sauran yaran da basa cikin gidan nan. Bana jin daɗin yanda kowa idan ya tashi yake ɗora mun laifi a ringa cewa ni ce na rabaka da yayanka. Kaga girma ya cin maka, ya kamata ace zuwa yanzu ka fara sakin wasu abubuwan ka bari Manyan yayanka suyi maka". Alhaji yayi tagumi yana kallon Hajiya Binta data sake gyara zama tana cewa "Ba harkar kasuwancinka nake nufi ba, wannan ai kana da magada daka rigada ka koya musu komai kuma suka goge akai ina nufin kamar harkokin aure, kaga daga kai har Yakubu kun manyanta ya kamata ku zauna ku huta ku fara sakarwa Yayanku suna jan ragamar abubuwa". "Wato ba zaki ringa karanta sunan Yakubu ba, Idan beci darajar girmata da yayi kin kirasa da Yaya ba ai kya bashi sunan da kowa yake kiransa dashi Alƙali" Alhajin ya tareta. Ta lanƙwashe kamar yarinya tace "Allah baka haƙuri saboda faɗa ne uffararan Baba Alƙali nake so nace, to da kai dashi duk ku huta ka kirawo Yayanka gaba ɗaya ka zaunar dasu kuyi maganar nan, ka ware wanda zasu ringa zuwa tambayowa Maza aure da kuma wanda zasu ringa karɓan na mata idan an zo. Amma kafin nan ya kamata duk wani abu daya taso ka ringa tarasu kana shawara dasu, ta hakane zaka jasu a jiki suma su sake dakai a hankali se kaga duk sun dawo gida a dena zagina a gari ana cewa na raba yaya da ubansu". Alhaji ya sakeyin shiru yana nazarin maganarta, Alƙali Yakubu ya taɓa yi masa makamanciyar magana irin wannan, yace ya kamata ace ya ringa janyo Yaransa a jiki domin ya gyara kuskurensa na baya. Rayuwarsa ta fara zuwa gangara, be kamatu ace ya mutu ya bar kan iyalansa a rarrabe kamar yanda suke a yanzu ba. Maganar Bintan se ta sakashi Nazari, tabbas abinda ta faɗa gaskiya ne domin Abokanansa masu Manyan Yaya kamar nasa da yawa yanzu a kwance suke suna hutawa komai da masuyi musu, ze gwada shawarar tata koda akan zuwa batun Neman aure ne da karɓar ze saka su yasan babu wanda zece bazeyi ba a cikinsu. "Kamar yanzu da zancen auran Ahmad dana Jafarun nan musamman na Ahmad da kake da kokwanto akan yarda ko akasin haka, ka tarasu, ka nemi shawararsu kaga zasuji daɗi suga ka mutuntasu kuma su sun fika sanin kan duniya yanzu se kaga an samu maslaha ai ko?" Ta sake faɗa. Alhaji ya jijjiga kai da alamar gamsuwa, tayi murmushin cin nasara sannan tace "Toh amma fa karka gayawa matanka ko Yan uwanka shawarata ce dan ka san cewa za'ayi da wata manufa nayi ni kuma Allah yaga zuciyata babu komai face Alkhairi so nakeyi ka shirya da yayanka ka haɗa kan zuri'arka", bata tashi daga gurin ba seda ta gamsar da Alhaji Alfanun abinda tace yayin ya kuma yarda da hakan. Babu ɓata lokaci a daren ya kira Alhaji Babangida, umarni ya bashi akan ya haɗo masa kan Yan uwansa daga Babannan zuwa Mu'allim, banda Matan da kuma Zayyad da Abdallah da basu isa ayi wannan shawarar dasu ba. Alhaji Babangida ya shiga mamakin ko lafiya wannan kira haka da Alhaji yayi musu amma babu damar tambaya. A washe gari ya sanarwa da waɗanda yake da numbers ɗinsu a waya ta hanyar Text message yace su sanar da sauran. Ya sake kiran Alhaji domin ya manta be tambayi ranar da yake da buƙatar ganinsu ba. "Ranar Asabar ɗin nan" Alhaji ya bashi amsa. Alhaji Babangida yace Zan sanar dasu ranar, amma naji Jafar yana tafe ranar Talata, ba za'a iya ɗage taron a jirayi zuwan saba?" "Aa, duk abinda aka tattauna idan ya dawo zaku sanar dashi" da haka sukayi sallama. Ya gayawa Alƙali ze zauna da yaransa duka ya kumayi murna da hakan domin an samu cigaba kenan Alhaji Audun ya shiryi samun daidaito tsakaninsa da Iyalansa. *Assalamu alaikum* *Ina matan suke, Manyan mata yan kwalisa da suka amsa sunansu na Mata ba muna mata ba Kawayen Binta gumama?* *MATAR MUTUM* *NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER* *BOOK 2* *PAGE 17* A bisa dole Iyalan Alhaji Audu suka amsa goron gayyatar daya aika musu dashi. Ba kalar mitar da basuyi ba amma haka suka zo domin koda basa ga maciji da mahaifin nasu sun sanshi sarai baya ɗaukar wargi, farillan rashin mutumchi kuwa sala sala yanadasu wanda yake amfani dasu gurin ladabtar da duk wanda yace zeyi masa giggiwa. A cikin su daman wanda yafi kowa taurin kai Alhaji Hussaini ne, da Dr Hassan ya sanar masa da kiran Mahaifin nasu take yace masa "Bazanzo ba, inada abubuwan da suka fi muhimmaci da sauraron kalaman son rai da wannan tsohon ze faɗa mun in kuma ya fara tafiya gargara ne yake so ya bada wasiyya ka karɓa harda tawa ka riƙe na bar maka in ma mutuwa yayi ni wlh na yafe gadonsa tuni". Seda Hajiya Zubaida Mahaifiyarsu tayi masa kaca kaca bayan da Dr Hassan ya sanar mata da abinda yace tace kuma tilas yaje idan kuma ya isa ya tsallake umarninta daman ita kaɗai take maganin Iya shegensa, yana son mahaifiyarsu yana tausaya mata yana kuma riƙe da abinda aka labarta musu cewar Alhaji Audun yayi mata tun kafin haihuwarsu da bayan zuwansu duniya. Ƙwato su da yayi ya maidasu gidan ya zube su a tsakar gida shine abun daya ƙara ta'azzara tsamar dake tsakaninsu. Yanda Hajiya Binta ta ringa yi musu, kalar azabatarwar da tayi musu har gobe yana addu'ar kafin ta mutu in sha Allahu seta ɗanɗani sama da baƙin cikin data shayar dasu. Matan da akace banda su dalilin irin wannan taro da ba'a taɓa yin irinsa ba suka san lallai da akwai wani babban Al'amari a ƙasa wannan tasa kowacce ta wanko ƙafarta ta taho ranar taron. Momy da Hajiya Rabi basu san wainar da ake toyawa ba har s ana i gobe taron da suka tsinkayi muryar Hajiya Binta na bada umarnin abinda za'a girka gobe da yawan wanda za'ayi. Lokacin Salim na falon Momyn yana cin abinci yayi tsaki yace "Wai me matar nan take shiryawa ne? Dan dai Alhaji bashida wata shawara tasa ta kansa se abinda tace masa" "Wani abu ya faru ne?" Momy ta tambayeshi shine ya faɗa mata kiran da Alhajin yayi musu. Tayi shiru, ita tayi girki jiya yauma itace amma ace Alhajin bega ya kamata ya sanar mata da komai ba ai shikkenan. Bata masa zancen ba har washe gari da Asuba kafin ta baro bangaren nasa taji yana waya da wani abokinsa yana sanar masa baze samu zuwa wani ɗaurin aure ba shine bayan ya gama yake ce mata wai ze gana da Yayansa duka akan maganar aurab Ahmad. Cikin mamaki tace "maganar auran Ahmad kuma? Yaushe zancen ya taso da ni ban sani ba? Sannan naji kace zaka tattauna da Yayanka akan maganar daman haka kakeyi idan auran yayan naka ya tashi ko kuwa wani sabon salo ne ka tsiro dashi da za'a fara akan Ahmad?" "Ya zaki ringa min wasu tambayoyi se kace wani ɗanki? Tsakanin nida ke waye yafi zamarwa dole daya san maganar auran Ahmad ko kuwa ke zakije ki tambayo masa auran?" Alhajin ya faɗa yana wani zare mata ido irin ta zo masa da raini. Zuciyarta ta harzuƙa domin ta tabbatar wata maƙarƙashiyar ce aka shiryota kuma Binta ce idan ba haka ba ita dashi basu taɓa zancen auran Ahmad ba, tabbas Ahmad ya gaya mata iyayen yarinyar sun bashi izinin ya turo magabatansa har yace tayiwa Alhajin magana tace ba zatayi ba ya same shi da kansa bayan nan kuma ya fara rashin lafiya ta tabbatar da ace sunyi magana da Alhajin tilas seya gaya mata yanda sukayi domin a ko ina zata shaideshi baya abu gaban kansa ba tareda yayi shawara da ita ba kuma duk yanda ake ciki seya koma ya gaya mata ta sake bashi haske akan abinda ya kamata yayi. To ace ma Ahmad ya masa magana sun tattauna shiya manta be koma ya gaya mata ba ai shi Alhajin a matsayinta na uwar Ahmad tana da haƙƙin ya sanar mata da zancen auransa ba wai taji a sama yaje ya shawarta da wadda a kullum bata da burin da taga kasawarsu. Ta sani ya fayyacewa Binta inda Ahmad ya nemo aure shine zatayi amfani da hakan dan ta tozarta yarinyar da iyayenta toh kuwa Allah ya fita ba zata taɓa cin galaba ba. "Ai ko riƙon Ahmad nakeyi ba wai ni na haifeshi ba ya kamata a fitar mun da ladan wahalata a sanar mun da zeyi aure, kuma a gidan nan baka taɓa haɗa taro dan wani Ɗa zeyi aure ba akan me za'a farashi akan Ahmad? Saboda shi me biyayya ne duk yanda aka bi dashi zece toh shi yasa kake so ka tauye masa haƙƙi ko yaya?" "Ki fita kuma ƙarfe goma ne taron, umarni ne na baki ba wai shawara ba ki kasance a gurin" ya bata amsa cikin halin ko in kula ba tareda ya bi ta kan maganganunta ba. Hawayen takaici suka zubo mata ta share ta fice daga ɗakin, tana can ƙuryar ɗakinta ta kira Yar uwarta Maimuna ta gaya mata abinda ake ciki. "Kije ki zauna a gurin saura kuma ki zama hoto kiyi shirun da kika saba a zartar da abinda ba haka ba dan nasan munafunci yasa aka shiryi wannan zaman ba wai dan Allah bane" Maimuna ta gaya mata. Tana shirya masa abin kari Hajiya Rabi ta shiga Falonta. Suka gaisa take tambayarta zaman da Alhaji ya kirata a waya yanzu yace mata wai ƙarfe goma. "Nima da Asubar nan ya gaya mun wai akan Ahmad ne, amma ita hamshaƙiyar ai tasan da komai tunda tun jiya naga tana bada umarnin abincin da za'a dafa" Momy ta bata amsa tana murmushin takaici. Hajiya Rabi cikin jimami tace "Ahmad kuma? Nasan dai ba laifi yayi ba koma menene Allah yasa Alkhairi ne, bari naje na shirya toh" daga haka ta wuce tana ta lissafin to wane irin abu kuma Ahmad yayi ko zeyi da har se an masa taron dangi haka? Tun tara Iyalan Alhaji Audu suka fara hallara a gidan. Wasu su kaɗai suka zo wasu tareda yayayensu da matansu dan haka gidan ya cika hayaniyar jikoki kota ina tashi takeyi suna ta guje guje. Ƙarfe goma Mazan suka hallara cikin babban falon da ke bangarensa a ƙasa gaba ɗayansu Jafar ne kawai babu a gurin. Bayan an buɗe taro da Addu'a tareda jawabin maraba daga uban garken, babu ɓata lokaci ya shiga zayyano musu maƙasudin kiransu wannan taro. Shiru falon ya ɗauka banda ƙarar Ac bakajin komai se salallamin da Hajiya Binta takeyi murya a sama tamkar wadda aka aikowa da mutuwar iyayenta dare ɗaya, yanda takeyi seka rantse da Allah yanzu ta fara jin maganar, tamkar bada ita ta tsarawa Alhajin daya tara su ba domin ta ƙaddamar da wani shiri nata. Can kuma ta zabura ta miƙe tsaye idonta akan Ahmad daya sunkuyar da kai ƙasa, abinda yake ji a zuciyarsa baze misaltu ba, wai duk akanme? A ina aka taɓa haka? Shi yaushe ya cewa Alhajin maganar aurensa ta tashi? Auran da yake ƙoƙarin yakicewa ya haƙura da yarinyar shine aka zo ana masa wannan taron dangin akansa? "Amadu ashe baka da hankali ban sani ba? Wayonka da nake gani na banza da wofi ne baka san komai ba se neman kuɗi kamar Ɓarawo?" Hajiya Bintan ta faɗa, Momy ta ɗago a karon farko tun zamanta a falon ta kalleta jin kalmar data jiɓanci gudan jinin nata da ita wai Ɓarawo ita kuwa Hajiya bata dakata ba a fusace taci gaba da cewa "Wallahi tallahi ko sama da ƙasa zata haɗe banga uban daya isa ya ƙulla auran nan ba, yar Bakanike Amadu? Mu zamu haɗa surukuta da Bakanike kuma Sadaka yallah mayu? to idan ita uwarka sallamammiya ce komai aka ce bata musawa ni bazan lamunta ba. Iyakar irin tsiyar da aka ɗakko mana sun isa ba se an haɗo mana da wanda zasu zo suna mana ɗauki ɗaiɗai suna ciyayya ba" Hajiyar ta kai aya tsabar masifa numfashinta har neman sarƙewa yakeyi. Alhaji Audu dake kishingiɗe akan kujera ya nisa yace "Duk wannan a ganina ba wani abun azo ana tayar da jijiyar wuya akai bane, magana ce ta aure kuma shi ma'auri yace yaji ya gani sannan ni da kaina nayi binciken iyayenta kuma ban samu wani abun ƙi da ze saka a hana shi auranta ba, ni kiram da nayi muku na taraku ne dan muyi shawara akan yanda za'abi gurin neman auran, suwa za'a wakilta suje". Momy da Anty Amarya suka kalleshi kamar yanda da yawan yayayensa dake zaune duk suka kalleshin. Harara Hajiya Binta ta maka masa kamar wani ɗanta tace "Lallai Alhaji, ya kake nema ka canza magana koda yake kwanakin nan ka zama me fuska biyu daman" Mamaki kamar ya shaƙesu jin abinda Hajiyar ta faɗa masa, kunne, baki da hanci duk suka zuba suna jiran suga matakin da ze ɗauka amma sukaji muƙus ko tari Alhajin beyi ba sema Hajiya data ci gaba da sababinta tana cewa "Da zakace bakaga wani aibu da ze hanashi auranta ba ai kuwa ita keda babban aibu, Talaka yar talaka jikar talaka kuma Mayya". "Amma Hajiya talauci fa ba fasiƙanci bane, sannan baya cikin sharuɗɗan da suke hana aure. Kuma maita da kike jifanta da ita kin san cewar fa ba ƙaramin abu bane idan sukaji zasu iya yin ƙararki akan hakan tunda baki da wata tartibiyar hujja data tabbatar da abinda kike jifansu dashi" tsautsayi ya saka Hajiya Rabi magana tamkar kuwa Hajiya Binta na jiranta daman tace "Babu shakka Rabi dole kice talauci baya cikin abinda ze hana aure saboda kinji zaki samu ƙarin yar uwa ko Ahalul fuƙara'u za'a ƙara yawaita? Koda yake ma a hakan ita ai ta fiki tunda nata uban ance yana da tsayayyar sa'ar da yake samun abun kaiwa bakin salati ba irin naki tsohon ba da se an bi gidaje anyi yawon maula kafin a tattara a kaiwa Iyali ya isa be isa ba a yayyafa aci shi kansa Alhajin daya kwaso wa kansa ƙaya gashi nan kullum cikin nadama da dana sanin auranki yake, jiya farar safiya gari ko gama haske beyi ba me dattin hula ya buga mana gida wai katangarku ta faɗi, daka fita ka bashi kuɗin ina dawowa kayi kana mitar daka saba duk sanda yazo maka maula irin rayuwar da kake so shima Amadun ka jefa shi a ciki kenan ya ƙare yana nema dangin Sadaka Yalla su dabaibayeshi su cinye sannan subi ɗan naman jikin nasa ma da ba auki ne dashi ba su lashe ni daman kwanakin nan zugewar nan da yakeyi ina ganin har sun fara lasar sane wlh sun zarge kurwa tab" Hajiya Binta ta faɗa tana tsaida idonta akan Alhajin. Baƙin cikin maganganunta suka sanya Anty Amarya barin falon babu shiri saboda kukan daya taso mata, shekaru kusan Ashirin kenan babu ranar Allah da zata fito ta koma ba tareda ta goranta mata talauchin da ba ita ko iyayenta suka siyawa kansu ba, dukda tabbas Mahaifinta shi yake ƙara zubar mata da mutunchi saboda ya kasa wadata da dan Abinda Allah ya hore mata take taimakonsu dashi haka shima Alhajin ta sani iyakar Ƙoƙari yanayi cikin su ukun ita kaɗaice duk watan duniya seya saukewa iyayenta buhunhunan Abinci da kuɗin cefane duk a son Baban nata ya dena banzar ɗabi'arsa ta yawon maula gidajen Masu kuɗi, ya dai rage amma fa kullum yana tafe gidan Alhaji Audu, sabulun wanka omon wanke wanke ko yana da kuɗin da ze siya se yazo ya roqa an bashi. Hajiya ta bita da Harara taja tsaki ganin Mu'allim yabi bayan mahaifiyar tasa bayan daya bi Hajiyar da wani kallon Tsana idanunsa sun tara ƙwallar baƙin ciki "Umma ta gaida Ashsha, dama banga tsegumin daya kawo ku ba Alhalin baku da abin faɗi" Hajiyar ta faɗa tana buga cinya kamar wata yarinya. Alhaji Babangida ne yayi gyaran murya, daga jin yanda yake magana kasan a tunzure yake yace "Amma Hajiya Binta ni banga ta inda zancen Auran Ahmad ko wadda yake son aure ya shafeki ba tun da dai ba ɗanki bane. Ita mahaifiyarsa batayi ƙorafi ko nuna rashin amincewarta akan abun ba se ke meye naki a ciki? Sannan koda ace mahaifin yarinyar nan yafi kowa talauci a duniya wannan ba hujjar ace ba za'a auri yarsa ba tunda talauci ba fasadi bane" "Nima abinda na gani kenan Yaya, duk ma ba wannan ba a gidan wa aka taɓa titsiyewa akan matar da yake son aure? Ina har yar rawar Tiktok aka auro mana gashi nan ta fitini kowa tana koyawa yaranmu shaiɗanci amma waya ɗaga kai yace wani abu kan hakan kodan saboda shi shafaffe ne da mai shiyasa ba'aga aibun abinda yayi ba se Ahmad da an san idan aka ce kar yayi ze haƙ Lura ai biyayya kuma ba hauka bace" Dr Hassan ya faɗa cikin ƙunar rai. Hajiya ta harari Alhaji Babangida, koda ta girme shi amma shakkarsa takeyi ta san ko shi Alhajin yana bashi darajar kasancewarsa Ɗa na fari a gidan, maganar Hassan ce tasa tayi kasaƙe tana kallonsa. Naziru ya zaburo masa yana cewa "Ka kira sunana kai tsaye ka dena wani kwane kwane, kuma na auri yar Tiktok ɗin koda abinda zakayi akai?" "Yi shiru da bakinka Naziru barni dashi" Hajiya ta gyara zamanta taci gaba da cewa "Yanzu kai Hassan tsabar baka da kunya ana maganar matar aure me Asali da tushe daga babban gida har ka saka baki? Koda yake kana da hujjar bin bayan Al'amarin, tunda uwarku ta auru a matsayinta na Tubabbiyar Karuwa ai dole kace wannan ma ba......" Tsawar da Hussaini ya daka mata me kama da saukar Aradu ta saka sauran maganganun bakinta maƙalewa. Cikin yanayin da yake nuna ƙololuwar ɓacin ransa dan hatta da jijiyoyin kansa daya sha askin Skin sun fito ruɗu ruɗu haka idonsa ya rikiɗa yayi jajir ya nuna ta yana cewa "Akul Binta, duk abinda kike ji dashi ya tsaya kan waɗanda kika raina karki yi kuskuren sako mahaifiyarmu a shirginki domin yanzu ba da bace idan kuma ba haka ba...." "Idan ba haka ba me zakayi?" Alhaji Zakariyya ya diro gabansa kamar wanda aka harbo da kwari da baka yana huci, Hajiya da tsoron Hussainin ya cikata jikinta har ɓari yake ta ja hannunsa Zakariyyah tana cewa "Barshi Ubana kasan ɗan hau ne" "Ki ƙyaleni Hajiya ku kuke nuna kuna tsoronsa a gidan nan idan zafin kai da ƙwaya yake ji dasu shi ƙaramin ƙwarone kansa baze ɗauki ko rabin chajin da nakeyi ba an faɗa ance Yayan Tubabbiyar Karuwa kayi abinda zak...." Marin da Hussanin ya ɗaukeshi da shi irin me jirkita ƙwaƙwalwar nan ya sakashi wuntsilawa gefe dafe da fuska yana raba idon, Hajiya Binta ta fasa ihu tayi kansa ganin yanda yake zare ido kamar tunaninsa ya kauce, a fusace shi kuma Naziru ya cakumi kwalar Hussanin ya kai masa naushi a fuska yana cewa "Wlh baka mari banza ba sena rama masa" kafin kace me dambe ya sarƙe a tsakaninsu kowanne ya shiga kaiwa ɗan uwansa mugun hari da yake jikinsu iri ɗaya ne, dukkaninsu sangangan suke irin jikin Audu Bechi wannan ya ƙarawa Damben nasu armashi dan kowa ya gagara kai ɗan uwansa ƙasa amma dai Hussainin yafi kai hari a zuciye. Ahmad, Momy da Dr Hassan ne suka shiga ƙoƙarin raba su sauran jama'ar falon kuwa seka rantse a Tv suke kallon wannan Al'amari babu wanda ma ya motsa balle ya kai agaji sema tattare ƙafafunsu da sukayi dan kar a faɗo musu. Hajiya na gefen Alhaji Zakariyyah dake kururuwa kamar mace sakamakon yanda Marin ya shammaceshi ya shige shi dagaske ga haƙorinsa ɗaya daya turguɗe a ƙasa, ihu Hajiyar take itama tana Zagin Hussaini, jafa'in duniya babu wanda bata janyo masa ba dashi da Hassan ɗinsa harda uwarsu dake can gida bata san wainar da ake toyawa ba ta karɓi rabonta se abi da Hajiyar ta manta ne bata ambata ba. Momy ta kalli Alhaji Audu dake zaune akan kujera tamkar gunki cikin kuka tace "Kana kallo Alhaji, jira kake se ɗaya ya kashe ɗaya kafin ka tsawatar musu? Wannan shine daidaiton da kake fatan samuwarsa cikin zuri'arka? Anya kuwa Alhaji ka shiryi tarar da ubangijinka cikin salama kamar yanda kowanne musulmi yake fata?" Tana gama faɗar haka cikin kuka ta fice daga falon, a bakin ƙofa taci karo da yayansu Mata a tsaitsaye cikin tashin hankali. Hajiya ƙarama datafi kusa da ita tacewa "Kira Babanku Alƙali ki gaya masa yazo babu lafiya a gidan nan" ta shige cikin gida tabar Hajiya ƙarama na ƙoƙarin kiran Baba Alƙali amma sau biyu wayar na suɓuce mata saboda yanda jikinta yake rawa daƙyar ta iya danna kiran. Momy kuwa harta isa ɗakinta hawaye be tsaya mata ba, ba kuma tasan ranar da zata dena zubar dasu ba hawayen baƙin ciki, takaici da dana sanin auran wannan mutumin da sam bata san me zata kirashi ba. Son zuciyane ko kuwa tsabar ƙin Allah ya saka Alhajin yin abubuwan da yakeyi bata sani ba amma koma menene ta tabbata muddin be tuba ya gyara alaƙarsa da Ahalinsa ba ya mutu a haka tabbas baze kwanta cikin salama a Kabarinsa ba. A can falon kuwa Hussaini ya mazge Hassan ɗinsa daya cukumi cikinsa yana ƙoƙarin janyeshi kafin ya kaiwa Ahmad ƙafa amma ya goce ba shiri suka matsa daga rabon damben suka barsu zuwa sannan Hussainin keda nasara dan ya kai Naziru ƙasa ya masa lilis har ya kai baya iya maida martani se Ƙoƙarin kare kansa kawai yake amma Hussaini be haƙura ba yaci gaba da jibgarsa kamar Allah ya aiko shi. Dama ce irin wadda ya daɗe yana fatan samu da ze huce kaɗan daga irin takaicin da Hajiya Binta da Yayanta suka ƙunsa musu a rayuwa. Lokacin yarinta tsoron hukuncin da Alhaji zeyi musu da izayar da zasu sha a hannun Hajiyar tasa yake haƙura idan zuciyarsa ta raya masa daya jibgi yayanta in suka musu abu, yasha ya kwatanta ya dake sun in yaso ya gudu ya bar gidan amma yasan Hassanbaze yarda ya bishi ba, saboda shi ya shanye duk wani wulaƙanci a gidan yanzu kuwa Allah ya bashi damar da duk wanda yace ze shigarwa Nazirun seya haɗa dashi ya zane. Seda Hussani gama yayiwa Nazirun casar gero kafin Allah ya bawa Alhaji Audu ikon yunƙurawa daga zaunen da yake tamkar wanda ya tafi hutu wata duniyar na wucin gadi ya dawo haka ya shiga jan numfashi kamar me Asthma. Ahmad yayi kansa yana cewa "kun gani ko ku bari idan ba kashe shi kuke so kuyi ba". Hussaini daya gama aikin Allah ya tsugunna ya ɗauki Agogon Azurfarsa daya tsinke a garin dambe bayan daya gaji da jibgar Naziru ya kalli Ahmad yace "Toh ya mutu mana, dama wa rayuwarsa ta dama bare idan ya mutu yayi baƙin ciki? Ƙilan ku da su daya ɗauka Yaya ya fifitasu akan kowa sune zasu shiga uku duk ranar da aka ce babu shi" sannan ya kalli Hajiya Binta da idanunsa da suka koma abin tsoro yace "Nan gaba idan wani daga cikin marasa kunyar Yayanki yayi niyyar tsoma baki a sabgata ki gargaɗeshi, idan ba haka ba zanci gaba da nuna muku abun da Ɗan Tubabbiyar karuwa ze iya aikatawa" yana gama faɗar haka ya fice daga falon a fusace fuuuu kamar kububuwa. Maganganun Hussaini sun daki ƙirjin Alhajin kamar shigar bullet, ya yunƙura cikin wani yanayi ya tashi tsaye dan bakinsa kamar an liƙe masa shi da glue yake ji yana tsayuwa akan ƙafafunsa jiri ya kwasheshi ya koma kan kujerar Yaraf kamar wata gingimemiyar giwa ta faɗi. Ahmad da Hassan suka rufu akansa, Hassan ɗin ya kalli Ahmad yace "Riƙeshi, bari na ɗakko Kit ɗina a mota mu gani idan kuma babu hali mu wuce Asibiti dashi kawai" yana gama faɗar haka ya fice da gudu kamar yaro ya nufi motarsa. Da wani irin yanayi Alhajin ya ringa kallon Yayansa Maza da suka fara miƙewa da ɗaɗɗaya suna barin falon harda masu sakin ƙananun tsuka dalilin ɓata musu lokaci da akayi da wannan wasan kwaikwayo da suka rigada suka saba dashi babu Wanda ya nuna damuwar cewa wai Mahaifinsa ne a wani yanayi da ko ba'a faɗa ba sunsan Hawan Jininsa ne ya tashi Allah ma ya taƙaita ba Paralysis ya samu ba irin wannan komawa da yayi ya faɗi akan kujera, wani abu ya tokarewa Alhaji Audu maƙoshi, hawaye ya ziraro a idanunsa abinda ya sake rikita Ahmad kenan a shekarunsa Talatin a Duniya sau ɗaya ya taɓa ganin ƙwalla a idon Mahaifinsa lokacin da aka kawo gawar Brigadier General Baballiya se yanzu kuma hawaye yake dagaske tabbas Al'amarin dake zuciyarsa ba ƙarami bane. Yanda Dr Hassan ya dawo yaga Alhajin yasa yace kawai su kamashi a tafi Asibiti. Seda ya ɗura Ashar kafin su Salim suka saka hannu aka fita da Alhajin dan Manyan daman tun yana wajen yaga suna ta shigewa motocinsu suna jiran Iyalansu su fito su tafi, da alama Abincin da Hajiya tasa akayi zeyi bandaro dan zama beyi daɗin da har za'a jira cin abinci ba. Hajiya ta ringa ihu kamar wadda ta shiga ƙaramin hauka, Ga Zakariyyah fuska harta suntume saboda haƙorin daya fita ba bisa ƙa'ida ba Naziru kuma na kwance numfashi ne kawai ya banbantashi da matacce Hussaini ya sauke masa duk wata giggiwa da yake fama da ita suma ɗin Dr Hassan ne yasa aka watsa su a mota duk suka rankaya a Asibitinsa. A hanya Ahmad ya kira Baba Alƙali yace masa yana tafe ya kusa isowa gidan Hajiya ƙarama ta kirashi se yace masa ai suna hanyar Asibiti be jira jin ba'asi ba yace ze same su acan domin yasan a runa. Haka nan rana tsaka Audu ya tattaro irin wannan haɗuwar ba tareda yabi matakan da suka dace ba, zuri'ar da kowanne yake da wani fushi ko miki a zuciyarsa ta yaya zaka ce a lokaci gida zaka sasanta komai ka samu yanda kake so? Ya tabbatar wani abun akayi ko aka faɗa masa da ze saka jininsa ya hau tilas Allah dai ya taƙaita. Emergency aka karɓi Alhaji Audu su Naziru ma aka watsa su inda ya kamata. Seda akayi stabilizing kowannensu kafin suka samu nutsuwar zuciya. Baba Alƙali ya ringa sababi kamar ya ari baki sanda Dr Hassan ya bashi taƙaitaccen labarin abinda ya faru. "Ka kira Hussainin ka mai komai dare ya sameni a gida yau wane irin abu ne yake damunsa duk me ubanku ya muku ai baze canza masa suna ba ya za'ayi ya faɗa masa irin wannan maganar? Kai bama shi kaɗai ba gaba ɗayanku ku hallara ina son ganinku tunda naga alamar so kukeyi ku janyo mana abinda ze fi ƙarfin mu". " "Nima dai haka na gani Alƙali, ni daga yin abu dan Allah da zuciya ɗaya nace a shirya taron nan ya janyo yayansa a jiki su samu daidaito amma kaga yanda abu ya ƙare dana sani bance ayi ba haka kawai wannan la'anannen yaron ya cutar mun da yaya ya barsu da jinya" Hajiya Binta ta faɗa. Alƙali ya kalleta, cikin tsanin fushi yace "Har akwai wani la'ananne bayan ke ne Binta? Ke ce saboda rashin tsoron Allah zaki ce kin shirya abu da zuciya ɗaya saboda Audu ya samu daidaito da Yayansa ko ki sake farraƙasu? Kinyi ne da niyyar ki tozarta Ahmad da matar da yake son aure tun gabanin ta shigo cikin mu kina so kuma ki lalata kyakykyawar Alaƙar da kikaga ta fara ginuwa tsakaninsa da Mahaifinsa ta hanyar saka Audu ya hanashi abinda yake so daga nan ki saƙa mumummunan zare a zuciyarsa ko? To ba zakiyi nasara ba da yardar Allah duk wani sharri da kike yi bazeyi tasiri ba, duk wani sharri da kika niyyaci ƙullawa akanki ze ƙare. Kin bawa shekaru hamsin baya, ubangiki yayi miki Arziƙin tsahon rai ya baki dama da zaki gyara kurakurenki na baya amma saboda kin rigada kin auri duniya shaiɗan ya gama samun isahshen guri a zuciyarki baze barki ki hango gaba ki tubarwa Allah ki gyara laifukanki na baya ba a kullum zuciyarki sharri ce a ciki shi kike ƙoƙarin aiwatarwa. Ni naji daɗin daya dake su, kuma da kaina zan bashi goyin bayan duk mara tarbiyyar daya sake taɓa martabar Mahaifiyarsa idan ya samu dama ya tsinke masa harshe, abu guda ne bazan lamunta ba rashin Ɗa'a ga ubanku, kome yayi muku tilas yaci arziƙin yin silar zuwanku duniya, in har da gaske yakeyi ya shirya neman sasanci daku ku bashi dama domin ubangiji ma muna saɓa masa kuma mu nemi afuwarsa ya yafe mana wannan shaiɗaniyar ita ce silar faruwar komai a rayuwar Abdulwahabu ku taru ku taimaka masa ku kaita ƙasa ku bata kunya tunda dai ita babu gyara a rayuwarta tamkar dabbar Daji take kullum ƙara nausawa dawa takeyi". Alƙali Yakubu be damu da cewar a Reception ɗin Asibiti suke ba kuma da mutane suna ta kai kawo a gurin duk anyi cirko cirko ana sauraronsa ya wanke Hajiya Binta tas da soson kaba haɗi da klin da hypo, yanda yake maganar murya a sama zaka tabbatar da cewar yau zuciyar Mazan ta harzuƙa dab kuma yake daya kwasa mata mari muddin tace zatayi inkari akan abinda yake faɗa. Hajiya kuwa hannaye biyu ta aza akai tana kuka tana cewa "Daman na sani kaf dangin Audu babu wanda ya tsaneni ya tsani zuri'ata irinka Yakubu, ni kake kira La'ananniya? Nice shaiɗaniya? To bari naje seya tashi ya Zaɓa koni ko kai. Idan kai ya zaɓa daga nan gidanmu zanyi dan babu abinda ze sake zaunar dani a inda ba'a san mutunchina dana Zuri'ata ba idan kuma ya zaɓeni wlh se dai ya rabu dakai ya zareka daga Al'amuransa tsaf babu mu babu kai. Shikenan kawai saboda kai matarka bata da zuciyar haifar Yaya Maza seka ringa baƙin ciki da ɗaukakar da Allah ya bawa nawa dana haifa? Ai nasan duk ba komai bane baƙin cikinka saboda Audu nada Magada kuma Yayana nane akan Dukiyar Audu yau idan ya faɗi ya mutu ko sillin gashi baka da gado a cikin tarin Arziƙinsa. Takaicinka kuma yanda kullum Yaya nane a gaba sunfi duk sauran yayan da aka haifa a gidan Ƙashin Arziƙi". Alƙali Yakubu yayi wata dariya, da alamu ya mance da inda suke shiyasa yake zaro maganganu duk yanda sukayi masa. Kallonta yayi sama da ƙasa yace mata "Ina Alfahari da Yayan da ubangiji ya bani Mata, Namiji gudan daya bani ya fiye mini taron Yuyuyu irin wanda ke kike iƙirarin kin haifa. Ke hai kinyi haihuwar da zaki bigi ƙirji kiyi Alfahari da ita Binta? Arziƙin yayan da yake cuɗanye da na sata da na ƙazantacciyar harƙallah? Bari kiji, wlh idan naso jirkita rayuwarki a cikin taƙaitattun sa'oi se kin bazama neman inda zaki boye a cikin ƙasar nan, kije ki fara gyara tarbiyyar Yayan da kike tinƙaho dasu kafin su zama abin Alfaharin, ina mai tabbatar miki Binta da raina ko na mutu akwai ranar da baƙin cikin waɗannan yayan da kika cuta kika gurbata musu rayuwa kika koya musu zalama da rashin wadatar zuci irin naki se sun saukar miki da Ciwon da in bakiyi wasa ba shi zeyi Ajalinki" "Dan girman Allah Baba kayi haƙuri, ba anan ya kamata ayi maganar nan ba, Ahalinmu sanannu ne yanzu se kaji zanje yana tashi a Kafafen sada zumunta daga nan Allura seta tono garma" Dr Hassan daya matsa kusada Baba Alƙali ya faɗa yana kama hannunaa, shiyasanme Alƙalin yake magana akai.