♣️DUHUN UNUWA ♣️ TAPING......📲📲📲 STORY AND WRITING✍️✍️✍️ BY NABEELAH SHEHU BINJ BISMILLAHHIR_RAHAMANIR_RAHIM PAGE 0️⃣1️⃣ Misalin karfe 5:30 na yamma wasu masoya ne zaune a kan fararen kujerun roba, fira suke cikin farin ciki da Nishaɗi. kallo ɗaya za kayi musu ka fahimci suna matuƙar so da ƙaunar junan su, saboda ba abunda kake gani akan fiskukin su sai yalwa taccen murmushi mai matuƙar ƙayatarwa. Saurayin ne ya kalli budurwar tasa cikin sakin fuska yace my noor tambayarki fa nakeyi kinyi shuru, nace wane event ne Kika shirya za kiyi. Sunkuyar dakai tayi tare da saka hannuwan ta ta rufe fuskarta alamar kunya. ɓata fuska yayi kamar zaiyi kuka yace haba my Noor wai meyasa kike min irin haka ne? a duk lokacin da nake miki maganar auren mu sai ki dinga nuna min jin kunya. gaskiya ni bana so ai idan da sabo mun zama ɗaya, ƴan kwanaki ƙalilan ne fa suka rage mana muyi aure, idan bamuyi shiri tun yanzu ba sai yaushe kenan? Ɗan muskutawa tayi ta gyra zaman ta tare da sunkuyar da kanta kasa, a hankali cikin sanyin muryar tace kayi haƙuri my Shadow, ba wai ban damu da shirin bikin nan bane wallahi matuƙar kunyarka nakeji musamman ma da bikin nan yayi gab, sai na keji duk abubuwa suna sauyamin ba kamar da ba. Murmushi yayi mai cike da nishaɗi yace wllhy kina bani mamaki my Noor, sai nakeji a raina kamar baki damu dani yadda na damu da ke bane. Dasauri ta ɗago ta kalle shi ta shagwaɓe fuska kamar zatayi kuka ta ce haka dai kake gani, but na damu da kai fin yadda ka damu dani, kuma lokaci yana zuwa zaka gani. Murmushi yayi mai sauti tare da tashi tsaye yace tohm zan tafi ranki ya daɗe, dama na faɗa miki akwai gurin da zanje, amma sai naji ba zan iya zuwa ba ba tare da nazo naga Haskena ba. Ya ƙarisa maganar yana murmushi. Ita ma murmushin tayi tace nagode Sosai my Shadow. Ba godiya a tsakaninmu my Noor fatana kawai shine idan munyi aure karki zamar min DUHUN INUWA ki riƙe amanata Noor ni mutum ne wanda ke son magana ta gaskiya da gaskiya, bana son ɓoye ɓoye akan komi duk abunda zaki faɗa yaza mana gaskiya ne, koda ace naji zafin abunda kikayi tohm zanfi jin farin ciki idan kin faɗa min gaskiya akan kiyi min ƙarya, idan kin kiyaye wannan tohm ni bana da wata matsala Noor. Ajiyar zuciya ta sauke tare da kallonsa tace na daɗe da sanin wannan my Shadow. kuma insha Allah zan zama mai kiyayewa akan duk abunda baka so, sanin kan kane ba abunda nake ɓoye maka a rayuwa, kuma insha Allah ba abunda zan ɓoye maka nan gaba. Allah ya yarda Noor,,, Ameen ya Allah Mijina,,, Salama yayi mata tare da hawa machine ɗinsa ya ta dashi yatafi. saida taga fitarsa daga gidan sannan ita ma tashiga gida tana murmushin jin daɗi. Bayan sati biyu da faruwar haka shirye shiryen ɗaurin aure ya kan kama saboda duk wani event da akeyi kamin ɗaurin Aure an riga da an gabatar dasu. Sai Diner da za'a gabatar gobe idan an ɗaura aure. Amarya Noor ansha kyau ta ko ina ta gibta sai tashin ƙamshi kakeji na mussamman. Ta ɓangaren shadow kam ba dama yau gaba ki ɗaya ya kasa samun zama saboda baƙine suke zuwa na nesa wanda idan sukace sai gobe ne zasu zo tohm fa ba shakka baza su samu halartar ɗaurin auren ba. Yanzu haka ma wasu Abokanan sa ne ya tarbo wa ƴan da sukayi Bautar ƙasa tare dasu a gombe. daya ke su ƴan asalin gomben ne, kuma sunyi zaman mutunci sosai da Shadow hakanne ma yasa su kaci Alwashin zuwa sokoto idan aurensa ya yazo. Fira suke mai cike da nishaɗi da kewar juna. ɗaya daga cikinsu ne mai Suna Kamal ya kalli Shadow cike da tsokana yace angon Noor, wannan Noor ɗin da ace baka sameta ba da (maybe) gidan mahaukata ne kawai zai iya ɗaukarka, cox ban taɓa ganin wanda ya sadaukar da lokacinsa da kumai nasa akan soyayya ba kamar kai. (sometime's) fa har tausayi kake bani cox nasan halin mata basu da tabbas sun ƙware agurin karya zuciyar mutum wllhy. Dariya Shadow yayi sannan yace kai Kamal ai ko matan ma suna suka tara, ni nan na yarda da Noor kuma na yarda da tarbiyar gidansu na yarda da soyayyar ta agareni ta gaskiya da gaskiya ce. wannan dalilin yasa bana saka Noor acikin ƴan matan wannan zamanin, har abada ina da (confidence) a kanta, ita ɗin ta musamman ce a rayuwata. Kamal mai yasa ka cika biyar diddiƙi ne wai? ka ɗauka ko wace yarinya kalar Sadey beb ɗinka ce? wace tasan kan yaudara da karya zuciyar samari. Haidar ya faɗa yana bushewa da wata irin dariyar ƙeta da son Ƙufulal da Kamal ɗin. Ai kuwa yayi nasarar haka dan nan take Kamal ya fara hauhawa kamar farashi. ya murtuƙe fuska kamar ba Kamal ba mai son wasa da dariya, ya kalli Haidar rai a ɓace yace wai Boss bana faɗa maka mun rabu da wannan yarinyar ba. kuma na faɗa maka bana son maganarta, but kai na lura duk lokacin da kayi nufin baƙanta min rai sai ka dinga min maganar ta ko? ya faɗa yana ɗauke kansa gefe ɗaya irin shi a dole an ɓata masa rai ɗin nan. Shadow ne yakashe fitinar ta hanyar bawa Kamal haƙuri yana dariya yace kai amma kuwa Sadey beb bata kyauta mana ba. Ni nazata idan ba kai bazata iya rayuwa ba. a dai yadda take nuna damuwarta akan ka gaskiya banyi zaton kwanton ɓauna tamaka ba kamal. Tsaki kamal yayi yace wallahi ashe ga baki ɗaya ƙarya da yaudara ne a cikin kalaman ta. Amma ai tayiwa kanta dan ita ce tayi rashi bani ba yafaɗa yana shafa sajen da ke kwance akan dogowar fuskarsa. shi a dole mai kyau ne. yace maybe ma anan nasamu Wata mai sa'a tayi wuf dani, dan naji ance ƴan matan garin nan akwai soyayyar gaskia da iya kula da saurayi ko? ya faɗa yana kallon Shadow. Dariya sukayi ga baki ɗayan su. fira suke cikin nishaɗi A haka har suka ƙarasa gidan su Shadow da ke a unguwar Minannata. RANA BATA ƘARYA.😞😞 Ayau 15/12/2021 dan dazon jama'a suka taru domin shaida ɗaurin auren Ahanaf Muhammad Imran (Shadow) da Noriya Mukhtar Salah (Norr). Kamar yadda aka Saba idan anzo ɗaura aure dole sai mutane sun haɗu dangin ango dana amarya bayan kowa ya hallarane aka zauna domin gabatar da abunda yatarasu agurin. Hankalin Shadow ya koma kan abokansa da suketa faman zolayarsa. Saiji yayi Gurin yakaraɗe da muryar wani ba banbaɗe. inda yake cewa Alhmdllh an ɗaura auren NORIYA MUKHTAR SALAH da angonta AL-ƘASEEM MUHAMMAD IMRAN akan sadaki naira dubu ɗari cif lakadan ba ajalanba. Shadow ne ya tashi da sauri har Yana tangadi ya kalli abban sa yace Abba kunyi kuskure fa sunana Ahanaf Muhammad Imran ba Al ƙaseem Muhammad Imran ba. Abba da Al ƙaseem aka daura auren Nan bani ba? Dan Allah Abba kagaya musu wannan sunan ƙanina ne ba nawa ba. Abba me yake faruwa ne? Dan Allah agyara sunan nan Abba, Shadow ya faɗa cike da ruɗewa da firgici kwallah fal idanunsa. Wanda yaketa faman Kira da Abban ne yakama hannunsa yace Ahanaf muje gida sai nayi maka bayani kaji. Dasauri ya kwace hannunsa daga na mahaifin nasa. Cikin murya Mai Amo da nuna zallar bacin Rai yace Abba baxan bar Nan gurin ba har sai kun gyara wannan Rikitaccen Al amarin da kuka kulla. Dan girman Allah Abba kugyarashi tunkan hankalin mutane yadawo Nan su fahimci halinda ake ciki. Abba Norr fa da Al kaseem? Me nayi muku ne haKa Mai zafi da har zaku dauki fansa ta wannan hanyar? Abba idan har laifi na maka kayi min komai Amma Banda hanani auren Norr dan Allah, wllhy Abba Ina sonta Kuma bazan iya rayuwa ba idan har Bata. Abba karka jefa rayuwar ɗan ka a cikin DUHUN INUWA plxx. Abba ko dai ba kaine mahaifin... Kafin ya rufe bakinsa sai jin wani zazzafan Mari yayi tasssssssssss a kumatunsa. Ɗagowa yayi da sauri ya kalli mahaifin nasa cike da matuƙar mamaki. Yau shine Abba ya mara Kuma akan gaskiyar sa? Abba da ko faɗa baya bari ayi masa bare a ɓata masa rai saboda Yana da sunan mahaifin sa. Amma yau har da Mari. Shin kodai mafarki nakeyi ne? Shadow ya tambayi kansa cike da rudani. Ba mafarki kake ba Ahanaf wannan zahiri ne cewar Abba dake ta faman sauke nunfashi cike da ɓacin rai. Abba ya ƙara da cewa Ni mahaifin ka Muhammad Imran na ɗaura auren Noriya Mukhtar Salah da na Al ɗaseem Muhammad Imr..... Ai kafin ma ya rufe bakin sa Nan take Shadow ya zube ƙasa ba alamar Numfashi a tare dashi. TIR ƘASHI🙆🙆🙆 Taya hakan tafaru? A Ina matsalar take? Menene dalilin da yasa su Abba sukayiwa Shadow hakan? Anya kuwa Norr zata yadda da Ƙaseem a matsayin miji? Shima Ƙaseem Zai karɓi Norr a matsayin mata duk da yasan irin son da yayan sa yake mata? Ko dai Shadow yanada wata matsala ne? Ku dai ku kasance tare Dani Nabeelah Shehu Binji Dan jin yadda wannan Al amarin Mai matukar sarƙaƙiya zai kasance. Nabila binji☎️☎️ 09064314811 09161107610 More comment More taping 😉😉 Share Fisabilillah 🙏🙏🙏 ♣️ DUHUN INUWAH ♣️ STORY AND WRITING ✍️✍️✍️ BY NABILA S BINJI PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞 ```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)``` /https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/                   *P.W.A✍️* Hadiths of imam An-Nawawi Verily the creation of each one of you is brought together in his mother's womb for forty days in the form of a nutfah (a drop), then he becomes an 'alaqah (clot of blood) for a like period, then a mudghah (morsel of flesh) for a like period, then there is sent to him the angel who blows his soul into him and who is commanded with four matters: to write down his rizq (sustenance), his life span, his actions, and whether he will be happy or unhappy (i.e. whether or not he will enter Paradise). By the One, other than Whom there is no deity, verily one of you performs the actions of the people of Paradise until there is but an arms length between him and it, and that which has been written overtakes him, and so he acts with the actions of the people of the Hellfire and thus enters it; and verily one of you performs the actions of the people of the Hellfire, until there is but an arms length between him and it, and that which has been written overtakes him and so he acts with the actions of the people of Paradise and thus he enters it. BISMILLAHHIR_RAHAMANIR_RAHIM Page 0️⃣2️⃣ Al amarin da ya janyo hankalin sauran mutanen da ke wurin kenan Wanda da tun farko Basu fahimci me ke faruwa ba. Da sauri Al ƙaseem yazo gurin da Shadow yake kwance a ƙasa ya durƙusa kan gwiwowinsa yaɗa goshi yaɗaura shi a saman jikinsa, Yana girgizashi cike da tashin hankali yake cewa Yaya Shadow Dan Allah katashi karka mutu ka barni idan kamutu nima mutuwa zanyi, wallahi in dai Norr ce ni Nan zan rubuta Mata takardar saki da hannuna, Yaya ban san menene dalilin da yasa su Abba suka yanke wanann mummunan hukuncin ba, Amma kasani koma Mai menene dalilinsu ni bazan taɓa lamuntar wannan zaluncin ba Kuma zanyi kumai dumin farin cikin ka Yaya. Dan Allah katashi kaji tausayina Yaya banida wani ɗan uwa a duk faɗin duniyar nan da yawuce ka, dan haka ba abunda bazan iya sadaukarwa ba saboda kai yaya. Ƙaseem ya faɗa Yana fashewa da wani matsanancin kuka Mai taba zuciya. Duk mutanen gurin sun fahimci abunda ke faruwa, kuma sunyi matuƙar mamakin wannan sauyin da aka samu Mai cike da rudani da Al ajabi. Sudai sun san Ɗaurin Auren Ahanaf suka zo, amma kuma sunji mai shelar ɗaurin aure yana cewa an ɗaura aure da Al ƙaseem ba Ahanaf ba. wanda duk duniya ta sheda cewa Al ƙaseem ƙanene agurin Ahanaf na jini kuma suna matuƙar kaunar junan su, idan kagansu baza ka taɓa cewa su saƙo bane, saboda ba wannan rashin jituwar a tsakanin su, idan kagansu zaka iya rantsewa tagwaye ne banbancin su kaɗan ne shi Al ƙaseem farine tas saɓanin Shadow da ba zaka iya kiran shi fari tas ba kai tsaye. Cikin ɗaga murya Ƙaseem yace Dan Allah wani yataimaka min da ruwa, ba ɓata lokaci Kamal Abokin Shadow ya bayar da gorar ruwan da Shima yanzu ya ɗauko su a Mota domin ceton ran Abokinsa, an zuba mishi ruwan yakai sau ukku amma ko motsawa baiyi ba na nuna alamar cewa Yana Raye cikin tashin hankali Ƙaseem ya warce gorar ruwan daga hannun Kamal ya zuba su gabaki ɗaya a fuskar Shadow. Wani dogon numfashi yaja tare da tashi zaune yana zare ido kamar wani taɓaɓɓe, Kalle kalle kawai yake da alamar akwai wanda yake nema, ganin bai ga wanda yake neman bane yasa shi mai da kallon sa a kan Al ƙaseem ya ƙure shi da manyan idanunsa da sukayi ja kamar barkono, da sauri Al ƙaseem ya sunkuyar da kasan sa ƙasa cikin tashin hankali da baƙin cikin wannan ranar fiye da kowace rana a rayuwar sa. Kafin zuwan wannan lokacin yana cike da matsanancin farin cikin auren Yayan sa kuma Garkuwansa. Amma a yanzu yama kasa tantance a wane hali zuciyarsa take ciki. Cike da tashin hankali Shadow yace" Ƙaseem Ina Abba yake?" da sauri Ƙaseem ya goge hawayen idonsa yace ya Shadow Ina ga fa kamar Abba Ya tafi gida. Cikin sauri Shadow ya tashi tsaye yanufi mota cikin sassarfa har yana tuntuɓe da nufin zai ja Motar da kansa. da sauri Haidar ya mara masa baya ya riƙesa tare da buɗe Masa gefen Mai zaman banza yasashi aciki ba musu ya zauna saboda shi duniyar ma gabaki ɗayanta juwa masa takeyi sunkuyar da kansa yayi ƙasa cike da tashin hankali. rufe murfin motar Haidar yayi tare da koma wa side ɗin driver ya zauna, Yayi wa motar key yabar gurin a 360. Shima Al kaseem Tashi yayi tare da bin bayan Kamal suka Shiga Mota suka marawa su Shadow baya. Anan aka bar mutane kowa Yana furta Albarkar bakinsa akan wannan abun da yafaru, da yawan mutanen gurin laifin iyayen yaran suke Gani musamman ma Alh Muhammad Imran Shi da har ya iya ɗaga hannunsa ya Mari Ahanaf a cikin wannan halin, tohm Wai menene ma dalilin wannan abun da suka akaita? Ko ma dai menene dalili zamuji Nan ba da jimawa ba insha Allah cewar Wani dattijo Yana gyara zamar babban rigar sa. Tafe suke cikin Mota ba Abunda kake ji Sai matsanancin bugun zuciyar Shadow Wanda yake sauke numfashi da kyar kamar Wanda yake dab da barin Duniya. kallon sa Haidar yayi cikin tausayawa da jimamamin wannan lamarin yace kadinga furta Kalmar Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raju'un Zaka Sami sauƙin abinda kakeji a ranka friend. Kuma ka kwantar da hankalin ka insha Allah bazaka Rasa Noor ba. Yazama lallai su Abba su Gaya Mana dalilin wannan abun da suka akaita, insha Allah Kumi zai zo da sauƙi friend, Haidar ya fada Yana kokarin danne damuwar sa da son kwantar wa Abokin nasa hankali, Amma Shi kadai yasan Abunda yake ji a zuciyar sa. Ko ɗagowa Shadow beyi ya kalli Haidar ba balle har ya aikata abinda yace Masa shidai Kawai burinsa yaganshi gida gaban mahaifiyarsa da mahaifinsa ya tambaye su dalilin da yasa sukayi Masa Hakan, yasan Koda ace kowa zai juya Masa baya a duniyar Nan tohm tabbas mahaifiyarsa da Norr ɗinsa bazasu taɓa juya Masa baya ba, wannan dalilin yasa yanzu su Kawai yake burin Gani Koda zai Sami salama a rayuwar sa, Shi Gani ma yake kamar ba tafiya Haidar din yake ba. Minannata Gidan su Shadow Hada Hadar biki Kawai ake da shirya abinci Yan Ɗaurin aure kafin su dawo. Tsaye take Tana faɗawa mai aikinta yadda take son abubuwa su kasance. Kawai Sai hango shigowarsa tayi tun a yanayin driven ɗinsa ta fahimci akwai matsala fitowa yayi daga motar Yana zuba sauri kamar zai kife yanufi part ɗinsa, gabanta ne yayi mummunan bugawa hankalinta yatashi sosai Dan Rabon da taga Abba acikin wannan halin bazata iya tunawa ba. Bayansa tabi da sauri aranta Tana fatan ace bawani mummunan abune yafaru a gurin ɗaurin auren ba. Palo tashiga Amma Bata ganshi ba Hakan yasa ta nufi bedroom dinsa direct ƙirjinta yana matsancin bugawa da sauri sauri. hannunta ta ɗaura akan ƙofar ta Murɗa bakinta dauke da sallama tashiga dakin, hangoshi tayi a tsakiyar ɗakin ya rungume da hannayensa a baya Yana Safa da Marwa. Ƙarasawa tayi gurin da yake cikin tsinkewar zuciya tace Abba Mai yafaru? Ina Ahanaf din Wani Abu ne yafaru a gurin ɗaurin auren? Ta jefo Masa waɗan Nan tambayoyin a lokaci ɗaya. Ko Kallonta ma beyi ba Barre ta sa ran zai amsa Mata tambayoyin ta. Baki ta bude da nufin Kara yi Masa Magana Sai taji an turu ƙofar an shigo, Juyawa tayi Dan ganin wanene, Ido hudu tayi da Ahanaf saida kirjin ta ya buga da ƙarfi a lokacin da taga Yaron nata abun Alfaharin ta cikin sassarfa ta karaso gurin da yake tsaye kamar an dasashi Tana ƙarasawa ya faɗa jikinta tare da fashewa da matsancin kuka Mai cin Rai. Tabdijam hankalin Ayiya yayi matuƙar Tashi ganin yadda jarumin ɗanta yake raira Mata kuka kamar mace tabbass tasan wannan lamarin ba ƙarami bane, dalilin da yasa itama ta fara kukan Kenan. Ba Abunda kake ji a ɗakin Sai sautin kukansu Abba ne yadaka musu wata irin gigitaciyar tsawa yace Sufitar Masa daga ɗaki Shi ɗakinsa ba gurin kuka bane. Cike da mamaki Ayiya tabishi da kallo tace Anya kuwa yau Abba kana cikin hankalinka kasan mekake cewa kuwa? Bana cikin hankalina Haj Shuwa duk abinda yazo bakinki Zaki iya fada kinji, Amma Dan Allah abinda nake so daku shine kufita kubarmin ɗakina plxx. Ba in da zamuje Abba har Sai ka Gaya Mana menene dalilin da yasa ka ɗaura auren Norr da Ni saɓanin Yaya Shadow, Al ƙaseem ya faɗa hawaye kwance a idanunsa, Wani irin Jiri ne ya fara daukan Ayiya Wanda yasa taji gabaki ɗaya duniyar ta tsaya Mata Cak, zaunawa tayi dabar a kasa cike da matsancin tashin hankali tama kasa buɗe baki tayi Magana, Kuma ta daina Jin duk Wani Magana da suke a tsakaninsu tunda take a Duniya Bata taɓa Shiga tashin hankali irin wannan ba. Tsawar da Abba yadakawa Al ɗaseem ce tayi nasarar dawo da ita Duniyar da muke ciki. Yace Kai yanzu Al ƙaseem har kayi kwarin gwiwar da Zaka tsaya a gabana Ina Fadi kana Fadi? Tohm wallahi bari kaji na faɗa Maka kana kuskuren sakin Noor Kai ba Ɗana bane Kuma Allah ya'isa ban yafe Maka ba. Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raju'un, Lahaula Wala kuwatah illah Billah Shadow yafada cikin sautin kuka. Al ƙaseem ya bude baki da nufin sake Magana cikin sauri Shadow ya Tashi tsaye ya rufe Masa baki tare da girgiza Masa Kai alamar Kar yakara wata Magana. Hanyar fita Abba yakama da nufin bar musu ɗakin gabaki ɗaya. cikin sauri Ayiya Tashiga gabansa har tana tangadi kamar wata Yar maye tace Abba ba inda zakaje baka faɗa Mana menene dalilin ka Na aikata wannan abun ba. Tsayuwar sa yagyara yana kallon cikin idanunta yace bawani dallili Shuwa kawai nadaiyi ra'ayin haka ne, shiya nayi saboda da Ahanaf da Al ɗaseem dukansu ƴaƴana ne ina da ƴancin yanke hukuncin da Naga Dama akan su, sbd haka ki matsa daga Nan na wuce Shuwa. Ba inda zakaje baka faɗa Mana dalin wannan abun da ka aikata ba Wallahi Muhammad. Cikin mamaki ya Kalle ta yau Shuwa da Fadin sunansa ba kunya ko Kara? Abunda Bai tabaji ba Kenan a tsawon rayuwar sa da ita, murmushi yayi yace lallai kuwa kin Isa Shuwa Kuma Nagode sosai da tsayayya. Zagayeta yayi da nufin fita daga ɗakin tayi saurin riƙo rigarsa tana cewa Ina Zaka tafi kabar mu a cikin DUHU? tabbass bazaka fita daga ɗakin Nan ba har Sai ka.... Wani wawan Mari taji a kumatun Wanda ya razana ta tare da yin baya kamar zata Faɗi. Dasauri Shadow yatare ta tafaɗa jikinsa ya rungeme ta ajikin sa Yana Jin Wani irin baƙin ciki Wanda tun zuwansa Duniya Bai taɓa cin karo da makamancinsa ba. Idonsa yadɗago wa ƴanda sukayi ja kamar garwashi ya zubasu akan fuskar mahaifinsa, Wanda izuwa yanzu ya kejin baya ma ƙaunar ganinsa gabaki ɗaya, Tabbass da a ce ba mahaifinsa bane yataɓa masa Ayiya da ko waye sai ya ɗanɗana kuɗarsa. hannunta yakama yakaita bakin gado ya zaunar da ita. Shikuwa Abba ficewa yayi daga ɗakin Ransa a matuƙar ɓace. Shadow Juyawa yayi ya kalli Al ƙaseem cikin murya wace take nuna tsantsan damuwa yace karka kuskura ka musawa Abba akan duk wani abunda kaga zai aikita, kuma karka kuskura sakin Noor idan dai bashine yayi maka umarni da hakan ba. Buɗe baki yayi da nufin magana Shadow ya ɗaga masa hannu yace bana son jin komai daga bakin ka dan Allah Ƙaseem. juyawa Ƙaseem yayi fuuuuh yabar ɗakin kamar zai tashi sama saboda tsananin ɓacin rai. Gurin Ayiya ya nufa wace take zaune tun ɗazu a inda ya ajiye ta kamar wata butun butumi. Zubewa yayi ƙasa akan gwiwoyinsa ya kamu hannayen ta yace Ayiya dan Allah ki saurari abunda zan faɗa miki, kar kiyi wani abu wanda zaisa mutanen da ke gidan nan susan Halinda muke ciki. koma menene kibari har mutane su watse dan Allah Ayiya yafaɗa tare da matse hannayen ta sosai acikin nasa. Zare hannayenta tayi cikin nasa cikin ɓacin rai tafara magana. Ahanaf bazan taɓa lamuntar wanan abunba, wannan zalincin yayi yawa ko da ace ba akan ƴaƴana wannan abun yafaru ba to ni nan mai iya tsayama koma waye ne dan ganin yasamu adalci. bare akan yarana. Ahanaf saidai kayi haƙuri a wannan ƙaron bazanja bakina nayi shuru ba wallahi, kuma kaji na rantse. Kansa yadafe tare da furta ya Allah wannan wace kalar jarabawa ce ya Ubangiji ina neman afuwarka ka sassauta mana wannan lamarin, wannan Rana ce dana ci buri akanta najima ina tsumayin zuwanta da muradin ganinta. dana san haka zata kasance dani da na roƙi Allah karma ya nunamin wannan BAƘAR RANAR. Yaƙarisa maganar cikin matsanan cin kuka tare da ɗaura kansa akan ƙafafun Ayiya, bayansa ta dinga bugawa a hankali cikin sigar rarrashi. A gidansu Noor kuwa tuni labari ya riski mahaifiyar ta najin saɓanin da aka samu gurin ɗaurin auren. cikin tashin hankali ta miƙe tsaye tare da cewa wllhy bazai yuyu ba wannan ai hauka ne ma. Nabeela Binji ce💃💃💃 Nabeelah Shehu Binji 09064314811 Or 09161107610 More comment More taping 😉😉 Share Fisabilillah 🙏🙏🙏. ♣️DUHUN INUWA♣️ STORY AND WRITING ✍️✍️✍️ BY NABILA S BINJI PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞 ```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)``` /https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/                   *P.W.A✍️* BISMILLAHHIR_RAHAMANIR_RAHIM Page 0️⃣3️⃣ Wannan abun ba zai taɓa faruwa ba Wallahi. saboda ko a lokacin mullkin mallaka ban taɓa jin irin wannan zalincin ba. Kallonta tamaida kan Yassar wanda ya kasance yaya ne a gurin Norr kuma shine wanda ya kawo mata wannan baƙin labarin Saboda a gaban idonsa kumai yafaru ba labari aka basa ba. Tace "Yassar ka tabbata Maganar da ka faɗa min gaskiya ce kuwa? saboda muddin na bin cika nagane ba gaskiya bane tohm fa kasani ranka sai yafi nawa ɓaci wllhy" Ta faɗa ba alamar wasa a tattare da ita. Cikin son tabbatar mata da gaskiyar Al'amarin Yassar "yace wllhy Mommy ba ƙarya nake faɗa miki ba, Har fa suma Ahanaf yayi agurin ɗaurin auren sakamakon jin da yayi an ɗaura auren Noor da Al ƙaseem. Nan fa Yassar ya kwashe duk abunda yafaru agurin ɗaurin auren ya faɗa mata cikin nutsuwa" Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raju'un ita ce Kalmar da Mommy tayi ta nanatawa, cikin kiɗima da tashin hankali Mommy ta nufi hanyar fita daga ɗakin. Cikin zafin nama Yassar ya Kama hannunta yace "Mommy Ina zakije haka? Dan Allah Kar kice zakiyi Wani Abu a cikin wannan Taron, saboda Hakan ba ƙaramar matsala zai jawo ba" Yassar ya fada cikin sigar rarrashi. "Yassar kasakar min hannu Idan ba so kake Na Ɓata Maka Rai ba yanzu" Mommy Dan Allah "ki tsaya kiyi tunani kafin ki yanke hukunci saboda yanke hukunci cikin fushi ba Abunda yake janyowa Sai nadama Mai matuƙar muni" Yassar yafaɗa cikin marairaice fuska. Wane hukunci Zan yanke Yassar? Ai Ni bani da abun cewa yanzu har Sai naji gaskiyar Magana agurin Dadyn Ku da Kuma dalilin yanke wannan danyen hukuncin" sannan nasan wane mataki yakamata Naɗauka. Sakin hannun nata yayi. Jiki ba ƙwari tabar ɗakin . Shima Yassar mara Mata baya yayi cike da jimamin wannan abun, Dan shi Allah yasani ba Wanda yake tausayi kamar Shadow. ganin halin da yashiga dazu yayi matuƙar daga Masa hankali sosai, Wane hali Norr zata Shiga Idan taji wannan abun? Gaskiya su Dady Basu kyauta ba kwata kwata. Ai da wannan abun da sukayi gwarama ace fasa ɗaura auren sukayi gabaki ɗaya zaifi sauƙi sosai akan wannan abun da suka aikata. Ko wannen su da Abunda yake tunani a ransa a haka har suka karasa part din Dady. Yassar yaja yatsaya yace "Mommy Dan Allah kibi komai a hankali, har muji menene dalilinsu Na aikata haka, "Duk abunda kwanciyar hankali beyi ba tohm fa tashin hankali ba Zai taɓa yinsa ba" To Insha Allah zansan ta yadda zan Ɓullowa lamarin, Zaka iya tafiya Allah yayi Maka Albarka. Ajiyar zuciya Yassar ya sauke tare da cewa ameen ya Allah, Nagode sosai Mommy. Juyawa Yassar ya Tafiyar sa. ita Kuma Mommy ta Shiga palon bakinta dauke da sallama, Dady ta hango tsaye agaban TV Yana kokarin canza channel. "sallamar da tayi ya amsa hankalinsa Yana Kan TV karasawa cikin palon tayi, ta zauna a Kan ɗaya daga cikin kujerun falon tare da cewa Ashe ma kana ciki ya gajiya. Alhmdllh ya amsa fuskar sa dauke da murmushi. Ya jama'ah dafatan kumai dai lafiya Ko? Ya tambaye ta cikin kulawa. Zamanta ta gayara tare da sauke ajiyar zuciya tace Ina fa lafiya Alhj? Yanzu nake Jin Abunda yafaru agurin ɗaurin aure Nan shine nace Bari nazo naji daga bakinka, saboda kasan ba a ɗaukar maganar Yara a haukai a zauna ba tare da ƙwaƙwaran bincike ba. Alhj Shin da gaske Abunda naji yafuru gaskiya ne Ko kuwa shatifaɗi ne? Ta kuwa yayi a hankali har ya Isa gurin da take zaune Shima ya zauna tare da Kama hannayenta yafara Magana, "Eh Abunda kikaji gaskiya ne ba shatifaɗi ba. mun ɗaura auren Al ƙaseem da Noriya Maimakon ita da Ahanaf" Gaban ta ne ya Faɗi sosai, Sai kuma ta danne cikin sanyin murya tace tohm Alh Ko Zan iya sanin dalilin haka? Murmushi yayi tare da murza hannayenta yace wannan ba hurumin ki bane ba Hjy. Ni yanzu Abunda nake so da ke shine kije kisami Noor ki Gaya Mata Abunda yake faruwa Kuma ki fahimtar da ita falalar yiwa iyaye biyayya akan duk Wani hukunci da suka yanke akan yaransu Idan har ba saɓon Allah bane. Cikin sauri ta kwace hannuwan ta a cikin nasa tace Wai da gaske kake kun daura auren Norr da Al kaseem? Kuma har kake tunanin ni naje nasami Norr Na faɗa Mata wannan maganar? Wllhy wannan abun bazai taɓa Saɓowa ba. Alh niba Zan faɗawa Norr wannan lamarin ba saboda Ina matukar sonta Kuma Ina son farin cikin ta sanin kan kane Norr Tana son Ahanaf Kuma so Bana Wasa ba, Har Takai Ga Bata iya Ɓoye wannan abun agurin kowa, Hatta Kai da kake mahaifin ta kasan haka. Batare da kayi tunanin halinda Ƴarka zata fada ba ka yanke wannan mummun hukuncin. Kuma abun baƙin cikin Wai bama fasaaura auren kukayi ba Sai kuka ɗaura da ƙanensa. Ina zakuje da hakkin Yaran Nan Alh? Ai Haihuwa ba hauka bace, bafa Dan kun haife su bane Zai baku Damar aikata duk Abunda kuka Ga dama a kansu ba. Allah da kansa a cikin Al Ƙur'ani Mai Girma Yana cewa ƴaƴayenku da matayenku ababen kiyone agareku, kuma zamu tambaye ko wannanne ku akan abinda muka baku kiyo. Kenan kaga Ko tsakanin iyaye da yaransu akwai hisabi ranar gobe ƙiyama. Alh "yakamata kuyi gaggawar canza wannan ba hagon tunanin naku tun kuna da sauran lokaci, saboda har yanzu kuna da Damar gyara kuskuren da kuka TAF KA tun lokaci Baiƙure muku ba. Ya'isa haka Dan Allah, Dady yafada tare da ɗaga Mata hannu, cikin matsancin fushi wanda tunda take Bata taɓa ganin yayi irinsa ba yace "Haj Ina Dai ce Norr ƴata ce Ko? Kuma Ina da hakki akan nasakata ko Kuma Na hanata, tohm Dan Allah Ina roƙonki da kija bakinki kiyi shiru akan wannan abun Kar ki tunzurani nayi Abunda bakya tunani" yafaɗa a hasale tare da ciro waya daga aljihunsa ya Danna Kira. Amaryar Shadow wannan wanka haka kin ganki kuwa? Wallahi kamar mutum ya saceki ya gudu dake tsabar kyau "cewar Meenal datake ta faman yiwa Norr picture's "ni ce Nan zan turawa Shadow su saboda abani kyakyawan Goro taƙarisa maganar tana dariya. Murmushi Norr tayi tare da cewa kanki akeji Kuma, Ni Kam nagaji da wannan ɗauke ɗauken naki da yaƙi ƙarewa tun dazu kike Abu ɗaya Dan Allah kibarshi haka Mana, nasamu nakira my Shadow naji muryar sa Ko zanji sanyi a Rai.. ringtone ɗin wayar tane ya hanata ƙarasa maganar da ta fara. hannu tasa takarɓi wayar daga hannu Meenal, tare da cewa Ɗan Halak kamar kasan yanzu nake Shirin kiranka. My Dad💞 Sunan da taga Yana yawo a screen din wayar ta Kenan, laaaah Ashe ma bashi bane Dady ne, tafaɗa Tana Kara wayar a kunnenta bayan tayi picking. Tare da cewa Assalamu alaikum "Norr kizo yanzu Ina nemanki a part Dina" Kitt yakashe wayar cike da mamaki take bin wayar da kallo a ranta Kuma tana ƙissima tabbas ba lafiya ba. Tashi tsaye tayi jikinta ba ƙwari, tacewa su Meenal Dan Allah kujirani Ina zuwa yanzu. Murmushi meenal tayi tace "yarinyar Nan fa tafara hankali daga daura aure, tohm Ina ga ta tare Sai a Zama Saliha ko" Dariya suka Saka gabaki ɗayansu Suna tsokanar ta. Ita dai ko ƙala Bata samu damar cewa ba Sai ma ƙokarin barin ɗakin da take cikin sauri, Cox ta Matso taji wannan Kiran da Dady yake Mata, Tun da aka wayi safiyar yau take jin faɗuwar gaba. Amma data gayawa Meenal "Sai tace Mata ai haka ko wace yarinya takeji Idan za'a ɗaura aurenta" Hakan ne ma yasa ta ɗauki abun ba Komai ba. Amma a yanzu faɗuwar gaban nata Sai tsananta yake sosai. Cikin sassarfa ta Isa part din Dady, ta Danna Kanta cikin palon Kai tsaye bakinta ɗauke da sallama, Amma ga mamakinta daga Mommynta har Dadyn nata ba wanda ya amsa Mata sallamar da tayi. Ƙarasawa tayi gabansu ta zauna Kanta a ƙasa tace Dady Gani, Gyaran murya yayi tare gayara Zaman sa yace "Noriya Ina So ki buɗe kunnuwanki da kyau kiji Abunda Zan faɗa Miki, Kuma Bana son musu a cikin umarnin da Zan Miki yanzu kina Jina ko"? Cikin sanyin murya wacce take tattare da tsoro fargaba tsinkewar zuciya tace Insha Allah bazan bijirewa umarnin ka ba Dady muddin Dai beci Karo da umarnin Allah ba. Masha Allah Allah yayi Miki Albarka. Ameen ya Allah Dady.. Dama dalilin da yasa na kiraki shine Ina son na faɗa Miki cewa Na ɗaura auren ki da Al ƙaseem ba Ahanaf ba, Kuma da Shi nake ra'ayin ki zauna a matsayin mijinki Na har abada. Ina fatan kinji Mai nace? Wani firgitaccen ihu Norr ta zuba Wanda gabaki ɗaya falon Sai da ya karbi Amon muryar ta, ciki Wani irin fitinan ne kuka tace "Dan Allah Dady ka rufamin Asiri, karaba wannan auren wallahi ni Bana Son kowa Sai Yah Shadow Kuma bazan taɓa iya rayuwar aure da kowa ba Sai shi, Dan Allah Dady kaji tausayina ka warware wannan auren. Da Jan gwiwa ta karasa gurin da Mommynta take, "tace Mommy Dan Allah kitaimake ni kibawa Dady haƙuri ya warware wannan auren wallahi Bana Son ƙaseem Ni Duk Duniya Yah Shadow kaɗai nake so Kuma kunsan da Haka Mommy. Kamata Mommy tayi ta rugumeta tare da bubbuga bayanta a hankali tace "ki kwantar da hankali Noor indai Ina numfashi ba Wanda ya Isa yasaka ki a cikin kuncin rayuwa, bazan taɓa barin haka tafaru ba Sai Inda ƙafina yaƙare insha Allah. Murmushi Dady yayi yace "wannan Karon kuwa kin ɗauki Alƙawarin da yafi ƙarfin ki Haj dan wallahi ba wanda ya isa ya raba wannan auren indai ina Nunfashi Noriya bata da wani miji bayan ƙaseem" sosai vulome ɗin kukan Norr ya ƙaru har tana shiɗewa tsabar tashin hankali. Mukhtar wallahi idan har yarinya ta tamutu bazan taɓa ɗaga maka ƙafa ba, kasani zanyi shari'a da kai har ƙarshen raina, wannan ai zalunci ne. kamata yayi ku faɗi dalilinku nayin haka idan akwai ƙwaƙwaran dalili kaga sai kowa yasan halin da ake ciki amma ai wannan cin haƙƙin yayi yawa wallahi. ko kallon inda take Dady baiyi ba barre tasaka ran zai mata magana. Ƙwafa tayi tare da kama Norr ta miƙar da ita tsaye muje kinji ba yadda za'ayi nayi shiru akan wannan lamarin zansa abunyi insha Allah, tana riƙe da ita har suka ƙarasa sashen Mommyn, Duk wanda yagansu sai yatambayi lafiya kuwa? Mommy ce mai ƙoƙarin cewa ba kumi bata jin daɗi ne. Har bakin bed ta kaita ta zaunar da ita akai tace ki kwantar da hankalinki Norr bana son wannan kukan naki, kiyi haƙuri musamu mafita. Mommy Ahanaf Al ƙaseem haba haba Mommy dan Allah kitaimaka mun karki bar hakan ta faru wallahi bazan iya zama dashi amatsayin miji ba Norr ta faɗa tana fashewa da wani irin kuka wanda da kajishi komi rashin imaninka dole ka tausayawa mai yinsa. Runtse idanunta Mommy tayi tanajin zafin kukan da ƴar ta guda ɗaya tilo take rairaiwa, zaunawa tayi kusa da ita tare da janyota jikinta ta rungume ta tafara karanta mata Addu'ar Sanyaya zuciya tana tofa mata, taɗauki tsawon lokaci tana haka can saiji tayi Norr ɗin tafara sauke ajiyar zuciya alamar bacci ya ɗauke ta. Gyara mata kwanciya Mommy tayi tare da ɗaura mata kanta akan pillow, tana goge Mata hawayen da ke Kwance akan fuskar ta. Ta Jima tsaye akanta tana ƙare mata kallo cikin tausayawa. "wannan ranar agurin kowace amarya rana ce ta daban wace take ƙunshe da duk wani farin ciki wanda bazata manta dashi ba a tarihin rayuwar ta, amma sai gashi yazo da matuƙar saɓani agurin ƴar ta. jiki ba ƙwari tabar ɗakin cike da tausayin halinda Norr da Shadow suka tsinci kansu aciki. Gidan su Shadow Abunda yafaru yagama kewa lungu da saƙo na cikin gidan, saboda mazan da sukaje gurin ɗaurin aure, tuni Suka bawa matan su da iyayen su labarin abunda yafaru agurin ɗaurin auren, kowa sai tofa Albarkacin bakinsa yake. Maganar duniya bata taɓa ɓoyuwa😰😰😰 Shadow zaune agaban Ayiya ta tasa shi gaba akan dole sai ya karya, shikuma bayajin akwai abunda zai iya sakawa bakinsa koda kuwa ruwa ne, Ayiya tace nasani ba abunda yake maka daɗi yanzu amma dan Allah ka daure kaci wani abu ko hankali na zai kwanta, bazan iya jurar ganinka cikin wannan halin ba dan Allah kaci ko kaɗan ne ta faɗa tana share hawayen da suke zubowa daga idanunta. Cikin danne tashi damuwar yace zanci Ayiya dan Allah kidaina kuka, ki bani wallahi zanci ya faɗa yana goge mata hawayenda ya zubo mata, Abincin ta bashi ya buɗe bakinsa Ta saka masa, Ya mutsa fuska yayi kamar wanda yake tauna maɗaci haka yake tauna abincin yana ya motsa fuska kamar ƙaramin yaro. Haka taci gaba da bashi abincin yana haɗiyewa dakyar, Duk lokacin da ya janye kansa alamar ya ƙoshi sai ta ɓata fuska. bisa dole yake ƙara buɗe bakinsa ya karɓa a haka har ya ƙoshi. Mikewa yayi tsaye yace kamar kar naci abincin nan Ayiya sai nakejin wani irin bacci sosai, Tohm ka kwanta anan mana Ahanaf kaga part ɗinku mutane sunyi yawa ba lallaine kasamu yin baccin a can ba. tohm nagode sosai Ayiya Allah yaƙara miki lafiya da nisan kwana, Ameen ya Allah yaron kirki Allah yayi maka Albarka yayi maka maganin damuwar ka. Ameen ya rab my Ayiya, ya faɗa tare da cire rigar jikinsa, ya faɗa kan gadon ya kwanta, yana ƙoƙarin yayi Addu'ar bacci amma abun ya gagara, saboda wani irin matsananci bacci da yaziyar ce shi wanda tunda yake bai taɓa jin irinsa ba, cikin seconds ɗin da Basu wuce 15 ba bacci yayi awon gaba dashi. Bayan awa huɗu da faruwar haka Shadow ne yafarka daga baccin da ya ɗaukesa tare da kurma wani raza nanne ihu.............. Nabeela Binji ce💃💃💃 Nabeelah Shehu Binji 09064314811 Or 09161107610 More comment More taping 😉😉 Share Fisabilillah 🙏 ♣️DUHUN INUWA ♣️ TAPING......📲📲📲 STORY AND WRITING✍️✍️✍️ BY NABEELAH SHEHU BINJI PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞 ```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)``` /https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/                   *P.W.A✍️* BISMILLAHHIR_RAHAMANIR_RAHIM Page 0️⃣4️⃣ Bayan awa huɗu da faruwar haka Shadow ne yafarka daga baccin da ya ɗaukesa tare da kurma wani raza nanne ihu.............. Yana ƙoƙarin saukowa daga kan bed Sai cewa yake Wallhi sai na kasheku ni zaku ciwa Amana dukan ku nine Nan ajalinku....... Ayiya ce tafito daga toilet cikin sauri Wanda yanzu Nan tashiga Domin ta ɗauro Alwalar sallar magrib. Kai tsaye gurin da Shadow yake tanufa cikin tashin hankali tace Ahanaf lafiya kake kuwa? su waye Kuma Zaka kashe? Tafada Tana kokarin rike Masa hannaye, tureta Shadow yayi da karfi tayi baya zata Fadi ƙasa, cikin sauri Al ƙaseem Wanda shigowar Kenan yanzu ɗakin ya tareta tafaɗa jikinsa. Ɗagowa yayi ya kalli Shadow yace Yaya kana cikin hankalinka kuwa? Ayiyar ce kake ture.. kafin ya rufe bakinsa tuni Shadow ya kamo wuyansa ya shaƙesa sosai, Nan take idanun Al ƙaseem suka firfito waje saboda tsabar shaƙar da yasha, cikin ƙaraji Shadow yace wallahi nine Ajalinka ƙaseem ni zaka ciwa amana ka aurar min mata? tohm wllhy daga kai har ita sai na KASHEKU yafaɗa cikin ƙaraji. Hunnu Ayiya ta ɗaura akai tare da fashewa da kuka tace dan Allah Ahanaf kasarmin yarona karka kashe shi, Ahanaf kodai kasamu taɓuwar hankali ne? nashiga ukku. Ayiya tayi iya ƙoƙarinta don ganin ta ƙwaci ƙaseem amma abun yaci tura, hakan ne yasa tafito ɗakin da gudu dan ta samo wanda zai ƙwaci Ƙaseem daga hannun Shadow. Tun daga nesa ta hango Haidar da Kamal zaune suna alwalar magrib tafara kwala musu kira, da sauri suka nufu inda take suna tambayarta lafiya kuwa? Ina lafiya Kamal ga Ahanaf can ɗakina yana ƙoƙarin kashe Ƙaseem. Ai basuma tsaya jin ƙarin bayani ba suka nufi ɗakin nata da gudu, koda suka shiga Shadow sai faman dukan ƙaseem yake yana surutai, da sauri suka riƙesa amma saida ya kufce musu yaƙara ko mawa kan ƙaseem da niyar ya ƙara shaƙarsa, sake cafko shi sukayi suka riƙesa sosai, Haidar yace wai bakada hankali ne Shadow me kake ƙoƙarinyi ne haka? Haidar yafaɗa cike da mamakin abokin nasa da tun zamansa dashi bai taɓa ganin faɗan saba sai yau. Ku sakeni wallah saina kashe shi daga shi har Norr ɗin yafaɗa yana ƙoƙarin kwacewa daga riƙon da suka masa, amma kuma yakasa Kwacewar saboda ba riƙon wasa suka masa ba. Shadow ka kwantar da hankalinka dan Allah wannan fa ba laifin Ƙaseem bane laifin su Abba ne (novel ɗin iyan Nabeelah 😜) sune suka tabka wannan kuskuren baruwan Ƙaseem aciki, hasalima baya sonta, kanaji fa agabanka yace shi sakinta zai.. Adaba Al Ƙaseem ya katse Haidar yana gyara tsayuwar sa tare da cewa wallahi yanzu ba wanda ya isa ya shiga tsakanina da Norr saboda ita ɗin matata ce ina sonta kuma bazan saketa ba. Kamal da Haidar tsabar mamaki basu san lokacin da suka saki Shadow ba, ai kuwa dama abunda yakeso kenan cikin zafin nama Shadow yasake cakumo Ƙaseem tare da buga kansa da bango, Wani irin kuka Ayiya ta saka tare da cewa dan Allah Haidar kuriƙesa mana kuna fa gani zaiyi kisan kai. Sunyi iya yinsu amma sun kasa ƙwatar Ƙaseem daga hannu Shadow "sai faman buga kansa yake da bango yana furta cewa sai ya kasheshi" Sai da kyar sukayi nasarar kwace Ƙaseem ɗin suka reƙe Shadow sai buge buge yake asake shi yaje ya ƙarasa Ƙaseem ɗin ko zai samu nutsuwa, wannan karon riƙon kwarai sukayi masa wanda yakasa kuɓucewa daga hannunsu. Da sauri Ayiya tayi kan Ƙaseem wanda gabaki ɗaya jini ya gama wanke masa fuska tana girgizashi, dan Allah katashi kar ka mutu Ƙaseem. "Ki zuba masa ruwa Ayiya ko zai farka sai ki kira Dr yazo ya duba shi ayi Masa dressing" Mu kuma Bari muje da Shadow part ɗinsu musan abunyi dan bai kamata abarsu a nan tare ba saboda kumi zai iya faruwa. Da kyar suka fitar da Shadow daga part ɗin Ayiya, sai faman turjewa yake shifa ba inda zaije sai sun barshi ya kashe Ƙaseem, Suna zuwa part Ɗin nasu direct bed room suka kaishi, Suna Shiga suka sake Shi tare da farayi masa fada. bayama sauraron Abunda suke faɗa, Sai suratansa yake marasa Kan gado. Kallon Juna sukayi cike da mamakin wannan abun da Shadow ya keyi kamar Wani taɓaɓe, kafin su Ankara tuni Shadow yayi hanyar fita da gudu, Dafa masa baya sukayi Sai Palo suka samu nasarar Kama Shi, suka sake mai dashi bed room din. Haidar ne yabada shawarar su kulle Shi a ɗakin, Idan ba haka ba kumai zai iya faruwa, haka kuwa suka kulle Shadow a ɗakin suka tafi masallaci Bayan sungama sallah suka dawo gidan, tundaga Palo suke jiyo ƙarar fashewar abubuwa, da sauri suka karasa dakin Suna budewa su kaci Karo da ɓarnar da Shadow yayi a ɗakin duk Wani Abunda ya danganci glass saida Shadow ya fashi, Ko Ina kwalba ce zube a ƙasa. Subhanallah Kamal inaga fa kamar taɓin hankali Shadow ya samu, saboda wannan abun yafara wuce mizani, yakamata aɗauki mataki tun kafin abun yaci Tura cewar Haidar idanunsa fall hawaye. Gaskiya Kam yakamata iyayen sa Susan halinda Ɗan nasu yake ciki. katsaya anan tare dashi ni Bara naje nakira Ayiya tazo cewar Kamal Yana fita daga ɗakin cikin sauri. Haidar baima sami damar ba Kamal amsa ba. Sai ma Maida hankalinsa da yayi akan Shadow, Wanda yanzu kayan zanensa ne yaɗauko yanata faman Zane a Bangon ɗakin, Yana surutai. Jikin ƙofa Haidar ya jingina hawaye Sai zarya suke akan fuskarsa Na matsancin tausayin Shadow, saboda yagama ƙissimawa aransa cewa tabbas taɓuwar kwakwalwa abokin nasa ya samu. Allah wadan iyaye masu irin wannan halin Na jefa yaransu cikin masifa akan Wani dalili Nasu Na banza. Anya ma kuwa da gaske su suka haifi Shadow? Haidar yayi ma kansa wannan tambayar da bashida mai bashi amsar ta. Saboda Shi a iya sanin sa da Shadow Muhammad Imran Abba shine mahaifinsa, kuma su biyu ne Kawai yaran sa shida ƙanensa Ƙaseem. Amma izuwa yanzu yafara shakka akan wannan lamarin. Tsayuwar sa ya gyara afili ya furta tabbas akwai wata sarƙaƙiya a ƙasa. ________________ Idanunta tafara buɗewa a hankali har tagama buɗesu tas akan fuskar Meenal, wace take zaune a gefen gado tana facing ɗinta, ta buga uban tagumi tazubawa ƙawar Tata IDO cike da tausayawa. "saboda Mommy ta sanar da ita duk Abunda yake faruwa" Meenal taci kuka har ta godewa Allah. Amma ga mamakin ta Sai Gani tayi Norr Na mata murmushi. Tashi tayi ta zauna tare da cewa Hi Madam wannan kallon fa? Ni Dan Allah Karki cinyeni, Ta faɗa Tana kai hannuna kan fuskar Meenal kamar zata tsone mata idon din cikin Wasa. Kauda Kanta Meenal tayi gefe cikin Al ajabi, tace Norr kina lafiya kuwa Ko kin manta ƙalubalen da ke gabanki ne? daura auren ki fa akayi da Ƙaseem Mai makon Shadow? Amma Naga kamar baki damu ba? Yamutsa fuska Norr tayi tace eh Ina sane Mana, Dady ya gaya min Kuma yace yanaso nayi Masa biyayya, wannan dalilin yasa ma kikaga nasaki Raina, Zan zauna da Dashi Meenal ai dukansu Abu ɗayane, Amma tunda har Dady ya yanke hukunci tohm tabbas banida Ja akan wannan lamarin Norr takarisa maganar tana murmushi. Tirkashi Abunda Mommy tasamu damar furtawa Kenan, Dan duk taji bayanin da Yar Tata tayi yanzu. Ita Meenal Suman zaune ma tayi saboda Takasa cewa Kala Sai bin Norr take da Ido kamar wata sokuwa. Kosa da ita Mommy ta zauna ta rungumeta ajikinta tana bubbuga bayanta a hankali tace Norr kinutsu kidawo cikin hankalinki Kisan Abunda bakinki yake furtawa, cewa fa kikayi kin Aminta da auren kaseem? Wanda dazu da dadinki yafadi haka ihun Kika dinga zunduma wa kina bakison auren, Kuma Nima nasan bakison sa, Amma Mai yasa yanzu daga tashinki faga bacci kice Wai kin amince kamar wata Mai Anjanu? Tohm Mommy ya kikeso nayi kefa da be kike cewa Nabi duk Abunda Dady ya umarce ni akai, yanzu Dan kawai Nabi umarnin nasa Sai kuma abun yazama laifi? Nifa Mommy banida JA akan maganar Dady, Kuma yanzu naji duk Duniya ba Wanda nake so sama da kaseem. Kuma Zan zauna dashi a matsayin mijina Kamar yadda Dady yace insha Allah. Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raju'un shine Abunda Meenal ta fada cikin tsantsar mamaki da tashin hankali saboda tasan wannan abun bana lafiya bane. Taya Norr Zata yadda da auren Wani akanta ba Shadow ba? A da Idan ka kwatanta fadar haka tohm fa Norr Bata da makiyin daya wuce Kai, kullum maganar shine Idan munyi aure da Yaya Shadow zanyi kaza zanyi kaza, ba Wanda zaiyi Zaman 30min tare da Norr baisan Shadow ba saboda yawan maganar sa datakeyi ako Ina Idan tazauna. Amma babban abun Al ajabin sai yau data kasance ranar daurin aurenta da Shadow dinta, aka fasa auren dashi aka daura da kanensa, Kuma har ta iya cewa ta yadda zata zauna dashi Tana son sa. Tabbas wannan abun ba lafiya ba. Ita ma Mommy Kanta ne yaɗauki zafi harma tarasa abun cewa Sai bin Norr din da Ido take wacce ita sabgogin gabanta mantake tana kokarin Shiga toilet. _________ Kanada hankali kuwa ƙaseem Norr ɗin ce Zaka bude baki kace kana so agaban Ahanaf? Ai Wallhi banyi tunanin hakan daga gareka ba Ko kaɗan. Gyara zama ƙaseem yayi tare da dafe kansa da yake Masa matsancin ciwo gashi Kuma yasha naɗi da bandage duk Wani iri yake jinsa. Yafara Magana cikin zafin ciwon da yakeji, yace Wallhi Ayiya tunda ɗazu da wani irin bacci ya ɗauke ni Wanda tunda nake Duniya Ban taɓa Jin irin sa ba shine fa Ina farkawa daga baccin, naji duk Duniyar Nan ba wacce nake so sama da Norr, Kuma da ita kaɗai nake ra'ayin Zama a matsayin Mata. duk Wanda yace zai rabani da ita tohm fa tabbas Sai Idan ba raina Ayiya............✍️✍️✍️ TIRKASHI 🙆🙆🙆 WAI MAI YAKE FARUWA NE? WANANAN WANE KALAR BACCI NE? TABBAS AKWAI WATA A KASA KOWAYE YAKE SHIYAR WANNAN MAKARKASHIYAR? Masu cewa sun matsu suji menene dalilin su Abba, tohm Dan Allah kuyi haƙuri Kuma kudaina ganin laifinsu plzz😥😥 Kudai Kawai ku ƙara haƙuri tabbas zakusha mamakin wannan lamarin 😭😭 Dan Allah kuyi haƙuri da Taping erro fita nayi yau hankalina baya kwance 🙏🙏🙏 Nabeela Binji ce💃💃💃 Nabeelah Shehu Binji 09064314811 Or 09161107610 More comment More taping 😉😉 Share Fisabilillah 🙏 ♣️DUHUN INUWA ♣️ TAPING......📲📲📲 STORY AND WRITING✍️✍️✍️ BY NABEELAH SHEHU BINJI PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞 ```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)``` /https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/                   *P.W.A✍️* BISMILLAHHIR_RAHAMANIR_RAHIM Page 0️⃣5️⃣ Saukar Wani firgitaccen Mari Al Ƙaseem yaji akan kumatun Wanda yayi sanadiyan Ƙaruwar ciwon kansa, cikin tsantsar masifa Ayiya tace "kana da hankali kuwa Ƙaseem kasan Mai bakin ka yake furtawa? Norr Ɗin ce Kuma kake so yanzu? Tabbas ba lafiya kake ba, yakamata ka dawo cikin nutsuwar ka kasan Mai yake fita daga bakin ka kaseem, Norr fa?" Ni Ina cikin hankalina Ayiya, Kuma nasan Abunda nake faɗa, menene Abu marar kyau anan Norr Dai Matata ce Kuma Ina da damar furta cewa Ina son ta, saboda haka Zan Koma faɗar cewa Ina son No.. hannu Ayiya ta ɗaga da nufin sake Zabga Masa Wani Marin Sai ji tayi an riƙe Mata hannu ta Baya, juyowar da zatayi sukayi Ido huɗu da Kamal. Cikin tashin hankali Ayiya tace Kamal Kanafa jin Abunda kaseem yake faɗa. Anya wannan Abun bawata kullalliya aciki kuwa? Bawata kullalliya Haj Shuwa saidai Idan kece Zaki kullata a yanzu, cewar Abba da yake ƙoƙarin shigowa cikin ɗakin, fuskar sa ba alamar Wasa yace "kifita daga idona Na rufe Shuwa, zamanki lafiya da kwanciyar hankalinki agidan nan shine ki daina kalubalantar wannan auren saboda akan wannan auren Zan iya samun matsala da kowa Wallahi" Abba ya faɗa Rai a ɓace. Kallonsa ya mai da Kan Ƙaseem Wanda yake tsaye a gefe ya rasa Abunda yake Masa daɗi a wannan rayuwar, shidai yanzu ba wacce yake burin Gani sama da Norr, sonta ne yake azalzalar zuciyar sa. Maganar Abba ce tadawo dashi cikin hankalinsa inda yake cewa, subhanallah Ƙaseem Mai yaji Maka ciwo haka? Ko kayi accident ne? Abba ya tambyi Ƙaseem hankali a tashe saboda ba Ƙaramin ciwo yaji ba. Kai kaseem ya girgiza alamar a'a ko ɗaya sannan yabuɗe baki da kyar yace Abba Yaya Shadow ne ya dakeni. Duka fa Abba ya tambaya cike da masifa, Kai jakine da zai dakeka haka? Ah lallai wannan Yaron Dani yake zance, ai bakai yakamata yasamu yadaka ba, Ni yakamata yadaka Nida Na ɗaura auren. Ina Ahanaf ɗin yake yatambaya cikin faɗa. Gyaran murya Kamal yayi cikin girmamawa yace Yana ɗaki Abba, Kuma gaskiya Ina tunanin Kamar bashida lafiya saboda Yana can Sai faman farfasa Kaya yake a part ɗinsu Kamar Wani Wanda yasami taɓuwar hankali, shine nace Ko zakuzo muje kuga halinda yake ci... Dan Allah da kata Abba ya faɗa Rai a ɓace, ba Wani taɓuwar hankali da yasamu tsabar rainin hankali ne da yayi Masa yawa. Kuma tinda Har Ahanaf ya nuna ban Isa dashi ba kuma ban isa nasaka doka yabita ba, tohm kusani daga yau ba ruwana da lamarin rayuwar sa yaje yayi duk Abunda yake ga yafi Masa a rayuwa Abba ya faɗa cikin sound Na gaskiya da gaskiya. Kamal da Ayiya mutuwar tsaye sukayi saboda tsabar mamakin wannan lamarin Na Abba. Janyo Ƙaseem Abba yayi kusa dashi tare da cewa Allah yayi Maka Albarka Ƙaseem naji daɗi sosai Kuma nagode da kamun biyayya akan Abunda Na umarce ka. Ita ma Kanta matar taka ta amince da kai a matsayin mijinta, ɗazu mahaifinta ya kirani a waya yake gayamin, kaga yanzu Sai kaje kayi duk Wani Shiri da zakayi katafi gidanka saboda natura motocin ɗaukar amarya tun ɗazu. Cike da matsancin farin ciki Ƙaseem ya rungume Abba Yana dariyar murna yace nagode sosai Abba Allah yasaka Maka da mafificin Al khairi, Amma Abba wane gida za'a kaita. Gidan da wancan shashan Yaron yagina Mana Ƙaseem, ai tinda daman dan ita Norr ɗin aka Gina Shi tohm shakka Babu a ciki zata zauna. Wallahi wannan Kam ƙarya ne Alh ai wannan Zalunci yayi yawa da wanne zaiji? "Budurwarsa, Sadakinsa, gidansa? Bazan bar haka tafaru ba Alh Yaron Nan fa Shima ɗanka ne Kuma jininka, ko menene ya aikata Maka Bai cancanci wannan mummunan hukuncin daga gareka ba" Idan ma ka Hana Shi auren yarinyar Nan kamata yayi kabar Masa duk Wani Abu da yake mallakinsa. Bazanyi haka ba Shuwa, "ba fa kece Mai mulkina ba nine Nan nake mulkinki, Ni nakeda hakki akan ki Dama yaran naki gabaki daya Dan haka Na gama yanke hukunci Akan kaseem zai tare a gidan da Ahanaf ya Gina saboda ana iyayen yarinyar suka Saka kayan Yar su, kinga Kuwa ba Inda yakamata su zauna sama da can. Bazan musamaka ba Alh saboda nasan Kaine mahaifin Ahanaf Kuma Kaine mahaifin Al kaseem, Amma Abunda nake so kasani shine bazan zauna Nan gidan ba, Zan bar Maka gidan ka, Kuma Zan tafi da Ahanaf gidanmu Naci gaba da kulawa dashi acan Amma alfarma daya nake rokonka shine kamanta damu arayuwarka Dan Allah tafada tana hada hannayenta guri daya alamar roko hawaye Sai zarya suke akan kumatun ta. Ba Inda zakije Shuwa kina gidan nan Insha Allah, Amma Shi duk gurin da zaije yaje Bani da matsala da haka, ya faɗa cikin nuna halin Ko in kula Akan Ɗan nasa, Wanda ada yake mutuwar so da kauna saboda shine ɗansa Na farko aduniya. Wannan Kuma kayi kaɗan Muhammad dole nabar Maka gdnka tunda ka nuna Ni ban isan nasan Abunda kake shiryawa ba, ban Isa nasan dalilin wannan hukuncin da ka yanke ba, tohm menene an fanina agurinka ai kaga gwara Kawai natafi. Abba yarasa abinda yasa Aduk lokacin da Haj Shuwa ta furta cewa zata tafi ta bar Masa gidansa Sai yaji Wani matsancin ɓacin Rai da fargaba sun dirar masa a zuciya. Ba Inda zakije Shuwa cewar Abba, wallahi muddin Kika fita daga gidan Nan to fa kisani bakin aurenki. Yana gama Faɗin haka yaja hannu Al ƙaseem suka bar ɗakin cikin sauri Kamar wa ƴanda zasu Tashi Sama. Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raju'un ita ce Kalmar da Kamal keta nanatawa, cikin tashin hankali da Al ajabin wannan lamarin shidai tinda yake arayuwa Bai taɓa Jin makamancin wannan abun ba, Ko a film Ko a novel Amma a yanzu ga abun yana faruwa agabansa Yana kallo. Gurin Ayiya Kamal ya ƙarasa Kamar Wanda kwai yafashewa a ciki, tare da Kama hannayenta ya zaunar da ita a gefen gado yace ki daina wannan kukan Dan Allah Ayiya, kuka fa bashine mafita ba a wannan halin, Kawai Neman mafita shine Abunda ya kamata muyi, Yanzu kitashi mutafi gurin Ahanaf ɗin kiga halinda yake ciki saboda lamarin Sana Sai ƙara ta'azzara yake. Bazan iya ba Kamal bazan iya kallon Ahanaf acikin halinda bazan iya taimakonsa ba Kawai kuje kuyi Masa Abunda yadace, Idan ma asibiti zaku Kaisa kukai sa Dan Allah Kamal. Cike da mamaki Kamal yake kallonta duk da yaga Kamar da ya nayin tausayawa a fuskar ta tayi maganar, Amma Bai kamata tace Wai bazata iya Zuwa taga a wane hali Ɗan nata yake ciki ba. Har zai buɗe baki yayi Magana kome yatuna Sai kuma ya rufe bakinsa, tare da Tashi yabar ɗakin ransa bace. Tabbas wannan jarabawar bama tabuwar hankali yakama a ce Shadow ya samu ba, kamata ma yayi ya mutu Ko zai Sami salama a rayuwa, haba wannan Bala'in Har Ina cewar Kamal hawaye nabin fuskar sa. Koda ya Koma ɗakin a yadda ya barsu a haka yasame su, Shadow Sai zuba zanensa yake a Bango, Kuma babban abun mamakin shine duk da Baya cikin hankalinsa zanensa yake Kamar yadda yasaba, cikin kwarewa irin ta kwararren Ɗan Zane. Kamal ya kalli Haidar yace Dan Allah ɗan zo Kaji, ba musu Haidar yabi Bayan Kamal tare da rufe k Ƙofar gudun Kar Shadow ya fito. Bayan sun dawo Palo ne sun zauna Kamal ya kwashe duk Abunda yafaru Bayan fitar sa daga dakin da sunan Kiran Ayiya ya fadawa Haidar. Tirkashi shine Abunda Haidar yasami damar furtawa Yana goge zufan da ya zubo daga goshin sa, Sun dauki lokaci Mai tsawo ba Wanda ya iya cewa Kala a cikin su, kowa da tunanin da yake a cikin zuciyar sa. Haidar ne ya dago ya kalli Kamal yace Kamal yanzu ya zamuyi Dan ganin mun taimaki Shadow? Nima tunanin da nake Kenan Haidar Amma duk iya tunanina nakasa samu Mana mafita. Dukan su shiru sukayi Suna tunani. Sai can Kamal ya dago ya kalli Haidar yace Na samu mana mafita Haidar Ciki zakuwa Haidar yace Mai Cece mafitar Kamal? Gayara Zama Kamal yayi tare da cewa Abbu, tabbas Abbu Shi kaɗai ne mafitar mu,. saboda nasan duk Wanda Abun da yake faruwa bashida masaniya Akai Shi Kawai yakamata mukira mugaya Masa Abunda yake faruwa Insha Allah Shadow zai Sami a dalci.........✍️✍️✍️ Wane ne Abbu? Shin waye Abbu agurin shadow? Kuma wane matsayi yake dashi agurin Abba da Har su Kamal suke tunanin Kai ƙarar Abba agurinsa? Kuma Idan sun Kai Masa ƙarar zasu samu Abunda suke so? Nabeela Binji ce💃💃💃 Nabeelah Shehu Binji 09064314811 Or 09161107610 More comment More taping 😉😉 Share Fisabilillah 🙏 ♣️DUHUN INUWA ♣️ TAPING......📲📲📲 STORY AND WRITING✍️✍️✍️ BY NABEELAH SHEHU BINJI PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞 ```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)``` /https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/                   *P.W.A✍️* BISMILLAHHIR_RAHAMANIR_RAHIM Page 0️⃣6️⃣ ________________Haidar ne ya ciro wayar Shadow daga cikin aljihunsa yace bara mugwada Kira muga Ko zata Shiga. Cikin Sa'a wayar tafara ringing shiru sukayi Suna jiran ya ɗauka, Amma har ta tsinke ba'a ɗauka ba sake Danna Kiran Haidar yayi Sai da suka Kira sau ukku kafin suji an ɗaga tare da sallama, Amsa sallamar Haidar yayi tare da gaida Shi, Amsa gaisuwar Abbu yayi tare da cewa Yan samari lafiya Dai Ina Ahanaf? Gyaran murya Haidar yayi sannan yace gaskiya Dai Kam ba lafiya ba Abbu, saboda........ Nan Haidar ya gayawa Abbu duk Abunda yake faruwa. Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raju'un Abbu ya faɗa cikin tashin hankali, ruɗu da Kuma Al ajabi. Abbu Yace yaro ka tabbar Abunda kake faɗamin gaskiya ne Kuwa? Wallahi gaskiya Na faɗa Maka Abbu, Ai wannan lamarin yafi ƙarfin ayi Wasa da Shi, yanzu ma haka maganar da nake Maka shine an kai Norr agidan da Ahanaf ya Gina, a matsayin matar ƙaseem. Haidar yafaɗa cikin ƙunar Rai. Subhanallah Lallai shigowa Nigeria ya Kamani gobe, zanzo insha Allah naji menene dalilin da yasa Muhammad ya yanke wannan mummun hukuncin, tabbas Idan har Bai gayamin dalili ba Toh wallahi ransa Sai yafi nakowa ɓaci. Sosai Haidar yaji daɗin furucin Abbu, Allah yakawo ka lafiya Abbu Haidar yafaɗa Yana ɗan murmushi saboda yasan Insha Allah Shadow zai Sami ƴan cin kansa. Ameen ya Allah yaro ya sunanka? Abbu ya tambayi Haidar. Haidar ne Sunana Abbu, Masha Allah Allah yayi Maka Albarka Haidar, Dan Allah kaciga da Kula da abokin Naka insha Allah gobe Zan zo. Tohm Insha Allah Abbu Allah Dai ya kawoka lafiya. Ameen ya Allah cewar Abbu Yana kashe wayar. Haidar ya kalli kamal cikin sakin fuska yace insha Allah kumai zai Zama tarihi abokina. Murmushi Kamal yayi yace Allah ya yadda Boss, Ameen ya Allah. Ɓangaren Abbu Kuwa yakasa koma wa bacci Sai Safa da Marwa yake Yana tunanin wannan lamarin, tabbas yasan Irrin son da Muhammad yakewa Ahanaf, baya Son Wani Abu ya same Shi ko kaɗan, harma Takai ga baya iya ɓoye son da yakeyi masa agaban Koma waye. Iska Mai zafi ya furzar Tabbas ba banza ba Abbu yafurta a Zahiri. Kai da waye Kuma cikin wannan tsohon Daren? Cewar Hajiya Mama wacce ta kasance Mata agurin Abbu. kusa da ita yaje ya zauna Yana dafe kansa yace Haj Ina ga gobe zamuje gida Nigeria, Nigeria Kuma tafaɗa cike da mamakin sa, saboda ita dai tasan ba yadda batayi dashi ba Akan yabarsu su tafi bikin Ahanaf ita da Yara, Amma Sai yace a'a tinda Shima Bai samu zuwa ba to ba Wanda zaije, dalilin da yasa yace haka kuwa shine saura kwana biyar ya su Koma gida Nigeria gabaki daya, a cewar sa Idan sunje Sai suga amaryar. Amma Kuma shine yanzu yake cewa zaije Nigeria gobe. Mai yafaru Mai zai kaika Nigeria Kuma? Bayan Nan aka Ɗaura auren ɗan ka Ahanaf bakaje ba Kuma muma baka barmu munje ba, sannan yanzu kace zakaje akan Wani aikin gabanka? Kasani fa Abunda kake Babu kyautawa a ciki Ko kadan Abbu, cewar Hajiya Mama wace da alama Dama acike take dashi. Ɗagowa yayi da idanunsa waƴan da sukayi Ja tsabar ɓacin Rai ya zuba su Akan fuskarta Yana kallonta. Cikin sauri tace subhanallah Mai yafaru ne Abbu Mai yasameka Wani Abu yafaru ne? Saboda tasan muddin taganshi a cikin wannan yanayin tohm tabbas tasan ba lafiya ba. Numfashi Abbu ya furzar tare da cewa tabbas nayi nadamar Rashin zuwa wannan ɗaurin auren Hajiya, Ni kaina Na Rasa dalilin haka. Haka Kawai naji bazan iya zuwa ba, wannan dalilin yasa Kuma Na Hana Ku zuwa, Nan Abbu ya faɗama Hajiya Mama duk Abunda Haidar ya faɗa Masa. Ai Ko kafin yagama Bata labarin Tasha kuka Na fitar hankali. Cikin kuka tace tabbas yazama dole muje Nigeria gobe Abbu, saboda muceto rayuwar Ahanaf. Anya Kuwa Muhammad Yana cikin hankalinsa? Nima Abunda nake tunani Kenan Hajiya, Amma Koma Menene gobe zamu tabbatar insha Allah. ____________ Ƙaseem ne zaune agaban Abba da kunburarriyar fuskar sa, Yana sauraren wa'azin da yake Masa Akan Zama da Mata. bayan yagama ne yace tohm Ƙaseem Zaka iya Tafiya, driver Yana waje Yana jiranka, Allah yayi Maka Albarka yabaku zuri'a Ɗayya ba. Ameen ya Allah Nagode sosai Abba, bara naje nayiwa Ayiya sallama Sai natafi. Kar ka fara Ƙaseem Ayiyar taka data nuna Bata son wannan auren, Kawai kai dai kayi Abunda nace Maka cewar Abba, Tohm insha Allah Abba, Ƙaseem yafaɗa Yana barin ɗakin cikin sauri, saboda yanzu ba Abunda yake da muradi Sama da ganin Norr a gabansa, saboda matsanancin sonta yakeji a cikin zuciyar sa. Yana fitowa harabar gida direct gurin Motar da yango haske a cikin ta yanufa, Yana zuwa ya buɗe Motar yashiga tare da cewa driver'n muje. Tafe suke a hanya Amma Kaseem Gani yake Kamar ba Tafiya ake ba, ɗan tsaki yayi tare da cewa Dan Allah mlm kayi sauri Mana, Idan Kuma ba Zaka iya bane ka Bani motor Ni Sai na toƙa da kaina. Kayi hakuri dan Allah oga cewar drivern tare da karawa Motar gudu. Suna karasawa cikin gidan Ƙaseem ya buɗe murfin motar ya fita Yana zuba sauri Kamar zai tashi Sama, Audu driver ne yabi bayansa cikin sauri yace oga gashi Wai inji Alh yace a Baka, karɓar ledar Ƙaseem yayi ya Tafi Abunsa ba tare da yayi wa Audu Magana ba. ________Zaune take Akan gado Sai uban murmushi take zubawa. Sallama yayi yana Tura ƙofar ɗakin yashiga, fuskar sa dauke da murmushi, Gefen gadon yazauna Yana ƙare Mata kallo farin ciki fall zuciyar sa. Gyaran murya yayi tare da cewa Amarya bakya laifi Koda kin kashe ɗan masu gida, murmushi tayi batare da tayi Magana ba. Norr ba Magana ne? Ƙaseem ya tambaye ta cike da Nishadi. A hankali tace Ina wuni Yah Ƙaseem. Murmushi yayi yace Bana so Sai da Na roƙa ko? Please sorry Yah Ƙaseem ta faɗa cikin shagwaɓa. Matsawa yayi gurin da take zaune ya saka hannunsa ya yane gyalen da Ke a Kanta. tozali yayi da kyakyawar fuskarta wace tayi fayau ba Ko dingon kwalliya Akanta. Murmushi ya sakar Mata tare da cewa Ina godiya a gareka Allah da ka mallakamin wannan kyakyawar yarinya cikin sauƙi. Ita ma murmushin tayi tare da Saka hannayenta ta rufe fuskarta alamar kunya. _______________ Ya kamata fa muyi sallar Isha'i mu kwanta saboda wallahi bacci nake ji, cewar Kamal. Eh Hakan yakamata gaskiya saboda kaga yanzu mun samu mafita. Bayan sun dawo daga gurin sallar ne suka zube a falo, Haidar Akan Capet shikuma Kamal Akan doguwar kujera, Fira suke Sama Sama Har bacci ya ɗauke su. Da asuba da suka farka daga bacci, ɗaya daga cikin ɗakunan suka Shiga suka ɗauro alwala. Basu Shiga ɗakin da Shadow yake ba gudun Kar su makara gurin Tara Tara dashi Kuma gashi Har sunji an tada Sallah. Bayan sun dawo daga masallaci ne suka ci Karo da Abba agurin Shiga gida, murya adakile Kamal ya gaida Shi, Haidar kam yi yayi Kamar Bai ganshi ba saboda mugun haushinsa yakeji. Shima Abba haka yayi Kamar Bai Gansu ba Dan Ko gaisuwar da Kamal yayi Masa sarai yaji Shi, Kawai Dai yaƙi amsa Masa ne, Saboda Shi yanzu duk Wani Abu da ya dan ganci Ahanaf bayama son yayi tozali da Shi, saboda yaji haushin musa Masa da Ahanaf yayi a cewar sa. Bayan sun Shiga falon Kai tsaye ɗakin da Shadow yake ciki suka nufa, Haidar yasaka hannunsa a cikin aljihu yaciro key din dakin ya bude, Suka Shiga ciki Amma me wayam suka Gani ba Shadow ba alamar sa. Tohm Ina yashiga Kuma cewar Kamal Yana kwala Masa Kira Shadow Shadow Shadoww! Amma shiru Bama alamar mutum a ɗakin. Cike da mamaki suka hau neman sa ba Inda Basu Duba ba Har cikin toilet, Abu Wasa Wasa Yana so yazama gaske, Dan su Kamal ba Inda Basu Duba ba Amma basu ga Shadow ba. tirkashi Abunda Haidar yasamu damar faɗa Kenan cike da mamaki. Yace Shadow Dai ba aljani bane balle ya ɓace, Kuma ba tsontsu bane balle ya fira. Tohm ta ina yafita Kenan? Tambaya ce da basuda Mai amsa musu ita a halin yanzu. Wani kyallen ƙofa Haidar ya buɗe, Ƙofa yagani cikin sauri ya Tura ta Kawai Sai Gani yayi ta bude, kofar yabi Kamal ya bishi, Sai ganin kansu sukayi ta bayan gida gurin Garden. Kalle Kalle suka fara yi agurin Suna Neman Shadow, Amma ba Ko alamar sa agurin. Suna tsaye kowannen su da Abunda yake saƙawa a ransa, Kawai idanun Haidar suka faɗa Akan ƙofar ɗakin Shadow. Ta gurin da suka biyo yanzu, ƙarasawa bakin Ƙofar yayi hannunsa yakai zai cire key ɗin da yagani a jikin ƙofar Sai Kuma yafasa. Cikin Al ajabi Haidar yace tabbas kowane Mai laifi yakan kwaɓar a yayin aikata laifinsa. Ma'ana yakan bar wata mafaka da zata tona asirinsa. Barin wannan key ɗin ajikin ƙofar shine ya nuna cewa tabbas daga baya aka buɗe wannan ƙofar Shadow yafice daga gidan..........✍️✍️✍️✍️ Tohm jama'ah ana wata ga wata Wanene yake bibiyar rayuwar Ahanaf (Shadow)? Kuma Koma waye menene dalilinsa? Mai zai faru Idan Abbu yazo Nigeria Bai Tarar da Shadow ba? Nabeela Binji ce💃💃💃 Nabeelah Shehu Binji 09064314811 Or 09161107610 More comment More taping 😉😉 Share Fisabilillah 🙏 ♣️DUHUN INUWA ♣️ TAPING......📲📲📲 STORY AND WRITING✍️✍️✍️ BY NABEELAH SHEHU BINJI PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞 ```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)``` /https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/                   *P.W.A✍️* BISMILLAHHIR_RAHAMANIR_RAHIM Page 0️⃣7️⃣ ___________ Cikin Mamaki Kamal yake kallon Haidar yace "Boss nifa ban fahimceka ba me kake nufi? Kana so kace Wani ne yazo gurin Nan ya Buɗe wannan ƙofar Shadow ya fita? Tabbas Kuwa, Haidar ya faɗa Yana gyaɗa kansa alamar tabbatarwa. Tabɗijam to waye wannan da yake aikata waɗan Nan abubuwan? Kuma menene dalilinsa nayin hakan? A Ina yake? Amsar da ya kamata mu nemo Kenan Kamal. Amma Koma waye yake wannan aikin tabbas yasan cikin gidan Nan sosai. Kuma Kai tsaye baza muce a cikin gidan Nan Mai laifin yake ba, Sai dai Zamu iya cewa akwai Saka hannu Wani agidan Nan, kodai ma menene bincike ne zai nuna Mana gaskiyar wannan lamarin. cewar Haidar Yana Ƙara Duba gurin da kyau. Wannan key ɗin shine Abu Na farko da Zamu Fara bincike akai, Saboda dole ne zanen hannu Wanda yabuɗe ƙofar yafito Idan anyi bincike, baza mu tabashi da hannu ba gudun matsala. "Kamal Shiga ka duba Mana handkerchief Sai mu cire key din Nan. To Kamal yace, "Ya Shiga ɗakin Yana Dube Dube Kamar Wanda za'ace ma kyat ya gudu, Dan Kamal badai tsoro ba gabaki ɗaya ya tsorata da lamarin wannan gidan abubuwa Sai ƙara Rincaɓewa suke. Maimakon a Samu Wani haske Sai ƙara tsunduma cikin DUHU akeyi. Dakyar ya samo handkerchief acikin kayan shadow ya kawowa Haidar, karɓa Haidar yayi ya buɗe Shi sosai sannan ya cire key ɗin tare da Dunƙulesa acikin handkerchief ya saka cikin aljihunsa yace "Kamal muje gurin Ayiya mu faɗa Mata halinda ake ciki Sai a san matakin da ya kamata a ɗauka tunkafin wannan Abun yayi Nisa, Haidar ya faɗa Yana Tura ƙofar ɗakin ya rufe ta. Tafiya suke kowanne su da Abunda yake saƙawa acikin rayuwar sa Har suka ƙarasa part ɗin Ayiya zasu Shiga Kenan sukaci Karo da ita Tana ƙoƙarin fitowa. Cikin ladabi suka gaidata Amsawa tayi cikin kulawa tare da tambayar su Ina Ahanaf yake? Batama Bari sun Bata amsa ba ta sake cewa Dama fitorwa danayi dubashi zanje nayi Naji A halinda ya kwana. Sunkuyar da Kai Kamal yayi idanunsa fall hawaye da mashi ba Dai saurin kuka ba, Haidar ne yayi gyran muraya sannan yace "Ayiya muje part ɗin Abba Sai muyi maganar a can" Ba Inda zanje Haidar, wane Abba Kuma Anya Kana cikin hankalinka Kuwa? Abba Wanda ya wufantar da rayuwar ɗan sa Akan Wani muradinsa. Ya aikata son ransa batare da ya bayar da Wani dalili ba, Shine kake cewa muje gurinsa? Ko munje ba Abunda zaiyi Sai Ƙara min ciwon zuciya. Dan Allah Idan Wani abune yasamu Ahanaf Ku gayamin nice Nan mahaifiyarsa komai Zan iya aikata Akan yarona, Dan Allah Ku faɗamin a wane hali Ahanaf yake? Kiyi haƙuri Ayiya Amma gwara Dai muje gaban Abba ɗin zaifi, Zatayi Magana Haidar ya dakatar da ita ta hanyar cewa yanzu fa kikace zakiyi komai dumin ceto ran Yaronki Ayiya, Dan Allah Ki ajiye duk Abunda kikeji a ranki yanzu muyi Abunda yake shine mafita. Ba yadda Ayiya ta iya haka tashiga gaba su Haidar Na binta a baya Har suka ƙarasa palon Abba, Zaune yake Akan 2sit Yana kallon News, Idan ka kalleshi zakayi tunanin gabaki daya hankalinsa Yana Kan TV ne, Amma Ina idanunsa ne Kawai Akai hankalinsa gabaki ɗaya bayama gurin ya Lula wata Duniyar daban. Saida Kamal ya ƙarayin sallama Sannan Abba yayi firgigit tare da amsa sallamar da suke Masa Yana binsu da kallon da wacce kuka zo Kuma. Akan kujera Ayiya ta zauna fuskarta ba yabo ba fallasa, Haidar da Kamal kuma a ƙasa suka zauna gefen Ayiya. Shuru ne yaratsa palon ba Abunda kakeji Sai ƙarar tv. Malamai Idan har bakuda Abun faɗa zaku iya Tafiya Dan Allah, saboda a halin yanzu nafi son Na zauna nikaɗai, Abba yafaɗa idanunsu Akan tv kamar badasu yake Magana ba. Ayiya zatayi Magana Haidar ya girgiza Mata ka Alamar Dan Allah tayi shuru kawar da Kanta tayi gefe batare da tace ƙalaba. Gyara Zama Haidar yayi cikin nutsuwa ya Fara faɗawa su Abba duk Abunda ya faru tun bayan kulle Shadow da sukayi ajiya da dare, da Kuma dubawar da sukayi Basu ganshi ba bayan sun dawo masallaci. Wata Matsananciyar faɗuwar gaba Abba yaji cikin tashin hankali ya dubi Haidar Wanda kansa yake a ƙasa, Har zaiyi Magana Sai kuma yafasa ya dafe kansa da yake matuƙar Sara Masa Kamar ana buga Masa guduma. Nan take Kuma Sai yaƙara jin duk Duniya ba Wanda ya tsana Sama da Ahanaf. Ga Kuma kukan Ayiya da yake taɓa Masa zuciya, Yama Rasa Abunda yake Masa Daɗi a duniya. cikin ƙaraji yace YA ISA YA ISA da wanne kuke so Naji ne? Ko su kuke Sai kun haukatani? Dan Allah Ku Tashi kubani guri Abba yafaɗa Yana nuna Haidar da Kamal a ƙufule, Tashi sukayi suka fita fuuuuuuu Kamar zasu Tashi Sama, Ita ma Ayiya Tashi tayi da nufin bin bayansu cikin sauri Abba ya riƙe Mata hannu yace "Ina Kuma zakije Haj? Kasakar min hannu Alh, Ka damu dani ne bare Har ka damu da gurin da zanje? Zan tafi Nemo yarona ne Kuma kasani muddin nasaka ƙafa Na bar gidan Nan naje Nemo Ahanaf Toh Koda Na ganshi bazan dawo gidanka ba Har Abada. Cikin sauri Abba ya rufe Mata baki yace haba Dan Allah me kike faɗa ne haka? Kamar bakya cikin hankalinki, Yaron Nan ki rabu dashi duk Inda yaje Shi da kansa zai dawo gida, kituna ba fa kurar sa mukayi ba, shida kansa yabar gidan Nan, Dan haka Shi da kansa zai dawo. Girgiza Kai Ayiya tayi tace Wai bakaji Abunda su Haidar suka faɗa bane? Haj Kira bu da zance "wa ƴan can Shashashun yaran duk halinsu ɗaya dashi Ahanaf ɗin. Abun da suke faɗa ba gaskiya bane. Kwace hannuwan ta tayi tare da cewa Idan Kai baka yarda Da Abunda sukace ba to Ni na yarda, Dan haka zanje neman Ahanaf yanzu ba Sai anjima ba, Ayiya ta faɗa ranta a ɓace tare da nufar hanyar fita daga palon. Ba da yawuna ba muddin Kika fita daga gidan tohm tabbas kisani Akan tsinuwar mala'iku Zaki fita, indai Ni Muhammad Imran nine mijinki Toh ban lamunce Miki kije neman wannan Yaron ba, Yana gama faɗar Hakan ya nufi hanyar bedroom ɗinsa ba tare da yajira yaji Abunda zata ce ba. Haidar Bai fa kamata muyi haka ba gaskiya, Idan har mukayi haka mu ba abokanan kirki bane, abokin kirki shine Mai tsayawa abokin sa a cikin wuya Ko Daɗi, Kaine kafaɗi haka. Yanzu Kuma Zaka ƙaryata kanka. Kamal yafaɗa Yana kallon Haidar Wanda Sai faman saka kayansa yake a cikin jaka Rai a ɓace. Kaga Kuma Abbu zaizo anjima Idan yazo betarar damu bafa? "A yadda Abba yatsane mu ma zai iya cewa da sanin mu Shadow yafita daga gidan nan" Kaga bamuda ruwan wanke Kan mu, Haidar idan hankali ya gushe hankali ake sakawa gurin Nemo sa, ya kamata kayi tunani kafin ka yanke hukunci. Cewar Kamal Yana marairaice fuska. Wani irin iska Mai zafi Haidar ya furzar tare da cewa wllhy Abba yaci Albarkacin furfurar da Ke ɗauke a fuskarsa da Kuma mutunci haihuwar Shadow da yayi da Sai Na Masa Rashin mutunci da Ko Sunana yaji an Kira Sai gabansa yafaɗi, Amma kashh ba damar haka. Zan tsaya Har Abbu yazo muyi Magana dashi baki da baki in yaso daga Nan Sai Sai mu tafi abun mu, Shadow Dai shine abokin mu Kuma Zamu cigaba da neman sa tare da yi Masa addu'ar neman tsarin Allah a duk Inda yake. Murmushi Kamal yayi yace Hakan ma yayi Boss dan wallhi Nima Bana son Zama a gidan Nan, gabaki ɗaya lamarin gidan tsoro yake Bani, gidan da Ada Idan kazo ko kai waye Sai rayuwar iyalin ta Burge ka, Saboda soyayya da shakuwa da take a tsakaninsu. Amma yanzu gidan ya Koma Kamar gidan wasu enemies. Allah ya tona asirin duk Wanda yake da hannu a cikin wannan lamarin. Ameen ya Allah cewar Haidar Yana jingi jikinsa da Bango. Misalin ƙarfe 20:15 Na Rana Abbu ne zaune a katafaren palon Abba fuskarsa a turnuƙe Kamar Wanda aka aikowa da Mala'ikan mutuwa, Cikin ɗaure fuska Abbu yace Muhammad Ina So kafaɗa min Menene dalinlin da yasa ka ɗaura auren waccan yarinyar da Ƙaseem maimakon Ahanaf? Cikin rawar murya Abba yace Amma Yaya Ai da Kabari ka huta kaci abinci tukkunna. Ɗaga Masa hannu Abbu yayi tare da cewa Ai Na huta 1 da Yan mitina muka sauka ƙasar Nan Toh Ina ga ba Wani hutu da nake buƙa yanzu. Kabani amsata shine Kawai Abunda nake buƙata, Menene dalilin aikata duk wannan Abun Muhammad? Abbu yafaɗa Yana ƙure Abba da idanunsa da suka Fara sauya Kala zuwa ja tsabar ɓacin Rai............✍️✍️✍️ Yanzu ma a kafara😥😥 Duk fa abun Nan da Abbu yakeyi be San cewa Ahanaf baya gida ba. Me zai faru Idan Abbu yasan yasan Ahanaf baya gida? Nabeela Binji ce💃💃💃 Nabeelah Shehu Binji 09064314811 Or 09161107610 More comment More taping 😉😉 Share Fisabilillah 🙏. ♣️DUHUN INUWA ♣️ TAPING......📲📲📲 STORY AND WRITING✍️✍️✍️ BY NABEELAH SHEHU BINJI PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞 ```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)``` /https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/                   *P.W.A✍️* BISMILLAHHIR_RAHAMANIR_RAHIM Allahumma salli 'ala Muhammad, wa-'ala ali Muhammad, kama sallayta 'ala Ibraheema wa-'ala ali Ibraheem, innaka Hameedun Majeed, allahumma barik 'ala Muhammad, wa-'ala ali Muhammad, kama barakta 'ala Ibraheema wa-'ala ali Ibraheem, innaka Hameedun Majeed. Allahumma a'innee 'ala zikrik, washukrik, wahusni ibadatik. Allahumma innee as-alukal-jannah, wa-a'u'zu bika minan-nar.🤲 PAGE 0️⃣8️⃣ ____________kayi haƙuri Yaya wallahi nima bansan dalilin da yasa n...... tasss Abba yaji saukar mari akan kumatunsa, hannunsa yasa ya dafe gurin da Abbu ya mare sa, ɗago yayi yana kallon Abbu cike da mamaki. "Kana da hankali Muhammad kasan abunda ka keyi kuwa? ka aikata wannan gagarumin laifin sannan harka iya buɗe baki ka faɗamin cewa bawani dalili? kar kazama Maha'inci Muhammad katuna fa Ahanaf amana ne agurinka Alƙawari kayi zaka kula da shi, zaka bashi farin ciki zaka mantar dashi ƙuncin rayuwa zaka zamar masa Garkuwa. Ina duk wannan Al'washin naka yake? Ashe dama bada gaske kake ba? Ashe dama raɗaɗin mutuwane yasa kafurta duk waɗan nan abubuwan? Mai yasa kake so kazamar ma Ahanaf DUHUN INUWA Muhammad? Wani matsanan cin kuka Abba ya fashe dashi wanda shida kansa bai san dalilin yin saba, Saidai yasan duk abunda yayansa yafaɗa gaskiya ne Ahanaf amana ne agurin sa kuma abun so da ƙauna agurinsa, amma yarasa taya akayi hakan tafaru. Agaban Abbu Abba ya zube akan gwiwoyinsa, yace "ka yanke duk hukincin da kaga yayi maka a kaina yaya" ni mai laifine agurin ka. Amma fa kasani har yanzu ina kan bakata bazan warware auren Norr da Al ƙaseem ba. "Ahanaf ya kasa yimin biyayya kamar yadda ɗan uwansa yayi, Ya nuna min cewa shi yaro ne mai taurin kai ba wanda ya isa dashi" yaya bari kaji daga yau na fitar da hannu acikin duk wani lamari na rayuwar Ahanaf yaje yayi duk abunda yaga dama bani bashi" Abba ya faɗa cikin ɗacin rai. Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raju'un, Muhammad yau Kaine kake wannan furucin Akan Ahanaf? Kuma har kake haɗa masa da ƙarya da ƙage? Tabbas da wata a ƙasa wannan abun bayin kanka bane. Ni bawani hukunci da zan yanke ma wanda ke fama da Matsalar taɓin kwakwalwa, Amma kasani daga yau Ahanaf zai bar hannunka ya dawo ƙarƙashin kulawata. Sanna zan tayaka da addu'a kuma zan sanya manyan malamai su taimaka mana da addu'a, saboda bazan zuba ido ina kallon ka cikin wannan halin ba. Muhammad kai Amana ce agurina zanyi kumai dan ganin na kiyaye wannan amanar da iyayenmu suka bani. Bana so koda da kan a kaifane Allah yakama ni da Hakkinka agobe ƙiyama, zan tsaya tsayin daka akanka da kuma iyalanka dukanku hakkine da ya rataya a wuyana. Har yau bazan manta mutuwar mahaifiyar muba bazan manta yadda ta dankamin amanar ka a hannuna ba Muhammad, duk duniya banida wani ɗan uwa sama dakai, kaima bakada wani ɗan uwa sama dani mu biyun nan mune kawai dangin juna bamuda kowa face Allah. Muhammad katuna yadda mukayi fafutuka da rayuwa kafin muzo wannan matsayin. Munyi fama da rayuwa Munyi fama da maraici Maunyi fama da rashin gata, uwa uba Munyi fama da ƙuncin talauci da rashin majingina. Amma duk da haka baisa munguji juna ba kuma baisa muka yada zumunci ba baisa nakasa riƙe amanar kaba Muhammad. Kuma kasani har yanzu bazan karya alƙwari ba. ni bakamar kai bane Muhammad kuma kasani bana fatan zama kamar kai har abada. Abbu yana gama faɗar haka ya miƙe tsaye da nufin barin palon saboda ransa yakai ƙololuwar ɓaci akan wannan lamarin na ƙanensa. Cikin sauri Abba ya bi bayansa tare da rungume shi ta baya yana kuka, yace "dan Allah ka gafarceni yaya wallahi ni kaina bansan dalilin akaita wannan abun ba. Yaya taɓa kirjina kaji bugawa yake da sauri. Hannun Abbu yakama yaɗaura a saitin zuciyar sa. Da sauri Abbu yajanye hannusa tare da furta Muhammad kashe kanka zakayi kaji yadda zuciyar ka ke bugawa da sauri? Mai yasa kake son kashe kanka ne? wannan abun duk fa kaine ka aikata shi. Ni fa gaskia kawai na faɗa maka. Wallahi Narasa dalilin da yasa nayi haka yaya, "dan Allah karka gujeni wallhi idan katafi kabarni mutuwa zanyi kaine Babana kaine mamana kuma kaine yaya na banida kowa sama da kai dan Allah kar katafi" Abba yafaɗa yana ƙara rungume Abbu ajikinsa tare da ƙara sautin kukansa kamar wani ƙaramin yaro. Tohm naji bazan tafi ba Muhammad ka kwantar da hankalinka, nima faɗa kawai nake ba gurin da zan iya tafiya nabarka a cikin wannan halin. cewar Abbu yana goge kwallar da tazubo masa. Shiru Abba yayi sai ajiyar zuciya da yake saukewa kamar wanda yayi gasar gudu. Bari naje na duba Ahanaf ɗin naga awane hali yake ciki, kafin nasan wane mataki yakamata naɗauka akan wannan case ɗin. Abba yace"Ahanaf baya nan fa Yaya ya tafiyarsa, dama na faɗa maka yanzu wannan yaron bayajin magana kwata kwata ba wanda ya isa da shi" Abba yafaɗa yana yamutsa fuska alamar ko ajikinsa baiji tafiyar ta Ahanaf ɗin ba. Abbu yace Subhanallah "Ahanaf yatafi kuma? ina yatafi? meyasa kuka barshi yatafi?" Nima bansan tafiyar tasa ba "ɗazu ne abokanan Shashancinsa suke faɗa muna wai baya nan Suma bayan sun dawo daga Masallaci ne suka nemesa suka rasa" Ni bam ma gama yarda da zancen Nasu ba saboda nasan duk bakinsu ɗaya dashi maybe ma da sanin su yatafi. Amma sunzo suna faɗawa Mutane maganar ban.... Tsawa Abbu ya daka masa cikin hargowa yace kasan mai kake faɗa kuwa Muhammad "Ahanaf ɗin ne baya nan kuma kake nan hankalinka kwance?" Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raju'un Abbu ya faɗa yana fita daga ɗakin cikin sauri kamar zai tashi sama, direct part ɗin Su Shadow ya nufa ransa a masifar ɓace, ƙofar palon ya tura da ƙarfi ya Shiga ba ko sallama yana kwaɗa kiran Haidar. Haidar da yake tsaye a tsakiyar palo yana waya da wani abokinsa D.P.O Abdul-Naseer akan wannan case ɗin na Shadow. Da sauri Haidar yajuya dan ganin waye yashigo haka ba ko sallama, kuma yana ta ihun kiran sunansa. Ido huɗu sukayi da Abbu wanda yake cikin matsanan cin tashin hankali. kallo ɗaya Haidar yayi masa ya gane Shine Abbu, Saboda yana ganin pics ɗinsa a cikin wayar Shadow kuma ko bayan haka suna matsananciyar kama da Abba. Ina zuwa D.P.O Haidar ya faɗa tare da katse wayar da ya keyi. Ina wuni Abbu barka da zuwa ya hanya? Duk a cikin gaisuwar nan da Haidar yakewa Abbu ba wacce ya Amsa, Saima tambayar da ya jefa masa, yace Haidar ina Ahanaf? Abbu dan Allah ka zauna mana sai muyi maganar. Ba musu Abbu ya zauna dan ya ƙagara yaji gaskiyar wannan batun. Shima Haidar zama yayi a ƙasa kusa da ƙafafun Abbu, ya sunkuyar da kansa ƙasa cikin nutsuwa ya fara bawa Abbu labarin duk Abunda yafaru jiya bayan sun gama yawa dashi. Da neman da sukayiwa Shadow basu ganshi ba har izuwa lokacin da sukaje faɗawa Abba Abunda yake faruwa da kuma irin koyar da Abban yayi musu. Iska mai zafi Abbu ya furzar ya ɗauki kusan 3min baiyi magana ba, a hankali ya maida kallon akan Haidar yace wane mataki yanzu kuke ganin yakamata a ɗauka? ko kuma akwai wanda kuke zargi? Gaskiya ba wanda muke zargi Abbu. Amma kuma akwai wani Abu da yayi matuƙar ɗaure muna kai, bayan mun duba ko ina bamuga Ahanaf sai muka ga wata ƙofa ta baya bayan mun bi hanyar sai muka ɓulla ta gurin garden, muna dudduba gurin sai mukaga key ajikin ƙofar ɗakin ta baya tohm a nan ne muka tabbar lallai wani ne ya buɗe ƙofar ta baya Ahanaf yafita. Yanzu ma haka key ɗin yana nan na aje muna su ayi bincike akansa dan gano zanen hannun waye akan key ɗin, Yanzu ma da kaga ina waya magana nake da wani abokinmu, shi ɗan sanda ne babba da ya ƙware agurin harka bincike. Yanzu ma haka yana hanya zaizo nan gidan saboda a ɗauki zanen hannu duk wanda yake gidan nan har masu aiki domin gano waye mai wannan laifi, kuma menene dalilin da yasa ya buɗe Ahanaf. Haidar ya faɗa cikin nutsuwa. Tabbas wannan tunanin naka abune mai kyau Haidar, Ba Shakka ku friends ne Nagari kuntsaya tsayin daka dumin abokin Ku. Ba kutafi kun barsa ba duk da Abunda mahaifinsa ya Muku. Banida Abunda Zan Saka Muku dashi Allah yayi Muku Albarka Kuma ya kare Ku Aduk Inda kuka Shiga. Ameen Abbu Mun gode. Wayar Haidar ce tafara ringing Yana dubawa yaga D.P.O ne Ke Kiransa, maybe ma ya karaso Haidar yaɗada Yana Kara wayar a kunnensa. Okey jirani agurin ina zuwa Haidar ya faɗa yana tashi tsaye, ya kalli Abbu yace Abbu muje D.P.O ya ƙaraso yana waje. Tashi Abbu yayi yabi bayan Haidar suka fita tare. ƙara gaisawa Sukayi da D.P.O Sannan D.P.O yace yakamata muyi Abunda ya kamata saboda inada meeting anjima kaɗan Insha Allah. Abbu ya kalli Haidar yace ina wannan Abokin naka da kake magana? yana gurin wanka Amma zai fito yanzu insha Allah. Duk wani Mahaluki da yake Rayuwa agidan ya Hallara a babban palon Alh Muhammad Imran. Cike da mamaki Abba yake bin kowa na falon da kallo, kafin daga ƙarshe ya maida kallonsa akan Abbu yace mai yake faruwa haka ne? menene dalilin duk wannan taron yaya? zaka kasani yanzu Abbu yafaɗa yana maida kallonsa akan D.P.O Abdul Naseer. Yace zaka iya fara aikinka D.P.O. Bayan an gamawa kowa a kazo kan Abba amma fafir yace shi baisan zancen, ba bazai bayar da hannunsa ba. Wallahi wannan ne kuma baka isa ba Muhammad........ ✍️✍️✍️ Taya akayi Shadow ya zama Amanar Abba? Raɗaɗin mutuwar waye yasa Abba ya ɗauki Alƙawarin rike amanar Shadow? Tohm waye ya Bawa Abba Amanar Shadow? Bayan Alh Muhammad Imran ( Abba) Shine mahaifin Ahanaf (Shadow). Tabbas akwai wata ƙullalliya a ƙasa😥 Nabeela Binji ce💃💃💃 Nabeelah Shehu Binji 09064314811 Or 09161107610 More comment More taping 😉😉 Share Fisabilillah 🙏. ♣️DUHUN INUWA ♣️ TAPING......📲📲📲 STORY AND WRITING✍️✍️✍️ BY NABEELAH SHEHU BINJI PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞 ```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)``` /https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/                   *P.W.A✍️* BISMILLAHHIR_RAHAMANIR_RAHIM PAGE 0️⃣9️⃣ Wallahi wannan ne kuma baka isa ba Muhammad............ ________________Yazama dole ayi bincike a kanka Kamar yadda a kayiwa Kowa, "Idan har Kuma kace baza ka Bari ayi ba tohm ba shakka Kaine ka buɗe wannan ƙofar kuma ka kori Ahanaf daga gidan nan. Idan har hasashena gaskiya ne wllhy Muhammad sai ka fuskanci mummunan hukunci daga gareni. Kuma kasani idan har hakan yazama gaskiya Wllhy bani ba kai har abada. Muhammad kasan wanene Aliyu idan na faɗi magana koda mutuwa ce zata gifta a gabana bazan canza ra'ayina ba. cewar Abbu cikin matsancin ɓacin Rai. Duk wanda yake a Palon yashiga tashin hankali da jin furucin Abbu. Shida kasansa Abba ya ruɗe sosai yajima baiga yayan nasa acikin irin wannan fushin ba. yaya dan Allah k.. ɗaga masa hannu Abbu yayi tare da cewa bana son jin komai daga bakin ka Muhammad, Wallahi dole ne kayi ɗaya daga cikin biyun Nan, kodai kabari ayi bincike akanka Kamar Kowa Ko Kuma ka gayamin gaskiyar Abunda yafaru da Ahanaf a Daren jiya. Maganar gaskiya bansan Abunda ya faru da Ahanaf ba a Daren jiya, Kuma wllhy Yaya bani na Buɗe ƙofa yafita ba. Hasalima Ni ban yadda cewa yasamu taɓuwar hankali ba, Kawai ya tafiyar sane Saboda Abunda yafaru, su kuma su kazo da nufin tayar Mana da hankali, Amma Idan har wannan binciken zaisa kadaina zargina Kuma kajanye wancan zance Na cewa Zaka tafi kabarni Na Har abada tohm Na yadda ayi Koma Menene Yaya, Abba yafaɗa cikin ɗacin Rai tare da ƙarajin tsanar Ɗan nasa Ahanaf, saboda gabaki daya Abba yadauki laifin komai yadaurashi Akan Ahanaf Wanda Idan aka saka shigaba akace ya faɗi dalilin Tsanar da yake yiwa Ahanaf Tabbas ba Wani dalili Dan Shi da kansa Bai San dalilin ba. Kallon d.p.o Abbu yayi yace Zaka iya Fara akinka Kamar yadda kayi Akan Kowa domin goge zargi. Bayan d.p.o yagama duk Wani binciken da zaiyine ya Koma Kan ɗaya daga cikin kujerun palon ya zauna tare da zare glass din idonsa ya kalli Abbu yace tabbas akwai sarƙaƙiya acikin wannan case ɗin Ranka yadaɗe. Mai aikata wannan laifin yanada matuƙar wayau da basira, saboda ba ta inda yabar wata shaidar da za'a iya kamasa, Tabbas Bai kwaɓar ba A Ko Ina ya kiyaye Akan abun harinsa da Kuma goge duk wata hujjar da zata nunasa, Yana aiki da kwakwalwar sa yayin da mu yake Mana Wasa da tamu kwakwalwar D.p.o yafaɗa Yana gyaɗa Kai cikin mamaki sai kuma yasaki murmushin da shine Kaɗai yasan dalilin yinsa. Kallonsa ya Maida Kan Abbu yace tabbas Koma waye yake aikata wannan laifin ya iya takonsa sosai ranka yadade, Amma hausawa sukance Karen Bana shine maganin zomon Bana, Mai laifi har yake da kwarin gwiwa ayayin da yake cikin ganiyar aikata laifinsa tohm Taya Mai bincike zai Sare agurin gano mai laifin? Yanzu za'a Fara wannan wasar, tabbas Sai an ban bance tsakanin Ƙarya da gaskiya. ka kwantar da hankaliki Alh Zanyi iya bakin ƙoƙarina dan ganin Na Nemo Maka Ahanaf tare da binciko Maka Mai laifin a duk inda yake a faɗin duniya insha Allah, d.p.o Abdul naseer yafaɗa cike da tabbatarwa. Gyara Zama Abbu yayi tare da cewa nagode sosai yaro Allah yayi Muku Albarka, sanna duk Wani Abu da kake bukata Na dangane da bincikenka Zaka iya tuntuɓar su Haidar saboda nasan bazasu ɓoye Maka komai ba insha Allah. Sannan a duk lokacin da kake son kayi bincike Ko Kuma kayiwa Wani wata tambayar Ni Nan nabaka damar shigowa gidan Nan Kai tsaye Domin gabatar da aikinka yadda yadace. Wani kayataccen murmushi d.p.o Abdul naseer yayi tare da cewa nagode sosai ranka yadaɗe, Yanzu Kuma Ina son Na keɓe da maigadin gidan Nan saboda akwai tambayoyin da nake so nayi Masa, Tabbas binciken da mukayi yanzu duk Wanda yake cikin gidan Nan yayi Nasarar kuɓuta a Karo Na farko ba musan mai bincike nagaba zai haifar ba. Saboda Kai tsaye baza muce Mai laifin daga waje yake ba, Kuma baza muce daga cikin gidan Nan yake ba. Bincike da ƙarfin addu'a ne Kawai zasu haskaka Muna wannan DUHUN INUWAR da ya baibaye kwakwalwar mu. Dukanku Sai kun bayar da haɗin Kai ta yadda Kumi zai tafi cikin sauƙi. Cewar d.p.o Yana bin kowa da yake palon da Kallo. Insha Allah cewar Mutanen da suke palon Banda Abba da duk Abunda suke haushinsu yakeji matuƙa. Sallama yayi Musa tare da cewa mlm Muntari Mai Gadi yabiyo bayansa suje. Malam Muntari tambayar ka nake so nayi Kuma Bana son ka Ɓoyemin kamai gaskiya Kawai nake son ji daga bakinka, saboda Faɗin gaskiyar ne zaisa mu rabu cikin salama, Amma kasani muddin ka faɗamin ƙarya zanyi bincike Kuma Idan Nagano ƙarya ka faɗamin tohm kasani Zaka fuskanci mummunan hukuncin wallhi cewar d.p.o fuskarsa ba alamar Wasa. Ba Abunda Zan ɓoye Maka ranka yadaɗe wllahi duk Abunda ka tambayeni Zan baka amsa ta gaskiya insha Allah, Idan kayi haka kataimaki kanka mlm Muntari. Tambaya ta a gareka ba Mai wahala bace. Waye yazo gidan Nan jiya da dare yafita da Ahanaf? D.p.o yafaɗa Yana ƙuresa da Ido. Gaskiya ba Wanda yazo gidan Nan yafita da Ahanaf ranka yadaɗe, hasalima jiya da dare Audu driver ne yayi shigowar ƙarshe agidan Nan bayan Shi ba Wanda yaƙara Shiga Ko Kuma fita daga gidan Nan Har lokacin rufe gidan yayi. Mlm Muntari yafaɗa cikin tsoro da kuma ƙoƙarin ganin ya kuɓutar da kansa daga zargi. Numfashi d.p.o ya furzar sannan yasa ke ce masa Kuma Kana Zaune a bakin gate ba kaje Ko Ina ba Har lokacin rufe gidan yayi? Wallahi ba Inda naje ranka yadaɗe Ina zaune a gurin Har lokaci yayi. Bayan Kai akwai Wanda yake da makullin gate ɗin? Gaskiya bazance akwai Wanda yake da makullan gate ɗin ba, saboda Nidai sanan iya Ni kaɗai nake amfani dasu Kuma Ina tunanin sune kaɗai makullan gate ɗin. Dan bazan manta lokacin da Alh ya Bani kuɗi nasiye Wasu makullan ba Saboda wa ƴancan sun lalace. Kuma gaskiya Ni nasan ban Bama Kowa makullan ba. Sannan Koda ma ace akwai Wanda yake da makullan agidan Nan ba yadda za'ayi a Buɗe wannan gate ɗin banji ba, saboda gate ɗin Yana ƙara Idan anzo ɓuɗesa Ko Kuma rufesa. Nagode sosai mlm Muntari ina fatan zaka bahi haɗin kai idan na sake dawowa? Eh insha Allah zan faɗa maka gaskiyar duk abunda ka tambayeni. Wani malalacin Murmushi D.P.O yayi tare da buɗe motar sa yashiga yabar gidan da mugun gudu...............✍️✍️✍️ Kaina bisa wuya Ina Matuƙar baku haƙuri ƴan uwana. Wallahi na ɗan shiga wasu sabgogine kwana biyu, kuma bayan haka naje wani gari da ake fama da matsalar network ɗin MTN dalilin da yasa kuka jini shuru kenan Ina fatan Zakumin Afuwa🙏😥 Nabeela Binji ce💃💃💃 More comment More taping 😉😉 Share Fisabilillah 🙏 ♣️DUHUN INUWA♣️ TAPING......📲📲 STORY AND WRITING✍️✍️✍️ BY NABEELAH SHEHU BINJI PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞 ```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)``` /https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/                   *P.W.A✍️* BISMILLAHHIR_RAHAMANIR_RAHIM PAGE 1️⃣0️⃣ Wani malalacin Murmushi D.P.O yayi tare da buɗe motar sa yashiga yabar gidan da mugun gudu. ____________Zaune suke a part ɗin su Shadow Suna fira Haidar ne ya kalli Abbu yace "Abbu wai dan Allah dagaske su Abba ne suka haifi Ahanaf? Iska Mai zafi Abbu ya furzar, tare da gyara Zaman sa ya fuskanci Haidar da Kamal, Cikin ɗacin rai da ƙunar zuciya Abbu yace "Tabbas Ahanaf Yaron sune, Muhammad shine mahaifin Ahanaf Kuma shine Ɗan sa na farin, Sai Daga baya Allah ya bashi Al kaseem, Muhammad Yana matuƙar son Ahanaf fiye da Kowa a rayuwar sa, ba yason ganin ɓacin ransa Yana riritashi fiye da tunanin Ku" Haka ita ma Haj Shuwa "Bata ƙaunar Abunda zai taɓa yaranta Ko kaɗan" Shekarun baya da suka wuce Idan nazo gidan nan Ko Kuma su sunje gidanmu Nakan tasa su gaba nayi musu faɗa Akan su rage nunawa yaran Nan So a gaban idon su, Saboda Hakan zai iya sadin lalacewar tarbiyar su. A iya sanina su iyaye ne masu nuna damuwa Akan yaran su, Basu ƙaunar Abunda zai taɓa ɗaya daga cikin su. Amma babban Abunda ya bani mamaki Kuma yake Kan Bani mamakin Har yanzu shine "ganin yadda Muhammad ya jefa rayuwar Ahanaf a cikin haɗari, Kuma ya nuna halin Ko'in Kula Akan sa" Tabbas wannan lamarin akwai wata kullalliya a ƙasa, ba Abunda zaiyi maganin wannan matsalar Sama da Addu'a, Dole Sai Mun Tashi tsaye Akan wannan lamarin, Idan har Muna so mukai ga Nasara da tonuwar Asirin Wanda yake son ganin bayan mu. Cewar Abbu Yana bin su Kamal da kallo. Zamuyi komai dan ganin Mun ceto rayuwar abokin mu Shadow insha Allah. Alhmdllh Allah yayi Muku Albarka Abbu ya faɗa Yana murmushi. Ameen ya Allah. Nan sukaci gaba da tattaunawa Kan matsalar da Kuma ta yadda zasu Ɓullowa lamarin. Gidan Amare _________ Norr ce tsaye a kitchen tana girkin dare, Al ƙaseem tsaye a gefenta ta Yana zuba Mata Salo da kwarewa Ita Kuwa sai faman dariya take Masa, ya mutsa fuska ya tare da langwaɓar da kansa Kamar Wani ƙaramin yaro cikin shagwaba yace baki yarda da Abunda Na faɗa ba Ko my Norr? Cikin dariya tace wacece Ni da zan ki yarda da maganar yallaɓai, ta faɗa cikin sigar zolaya. Kwafa yayi yace wata Rana Sai munyi gasar girki Sai anga Wanda yafi iya girki Nida Ke a cikin gidan Nan. Murmushi Norr tayi Sannan tace a'a Ai basai anyi ba Kawai na yarda mijina gwani ne agurin girki, shikenan Nan maganar ta wuce Ko? Tafaɗa tana kallon sa Tana dariya ƙasa ƙasa. Bata wuce ba Kam Sai anyi girkin Nan insha Allah munyi maganin Raini, Al ƙaseem ya faɗa cikin kwarin gwiwa irin Shi ga kwarrare agurin girki. Toh Allah ya kaimu ranar wannan gasar cewar Norr tana Maida hankalinta Akan Abunda takeyi, Cox dare yafari Kuma har yanzu Bata Gama aikinta ba, ta tsaya gardama da Al ƙaseem. Gabaki ɗaya Kona su zanyi wallahi, Ai wannan rainin hankali ne Taya zai cika mana gida da pic's din sa, Al kaseem ya faɗa Yana faman huci Kamar Wanda yaci gudu. Pic's ɗin Shadow ne zube a ƙasa gurin da yake Shi kaɗai, da gurin da yake tare da Norr. Masu glass Har sun farfashe saboda jifar da Al ƙaseem yake da su, babban baƙin cikin sa shine ganin Zanen da Shadow yayi Shida Norr kamar pic's akayi musu ba Zane bane yayi masifar kyau. Saboda Shadow ya kware sosai agurin Zane, Idan ya Zana mutum Zaka iya rantsuwa cewa pic's ne ba Zane ba. Norr ce ta riƙe sa tace Dan Allah kayi a hankali Mana Kar kajiwa kanka ciwo, basai ka Kona "Masa abuba ka hadasu guri ɗaya ka Tura Masa kayansa" Kina da hankali kuwa Norr? Pic's ɗin naki ne Zan turama Wani gardi ya dinga Kalla? Toh wallahi bazan tura su ba, gabaki ɗaya Kona su zanyi ni ba Shashasha bane, Al ƙaseem ya faɗa cikin masifa da ɓacin Rai. Baya Norr taja Dan ta lura ran mijin nata yayi masifar ɓaci, Sannan ga matsancin Kishi da yake faman Ɗawainiya dashi. Hakan yasa taja bakin ta tayi shuru Bata ƙara ce Masa ƙala ba. Bayan yagama haɗa pic's ɗin gabaki ɗaya ne ya kwashe su ya Kai su hara bar gida ya Cinna musu wuta, Saida yaga sun Gama cinyewa Tass Sannan ya Koma cikin gidan Yana Jin Wani irin zafi a zuciyar sa. ____________ kwance yake a gefen hanya ba alamar numfashi a tare da Shi, Saboda yasha Duka Na fitar hankali. Sanyi asuba ne da ya fara bugawa yasa ya Fara motsa hannunsa a hankali, Ya ɗauki tsawon lokaci a Haka kafin Daga baya ya fara motsa jikinsa alamar Yana so ya Tashi zaune Amma ya kasa. Sai da kyar ya samu damar Tashi zaune tare da sa hannuwan sa ya riƙe kansa da yake masifar yimasa ciwo Kamar zai Rabe gida biyu. Sai Wanda yayi Masa farin sani ne zai iya gane SHADOW a cikin wannan halin, Saboda yafita daga hayyacinsa sakamakon dukan da yasha Na fitar Ariƙi. Yayi yunƙurin Tashi yafi sau ukku Amma yakasa Saboda Ko Ina na jikinsa ciwo yake Masa ga Jiri da yake Gani Har idanunsa Na ƙoƙarin sake rufewa da kansu. Sake rufewa idanun sukayi yayi baya luuuuuh yaƙara zubewa ƙasa sumamme.......✍️✍️✍️😥 Tirƙashi wannan lamarin Anya ba tuggu a ciki Kuwa? Suwaye suka jefar da Shadow agefen hanya? Waƴanda suka jefar dashi yin kansu ne ko kuma saka su akayi? Idan saka su akayi tohm waye yasaka su? Idan kuma yin kansu ne menene dalilin su? Laifin me Shadow yayi musu? Da Shi suke faɗa Koda iyayenshi? Wace kalar yaruwa Shadow zaiyi a wannan garin da bai masan ko ina bane? Waye zai taimaki Mahaukaci a wannan zamanin da ko mai hankali yakasa samun taimakon Al ummah? Share Fisabilillah 🙏 ♣️DUHUN INUWA♣️ TAPING......📲📲 STORY AND WRITING✍️✍️✍️ BY NABEELAH SHEHU BINJI PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞 ```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)``` /https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/                   *P.W.A✍️* BISMILLAHHIR_RAHAMANIR_RAHIM PAGE 1️⃣1️⃣ Sake rufewa idanun sa su kayi yayi luuuuuh yaƙara zubewa ƙasa sumamme.. __________Wasu dattijai ne su biyu suka zo wucewa, tun Daga nesa ɗaya yace "Kamar mutun nake Gani kwance agurin can" Sai ɗayan yace toh muƙarasa mugani, Cikin sauri su ka ƙarasa gurin da Shadow yake kwance ba alamar numfashi a tare dashi, Ba shakka mutum ne dattijon guda ya faɗa cike da mamaki. Ɗayan ne ya durƙusa ya Kama babban farce Shadow Na ƙafa yayi Jim Yana saurare Sai can ya ɗago ya kalli abokin tafiyar sa yace Masa Yana da Rai Saidai ya Suma ne. Gorar ruwan ya ɗauko Yaba ma dattijon da yake riƙe da Shadow yace zuba Masa Muga Ko Zai Tashi. Ana zubawa Shadow ruwan cikin sauri ya buɗe idonsa Saboda ruwan ya Shiga Har cikin raunin fuskarsa Wani Irin raɗadi yaji Yana ratsashi. Da sauri ya Tashi zaune Yana binsu da kallo, Sannu yaro dattijon guda ya faɗa Yana ƙoƙarin Kai hannunsa a jikin Shadow, da sauri Shadow yaja baya alamar Baya Son su taɓa Shi. Ɗan samari Daga Ina? Mai ya sameka haka? Ko azzaluman Mutanen Nan ne suka Kama ka? Da Ido Kawai Shadow yake binsu Amma ya kasa Buɗe baki yayi Magana, Sai ma ƙoƙarin Tashi yake tsaye, "kayi a hankali yaro Kar ƙarawa kanka Wani raunin" Ko kulla su Shadow bayi ba, ya Tashi tsaye ya saka hannunsa ya dafe kansa da yake Masa ciwo Kamar zai Rabe gida biyu tangaɗi yake kamar Wani ɗan Maye. Duƙawa yayi da ƙyar ya ɗauki jakar kayan Zanen sa wace yagani yashe a gefe. A hankali yafara Tafiya ba tare da ya juya ya kalli waɗan Nan tsofaffin ba. Cike da mamaki suke binsa da kallo. Anya Yana da hankali kuwa? Cewar dattijon da ya zubawa Shadow ruwa. Gaskiya Kam ba alamar hankali anan Saboda Idan yana da hankali Ko da Baice Mana komai ba Ai yakamata yayi Muna godiyar ceton ransa da mukayi. (Allah sarki rayuwa su Basu ma San Bada Mai Hankali suke tare ba) Tafiya yake bai masan gurin da yake jefa ƙafar sa ba, Abu ɗaya yasani yanzu shine ciwon da yake ji ajikinsa Wanda baibsan yadda zaiyi dashi ba. Tafiya Mai matuƙar Nisa Shadow yayi kafin yasamu ƙarasawa cikin gari, (Da ace Shadow cikin hankalinsa yake da koda da kuɗi aka haɗashi bazai iya wannan uwar tafiyar ba.) Ji yayi ya kasa Tafiya ya Samu gefen Wani gidan Mai ya zauna tare da sunkuyar da Kan sa ƙasa. Kamar Mai tunanin Wani Abu bayan mintina kaɗan ya Tashi yaci gaba da tafiyar sa Tafiya Kawai yake bai masan Inda ya dosa ba, Saidai Idan yaga Wani Abu Ko yaga Taron mutane yakan tsaya ya Kalla Idan yagaji da tsayi yayi tafiyar sa. Kusan kwanaki ukku Kenan Shadow Yana yawo a wannan Garin dashi baima san Ina ne ba. Gabaki ɗaya Alamar hauka tagama bayyana a tattare dashi Saboda kayan jikinsa sunyi masifar Datti. Ga ciwon da yaji Har ya fara caɓewa Saboda Rashin Samun Kulawa. Ba abinci ba drugs babu kyakyawan makwanci. Ahanaf yaga rayuwa agarin da baisan Kowa ba bashida Wani Wanda zai taimaki rayuwar sa Sai Allah. Yanzu ma Tafiya yake cikin yanayi na Wanda yunwa tagama rarakewa, tun safe ba Abunda yaci, Har Kuma gashi Yamma tayi Yana yawo Yaran gari na Kiransa da mahaukaci. A haka har ya ƙarasa Gurin wata Mai awara ya tsaya Yana kallonta. Matsananciyar yunwa yakeji Amma baisan yadda zaiyi ba. Gefe ya Koma ya tsaya tare da buɗe jakar hannunsa ya ajeta ƙasa fitar da kayan Zanensa, ya fara Zana wannan matar Mai Awara. Wani ne Wanda Shima awarar yazo Siya shine ya nuna Mata Zanen da Shadow yayi nata. Cike da mamaki take kallon Zanen tabbas Koda Bata taɓa ganin Kanta a madubi ba tasan ba Shakka ita ce wannan Mahaukacin yazana a Bango. Kai tsaye gurin da Shadow yake ta nufa sauran Mutanen da suka lura da Abunda yake faruwa suka mara Mata Baya. Tsayawa su kayi Suna kallon Zanen tabbas wannan kwarraren Mai Zane ne. Kayan Zanen sa ya kwa she ya mayar acikin jakar sa. Duk maganar da suke Shadow Baice musu Kala ba. Da matar ta lura Mahaukacin Nan Dai bazaiyi Magana ba Sai Takoma gurin da take soya awarar ta tazuba Masa ta 200 a Leda baƙa ta Kai Masa. Ai Kuwa cikin sauri ya warci ledar a hannunta yafara cin awarar Kamar wanda Bai taɓa tozali da abinci ba a rayuwar sa. (Ilimi Wani abune Na musamman a rayuwa, shine kaɗai Abunda zai Zama mallakinka a Ko wane hali kake ciki, Idan ka mutu ba Mai gadon ilimin ka, haka zalika Idan kasamu taɓuwar hankali ba Mai gadon ilimin ka, duk ƙiyayyar da Wani Bawa yakeyi gareka bazai iya kwace Maka ilimin da Allah ne yabaka Shi ba. Kamar Shadow yanzu iliminsa ne ya ciyar dashi a yanzu duk da Baya cikin hankalinsa. Allah yasa mudace) Cikin tausayawa take binsa da kallo "wannan da Gani sabon Shiga haukane Saboda kallo ɗaya Zaka Masa kagane cewa a cikin Daula da Hutu ya Tashi Dattin da yayine Kawai Zai nuna Maka cewa bashida cikakkiyar lafiya" Tafiya yake Yana cin awarar sa Har ya Kai gurin Wani kangon gida Kai tsaye ciki ya shiga, da alama dai ya saba da gurin a kwana biyun Nan da yayi. A ƙasa Ya zauna Yana cin awarar sa Yana ta faman zare Ido kamar wanda yake gudun Wani yazo ya kwace Masa awarar, bayan yagama cine ya Samu guri gefe ya kwanta ya lumshe idanunsa. Ba jimawa bacci yayi awon gaba dashi. A kwana a Tashi Bata bar kumai ba, yau har Shadow yacika wata huɗu a cikin ya nayin hauka, ba Wanda zai ga wannan Mahaukacin yayi tuanani Shadow ne ɗan wanka ɗan ƙwalisa ya Koma haka. ______________ A ɓangaren su Abbu Kuwa har yanzu sun kasa samo Mai laifin Saboda ba wata kwakkwarar hujja. Wannan lamarin yayi matuƙar tada hankalin d.p.o Cox Shi a rayuwar sa Bai taɓa cin Karo da case ɗin da ya Caza Masa Kai kuma yake ci masa tuwo a kwarya ba Kamar wannan. Hakan yaƙara harzuƙa d.p.o da Kuma cin Alwashin Sai ya kamo duk Wanda yake da hannu a cikin wannan case ɗin Kota halin Yaya da yarda Allah. Abbu yayi Rama sosai kallo ɗaya zaka Masa kasan Yana cikin matsancinyar damuwa. Yana son sanin halinda Ahanaf yake ciki, Yana son ƙara ganinsa Koda sau ɗaya ne a rayuwa. Tabbas Nemo Ahanaf hakkine da ya rataya a wuyansa, Amma ya kasa Hakan, Duk iya binciken su da sanarwar su sun kasa Samun Wanda ma yace yaga Mai kama da Ahanaf ɗin. Abbu Yana son ganin Ahanaf Koda a cikin halin haukane shidai muradinsa Kawai ya ganshi Kuma yaga ya sauke duk Wani hakkinsa Wanda Abba ya kasa saukewa. Shima a ɓangaren Abba yayi Rama sosai Kuma Yana cikin damuwa wadda Shi kansa ya Rasa gane dalilin Hakan, Yana Jin k Ƙunci sosai a zuciyar sa Amma baisan Ko Na menene ba, Wani Irin nauyi yakeji a zuciyar sosai. Baya son Ko kaɗan ayi masa maganar Ahanaf. Ji yake Kamar zai mutu tsabar ƙiyayyar da yake yiwa gudan Jinin nasa. Duk Wani Abu da Abba yasan mallakin Ahanaf ne ya mayar dashi mallakin ƙanensa Al ƙaseem. Batare da Sani Abbu Ko Ayiya ba. ____________ Tsaye yake gefen Wani gidan Mai Yana Zane Zanen sa Sai faman Kore ƙuda yake a fuskarsa da ƙasumba ta taru sosai Saboda Rashin Samun gyara. Tsaye take a jikin Mota gefen gidan Mai. Tana bin layin mai Gajiya tayi da Zama cikin Motar yasa ta fito waje ta tsaya. Sai faman dan na waya take Tana ya mutsa fuska alamar tagaji da jiran layin Nan. Shabana! Shabana! Shabana! Wata matashiyar buduwar ce ke fitowa a cikin Motar tana kwala Kiran buduwar da Ke tsaya tana Dan na waya. Wace aka Kira da Shabana ce ta juyo cikin masifa da ƙufula Saboda jiran da take famanyi tin ɗa zu tace " Wai Ke Malama lafiya kike kwalamin Kira haka Kamar wacce taci Miki bashi? Tin ɗazu kina Mota zamanki kin barni a waje Ina faman jira Sai kace wata yarinyarki, Kuma Sai kifito kina min ihu a kunne Bana son irin wannan Kiran Karki ƙaramin irin sa wallahi. Dan Allah ya Isa haka masifaffiya Ke ba halin ayi miki Magana Sai ki Wani tasowa mutane da rigima. Kalla kiga Abunda nake Gani kodai idanuna ne suke gani ba daidai ba. Saitin hannunta Shabana tabi da kallo, Cikin mamaki ta ƙara gyara tsayuwar ta tare da Saka hannuwan ta ta murza Idanunta. Bata ma lura da wayarta da ta faɗi a ƙasa ta tarwatse ba tsabar ruɗanin da tashiga..............✍🏻✍️✍? ♣️DUHUN INUWA♣️ TAPING......📲📲 STORY AND WRITING✍️✍️✍️ BY NABEELAH SHEHU BINJI PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞 ```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)``` /https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/                   *P.W.A✍️* BISMILLAHHIR_RAHAMANIR_RAHIM PAGE 1️⃣2️⃣ _____________ Kai tsaye Gurin da Shadow yake Shabana ta nufa cikin sassarfa, dab da Shadow ta tsaya tana kallon Zanen da yake a Bango sake da baki Kamar wata wawiya, Tama kasa cewa ƙala tsabar mamaki. Buduwar da ke tare da Shabana ce ta ƙaraso kusa da su tace Ikon Allah Sai kallo. Haka suka tsaya Suna kallon Shadow Har yaƙarasa Zanensa Tass Tabɗijam "wannan mutum fa da alama Bashida issashen hankali but Duba kiga aikin da yake Kamar na Wani Mai cikakken hankali" tafaɗa a hankali cikin raɗa. Wannan ba Shakka Mahaukacine Hafeeza Amma Mai tattare da abubuwan Al ajabi, Taya Mahaukaci ya iya wannan Zanen? Shabana ta faɗa cikin mamaki. Shadow Yana Gama Zana Shabana ya juya Yana kallonta Yana jiran ta sallame sa, ita hankalinta Baya ma kansa kwata² Zanen Kanta Kawai take kallo,. Sai Daga Baya ta Maida hankalinta Kan Shadow tana murmushi tace "bawan Allah ya sunanka?" Kawar da kansa yayi gefe batare da yace Mata ƙala ba, Sake maimaita tambayar tayi Nan ma dai Shiru Shadow yaƙi yayi Magana. Kodai Baya Magana ne cewar Hafeeza Tana kallon Shadow. Bai kallesu ba Kuma Bai tan kasu ba. Jakar hannunta Shabana ta buɗe ta ɗauko kuɗi masu yawa tabama Shadow tace gashi Malam. Kuɗin ya Kalla ya ɗauke kansa alamar Baya so. Wasu kuɗin taƙara Akan na farko ta bashi Nan ma yaƙi karɓa. Shabana batan San cewa "Shadow ba kuɗi yake So ba Shi Abinda yaci yake nema, tunda ya fahimci Idan ya zana mutum Akan ɗauki abinci a bashi, Sai ya Maida hakan Kamar sana'a duk lkcn da yaji yunwa yakan Zana duk Wanda yake kusa da Shi, Idan ka bashi Abinci ya karɓa yaci Idan ka bashi kuɗi Kuma Sai ya Tafiyar sa. Yanzu ma Hakan ce tafaru dan fafir Shadow yaƙi ya karɓi kuɗin da Shabana ta bashi. Tohm Shi wannan me yake so Kenan? Cewar Shabana Tana kallon Hafeeza. Oho Kuma kinga yaƙi Magana balle musan Abunda yake so. Tafiya Shadow ya Farayi Yana Sosa kansa da yasha datti Yana Masa ƙaiƙayi. Bayansa Shabana tabi Tana faɗin bawan Allah mekake so ne? Ko kulata Shadow baiyi ba ya tsallaka titi ya tafi Abunsa. Tsayawa tayi tana kallonsa har ya ɓacema ganinta juyawa tayi ta Kuma Gurin Hafeeza jikinta ba ƙwari. Sai ɗaukar hoton Zanen Hafeeza keyi, kallon fuskar Shabana tayi taga ba ɗigon walwala a tare da ita, Hafeeza tace dan Allah kizo kusa da Zanen Nan Na ɗauki hoton yadda Zan ƙara kafa shaida da kayan jikinki tunda Har su ya Zana. Ba musu Shabana ta matsa kusa da Zanen Hafeeza tayi Mata hotona masu kyau. Tafe suke cikin Mota Hafeeza ta kalli Shabana tace "Kai Wallahi Mahaukacin Nan fa ya kwashi gayya kinga fa kusan mutane 27 ne su kace Suna Son wannan Mai Zanen ya Zanasu" Murmushi Kawai Shabana tayi batare da tace wa Hafeeza ƙalaba. _________Bayan sati ɗaya A kullum Shabana Sai tayi tunanin wannan Mahaukacin da Ko sunansa batasani ba, haka Kawai takejin Tana son sake haɗuwa dashi. Taje gidan Man da tafara ganinsa yafi a ƙirga Amma Bata sake ganin Ko Mai kama dashi ba. Takan tsaya Gurin da Zanen yake ta ƙura Masa Ido Kamar wacce Bata taɓa ganinsa ba. Har masu aiki gidan Man sun Saba da ganin Shabana, saboda Idan tazo takan kwashe kusan sa'a ɗaya agurin Tana jira taga ko wannan Mahaukacin zaizo Idan tagaji da tsayuwa Sai ta buɗe Mota ta zauna. Amma Haka zata ƙaraci zamanta ba Shadow ba alamar sa. Cikin firgici Shabana ta tashi zaune Kan makeken gadonta, tana furta Kalmar Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raju'un, Hannayenta tasa ta dafe Kanta da yake matuƙar Sara Mata tamkar Zai tsage gida biyu. Runtse idonta tayi tare da cewa Oh! Allah Gani gareka, "wannan wane kalar Mahaukaci ne? Kodai da Aljani nayi gamo ne?" Tun lkcn da nayi tozali dashi nakasa samun sukuni, kullum Sai Na tunashi yafi a ƙirga na Rasa dalilin da yasa nakasa mantawa dashi. A hankali tafara buɗe idanunta da suke cike da tsantsar damuwa tafara sau kowa daga kan gadon. Kai tsaye toilet ta nufa, bajimawa ta fito kaya tasaka ta ɗauki car key ɗinta tafita cikin sauri. Wani ɗaki ta nufa Tura ƙofar tayi bakinta ɗauke da sallama. Matar dake tsaye Tana waya ce ta amsa sallamar Tana bin Shabana da kallon tuhuma. Dagani Babu tambaya wannan farar dattijuwar mahaifiyar Shabana ce Cox Suna masifar Kama da Juna. Bayan ta gama ne ta sauke wayar daga kunnenta tare da Cewa "Sai Ina Kuma? Keda Kika ce kanki na Miki ciwo sosai" Tafaɗa tana ƙure Shabana da manyan idanunta Dan talura yarinyar Tata tafara sauya halayenta. Duk Wanda yasan Shabana yasan rigimammiya ce ta ƙarshe, but yanzu tazama wata silent kamar ba ita ba. Kanta taɗan Sosa tare da cewa gidansu Hafeeza zanje Ammi. Bazakije ba cewar Ammi tana ɗaure fuskarta, Kusa da ita Shabana ta matsa tare da rungumeta ajikinta cikin shagwaɓa tace Dan Allah kiyi haƙuri Ammi kibarni naje akwai Abunda zamuyi ne. Harara Ammi ta ɓalla Mata Ai kullum zan cen ki kenan, Kifita daga idona Na rufe Shabana Naga kina so ki ɓaci da yawo yanzu Wanda da ba halinki bane. Kije Allah ya tsare Amma Dan Allah Karki yadda mahaifinki ya dawo gida baki dawo ba. Kinfi kowa sanin halinsa Idan yafara faɗa kamar Zai tayar da gari Ammi tafaɗa tana Dariya. Ita ma Shabana dariyar tayi tare da cewa insha Allah Zan dawo da wuri Ammi. Tohm Allah ya yadda Ameen ya Allah. Har ta buɗe ƙofar zata fita tajuya tana kallon Ammin taɗan marairaice fuska tace bakimin Addu'a bafa Ammi. Murmushi Ammi tayi tare da cewa Allah ga ƴata zata fita, yadda tabar gida lafiya ya Rabi ka mayar min da ita lafiya, Allah kayi Mata Albarka Kuma ka tsareta da sharrin mutum ko aljan. Wata sassanyar ajiyar zuciya Shabana tasaki tare da furta Ameen ya Rab Ammina tana murmushi. Fita tayi daga gidan ranta fari ƙal ba yaune mahaifiyarta ta Saba yi Mata Addu'a ba Amma Sai taji tafi Jin daɗin ta Yau fiya da ta kullum. Duk lokacin da zata fita Sai Ammi ta mata Addu'a sannan take tafiya tun tanada ƙurciya take wannan halin nata shiyasa Ammi ke matuƙar ƙaunarta. Kai tsaye gidansu Hafeeza tanufa a Palo ta Tarar da ita zaune tana cin Abinci. Wata uwar harara Shabana ta ɓalla mata tare da cewa acici mala'ikun tukunya. Dariya Hafeeza zayi tare da cewa oh ni Hafeeza naga ta kaina da ace ke kike ciyar Dani da na Boni Kenan. Ba halin kiganni Ina cin Abinci Sai kin min gori? tohm Bismillah zo kema kici Hafeeza ta faɗa Tana murmushi. Ya mutsa fuska Shabana tayi sannan tace ke Malama ni ba wannanne ya kawoni ba zuwa nayi ki rakani gidan Mai plz. Cike da mamaki Hafeeza ke kallonta tare da cewa ba kince bazaki Koma neman Sa ba? Kirufawa kanki Asiri Shabana maybe fa wannan Mahaukacin ba mutum bane tun fa wannan lokacin bamu ƙara ganinsa ba har Yau. Kusa da ita Shabana ta zauna tare da sauke ajiyar zuciya tace "Naso matuƙa na manta da wannan Mahaukacin amma nakasa Hafeeza kullum lamarinsa ƙara girma yake a cikin zuciya ta, Hafeeza bansan wannan Mahaukacin ba hasali ma Gani ɗaya na taɓa Masa a rayuwata. Amma narasa dalilin da yasa nakasa mantawa dashi nakasa manta fuskarsa nakasa manta kallon da naga Yana mun" Hafeeza kallon da yake min kallone Wanda yake ɗauke da abubuwa da dama Neman taimako neman tausayawa Amma nakasa taimakon sa Cox ban san Abunda yake so ba bansan menene a cikin zuciyar sa ba Amma tabbas a wannan lokacin akwai Abunda yake so agurina Kuma nakasa sanin Menene" Hafeeza intaƙaice miki zance yanzu ma daga bacci na tashi Kuma nayi mafarkin wannan "Mahaukacin still irin wannan kallon Naga yana min kamar Koda yaushe Idan nayi mafarkinsa" tafaɗa tana goge guntun hawayen da ya taru a gefen idanunta. Tohm yanzu ya kikeso ayi Shabana? ta Ina zamu Sami wannan Mahaukacin? Sannan Idan Mun sameshi mai zaki masa ta Ina zaki taimakeshi? Hafeeza ta faɗa Tana ƙure Shabana da Ido. Numfashi Shabana ta furzar tare da gyara Zamanta tace Nima kaina banida amsoshin waɗan nan tambayoyin naki Hafeeza, Abunda nasani kawai shine Ina son sake ganinsa. Kallonta Hafeeza tayi ta girgiza Kai tace okay Bari nashiga na shirya Sai muje. Murmushi Hafeeza tayi tace nagode Goty. Harara Hafeeza ta ɓalla Mata tace eh Ai duk lokacin da kike son yaudara ta haka kike kirana da Wani Goty na cuta. Gabaki ɗayansu dariya suka Saka. Nifa gaskiya na Fara gajiya Shabana tun ƙarfe Nawa muke nan gurin Kamar wasu marasa mafaɗa Muna zaman jiran Abunda ba tabbas. Maybe fa Ina ga bawan Allah nan ba lafiya yake ba Hafeeza. Idan baki Manta ba farkon ganin mu dashi irin lokacin ne Kuma kullum irin wannan lokacin nake zuwa Nan nayi ta faman jira but Shiru. Tsayuwa Hafeeza ta gyara tace to Kodai zamu tambayi masu Saida Man nan muji yaushe ne last ɗin zuwansa nan. Kai Shabana ta gyaɗa tabbas Abunda ya kamata muyi Kenan tun farko. Gurin masu Saka Mai su kaje, Bayan sun gaisa ne Shabana ta tambayeshi Shadow. Tana masa kwatance ya gane Wanda take nufi. Jim yayi kaɗan sannan yace tabbas Na gane Shi Amma gaskiya ya kwana biyu baizo nan gurin ba Hajiya. Hannunta ta dunƙule taɗan daki goshinta tace kashhhhhh! Kuma dan Allah bakasan gurin da zan iya samun sa ba? Kai ya girgiza yace gaskiya ban Sani ba Hajiya. Godiya suka masa sannan suka Shiga Mota suka nufi hanyar gida. Hanyar da sukabi ɗazu ba ita Shabana tabi ba, wata hanyar tabi daban. Kallonta Hafeeza tayi tace Madam ina zaki kaini ne? Kodai kema kin Sami taɓuwar hankali ne? Ko kulata Shabana batayi ba taci gaba driving ɗinta, dalilin da yasa Shabana ta canza hanya shine ganin Yamma tayi za'a iya samun cinkosun ababen Hawa. Ta wata sabuwar unguwa suka biyo unguwar sit ba hayani. Ke Dalla Malama kashe Mana wannan banzar waƙar Shabana tafaɗa tana hararar Hafeeza. Bazan kashe ba ba ruwanki da waƙata hausawa sunce Shan Koko buƙatar Rai dan haka ki barni da ra'ayina Tohm Wallahi baki Isa ba Sai kin kasheta, Shabana ta faɗa Tana ƙoƙarin kwace wayar hannu Hafeeza, gabaki ɗaya hankalinta ya bar Kan driving ɗinda take ya Koma Kan Hafeeza. Saiji tayi tabugi Abu kamar mutum da sauri ta take Burki kuuuuhhhhh tare da furta Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raju'un, cikin tashin hankali suka fito daga cikin Motar gabaki ɗaya Shabana ta ruɗe jikinta har rawa yake tsabar ruɗani, Cikin kuka tace na Shiga ukku Hafeeza nayi Kisan Kai Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raju'un. Riƙeta Hafeeza tayi tace kinutsu kidawo cikin hankalinki Shabana, nifa Gani nake kamar wannan Mahaukacin ne da kike nema......✍️✍️✍️ Nabeela Binji ce💃💃💃 More comment More taping 😉😉 Share Fisabilillah 🙏 ♣️DUHUN INUWA♣️ TAPING......📲📲 STORY AND WRITING✍️✍️✍️ BY NABEELAH SHEHU BINJI PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞 ```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)``` /https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/                   *P.W.A✍️* BISMILLAHHIR_RAHAMANIR_RAHIM PAGE 1️⃣3️⃣ ______________Ware idonta tayi da kyau tana kallon wanda ta buge ba Shakka wannan Mahaukacin ne da ta shafe sati ɗaya tana nema. Ya Allah yanzu ya zumuyi dashi Hafeeza? Ya Kuwa zamuyi dashi in Banda mukaishi asibiti cikin gaggawa, cewar Hafeeza Tana kwala Kiran Wasu samari da su kazo wuce wa ta gurin, Suna zuwa Hafeeza ta roƙesu dan Allah su taya su Saka Shadow a Mota, daga farko har sun so suƙi Amma ganin magiyar da Shabana take Musu ne yasa su kama Shadow suka saka musu Shi a Motar. Godiya suka Musu sosai sannan suka Shiga Mota suka bar layin da gudu Kamar zasu tashi Sama. Ki tafi a hankali mana Shabana haka ai Sai kisa mu sake Wani accident, kina driving na ganganci Kuma kina kallon Baya haba dan Allah. Shiru Shabana tayi Kamar bataji Abunda Hafeeza tace ba, ita Bata da burin da yawuce taganta A asibiti, gabaki ɗaya ta ruɗe ba Abunda zuciyarta keyi face bugawa da sauri sauri. Cikin Wani katafaren asibiti tashiga parking tayi a daidai gurinda ake parking motoci, cikin sauri ta fita har tana haɗawa da ɗan gudu gudu, takira waɗan da zasu shigar da Shadow ciki, A kan gadon asibiti suka ɗaura Shadow da ko motsi Baya yi suka Fara Tafiya dashi cikin sauri, Bayansu Shabana tabi har bakin ƙofar Wani ɗaki, shigar dashi ciki sukayi. Shabana tafara ƙoƙarin Shiga Amma sai suka hanata. Kiyi haƙuri kijira mufito Shabana ba'a Shiga nan ɗin kinji. Dan Allah kabarni nashiga Dr tafaɗa tana goge hawayen idonta. Da hakan zai yiyu da ba Abunda zaisa na hanaki Shiga kiyi haƙuri plx, cewar Dr Yana rufe ƙofar ɗakin alamar Baya so taƙara yi masa wata Maganar. Zama tayi a hankali Kan kujerun da suke gefen ɗakin tare da dafe Kanta da yake matuƙar Sara mata. Kusa da ita Hafeeza ta zauna ta dafa kafaɗarta tace dan Allah ki daina zubar da hawaye haka Shabana, ba kuka ne Abunda ya dace muyi ba, kamata yayi muyi masa Addu'a Allah yabashi lafiya kinji, Hafeeza ta faɗa cikin sigar lallashi da son kwantar wa Shabana da hankali. Saboda ita ma da Kanta ƙarfin hali take bataso tayi hawaye ne har Shabana tagani. Yanzu ya zanyi Hafeeza? Me zancewa Ammi? Kima janye zancen Ammi mezan cewa Dady? Kinfi kowa sanin halinsa Baya yiwa kowa uzri, yanzu abun nan da yafaru bazai taɓa yadda ƙaddara bane Saidai yace tuƙin ganganci ne. Dan Allah ki faɗamin menene mafita Hafeeza. Ta ƙarishe maganar tana fashewa da kuka mai sautin gaske. Rungumeta Hafeeza tayi tana bubbuga bayanta a hankali kidaina kuka Shabana insha Allah komai zaizo da sauƙi. Karɓi waya ki Kira Ammi ki faɗa Mata halinda ake ciki, dan wannan ba Abun aja baki ayi shuru bane. Wayar ta karɓar ƙirjinta ta Sai ƙara bugawa yake, No ɗin Ammi ta danna wa Kira cikin fargaba da tsinkewar zuciya, a ringing na biyu Ammi ta ɗaga tare dayin sallama, Cikin sanyi murya ta amsa sallamar tare da cewa barka war haka Ammi. Barka dai Shabana, kina lafiya Kuwa? Mai yake damunki? Naji sautin muryarki Kamar kina cikin damuwa. Ajiyar zuciya Shabana tayi tace akwai matsala Ammi, Wani na buge da Mota, yanzu haka Mun Kaisa asibiti nida Hafeeza, Ammi bansan awane hali yake ba, tsorona ɗaya Kar ya mutu a ta dalilina, Shabana tafaɗa cikin sautin Kuka. Ya subhanallah Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raju'un. Yanzu Mai Dr yace muku? A wane hali marar lafiyan yake? Basu fito ba Ammi Suna can tare dashi. Okay gani nan zuwa asibitin yanzu insha Allah zan kira mahaifinki na faɗa masa halinda ake ciki. Tohm Ammi na gode sosai Shabana ta faɗa Tana goge hawayen idonta. Ki kwantar da hankaliki kinji zai Samu lafiya da yardar Allah. Tohm Ammi insha Allah. Sun shafe awanni biyu suna jiran likitocin sufito daga ɗakin da aka Shiga da Shadow, da sauri Shabana ta miƙe tsaye tana tambayar Dr ya jikin nasa. Ku biyoni office shine Kawai Abunda Dr ya faɗa ya juya ya tafi Abunsa. Cikin sauri Ammi Hafeeza da Shabana suka bi Bayan Dr. Suna Shiga Dr Fahad ya Basu izinin zama, Gyaran murya yayi tare da zare glass ɗin dake saƙale a idonsa. Magana yafara cikin nutsuwa jikinsa da sauƙi alhmdllh, bawata matsala yanzu saidai ƴan raunukan da yasamu a kafa da Kuma gefen kansa, Suma ba wasu masu yawa bane, zai warke nan bada jimawa ba Insha Allah. Kallon Juna Shabana da Hafeeza sukayi cike da Al ajabi. to ya akayi Dr baiyi Magana akan taɓin hankalin wannan mutumen ba? Tambayar da take saƙale acikin zuciyoyinsu Kenan. Shabana ce ta kasa daurewa tace Dr Fahad kace bawata matsala fa? Kuma har gwajin kwakwalwa kun masa ba matsala? Shabana tafaɗa cikin mamaki. Ko Ina Mun Duba Shabana bawata matsala Kamar yadda na faɗa Miki tun a farko. Tabɗijam shine Abunda Shabana tasamu damar furtawa. Dr wannan mutumen Mahaukaci ne fa Yana da matsalar kwakwalwa. Anya kun bincikesa da kyau Kuwa? Cewar Hafeeza Tana kallon Dr Fahad tana son tasami cikakken bayani daga bakinsa. Mahaukaci Kuma Hafeeza? Koda yake ba Abun mamaki bane, tun daga Yanayin kayansa da kuma dattin da nagani a jikinsa nasan cewa Mahaukaci ne. Amma fa tabbas ba Abunda yake damun kwakwalwar sa.............✍️✍️✍️ Nabeela Binji ce💃💃💃 More comment More taping 😉😉 Share Fisabilillah 🙏. ♣️DUHUN INUWA♣️ TAPING......📲📲 STORY AND WRITING✍️✍️✍️ BY NABEELAH SHEHU BINJI PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞 ```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)``` /https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/                   *P.W.A✍️* BISMILLAHHIR_RAHAMANIR_RAHIM PAGE 1️⃣4️⃣ __________________Tabɗijam to Kodai sanadiyar accident ɗin da ya samu ne kwakwalwar sa ta dawo normal? Shabana ta faɗa Tana kallon Dr Fahad. Aa gaskiya cox raunin da yasamu kwata² ma bai Shafi kansa ba raunin iya hannu da ƙafarsa ne. Kuma tabbas Mun bincikesa sosai ba abinda yasamu kwakwalwar sa. Dr Fahad ya faɗa cike da kwarin gwiwa Iska Mai zafi Shabana ta furzar tare da cewa Iko Sai Allah, Kenan Dama wannan bawan Allah ba haukaci bane? Tohm Taya akayi mu kaganshi cikin yanayi na taɓuwar hankali? Hakan zata iya faruwa bisa dalilai guda biyu, Kodai shi ma'aikacin Sirrine ko kuma criminal ne Yake ɓuye kama a matsayin mai taɓin hankali, cewar Dr Yana kallon fuskar Shabana. Sunkuyar da Kanta tayi ƙasa Batare da tace komai ba, Amma har ranta Bata yarda da maganar Dr ba. Kallonta Ammi tayi cikin ɗaure fuska tace Ina kiksan Mahaukacin nan Shabana? Menene a cikin zuciyarki kike ƙoƙarin ɓoyemin? Kwana biyu naga kin canza sosai ba Kamar daba, Nida a iya sanina ba Abunda kike ɓoye min a rayuwa, duk Abunda kikayi daidai da ba daidai ba Sai kin faɗa min, saidai nayi miki faɗa Idan kinyi Rashin kyautawa, Amma kwana biyu kin canza Mai yasa? Ammi ta faɗa cikin ɓacin Rai. Dan Allah kiyi haƙuri Ammi Bari Idan Mun fita zanyi miki bayanin komai da komai insha Allah. Cewar Hafeeza cikin sigar rarrashi. Tashi Ammi tayi tafita daga office ɗin Hafeeza ta mara Mata Baya cikin sauri. Dr Zan iya Shiga na duba shi? No Shabana yanzu Yana buƙatar Hutu gaskiya Sai ƙarfe 9 zaki Samu damar ganinsa. Okay godiya nake Dr Ba kumi ranki yadaɗe. A parking lot ta Tarar dasu Ammi tsaye tana Magana da Hafeeza, Tana ƙarasowa Ammi ɗaure fuska tana ƙoƙarin Shiga Mota, Hakan yasa tabawa Shabana Baya. Rungumeta Shabana tayi cikin sauri tafara Magana Dan Allah kiyi haƙuri Ammi tabbas ni Mai laifi ce agurinki Amma Ina Neman afuwarki dan Allah, Idan kikayi fushi Dani a yanzu bansa waye zai tallafi lamarina ba, Dan Allah kijuyo ki fuskance ni Ammi zuyawar da kikayi kika Bani Baya ya Sare min gwiwa yasani cikin ƙunci fiye da tunani, Dan Allah kigafarceni Ammi, Shabana tafaɗa tana fashewa da kuka Mai tsuma zuciya. Cikin sauri Ammi tajuyo ta rungume Shabana Tana ɗan bubbuga bayanta a hankali. Kukan ya Isa haka kinji, nifa Dama ba fushi nake dake ba, Kawai Abunda ya ɓata min rai shine ɓoye min gaskiyar da kikayi Akan wannan mutumen. Ammi ta faɗa cikin sigar rarrashi tana cigaba da shafa Bayan Shabana. Ajiyar zuciya Shabana ta sauke tare da janye jikinta daga na Ammi Tana ɗan murmushin yaƙe tace nagode sosai Ammi. Ita ma Ammi murmushi tayi sannan tace tohm yanzu yaushe Zaki Kuma gida? dan nikam yanzu zan kuma Cox da misalin ƙarfe 8 Dadyn ki zai dawo gida, Inaso na Kuma kafin ya iso tafaɗa tana kallon Shabana. Ɗan sosa Kanta tayi sannan tace Ammi Dr yace Sai misalin ƙarfe 9 Zai farka, Toh ke yaushe zaki kuma gida kenan? Sunkuyar da Kanta tayi sannan tace Ammi nan nake so na kwana Dan Allah. Ido Ammi ta ware cikin mamaki tace kina cikin hankalinki kuwa? Ki kwanta Ina? kuma gurin wa? Baki Shabana ta buɗe da nufin sakeyin Magana Ammi ta ɗaga mata hannu alamar ba tason jin komai Daga bakinta. Hakan yasa taja bakinta tayi Shiru. Ammi tamaida kallonta Kan Hafeeza tace 9:30 tayi muku a gida Hafeeza wllhy Idan kuka wuce haka ranku Idan yayi dubu sai ya ɓaci, Ammi tafaɗa cikin ɗaure fuska. Yah Salam tohm agurin wa zamu barshi Ammi? Majinyaci ne fa, Kuma nice nan nayi sanadiyar shigarsa wannan halin Idan mukayi haka bamu kyauta Masa ba Ammi. Iya Abunda Zan iya Kenan, Kuma ki tanadi Abunda Zaki faɗa wa mahaifinki Akan mutumen da Kika kaɗe, nariga da nafara faɗa Masa Abunda ya faru ɗazu a waya, Nima nan Inaso naji Taya kika San Shi, kinfi kowa sanin halinsa mahaifinki ba Abunda ya tsana sama da ƙarya, Al Adar shice Idan an faɗa masa Magana Sai ya bincike asalinta kafin ya yanke hukunci. Ruwanki ne ki faɗa masa gaskiya ko kuma ki masa ƙarya. Ammi ta faɗa tare da buɗe mota Tashiga tabar asibitin. Cikin asibitin suka Koma Hafeeza ta zauna a kan ɗaya daga cikin kujerun da ke ƙofar ɗakin da akan kwantar da Shadow, Shabana Kuwa tsayawa tayi kusa da Hafeeza tare da jingina jikinta da Bango kamar wacce ke gadin Hafeezar. Ki zauna Mana Shabana Ai Har yanzu da sauran lokaci kafin ya farka fa 8:11. Bana buƙata shine Kawai Abunda Shabana tasamu damar furtawa a hankali. Tohm ai sai kiyita faman tsayuwar cewar Hafeeza a ƙufule. Ƙarfe 9 daidai Shabana ce tsaye a office ɗin Dr Fahad tace time ya cika Dr Zan iya shga yanzu? Murmushi yayi rigimammiyar Ammi Idan kina son Abu Toh tabbas ba Wanda zai zauna cikin kwanciyar hankali, Dr Fahad ya faɗa cikin zolaya. Ita ma murmushin tayi batare da tace komai ba. Dr yace okay muje muganshi maybe yanzu ya farka Insha Allah. Dr a gaba Shabana a bayansa a haka har suka ƙarasa ɗakin da Shadow yake, Hafeeza da Ke zaune Sai faman Danna wayarta take ta miƙe tsaye tare da gaida Dr Fahad. Amsawa yayi cikin sakin fuska tare da cewa ya Fama da rigimammiyar Ammi? Murmushi Hafeeza tayi sannan tace Muna kanyi Dr. Shabana tanajin duk Abunda suke faɗa Amma taƙi ta kulasu Cox ita Bata da burin da yawuce taga Shadow yanzu. Dr ne ya murɗa ƙofar suka Shiga zare Ido sukayi tare da furta Innalillahi Wa'inna illaihi Raju'un a tare tsantsar tashin hankali ɗauke a fuskukin su.............✍️✍️✍️✍️ Nabeela Binji ce💃💃💃 More comment More taping 😉😉 Share Fisabilillah 🙏. ♣️DUHUN INUWA♣️ TAPING......📲📲 STORY AND WRITING✍️✍️✍️ BY NABEELAH SHEHU BINJI PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞 ```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)``` /https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/                   *P.W.A✍️* BISMILLAHHIR_RAHAMANIR_RAHIM PAGE 1️⃣ 5️⃣ ________________ Idanun su tar Akan "Shadow da ya gama hargitsa kayan ɗakin, Jini Sai zuba yake a gurinda akayi masa dressing, Saboda ya bubbuge gurin, ya ƙara jiwa kansa ciwo" Kaga Abunda nake faɗa maka ko Dr na faɗa maka yana da taɓuwar hankali, Shabana ta faɗa cikin tashin hankali Saboda jinin da taga yana zuba daga jikin Shadow. Tafiya Dr yafara a hankali yana bin ɗakin da kallo har ya ƙarasa gurinda Shadow yake tsaye tamkar an dasashi. Hannunsa yayi ƙoƙorin riƙewa Amma Shadow yaƙi yarda Dr ya taɓa Shi, cikin sauri yaja da Baya. Sunyi magana har sungaji Shadow yaƙi yace musu uffan, Dr "kodai kurma ne? haka ma farkon ganin mu dashi nayi masa Magana Amma ko kallon gurinda nake baiyi ba" girgiza kai Dr yayi sannan yace "ba kurma bane Shabana yana Jin duk Abunda muke faɗa, maybe dai akwai Abunda ya hana shi Magana ne" toh mai ya kamata muyi masa yanzu? Shabana ta tambayi Dr Fahad idanunta akan Shadow tana kallon sa cike da tausayawa. Allurar bacci zamu ƙarayi masa tukkunna. Lokaci fa na Tafiya Shabana, yanzu 9:20 yakamata kizo muje gida Cewar Hafeeza Tana kallon wayar hannuta, Wani haushi ne yakama Shabana jitake kamar ta laftama Hafeeza Mari ko zataji sanyin a ranta, har tabuɗe baki da nufin tace ba zataje ba Amma tunawa da garganɗin Ammi yasa taja bakinta tayi shuru tare da Maida hankalinta Akan Dr Fahad tace masa zan tafi gida Dr Ammi tace karmuyi dare Dan Allah Dr ka Kula dashi kamasa duk Wani Abunda ya dace kuɗi ba matsla bane, Amma ina neman alfarmar a Kula dashi Kamar sauran mutane Dan Allah Dr, taƙarasa maganar cikin raunin murya. Ki kwantar da hankaliki inshallah zamu bashi kulawa yadda ya dace, mu ai taimakon mutane shine aikin mu inshallah za'ayi yadda kike So, Murmushi Shabana tayi tace Sai nakiraka naji halinda Ake ciki, ta faɗa tana kallon Shadow da tun ɗazu yake tsaye guri ɗaya Kamar Robot. Hanyar fita ta nufa batare da tasake Magana ba. Girgiza kai Hafeeza tace "Saida safe Dr" murmushi yayi yace Allah ya tashe mu lpia Hafeeza. Tafe suke cikin Mota ba Wanda yake Magana a cikinsu kowa da tunanin da yake a cikin ransa, a haka har suka ƙarasa gidan su Shabana, ƙofar gidan Hafeeza tayi parking, ta Kalli Shabana tace "madam Sai da safe zan kawo miki Motar ki, dare yayi Kuma kinsan Dai bazan hau Adaidaita ba yanzu. Buɗe Motar Shabana tayi ta fita, tana gyara mayafin kanta, gidan Baya ta buɗe ta ɗauko jakar Shadow wacce a lokacin da suka bigeshi sun ɗauko har jakar tasa, ta gefen Hafeeza ta koma a hankali ta furta sai da safe nagode Goty. Murmushi Hafeeza tayi sannan tace Allah ya tashemu lafiya. Cikin gidan Tashiga, ita kuma Hafeeza ta ɗauki hanyar gidansu a ɗari 360. Koda Shabana tashiga gida Bata Tarar da Ammi a parlour ba tasan tana gurin Dadyn ta, cikin sauri tashiga ɗakinta tare da aje jakar hannunta ta hau tuɓe kayan jikinta dan yanzu ba Abunda take buƙata sama da tayi wanka, toilet ta faɗa cikin sauri. Ta ɗauki lokaci kafin tafito. tana fitowa ta shirya ta saka wata dogowar Riga marar nauyi, hijab ta ɗaura Saman rigar sannan tafito waje cikin sauri, direct part ɗin Dadyn ta tanufa. Sallama tayi Saida taji an amsa mata sannan ta Tura ƙofar tashiga a hankali. Gaidasu tayi tare da yiwa Dadyn ta barka da zuwa, Amsawa yayi yana tsokanar ta da Auta iyayen rigima, Murmushi tayi sannan tace Dady Ai yanzu na girma na daina rigima ba Wanda nake tsokana ko Ammi? Taɓe baki Ammi tayi tace Ina Girma anan kullum ana Fama dake Kamar wata ƙaramar yarinya. Shagwaɓe fuska tayi tare da Maida kallonta kan Dady tace "Dady Kaji Abunda Ammi tace ko? Murmushi Dady yayi yace a'a Ni ba ruwa kunfi kusa keda Ammin taki, kin manta Wani lokaci Idan Kuka tashi haɗe min kai ku ke nakasa gane gaskiyar kowane lamari. Tohm yanzu nabar team ɗin Ammi nadawo team ɗinka Dady ta faɗa tare da matsawa kusa da Dadyn. Dukansu dariya sukayi, Ammi tace badai gyaran gyaran ba tayi Mai, indai Shabana ce yanzun nan zaku ɓata. Bazama mu ɓata ba ko daughter? Nodding ɗinkata tayi tana murmushi. Gyaran murya Dady yayi tare da ɗan ɗaure fuska Kamar bashine yake Wasa da dariya ba yanzu, cikin kakkausar murya wacce ba alamar Wasa a cikinta Dady yace "Shabana Ina so ki faɗa min gaskiya akan batun wanda kika bige ɗazu, mahaifiyarki tafara faɗamin Abunda yafaru a office ɗin Dr Fahad, allamu sun nuna cewa kinsan wannan mutumen, tunda har Dr yana faɗin ba mahaukaci bane Amma kekuma kina ƙoƙarin musa masa akan aikinsa. Ki gayamin Ina kika san Shi? Me yake tsakaninku? Taya ki kasan shi mahaukaci ne? Wasu yawu Shabana ta haɗe da kyar jikake kut, gabaki ɗaya ta ruɗe tama rasa mai zata cewa Dady, ita Dai tasan bawata alaƙa a tsakaninta da wannan mahaukacin Abu ɗaya tasani shine Yana bata Tausayi, tun Ranar da taɗaura idonta akanshi takasa mantashi takasa Manta kallon da taga yana mata, tundaga ranar kullum sai tayi mafarkinsa..... Ke muke saurare, maganar Dady ta maidata cikin hankalinta. A hankali ta buɗe bakinta tafara Magana cikin sanyin murya tace "ba Abunda yake tsakanina dashi Dady hasalima sau ɗaya na taɓa ganinshi a rayuwa Sai kuma Yau Dana Masa Gani na biyu! Nan Shabana tabama iyayenta labarin duk Abunda yafaru, tare da nuna masu Zanen da Shadow yayi nata. Gyaɗa kai Dady yayi sannan yace zaki iya faɗamin wane gidan Mai ne kuka Fara haɗuwa dashi. Eh Dady gidan Man AA Rano. Okay zaki iya Tafiya. Tashi tayi jiki ba ƙwari tare da cewa Sai da safenku. Allah ya bamu Alkhairi. Tana fitowa daga ɗakin direct dining area ta nufa, Abinci ta Saka kaɗan tafara ci cox rabonta da Abinci tun 12pm. tana gamawa ta Koma ɗakinta a gefen gado ta zauna tana danna waryata idanunta suka faɗa kan jakar Shadow, Ido tazuba tana kallon jakar ba Shakka wannan tsadaddar jaka ce kuma daga ganinta kasan bata Wani tsufa ba datti ne Kawai matsalar ta. A hankali tasaka hannunta ta ɗauko jakar, buɗeta tayi tana Duba abubuwan da ke ciki, duk kayan Zane ne wasu ma har sun Fara bushewa, Haka taci gaba da duba saƙo da Lungu na jakar Wani zip ta buɗe taci araba da wasu takardu, ɗaukosu tayi ta fara buɗewa a hankali. Ido ta ware tana Duba takardar da kyau tirƙashi shine Abunda Shabana ta furta cikin mamaki..............✍️✍️✍️ Nabeela Binji ce💃💃💃 More comment More taping 😉😉 Share Fisabilillah 🙏. ♣️DUHUN INUWA♣️ TAPING......📲📲 STORY AND WRITING✍️✍️✍️ BY NABEELAH SHEHU BINJI PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞 ```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)``` /https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/                   *P.W.A✍️* BISMILLAHHIR_RAHAMANIR_RAHIM PAGE 1️⃣ 6️⃣ ____________________ Zanen wannan mahaukacin tagani raɗau Akan pepper kamar an ɗauki photon sa, ban banci kaɗan ne ƙasumbar sa da taƙara yawa Kuma Bata samun Kulawa kamar yadda yake a Zanen Amma kallo ɗaya zaka masa kagane shine a Kan pepper. Rubutun da yake a ƙasan Zanen ne yaja hankalinta, Ahanaf Muhammad Imran (SHADOW THE BEST ARTIST) Shine Abunda tagani a ƙasan Zanen ta maimaita sunan yafi a ƙirga tana juya takardar a hannunta tana kallo cike da mamaki. Ɗayar pepper ta buɗe Shima Wani Zanen taci Karo dashi Amma saidai wannan Zanen na mace ne, ƙurawa Zanen Ido tayi tana kallonta ba Shakka kyakyawa ce ajin farko ga Kuma Zanen ta yafita raɗau Kamar zatayi Magana. Ƙasa tayi da idonta tana kallon rubutun da yake a ƙasan Zanen wannan yafi na Shadow yawa Cox Shi ba iya Suna bane, a hankali tafara karantawa. Noriyya Mukhtar Salah (Norr) Haƙiƙa ke ɗin haskena ce Kuma Abar so da ƙaunata, Ina sonki fiye da So Ina ƙuanarki tamkar Raina Ke komai nace. I luv u from the bottom of my heart my Norr my wife. Ta karanta wannan rubuntun yafi sau Biyar, tamabayoyi ne da yawa suke yawo a kwakwalwar ta. Dama Yana da Mata ne? Menene dalilin taɓuwar hankalinsa? Daga wane guri yake? Kodai maganar Dr Fahad gaskiya ce? Batada Wanda zai amsa Mata waɗan nan tambayoyin Sai wannan mahaukacin Ahanaf Shadow Amma Taya Kenan? Wanda Har yanzu Bata Ji Maganar sa ba, Jin Kanta Yana mata ciwo ne yasa dole ta haɗa kayan tamayar dasu cikin jakar Amma Banda takardun da suke ɗauke da Zanen Shadow da Norr. Wayarta ta ɗauka ta Danna Kiran Dr Fahad. Bayan ya ɗaga ne take tambayar sa ya jikin Mara lafiyar? Tohm da sauƙi za'ace Dan wllhy da kyar na samu aka ririƙe shi na sake masa allurar bacci, Amma wannan Karon biyu nayi Masa Saboda na lura Yana da ƙarfin Jini, Idan akayi Masa ɗaya Zai iya farkwa kafin safe, Kuma kinga ba musan me zai iya faruwa cikin Daren ba. Hakan ma yayi Dr. Dr amma har yanzu baka yarda wannan mutumen mahaukaci bane ko? Aa Shabana bawai ban yarda bane na dai faɗa miki gaskiyar Abunda bincikena ya nuna min ne a kansa, bashida ko wace cuta a kwakwalwar sa gaskiya, Kuma Duk Inda zaki kaishi a duba shi wannan amsar za'a baki. Ya Allah to wai mai yake faruwa ne? Shi ba mahaukaci ba kuma ya dinga jiwa kansa ciwo? Tabbas wannan lamarin a kwai DUHUN INUWA a ciki wanda ya hana mu gane gaskiyar Hasken sa. Babbar matsalar ma shine Rashin maganar sa Dr. Hakane Shabana Amma yanzu mufara ganin yasamu sauƙin raunin da ke jikinsa sannan sai musan me yakamata muyi nan gaba. Okay nagode Dr anan sukayi sallama ta kashe wayarta. Gyara kwanciya tayi tare da furzar da Iskar bakinta, tambayoyi ne da yawa a Ranta Amma ta rasa mai amsa mata su. A haka dai har bacci ɓarawo yayi awon gaba da ita. Da safe Misalin 9am Zaune take a parlour tana breakfast wayar tace tafara ringing da sauri tayi pickup ganin sunan Dr Fahad ne a kan screen ɗin wayarta. Bayan sun gaisane yace " kizo yanzu Shabana akwai matsala gaskiya" da sauri tasaki fork ɗin da yake hannunta tare da cewa matsala kuma Dr mai yafaru? Kawai Idan da Hali kizo yanzu. yana gama faɗar haka ya katse wayar sa. Ya Ilahi! Ɗakin ta tanufa tafara Shiri cikin sauri, tana gamawa ta fito parlour anan ta Tarar da iyayenta Bayan ta gaidasu ne Ammi take tambayar Ina zuwa haka? Langwaɓar da Kanta tayi tare da cewa asibiti zanje Ammi yanzun nan Dr Fahad ya kirani yace wai nazo akwai matsala. Matsalar me? Dady ya tambayi Shabana. Nima bansani ba Dady yace dai sai nazo zanji. Kai ya gyaɗa tare da cewa tashi muje asibitin. Cikin sauri ta tashi tsaye Cox ta ƙosa ta Gakanta a gaban Dr Fahad. Sai Mun dawo Hajiya Dady ya faɗa yana kallon Ammi. Murmushi Ammi tayi tare da cewa Allah ya tsare hanya. Ameen ameen. Zaune suke a office ɗin Dr Fahad, Bayan sun gaisane yafara musu bayani yana duba takardun suke gabansa. Shakka Babu ban taɓa cikin karo da case ɗin Rashin lafiya irin wannan ba. Akwai ruɗani sosai a cikin wannan lamarin. Jiya da Misalin 1am Ina gida a kwance masu kula da wannan mutumen suka kira hankali tashe suke faɗamin cewa wai ya farka Sai jifa yake da kaya ya hargitsa Kumi da yake a ɗakin. Cikin sauri nazo asibitin natarar da abunda suka faɗa tabbas hakane, Kuma daga an buɗe ƙofa sai yadaina Abunda yakeyi yasamu guri ya tsaya cak kamar wani Robert. Hakan tasa nakira Wani abokina Dr Bilal Shi kwarraren likitan brain ne. A Daren muka tafi dashi asibitin su Dr Bilal suka sake Shiga dashi ɗakin na'ura suka Duba Shi. Amma Kuma kinsan menene Babban abun ban mamakin? Kai ta girgiza alamar a'a. Brain ɗinsa lafiya Lau take tamkar taki, tawa, Dama ta sauran mutane Dr ya faɗa yana kallon Shabana da taƙuresa da Ido tana kallonsa tun lokacin da yafara Magana. Sunkuyar da Kanta tayi ƙasa tama rasa mai zatace..........✍️✍️✍️ Nabeela Binji ce💃💃💃 More comment More taping 😉😉 Share Fisabilillah 🙏.