🪐 *ALK'AWARIN ALLAH* 🪐 _HUGUMA_ 0️⃣1️⃣ "Allah ya taimakeki" lafazin da ya shiga kunnenta kenan,lafazin da a bakin mutum daya take jinsa,furucin da ko mutuwa tayi ta dawo bata jin zata kasa tantance daga bakin wanda yake fitowa dare da rana,a hankali ta waiwaya fuskarta qunshe da murmushi,yana tsaye daga bayanta kamar koda yaushe,wannan annurin data saba gani kan fuskarshi kowanne lokaci na nan shimfide saman fuskarsa,kwarjini cikar zati da haiba cakude saman kyakkyawar fuskarsa,batasan me ya shigeta ba,sai taji bacin rai ya sauko mata a take,b'acin ran daya sanyata ta dinga ja da baya,ja da bayan daya zama silar data soma ganinshi dishi dishi,yana tsaye hannayenshi goye a k'irjinsa,dubanta yake ba tare daya tsaidata ko yace mata komai ba,saidai annurin fuskarshi ya ragu cikin kaso d'ari zuwa kaso ashirin cikin d'ari. A firgice ta farka,sa'annan tayi zumbur ta miqe tayi zaman dirshan saman gadon nata,dukka hannayenta ta sanya ta dafe kanta dasu bayan ta dora gwiwar hannunta saman cinyoyinta,gashinta mai tsaho da sulbi ya sako ya rufe fuska da hannayen nata gaba daya,inda zaka ga fuskarta a sannan zazzafan hawaye ne ke layi saman kuncinta,inda ace tana da iko data hana kanta mafarkinsa,da ta isa data hanashi bayyana a duniyar mafarkinta,sam ko kusa ko alama bata da buqatarsa a duniyar mafarkinta kamar yadda bata da buqatarsa a zahiri "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un" idan ka kasa kunnenka da kyau zakaji tana fada cikin muryar kuka. Ta jima cikin wannan yanayin kafin ta iya lallashin zuciyarta,kanta ta dago sannan ta sanya hannayenta guda biyu ta tattare gashinta baya ta daureshi,kyakkyawa kuma sassanyar fuskarta datayi jajur ta kuma tasa saboda kukan data yi ta fito fes duk da qarancin haske da d'akin keda shi,a hankali ta zuro qafafunta qasa sannan ta yunqura ta miqe,kai tsaye ta nufi wata qofa dake kallon gadonta ta murda ta shige. Mintuna biyar kyawawa tayi ta fito daure da alwala,ta bude ma'ajiyar kayanta ta fidda after dress da hijabi ta sanya,sannan ta nufi wani kebantaccen waje dake daura da gadonta tahau saman abun sallar dake shimfide a wajen ta kabbara sallah. Ita kanta batasan adadin lokutan data kashe zaune saman abun sallar ba,don sam bata marmarin sake komawa barcin da tayi mafarkinsa a ciki,saidai shi bacci ba wanda yafi qarfinsa,saboda haka sanda yazo yayi awan gaba da ita bata shiryawa hakan ba,sai jingina da tayi da jikin gadon,carbin hannunta kuma ya silale ya fadi nan saman dardumar. ******* **** ******** Qarfe takwas na safiya ta kammala shirinta tsaf,tsaye tayi kawai tayi gaban mudubin tana qarewa kanta kallo,tayi kyau iya kyau,irin kyan nan mai sanyi,saidai wasu abubuwa da suka soma mata yawo akai take suka d'auke duk wata sauran walwala da taketa yunqurin d'orawa fuskarta,qarar kira daya shigo wayarta yaso janye hankalinta,saita zubawa wayar dake gefan mudubin ido tana kallonta ba tare data tabata ba gudun zuciyarta na qaruwa,bata kuma da niyyar hakan ma gaba daya,har ta qaraci b'urarinta ta katse,tamkar mai jira kiran ya katse din kuwa tayi gaggawar surar wayar ta kasheta gaba daya sannan ta jawo locker din madubin ta jefata ta maidata ta rufe. Cikin kasala kamar wadda tayi wani babban aiki ta koma da baya ta zauna gefan gadonta tana ci gaba da kallon fuskarta cikin mudubi,ko kad'an bata qaunar ta raba wani abu ajikinta da zai sata tayi kyau,don dai kawai bata k'aunar bata ran anty zubaida ne,amma da bata ga dalili ko alfanun kasancewarta a haka ba. "Auntyyyyy...." Muryar huda ce ta ratsa kunnenta,firgigit tayi tana dubanta kafin ta samu qaqaro murmushi wa fuskarta "Anty ina kwana" "Lafiya huda ta,kin shirya kenan?" Ta furta tana janyo yarinyar kusa da ita tana gyara mata daurin jelar rigar makarantar dake jikinta "Ummi tace ki fito karmu makara" "Muje na gama ai,fitowa kawai xanyi" ta fada tana miqewa,ta qarasa ma'ajiyar jakankunanta ta ciro daya daga ciki da zata dace da shigarta,sannan ta dauko wata daban ta zuge,ta fiddo da tarkacen ciki ta maida wadda zata fitan da ita sannan ta kama hannun huda suka fice. A kitchen suka tadda anty zubaida tsaye tana shirya lunch box din huda,sanye take da rigar bacci da qaramin hijabi,kallo daya anty zubaidan tayi mata ta karanci yanayin data shiga,don haka bayan sun gama gaisawa ta shigar da qorafinta "Yauma kinyi halin ne?" Murmushi kawai tayi wanda ya fito da ciwo tun daga zuciyarta zuwa labbanta,maimakon ta amsata saita shigo da wata maganar "Yanzu anty dan Allah ta yaya zanci gaba da kwanciya kina tashi kina girki bayan kula da uncle aby da kike?" "In kinason komawa kitchen sai kiyo qoqarin maida mode dinki yadda yake....." Cikin seriouse ness ta waiwayo tana dubanta "Cikin shekaru biyu mun soma yin nasara shahida....saidai bansan meke neman tarwatsa nasarar da muka samu muka yi ta tsahon shekara biyun ba" ta fada cikin nuna damuwa,shuru shahida tayi tana k'okarin kokawa da damuwar data taso mata,tun lokacin data san cewa suna rayuwa ne ashe cikin gari d'aya da anwar bata sake samun peace of mind ba,murmushin yaqe kawai ta jefi anty zubaida dashi,don bata son dukkan abinda zai sake jagula nutsuwar da take ta yunqurin samarwa kanta,shuru ne ya ratsa tsakani,ganin bata da niyyar magana anty zubaidan ta saki hannayenta tana dauko lunch boxs din huda ta miqa mata gami da cewa "Shikenan,ku wuce ku karya karku makara,amma dai.....kota halin qaqa karki bari abinda ya riga ya gabata a rayuwarki ya bata future dinki,koda anwar ko babu ki baiwa kanki qwarin gwiwar xaki rayu,rayuwa mai inganci...." "Zan rayu babu shi ne anty rayuwa mai inganci,babu batunshi ma cikin babin rayuwata" ta fada wani radadi na tasowa tun daga cikin zuciyarta har saman fuskarta,murmushin da ita kadai tasan ma'anarsa anty zubaida ta sako,shahida mutum ce me confidence,tana da qwarin gwiwa saidai har zuwa yau kaman hakan yaqi tasiri ga wannan lamarin,duk da koda yaushe tana yunquri da fadi tashin baiwa kanta wannan qwarin gwiwar,da idanu ta bisu har suka fice daga kitchen din ita da huda sannan ta saki ajiyar zuciya tana yiwa deejan addu'a a fili da zuciyarta. Suna gama karyawar abby ya fito,sanye yake da jallabiyya,mutum d'an kimanin shekara arba'in da takwas,mai cikar kamala da fara'a,cikin girmamawa shahida ta gaidashi,ya amsa fuskarsa qunshe da fara'a yana fadin "Teacher uban karatu....baku wuce ba kenan?,hala yau keda dalibar taki tare zakusha bulalar latti" murmushi ta fidda,tana mamakin abbyn sau da dama,wuta ne shi a wasu lokutan,amma wani lokacin yafi xuma dad'i "Yanzun nan zamu wuce abby" ta fadi tana sab'a jakarta "Gwara kam,don qila hadi(mai adaidaitan dake kaisu makaranta)yana waje yana jiranku na sanshi da himma" dai dai sanda anty zubaida ta fito daga kitchen din sukayi mata sallama suka wuce. A bakin k'aton gate din *NOOR INTERNATIONAL ACADEMY* ya saukesu "Daganan zan kai adaidaitan wajen gyara....amma zanyi qoqari in sha Allahu na dawo na d'aukeku" "Karka damu,yauma muna shirye shiryen wasu abubuwa da za'a gudanar a makarantar,ina zaton ma zamu d'ara lokacin tashi,zamu bi ta haya mu koma" "To na gode,amma du da haka idan na gama akan lokaci zanzo" bata sake ce masa komai ba ta kama hannun huda suka ratsa gate din makarantar zuwa ciki. Dukansu ita da hudan sashen 'yan nursery da primary suka nufa,saboda a nan ne deejan ta zabama kanta ta koyar,duk da tarin ilimi da Allah ya bata,wanda tana da cikakkiyar damar da zatayi lacturing amma bisa wani dalili nata ta zabi koyarwa a qaramin mataki na 'yan nursery da primary,tun daga bakin section din yara ke gaidata cikin nuna qauna da soyayya,yayin da ita kuma take amsa musu cikin fara'a da jansu a jiki,sai da zata shiga staffroom sannan suka rabu da yaran,suka wuce azuzuwansu ita kuma ta shiga ofishin malamai. Office ne madaidaici mai girma da tsari,duk da girman office din su uku ne kacal a ciki,makaranta ce da kallon farko.idan kayi mata zakayi tsammanin private ce irin mai tsadar nan,saidai sam ba haka abun yake ba,makaranta ce da wani shahararren d'an kasuwa ya ginata saidai akwai sa'ido da kulawar gwamanti akanta,duk da cewa shike dauke da duk wani nauyi na makarantar,kama daga school unifoarm,littafan karatu,abincin da yaran zasuci na break da dai sauran dukkan wasu lalurori,aqidarshi ce haka,yakan gina makarantar a duk inda yaga hakan ya dace,ya kuma hada hannu da gwamnatin garin donta tayashi lura da makarantar,bawai lura na su bada wani abu ba,a'ah,tsarin gudanarwa tsaro da sauran abubuwan da ya kamata,kusan kowacce qasa dake africa ya gina makarantu d'aya,saidai a inda makarantun suka fi yawa a nigeria ne yankin arewa,duk dalibin dake karatu cikinta yana farinciki haka iyayensa farinciki da kasancewar dansu a cikinta,saboda ta tsaru da tsari mai kyau,hakanan tana da dukkan wani qualities da akeson makaranta dashi. Hidaya kawai ta samu cikin office din tana hada littafan dalibai da tayi marking,da alama tana da ajine qarfe takwas,murmushi suka yiwa junansu "Kinso makara yau malama shahida" "Yau da gobe hidaya...." Ta fada tana zaman kan kujerar teburinta. "Sai Allah..." Hidayan ta qarasa mata kana ta gyara yafen mayafinta "Mun tashi lpy...."cewar hidaya "alhmdlh....mun godewa Allah" "Ma sha Allah....zan wuce aji don Allah idan kausar ta iso kice mata ga kayan nan ta duba" "Babu damuwa" cewar shahida,tana kallon hidaya ta bude office din ta fice sannan ta maida qofar ta rufe musu,saita maida kanta a hankali ta kwantar saman teburin dake gabanta,idanunta a lumshe,batason tuna komai,batason tunanin komai,tanason ta saita kanta kafin lokacin shigarta aji yayi,don nan da minti goma sha biyar periode dinta zai shiga. *********************** "Dukkanin takardun na cikin wannan file din,sauran takardun da za'ayi amfani dasu a d'akin taron ma gab suke da kammala,na shiga dakin buga takardun na musu magana sunce nan da mintina goma da izinin Allah....engine ne yaso basu matsala" mutumin d'an kimanin shekara arba'in dake zaune saman d'aya daga cikin qawatattun kujerun dake shirye a qayataccen office din ya fada,yana bayanin ne ga dogo kuma tsayayyen matashin dake tsaye tsakiyar office din yana kai kawo a hankali,hannunshi riqe da dan madaidaicin glass cup,yayin da d'aya hannun nasa yake riqe da wata zungureriyar takarda yana dubawa,sanye yake da suit masu azabar kyau da d'aukar idanu,wankan tarwada ne shi,dogo wanda ke tafe da tsaho da kuma 'yar qiba kadan,wadda kai tsaye ba zaka kirata da qiba ta zahiri ba saidai ace murjewar jiki,doguwar fuska gareshi wadda take cikakka,lumsassun idanu mai kama da wanda kejin bacci,saidai da girmansu idan ya budesu sosai aduk sanda yaso hakan,bashi da cikar gashin gira can,saidai gashin idanunshi a cike suke,siraran labba masu taushi,da qawataccen qasumba da aka gyarata aka rage mata yawa da fadi,ta zagaya ta hade da habarsa da kuma qasan hancinsa,kanshi saisaye ne wanda ya qawata fuskarshi saboda gyaran fuska da aka yi masa,kana kallonshi kasan tsafta hutu da iya dressing sun kama gida a wajensa,kana kallonshi kasan ba ma'abocin fara'a bane,sosai ya bada hankalinsa kacokam kan takardar hannunsa da gani kasan abune mai muhimmanci yake dubawa,yayin da ta wani b'angaren daban ya bada hankalinsa ga wanda ke masa bayanin "Ina imran?" "Yana sashen aje tsaffi da sabbin qarafa" kai ya gyada yana ci gaba da takawa sannu a hankali,har yanzu hankalinsa na kan takardar hannunsa "Amma ba tuni na bada umarnin a cire wancan a sanya sabon da mukayo order ba?" "Sorry sir.....engineer din ake dako,yaudai yayi alqawarin zuwa ya hada" ya fada cikin nuna tsantsar ladabi,bai sake cewa komai ba har na tsahon wasu mintina,sannan ya isa gaban teburinshi ya aje kofin hannunsa,ya taka zuwa gaban matashin dake zaune ya bude files din dake gabansa ya sanya takardar ciki ya rufe,sai a sannan ya dubeshi "Karku wuce qarfe biyu ba'a gama kammala komai ba,bana son delay...."kafin ya gama fada qofar office din nashi dake aiki da lantarki ta bude da kanta,wanda hakan ke nuna muhimmin mutum ne zai shigo ciki,don ba kasafai take budewar da kanta ba sai bayan sakatariyarshi ta sanar masa ya bada umarni sannan ta bude din. Dukkansu maida idonsu sukayi kan qofar,tun kafin ta qarasa shigowa ya fahimci wacece,hakan ya sanya ya maida idanunsa kan yaqub,don bashi da tabbacin yanayin da zata shigo dashi,don haka ya sallameshi "shikenan....zaka iya tafiya" a bakin qofar sukayi clashing da ita tana shigowa,cike da girmamawa ya rusuna yana miqa mata gaisuwa,kaman yadda aka saba haka ta amsa a daqile,cike da izza,shan qamshi taqama da isa,yaqub ya wuce ita kuma taci gaba da takowa cikin office din. Fuskarta qunshe da murmushi,hakanan idanunta na kan fuskarshi,taku take d'ai d'ai harta kusa cimmasa,yayin da shi kuma yake kallonta yana nazarin shigarta,babu laifi shigar tata tayau,doguwar riga ce mai wrapper,saidai kuma gajeran hannu ce,tayi rolling mayafi qarami a kanta,high hill ta saka a qafafunta,hannunta ba komai daga waya sai key din motarta "It seems kamar bakayi farinciki da ganina ba M.A" ta fada a shagwabe tana kallonshi "Uhummm....who told you?" "Ba kowa....kawai yau nayi missing ganin cute face dinka,ka fita tun da sassafe ban samu ganinka ba,me yasa baka yi break fast ba yau a gida?" Takawa yayi zuwa d'aya daga cikin kujerun wajen yayiwa kanshi mazauni,itama yayi mata nuni da yatsa yana nufin ta zauna,sai data zauna sannan yace "Me yasa zaki fito a irin wannan lokacin?" Farrr tayi da ido,tana jin wani dad'i na ratsata,a duk sanda ya nuna kulawa a gareta takanji babu ya ita a fadin duniya,sai data saki murmushi sannan tace "Kai kadai na fito don na gani,kasan bazan iya wuni ban ganka ba" shuru yayi yana dubanta,can qasan ranshi yana jinjina wanne irin so nafisa ke masa?,kalamanta sunyi shigen kama da na wata,wadda ya soma qoqari da kokawar badda ta daga ranshi a yanzun da takeson taso mishi,don ko kusa bashi da sha'awar hakan,itama kallonshi take,tasan cewa wannan plan din nata ya d'anu,tanason dukkan wasu kalamai nata da yanayin kulawa yayi kama dana waccar da tasan ta taba wanzuwa cikin rayuwarshi,duk da tana baqinciki da cewa kwaikwayonta shine zai sama mata wani gurbi data dauki tsahon lokaci tana neman samu a zuciyarsa,duk da irin baqin fenti da qin jini da yayyabe tarihinta a zuciyarsa,amma duk da haka kishinta take fiye da komai a rayuwarta "Naso na iso tun dazun sai aka samu akasi" ta katse kallon kallon da sukema juna,dan muskutawa yayi kadan,cikin muryarshi dake nuna halayyarshi yace "Akasi?,name fa?" Sai data d'an jaa fasali sannan ta sake cewa "Wallahi wasu 'yammata ne suka so yiwa motata b'arna..." "Me ya gamoki dasu?" Ya tambayeta kai tsaye yana ci gaba da dubanta,kafad'a ta daga sannan tace "No,karka damu,na musu uzuri saboda a make suke,kana ganinsu kasan sunsan sirrin shan syrup,har zan hadasu da police sai kuma na wuce don bai kamata na b'ata lokacina akansu ba" sexy eyes dinshi ya lumshe gaba dayansu,yana jin wani abu mai ciwo na sauka saman zuciyarshi kamar ana d'iga masa wuta,wani boyayyen murmushi ta saki sannan cikin shagwaba tace "Karka damu nawan....ba abinda ya faru dani,am safe..." Bude idanun nasa yayi kaman zai kalleta saiya kalli wani sashe na daban,yana sauke ajiyar zuciya a boye,a duk sanda yaji ko yaga labari irin wannan babu wadda yake tunawa sai ita,hakanan haushi tsana da qyamarta yakan sake ninkuwa a ransa. "Yaya" ta kirashi tana son kauda damuwar data ziyarceshi,tunda haqarta ta cimma ruwa "Yaune fa zamuje yaya?,don Allah karki sake cewa kana da wani uzurin" "Saura minti goma sha biyar mu shiga meeting....saidai bayan mun kammala kuma" ya fada yana miqewa a hankali kai tsaye ya wuce bandakin dake cikin office din nashi ta bishi da idanu tana tantamarsa. A hankali ya tura qofar bandakin sannan ya maidata ya kulle,gaban dan fanfon dake maqale a bango mai hade da madubi dake manne a samanshi ya isa,yasa dukka hannayenshi ya dafe sink din tangaran dake qasan famfon,qirjinsa na zafi haka zuciyarshi,ya jima a haka kanshi a duqe yana kokawar maida yanayinsa yadda yake sannan ya dago yana duban kanshi a madubin kamar baisan halittar kansa ba saiyau,maganganu yake da zuciyarshi,magana yake gayawa kansa wanda shi kadai yasan meke kai kawo a ranshi harna tsahon wasu lokutta sannan ya zare 'yar samam suit dinshi ya daura alwala bayan ya tattare dogon hannun ta ciki,sai daya saka dan qaramin towel ya tsane ruwan jikinsa sannan ya maida rigar ya fito. Da sauri ta jiyo a firgice suka hada idanu dashi,tana tsaye gaban wani dan qaramin akwatinsa da ake budeshi da lambobin sirri,wanda ta budeshi ta kuma soma fiddo wasu kayayyaki dake ciki,dauke idonsa yayi daga kallonta ya maida kan d'an akwatin dake zaune dirshan daga can wani saqo na office din,baya taja cikin rawar murya muryarta can qasa tace "Am sorry" baice mata uffan ya taka a hankali zuwa wajen,inda ta janye jikinta ta rabe a bango,ya durqusa ya dinga daukan kayan d'aya bayan d'aya yana maidasu muhallinsu,duk abu guda idan ya dauka yana jin kaman yana qarawa zuciyarsa nauyi ne. Har ya saka wani abu ya sake cirosu ya kalla,suna nan kamar yadda ta bashi su,hatta da ledarsu itace dai wadda ta qullesu a ciki,d last thing data bashi a tarayyarsu,da hanzari ya maidasu ya rufe sannan ya sauya lambobin sirrin ya miqe zuwa gaban teburinsa ya amsa wayar daketa burari,sai daya kammala a nutse sannan ya aje,ya kalli nafisa data tsarki kanta tare da ala wadai da shegen qwaqwqwafinta da yakeson ya bata mata dukka plan dinta "Ki wuce gida,saina qaraso" daga haka ya soma diban wasu files,dai dai sanda P.A dinshi ya shigo suka soma yunqurin barin ofishin,hakan ya sanya dole tabi bayansu jiki a sanyaye,a wajen elevator suka rabu,su suka hau wadda zata kaisu third floor ita kuma tayi qasa don barin companyn. *GA MAI BUQATAR WANNAN LITTAFI ZAI BIYA NAIRA KACAL 200 YA SAMESHI,WANDA KE BUQATAR DUKKA ZAFAFA BIYAR DUN KUWA ZAI SAMESU NE AKAN FARASHIN NAIRA 500* 👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽 *_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_* 2260792279 _MARYAM SANI_ _ZENITHBANK_ saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇 *07067124863* *_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇 *09032345899* _Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_*ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER* 07067124863 *Ko kuma* 09032345899 *ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*🙏🏽 https://www.youtube.com/channel/UC4kJO342hmb_Pd2luKHBjFA/videos *** 0️⃣2️⃣ Qarfe biyu na rana suka shigo gidan ita da huda,a falo suka tadda anty zubaida gabanta plate ne dauke da alala guda uku tana ci "Wash" kadija ta fada tana zama saman kujerar dake falon,sannan ta zame dankwalin kanta don tasha iska,dogon gashinta da bashi da cika saboda santsi da tsahonsa ya bayyana "Ina kuka jima haka yau?" Muskutawa shahida tayi,muryarta dauke da alamun gajiya tace "Kin manta na gaya miki muna shirye shiryen ziyarar da mai makarantarmu zai kawo mana next week?" "Af,na manta haka ne fa....amma da alama ba qaramin shiri kukewa zuwan nasa ba,ga dalibarku nan ta kasa zaune ta kasa tsaye" inji anty zubaida tana duban huda dake zare safarta tana dariya,yatsina fuska shahida tayi cike da qosawa "Nima abun duk ya soma ginsata anty,duk sun d'aga hankalinsu duka malaman makarantar.....amma hakan qila baya rasa nasaba da halayyarsa,don a yadda kausar ke gayamin bashi da sauqi sam,kuskure kadan zai gani da bai masa ya dauki mataki,don bai qaunar abinda zai taba students din,last year yazo lokacin ban soma koyarwa a makarantar ba" "To Allah ya taimaka yayi jagora...kece ma,da kin amshi aikin kamfaninsu abban huda da duk wannan jigilar kin huta da ita,har mota zasu baki kyauta saboda matakin da aka baki aiki akai yakai a bakin" murmushin gefan baki kawai tayi,sannan tayunqura ta miqe tana tattara mayafinta zuwa dankwalinta da jakar makarantarta "Au....kinga naso na manta...nuraddin ya bada saqo,yayita kiran wayarki wai bai samu ba" cak shahida ta dakata da abinda take ba kuma tare data juyo ba,fitar furucin daga bakin anty zubaida zuwa kunnuwanta jinsu take kamar harbin bindiga "Waima....ina kika aje wayarki?,nayita kira ni dinma ban sameki ba......anya shahida anya?,sai yaushe zaki saki ki koma dai dai?,saboda nuradden ne kika kashe wayarki?,nuradden kuwa deeja ya cancanci haka kuwa?" Batasan idanunta sun soma fidda hawayen da suka cikasu ba sai data ji saukarsu kan hannunta dake cukuikuye da mayafinta,kasa jure tsaiwa tayi saitayi gaba cikin sassarfa. Da kallo anty zubaida tabita harta bacewa ganinta sannan ta girgiza kai tana furta "Allah ya kyauta" bata sake tankawa ba saita maida hankalinta kan alalanta da take ci. Ganin har huda ta gama komai shahidan bata sake ko leqowa ba,sai anty zubaida ta bawa hudan saqon tace ta shiga ta kai mata,sannan ta gaya mata ta fito taci abinci. Qarfe hudu na yammaci ta fito a shirye tsaf cikin doguwar riga abaya wadda ta wadatu da adon duwatsu,tayi rolling da wadataccen mayafinta,tayi kyau duk da babu ko digon hoda fuskarta bare akai ga kwalliya,hakanan idanunta tarwai suke babu kwalli ko d'aya a cikinsu. Ci gaba da kallonta anty zubaida tayi harta kammala tsakurar alalen sannan tace "Zanje na dubo umma" "Saikin dawo,Allah ya tsare,bari na baki saqo" ta fada tana miqewa zuwa cikin dakinta,mintina qalilan ta fito da leda ta miqa mata "Gashi kikai mata" hannu biyu ta saka ta amsa sannan tayi mata sallama ta fice daga gidan,don 'yar rakiyar tata huda yau akwai islamiyya ta riga data wuce kuma,tilas ta wuce ita d'aya. A hankali take takawa zuwa bakin titi,jikinta a mace yake kamar yadda take jin zuciyarta sam babu wani qwarin gwiwa ko karsashi tattare da ita,tun daga can nesa ta hango shigowar motar,kallo d'aya tayi mata ta gane motar kota wace,hakan yasa ta sake tsananta d'aure girarta gami da kau da fuskarta tamkar bata ga motar ba. Ilai kuwa yana zuwa dab da ita ya rage saurin motar,saidai yadda ta dauke kai tare da qara saurin tafiyarshi ya hanashi damar ce mata komai,tana jinsa ya qara yin gaba,hakan ya nuna mata reverse zaije yayi ya dawo,don haka ta qara sauri,cikin sa'a ta cimma titi kafin ya juyo ta samu abun hawa ta shige ko waiwayenshi ma batayi ba bare ta san ya iso ko bai iso ba. Tsam tayi da ranta cikin abun hawan lokacin da yake sake kusantata da ainihin unguwarsu,wadda anan komai na rayuwarta ya samo asali,a nan duk wani babu na quncinta ya bude,anan komai ya wanzu ya kuma wakana cikin shafukan rayuwarta. Tafiyar mintina talatin suka iso,ya gangara da ita cikin layinsu kamar yadda ta saba aduk lokacin da tazo unguwar tasu bata sauka a titi saita dangana da qofar gidansu,kanta ta dauke gefe guda lokacin da sukazo gifta wani katafaren gida,bata maida kanta ga kallon gabanta ba har sai da suka isa qofar gidansu,sauka tayi ta sallami mai motar tana cusa kai cikin gidan gami da yin sallama. Fakadeden tsakar gidan nasu wanda ada can zamanin quruciya takejin babu wajen daya kaishi dadin xama da dadin yin wasa,kafin wasu murd'addun al'amura su zama silar da zaman tsakar gidan ya zame mata tamkar zama kusa da ramin maciji,babu kowa a tsakar gidan saidai a share yake sarai fes cikin tsafta da kulawa,batayi mamakin ganin babu kowa din ba don tasan a irin wannan lokacin saura qannenta na islamiyya. Daga falonta ta amsa mata sallama,shahida taci gaba da takawa har zuwa qofar falon ta sabule takalmanta ta shiga tana sake maimaita sallamarta. Cikin sanyi ta amsa mata kamar kowanne lokutta,wanda hakan kusan ya zame musu jiki ita da umman tata "Yanzu kike tafe?" Umman tata ta fada cikin jin nauyin d'iyartata wanda har yau ya kasa barinta "Wallahi umma,na manta yaune ranar da nake zuwa sai wajen uku na rana na tuna" "Da kin bari sai gobe ai,tunda yamma tayi.....mubina ma ta riga da tayi wankin harsun bushe ta shanya,tunda taga rana ta soma baki zoba tace wataqila yau yaya ba zata samu zuwa ba" "Me yasa?,da ta jirani ai ina kan hanya" gaida ummantata tayi ta amsa tana tambayarta anty zubaida huda da mai gidan,ta miqa mata saqon da anty zubaidan ta bata wanda itama batasan meye a ciki ba,bayan umma ta gama godiyarta ne kuma shuru ya biyo baya,shahida ce ta dinga qoqarin sako hira jefi jefi,ko kusa a yanzu batason yadda umman take qin sakewa da ita,kaman ba ummanta ba?,komai ya canza tsakaninsu tun shekarun baya da suka shude. Qarfe biyar ta shiga kitchen ta soma dorawa ummantata abincin dare da taga tana niyyar daurawa,ita kuma tana daga tsakar gida zaune kan tabarmar da suka shimfida,duk wani motsin rahama na kan idanunta,itama rahaman ta ankara da hakan saidai ta nuna bata kula ba,irin wannan kallon umman tata ta saba binta dashi da dadewa,kallon tausayi,kallon nadama,kallon kaicon biyewa son rai da son zuciya da sukayi ita da mahaifin rahama shekarun baya da suka shude,har hakan yaso jefa diyar tasu cikin hallaka,da tuni yanzu bayan shudewar mai gidan ita daya zata ci gaba da kurbar baqinciki da bacin ran abinda suka aikatawa rayuwar rahaman. Qarfe shida qannenta nata suka shigo,ta bisu da kallo sanda suke shigowar cikin jin dadi tare da musu addu'a cikin ranta,koda yaushe tana jin dadi har cikin ranta na yadda rayuwarsu ta banbanta da tata rayuwar a sanda take da shekaru kamar nasu,kallo daya zakayi musu kasan suna samun kulawa da tarbiyyar data dace,mubina ke bin rahama(shahida),sai khadija,faruq,sajid sai qaraminsu nasir. Dukkansu fuskarsu qunshe da walwala suka iskota,ta jima cikinsu yayin da mubina ta amshi aikin girkin,tana yi suna hira da yayarta da sauran qannunta. A nan kan qatuwar tabarmar suka ci gaba da zama,suka gabatar da sallar magariba,sannan mubina ta zuba abinci cikin babban tray. Gaba dayansu kowanne ya sanya hannunshi suka soma ci,suna hira lokaci lokaci,har cikin ranta tana jin dadin kasancewa cikin 'yan uwanta,saidai wannan kallo da duba da umma ke mata tana qaunar ya gushe daga idanunta,ta manta da faruwar komai,ya zama tarihi kamar ma bai taba faruwa ba. Sallamar usman d'an maqotansu shi ya katse hirar tasu,ya gaida ummansu sannan yace "Ana sallama da anty shahida" hada idanu sukayi da umman,yayin da kowa abinda ke yawo a zuciyarsa ya tashi daban da na d'an uwanshi,qas da kanta shahida tayi tana kokawar hadiye lomar tuwon data riga ta saka abakinta,batakai ga hadiyewa ba saqon usman ya shiga kunnenta,sai taji gaba daya abincin bai mata dadi a bakinta,ya kuma gagara wucewar,hakan ya sanya ta miqe tsam ta isa bakin rariyarsu ta zubda tuwon sannan ta wuce dakin umman ba tare data bi takan aiken da akayo mata ba. Suya kawai qirjinta yake,waye wannan yakeson mata kutse ne cikin rayuwarta a sanda bata shiryawa hakan ba?,waye shi da zai tunkari rayuwarta a sanda bata da dukkan wani tsari akan kowanne d'a namiji?. Shigowar umma dakin shiya katse mata tunaninta,ta yunqura ta miqe ta zauna sosai daga kasalalliyar kwanciyar da tayi,wani mummunan tashin hankali ya ziyarceta sanda ta dubi idanun umman taga hawaye na biyo kuncinta,cikin matuqar rudewa da gigita tace "Um....umma...hawaye fa kike umma meya sameki?,don Allah kibar kukan,kiyi shuru kice wani abu" "Dole nayi kuka shahida....bazan daina kuka ba harsai sanda abinda yake damuna ya gushe,tashin hankalin da kika shiga kadai sanda aka aiko kiranki ya tabbatarmin akwai sauran rina akaba,kuma hakan ke nunamin cewa dafin da muka zuba a zuciyarki har yau bai gama wankewa ba" zamowa tayi daga saman kujerar tayi gurfane a gaban umman tata itama hawaye na sakko mata cikin tashin hankali "Ko kad'an umma,kufa iyayena ne,kune kukayi silar zuwana duniya,umma....ba tun yauba na gayamiki ki goge duk wani abu daya faru daga ranki,ki daina alaqanta duk wani yanayi da zaki gani tattare dani da cewa laifinku ne" "Indai kinason hakan ta faru shahida ki koma yadda kike....ki amshi wani cikin masu sonki kiyi aure,anwar bashi kadai bane namiji da don ya miki wani abu zai zama silar da zaki maida kanki wata aba daban ba,indai ina ci gaba da ganinki a haka baki sauraren kowa bare akai ga batun aure bazan daina zargar kaina ba har na koma ga mahaliccina,kamar yadda mahaifinki bai daina zargin kanshi ba har ya koma ga mahaliccin......" Maganar tata saita riqe,kuka sosai ya qwace mata,tana tuna abubuwa marasa dadi da suka faru a rayuwarsu,tana tuna komai tar cikin kwanyarta,qaruwar kukanta ya qara dasa tashin hankali a zuciyar shahida,wadda ta miqe ta figi mayafinta cikin rawar murya tace "Zanje,zan fita umma indai hakan shi zai sanya farinciki da walwala a cikin zuciyarki" bata qara second guda ba tayi waje,kai tsaye kuma ba tare da saurarar komai ba ta wuce zuwa qofar gidansu.*ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER* 07067124863 *KO KUMA* 09032345899 *ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sabbabi,karku manta ky danna SUBSCRIBE,kuyi LIKE sannan kuyi SHARING🙏🏽* 👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽 https://www.youtube.com/channel/UC4kJO342hmb_Pd2luKHBjFA/videos 0️⃣3️⃣ Jingine yake jikin motarsa ya qurawa qofar gidan idanu,ji yake kaman ya shiga ya fito da ita,ganin fitowarta ya sanyashi kasa tsaiwa jikin motarsa kamar yadda yake tsaye a dazun,sai ya tsaya qyam yana dubanta,ji yake tamkar an masa rahama,shi kadai yasan yadda yake jinta cikin jiki da ruhinsa,wani irin so yakewa shahidan,kamar ya rufe ido ya bude ya ganta cikin gidansa,ta zama matarsa kuma mallakinsa. "Barka da fitowa,Allah yasa ban takura ki ba" ya fada yana sakin murmushi,duk da ya fuskanci kamar bata cikin ainihin nutsuwarta,kai kawai ta iya gyadawa "Kiyi haquri idan na takurakin,na kasa jurewa ne,na kira wayarki yafi sau nawa bakya picking,naje gida nemanki na bada saqo amma banga respond ba" ya fada yana tsagaitawa da maganar don ya bata damar cewa wani abu,duk da bashi da yaqinin zata amsa din,tsahon zamanshi da shahida duk daba wani dogon lokaci can suka dauka ba,zai iya qayyade adadin kalmomin bakinta daya ji,ko dama can tun asalin shahida mutum ce mai qaranta magana qwarai,bata da yawan surutu,tafi ganewa zaman shuru da kad'aita. Ason ranshi ta shiga gaban motarshi ta zauna suyi hira sosai da ita,saidai yasan hakan bamai yiwuwa bane,ko a yanzu daya zo yayi shahadar quda ne kawai,don bai tsammaci fitowar tata ba "Ko zamu qarasa can ki samu ki xauna karki qosa da tsaiwar" yayi qarfin halin fada yana nuna wani dakali dake qofar gidan nasu gab da qofar shiga zaurensu,a nutse ta daga jigatattun idanunta ta kalli bigiren da yake nunawar,kasancewar akwai wadatar hasken wutar lantarki taga wajen sosai,idanunta ta lumshe wani abu na takore mata wuya,kallon wajen a koda yaushe yakan tuna mata dashi,abinda bata da muradi ko kadan,kai ta girgiza cikin qarfin hali tace "Nan ma ya isa,don ina saurine zan wuce gida dare yana yi" cikin zumudin da yake yunqurin boyewa ya muskuta kad'an "To idan babu damuwa me zai hana ki shigo saina saukeki?" Hannunta saman wuyanta kamar wadda ke taba yanayin zafin jikinta,duk da tana jin kamar zazzabin ne ke shirin kamata tace "Babu buqatar hakan.....zan iya komawa ciki?" Kafin yakai ga bata amsa tuni har ta soma tattaki,kasa cewa komai yayi yana kallonta harta shige cikin gidan. Sit din driver ya koma ya zauna cikin matuqar kasala da mutuwar jiki,zazzafar ajiyar zuciya ya saki gami da furzo iska mai zafi daga bakinsa,kallon kansa ya shiga yi a madubi,haryau bai gano wani naqasu tattare dashi ba ko makusa daya sanya shahida ta kasa sakewa dashi,iya kyau Allah ya baiwa noraddeen kyau,kudi aji da nasaba,baisan wacce hanya zaya bi ya shawo kan shahida ba,da yana da masaniya kan hanyar da babu shakka yabi ko don ya mallaketa zuciyarsa ta huta da abinda take ji,sai daya kusa a qalla mintuna goma kafin ya iya miqa hannu yaja murfin motar ya rufe ya tadata yabar layin. Bakwai taso barin gidan,amma ba ita ta tafi ba sai qarfe tara,sai data tabbatar ta kwantarwa da ummantata hankali duk da tata duniyar a rude take,haka ta shirya tayi sallama da qannenta ta wuce gida. 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺 Sannu a hankali yake takowa cikin gidan saman shinfidadden marbles daya malale ilahirin gidan,hannunshi d'aya soke a aljihun wandonsa yayin da daya yake riqe da wayarshi da yake amsa kiran daya shigo masa,ya jima tsaye tsakiyar qawataccen falon yana amsa wayar kafin daga bisani yayi sallama da wanda suke wayar ya soma qoqarin shiga akwatin tura saqonni. "Ka iso kenan?" Cewar wata farar mace data fito daga daya daga cikin qofofin dake jere a falon,shekarunta na haihuwa a qalla zasu doshi arba'in da biyar,tana sanye da atamfa wadda tayi matuqar yi mata kyau,a kallon farko idan kayi mata zaka ga kama ta zahiri tsakaninta da anwar,saidai banbancin launin fata,wanda shi tashi fatar choculet colour ce wato wankan tarwada mai kyau,yayin da tata fatar ta kasance fara ce duk da ba irin farin nan can can ba,anty usaina kenan 'yar uwa daya tak data ragewa anwar a duniya,kanshi ya daga ya dubeta sannan ya maida kan wayar yana amsa mata da eh,lokaci guda kuma shima yana yiwa kanshi gurin xama kan daya daga cikin kujerun. Second goma ya qara ya aje wayar gefanshi sannan ya dago yana gaidata,ta amsa tana tambayarsa yanayin aikin da iyalin gidan alhj sambo,ya amsa mata da duk lafiya kowa yake "Ina duka yaran?,suna makaranta ko?" "Eh ai yau tun bakwai suka wuce,saboda anata shirye shiryen zuwanka,duk sai murna suke suce malaman sun shirya abubuwa da yawa" murmushi kawai ya saki,donshi karan kansa yakanji dadi a duk sanda ya tsinci kansa cikin daya daga cikin makarantun daya gina da kansu yaran al'umma kuma ke amfana da hakan,goshinsa yadan shafa kadan sannan yace "Naji kince nazo anty,Allah yasa dai lafiya" zamanta ta dan gyara sannan tace "Lafiya lau,kan maganarka ce da nafisa.....naji kayi shuru,yarinyar ta qagu,kuma nima ina kuma tsoron halayyarku ta maza,musamman kai da ludayinka ke kan dawo,kada ya zamana wani abu da zai sauya ra'ayinka ya gitta,ina tsoron faruwar hakan kodan halaccin mahaifinta a gareka" shuru ya ratsa na wani dan lokaci kafin daga bisani yace "Kawai dai ta kasa sama ranta nutsuwa ne,kishinta yayi yawa,kinfi kowa sanin halayyata anty,so banga abun d'aga hankali ba,komai na rayuwa idan aka bishi da tsari saiyafi bada ma'ana,ina sane kuma sauran wasu 'yan lokuta kadan akai gabar data dace nayi magana" kai take jinjinawa,tunba yauba tafi kowa sanin halin qannin nata,idan yace yes wuya ko rintsi basa sauyashi,hakanan idan yace no to ya bari kenan har abada,bata taba ganin abinda yace A'ah ba daga baya kuma yazo yayi accepting dinsa "Shikenan,zan mata bayani,Allah ya dafa mana" bai amsa ba ya shigar da wata tambayar "Zuwa tayi ta sameki?" Ya tambayi anty usaina yana dubanta,tasan halayyarshi tasan meye baiso da wanda yakeso saboda haka ta kada kai "Wannan ba abinda ya shafeka bane.....ga abun kari can ko zaka karya kafin ka wuce,tunda baka aje mai maka ba" siririn murmushi ya saki kawai yana shafa kansa,sannan ya miqe suka jera da antin zuwa dining suna hirarsu ta zumunci. "Har yau baku manta baya ba,gargajiyarku tana tare daku" anwar ya fada yana kallom coolers din abincin dake saman dining din,duk da baisan meye a ciki ba amma ya sani cima ce irinta bahaushe ba kayan ciye ciye na bature ba,murmushi anty usaina tayi "Laifin abbansu,yace manta baua butulci ne" murmushi kawai yayi yana kada kai,ko shi dinma ya fada ne kawai don ya tsokaneta,amma bashi da cima data wuce irin tasu wadda aka gada kaka da kakanni,sam ciye ciye zamani ba kasafai suke burgeshi ba,yakan ci lokaci zuwa lokaci amma ba komai da komai ba. Tunda ta fara zuba abincin hankalinsa yaji yayi matuqar tashi,duk lokaci haka duk a inda yaga wannan cimar saiya tuna da ita,cimar da a baya bashi da sama da ita musamman da safe,cimar da take burgeshi a baya,take rubuce cikin kundin abubuwan daya fiso,kunun gyada ne lafiyayye da yasha madara,sai qosai lafiyayye shima daya ji attaruhu da albasa ya bugu yayi luhu luhu kamar an saka masa qwai. Tsam ya miqe ba tare daya ce da anty usaina komai ba ya soma sauka daga wajen "A'ah,ina kuma zaka?" Ta tsaida abinda take ta bishi da kallo bayan ta tambayeshi "Na qoshi anty zan wuce office ne na tuna ana jirana" maida kanta tayi tana duban kunu da qosan dake gabanta,saita sake daga kai tana dubansa sanda yake daukar wayarshi daya aje a hannun kujera dazu,ko bai waiwayo ba,ko baice mata komai ba ta fuskanci me ya faru cikin 'yan sakannin,cikin hanzari ta aje plate ta sauko,ta cimmasa sanda yake niyyar bude qofar falon don ya fice ta dakatar dashi "Anya ko anwar anya?,har yanzu dai babu wani da zai sauya?,abun har yakai tsananin haka a zuciyarka?,anya ko wannan butulci ne kayi mata ko adalci?" Take idanunsa suka kada cikin qaramin lokaci,banda anty hasanan duk duniya baiga wanda zai tsaya ya soko masa zancanta ba tare daya kauda shi daga gabanshi ba "Ka taba kwanciya dai dai da rana daya ka tariyo alkhairanta a gareka?,ka taba xama ka banbance aya da tsakuwa kuwa?" Kalamanta na masa wani irin suya ne a qirji bashi da jarumatar ci gaba da sauraronta saboda haka ya qarasa ficewa cikin sassarfa daga falon,ya fada motarshi ya tashe da gaggawa ya fice daga gidan. Ta jima tsaye a wajen,dukkan wata laka ta jikinta tayi sanyi qalau,wannan wanne irin abune?,ko a mafarko ba wanda ya taba tunanin wannan kyakkyawar alaqa tarayya da abota zata juye watan watarana ta zama irin haka,jikinta ba qwari ta koma ciki ta samu d'aya daga cikin kujerun falon ta zauna tana tuna wasu daga abubuwan da suka shude cikin rayuwar muhammad da rahama. "Ita ta rusa dukkan komai,ita ta kawo dukkan wata damuwa da baqinciki da nake kwana nake tashi da ita,ita ta butulcewa ni'imar Allah ta wulaqanta rayuwar da Allah yayi mata baiwarta" kalaman daya dinga fada kenan a sandaya samu qasan daya daga cikin bishiyoyin dake jere reras a harabar kamfanin ya faka motarsa,ya kashe wajen awa guda cur yana ciki yana qoqarin controlling kansa,yana ganin wayoyin jama'ar da suke da appointment dashi amma ya kasa daga ko guda daya,baisan me yasa yake iya dealing da duk wani daya tunkaroshi ba cikin qanqanin lokaci,amma akan wannan sabgar har yau ya kasa maida kansa jarumi,ya kasa daina jin ciwon dukkan abubuwan da suka jima da shudewq,ya kasa daina jin tsanarta,ya kasa tsayawa yayi mata adalcin dako yaushe antyn da zuciyarsa ke qoqarin gaya masa yayi mata. Sai daya shafe awanni biyu sannan ya iya fitowa bayan ya rufe motar,ya dinga takawa ahankali zuwa babban ginin kamfanin daya mamaye iya kallon mai kallo,sauran mutane dake dakon jiranshi suka yo masa caa,yayi qoqarin ganin ya dawo da mode dinsa duk da yadda yake jin kwanyarsa a birkice. Tsaki taja bayan ta kammala karanta saqon,kafin daga bisani ta cilla wayar gefanta,dawowarta kenan daga makaranta a matuqar gajiya ta zauna a falon,bata ma kai ga qarasawa dakinta ba saboda gajiya,gaba d'aya ta gundura da wannan d'an banzan shirye shirye da hukumar makarantarsu keyi na zuwa shugabanta,wanda ita a ganinta ko president ne zai kawo musu ziyara iyaka kenan,ta k'agu yazo ya tafi a wuce wajen,saiga saqon nuraddeen kuma wanda ta tsani gani kamar yadda ta tsani mutuwarta,batasan sai yaushe zai gaji da halin shakulaton b'angaron da take yi dashi yayi zuciya ya barta ta rayu ita d'aya ba kamar yadda ta sama ranta. Sun riga sunyi waya da anty zubaida tasan ta fita yau bata nan,don haka girkin gidan na yau na wuyanta,ga huda da suka dawo tare tasan yunwa takeji,don ma ta siya mata cake da lemo a makaranta kafin su iso gida. D'aki ta shiga ta tube ta fada wanka,bayan ta fito ta sanya huda itama ta shiga tayi don yau babu islamiyya,a gurguje ta shirya tayi sallar azahar sannan ta shiga kitchen. Indomie ta soma dora musu sannan ta dora girki a dayan wajen "Anty kin gama?" Huda data shigo yanzu ta fada tana qarasowa inda shahida ke zaune sosai qasan kitchen din tana gyara kayan miya,don ta duba nasu markadadden da suke ajewa ya qare "Sauran kadan hudallah....dadina dake bakya juriyar yunwa" "Anty yunwa bata da hankali,haka d'an almajiri fa yake cewa" murmushi shahida tayi wanda ya qara kyawun fuskarta,hakanan ya bayyana wushiryarta,kafin tace wani abu hudan ta sake cewa "Anty...dama d'an wake kika yi mana,inason d'an wake" a hankali ta juya ta dubi yarinyar saboda tuna mata wani abu da tayi,yana matuqar son d'an wake a rayuwarshi,a duk sanda taga abincin ko taji an ambaceshi saita tuna dashi.*ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH)KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER* 07067124863 *KO KUMA* 09032345899 *ku ziyarci tasharmu ta youtube don samun shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sabbabi* https://www.youtube.com/channel/UC4kJO342hmb_Pd2luKHBjFA/videos *AA* 0️⃣4️⃣ Kasa cewa komai tayi,maganar hudan ta cillata tunanin wata duniya can baya,wanda duk yadda takai ga hana kanta batasan sanda ta fada ba. Sai data sallami huda sannan taci gaba da sabgar girkinta,batasan me yasa ba sam batajin yunwa,ko zancan da huda tayi ne ya cushe mata cikinta gaba daya ya sanya har walwalarta ta ragu. Tana tsaka da kwashe abincin cikin coolers huda ta shigo da sauri hannunta dauke da wayar shahida tana fadin "Anty ana kiranki,zata katse" ta fada tana miqa mata,bata amsa ba ta kalli screen din wayar dake hannun huda,nuraddeen ne,saita dauke kai taci gaba da juye abincin tana cewa "Ajiyeta kawai huda,aiki nake" juyawa yarinyar tayi ta fice da wayar zuwa falo da gudu don kada cartoon din da take kallo ya wuceta. Tana cikin kintsa wajen sallamar anty zubaida ta karade falon sannan ta taddata cikin kitchen din "Sannu da dawowa maman huda" "Yauwa sannunki shahida,kin ganni sai yanzu ko?,wallahi layi yau na samu....me aka dafa mana ne yau da yunwa na dawo" nuni shahida tayi mata da food flask din dake jere a wajen,ta qarasa tana budawa "Hmmmmm,kice yau na musamman ne abincin,bari wannan sai nayi wanka zan zauna sosai tukunna na kwashi dabge" qaramin murmushi shahida tayi mai fitar da d'an sauti tana duban anty zubaidan,har takai bakin qofa ta dawo "Au....ni kuwa kinsan nuradden na qofar gida zaune cikin mota yana jiranki?" Asanyaye ta daga kai ta dubi anty zubaidan,sai ta sadda kanta tana goge plates din data wanke zata jerasu a muhallinsu,hakan da tayi shi ya tabbatarwa anty zubaida ya kira bata daga ba kenan "Shahida.....wannan wacce irin rayuwa ce kika daukarma ranki?,mai sonka fa ya wuce ka wulqantashi,laifin wani dama yana shafar wani?" Shuru ta sake zabar tayi,saboda tana ganin sun gaza fahimtarta ne gaba daya,ta yiwa soyayya hidima,ta yiwa soyayya halacci,ta yiwa soyayya dukkan wata kara da alkunya,qarshe data tashi ita mai ta bata?,data tashi da wanne sakamako tazo mata?,sunfi kowa sani saboda haka sunfi kowa amsar dukka tambayoyinta,ko daya bata tsinci komai cikin soyayya ba face tsantsar butulci mummunan sakamako da kuma mummunar makoma,shin ta yiwa kanta a dalci kenan idan ta sake cusa kanta a wannan bigiren? "Nidai ya roqeni alfarma,saboda haka idan na isa dake ki leqa ko gaisawa ne kuyi" zancan anty zubaida ya katse tunaninta,daga haka bata sake cewa komai ba ta ida ficewa daga kitchen din,tana jinta sanda ta kira huda suka haye sama tare,tasan kuma tayi hakanne don sanin halinta,ba qaramin aikinta bane ta fita ta baro masa huda ta cikashi da surutu wanda idan ya gaji da zama yake sallamar huda shima ya wuce nashi guri. Anty zubaidan tafi qarfin komai a wajenta,don haka ta dauraye hannayenta ta wuce dakinta,ta zari hijabi ta saka ta sanya slipper dinta ta wuce qofar gidan. Kamar kowanne lokaci yana zaune cikin motar,bayanshi jingine da seat din kujerar dayake kai,da alama ya jima zaune a wajen,duk da haka ganin fitowarta bai hanashi miqewa ba yana sakar mata murmushi harta qaraso "Barka na tunda na samu kin fito" ya fada tamkar wanda baiyi zaman jiranta ba "Inda kayi aiki da shawarata tun a karon farko da duk bamu kawo wannan matsayin da muke kai yanzu ba" ta fada kanta tsaye tana dubanshi,kafin daga bisani ta janye idanunta,har ga Allah wulaqanta dan adam ba dabi'arta bace,zatafi kowa farinciki idan har noraddeen ya janye daga qudurinsa daga kanta,ga sabanin tunaninta sai taga ya saki murmushi "Bani da damuwa shahida,nasan cewa mahaqurci mawadaci,zan iya jure koma meye indai a kanki ne shahida" idanunta ta lumshe tana jin kamar jiri zaya kada ta,a rayuwa yanzu babu abinda ke damunta sama da matsalar nuradden,ya soma shiga jiki da zuciyar makusantanta,bata da buqatar a yanzu dukkan abinda zai kuma d'aga ma rayuwarta hankali. "Koma meye tabbas mai wucewa ne watan wata rana" furucin nuradden ya sake ratsa dodon kunnenta,a sanda take kiciniyar dai daita kanta "Don Allah.....shahida inason ki bani dama,ki saurareni koda wayata ce kadai ki dinga dagawa,bazan takuraki kan koda yaushe saikin fito na ganki ba,amma ki daga wayata,hakan kadai ya isarmin....don Allah" ya fada yana hade hannayensa waje d'aya alamar roqo "Naji ya isa,ka sameni ta wayar" ta fada tana juyawa don ta shige gida kamar wadda take kan qaya ko wuta "Tsaya mana shahida....." Yayi hanzarin fada,tsayawa tayi cak kamar yadda ya umarta,saidai bata waiwayo ba a haka ya cimmata,gabanta yasha,yana murmushi ya miqa mata wata leda "Ga wannan,ki karba don Allah....." Batason doguwar magana saboda haka ta saka hannu ta amsa kawai ta shigeshi,kallo ya bita dashi yana jin dad'i cikin ranshi,yau an samu wani ci gaba da har shahida karo na farko ta amshi abun hannunsa,tabbas watarana yana saka ran komai zai wuce,bai taba tsammatar tsintar kanshi cikin soyayya makamanciyar wannan ba,saidai shahida ta cancanci komai,tana da nutsuwa tana da hankali uwa uba kyau,shahidan tayi masa,tako ina ta amsa sunan irin macen da yakeso,yake da burin mallaka,macen da cikin dubu sai an duba. Tana shiga a nan falo ta ajewa huda ledar,tace ta dauka ta bata,tana jin huda na tsallen murna da kacaniyar bude ledar tawuce dakinta ta hau sabgar gabanta,duk don ta yakice komai,wanka ta soma yi,sannan ta jawo plate din abincin data shigo dashi daxu sanda zata fita wajen nuraddeen din ta soma tsakurar abincin ciki,ci take kawai,amma ko za'a rutsata da bindiga batasan wanne taste ke ga abincin ba,tana cusa wa ne kawai maganin yunwa,duk sanda taji irin wannan yanayin tattare da ita tasan cewa can cikin zuciyarta ba lafiya qalau take ba,ta hanata kanta dukkan wani tunani,ta bude jakar makarantarta ta dauko exams din dalibanta ta shiga marking tana shigarwa cikin paper din dake dauke da sunayensu. Tana tsaka da haka wayarta dake aje can gefe ta soma haske,don dama abadan wayarta a silent take,batason wani qwaqwwaran motsi da xai dameta,daga kai ta dubeta,kamar ba zata daga ba saita miqe tsam tace ta duba,anty amina sunan dake yawo saman screen din kenan,dan qaramin murmushi ta saki wanda bai bayyana ba koda saman fuskarta ba bare mutum ya gane,saida ta bari wayar ta katse da kanta sannan tabi kiran "Ranki ya dade yallabiya,don naga alama kin xama hukuma saida lallashi,kinbar rayuwar kowa bare ki nemeshi ko?" Wani murmushin ta kuma saki wanda yafi ja daxu armashi fa bayyana,sai data koma ta zauna inda ta tashi sannan tace "Ni na isa,ta yaya zan manta da anty amina ta?" Ta fada tana tura hular kanta zuwa baya,hakan saiya qara fidda kyanta,sakamakon gashinta mai santsi daya bayyana "Gashi kuwa?,kin d'aura aniyar mantawa dani din?,anya duniya da amana kuwa shahida?" Duk sai komai ya tsaye mata cak,duk da cewa gaskiya anty aminan ta fada,abinda bata sani ba tana gujewa kiranta ko haduwa da itane,saboda tana daga cikin abubuwan dake tuna mata baya,wanda take ra yaqi shafe komai shekara da shekaru "Yanzu dai ayimin afuww,inayini anty amina mun yini lpy?"ta fadi tana kada biron dake hannunta hagu da dama "Lpy alhmdlh....ya gida?" "Lpy qalau muke,ina yarana?" "Yaranki duka sunyi fushi" murmushi ta sake saki "Suyimin afuwa,ina nan zuwa,zuwan ba zata" "Haka dai,kullum maganar kenan,fafur kin qimu kin gujemu,na rasa ma LAIFIN NA WAYE?" jin anty aminar nason fadawa wani bigiren na daban ya sanyata soko wata hirar don kauda waccar maganar "Zan baku mamaki anty amina,kedai ki sharen hanya" "Yo sharar hanya kuma ta nawa,na share na share har na gaji,kedai sai an ganki kawai" sai ta miqawa yaran nata wayar suka shiga gaisawa d'ai d'ai da d'ai,su dinma bikonta sukeyi duk tace musu tana nan zuwa susha kuruminsu,daga bisani suka miqawa mamarsu wayar suka dan sake tattaunawa sannan sukayi sallama da juna. Tana shirin aje wayar wani kiran ya sake shigowa,anty zubaida ce take kiranta "Ki sameni a falo" ta fada kawai ta yanke kiran,saita sauke wayar daga kunnenta tana miqewa tsaye ta gyara daurin zaninta,tana zura hijabinta wayar ta sake haske,nuradden ne ke kira saita dauke kai ta qarasa saita hijabin nata ta fice a falon. Abbi anty zubaida da huda ne zaune gaban kwanukan abincin,kamar yadda al'adar abbi take bai hawa dining saidai a sauke masa abinci a qasa a shimfida masa table mat,yanzun ma abincin suke ci,ta qarasa cikin nutsuwa ta zauna gefan huda tana gida abbun,ya amsa mata fuska a sake kamar kullum yana tambayarta dalibai,murmushi tayi ta sani sarai baison koyarwar da take ko kad'an,amma ya haqura ya bata damarta don baison ya tauyeta ko ya hanata abinda ta zabawa kanta,duk da cewa tana koyarwa ne bisa wani sharadi da bata tunanin ma akwai randa sharadin zai gindaya yayi sababin afkuwar barinta makarantar "Wannan kayan da kika baiwa huda fa?" Cewar anty zubaida tana nuna ledar da baki,waiwaya tayi yana duban ledar don sam ta mance ma tayi kyautarta,kunya ce ta dan kamata ganin kayan da suke ciki,katuna ne masu dauke da kalaman soyayya sai sauran tarkacen kaya da suka shafi masoya,idan ma akwai abinda ya shafi huda a ciki bai wuce choculet masu tsada dake ciki ba,dan satar kallon uncle abbu tayi taga shi sam hankalinshi ma ba'a kansu yake ba,saita maida wajen antyn "Ki cire mata choculets din saiki ajemin sauran kayan" "Eh da yake ni aka bawa ko?,to tattara kayanki ki bar wajen dasu tun ban gayawa abbu abinda kike yi ba" da hanzari ta miqe tana miqawa anty zubaidan ban haquri da ido,haka ta tattare kayan tana jin kamar ta watsar dasu a wajen "Yaushe zakuyi hutu ne khadija?,inason wannan karon kuje kankia kuyiwa su dada hutu,tanata qorafin kin yada su gaba daya bakya ta tasu" "Kwana uku ya rage,donma sun tsaya jiran zuwan mai makarantar ne" "Na qagu abbu ranar tazo wallahi...." Cewar huda cikin zumudi,waiwaya shahida tayi tana duban hudan,batasan me yasa take yawan zumudi da zuwan mutumin da kowa yake masa shaidar baida sauqi ko rangwame ba,kamar anty zubaida tasan tadin me take a ranta tace "Oh hudaaaa...irin wannan zumudi kullum zancanki kenan?" "Ummi....yana da kirki wallahi,yanasonmu,idan yazo kowa sai an bashi chaculets masu dadi da biscuits manya manya" "Sarkin kwadayi...." Abbu ya fada yana lakuce mata baki,dariya sukayi gaba daya "Ina tunanin randa zakuyi hutu ranar su faruq zasu dawo suma" abbu ya fadi yana zuba lemo a cup,shahida dake niyyar barin falon ta dakata,fuskarta qunshe da murmushin data kan jima bata yi ba,tayi kewarsu sosai,duk sanda suka koma makaranta gidan baya mata dadi,tace "Abbu amma baka gaya mana ba sai yau?" Dubanta yayi,yana mamakin shaquwarsu "Eh,saiku hanamu sakat da shirin zuwansu,kaman su kadai ne mutane a gidan" ya qarashe zancan nasa yana duban anty zubaida,tasan sarai su yake tsokana ita da shahida,don haka ta dauke kai kaman bata jishi ba,murmushi mai sanyi shahida ta saki ta juya tana ci gaba da tafiya "Allah ya dawo dasu lafiya" "Amin" ya amsa,huda kam ta kasa zaune ta kasa tsaye,yayun nata kamar qawaye suke a wajenta,ita daya ce mace banda zuwan shahida gidan itama idan suka koma makarantar ita kadai ke watangaririya a gidan,saidai idan ta gaji ta gudu gidan kakanninta na wajen uwa. 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺 A nutse yake kai abincin bakinsa,yayin da rabin hankalinsa ke kan wayarsa dake aje gefan plate dim abincin,zaune take kan kujerar dake fuskantar tasa,tasha kwalliya iyaka,kai kace zata je wajen wata dinner dinne,cikin dinkin lace riga da skert take,hannayenta gaba daya biyun ta tallafe kumatunta dasu,yayin data zuba masa idanunta,duk wani wani motsinsa yana yinsa ne kan idanunta,batasan wanne kalarso take masa ba arayuwa,saidai koma meye tasan cewa son da take masa wani bangarene mai girma a rayuwarta. Kanshi ya daga daga wayar yana sake kai wani spoon din abincin bakinsa,sai a sannan ya lura da irin kallon da take masa "Hey!" Ya fada yana murza yatsunsa,hannayen ta sauke tana dan qaramin murmushi bayan ta sauke ajiyar zuciya "Kallon fa?" Ya tambayeta a taqaice,muryarta cikin rauni da nuna fargaba wanda ya wanzu har saman fuskarta tace "Ina tsoron kar na rasaka anwar,ina jin kamar watan watarana zan rasaka" ta fada can qasan ranta tana jin kishinta na cin zuciyarta,tana jin kamar zata dawo rayuwarshi ta rabasu,ta san cewa a yanzu sun yiwa rayuwar juna nisa saidai ta kasa samun nutsuwa da kwanciyar hankali duk da haqarta ta cimma ruwa,aje cup din da yayi niyyar kaiwa bakinsa yayi,ya hade hannayenshi waje guda gami da saka yatsunsa cikin na juna "Meye abun jin tsoro a ciki?" Kai ta kada tana gyara zamanta bayan ta goya hannayanta a qirji "Kai din kalar namijin da kowacce mace keso da buri ne,don me bazanji tsoron kar a rabani dakai ba?" Bai bata amsa ba sai kofin daya aje dazun yanzu ya sake dauka,yana mamakin yadda take daukar abubuwan da suka shafe shi da girma haka,saidai har yanzun baya jin wani feeling na daban ko na musamman tattare da ita,yana dorata ne kawai bisa mizanin wasu abubuwa da martabarta ke alaqantuwa dasu "Shine dalilin kenan da kikai qorafi wajen anty hasana?" Ya jefo mata tambayar yana kafeta da ido,gefe guda kuma yana karantarta a fakaice "Aure kikeso?" Kai tsaye ta gyada masa kai a sanyaye tana mai fata da addu'ar cikar burinta,shuru ya ratsa na tsahon minti daya ba tare da wani daga cikinsu yace komai ko yayi wani qwaqwaqwaran motsi ba,ture kujerar da yake kai yayi baya sannan ya miqe tsaye yana kwashe wayarshi da muqullin motarsa "Zamuyi magana later" ya fada yana sauka daga step din da dining din yake kai,da hanzari ta biyoshi a baya tana son tace wani abu,kacibus sukayi da hajiya bilkisu mahaifa ga nafisa,dan dakatawa yayi kadan cikin girmamawa "Au harka kammala kenan?" "Eh zan wuce office ne ana jirana" "To ko saika dawo din?,da akwai maganar da da nakeso muyi" "To ba damuwa" ya fada yana ja da baya,ta wuce yabi bayanta zuwa cikin falon. "Alhaji ne yace na tuntubeka,me zai hana ka dawo cikin gidan nan kaci gaba da zama damu kamar yadda ake a baya?" Nafisa dake lafe kusa da hajiya bilkisu ta daga kai a hankali tana satar kallonshi,addu'a take a ranta Allah yasa ya amince da hakan,da tafi kowa jin dadi a duniya,koda yaushe bata da burin daya wuce ta ganta kusa dashi "Ayima alhj godiya na gode sosai,saidai yanayin aikina bazai bani damar hakan ba,hakan ma alhmdlh babu wata a matsala" dan shuru tayi sannan ta jijijjiga kai "Toh shikenan...babu damuwa Allah ya dafa...." "Don Allah ya an....." Nafisa tayi hanzarin fada don ba hukuncin dataso anwar din ya yanke kenan ba,harara hajiya bilkisu ta jefa mata wanda shine silar yankewar sauran maganar tata,miqewa yayi yayi mata sallama kana ya fice daga falon gaba daya zuwa inda ya aje motarshi. "Ke wace iriyar yarinya ce ne nafisa?,bakiji gargadin da nake miki koda yaushe akan ki dinga kama kanki gaban anwar?,a haka kike tunanin zaki samu qima da daraja wajenshi?" Langabe kai tayi cikin sigar tausayi tace "Afwa mom...." Bata sake ce mata komai ba ta gyara zamantabta dauki wayarta ta shiga danne danne,hakan ya sanya nafisan itama miqewa ta haura sama inda dakinta yake. Kai tsaye gaban mudubi ta isa ta tsaya sosai tana qarewa kanta kallo,har yau cikin zuciyarta bata jin ta mallaki anwar yadda takeso,tanaji a jikinta har yau zuciyar anwar ba tata bace,meta rasa?,meye bata shi?,ta fita komai,ta kere mata a komai,tun daga kyau,kudi zuwa matakin karatu,amma tana jin har yau kamar ta kashe maciji ne bata sare kanshi ba. Da hanzari ta koma da baya ta lalubi wayarta dake aje gefan pillow dinta,sai data fara tura mishi saqo dake qunshe da kalaman soyayya sannan ta lalubi number mema ta kira,bugu hudu ta d'aga "Yayinki ake" mema ta fada cikin daga murya mai cakude da dariya dariya,murmushi nafisa ta saki tana shaf fuskarta zuwa wuyanta,yayin da take sake qarewa kanta kallo a madubi,wannan kalma na mata dadi,amma gaba daya kaman bata aiki akan anwar,duk da cewa bata da wata qwaqwqwarar hujja da zata nuna cewa babu sonta cikin zuciyarshi,saidai ita din bata gamsu da yadda mu'amalarsu ke gudana ba har zuwa yau "Wannan kalma mema taqi amfani akan anwar har yau" "Kai haba?,wane mutum?,shi ya isa?,me ya fiki dashi da zai...." "Dakata mema....kice komai a kaina amma banda akan anwar....mema,ina tunanin mun kashe maciji ne amma bamu sare kanshi ba,zuciyata da ruhina har yau basu gamsu ba,ta yaya zan sake binneta da ranta?,ta yaya zan sake b'atar da ita daga duniyarshi?,inason haskena shi kadai ya wanzu a cikin ruhi da rayuwarshi" "Yanzu me kike tunani?,me kike gani?" "Ke zanwa wannan tambayar" shuru mema tayi na wasu 'yan sakanni sannan tace "Alright ina da wadansu 'yan dabaru da shawarwari,amma yanzu bana qasar,ina benin republic...." "Ubanme kike jeyi can?,ke mema???" Nafisa ta katse meman cikin zabura,tun kafin ta gama bayanin nata,dariya mema ta saki sannan tace "Share kawai" "Ohk....ya zama dole ki dawo to" "Saboda me?" Ta fada a dan tsiwace "Saboda matsalata,kin sani sarai bana son jira?" "Haba hajiyata....kinsan me ya kawoni nan din?,asara kikeson janyomin kenan" "Har ta nawa?" Ta tambayeta kai tsaye "Dubu dari ce ba yawa" "Zan biya....ki tabbatar gobe kin dawo,wajen yammaci mu hadu a indomie joint" "Allah ya barmin hajiyata,karkiji komai,bari na fara hada kayana" ta katse wayar yana fadawa saman katifar dakinta,ba wani benin da taje,ba nisa tayi ba,don a yanzu haka ma tana cikin katsina. Aje wayar nafisa tayi,sannan ta juya ta shige bandaki. Jujjuya wayar yake a hannunshi bayan ya kammala karanta saqon nafisan,sau tari bai fiya maida mata amsa ba,har hakan ya zame mata jiki bata fiya damuwa ba,har zuciyarshi yake hakan bawai da gayya bane,bayajin wani abu dangane da duk wata kalma da zata fito daga bakinta ko ta saqon waya,maida wayar yayi aljihunsa sannan ya fito daga motar tashi ya kashe ya tunkari ginin kamfanin.*ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER* 07067124863 *KO KUMA* 09032345899 *ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sabbabi,karku manta ku danna SUBSCRIBE,kuyi LIKE sannan kuyi SHARING🙏🏽* 👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽 https://www.youtube.com/channel/UC4kJO342hmb_Pd2luKHBjFA/videos *AA* 0️⃣6️⃣ Saida gari ya danyi duhu kadan sannan ya dawo cikin gidan,ya duba garinsa yayi laushi,ya zuba suger dai dai gwargwado ya zauna gefan 'yar katifarsa ya soma sha,inda ya kunna redio da wayarsa qarama keypad samfutin tecno yana sauraren labarai. Kafin ya kammala an kirayi isha'i,sake miqewa yayi ya fice zuwa masallaci,don sam baya wasa da sallar cikin jam'i,koda aka idar nan majalisar dake kusa da gidanshi yadan xauna aka taba hira,bai jima can da yawa yayi sallama dasu,kasancewar yana da masaniyar gobe yana da lacture ta qarfe tara,kuma dama bai fiya zama cikinsu ba ba dabi'arsa bace wannan,hakan yasanya wasu kejin haushinsa tare da yi masa kallon mai girman kai,yakan zauna lokaci zuwa lokaci saboda kauda wannan zargin daga ransu,bugu da qari ya sani dole kuwa ya fita tun bakwai,don kuwa da qafarshi yake takawa har zuwa makarantar,zuwanshi mota a abun hawa abune mai matuqar sa'a,imma wani aikin qarfin ya samu yayi ya samu kudi,ko idan anty usaina ta d'anyi samuwa ta kirashi ta bashi wani abun,ko Allah ya hadashi da d'aya daga cikin 'yan makarantarsu ya rage masa hanya. Allah ya taimakeshi yau cikinsu ba wanda ya shigo masa gida,saboda haka ya kulle ko ina yayi nafilfilunsa kamar yadda ya saba,ya roqawa iyayensa da 'yan uwanshi gafara sannan ya kwanta bayan ya sake kunna rediyon yana sauraren shirye shiryen da sukeyi. Sannu a hankali tunaninta ya kutso cikin kaiwa da kawowar da qwaqwalwarsa keyi tun dazu,ya dan saki murmushi yana wassafo kamanninta,yanayinta tsarinta da tafiyarta,da ganinta zatayi hankali,da ganinta akwai nutsuwa tattare da ita,da ganinta ba maison hayaniya bace "Duk taya akayi kasan hakan?" Ya tambayi kansa da kansa,saiya sakarwa kansa murmushi yana girgixa kai gami da runtse idanunsa,shima baisan ya akayi ya tsinci kansa da fadawa wannan bigiren ba,saiya juya zuwa daya barin yana son maoda hankalinsa kan programe din da ake gudanarwa a gidan redio a sannan. Tun bayan sallar magariba ummantata keta sintirin aiken qannen nata kan ta fito taci abinci,saidai sam ta qiya,tayi kwanciyarta abinta,ranta ne kawai ke mata suya,a duk sanda irin wannan balahirar ta faru a gidansu idan da safe ne wuni take cikin qunci da damuwa,hakanan idan da yammaci ne koda dare kwana take cikin qunci shima da damuwa,wani lokacin takance inama kurma Allah ya halicceta?,inama makauniya ce ita ta huta da ganin wannan baqon lamari,wanda ya zama tambarin gidansu,ya kuma zama abinda jama'ar unguwa ke goranta musu dashi,don babu wanda baisan irin rayuwar da ake tsakanin uammansu da babansu ba,tayi kuka har sau babu adadi,tabi hanyoyin gyara bila adadin amma babu alamun ma sauyi bare akai ga gyaran gaba daya,tayi tunani iri daban daban masu kyau da marasa kyau amma bata samu hanya mai bullewa ba,tayi yaji tabar gidan batasan adadin sau nawa ba amma sun bita sun dawo da ita kan alqawarin komai ya wuce zasu gyara amma babu alamun sauyawar lamuran,ta tambayesu me yasa suke hakan amma su kansu basu san amsa ba,abu d'aya ta sani shine,dukkaninsu tsakanin ummanta da babanta babu wani mai haquri acikinsu,ummanta bata da haquri ko kad'an kamar yadda mahaifinta yake,bata raga masa ko daya,idan ya mata taga bai mata dai dai ba take zata rama,shi kuma yaga ta rainashi kenan haka zai biye mata suyita yi. Basu san ciwon da hakan ke mata a qirjinta ba,basu san illar dahakan ke haifarwa ga tarbiyya yara da tunaninsu da ginuwar hankalinsu,iyayenka a wannan bigiren na fada da juna kulli yaumin har sauran jama'a su shaida hakan kai me yayi saura a rayuwarka?. Saida umman taga da gaske take bazataci abincin ba kamar yadda ta saba a duk sanda ta samesu suna cecekuceb da suka saba,saita dire faruqu ta nufi dakin nata,ta yaye labulen tana tsaye daga dokin qofa tace "Tunda sai abinda kikaga dama zakiyi bismillah,dadin abun cikinki ne ba nawa ba,yunwa kuwa dai dai take dake matsalarki ce wannan,ki tashi ki gayamin ya akayi sauran botikaina sabbi suka fashe haka?" Da qyar ta juya daga kwancen da take ta d'aga kai ta dubeta "Wasune garin wawaso suka fasa su" "Botikan duka?" Kai ta gyada mata "K'nnnn,ai shikenan,Allah ya kyauta" ta fada tana sakin labulen,maida kanta tayi ta kwantar,inama ace haka takewa mahaifinsu a duk sanda wani abu ya hadosu?,ta tabbatar da shine tsautsayi irin haka ya faru da yau Allah ne kadai yasan qarshen fadansu. Mubina ce ta shigo da kwananon abincin ta dire mata ta juya ta fice,bata dai kallesu ba tana ci gaba da kwanciyar "Idan baki tashi kin kama abinci kinci ba na shigo sai nayi mugun saba miki" ta jiyo muryar umman daga tsakar gida tana gaya mata,hakanan badon son ranta ba ta sauko ta tanqwashe qafa ta dinga cusa abincin har sai dataji kaman zatayi amai sannan ta maida murfin ta rufe ta sake kwanciya. Runtse idanunta tayi tana fatar bacci ya dauketa,sai taga wata fuska data sanyata saurin sake bude idanunta,dawo mata yayi tar a kwanyarta,bacin ran da take ciki yasa bata sake tunowa dashi ba sai yanzu,saita gyara kwanciyarta tana kallon bango,ta dinga tuno fuskarsa da yadda tafiyarsu ta kasance daga bakin masallaci har zuwa gida,hakanan taji nauyi da bacin ran zuciyarta ya ragu sosai,ta shagala da tunanin daya d'auketa zuwa bacci mai nauyi. Qarfe biyu na rana gaba ya tsinci kansa hankalinsa ya tafi bakin masallaci gurin da ba wajen zuwansa bane idan ba shagin balarabe zashi ba ko wani babban uzurin ya kamashi na zuwa wajen,sai ya sake tsintar kansa da sake yin wanka bayan ya gama hutawa duk da kusan dabi'arsa ce a duk sanda ya dawo daga makaranta,amma wannan karon saiya laluba kayanshi har ya zaro zai saka ya maida ya sauya wasu,abinda bai taba yi ba,bai taba damuwa da suturar da zai saka,kawai dai yasan dukka kayan sawarshi a tsaftace suke kullum,hakanan basa rabo da guga,duk da cewa ba wasu masu shegen kyau da tsada bane,Allah dai yayi masa wata baiwa ta duk kayan daya saka jikinsa na dauka,hakan yasa matasan anguwar da dama ya tsone musu ido,wanda yawancinsu dukka sunfishi gata rufin asiri da komai da komai,tsaftarsa tasa baka gane kaashinsa. "Ki kulamin da botikai na,karki sake bari su fasamim botiki,kai jamilu idan ka aje mata ka dawo ka kaimin shara" cewar ummanta wadda take rufe botikin abincin data gama zubawa almajirin ya qaraso wajen ya dora a kanshi suka fice tanawa umman sallama. Har sunje soron gidan hakanan taja ta tsaya,saita juya da hanzari ta koma ciki "A'ah,lafiyarki kuwa?" Umman tata da taga wucewarta ciki ta fada "Lafiya umma ina zuwa" kai tsaye ta dauko dan kwandon kayan kwalliyarta dake saman akwatin kayanta,ta ciro ruwan madubi mai fadi dake soke a ciki ta kalli fuskarta "Hoda na miki kyau wallahi shahida,don Allah ki dinga d'an shafawa mana" ta tuna maganar da qawarta ta gaya mata daxu a makarantar boko,saita samu kanta da ciro hodar ta bude ta shafa,data sake kallon fuskarta sai taga ta canza din kuwa,sosai hodar tayi mata kyau ta sake fidda kyau da qyallin fuskarta,murmushi ta saki ta aje mudubin ta juya ta fice da sauri. Yana zaune daga shagon balarabe yana kallon duk wani motsinta dake bayyanar da hankali da nutsuwarta da kuma ainihin ita wace,duk surutu da hirar da balaraben yake masa baya gane abinda yake fada sam,shi kuma bai fahimta ba bare yaja bakinsa yayi shuru ya barshi. Haka ta dinga raba abincin kamar yadda ta saba,saidai tanata dube duben kadan kadan da batasan meye dalili ba,harta kammala tsaf ta hada kwanukanta waje daya,haka kawai saitaji ranta ya baci lokacin data gama shirin komawa gida,duqawa tayi don daukar botikan taga an sako hannu an dauka,da hanzari ta dago don ganin waye?,ta tsammaci ma su ahmadi ne ma basu gargadin da aka musu jiya ba yau suka dawo,saidai ga mamakinta saurayin jiya ne,gaba yayi abinsa sai tabi bayansa sukaci gaba da tafiya ba tare da kowa yace da d'an uwansa wani sbu ba. Basuyi wani nisa ba ya janye ta koma ita ce a gaba shi yana baya,bata kawo komai a ranta ba ta tsammaci bazai gane gidan nasu ba shi yasa yayi hakan,kamar tafiyar jiya har suka je inda ya dakata a jiya ya aje mata botikin,saidai yau din ta daga ido ta kalleshi,akaci sa'a shima ya kalleta a sannan,wani irin zallar kyau da kwarjini idanunta suka gani,sai taji wani abu tun daga qwaqwalwarta har tafin qafarta,mazewa tayi gami da d'auke kai tana jin izzarta ta diya mace na motsawa,a nashi bangaren ma wani abu mai qarfi yaji yana janshi game da ita tamkar maganadisu da mayen qarfe,sai bakinsa yayi nauyi,bai furta mata komai ba ya juya ya soma takawa don barin wajen,daga manyan idanunta tayi tana bin bayanshi da kallo har sai daya bacewa ganinta,batasan me yasa ba bakuma tasan sanda ta saki murmushi ba ta daukin botikin nata ta fada gida. Tsahon kwana uku irin hakan na faruwa tsakaninsu,ba wata magana data taba shiga tsakaninsu,duk sanda tayi yunqurin yin wata magana saita kasa sabida kwarjinin da yake mata,tana son tace ya daina rakota saboda ganin yadda idon sa'idinawan unguwa ya soma dawowa kansu saidai ta kasa furta masa hakan,cikin ranta takejin nishadi a duk sanda suke wannan tafiyar ta kurame tun daga masallaci zuwa qofar gidansu,ko sunanshi bata sani ba,sai taga meye nata na tambayar sunansa ma,aishi ya kamata ya soma tambayarta sunanta,wani sashe na zuciyarta ya qalubalanceta da a'ah ba haka ake ba,ke yakewa alkhairi,ko godiya baki taba yi masa ba kan rakokin da yake,ta jinjina kai tana tabbatarwa da kanta rashin kyautawarta,ta kuma quduri aniyar a gobe zata masa godiya ta kuma tambayi sunanshi,kai ta girgiza kuma tana sake sakin murmushi,batasan dalilin daya sanya take yawan tunashi ba,batasan me yasa takejin wani baqon yanayi game dashi ba tun ranar data soma dora idanunta a kanshi,bata da amsa,tilas ta aje tunaninta a gefe sanda ta jiyo muryar babanta sun soma rabon halin nasu shi da ummanta,saita miqe a hankali ta isa bakin windon dakinta,ta yaye dan labulen net din dake maqale jikin window din tana kallon yadda suke dagawa juna murya kamar zasu yagi juna,batasan lokacin da wani hawayen baqinciki ya sauko mata ba,baqinciki da b'acin rai ya bata dukkan wani farinciki data tsinci kanta a ciki,wannan wacce irin rayuwa ce?,ina zata je ta daina ganin wannan baqincikin da bacin ran?,tabbas da akwai inda zata ta qauracewa wannan masifar da tuni ta jima da tafiya,tana son mamarta,hakanan tana son bananta,duk cikinsu babu wanda take goyon baya a cikinsu,batasan me yasa suka zabi wannan rayuwar ba bayan ga zuria suna tarawa,hakanan kowa yayi musu shaidar kyakkyawar mu'amala a waje amma me yasa gidan aurensu ya gurbace haka kamar sansanin yaqi?,haka ta zauna cikin dakin ita d'aya tana rusar kuka harta gaji da jin sautukansu ta dannan kanta qarqashin filo tana ci gaba da zubda ruwan hawaye. Kamar kowanne lokaci yauma ta shirya tsaf cikin atamfa riga da zani,sai hijabi mai hannu da yasha guga,kasancewar ummanta mai tsafta ce,hakan ya sanya dukka yaranta tun daga kan shahida zuwa faruqu zaka samesu fes dasu,hakanan ma gidanta da duk abinda ya shafi gidan,sosai higabi mai madauri purpule colour yayi mata kyau sosai,yau shigar ta musamman ce ita kanta tana jin hakan a jikinta,yau mai d'aukar matan bai qaraso ba tilas tadan zauna jiran zuwansa,tun tana jin ba komai harta soma qaguwa,haka kawai taji ra zaqu taje wajen,ta leqo agogo yafi sau nawa amma shuru yaron bai iso ba,saita kasa zama taci gaba da duba agogo har ummanta ta fuskanci haka,iya saninta shahida na zuwa kai sadakar abincin nan ne don kawai tana tsananin jin nauyin uncle isma'il,kusan kullum fuska a hade take tafiya a haka kuma take dawowa "Ya akayi ne shahida?,ko tsoron makara islamiyya kike?" Cikin rashin jin dadin ranta ta kada kanta "Toko yau zaki zauna kawai idan yazo saiya kai shi?" "A'ah umma....zan kai bari dai yaxo din" ta fada da hanzari,don bata jin zata iya jurewa rashin zuwanta wajen "To ai shikenan" umman tata ta fada tana kwashe shanyar kayan sawarsu da shahidan ta gama wankewa daxu,ciki harda ba mahaifinta don sam bata da quya ko gandar aiki. Yana isowa ko zama bata barshi yayi ba ta sakashi ya dauka suka wuce,sai taga kaman bata sauri,kamar tabar wani yana jiranta,haka dinga ji har suka isa wajen. Daga nashi bangare shima har ya soma tunanin me ya hanata zuwa har yanzu?,yana daga zaune cikin shagon bala yana duba agogon wayarshi,sama sama yake amsawa bala hirarsa,ya daga kai don sake kallon muhallin da take zama din sai yaga isowarta,wata ajiyar zuciya ya sauke ya zuba mata ido daga inda yake,kaman ance mata ta waiwayo sai suka hada ido,ta danso ta dirirce amma saita maze,ta samu waje ta zauna yayin da kowa ya soma fitowa da kwanonshi yana amsa. Duk motsin da take sai taji kama idanunsa ne a kanta,eh ba kama bane kallon nata yake,a yau ya hana kansa kallonta,duk da ta kamashi yana kallon nata yafi sau shurin masaki amma ya gaza dainawa,haka suka dinga hada ido lokaci zuwa lokaci har abincin ya qare,hakanan yau take jin wani faduwar gaba,ta dinga hada kwanukanta da sauri tana son yau ta bace masa,saidai burinta bai cika ba,tana gama hadawar ya iso wajen,ya dauki botikin ya soma takawa,bata da abinyi illa binsa. Suna isa inda suka saba ta zaci zaiyi yadda ya saba,amma ga sabanin tunaninta wannan karon sai yaja ya tsaya tsam yana riqe da botikin "Baki da kirki" taji ya ambata,ba shiri ta dago suka hada ido,qwayar idonta cikin nasa,yayi.mata wani kallo fuskarsa dauke da murmushin da yasa gudun zuciyarta qaruwa,cikin hanzari ta sadda kanta jin yadda yake shirin karya lagonta cikin qaramin lokaci "Nima na san haka ko baka fada ba....kayi haquri.....na gode da karamcin daka yimin harna tsahon kwana hudu,Allah ya saka maka da alkhairi" "Amin...amma bawai kyauta nayimiki ba,nayi miki ne donki biyani" ya fada cikin salon tsokana,a nata bangaren ta zata da gaske yake,take mummunan tunani ya darsu a ranta game dashi,baya ta danja kadan sannan tace "Ni bani da kudin biyanka,tun farko ma bansan biyanka kakeso nayiba da nace ka barshi" kai yake girgixawa dariya nason subuce masa,dariyar data qara masa kyau har tasa adam apple dinsa ya dinga motsawa "Ba kudi nakeso ba 'yammata....zuciyarki kawai nakeso ki mallaka min" ya tsinci kansa da fada,don ya shagalta da kallonta har baisan maganar da yake qasan zuciyarshi ya bayyana ba,a bazata taji maganar,don bata taba tsayawa ga da ga wani namiji ya gaya mata hakan ba ita dashi baki da baki sai wannan karon,ganin ta riga dataji me yake fada ya sanyashi kada kanshi yana ci gaba da jifanta da murmushi "Eh zuciyarki nakeso" cikin mintina qalilan kwanyarta ta hakaito mata abinda yake nufi,wata iriyar kunya da nauyi suka kamata,ta rasa tudun dafaww,saboda haka saita juya gudu gudu sauri sauri ta shige gida,yana tsaya mana amma ina ba zata iya ba,bata taba zaton a shekarunta sha biyar akwai saurayin da zai gaya mata wai yana sonta ba,kalmar tayi mata nauyi da yawa. Murmushin jin dadi ya saki,ya zauna dakalin dake daura da gidansu,abinka da d'an makaranta ba'a rabashi da takarda,sai ya ciro qaramar jotter din dake aljihun wandonshi wanda ya gama duba wani karatu da ita yayi rubutu da basu wuce layi goma ba ya jefa cikin botikin,ya kira yaro ya bashi botikin shi kuma ya wuce. *ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER* 07067124863 *KO KUMA* 09032345899 *ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sabbabi,karku manta ky danna SUBSCRIBE,kuyi LIKE sannan kuyi SHARING🙏🏽* 👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽 https://www.youtube.com/channel/UC4kJO342hmb_Pd2luKHBjFA/videos*ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER* 07067124863 *KO KUMA* 09032345899 *ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sabbabi,karku manta ky danna SUBSCRIBE,kuyi LIKE sannan kuyi SHARING🙏🏽* 👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽 https://www.youtube.com/channel/UC4kJO342hmb_Pd2luKHBjFA/videos *Alqawarin Allah* 0️⃣7️⃣ Saida umma ta dinga qwala mata kira kan ta fito ta wanke kwanukan ta dauki abincinta taci kada lokacin islamiyya ya wuce sannan ta taso daga rub da cikin da tayi saman katifarta,ta harhada kwanukan ta kada ruwan kumfa ta soma sabesu,tanayi tana tunanin kalmar daya furta mata,ashe kalma ce mai nauyu da dadi haka,lokaci lokaci ta dinga sakin murmushi ita daya,harta zubawa botikin ruwa ta zubda ruwan sai taga takardar,ta tsame hannunta cikin kumfar ta dauki takardar sannan ta bude. Soma fahimta da tayi takardar meye yasa tayi sauri ta shige dakinta,ta samu kebantaccen waje ta budeta inda zata sha iska ta bushe sosai sannan ta dawo taci gaba da wanke wankenta. Kafin ta kammala shirin islamiyyarta saiga qawarta zunnurah ta iso cikin unifoarm din islamiyya "Yauwa,dama banason cin abincin nan ni kadai,don Allah bari na dauko ki tayani" cewar shahida tana nufar kitchen ta fito da kwanon abincinta ta aje a qasa ta zauna dirshan "Sauko malama muci" "Ke nifa a qoshe nake wallahi ba abincin da zan iya ci" "Ni zakima wulaqanci ko?,zaki sake cewa naci abinci a gidanku" tq fada tana saka hannu tayi bismillah ta soma ci zunnurah na mata dariya,wai ita zata cewa tana cin abincin gidansu,matar da nata abincin ma sai ya huce bata ci ba,hira suke jifa jifa shahida nacin abincin tana kuma duba lokaci kada a fito saga sallah a shiga aji basu tafi ba,saidai rabi da rabin hankalinta nakan takardarta dake shan iska "Yauwa shahida....wai waye wanda yake rakoki ne kullum daga wajen sadaka" tsaida lomar da zata saka a bakinta tayi tana duban zunnuran "Au har kin samu labari kema?" Harara ta watsa mata "Uwar labari na samu,waye baya ganinku a tare wai kwana hudu kenan,tunda ansan baki kula kowa...." "K'nnnn...nima ban sanshi ba wallahi zunnurah,acan nake ganinsa" dariya zunnurah ta saki "Qawata nasan halinki sarai,duk yadda akai wannan din na dabanne tunda har kika kasa gwada masa halinki" murmushi ta saka,ita kanta tasan na daban dinne nasai zunnurah ta fada ba,tun kallon farko taji yakai mata ko ina,ganin farko taji wani qaqqarfan lamari dangane dashi,takan iya raba dare tana tunaninsa,kowanne second nata da tunaninsa take rayuwa "Amma fa kinsan shaik hafiz zai shiga wani hali?" Dagowa tayi tana duban zunnurah kafin ta galla mata harara "Kamar yaya?,sonshi nake?,ko ce miki yayi yana sona" nan ta zauna tsaf ta kwashe mata yadda dukkan dalibai suka lura da soyayyar da yake mata,baki ta tabe tana miqewa daga gaban kwanon,don ita dai tasan ko doguwar magana bata hadata dashi bare kuma wani abu daban can,fita tayi ta wanke hannunta ta dawo tana ware gogaggen hijabinta "Qawata baki da mutunci fa,shaik ke kanki kinsan yammatan makaranta rububinsa suke,kuma kema kanki qaryarki kice baki san yana sonki ba,maimakon kiyi murna sainaga ke ko a jikinki labarin bai faranta miki ba ko d'aya" "Don Allah zunnurah ki qyaleni da zancansa,sai....." Maganar tata ta katse jin sallamar fiddausi,yarinyar da tsakanin gidansu shahida da nasu gidan layi biyu ne,tun zuwanta islamiyyarsu shahida takeson qawance da ita,tun shahidan na janyewa harta saki jiki da ita,saboda ta lura yarinyar itama nada hankali,yawan shuru shuru da rashin son hayaniya. Tuni zunnurah ta hade rai,hakanan a duniya taji sam fiddausi bata yi mata ba,ko kadan jininsu ya kasa haduwa,shahida ta rasa dalili,tun tana sharewa har tazo tanawa zunnurah fadan ta daina haka,wulaqanta dan adam babu kyau,yarinyar na sonsu hakanan bata da wata matsala meye abun sha mata qamshi da take "Hakanan wallahi nidai naji batayimin ba" amsar da zunnurah ta baiwa shahida kenan. A tsakar gida fiddausi ta duqa ta gaida umma cikin ladabi,ta amsa ba tare data tsaya ta mata wani cikakken kallo ba taci gaba da sabgoginta(babban kuskure na biyu da ummanta ta sake tafkawa bayan fada da miji gaban 'ya'ya),fiddausi ta shige dakin shahida,cikin fara'a suka gaisa ita da shahida,yayin da xunnurah ta kauda kai ta amsawa fiddausin sama sama,dif zunnurah tayi sai shahidan da fiddausi dake hira sama sama,har shahida ta gama shiryawa suka fice daga gidan. Suna gab da shiga gate din makarantar xunnurah ta kamo hannun shahida tayi baya da ita,duk sai suka tsaya ta hade gira tace da fiddausi "Me kike jira?,magana zamuyi da ita" sum sum fiddausi ta juya ta wuce ciki "Wai me yasa kikeson koyon halin daba naki ba zunnurah me fiddausi tayi miki?" "Shahida,ba haka kawai naji banson yarinyar nan ba,an bani labari fiddausi tana taba shaye shaye..." Rufe bakinta shahida tayi da hannu tana kallon zunnurah gami da zaro ido "Haba zunnurah,haba,zato fa ance zunubi ne,ya zaki jefeta da wannan mummunan kalmar don kawai tana son mu'amala damu?" "Da gaske nake miki shahida,daga bakin namiji na samu wannan labarin,kinsan kuwa su basu fiye munafunci kosa ido ba bare kice,sannan kuma idan zaki lura da kyau zaki ga yanayin fiddausi ba irin namu bane,yawan bacci da kasala kawai alamune na mutum yana taba shaye shaye,zaman kadaici rashin so magana da yawa" zame hannunta shahida tayi daga na zunnurah,don sosai taji babu dadi ta kuma ji ranta ya baci "Duk abinda kika fada zunnurah baki da tabbaci a kanshi,karki fadi abinda zaki jawo a tsaidaki a miki hisabi ran gobe qiyama,ni fiddausi ta gayamin bata da cikakkiyar lafiya,tana da sicklier shi yasa take yawan bacci" kada kai zunnurah tayi "Shikenan shahida tunda baki yadda dani ba,kinfi kowa amma sanin halina,nidai ina baki shawara kibi a hankali,don bazanso abinda zai cutar dake ba" "Babu abinda zai faru in sha Allahu" daga wannan suka rankaya suka shige cikin makarantar. Washegari da wuri taje wajen bada sadaka ba kamar yadda ta saba zuwa ba,hakanan takejin wani nauyi da kunya tunda ta karanta kalaman da yarubuta mata jikin takarda,niyyarta tayi da wuri ta koma gida ba tare daya sameta ba,saidai abinda bata sani ba tuni ya rugata ma zuwa,saboda gaba daya ya rasa nutsuwarshi Allah Allah yake gari ya waye yamma tayi yaje ya ganta,bai taba tsintar kansa cikin irin wannan yanayin ba,duk yanayin rayuwa da yake ciki hakan bai hanashi bacci ba,sai gashi a karon farko saboda ita ya kasa bacci daren ranar gaba daya,duk juyin da zaiyi itace cikin ranshi. Yana biye da ita bata sani ba,baiyi mata magana ba saida suka gota wajen suka shiga wani layi "Yanzu yau kuma haramiyar ladan rakiyar za'a yimin?,wanne irin laifi nayi haka?" Cak ta tsaya,farinciki da kuma faduwar gaba na cakuduwa cikin ranta,idanunta a waje har ya iso gabanta yasa hannu ya amshi botikin,ya jera kafada da ita "Muje" ya fada cikin sassanyar muryarta da kullum take mamakin dad'in muryar da Allah ya bashi,idan yana magana dole sound dinshi yaja hankalin duk mai sauraro,yau saitakejin nauyin tafiya dashi,ta kasa yin gaba,ya sake dubanta "Waiko amsar tambayata itace a'ah akemin irin hakane" wani wal tayi da ido,saiya dafe qirjinsa da hannunsa daya "Kiyi haquri karki qarasa tarwatsamin zuciya,wannan zuciyar mai rauni ce akanki" Fuskarta ta qunshe cikin hijabinta tana dariya qasa qasa,wawiyar ajiyar zuciya ya saki "Wai Allah na,alhmdlh,ko iya haka aka tsaya na tabbatar da cewa ina da nasara...amma dai a gayamin ana sona?" Kai ta kada cike da tsananin kunyarsa,wani dan tsalle ya saka sannan yace "Alhmdlh,alhmdlh" yana rungume da hannayensa. A hankali suka ci gaba da takawa shida ita,saidai ita gaba daya nauyinsa takeji,yayin da shi kuma yake janta da hira jefi jefi,yau duk masu binsu da kallo mutanen cikin unguwarsu basu dameta ba,har sai taji ma batason su isa gida yace zai wuce. "Kina son wanda bakisan sunanshi ba hakanan bakisan waye shi ba" ya fada bayan ya miqa mata botikinta,ita sam bata damu da wayeshi ba,sonsa takeji irin wanda bata taba zata ko tsammatar akwai irinsa ba a duniya,tanajin koma wayeshi yayi mata hakan "Ni sunana muhammad anwar aminu,haifaffen kano ne kuma dan kusa da unguwarku ne ni,maraya ne ni bani da uwa bani da uba,sai 'yar uwata d'aya data ragemin anty usaina,ina karatu ne a fce kano...kefa?,shahida ko?" Murmushi ta saki tana dubanshi cikin tausayi jin cewa maraya ne,kai ta kada sannan tace "Khadija amma shahida,nice ta farko wajen umma da abbana,ina da qanne hudu,nan ne gidanmu a nan aka haifeni,ina SS 2 yanzu" kai ya kada sannan yace "Idan nazo anjima za'a barni na ganki" kai ta gyada da sauri,don tasan yadda zatawa ummanta bayani yadda zata fahimta "Shikenan zanzo anjima in sha Allahu,inason mu soma mu'amala cikin fahimtar juna gaskiya da amana...ki shiga gida lokacin islamiyya ya kusa ko?" "Na gode" ta furta cikin siririyar muryarta data dauki hankalinsa,kai kawai ya iya gyadawa ya bita da kallo harta shige. "Waye a waje kuke tsaye dashi?" Tambayar da ummanta ta soma jefo mata kenan sanda ta aje botikin tana shirin zama,kunya ta d'anji ta kamata,saita kasa amsa mata da wuri har sai data maimaita "Ba kowa umm,yadai taba rakoni gida sanda su ahmadi suka fasamin botiki,shine...shine...." Saita kasa qarasawa,murmushi kadan ummantata tayi,saboda burinta bai wuce su aurar da shahida ba da zarar ta kammala secondry schl,ita kanta tasan basa kyauta mata yadda koda yaushe suke cikin fada da juna suna sakata kuka qunci da baqinciki "Shine me?" Ta sake tambayarta tana tura mata kwanon da tayi kwadon zogale ta rage mata saboda tasan tana sonshi,sai data sadda kai sannan tace "Shine yace wai anjima zaizo idan za'a barni na fita" "Allah ya kaimu" ta fada tana miqewa don ta wanko hannunta,cikin farinciki taja kwanon ta soma cin zogalenta,wanda tana gamawa ta shige bandaki ta sake watsa ruwa saboda ranar da ake,fitowarta kenan daga bandaki dauke kwandon wanka zunnurah ta iso,tana shiryawa tace "Zunnu...akwai labari fa yau"bakin zunnnura a washe tace " ta samu kenan?"kidai muje na baki kisha,ta fada tana zura plate shoes dinta,ta dauki jakarta suka leqa suka yiwa umma sallama suka wuce. A hanya ta labartawa zunnurah komai,dariya ta dinga "Kai amma wannan gayen yayi addu'a tuquru kafin yazo,shahida da babu wanda ya isheta kallo?,da kinga wata da saurayi ma zakice wannan ai iskamci ne dududu shekarunmu nawa?,ashe harkin girma" dundu ta dumawa zunnurah "Banason iskanci qawa,wallahi nayi mamaki nima sosai,dama haka abun yake?,kinji kuwa yadda nakejinsa a raina?,har banason mu rabu,idan yana kallona wlh zunnurah ni kadai nasan me nake ji a zuciyata,ban taba tsammanin akwai wani da zanji haka a kansa ba" dariya zunnurah taketa tiqawa "Na shiga uku ni zunnu,sati daya kacal amma shine kika zare haka?,Allah yasa to nan gaba kar ya haukatamin qawa ya cuceni" "Ba komai idan ya haukataninma zunnu" ta fada tana tayata dariyar,gab da zasu shiga makarantar sukayi kacibus da fiddausi,da fara'arta take musu magana amma shahida ce kawai ta amsa suka rankaya suka shige makarantar tare. Tunda ta dawo daga islamiyya ta kasa zaune ta kasa tsaye,qiyasta da qimanta yadda haduwarsu zata kasance take,wannan ne karon farko data soma son wani a rayuwarta,kuma karon farko da zata fara tsayawa zance da wani. Tuni ummanta ta yiwa babanta bayani,bai kuma ce komai ba,illa ya kirata ya masa tambayoyi game da shi,ta bashi amsa gwargwadon abinda ta sani game dashi,yace ta kula kuma idan sun fahimci juna zaiyi magana da yaron. Ba wani kwalliya tayi ba,tadai saka kayanta masu kyau atamfa riga da skert,ta kuma yafa wadataccen mayafinta,sanda ya aiko kiranta tare da mubina suka fita,yana zaune saman yalwataccen dakalin qofar gidansu,daga soron ta tsaya tana qare masa kallo,yayi kyau sosai fiye da dazun cikin qananun kaya,iya kwanakin kadai da tayi tana ganinsa ya tabbatar da cewa shi din dan gayune kuma mutum mai son tsafta,bata taba ganin kayanshi babu guga ba,hakanan bata taba ganinsa da datti ko wani abu makamancin haka ba "Daure ki fito princess...saiki kallenin da kyau" habawa,wata iriyar kunya ta taso ta lullubeta,bata taba tsammanin yana kallonta ba,saita sake lafewa ta kasa fitowa,tashi yayi yana murmushi ya tsaya a qofar soron nasu yana kallon mubina dake gaidashi,ya amsa yana shafa kanta gami da yi mata wasu tambayoyi tana amsa masa,rabi duk a kan shahidan ne,kunya duk ta sake kamata ganin yadda mubina ba abinda ya shalleta,komai ya tambayeta gaya mishi take,saida suka gama hirarsu sannan yace "ALLAH YA TAIMAKEKI...kona koma ne yau ba za'a samu ganina ba?" Dole ta fito ta saka musu tabarma daga soron nasu,da yake yana da yalwa sosai masu wucewa ba zasu takurasu ba. Gaisheshi ta sakeyi ya amsa yana tambayarta gida kaman ba dazu suka rabu ba,cikin wani shauqi da yake fusgarsu gaba dayansu.https://www.youtube.com/channel/UC4kJO342hmb_Pd2luKHBjFA/videos *ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER* 07067124863 *KO KUMA* 09032345899 *ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sabbabi,karku manta ky danna SUBSCRIBE,kuyi LIKE sannan kuyi SHARING🙏🏽* 👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽 https://www.youtube.com/channel/UC4kJO342hmb_Pd2luKHBjFA/videos ALQAWARIN ALLAH 08 Anwar dinne ya soma cewa"Kamar yadda kika sani na gaya miki daxun cikakken suna na sannan kuma ni maraya ne,na rasa mahaifina da mahaifiyata da qannena guda biyu duka rana guda" zaro idanu shahida tayi cike da mamaki da tausayi tana duban anwar "Eh rana daya,sanadiyyar hatsarin mota da sukayi a hanyarsu ta dawowa daga qauyenmu" "Wayyo....Allahu akhbar" ta fada fuskarta na nuna tsantsar tausayi,qwalla na cika idanunta,tausayin anwar ya kamata,rayuwa ba uwa ba uba ya zata kasance kenan? "Mu biyu muka rage a gidanmu,ni da yayata kaman yadda na gaya miki,yayata nada aure tun kafin rasuwar iyayenmu,yanzu haka tana gidan aurenta ni kadai na rage ina rayuwa a gidanmu,maganar gaskiya shahida zan gaya miki ba boye boye a tarayyarmu,saboda ina fata Allah ya shiga lamarinmu,niba mai kudi bane,bani da komai sai abinda Allah ya tsagamin,karki tsammacin samun rayuwa mai tsada,kyauta mai tsada ko nauyi daga wajena irin wanda samari sukewa 'yammatansu,indai kina ganin tafiyarmu akwai matsala,duk da tsananin soyayyar da raina ke miki zan iya haqura na barki da muradinki" kai take girgizawa,sam a batajin zata iya rabuwa da anwar,qaunarsu dashi daga Allah take,wata qauna ce mai qarfi data kama dukkaninsu cikin qasa da kwana bakwai,tasan cewa ba qaramin lamari bane a tsakaninsu "Ni dinma ba wata bace,kaman yadda kake gani rufin asirin Allah ne da dukka bawa yake qarqashinsa,ina addu'ar yadda muka hadu Allah ya tabbatar damu a haka" sai data fada kuma taji kunya ta kamata,sun d'an jima kadan suna hira ita dashi,yana bata labarin abinda yake karanta yanayin makarantar da dai sauransu. Qarar wayarsa ce ta sa ya dakata da abinda yake gaya mata,ya ciro wayar daga aljihunsa yana duba mai kiran,gabansa yadan fadi,don sam zuwansa wajen shahidan ya mantar dashi abinda ya tunkarosa,neman mudin rigestration,hausawa suka ce mai kurmin ido da wuri yake fara kuka,haka yake duk sanda suka soma exams tun a lokacin yake fara fafutukar neman kudin,wanda tunda ya soma karatu haka yake,Allah gatan bawa ne,sai yake bashi kafin lokacin da za'a rufe,saidai wannan karon yana fargaba,saboda ganin yadda rayuwa ta sake cudewa,fadi tashi ya yiwa mutane yawa,babu ta sake samun gindin zama a rayuwar al'umma. Saida aka sake kira ya sami ya daga da sauri,don babu ko ficika a layin nashi "Ina zuwa in sha Allahu" kawai yace ya latse wayar ya maida aljihu,miqewa yayi tsaye hannayensa cikin aljihun yana duban shahida qasa qasa,ta masa kyau qwarai,bai taba ganin macen data masa kyau kaman shahida ba,komai nata mai kyaune,tun daga yatsun qafarta har kanta,dauke kai yayi da sauri yana kwabar kansa daga kallon qurillar da yake mata sanda ta dago kai tana dubanshi sanda taga ya miqe "Allah ya taimakeki zan tafi" ya fada yana qawataccen murmushin daya sake fitar da sigar kyansa, "Allah ya tsare hanya...na gode"murmushi ya saki "nine da godiya,yau an shayar dani irin abinda nake ji abokaina na fada....zumar soyayya.....dama haka take?,haka akeji?" Dora tafin hannayenta tayi saman fuskarta ta rufe tana murmushin jin kunya,yayin da ya zuba mata idanu yana kallon zara zaran yatsun hannunta da suka dauki hankalinsa,ya sauke sassanyar ajiyar zuciya cikin ranshi yana roqon Allah daya sanya yana kammala karatunsa ya shiga cikin sahun daliban da suke samun aiki da wuri,don a yanzu jikinsa har ya soma sanyi da irin kyan daya lura shahida nashi,irin matan da masu kudi ke rububin samu su aure,Allah kada ya sanya shahidan ta subuce masa,ubangiji yasa rabonsa ce,da ya gama dacewa nan gidan duniya,tunanin daya dinga yi kenan har sukayi sallama ya wuce. Koda yaje inda ake kiran nasa ma ba wani biyan buqata ya samu ba,kudin da yake nema bai samu ba,amma sai sam baiji wata damuwa can ba wadda ya saba ji a baya duk sanda yaje neman kudin registration dinsa bai samu ba,wannan karon darensa cika yayi fal da tunaninta da begenta,ya dinga juyi saman katifarsa,ya danna wayarsa yana zargin kansa me yasa bai karbi number wayarta ba?,sai kuma ya saki murmushi daya tuna koya karba dinma ina yaga credit din kira?,da gaka ya lallashi kansa yana addu'ar Allah ya kaimu gobe lafiya. Tun daga wannan lokacin wata iriyar soyayya mai qarfi ta shiga tsakanin anwar da shahida,dukkan tunaninsa nata ne,duk wani motsinsa shahida na ciki,tuni labari ya kai kunnen anty usaina,kallon anwar din kawao tayi tana mamaki,tunda suke dashi bai taba kawo mata zancan wata yarinya ba,hasalima koda da tsokana tayi masa zancan budurwa tabe baki yake sannan yace "Uhmmmm,anty kenan,anata kai wa yake ta kaya?,yanzu kojin labari kikayi ina kula wata ba zaki tsawatarmin ba?,a wannan yanayin da muke ciki anty mu tsira da rayuwarmu ma,indai ina da abun kula budurwa na kasa baki ba shakka bani da wani amfani a rayuwa" tunda har taga yadda anwar ke muradin shahida sai batace komai ba,tunda haka ta faru tasan cewa soyayya ce tayi masa mugun kamun da bai zata ba "Su anwar manya,ashe an fada tarko" dariya yayi yana shafa kansa "Anty,shahida ta dabance,na soma sonta a sanda babu tsarin soyayya a rayuwata gaba daya,tana da hankali da kamun kai yarinyar,anty koke na kawowa shahida kika ganta zaki sota,fatana kawai Allah ya dubeni dana kammala karatun nan na samu aiki,na kula dake anty na kuma samu damar auren shahida" damuwar qaninta tata ce,su biyu suka ragewa juna a duniya,anwar irin mutanen nan ne jajurtattu,duk da bashi dashi,duk da shima neman dafawar wani yake amma indai ya samu ko yaya samun yake saiya tuna da ita,akwai sabo sosai a tsakaninsu,ba wanda ke iya boyewa wani wani abun,sun zama iyayen juna abokan shawarar juna "Kullum fatana kenan anwar,ina maka addu'ar wahalar da kakesha a rayuwarka ta zame maka alkhairi dajin dadin da har iyayenmu dake kwance a kabari xasu ji dadinsa" "Allah ya amsa anty" "Yanzu ya ake ciki da kudin resgistratin dinka?" Ta fada bayan ta aje masa shinkafa kwano guda da wake rabin kwano,wanda aduk sanda ta samu budi take bashi ya samu ya sauya kalar cimar da yake ci,duk da itama ahalin ni 'yasun take,amma haka suke raba wuya da dadi tare,kamar yadda idan shi dinne ma hakanne,duk da yana qoqarin boye mata wasu abubuwa da dama amma takan fuskanci wani abun koda bai gaya mata ba da bakinsa "Muci gaba da addu'a,in sha Allahu kafin sannan Allah zai kawo" "Allah ya dafa mana don isar annabi" "S A W" ya qarasa mata,daga haka ya miqe,saita kwance bakin zaninta,yasan me take da nufin yi saboda haka ya dakatar da ita "Ina da hamsin dina da zan hau mota,bar kudinki" kai ta daga tana kallonshi,tanason karanto gaskiyarsa ko akasin haka,don ya saba gaya mata haka,qarshe kuma dabawa yake a qafa har gida duk da tazarar dake tsakaninsu saboda bashi dako sisi,ganin haka saiya juya da sauri yana mata sallama,bai tsaya saurarenta ba ya fice. Yana tafe a hanya tunani fal ranshi,shi daya idanunsa sun kada sunyi ja,fatansa da addu'arsa Allah ya bashi abinda zai sakawa anty usaina dashi,tunanin shahida daya fado masa a rai shiya dauke duk wani radadi dake ransa,har ya murmusa shi kadai ba tare daya san ma yayi hakan ba,ya dinga tuna wuninsu na yau,yana zaune daga shagon balarabe kamar yadda ya saba yana more kallonta,lokaci lokaci sukan hada ido su sakarwa juna murmushi,wani kallo da yayi mata ya sanya man abincin dake hannunta ya kware duka cikin botikin shinkafar,kunya ta kamata yayin dashi kuma ya dinga mata dariya,har a hanyar komawarsu gida ya dinga tsokanarta kan ashe raguwa ce ita bai sani ba?,anya idan anyi aure zata iya dauke soyayyarsa kuwa?,kunya ta sakata guduwa ta barshi da botikin,sai mubina ce ta shigo dashi,wannan tunanin na shahida shi ya hanashi jin nisan tafiyar,har ya iso gida,sai yaji kamar baiyi tafiyar komai ba,bai zauna ba ya kunna risho dinsa ya dora shinkafar,sannan ya tube kayanshi ya shiga wanka saboda idan ya fito yaji dadin duba karatun jarrabawarsa. Cikin wasu 'yan qididdigaggun kwanaki qalilan wata iriyar alaqar soyayya mai qarfi ta qullu tsakanin shahida da anwar,wata iriyar soyayya mai ban mamaki da daure kai,zaka rantse da Allah sun doshi shekaru masu tsayi tare,kowannansu yayi amanna da d'an uwanshi,kowanne ya yarda cewa rayuwarshi ta d'an uwanshi ce,baqincikin dan uwanshi nasa ne haka farincikinsa,wuya da dad'i basujin zasu iya rabasu,qaddara kuwa sun jima dayi mata magiyar kada ta shiga tsakaninsu,komai nasu ya zama iri guda,tunanin da wannan yake a mafi yawancin lokutta zaku samu irinsa dan uwanshi yake,tamkar tare aka haliccesu haka sukeji,tamkar zuciya daya aka halitta musu su biyun kowanne bari daya na cikin jikinsa na aiki,anwar kullum kwanan duniya shike rakota gida,bayajin an halicci wani uzuri a duniya da zai iya hanashi rakota gida,yakan xauna a rumfar balarabe yana hangota cike da kishi,duk wani motsinta yana kan idanunshi,baya samun nutsuwa ko sukuni har sai ta kammala ya tattara mata kayanta ya kaita gida,da ace yana da iko da tuni ya hanata zuwa wajen,kishi yakanyi kamar xai halakashi duk sanda take zaune tana rabon abincin,daga bisanima da yaji bazai iya jurewa ba shike amsa ya zubawa kowa,itama a nata bangaren tanajin shine karsashinta,duk motsi d'aya idan zatayi saita daga kai ta kalli qwayar idanunshi take samun salama,tana jinsa har cikin jini da jijiyarta,zata iya sadaukar da komai dominshi,saidai tana mamakin yadda ko sau d'aya bai taba zuwa ya karbi abincin da take rabawar ba kamar yadda sauran mutane ke amsa. Bangare guda kuma bai taba gaya mata yanayin wahalar rayuwar da yake fuskanta ba,tadai san cewa bamai qarfi bane,hakanan yanayinsa ya tabbatar mata da cewa shi din mai wadatar zuci ne,don bata taba jin wani qorafi daga bakinsa ba,ko nunawa kasawa ko gajiya a fuska da jikinsa ba gaba daya,hakan kuma ya sake burgeta dashi,ya kuma sake saka mata qaunarsa. Yau bayan ya rakata sunyi sallama ta amshi botikinta ta juya zata shiga gida taga baquwar mota qofar gidan nasu,tana kallon motar ta tabbatar da cewa sunyi baqi ne,kuma bata raba d'ayan biyu uncle hisham ne,wanda shine ya baiwa ummanta kwangilar dafa abincin sadaka da kullum take kaiwa bakin masallaci a rabar,da farincikinta ta qarasa cikin gidan,don kuwa jininsu ya hadu qwarai da matarshi aunty zubaida,a tsakar gida ta taddasu,fuskarta washe da fara'a ta aje botikin nata ta qaraso saman tabarmar da suke zaune anty zubaida na cewa "Oyoyo 'yammata....sannu da qoqari" tana dariya dariya ta gaidasu,cikin kulawa suka amsa ta juya tana tambayar yaron anty zubaida na faro farouq yashe sukazo?, "Sannu da qoqari khadijatu....lallai na yarda ba qaramin qoqari da amana gareki ba.....gaskiya ali Allah yayi maka baiwa da yarinyar qwarai" cewar uncle hisham,kanta na duqetana murmushi "Alhamdulillahi kam,Allah ya azurtamu da diyar qwarai,mu kanmu muna alfahari da hakan" umma ma kai take jinjinawa,don ita kanta zata iya cewa cikin yaranta shahidan ta dabance,wani irin hankali da nutsuwa gareta,biyayya da kyautata iyaye tana sahun gaba,hakanan take qaunarsu,dalili kenan dako yaushe itama take ta qoqarin daina biyewa mahaifinta suna raba gari shahidan na kallo,sunfi kowa sanin cewa abun ba qaramin ciwo yake mata ba a rayuwa "Nawa ake bina ne kudin kai sadaka khadija?" Uncel hisham ya tambaya yana fiddo kudi daga aljihunsa,dariya ita abun ma ya bata,wanne irin binsa kudi?,mutum mai tsananin kirki da kyautatawa a garesu?,ko iya kai abincin ma da take ita ta sani Allah ne kadai yasan ladan da take samu "Ba kudin da nake binka uncle....nima ai ina samun ladar kaiwa" kai ya gyada "Na sani,wannan amma dole na baki haqqinki ne" "Banda abin shahida aiko kayan kwalliya kya saya ki dinga gogawa idan surukin namu zaizo ko?" Kunya ta kamata ta dan duqar da kanta qasa tana murmushi,mubina uwar surutu kuwa tayi caraf "Kullum sai yazo kuwa mamansu faruqu,yana da kirki kullum saiya kawo mana tsaraba,ko ya bamu goma goma yace mu siya" kunya tasa shahida kasa zama saita miqe zata gudu,yayin sa antu xubaida ta soma tsokanarta "Ah lallai,zanso naga wannan surukin namu,na tabbatar shima yana da kyau da nutsuwa kamar diyarmu..." "Rabu dasu shahida....dawo ki xauna muyi lissafi" uncle husham ya tare mata,haka ta dawo tana sunkui da kai ta zauna "Mu lissafa kwana nawa akayi ana kaiwa?" "Allah uncle ka barshi kawai" "Naqi din" ya fada yana soma irga kudin "Ki fada kona baki yadda naga dama"dariya ta danyi tana basar da maganar,kudi mai yawa ya irgo yace "toh gashi" "Uncle ka bawa umma ta ajemin" "A'ah a'ah,ba ruwan umma,wahalarkice karbi kiyi duk yadda kikeso dashi...iyakata in baki shawarar me zakiyi dashi" cewar umman tana miqews don zuwa kitchen ta hadowa su anty zubaida abinci,hannu biyu ta saka ta amsa tana masa godiya,a nan ta barsu anty zubaida harta gama shirin islamiyya suna zaune suna hirarsu,tayi musu sallama ta wuce. ************************ "Malam balarabe ina kayan anwar?" Shahida ta tambayi balarabe mai kanti lokacin da anwar din ke can yana hada kwanukanta don lokacin komawarta gida yayi "Gashinan ina aunawa...bari na hada miki harda kwakin"murmushi tayi sanda take amsar ledar kwakin daga hannunsa "Anwar...anwar kaina dabanne,ko me zakayi da garin kwaki kuma?" "Na'am?....ai aikin muhammadu kenan,ba yadda banyi dashi ya dinga sauyawa da wani abun ba,ya amshi bashi duk sanda Allah ya hore masa ya biyani amma sam sam ya qiya...gaskiyarki kuwa shi na dabanne,rayuwarsa ma haka,ni tsorona ma kar yayi masa illa yawan cinsa da yake,bashi da abinda ya wuce gari" sam batasan zancan zucin da take ya fito fili ba saida taji sharhin malam balarabe fadi ba'a tambayeka ba,saidai maganar tashi ta taba ta,ko a fuska bata taba ganin wani abu makamancin haka daga wajen anwar ba,hasalima bai taba karbar abincin da take kawowa wajen ba ko sau daya kuwa,a gabansa take rabarwa har ya qare iyakarsa ya dauka mata kayanta suje gida ya aje mata ya wuce,a sanyaye take bin ledar garin da kallo,tausayin anwar din ya kamata,ta yaya mutum zai rayu da cin gari kullum?,tsananin maraicin ne yasa haka?,amma indai da gaske ne sun zama abu daya mai yasa bai taba gaya mata ba?,ta yaya tana cin shinkafa kullum anwar yaci gari?,sosai taji haushin boye matan da yayi,wasu qwalla suka cika mata idanu,saita dauki ledar kawai ta juya ta fice daga kantin ba tare data ce komai ba. Sanda ta isa wajen har ya gama hada komai tsaf yana dube duben nemanta,fuskarshi yadan tsuke kadan "Ina kuma kika shiga?,banason ki dinga darawa ko ina daga nan fa,kinsan halin mutane da shegen kallo da sa ido" "Ba wani waje naje ba,na karbo maka saqonka ne daga wajen malam balarabe" "Balarabe kuma?"ya tambayeta yana nazartar fuskarta,fes ya fuskanci yanayinta ya sauya,ganin bata ce komai ba yasa shi daukan botikin ya soma yin gaba,ga tunaninshi zata biyoshi amma saiyaga bayansa take bi kamar yadda suka fara can watannin baya da suka shude sanda suke baqin juna. Cikin jinin jikinsa yaji sauyin yanayin shahidan bai masa ba,ko shakka babu akwai abinda ya faru shigarta shagon zuwa fitowarta,zuciyarsa yaji ta tsinke sanda ta qyasa masa wani tunani game da malam balarabe,baisan sanda yaja birki ba,ya waiwayo a sukwane,wanda saura qiris suyi karo da juna,baya ta danja kadan tana duban qwayar idanunshi da suka sauya launi,saiya sake matsowa gab da ita,kanta ta girgiza qirjinta na bugawa gana duban hagu da damarta,layin tsit yake babu kowa,yana daya daga ciki layukan da yake da qarancin zirga zirgar jama'a " me malam balarabe yayi miki?"ya tambayeta da wata iriyar rikitacciyar murya,tuni qwallar data cike da idanunta ta soma silalowa,rikicewa yayi jikinsa ya soma rawa,kafin ya sake furta komai ta bude ledar hannunta garin ciki ya bayyana,kallan garin yayi sannan ya kalleta,tashin hankalin daya sauko masa yaji ya soma yayewa,hankalinsa ya soma kwanciya ganin ba abinda zuciyarsa ta raya masa bane,ya saki wata wawuyar ajiyar zuciya wadda ta sanya duk wani qarfi na jikinsa raguwa,har sai daya jingina da bishiyar da suke tsaye qasanta yana sauke wata qatuwar ajiyar zuciya "Me yasa zakamin haka?,wannan abincine yanzu?" Sai yanzu ya sake fahimtar dalilin sauyawarta,kuka take sosai,saiya amshe ledar ya dora saman botikin daya aje gefansa "Wannan bai isa ya zama dalilin da zai saka min ke fidda wannan tsadaddun hawayen ba,wanda duk duniya babu kudin da zasu iya sayen darajarsu a wajena.....ungo nan share hawayenki" ya fada yana bata qaramin handkherchief dinsa wanda baya rabo dashi saboda share zufa da yake gwanin zufa ne,hannu ta saka tana goge fuskarta,tsahon minti biyar ya bata don ta nutsu sannan ya bata damar magana "Ohk...yanzu fadi duk abinda yake damuwarki" "Kafi kowa sanin ba haka mukayi alqawarin gina tarayyarmu ba,munyi alqawarin xamu ji dadi da wuya a tare,kukanka nawa ne,kukana naka ne,haka nan dariyarmu,don me zaka boyen wannan?" Murmushi mai kyau da qayatarwa ya subuce masa,kullum kwanan duniya yana jin ana qara masa sonta ne,duk sujjadar da zaiyi saiya roqi Allah yasa shahida mallakinsa ce daga duniya har lahira "A ganina wannan ba wani abu bane Allah ya taimakeki,na jima ina cinsa har kawo yau gashi ina raye ban mutu ba..." Saita mele baki cikin muryar kuka tace "Zancan mutuwa ma kake?....." Kasa qarasawa tayi ta sake sakin masa wani kukan,kanshi ya dafe sosai,ya tsani kukanta,idan yana ganin hawayenta ji yake kaman wani babban tashin hankali ya sameshi "Ya salam shahidaaah....,Allah ya baki haquri,kin manta cewa mu mutu ka raba ne?" Da tausasan kalamanshi dake sawa rayuwarta nutsuwa yayi amfani ya lallasheta sannan suka ci gaba da tafiya,bayan ta sa yayi mata alqawari bazai sake shan gari ba saidai da marmari. Sanda suka isa tsaidashi tayi ta shiga gida cikin sauri,bata zarce ko ina ba sai kitchen dinsu,tasan ba'a rasa abincin a gidan nasu,koda bamai yawa bane amma za'a dafa,foodflask dinta ta dauka ta cika masa shi da taliya da wake sannan ta fita. Yana tsaye harde da hannayensa a qirji,idan ka dubeshi da kyau ya zaka fahimci ya fada zurfin tunani ne,ledar hannunta ta miqa masa baqa wadda babu ta yadda za'ayi ya iya gane meye a ciki,saida dubeta ta masa alama da kai akan ya karba sannan yasa hannu ya amsa "Ka tafi dashi" "Meye wannan din?" "Guba na baka kaci nima naci saimu mutu tare" dariya ta bashi sosai har sai daya dara,itama sai data fada din maganar ta bata dariya "Kinsan kuwa zai zame min abun alfahari...kuma babban labarin da zai karade duniya...masoyiya ta baiwa masoyinta guba donsu mutu tare" murmushin daya qarawa fuskarta daraja da kyau ta saki "Zan iya cin guba don tunkudeka daga cinta" girarsa daya ya dage sannan ya sassauta murya "Idan babu ke ai babu ni shahida....kina tunanin idan kika mutu kika barni zan iya qara kwana daya a duniya" wani far tayi da ido wanda ya sanyashi yin baya da sauri "Inni sa'im...naga alama so kike ki....." Da hanzarinta ta juya masa baya cikin shagwaba tana dan buga qafa alamun batason ya qarasa maganar da yake "Shikenan.....sai anjima,na gode" ya fada yana takawa don barin wajen,tana wajen tsaye harya bacewa ganinta,saita lumshe ido ta saki hannayenta tana sakin siririn murmushi,tsakanin ita da anwar batasan waye yafi wani son dan uwanshi ba,wannan amsar kuwa tasan cewa Allah ne kadai masaninta. Cikin kudinta ta cire dubu uku ta siya qaramar waya sabuwa irinta anwar,ummanta bata hanata ba bare abbanta,sunsan cewa waya ba damun shahidan tayi ba,yanzun ma sun tabbatar saboda anwar ta siya,wanda dukkansu zuwa wannan lokacin anwar ya zama kamar d'a a wajensu,mutum ne da Allah yayi masa baiwar saurin shiha zukatan al'umma,hakan kuwa baya rasa nasaba da hankali nutsuwa uwa uba tarbiyya da yake da ita,ko cikin unguwarsu dattawan nan son anwar suke,kusan kowa zakaga yana janshi a jiki,shi kuwa ya daukesu dukkansu tamkar mahaifansa,dalili kenan daya sanya wasu daga cikin matasan unguwar kejin haushinsa suka kuma qwafa masa,hakanan suka daura dambar sake danqwafar dashi,hakanne yasa duk sanda ya samu wani abu sakakke sai an haura gidan an sace,kama daga sutura zuwa takalma ko d'an kudi,ya rasa su waye?,baisan kuma meya tsare musu ba,shi da bashi da komai?,bai baiwa kowa ajiya ba amma ya tsone musu ido. *ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER* 07067124863 *KO KUMA* 09032345899 *ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sabbabi,karku manta ky danna SUBSCRIBE,kuyi LIKE sannan kuyi SHARING🙏🏽* 👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽 https://www.youtube.com/channel/UC4kJO342hmb_Pd2luKHBjFA/videos*ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER* 07067124863 *KO KUMA* 09032345899 *ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sabbabi,karku manta ky danna SUBSCRIBE,kuyi LIKE sannan kuyi SHARING🙏🏽* 👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽 https://www.youtube.com/channel/UC4kJO342hmb_Pd2luKHBjFA/videos *Alqawarin Allah* 0️⃣9️⃣ Tun daga lokacin ta maida abincin anwar ya zama wajibinta,duk sanda ya nuna alamun turjiya na bazai amsa ba anan ne zasuyi fada,har hakanma ya zame masa jiki. Gefe daya kuwa rayuwarshi sai hamdala kawai,kusan duk wani fadi tashi ya zame ma rayuwarshi jiki,ta fannin kudin registration kuwa ba wani ci gaba da aka samu,iyakar qoqarinsa bai hada komai ba kaman yadda ya saba,yaqi kuma sanarwa anty husaina,tun yana jin babu komai harya soma shiga damuwa,ganin lokaci yana quracewa,sannu a hankali ya soma yanke tsammanin samun kudin ma gaba daya,wanda hakan ya jefashi cikin damuwa mai tsanani,damuwar da tasa anty husaina ta gane halin da ake ciki,ta kirashi tayi masa fada sosai,ta kuma saida dan abinda ke gareta na kudi,saidai kudin basu cika ba,kaso d'aya aka samu cikin biyu,a lokacin ya rage saura kwanaki makarantar su rufe registration. A hankali take takowa zuwa cikin soron nasu,niyyarta ta tsoratashi kaman yadda yayi mata shekaran jiya ya tsoratata,taji tsoro sosai ya koma gefe yana mata dariya yana fadin "Ashe farar kura ce ke bansani ba?". Yau da yazo kan dakalin qofar gidan nasu yaci burki,hakanan yake jin ranshi babu dadi,wanda hakan ya bayyana har gangar jiki da fuskarshi,saidai duk sanda ya tuna yanzu zaiga sanyin idaniyarsa sai yaji yanayin da yake ciki din ba komai bane,wayarshi dage aljihun wandonshi ta dauki qara,ya zura hannunshi a hankali ya zaro wayar,anty husaina ce ke kiranshi,yasan kuma kiran bai rasa nasaba da cikon kudin registration dinsa ba,zayaso kunnuwanta su jiye masa ya samu,saidai ba mai yiwuwa bane yayi mata qarya,abokin kuka shi ake gayawa mutuwa,sannan uwa uba bayaso wani abu ya kawowa karatunshi tsaiko,babban burinsa a yanzu shine ya kammala karatunsa ya samu aiki,ya auri shahidansa ya kuma kula da anty husaina,itama ta huta taji dadinsa "Yaya dai muhammadu an samu cikon kuwa?" Ta tambayeshi bayan ya gama gaidata,cikin nuna kasawa da sarewa yace "Anty ina ganin saidai nayi haquri....wannan karon duk wani qoqarina na samun cikon kudin na gaza,kudin sunqi samuwa....ina tsoron asarar karatuna..." Tausayinsa ya kama anty husaina,tasan abune mai wuya ganin karayar anwar "Kaci gaba da addu'a,ina nan ina nawa qoqarin mu zubawa sarautar Allah ido,in sha Allahu yana tare da mu" "A'ah anty.....karki takurawa kanki karki damu,nima zanci gaba da nawa qoqarin...". A hankali ta koma da baya cikin tsananin mutuwar jiki,ba labe tayi musu ba amma ta kasa tafiya sanda yake wayar da anty husaina,cikin mutuwar jiki da karaya take juyawa zuwa cikin gidan,qirjinta ya quntata qwalla ta cika mata idanunta,dama akwai wani abu da anwar zai iya boye mata game dashi?,da wannan tunanin ta isa dakinta,gefan katifarta ta samu ta zauna tallafe da kumatunta,batasan adadin lokacin data dauka a haka ba har ya tarawa wayarta miscal bata gani ba,saida ummanta ta daga labulen dakin "Wanne shashanci ne kike haka shahida?,kinsan ba zaki samu fita ba kikabar anwar qofar gida yana jiranki?" Hannayenta ta sauke tana cewa "Yanzu zan fita umma" sakin labulen tayi ta juya ta fice tana mita "To ke kuma ya isa haka malamar mita,tunda ta baki uzuri basai kija bakinki ki shuru ba?" Ta jiyo abbanta yana fada "Kaga kar kace zakamin fada,don na mata magana laifi nayi?" "Ba laifi bane,mitar ne ni banason ji karki cikamana kunne" "Wai yau cin mutuncin naka ne ya motsa baban shahida?" Ta saki abinda take ta zuba masa idanu tana tambayarsa,saiyayi banza da ita ya zubda ruwan daya kurkure bakinsa ya dauki hularsa ya fice,ajiyar zuciya shahida dake tsaye bakin window ta saki,ta godewa Alla daya taqaita cecekucen nasu baiyi tsaho ba har yaja hankalin anwar ko yajisu. Katifarta taje ta daga,kudaden da uncle hisham ya bata ta dauko,ta zauna ta qirgasu a nutse sannan ta shiryasu,koda batasan nawa anwar ke buqata ba tasan cikon kudin bazaikai yawan kudaden dake hannunta ba,don kudaden da uncle anwar din ya bata suna da yawa,don taji ma anty amina na cewa mama su aje a karba a siyawa shahidan tukunya mai sha biyu a aje mata,lanqwashesu tayi sannan ta miqe ta gyara mayafinta ta fice. Sanda ta koma yana zaune kan dakalin,ya zubawa qasa idanu wanda hasken farin wata ya haske jikinsa yake bashi hoton inuwarsa,a hankali ya dago kai idanunsu suka hadu da juna,wani sanyi yaji har cikin rai da zuciyarsa,saiya sakar mata murmushi yana jin kaso tamanin na quncin da zuciyarsa ke ciki ya tafi,kallon farko ana biyu ya karanci lallai akwai abinda yake damunta,duk sai yaji wani iri,yaji babu dadi,duk wata walwala da karsashinsa ya shiga yin nashi guri,shi ya amshi daddumar hannunta ya shimfida ya kuma yi mata nuni data zauna,batayi musu ba ta zauna din,yana tsaye qyam a kanta yana qare mata kallo,ya samu kanshi da kasa zama "Mene ne yayi kutse cikin farincikin gimbiyata?" "Kaine...." Ta fada kanta tsaye,cikin sanyin jiki ya samu dan wani dutse dake daura da ita ya zauna samanshi "Bana fatan kasancewar wannan ranar....wane kuskure na tafka haka harya zama tarnaqi wa farincikin zuciyata?" Hawaye ta soma zubarwa,bana komai bane saina tausayinsa,zurfin cikinsa yayi yawa,kara da kawaicinsa sun baci,amma ko daya bata son ya sake boye mata wani abu daya danganceshi,tana ganin kaman hakan wani naqasu ne tattare da dangantakarsu,zai zama tamkar bai bata muhimmancin da take tsammanin ya bata ba "Ashe dukan inda nake tunanin nakai bankai can ba a zuciyarka?" "Ya salam" ya furta fuskarshi na nuna tsantsar tashin hankalin daya shiga,wanda har cikin zuciyarshi haka ne,wanda har yanajin ya zarce na rashin kudin registration da bai samu ba "Shah......" "Kar ka sake cemin komai....na kamaka da laifuka guda biyu kawo yanzu,ban taba boye maka komai daya danganceni ba....amma kai ka boyemin abubuwa har biyu,ban sani ba ko.matsayina baikai nasan wannan fannin ba...." Sanyi ya dinga ji yana ratsa qasan zuciyarshi,duk da bai fuskanci me yayi mata ba,dubanta yake cike da qaina soyayya sa shauqi mai yawa,ta damu da lamuransa fiye da tunanin mai tunani kamar yadda ya damu da nata,bai tsammaci zata soshi kamar yadda yakesonta ba,ya zaci zata soshi ne irin son da baikai ya kawo ba,kodon kyau da Allah ya bata,kodon gata data d'arashi,ko don saboda farinjini da Allah yayi mata "Yanzu karatunka ba nawa bane?" Ta fada maganar quruciyarta na fitowa fili,hakanan ta b'ata rai sosai ta kuma tsareshi da ido,murmushi ya saki wanda ya bayyana fararen haqoranshi "Nakine my shahida" "Don me baka gayamin halin da kake ciki ba?" Dan shuru yayi yana tauna amsar da zai bata,tsahon minti guda kafin yace "Shahida....kin wuce duk inda kike zato kike tsammani a wajena,tunda Allah ya busan numfashi ban taba qaunar wata d'iya mace ba saike,nine namiji,ni nake nema,kuma nine sama dake,bai cancanci ace dukkan wata wahalata tana wuyanki ba" "Koda bani da abun da zan taimaka dashi ai na sanyaka cikin addu'o'ina ko?" Idanunsa ya lumshe idanunsa yayi yana sakin murmushi "Ni na sani shahidana koda banda damuwa ba zata daina sakani a addu'arta ba" "Ta yaya zan aminta cewar mun zama daya kana boyemin ire iren wadan nan abubuwan?" "Shahidaa...karki sake tunanin bamu zama daya ba,kin zama muhammad anwar,na zama rahamatulshahida" sunan ya bata dariya har sai data murmusa,tafin hannunta ta bude sannan ta miqa masa kudin hannunta "Ungo qirgamin" amsa yayi yana zolayarta,sannan ya soma qirgawa yana cewa "Shahidana ta zama hajjaju" sai daya gama qirgawa sannan ya dago ya dubeta yana gaya mata nawa ne,kai ta gyada duk da tasan nawa ne dama "Kayi amfani dasu" sak ya tsaya yana dubanta kafin yace "Shahida...." Idanunta ta ware masa tana dubansa itama,ya gane me take nufiSai ya saki murmushi "Aro na baka,amma kayi duk amfanin da kakeson yi dasu" "Kai amma wannan yarinya kin iya bada rance....to na gode Allah ya bani ikon biya" daga haka sukaci gaba da hirarsu,saidai rabin hankalinsa dukka yana kan halayen shahidan,yana sake godewa Allah tabbas baiyi zaben tumun dare ba,hakanan ya tabbatar bai miqa zuciyarshi inda bai cancanta ba. Wannan abu da shahidan ta yiwa anwar ba qaramin qara mata qima yayi a idanun anty husaina ba,wata qauna take mata tamkar diyar cikinta tun kafin ma ta yiwa anwar hakan,ta yadda ta kuma yi amanna cewa anwar yayi dace da matar aure,ta kuma shiga sahun masu masa addu'ar Allah yasa shahidan ta zama mallakinsa. Ta gefan anwar dinma tuni ya shiga bakunan 'yan uwan shahidan musamman 'yan gidansu da anty amina wadda sukafi dasawa da shahida duk cikin 'yan uwan mamanta,kasancewar tasu tafi zuwa daya da mamanta,kuma ita daya ke gaya mata magana itama maman da ita take shawara. Cikin ikon Allah anwar yayi registration dinsa,komai yaci gaba da tafiya dai dai,rayuwarsu da shahida kuwa ta zama abar kwatance ga duk wanda ya sansu,kowa najin jinin danuwansa na yawo a nasa jikin,tun mutane na mamakin yadda sukeson juna har abun ma ya zame musu jiki,su kansu yadda suke nunawa kansu qauna basusan sunayi har haka ba saidai a gaya musu. Sannu a hankali rayuwa taci gaba da juyawa,ta wanni fannin ana samun ci gaba yayin da wani bangaren yake zamowa koma baya da babban naqasu wajen bawa. Zuwa sannan shahida sun shiga ss 3 term din farko,a sannan ne Allah ya yiwa mahaifin zunnurah rasuwa,hakan ya zama silar barinsu garin kano sukayi qaura suka koma katsina cikin danginsu,dalilin kenan daya sanya kusancin shahida da firdausi ya sake samun tagomashi mai yawa,ta maye mata gurbin zunnurah,yayin da ita da zunnurah ya zama sai a waya,lokaci lokaci idan sukayi waya tana sako mata zancan fiddausin tare da sake ja mata kunne kan tayi hankali da ita,murmushi shahida keyi yawancin lokaci,ta sake yarda Allah ne kadai.ya isa ya hada zukatan bayinsa,har yau bata tana ganin wani abu mai kama da abinda zunnurah ke tuhumar fiddausi dangane da ita ba. Anwar ya samu ya kammala karatunsa cikin wahala da dagiya da kuma taimakom anty husaina wadda ta sadaukar da dukkan wani abu nata don ci gabanshi,yayin da shahida ta zamo mutum na biyu data sadaukar da dukkan wani abu da take ganin ta mallaka saboda anwar din. Bayan fitowar sakamakonsa wani yayan abokinsa ya kirasu yayi musu tallar aikin d'an sanda da za'a soma dauka,rimi rimi sukayi komai da karime karime da qarfafawar gwiwar shahida data dage kan sai yaje,sai kuma batun tafiya training ya taso,a nan ne ya sare saboda lissafen lissafen abubuwan da za'a buqata daga garesu,wanda kusan duka harka ce ta kudi,koda wasa bazai doshi anty husaina da wannan batun ba saboda yasan cewa wahala ce da nauyi kawai zai dora mata,saiya shiga neman kudi babu ji babu gani,sai lokacin da tafiyar ta matso sannan ya shaidawa anty usaina,ta masa addu'a sosai,ranar da zaiyi sallama da shahida ta dauko baqar ledar viva ta dire masa. Sai daya gama kalla sannan ya dago yana dubanta,baisan ma da wanne baki zai mata magana ba,da wanne harshe zai gaya mata yadda take a wajensa?,kaya ne da tasan cewa zai iya buqata a ciki,wanda ko bata fada ba yasan a qalla zata kashe dubu biyar,Da hannu ta masa nuni dole yayi shuru,tamkar ba zasu rabu ba ranar,ji yake kaman idan yaje zaiyi shekara ne bai dawo ba. Kwanansa uku acan shida wasu mutum biyar suna cin wuya saboda ance sam babu sunansu cikin list din,bawai kuma babu dinba,yanayin qasarmu ne kawai,an suba wadanda sukafi kowa rashin galihu an cire sunayensu daga list din an maida gurbinsu dana wasu,hakanan suka tattara suka dawo gida. Randa shahida ta ganshi ya dawo ba qaramin jin takaici tayi ba,har kuka ta kusa yi,shi ya dinga lallabata yana bata haquri "Duk randa Allah ya horemin abu na farko da zan fara ginawa shahida shine makaranta,zanyi irin makarantar da yaran masu kudi suke zuwa,irin makarantar da suke karatuna zuba yaran masu qaramin qarfi,su samu irin ilimin da yaran masu hannu da shuni suke samu,su samu gata da kulawa irin na yaran masu dashi"shuru shahida tayi tana karantarsa,har cikin zuciyarsa maganar take fitowa saboda yadda hakan ya bayyana saman fuskarsa "Yaran marasa shi suna shan wahala,suna shan wahala matuqa wajen neman ilimi,bayan sun samu karatun da qyar ya zamana karatun ya kusa zama na banza,sakamakon yadda aiki ke musu wahala,wanda wasunsu daga qarshe sakamakon karatun nasu kusan dai dai yake da takardar tsire" nan ma dan shuru yayi yana hadiyar yawu,sosai lamarin ke sukar zuciyarshi,sun jima suna tattaunawa game da halin rayuwa sannan daga bisani sukayi sallama. Anwar bai gajiya ba bai kuma sare ba yaci gaba da neman aiki baji ba gani,burikansa din nan guda biyu su yake fafutukar ganin ya cimmawa,yana tsoron shahida ta kammala secondry ba tare daya samu aiki ba,babban burinsa a duniya suyi aure sanda zata kammala makaranta,ya kuma tsaya mata tayi karatu kaman yadda takeso harsai tace ya isheta,yana da burin yi mata halacci kwatankwaci koma fiye da yadda tayi masa. *BAYAN WATA HUDU* Kallonshi take tamkar ta zabga masa mari haka takeji,saidai hakan ba maiyuwuwa bane tunda ba tarbiyyarta bace,dawowarta kenan daga gidan anty amina ya tsaidata,sam batasan yana biye da ita tun daga qofar gidan anty amina ba cikin motarsa saida ta iso layin nasu,ta shiga gida da niyyar ba zata saurareshi ba yadda yaketa zabga aike yasa umma tace ta fita ta saurareshi. Hakanan cikin jikinta takeji kamar akwai wanda yake kallonta,kamar anwar na wajen tare dasu,a hankali ta kalli damanta,shine kuwa sanye cikin jibgegiyar rigar sanyi da wandon jeans,kasancewar ana cikin yanayin sanyi,yayi kyau matuqa,kai kace wani ne ko dan gidan wani,kyansa ya sake fitowa,fitilun motar daya bari a kunne sun haskeshi sosai kaman yadda suka haskesu,idanunta cikin nashi saiya ja da baya ya juya ya soma barin wajen. Wani tashin hankali ya ziyarceta,da wanne baki zata yi masa bayani?,ganin yadda hankalinta ya wajen ya sanya saurayin shima juyawa yana kallon wajen saidai baiga komai ba,bata sake bi ta kanshi ba ta shige gida da hanzari,wayarta ta laluba ta soma kiran layin anwar din,saidai harta qaraci ringing dinta ta gama bai daga ba,hakan ba qaramin daga mata hankali yayi ba,ba zata manta ba shekaran jiya suna hira yake ce mata "Shahida tsoro nakeji,gani nake kaman zan rasaki,kaman kinfi qarfina" cikin mamaki tace "Me kake fada anwar?" Murmushi yayi saidai ya taba har zuciyarsa "Shahida...kina kallon kanki a mudubi kuwa?,irinki ba qananun mutane ke aurenki ba....ina tsoron kada wani mai motar yasha gaba na" sosai taji haushi harma ta shige gida ta barshi ko sallama basuyi ba,da qyar yasha kanta ya waya,to jiya bai samu zuwa ba kasancewar ya samu dan wani aiki yana kulawa wani da provision dinsa cikin anguwarsu,ladan da yake bashi ba wani mai yawa bane kasancewar kanti ba wani girma gareshi ba,amma ya karba yana yi saboda ba mutum ne shi mai raina sana'a ba komai qanqantarta. Kusan ranar kwana tayi tana kiran layin nashi amma ko sau daya bai daga ba,daga nashi bangaren hankalinsa a tashe yake,hakanan zuciyarsa ke wani irin tafasa,kishi ne ki cinsa sosai,fargaba ta lullubeshi,fargabar kada ace zancansa ne zai tabbata zai rasa shahidansa,duk sanda ta kirashin bai daga ba sai yaji wani qunci na sake ziyartar zuciyarsa,bai iya daurewa yana jin kiranta na shigowa amma ya kasa dagawa,daga bisani tilas ya kashe wayar duka yana fatar ta haqura tayi bacci. Kwana biyu ba anwar din ba dalilinsa,hakan ya daga hankalinta don har wajen kai sadaka bata ganinsa,da yammacin kwana na ukun bayan ta dawo daga kai abinci wanda yanzu ajewa kawai take wajen baba ado dake wajen ya raba a aiko da botikin don fir anwar yace ta daina kaiwa,shiryawa tayi ta tadda ummanta zaune tana jan carbi bayan ta idar sallar la'asar "Umma....zanje gidan anty amina"kai ta daga ta dubeta sannan ta shafa addu'arta "gidan amina kuma?,makarantar fa?"kanta tadan sunkuyar tana wasa da farcenta "hadda ake karba,kuma ni na bada tawa tun jiya" dan jim tayi sannan tace "Shikenan,ki gaisheta....yauwa....kice mata yaushe za'a fitar da ankon umaiman,ki gaya mata lokaci yana qurewa fa" "Tohm umma....saina dawo" "Zan rakaki yayaa" cewar mubina wada ke shirin islamiyya ta fada bayan ta watsar da hijabinta wajen "Babu inda zaki,makaranta zakije" cewar ummanta,tana jiyo ihunta ta saka kai zata fice tana dariyar rikici irin na mubinan,dai dai lokacin abbanta ya shigo,saita koma da baya tana masa sannu da zuwa yayin da yake tambayar abinda aka yiwa mubinan "Wai gidan anty amina tace zata bini,kuma islamiyya zata" "Ke ina taki islamiyyar?" "Hadda ake amsa abba kuma na bada tawa tuni..." "To ma sha Allahu,dama inason ganinki" "To abba gani" ta dawo tana dawowa saman kujera 'yar tsuguno ta zauna, "Shahida....ina fatan ba wani abune ya shiga tsakaninki da yaron nan ba anwar?" "Abba meka gani?" Ta tambaya a sanyaye "Kwana biyu bana ganinsa yana zuwa" shuru tayi tana tunanin amsar da zata bashi,dukkaninsu ummanta da abbanta wani irinso sukewa anwar din,halayen anwar abun sone,nagarta gareshi wadda ta zama tilas ko waye kai ya burgeka "Uhmmm...bakice komai ba" "Abba in gaya maka?" Mubina dake goge hawayenta ta fada,harararta shahida tayi amma hakan baisa ta fasa magana ba "Wanine mai mota yazo...umma tace taje ta sallameshi,shine yaya anwar ya ganshi ya tafi" "Ubanki mai shegiyar magana" umman ta fada tana kai mata duka "A'ah hadiza barta ta fada....kice kawai kin soma shanshano wani ne....ke shahida tashi ki tafi,kema zamu gamu dake" "Duk abinda kaga dama ka fada,tunda dai ba zuciyata ka shiga ka hangi haka ba shikenan na gode Allah" tun kan ta fice daga soron nasu ranta ya soma baci,saboda taji suna gab da kaurewa da halayyar tasu da suka saba,saitayi maza maza ta ficema don kada ta jiyo abinda wunin yau zai sa ta kasa walwala,sam bata iya daurewa duk sanda wani sabani ya hasu tafi kowa jin zafin abun,tqfi kowa shiga qunci,ta rasa me yasa dukkansu basu haquri da juna,kowa kaman jiran kowa yake,kamar wadanda aka sakawa hannu cikin mu'amalarsu. Ba dadewa ta isa gidan anty amina,ta taddata tana wanki ta saka mata hannu suka gama tare,tanata tambayarta anwar kwana biyu bai leqo ba batace komai ba,har sai da suka gama suka zauna dakinta suna ninke wasu kayan da suka soma bushewa "Anty....nifa zuwa nayi ki mana sasanci da anwar" "Sasanci kuma,me ya hadaku kenan?,yau kwana uku kuwa da zuwanshi ya gaidani"ana ya gobe abun zai faru kenan?,shahida ta raya a ranta,batasan ma yazo din ba,jininsu ya hadu da anty amina,gashi kuma ba wani nisa sosai tsakanin gidanta dana anty usaina,don har zumunci ma suke yanzu ta sanadinsu,tsaf ta kwashe komai ta gayawa anty aminan,a take tasa shahidan ta kirashi,saidai harta gama ringing bai daga ba "kin gani ko anty?"shahidan ta fada idanunta na cikowa da qwalla "Bari na kirashi da wayata" anty amina ta fada tana daukan wayarta,ringin biyu ya daga cikin girmamawa "Anty amina...da kanki?" Ya fara fada cikin girmamawa "To ya zanyi?,diyata ta dagamin hankali?"dariya ya danyi "Shahida ko?" "Ita mana" "Karki qona katinki anty bari nazo" "Da kuwa ka taimakeni karta fashemin gata nan ta cika fam" da haka sukayi sallama tana duban shahidan "Shima a muryarshi kadai ya isa kasan cewa yana cikin damuwa da kewarki,wanne irin so kukewa juna shahida?" Kunyace ta kamata saita soma sinne kai. Ba'ayi minti talatin ba cikakke d'aya daga cikin yaran anty amina suka shigo suna cewa ga uncle da yake haka suke kiranshi,anty amina ta saka hijabinta tace suce mishi ya shigo.https://www.youtube.com/channel/UC4kJO342hmb_Pd2luKHBjFA/videos *ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER* 07067124863 *KO KUMA* 09032345899 *ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sabbabi,karku manta ky danna SUBSCRIBE,kuyi LIKE sannan kuyi SHARING🙏🏽* 👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽 https://www.youtube.com/channel/UC4kJO342hmb_Pd2luKHBjFA/videos *Alqawarin Allah* 1️⃣0️⃣ A nutse cikin sallama ya shigo ta daga kai a hankali ta kalleshi saboda ita kadai tasan yadda tayi missing dinshi,shi dinma idanunshi na bisa kanta ji yake kamar ya shekara dari bai ganta ba,amma duk da haka saiya gintse saboda tuno ganinta da yayi da wani,daya daga kujerun falon ya samu ya zauna suka gaisa da anty amina sannan ta soma tambayarsa "Wai me ya hadaka da shahida?,duk ka firgitamin diya?" "Ta firgitani dai anty...bakiga har rama nayi ba?" Murmushi anty aminan ta saki,yadda sukeson junan nasu na bata sha'awa,bai boye komai ba ya gaya mata sannan ya dora da cewa "Wallahi anty wani irin kishine dani,ina da matuqar kishi kan abinda nakeso,ranar dana ganta wallahi anty ban iya bacci ba" "To kayi haquri mr kishi....bari kaji me ya faru" ta shaida masa kamar yadda shahidan ta gaya mata,nannauyar ajiyar zuciya ya saki yana jin kaman an sauke masa qaton dutse daga zuciyarsa,sai a sannan ya sami salama "A rude nake anty,shahida ba ruwanmu bace mu talakawa,hankalina a tashe yake kada wani ya qwace min ita"dariya ya baiwa anty amina sosai har sai data dara "karka damu anwar,shahida taka ce in sha Allah,yo shahida muka bata wani bakaiba ai inajin fiya fiya zata sha ta mutum" sosai anty amina ta baiwa shahidan kunya,har sai data diba a guje ta shige dakin anty aminan,shima ya miqe ya fice yana dariya. A dakin ta taddata ta dubeta "To laila majnun,saikije ku sameshi tunda na kashe case din,saiki kula a gaba" "Na gode anty amina ta" "Eh kyace haka mana tunda na dawo miki da hasken rayuwarki ko?" Dariya ta tuntsire dashi sannan ta miqe ta zura hijabinta ta fice. Yana tsaye a soron gidan amma qofar fita yake kallo,tadan tsaya kadan a bayanshi,a jikinsa yaji tana wajen saiya juyo a hankali idanunsa zube fes a kanta,takowa yayi har sai daya rage tazarar dake tsakaninsu sannan ya tsaya,a hankali cikin wata murya dake cike da mayen so yace "Nayi kewar wannan kyakkyawar fuskar,wannan ruhin ya hana ruhina samun barci bare ya samu salama,na cika da fargabar cewa na rasa hasken idaniyata,ashe abun duka ba haka bane" sosai kalamanshi suka sanyaya mata rai cikin daqiqu kadan,tayi qas da kanta tana fidda murmushi "A'ah dago kanki sosai don na samu qwarin gwiwar fada miki albishir din danaso yi miki tun rannan mai mota ya korani" "Don Allah ka daina zancan mai motar nan honey haba" "Na daina" ya fada yana murmushi "Na samu aikin kamfani Allah ya taimakeki...wani maqocinmu ne ya sama min,kwana goma sha biyar zan dinga aikin kwana,kwana goma sha biyar aikin wuni,zasu dinga biyana albashi duk wata dubu sha biyar" sosai fuskarta ta washe da fara'a tana jin farinciki na ratsata,tana jin burinsu ya soma daukar hanyar cika,rasa inda tsoma ranta zatayi har sai daya tsaya yana kallonta cikin mamaki,sun jima a soron gidan anty aminan kafin ya sanyata ta tattaro kayanta tazo su wuce gida,napep ya tsaida musu har qofar gida,sanda suka sauka ta zaro kudi zata biya ya harareta ya ciro daga aljihunsa ya biya,dariya kawai tayi,ko yaya idan yana da kudi ko iyakarsu kenan jikinsa baya yarda tayi masa hidima da kudinta,nan ma sun dan jima kafin suyi sallama ta wuce gida shima ya wuce. Cikin taimakon Allah ya soma zuwa aikinsa,saidai babban qalubalen daya soma fuskanta shine na rashin kudin mota,tafiya ce mai nisa tsakanin unguwarsu zuwa kamfanin haka yake niqar gari ya tafi,duk da cewa ya saba tun sanda yana makaranta amma tafiyar bata kai ta makaranta nisa ba,sai kuma abincin da zaici shima saiya dawo zai jiqa kwakinsa yasha musamman idan aikin dare yayi zai dawo da safe,duka wannan bai dameshi ba tunda yasan cewa komao lokacine,hakanan bai yarda shahida ko anty usaina sun sani ba saboda baiga dalilin da yana namiji zai dinga daura nauyi wa mata ba,a haka ya cinye watanshi guda,saidai kafin cikar watan ya fada yayi baqi,hakan ya sanya shahida ta sanya ayar tambaya a kanshi. Ranar daya amso albashinsa yazo da daddare,duka ya zube mata albashin nasa yana dubanta "Me zanyi dashi honey?" Ta fada bayan ta gama saka musu albarka "Inason ki dauki iya abinda ranki yayi miki,a matsayin albashin mijinki na farko" kai ta girgiza tasan ko tace masa a'ah cewa zaiyi bata isa ba saiya dauka,saboda haka tasan maganinsa. Da fari ta ware wasu kudaden tace wannan kudin kayan abinci da zai siyo ya dinga dafawa yana tafiya dashi kamfani,ta sake ware wasu tace ya sake dinka kaya kala guda duk wata zai dinka kala daya,ta sake ware wasu tace ya riqe ya kashewa ne,sannan ta cire wani abu a ciki tace wannan ya kaiwa anty usaina ita yafi cancanta ta sanya albarka,next month kuma idan ya sake amsa to ya fara ajiya saboda lalurorin yau da kullum,duk sai data gama kasafin ya cakude kudaden waje daya sannan yace "Qurun qus kin gama tatsuniyar taki?,toni ba haka nakeso ayi ba,da safe me mike ci idan zaki makaranta?"baki tadan cuno "Kome meye ya samu" "Good" ya fada yana cire wasu kudi ya aje "Indomie da qwai nakeson ki koma ci" idanu ta zaro tana kallonshi baki bude "Honey...me kake fada ne?" "Abunda kunnuwanki suka jiyr miki.....wannan kuma kudin kashewarki na wata gud....." "Kaga...don Allah ka tsaya ka daina wannan lissafin mana" nan sa'insa ta kaure tsakaninsu,da qyar ya yadda da nata lissafin bayan ta masa alqawarin wata na gaba ta yadda za'a sata cikin kasafin,saidai duk da haka yayi cancel kudin kashewarsa ya bata dole ta amsa saboda ya kafa mata sharadi. Koda ya kaiwa anty usaina ma itama cewa tayi ba zata soma amsa yanzu ba,ya aje wajensa zata masa magana idan lokacin daya dace yayi,haka ya dawo dasu ya miqawa shahida "Shikenan...zan saya banki na dinga tara maka,duk sanda kake da buqata saika amsa" washegari kuwa ta sayi bankin ta zuba masa harda kudin daya bata,ta nuna masa sannan ta roqeshi "Don qaunar da kakemin kada kace a'ah,za'a tara ne ka siya abun hawa ko keke ne,ko baka fadimin ba nasan tafiyar qafa kake" da qyar ya amince da shawararta,donshi a son ranta tayi hidimar gabanta kawai dasu. Wata hudu cif da fara aikinsa komai ya soma tafiya babu laifi,ta wanni fannin abubuwa da dama sun soma sauqi,cikin godiyar Allah da yadda da cewa komai lokaci ne. Cikin haka aka fitar da ankon bikin umaima,wadda take cousin ce a wajenta,ranar data kawo musu ankon wuni tayi a gidansu,har dare tana nan,sanda ta tashi tafiya anwar yazo shahidan na wajensa,mubina ce ta rakota tana nanata mata idan ta tashi dawowa ta kawo mata alawarta,qarasawa tayi wajensu shahidan tana mata sallama daga bisani tace "Ina zuba ido saikinzo siyan ankon,kuma wlh baki isa ba ba wani daya da zaki duka biyun zakiyi" "To ummata" ta fada tana hararta,don batason ta tada zancan a gaban anwar din,sun riga da sun gama maganar su tun cikin gida,da haka sukayi sallama umaima ta wuce. "Wai ina bankin nan kuwa?" "Yana cikin gida" "Idan yana kusa daukomin shi idan yana kusa" bata ce komai ba ta shige gidan ta fito dashi,bankin qasa ne ya amsa saiya sakeshi ya fadi take ya fashe kudin ciki ya bayyana,baki ta bude tana zaton itace bata bashi dai dai ba ya riqe ya fadi haka,sai taji yace "Yauwa yayi dai dai,tayani qirgawa" cikin mamaki ta duqa ta soma tayashi hada kudin,bayan sun gama hadawa ya miqa mata yace ta irga,cikin murna da mamaki tace "Da gaske ne kudi wawayene....ban zaci zasu kai haka ba wallahi" murmushi shima ya saki,walwalar da take kawai ta isheshi farinciki "Kije ki sayi ankon ko kala nawa ne,saura kiyi dinki,idan ba zasu isa ba kiyimin magana" ranta ta ba'ta sannan tace "Me kake fada ne?,kudin keken naka zaka bani kace nayi anko bayan sunkai kudin keke sabo harda canji?,kuma ma tuni umma tace zatamin daya abba guda daya" "Duk bansan wannan ba....abinda kawai na sani shahidana zata saka kaya kamar yadda kowacce mace zata saka...kada kice zakimin musu indai baso kike raina ya baci" kaita duqar "Allah ya baka haquri" dole ta fidda kudin ta sayi ankon kala biyu mayafi da abun daurawa,cikin sati uku suka shiga hidimar biki amma hakan bai hanata ganin anwar ba,shima hakan ya masa dama tunaninsa rashin ganinta. Ranar da za'ayi dinner tun safe suna gidan kwalliya,qarfe biyar da rabi na yammaci ya kirata yazo ganinta tana ina,itama yana ranta don jiya basu samu ganin juna ba basa unguwar kwata kwata suna can aikin snacks,ta kwatanta masa gidan kwalliyar,ya gane gidan saboda cikin anguwarsu ne. Sanda ya iso tuni an gama mata tata,zata wuce kuma gidan bikin ta saka kayanta kafin a soma dibansu zuwa wajen da za'a gudanar da shagalin. Dan kwalinta a hannu ta fito soron gidan don kada ya bata mata kwalliyarta,dubansa tayi yadda yayi mata kyau cikin wani sabon yadi blue black,wanda aka yiwa dinki irin na matasan zamani,bata mancewa da ita yayi shawara kafin ya sayi yadin ta kuma zabar masa dinkin qarshen wata sanda aka biya salary ya cira a ciki yayi,anwar nada wata baiwa ta daban,idan yayi dressing kai kace shi din wani ne,daga kai yayi daga danna wayarsa da yake yana dubanta,subhanallah ya fada a sarari,wani azababben kyau yaga ta qara masa,kai kace ba shahidarsa bace,sai yayi sak yana ci gaba da dubanta,abun ba qaramin dariya ya baiwa shahida ba har sai data d'an dara "Yaya anwar wucewa zanyi fa ana jirana.....tun daxun kake kallona sannan kuma kai baka ce komai ba" ta fada a shagwabe tana langabe wuya,ajiyar zuciya ya sauke sannan ya dubeta "Ba inda zan barki ki fita a haka shahida....gaskiya zuciyata ba zata iya jurewa wasu su kalleki a haka ba a filin Allah wajen bikin dake cakude da maza da mata" "To a yaya kakeso na fita?" Ta fada tana cuno baki wanda hakan ya sake tafiya da imaninsa,dan qaramin bakinta mai dauke da pink din labba yasha maroon din jambaki "Mafita kawai ki wanke fuskarki" idanu ta zaro tana dubanshi "Haba yaa anwar....haba don Allah" ta fada kaman zatayi kuka tana dan buga qafarta,fuskarsa ya hade sosai,harga Allah yana da wani irin kishi akan shahidan,yana jin kaman zai mutu idan wani ya zuba mata idanu bare akai ga batun furta yana sonta "Ashe kuwa zaki shekara a soron nan,don na rantse ba zaki matsa ko inaba indai fuskarki da wannan kwalliyar" tasan cewa da gaske yake saita rasa ya zata masa,hakan yasa ta juya ciki ta yiwa amarya umaima magana,ita tazo ta roqa mata alfarma wanda daga qarshe yace saidai ta cire eye lashes din da aka qara mata don nata ma ya isheta,sannan kuma a goge wasu abubuwan da aka sa mata a fuska,saida akayi hakan sannan ya qyaleta,duk da haka a gaba ya sakata tana gaba yana bayanta,sai faman sakin ajiyar zuciya yake,duk da an rage kwalliyar gani yake kowa ma kallonta yake,adaidaita ya tare mata bai barta ba sai daya rakata har qofar gidan bikin,yana mata sallama zai juya itama ta tubure kan dole yaje wajen bikin,yasan da biyu tayi hakan don bai fiya zuwa wajen fate fate ba,to amma abinda bata sani ba gata tayi masa,don har yanzu hankalinsa bai aminta ba da zuwanta wajen ita kadai,gani yake tafi kowacce mace kyau,hakanan idanun kowanne namiji yana akanta "Zanje na dawo,idan kun gama shiryawa kimin magana" tana masa dariyar cin galaba ta shige ciki. Qarfe shida aka soma daukan 'yammatan,a sannan tuni ta yiwa anwar waya,shida da rabi ya kirata yace ta fito yazo,su biyu ne ita da 'yar anty umma yayar ummanta,ga mamakinta yana jingine jikin wata qaramar mota mai kyau qirar kia,ya sauya shigar jikinsa,wannan dinma yadine wanda tare ya siyesu da wancan,saidai wannan ruwan madara ne lallausa,shima bamai tsada bane amma sai taga kaf mazan wajen ba wanda ya kamoshi a kyau duk dacewa jayan jikinsu yafi nashi tsada nesa ba kusa ba. Shi dinma gaba daya saiya daina ganin 'yammatan dake kai kawo a wajen,ita kadai take gani cikin dinkin ankon da ya amshi fatarta fiye da zato,kowa idonsa cikin na dan uwanshi a haka ta qaraso,baice mata komai na sai gaban motar daya bude mata ta shige,shima ya bude sit din driver ya zauna bayan kubra 'yar anty umma ta shiga gidan baya ya tada motar. Saitake jinsu yau kaman rana ta musamman ce a wajensu,wani farinciki taji yana ratsata,ta samu kanta da addu'ar Allah ya shiga lamarinsu ya buda ma anwar din,motar tayi masa kyau qwarai da gaske kaman tashi "Wani abokina ne ya dage lallai lallai yau sai na amsheta na dana,tun tana sabuwa yamin tayi ban taba danawa ba,kinga kuma bai kamata naqi ba karya dauka wani abun ne na daban kuma" kai ta gyada yayin daya dinga satar kallonta lokaci zuwa lokaci,har bintu ta fahimta ta d'an masa tsiya,kunya ta sanya shahida daukan wani plate data gani ta saka jikin redion motar,tadan qaro volume sanda taji batajin me yake fita daga cd din,waqa ce ta hamisu breaker waqar jarumar mata,sautin waqar ya ratsa motar,kidanta ya fita sosai ta speakers din motar ya karade ko ina,har ta saka hannu zata kashe anwar ya daga mata hannu alamar ta barshi,shuru ya ratsa motar saidai gaba dayansu waqar na ratsasu ne,ji suke kaman su suke rerawa junansu,shurun yaci gaba da yi musu jagora har zuwa inda za'a gabatar da bikin. Sai daya rakata har ciki yayi mata mazauni,ya kuma gaya mata bai yadda da shiga rawa ba sannan ya fito ya dawo cikin motar ya zauna,wanda ya faka ne a bakin titi,sai yabar murfin motar a bude iska na shigowa qafarsa daya a waje. Awa guda da fara gabatar da bikin yana zaune yasa sauraren redio "Yauwa ga wani can....salamu alaikum" yaji an ambata,kanshi ya dago yana dubanta sannan ya amsa,matashiyar budurwa ce wadda a qalla ta doshi shekara ashirin da d'aya,sanye cikin doguwar riga da siririn mayafi,fuskarta saye da tafkeken glass,gabanta ne yayi mummunar faduwa saboda cika mata idanu da kwarjini da yayi mata,uwa uba kyau data jima bata ganshi tattare da wani d'a namiji ba,da qyar ta tattaro miyan bakinta tace "Don Allah bawan Allah ko zaka taimaka ka duba mana motarmu?" Tayi maganar tana qare masa kallo ta cikin glass dinta,sai daya kashe redion sannan yace "Me ya sameta?"yarfar da hannu tayi cikin yauqi "toh wlh ban sani ba,ina cikin driving ta soma slow sai kuma ta tsaya gaba daya" dan jim yayi kafin ya jinjina kai ya fito daga motar ya rufeta sannan yayi gaba zuwa inda motar tata take. Tsahon wani lokaci yana qoqarin ganin ya gyara saita tashi saita sake mutuwa,saboda haka ya dago yana goge hannunsa da tsumma "Gaskiya dole sai bakanike yazo"ya fadiwa nafisa dake gefe tsaye suna qare masa kallo ita da qawarta mima "Ya salam...bari na kirashi Allah yasa yana kusa" ta ciro tsadaddar wayarta ta soma nemanshi,cikin sa'a yace yana kusa ta bashi adress din inda motar take "Idan ba damuwa ko zamu dan zauna cikin motarka kafin ya iso saboda zama a wajen ba dadi" nafisa ta fada sanda anwar ke komawa zuwa cikin tashi motar,tsayawa yayi ya waiwayo,kaman yace a'ah sai yaga mata ne bai kamata ya barsu tsaye ba,tunda motar tasu ba zasu iya zama cikinta ba,shi kuwa diya mace ako ina take yana da kishi da qoqarin kare mutunci da martabarta bakin gwargwado koda bai santa ba "Ba damuwa" ya fada yana sake yin gaba,idanu suka hada da mima ta kashe mata ido gami da sakin murmushi suka bi bayansa. Ya tsammaci duka baya zasu shiga,sai yaga mima ce kawai ta shiga bayan,nafisa ta shiga kujera mai zaman banza,sai data zauna sosai sannan ta waiwayo ta dubeshi tana murmushi "Suna na nafisa....kaifa?" "Muhammad anwar" ya bata amsa a taqaice,idanu ta lumshe "Nice name...sunan ya dace da maishi" saiya waiwayo ya dubeta kafin ya dauke kai,murmushi ta sake saki "Dan wanne anguwa ne kai?,Allah yasa ban matsanta maka ba da tambaya" kai ya jinjina sannan ya gaya mata unguwar da yake "Kai ai bamu da nisa sosai" itama tasu unguwar ta fada masa,kusan duk unguwannin nasu maqotan juna ne,shuru ne ya sake ratsa tsakani yayin data lula duniyar tunanin yadda zata sha kan anwar,don ba zata cuci kanta ba kallon farko taji anwar yayi mata,infact ma zata iya cewa ta kamu da sonshi ne kai tsaye. Isowar mechanic din shi ya katse duk wani tunaninta,hanya daya ta rage mata saboda haka ta miqa mishi wayarta "Idan ba zaka damu ba ka sakamin numberka mana,saboda nayi maka godiya" kai ya girgiza "Basai kinmin godiyar komai ba" kai ta langabe "Ya zama dole na gode maka,saboda alkhairi kayi min" baison jan zancan saboda ya gaji da surutunta,saboda haka ya amshi wayar daidai sanda shahida ke takowa zuwa inda motar take,tana iya hango komai saboda akwai haske cikin motar,mummunar faduwar gaba ta samu,saidai ta kasa hana kanta qarasawa wajen,saitaci gaba da takawa harta isa bakin motar,daidai sanda ya gama saka mata number din ta amsa tana murmushi tace "Na gode,sai gani na gaba" ja baya shahida tayi a hankali sanda nafisa ke fitowa daga gaban motar,idanunsu suka hadu dana juna,kallon kallon suka yiwa juna kafin nafisan tayi gaba mima ta rufa mata baya,binsu shahida tayi da kallo har suka bacewa ganinta cikin duhuwar wajen sannan ta dawo da dubanta ga anwar wanda sai sannan ya lura da tsaiwarta a wajen.*ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER* 07067124863 *Ko kuma* 09032345899 *ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*🙏🏽 https://www.youtube.com/channel/UC4kJO342hmb_Pd2luKHBjFA/videos *Alqawarin Allah* 1️⃣1️⃣ "Wacece?,me takeyi a nan wajen?" Ta tambaya tana daga tsaye ba tare data shigo cikin motar ba "Motarsu ce ta lalace nayi qoqarin gyara musu,bata ma gyarun ba sai data kira bakinikensu" "Shine tazo kusa da kai ta zauna?,har kana amsar wayarta tana jifanka da murmushi?" "Shigo tukunna sai muyi maganar" ya fadi yana bude mata murfin motar sosai,kaita girgixa sai kawai ta juya tabar wajen idanunta cike fal da qwalla,cikin hanzari ya fito don ya cimmata saidai ina tuni ta kutsa cikin mutane ta bace masa bat,haka ya qaraci nemanta bai ganta ba,dole ya dawo gaban motar ya dinga jera mata kira amma bata daga ba. A hankali wajen ya soma yoyewa,ya sake shiga ya dubata amma kome kama da ita bai gani ba bare ita "Ya salam shahida....ya salam" ya dinga furtawa a jejjere sanda yake tuqa motar zuwa hanyar gidansu amaryan,ba qaramin tashi hankalinsa yayi ba,bai samu 'yar nutsuwa ba sai daya isa gidan yasa aka shiga aka binciko masa aka tabbatar masa ta dawo gidan nan sannan ya saki ajiyar zuciya,nan kuma ya shiga jera aiken kiranta,saidai mirsis taqi zuwa,ganin dare ya soma yi ya sanyashi haqura kan tilas yaja motar yabar unguwar,bai je gida ba sai daya soma kaiwa abokinsa matar,yace daya barta ma sai sun gama bikin don tafiya ma zaiyi ta sati guda,murmushi ya saki wanda kusan na yaqe ne,donshi kusan sam baiji dadin hawa motar ba,yana ganin kaman itace silar faruwar komai,inda ace a motar haya suka tafi shikenan nafisa ba zata ganshi ba,da amotar haya suka tafi nafisa ba zata rabi wurinsa ba saidai wajen wani,don bashi da gurin da zata roqi alfarmar zama har shahida ta gansu tare,da a motar haya ne da tuni tare zasu dawo da shahidanshi su rabu cikin farinciki sa walwala. Ta gefan shahida kuwa hankalinta a tashe,gani take kaman za'ayi mata qwacen anwar din,duk kwanan duniya idan ta kalli anwar din sai taji fargaba ta cikata,anwar nada kyau kwarjini da cikar zatin da zai zama abun kwadayin mallakar kowacce mace,kallo daya ta yiwa nafisa ta tabbatar 'yar masu dashi ce,idan hakan yayi nasarar janye hankalin anwar fa tayi yaya?,da sauri ta kori wannan tunanin daga ranta,don fatan dorewar hakan,a ranar da qyar ta sami bacci duk da wayarta na silent tana da yaqinin ta tara miscal na anwar din. Itama kusan tubure masa tayi yadda ya mata kwanaki,qarshe dai saida suka dangana da anty amina tayi sasanci kamar yadda ta saba,zuwa lokacin ba qaramin jigata yayi ba,wanda hakan ya faranta ran shahida ta wani gefe,tunda ko babu komai ta sake sanin mizanin da zata dora soyayyar da yake matan. A haka rayuwar wannan masoya take ta kuma ci gaba da gudana,kowanne cike yake da tsananin so qauna da kuma kishin dan uwanshi,kowannensu cike yake da buri da fatan farantawa dan uwanshi,har zuwa sanda shahida suka soma shirye shiryen yin candy,a boye ba tare da saninta ba don yasan zata iya hanashi anwar yasa akayi mata jaka da memo,yace bazaiyi calender ba bare wani qato ya rataye a dakinsa ya dinga kalle masa mata,ko memo dinma babu hoto a jiki,yayi mata key walder hakanan ya soya kayan da zata saka ran walima complete,dukka yayi hakanne bada saninta ba don yanason mata suprise ne. _*TAURARUWA MAI WUTSIYA*_ Tsaye take a hamshaqin falonta gaban window,wanda yaji komai da komai na kayan alatun more ruwa,falone dan qarami saidai ya wadatu da dukkan wani abun buqata domin hutawa da nutsuwar ruhi,tana sanye da riga da skert wanda iyakar skert din qaurinta "Ina jinki mema....na zaqu naji daga gareki,wallahi tun ranar dana soma ganinshi har yau ban sake samun nutsuwa cikin rayuwata ba....duk iya qoqarina na ganin na samu zuciyarsa abun yaci tura,yana da wata izza kaman d'an wani,kwarjininsa shike sake dakusar dani,inajin sonshi ya kaimin ko ina cikin jiki da ruhina" tayi maganar duka tana tsaye jikin window din ba tare data juyo ba,idanunta na farfajiyar gidan data wadata da korayen tsirrai. Tabe baki mima tayi,ita duka mamaki ya cikata,ta yadda feena ta fada qaunar talaka matsiyaci kaman anwar din,ta kuma fita hayyacinta lokaci guda,haka kawai tana tsaka da more rayuwarta,to amma ita nata yi mata aiki ta kuma biyata,indai zata biyata din ai shikenan "Ba haka kawai kika kasa samo kanshi ba ai feena" meman wadda ke zaune kan daya daga cikin kujerun falon qafarta daya kan daya tana karkada takardar hannunta ta fada,da hanzari nafisa ta baro inda take ta qataso gaban feena sannan ta yiwa kanta mazauni kan wata kujerar daban tana duban feena idanu bude "Kaman yaya?,meye dalili?" Wani shu'umin murmushi ta saka tana qiyasta kudin da zata tatsa wajen feena a yau sanadin wannan zazzafar jaridar da zata saida mata "Zaki iya tuna yarinyar da kukayi kallon kallon da ita ranar da muka zauna motarshi" yatsanta manuni ta daga sama da sauri kaman maishirin bada amsa cikin aji "Exactly....na tunata,tun ranar yarinyar na tsaye cikin raina...na rasa wacece mai shegen kyau da izza haka,da farko nayi tunanin qanwarsa ce saikima naga basuyi kama ba tako ina" "Right....budurwarsa ce" gaban feena ya fadi ta zaro idanu "Wait....da saura fa" mima ta fada tana dariya qasa qasa sannan ta gyara zamanta "Idan kin taba karanta labarin soyayyar romio da Juliet wannan sun wuce haka,qauna ce irin wadda zata bawa bahaushen mutum mamaki,son junansu suke kaman tare aka haliccesu,daya baya komai saida shawarar daya,daya baya iya tafiyat da komai saida daya,bari dai na baki a taqaice a dunqule,sun narke sun zama abu daya...." "Dole su rabu su zama abu biyu kuwa...na fahimta,wato saboda itane na kasa cimma burina kenan?" Ta tambayi mima kai tsaye,kai ta jinjina tana lumshe idanu sannan ta bude "Qwarai kuwa....amma saidai karki damu akwai mafita" ta ambata tana warware takardar hannunta,daki daki ta soma karanta mata abinda shahida tafiso da wanda bataso har sai da nafisa ta gaji daji ta daga hannu tana dakatar da ita "Jin wannan abun dame zai qare ni?,qara qonamin rai kikeson yi mima" "Kina da gajen haquri inda matsalarki take kenan....amma tunda kina ganin haka shikenan bari na wuce" ta fada tana ninke takardarta,caraf ta kama hannunta "Mtsweeww,banason ko jin sunanta ne wlh,zauna mu qarasa" bata wani jaa ba ta zauna din don tana lissafin abinda zata samu ne,taci gaba da karanto mata inda gabar qarshe take dauke da "Ta tsani cin amana,ta tsani munafurci,ta tsani ta zauna dakai zuciya daya kai kuma ashe da zuciya biyu kake tare da ita" tana kaiwa nan ta daga kai tana duban shahida sannan taci gaba da karatunta,fagen anwar ta shiga,abinda yakeso da wanda bayaso inda shima tashi gabar qarshe ta zama "Ya tsani mace mara kamun kai,ya tsani macen dake bin maza,sannan yayi masifar tsanar mace 'yar shaye shaye" ta sake yin shuru tana duban feena,dan jim tayi sannan ta gyada kai tana sakin murmushi sosai tana nuna mema "Shegiya mima,sai yanzu na gane...ko shahidan yana tsoron kaidinki qarashe bayaninki" sosai taji dadin yadda take sake samun karbuwa wajen feena koda yaushe,ta ninke takardar sannan ta sake tattara nutsuwarta "Yarinyar tana da ciwo tana da matsala cikin rayuwarta,duk da har yanzu ba'a gano wace damuwa gareta ba,amma zamuyi amfani da wannan damar mu sanyata ta zama 'yar maye,kinga mun samu matakin farko na rabasu,zai zama matakin farko ne saboda wanna kadai bai isa ya rabasu ba bayan bai kamata da wani laifi ba bayan wannan,itama bata kamashi ba,bayan ta zaba tantiriyar mashayiya zamu qara mata da sharrin bin maza...wannan kuma aikin wadanda suka san kan na'ura mai qwaqwalwa ne,zamu saka mata cewa baya sonta ita kuma yana tare da wata,duk zan kula da yadda komai zai kasance,naki kawai ki saki kudi ki zuba idanu" murmushin nasara ya subucewa feena,ji take kaman ta samu anwar ta gama,dukka kudin da yayi saura a jakarta ta zazzagewa mima,ta kuma yi mata alqawarin wasu "Ya...zaki dinner dinsu mu'az dinne" idanu ta fiddo "Me zai hana?,ai har na shirya qaryar da zanwa momy ta barni na fita,kedai jirani na shirya" cikin mintina qalilan ta fito cikin wasu matsiyatan riga da wando,hannunta riqe da burmemen hijab da take qoqarin sakawa mima na zaune na sheqa dariya,ta zuba duk kayan makeup dinta cikin haka ta maqaleta cikin hijabin sannan ta dubi mima "Mu hadu a bakin gate,don da mun shiga tare ta ganki zata saka ayar tambaya" haka kuwa akayi,ta isa wajen momy ta shirya mata qarya ta yadda ba yadda za'ayi ta ganota sannan ta fice suka hadu da mima,tun a cikin motar ta cillar da hijabinta tahau tsara kwalliyarta yayin da mima ke driving. Cikin nasara da taimakon ubangiji ta kammala rubuta jarabawarta kaf,wanda a ranar sukayi bankwana da dalibai da sauran malamai 'yan uwansu,a daren ranar anwar yayi shiga ta musamman yazo don tayata murna,ya kuma bata duk wani gift daya tanada saboda ita,sai data shiga dakinta tana dubawa abun ya sake burgeta,duk da anwar ba wani mai hali bane amma Allah ya hore masa tsari da iya siyayya,komai daya bata ya burgeta,ta jima tana kallon wani zobe,duk dana azurfane amma an qawatashi qwarai dole ya burgeka,zanen heart ne a jiki amma heart din rabi ne,murmushi ta saki tana sakashi cikin yatsunta,yayi masifar yi mata kyau,saita tattara kayan ta kaiwa ummanta wanda ita kanta ta yaba da qoqarinsa kaman yadda abbanta ya yaba,hakan ya mata dadi qwarai,ya kuma bata tabbacin kenan bata da matsala bata da wani shamaki da zai hanata mallakar anwar,tuna haka cikin jin dadi ya sanyata qanqame filon da take kai tana hango kanta da anwar dinta a matsayin ango da amarya qarqashin inuwa guda. Cikin farinciki da walwala ta gabatar da walimarta,komai ya tafi lpy ya kuna qayatar sai jiran sakamako,a sannan komai na tafiyar mata lpy,rayuwar tana hangen nan gaba kadan zata yi mata kyau,komai zai qarasa dai daita musu,anwar ma an masa qarin albashi wanda hakan dukka su biyun ya musu dadi. *SANADIYYA* Ana tsaka da haka gagarumin tashin hankali da yayi sanadiyyar lalacewa komai,ya zama silar tabuwar rayuwar mutane da dama,yayi sanadin wargajewar wannan iyali,ya kuma silar tarwatsa rayuwar shahidan...ya zama wani sanadi na dasa baqinciki mai tarin daci da zafi a rayuwarta ta faru. Rayuwa tsakanin mahaifinta da mahaifiyarta rayuwa ce ta rashin haquri,dauke kai yafiya da juriya da akasan dukkan ma'aurata da yiwa junansu,fada gaban yaransu wannan ba wani sabon abu bane tun tasowar shahidan,wanda hakan ya sanya bayan girmanta abun ya zame mata wani ciwo da duk sanda ya taso mata yake mata zafi da quna a zuciya,dukkan wani mataki da take ganin ya dace ta dauka a matsayinta na diya mai qarancin iko da abun fada ta dauka harma wanda ya zarta huruminta amma babu abinda ya sauya,duk da alqawari da qoqarin sauyawar da suke. Kwatsam dare guda mahaifinta ya jijjigo maganar qarin aure suna tsaka da rayuwarsu cikin rufin asirin Allah,wanda hakan ya sanya mahaifiyarta tayi tsalle ta dire tace batasan wannan zance ba,dalilin daya janyo tashin tashina da fadan da bata taba gani ya wanzu tsakaninsu ba,hakan ya sanya walwalarta da duk wani kuzari nata ya ragu,anwar ne mutum na farko dayafu kusanci da ita a sannan shiya soma gane tana cikin damuww,amma baisan dalili ba,taqi kuma sanar masa,ta yaya zata gaya masa wannan murdaddeb zance?,tun baya baisan halin da gidan nasu ke ciki ba saboda kare martaba da qimar iyayenta,duk sanda ta fuskanci akwai rashin jituwa tsakanin iyayen nata bata taba yin zance a gidansu,a gidan anty amina take zancanta,toko yanzu ma da lamarin gidan nasu ya lalace can take tafiya ya sameta anan,don ba zataso wataran wani mummunan abun ya faru a gabansa ba duk da yana musu kallon iyayensa amma asirin ciki sai hanji. *MAFARI* Cikin tashin hankalin da bata taba tsintar kanta a ciki ba ta fito daga gidan nasu tana hawaye,yau a gidansu a gaban idanunta ake doki in doka tsakanin ummanta da abbanta?,wanne irin iyaye gareta?,ya ilahi ji take kaman zuciyarta zata fashe,ji takae bugawa zuciyarta zatayi,ita kadai tasan yadda takeji tana jin kaman zuciyarta ta kumbura ne ta cika qirjinta,zataso ace zunnurah na nan saidai ina,gidan anty amina takeson zuwa amma babu ko nutsuwar daukan kudin mota a wajenta,ba tare da tuna nisa da tazarar dake tsakaninsu ba ta hau tafiya cikin fitar hayyaci da tashin hanakali bacin rai da baqinciki. Dawowarta kenan daga inda taje ta sauka a abun hawa,tana yunqurjn shigowa layin nasu ta hangi kaman shahidan,tayi mamaki don shahidan bata taba zuwa gidansu ba,hakanan bata yowa layinsu don asalan ita bamai yawo bace,sauri ta qara donta cimmata,sai taga itace dince kuwa,amma a binda ya bata mamaki hawayen data gani shabe shabe a i fuskarta,hannu tasa ta kamota tana cewa "Shahida,meye haka kuka kike fa akan hanya" sai a sannan ta kula da fiddausin,sake fashewa da kukan tayi,ita koma waye ta gani zata iya fada masa abinda ke damunta ko zataji sassauci a zuciyarta,abun ya mata yawa,wannan damuwar bata shekara daya bace ko biyu,ganin haka sai fiddausin ta janye shahidan zuwa gidansu,ta tura gate din gidan suka shige sannan suka nufi dakinta ta qofar baya,sau tari takan iya shigowa ba tare da an sani ba saboda gidan nada girma babu laifi. Kuka take sosai tana cewa "Na gaji fiddausi....na gaji da wannan bacin ran,ina zanje naji dadi,me zanyi na samu sassauci?" Murmushi fiddausin ta saki,duk da shahidan bata gaya mata damuwarta ba amma tana ganin sara ne yazo kan gaba "Ina da maganin damuwa shahida,maganin da zai dauke duk wata damuwa da kike ciki komai qarfi da girmanta,zaki jiki fresh kaman yau aka haifeki,nauyi da zuciyarki keji ya sauka kaman bai taba faruwa ba" idanunta dake jiqe da hawaye ta daga tana kallon fiddausi "Don girman Allah ki bani kona daina jin suyar da qirjina yakemin" "Kwantar da hankalinki basai kin hadani da girman Allah ba" ta fada tana zuge jakar data shigo da ita,kwalabe ta fito dasu ta hada abubuwan ciki ta gauraya sannan ta miqawa shahida "Daga kanki ki shanye nina daga wajen likita nake shi ya rubutamin shi yace maganin damuwa ne" ba tare da kowanne tunani yazo kanta ba,ba tare da tayi lissafin komai ba,ba tare da ta jinkirta ba ta daga kai ta shanye duka din kamar yadda fiddausin tace mata,cikin wasu qananun mintina ta soma jin dummm,ta soma ji kamar ana sauyata daga tata duniyar zuwa wata daban,ta soma daina gane komai,take a nan ta zube saman gadon fiddausin,lokaci qanqani nannauyan bacci yayi awon gaba da ita,dariya fiddausin ta saki tana rufe kwalabenta tare da maidasu haka tana cewa "WASA FARIN GIRKI YARINYA". *ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER* 07067124863 *Ko kuma* 09032345899 *ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*🙏🏽 https://www.youtube.com/channel/UC4kJO342hmb_Pd2luKHBjFA/videoshttps://youtu.be/T9a10h1Apqs 👆🏽👆🏽👆🏽👆🏽👆🏽👆🏽👆🏽 *zafafa biyar na kudi ne,idan kika gani DON GIRMAN ALLAH karki sharing,idan kina da buqata ki tuntubi wadan nan numbers din* 07067124863 *ko kuma* 09032345899 *Alqawarin Allah* 1️⃣2️⃣ A hankali ta farka tana mutstsuka idanunta da taji sun mata nauyi,sam ta mance inda take saida tayi dan tunani sannan ta tuna,da hanzari ta tashi ta zauna ganin gari yayi duhu sabanin sanda suka shigo gidan akwai hasken rana,agogon bango ta kalla sai taga qarfe takwas,hakan yana nuna kenan ta rasa sallar la'asar magariba dama isha'i. Da hanzari tayi nufin tashi saidai gaba daya jikinta a mace yake babu qwari,daidai lokacin da fiddausi ta shigo dakin dauke da plate din abinci,cikin murmushi take duban shahida "Sannu kin tashi?,ya kike jin kanki yanzu fresh ko?" Eh to,lokacin da tayi baccin ta mance komai,saidai yanzu bayan ta farka komai ya sake dawo mata,saidai baccin da tayi din ya rage mata bacin rai kadan,amma duka ba wannan ba,sallolin data rasa lokacin da take bacci su sukafi damunta,saboda haka tace "Banyi sallah uku ba fiddausi,nunan bandaki na daura alwala"ta fada tana jin babu dadi har cikin ranta,wannan wanne irin bacci ne?,bata taba irinsa ba,hakanan koda bata da lafiya bata taba hada salloli ba. Qofa ta nuna mata wadda take cikin dakin gadon nata,nan shahida ta shiga ta daura alwala,ta fito sannu sannu saboda yadda takejin jikinta sam.babu qwari,gagara yin sallar tayi a tsaye saboda yadda takejin qafafunta kamar lagwani tilas ta zauna ta yita a zaune. Tana gamawa ta miqe don hankalinta yayi gida kuma,don bata taba tsayawa a waje har wannan lokacin ba bata koma gidan ba "Ki tsaya kici abinci saiki sake samun qarfin jikinki" "A'ah fiddausi gwara na wuce gidan,ba wanda yasan inda naje" "Shikenan....bari na baki wannan duk sanda kike cikin bacin rai kina sha zaki baccinki ki manta da kowa" sam a cikin ranta batajin zata sake sha,saboda bata taba bacci irin haka ba,bugu da qari ita babu wani raguwar bacin rai data ji,don kada ta gwasaleta kawai ta amsa "Maganin damuwa ne,zaki samu relief,kin ganni nan,ko bacci ne yaqi daukata saboda wani bacin rai dana sha zanyi baccina hankali kwance" kai kawa i ta gyada,fiddausi ta rakota har qofar gida ta wuce ita kuma ta koma cikin saurin don ta labartawa mima komai da yadda abubuwa suka gudaba,sannan ra fara da turo mata kudin data alqawarta mata,don syrup dinta dama ya qare tana buqatar siyan wasu ta aje. Tsakar gidan nasu babu wadatar hasje sosai kasancewar babu wutar nepa,bata nemi kowa ba don bacin rai ke sake taso mata na yadda tabar gidan nasu dazu,uwa uba kuma wani sabon baccin take ji,gqba daya jikibta jibsa take kaman an tsoma lagwani a ruwa. Kan katifarra ta fada rub da ciki tana lumshe idanu tanajin yadda gabobinta sukayi rauni,idanun nata na arufe taji wayarta na ruri,sam baki daya ta mance da ita,ta miqe cikin kasala ta daukota daga saman akwatin kayanta,anwar ne yake kira,take ta dannan ta kara a kunneta "Ina kika shiga haka shahida?,nazo gida ana nemanki sama da qasa ba'a ganki ba?,na kira wayarki ya kusa sau hamsin ba'a daga ba" sai data lumshe ido sannan tace "Babu inda naje fa,ina gidansu fiddausi,wayar kuma na manta ta ne cikin akwatin kayana,koka kira babu lallai aji sautinta" ajiyar zuciya ya sauke yana jin tashun hankalin da yaji dazu na sauka "Karki sake irin wannan fitar,hankalin umma ya tashi sosai" "In sha Allahu" ta fada amma cikin zuciyarta tana fadin koma meye sune suka ja "Ya naji muryarki haka?,lafiya kike?" Saidata gyara kwanciyarta saboda baccin dake fisgarta tace "Lafiya qalau....kawai...bacci ne yakeson saceni" "Bacci yau kuma?" Ya tambaya cikin mamaki,sabida yasan a qalla suna kaiwa sha daya suna waya,a hakama shike datsewa yace tayi bacci,sam bata iya baccin wuri ba "Wallahi" ta fada a gajarce,saiya raya a ransa jiki da jinine kawai don haka yace "Alright,asuba ta gari to,tunda yau anmin ruwa gani da jin muryarki" murmushi ta saki a kasalance tace masa na gode ta datse wayar ta cillar gefe tana maida kanta saman filo hadi da sake lumshe idanunta. Mubina ce ta dago labulen dakin ta shigo "Yaya kizo inji umma...ashe kin dawo tun dazu ake nemanki" juyar da kanta tayi daya side din cikin muryar jin bacci tace "Saida safe...kice mata nayi bacci" yau ba 'yan maganar bane akan mubinan don haka ta fita ta shaidawa umman tasu saqon shahida,sai gata ra taso da kanta "Ke shahida....ina kika je tun dazu?" "Gidansu fiddausi" ta bata amsa ba tare data juyo fuskarta inda umman tata ke tsaye ba "Tashi ki dauko abincinki a kitchen kici" "Ba qoshi" ta sake fada cikin muryar bacci,sam umman tata bata lura da sauyin dake tattare da ita ba,ga tunaninta fushi tayi kaman yadda ra saba a duk sanda wani abu ya gilma tsakaninta da mahaifinta,saboda haka ta tabe baki "Indai ba zaki sawa ranki haquru da kauda da kai ba zakita ganin bacin rai,kije ki hadu da hawan jini a banza,babanku baida haquri kuma baida adalci,ni kuwa bazan tsaya ya tauyen haqqina ba atoh" tana gama fada ta juya ta fice,sama sama take jin abinda umman ke cewa,ga mamakin kanta da kanta,maimakon ta sake jin haushi yadda ta saba sai taji sam maganganun basu d'a d'ata da qasa ba,baccinta ya fiye mata komai,idanu ta sake rintsewa ba jimawa kuwa wani nannuyan bacci ya kwasheta. Kwana biyu tsakani suka ci gaba daga inda suka tsaya,a lokacin tana daki zaune tana turawa anwar tex,tun tana daure zuciyarta harta kasa,ta toshe kunneta duk a banza,takai ta kawo cikin dakin ita kadai saita fita,haquri ta soma basu tana kuka kowa idanunshi ya rufe ba wanda ya saurareta bare yayi shuru ya ragawa dan uwanshi,dare yaui ba damar ta fice daga gidan ta huta,sai kawai maganin da fiddausi ta bata ya fado mata ta juya da sauri ta koma dakin ta rufo qofar don sautin tartsatsin fadan ya ragu,ta duba saman madubinta yana aje ta dauka ta bide ta shanye gaba daya,ta koma gefan gadon ta zauna tana kuja gamida addu'ar Allah yasa yayi mata aiki,Allah yasa baccin yazo da wuri ya dauketa kota huta dajin meke faruwa cikin gidan. Cikin mintina qalilan bacci ya soma zuwa mata,kafin kace ta sheme a wajen,ba ita ta farka ba sao washegari da safe bayan gari yayi tarwai rana ta take,da hanzari ta miqe tana tariyo abinda ya farun,sosai taji dadi har ranta da Allah baisa taji qarshen masifar ba,don haka batasan ya aka qarke ba,ta bude sakatar dakinta ta fita tsakar gidan nasu,a share yaje fes saidai gidan nasu yayi tsit alamun ba kowa ko duka yaran basa nan,tasan da hakan don lokacin tafiya makaranta yayi,saita tari ruwa ta shiga bandaki,wanka tayi don tafijin qwarin jikinta sannan ta hado da alwala ta fito ta shiga dakinta ta sauya kaya ta tada sallar asuba da bata samu tayi ba,bayan ta kammala ta wuce dakin ummanta,ta sameta a zaune a falonta tana tsintar shinkafa,ta dago suka hafa idanu,kallo daya zaka mata kasan ranta a masifar bace yake,wanda tasan hakan bai rasa nasaba da kace nacen da sukayi jiya da babanta,gaidata tayi ta amsa sama sama "Wato don wulaqanci da iskanci da asuba kina ji ana bugun qofarki ki tashi kiyi sallar asuba kikaqi ko?" Ita sam batasan anyi hakan ba,batasanma yaushe aka buga qofar tata ba,amma kawai sai tace "Kiyi haquri umma,bacci ne yaci qarfina" "Oho ke kika sani,naga alama kin fara goyawa mahaifinki baya,to wallahi kikace haka zakiyi wahala zakisha" ko kadan ranta bai baci ba sai tace "Kiyi haquri" banza tayi da ita,sai bayan mintina wajen goma sha biyar sannan tace da ita "Saikije ki dauki abun karyawarki a kitcheni,idan kin gama ki kunnan wuta na dora shinkafar nan" "Toh" ta fada tana miqewa zuwa madafa. Tana cin abincin tana tunanin abinda ya farun jiya,gaskiya baqaramin rage mata radadi maganin yayi ba,ko banza batasan qarshen abun ba,hakanan bata ji wani bacin rai ba,saita yanke kawai yau ta sake zuwa gidansu fiddausi ta gaya mata inda ake saida abun ta siya,duk sanda suka soma balahirarsu tasha ta samu bacci ta qyalesu. To tun daga lokacin shahida ta shiga ruwa tsundum,batasan illa da giraman abinda takeyi ba,batasan yadda take rushe rayuwarta ba,kawai ita ta bada amanna ne tana shan maganin matsalarta,batasan tana sake qarawa rayuwarta matsala bane,tana tunanin maganin bacci kawai takesha,batasan ta fada shaye shaye bane tsundum,wanda ba wanda ya kula da sauyawarta banda anwar,lokaci zuwa lokaci idan yazo fira wajenta da zarar sun fara zata soma gyangyadi,haka zai mata sallama ya tafi,ya nazarceta sosai baiga wani abu daya sauya dangane da ita dinba bayaga yawan jin baccin,hakan ya sanya yayi tunanin ko shawara ce da ita?,baiyi qasa a gwiwa ba ya amso mata magungunan gargajiya harda na sanyi,ta amsa dai kawai ta jibge taci gaba da sha'aninta. Zuwa sannan sam abinda ke faruwa tsakanin mamanta da bbanta ya daina damunta,wani lokaci takan iya shigowa gidan ma ta taddasu sunayi tayi wucewarta daki ta kwanta abinta tahau baccinta,dukkan wadan nan sauye sauyen basu ganshi ba,ga ummanta kawai tayi mata shaidar ta koyi nunqufurci tana goyon bayan babanta,yayin da abban nata yake ganin hankali tayi ta daina damuwa da al'amarin dake faruwa. Ta bangaren fiddausi kuwa da akayi amfani da ita don cusa shahida cikin wannan harkar nasara ce a wajenta,don duk yadda aka tsara abun ya tafi dai dai,hakan yayi sanadiyyar samun kudade mai yawa daga wajen nafisa,plan dinsu na gaba shine cusa samari masu kudi 'yan duniya rayuwar shahidan,saidai duk yadda sukaso ga ganin hakan ya yiwu abun bai kasance ba,saboda sam shahidan tun asali a jininta yake,bata da kule kule,haka suka qaraci shirya plan din nasu suka gaji,hakan ya sanya suka sauya dabara,suka sake sabon shiri sabon taku da sabon tsari,wanda suke fatan shine mataki na qarshe da zai tarwatsa mu'amalar dake tsakanin anwar da shahida komai qarfinta. *_SHARRI KAYAN KWALBA_* Kusan a yanzu babu wata qawa kuma aminiya da shahida ke da ita data wuce fiddausi,kusan koda wanne lokaci suna tare,hudubar farko data soma yiwa shahida shine anwar ba son shahidan yake ba,yasha fada cewa mai zaiyi da yarinyar da iyayenta suka kasance tamkar karnuka saboda fada,sosai xancan ya daki shahida,saidai iya saninta anwar baisan badaqalar dake faruwa a gidansu ba,don tuni ta yanke yin zance dashi a gidansu bama gidansu kawai ba unguwar baki d'aya,yanzu kacokam gidan anty amina take tafiya su hadu a can,saidai kuma akace yau da gobe tafi qarfin wasa,sai maganar ta dinga tsayewa shahidan aranta,duk da cewa ko daya bata yarda ba bata gasgata ba,hakanan ba abinda ya ragu game da son anwar daga zuciyarta,duk sanda taso yin wani dogon nazari kan maganar fiddausi na kadar da hankalinta ta bata wani abun mayen sai zancan yasha ruwa. Ta gefan anwar gaba daya hankalinsa ya ta'allaqa ne kan nemawa shahida gurbin karatu cikin daya daga cikin makarantun gaba da secondry dake jahar kano tunda aka yi musu qarin albashi,bai gaya mata ba saboda yana sonne yayi mata ba zata,yaci wahala ya kashe kudi kafin komai ya kammala. Ana ya gobe zai shaida mata yana gurinta,ranar sun jima tare suna hira,sunyi hirar da suka jima basuyi irinta ba,kowanne yan jaddadawa d'an uwanshi yadda yake jinsa cikin jikinsa da zuciyarsa,sun tsokani juna sunyi raha wasa da dariya sosai,har anwar ta saka ranakun cikin daya daga cikin kundin ranakun farincikinsa da bazai taba mantawa dasu ba,ta bashi hotunan data dauka musamman sabodashi wanda ba qaramin kyau tayi cikin hotunan ba,kyanta ya fita muraran,ya qurawa hotunan idanu yaga kada kai "Wannan hotunan bazan iya maidasu enlargment ba" dubansa tayi tana narke ido tana dubanshi "Saboda banyi kyau ba ko?" Dariya ya saki yana cewa "Dama akwai wani lokaci da zaki qiyin kyau a idanuna koda wankan kashi kikayi?" Dariya sosai ya bata har shima ya tayata darawa "Dama ana wankan kashi ya anwar?" Girarsa ya dage "Eh waikoda ace anayi din...kyan da kikayi ne shahida yayi yawa,ina kishin mai aikin budawarma ya ganki" baki ta bude tana dubanshi "Ya anwar" "Shahida....kaman har yau kina kokwanton yadda nake sonki da kishinki ko?" Kai ta girgiza tana dariya "Xaki fahimta,sai ranar da aka kawoki dakina a matsayin matata" kunya ta sata sadda kai tana qiyasta ranar a ranta,gata ita dashi a matsayin miji da mata. Daya tashi tafiya saita miqo masa dari biyar bayan wata baqar leda,wadda daya bude links ne da agogo guda biyu masu matuqar kyau irin wanda tasan yana masifar so,kallonta yayi itama shi take kallo "Kada kacemin komai,na fuskanci yau miskini kake baka dako sisi(ta furta cikin sigar zolaya)"murmushi ya saki,gaskiya ta fada,don duka albashinsa ma na wajen wata uku ya qare ne wajen sama mata admission,dan abinda yaje riqewa bamai yawa bane,kudi ya dinga badawa don ta samu gurbin karatun,don yasan cikar burinta kenan shida ita,hakan bai dameshi ba ko kadan,yana jin zaiwa shahidan fiye da hakanma indai ita dince " har saika fada?"ta katse masa tunaninsa "Ina iya karantar zuciyarka ba tare daka furta abinda ke cikinta ba" ta fada cikin sanyi da taushi,sun riga da sun zama daya,sai ya saka hannu ya amsa yana murmushi "Na gode matata" kalmar data yi mata dadi sosai,cikin farinciki walwala da qaunar juna suka rabu,yana tafe yana tariyar dukka kalamanta,saiyakejin kyautar data masa tayau din daban take,hakan ya sanya ya kasa fasa kudin ya hau mota,ya taka har zuwa gida da qafa yana juya ledar data bashi gift din a ciki,gift din data bashine da sunan tayashi murnar xagayowar ranar haihuwarsa,wanda sam shi ya mance ma da yaune ranar haihuwarsa. 🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍 Qarfe biyar na yammaci da 'yan mintuna ta sauke wayar daga kunneta tana sakin ajiyar zuciya,itakam har cikin zuciyarta sam batajin zuwa ko ina,haka kawai taji batason fita.https://www.youtube.com/channel/UC4kJO342hmb_Pd2luKHBjFA/video *zafafa biyar na kudi ne,idan kika gani DON GIRMAN ALLAH karki sharing,ga mai buqata saiya tuntubi wadan nan lambobin* 07067124863 *ko kuma* 09032345899 *Alqawarin Allah* 1️⃣3️⃣ Fiddausi ce ta kirata tanason ta rakata wajen da take siyo musu kayan zaqi kamar yadda ta sawa syrup din da take baiwa shahidan suna,duk sanda shahidan ta buqata tana amsa ne kawai daga wajen fiddausin,wanda nafisa ce ta baiwa mima kudin da za'a siya a jibgewa shahidan,ita kuma mima ta baiwa fiddausi kudin ta saya ta aje din take bata,don ita bata harkar shaye shaye,barta da biye biyenta kawai,shahidan taso ta tirje don yau din anwar ya gaya mata zaizo akwai wata muhimmiyar magana da zasuyi,amma sai fiddausin taji haushi ta katse wayar sanda tace ba zata samu zuwa ba,ita dinma a karan kanta sai taga bai kamata taqi rakata ba,tunda abun nan tare suke amfana dashi,bugu da qari duk sanda takeso kyauta take bata shi ba tare dako sisinta ba. Tilas ta shiga bandaki ta sake gyara jikinta kasancewar tana al'ada ne,kuma idan tanayi din tana bleeding ba laifi,hakan ya sanya duk sanda zata fita take saka always biyu ko kuma pant biyu,yau always din tata ta qare saura daya saboda haka ta saka pant biyu duk da tana tunanin Allah yasa ya riqeta. Tsaf ta shirya ta shuga wajen umma "Umma....zan raka fiddausi gaisuwa,baban wata 'yar ajinsu ya rasu" "Ina ita fiddausin?" "Ta gidansu zan biya ai umma yafi kan hanya" "Saikun dawo" ta fada tana miqa mata dari biyu kudin mota,ta amsa ta miqe ta fice daga gidan. A qofar gida suka hadu da fiddausi "Amma karmu jima don Allah fiddausi saboda anwar kar yazo bai sameni ba,kinsan baison yawan fita" baki ta tabe cikin ranta tace "Yau za'ayi mai gaba daya ma ai" amma a fili sai tace "Sannu matar kulle,yaushe aka daura auren naku ban sani ba?" Harararta shahida tayi "Kinga banason wulaqanci,kome zakiyi ki tsaya iyani,koda ba'a daura aurenmu ba ya isane dani" "Allah ya baki haquri...shi yasa har na kira daddy A yazo ya kaimu saboda mufi sauri sai kuma nace ya barshi,don nasan halinki yanzu zakice ba zaki shiga motarsa ba" dan hade rai shahida tayi "Kinfi kowa sani ai,nifa banason kina hada alaqarmu data wadan nan tarkacen samarin naki,tunda dai mu ba 'yan bariki bane" "Iyee,wato samarina ne ma tarkacen,ba komai zan rama" "Saidai ki rame" da haka suka qarasa wajen. Tunda suka shiga wajen gabanta ke faduwa,gaba daya jinta take a tsarge,har qasan zuciyarta takejin kaman tana aikata wani abu daba dai dai ba,wajene da yake kama da gida daki daki,kaman gidan masu zaman kansu,daya daga cikin dakunan suka nufa ba tare da sun kula kowa ba,saida fiddausi ta tura qofan suka shiga taga ashe falone babba,akwai maza wajen biyar ciki,ga kayan da sukazo nema zube a gabansu da alama ciniki ake,guri daya shahida ta samu ta zauna duk ta takura,sai taga fiddausin ma ta samu waje ta zauna bayan sun gama gaisawa da mutanen cikin sanayyar juna. Ganin lokaci nata ja fiddausin bata sake cewa komai ba hakanan basuyi abinda ke gabansu ba ya sanya shahidan tabo fiddausin ta mata magana "Sorry....sallamemu uban gayya...qawata na sauri zata koma gida ne" "Kuxo ku xaba mana" ya fada ba tare daya dubesu ba yana ci gaba da lissafin uban kudin dake gabanshi,fiddausi ce ta soma zuwa wajen kayan dake tsakiyar mazan ta zazzaba kaloli daban daban sannan tacewa shahida taje ta zaba itama,a darare ta tashi ta nufin wajen,tana zuwa tsakiyarsu dab da zata isa wajen kayan wani santsi da batasan na meye ba ya kwasheta ta tafi zata fadi,daya daga cikin mazan wanda tunda sukazo yake tsaye a wajen yayi caraf da ita ta fada jikinsa. Cikin wani irin hanzari da tashin hankali tayi yunqurin miqewa daga jikinsa saidai ya riqeta gam,ta tattara dukkan qarfinta ta hankadeshi ta miqe,harara ta dalla masa kana taja tsaki cikin bacin rai da dana sanin zuwanta wajen,ko fiddausi bata kalla ba ta fice a wajen,kanta take baiwa laifi tare da jin haushin kanta da kanta,me ya kaita zuwa iri wadan nan wuraren?,sam wannan ba tarbiyyarta bace. Har taci rabin tafiya don bata tsaya taren abun hawa ba sannan ta biyota,gabanta tasha "Matsamin na wuce,dama wajen wadan can watsattsun zaki kaini?" Kan fiddausin ta langabe tana share qwalla "Wallahi na fiki baqincikin abinda yayi miki shahida,abinda ya tsaidani kenan ma yace na baki haquri shiba don wani abu yayi ba ganin zaki fadine" ta iya dadin baki da tsara kalamai,haka ta dinga baiwa shahida baki harta sauko "Kin fasa daukan abun ne?,kinga ni gobe zanyi tafiya kuma zan dan kwana biyu ban dawo ba,shi yasa nace kizo ki dauki wanda zaki amfani dashi kafin na dawo" "Inaso,amma bazan sake komawa gidan wadan can 'yan iskan ba" da haka tasha kan shahida tace gidan wata qawarta zasuje. Gidan qawartata ne,wanda itama ta fito musu da kayan,fiddausi tace bari tayi testing,bayan tasha ta dubi shahida "Kai wannan sunyi,kinji taste dinma daban da irin namu,don Allah sha kiji shahida" kai ta girgixa "Ni bani da qarfin jini irin naku,bacci yake sakani sosai,kuma yau banason inyi baccin nan da wuri,saboda anwar zaizo" juna suka kalla suka tabe baki ba tare da shahidan ta kula ba sannan qawar fiddausin tace "Lahhh,wannan na musamman ne baya saka komai,mai kyan ne,banda ma fiddausin da babu wadda zan bawa shi" qawar ita ta hada mata ta miqa mata kwalbar,ta karba ta dan sha,sai taji yayi dadin fiye da wanda suka saba sha kamar yadda fiddausin tace,saboda haka ta shanye duka. Tun tana jin hirarsu sama sama har sai data fara ganinsu bibbiyu ta kuma kasa gane me suke fada,abu daya zata iya tunawa,sun dagata sun cire pant da pad din jikinta,taga jini na sake fitowa sosai daga jikinta,wanda batasan cewa cikin syrup din suka saka mata qwayar da zata sake sakata yin bleeding sosai ba. Tsahon wasu awanni wanda batasan awa nawa bane jikinta yayi danshin jini sosai,tanason tashi ta gyara kanta ta maida pant dinta ta kasa,sai malelekuwa take a tsakar dakin qawar,saita tashi saita koma yaraf,da qyar ta iya hada kalmar fiddausi ta kaita gida "Yanzu kuwa" ta fada. Tasan sanda ta kamata suka sata a motar wani saurayi gaban motarshi wanda ba zata iya tantace waye ba,suka rufe yaja motar. Tun daga nesa ta hangi kaman anwar zaune saman dakalin da lokaci zuwa lokaci suke zama,kanshi a duqe wayarshi na hannunsa yana dannawa da alamu ita yaketa qoqarin kira,hankalinsa na a tashe saboda ya iske gida suna bulayin nemanta ne su dinma. ,tanaso tacewa drivern ya sauketa amma ta kasa bude bakinta bare ta furta komai,tana son ta yunqura ta sauka amma ta kasa,tanaji tana gani ya isa dab da anwar din,yayi parking din motar,ya fito daga mazauninsa ya bude mata qofa sannan ya kamata ya fito da ita yana cewa "Saida nace miki kisha kadan kisha kadan amma da yake shegen hadamar tsiya ne dake,abu ya riga yabi jini saida kikayi tatul" lafazin daya sanya anwar dagowa daga danna wayarsa da yakeyi kenan,don tunda motar ta tsaya hankalinsa bai wajen saida yaji maganar dake fitowa daga bakinsa,yayi kuwa mummunan gani,yayi tozali da abu na farko daya ji kaman zuciyarsa zata tarwatse,shahida ce,shahida ce wani riqe da ita tana tangadi,wanda kana mata kallon farko kasan cewa cikin maye take,idanunta na cikin na anwar din,tana son qwace kanta,tana son yi masa magana,tanason qaryata abinda saurayin ke fada akanta,tanason tabbatar masa da meye ainihin abinda yake gani amma idan ta bude bakin shirme ne yake fita wanda shi kansa shirmen can qasan maqoshinta sautin ke fita,sakinta yayi daura da anwar wanda banda Allah yasa tayi hanzarin dafe bango zubewa zatayi a wajen,ya koma cikin motar ya riqo pant dinta da jakarta ya dawo inda take yana cewa "Saiki kula wajen shiga gida,ga jini nan duk ya bataki,gaba kya sake bari ciki yayi qwari a jikinki kafin a cireshi" ya qarasa maganar yana sakin kayan hannunsa,jakar ta fadi dama zip din a zuge yake,take tarkacen ciki suka fado dai dai qafafun anwar,kwalaben syrup dinta ne da tarkacen qwayoyin da ba shansu ma take ba,bata taba kwatanta sha bama. Anwar dake zaune daskare a wajen yaji kaman an jona mishi shociking,baisan ya akayi ba baisan kuma yaushe ya miqe ya kaiwa matashin kyakkyawan naushi a fuska ba,wanda karon farko yayi nasarar fasa masa baki da fitar haqorin bakinsa guda daya,sosai ya tsorata ya kuma razana da yadda yaga yanayin anwar ya juye ya zama,cikin hanzari ya juya don tseratar da kanshi,saida tuni anwar ya damqo kafadarsa ya juyo dashi ya watsa masa wani kyakkyawan mari,bai jira ya gama wartsakewa ba ya kwasa da gudu ya nufi motarsa,anwar ya rufa masa baya,kafin yakai wajen har ya shige motar ya kulle qofar,iya qarfinsa anwar ya saka ya dinga dukan glass din window din motar,wanda kafin yakai ga tasar motar anwar yayi nasarar fasa glass din motar dai dai da sanda matashin ya figi motarsa yabar layin a guje. Hannunsa na digar jini ya dawo inda shahida ke zube,duk da bata cikin cikakken hayyacinta amma tasan cewa babban tashin hankali ne ya sameta,dubanta yayi sosai wani abu mai tauri ya tsaye masa a wuya,ji yake kaman ya farka maqogaronsa zuwa qirjinsa ya cillar ya huta,yau shahidansa ce yashe a qofar gida?,ba hijabi ba dankwali?,cikin maye?,cikin jinin da aka kira da jinin cire ciki ne?. Wasu mutum uku da sukazo wucewa ne suka dawo da baya don ganin me yake faruwa?,yaga sadda suka dawo din hakan ya sanyashi cikin hanzari ya damqi kafadar shahidan da kayanta ya turata soron gidansu sannan ya jawo qofar soron. Koda suka dawo din suna tambayar ba'asi banza yayi dasu har suka qaraci tambayarsa sukaji haushi sukayi gaba. Tamkar shima d'an mayen haka ya dinga takawa yana hada hanya,tun daga gidansu shahidan har zuwa nashi gidan,yana shiga ya danna sakata,bai ma tuna da abokansa da zasu zo kallon ball yau a sabuwar qaramar plasmar daya sakawa falonsa ba cikin salary dinsa. Kan carfet din dake malale a falon ya zube,bai damu da ciwon hannunsa dake zubda jini ba,ciwon da yakeji cikin zuciyarsa ya ninka ciwon da yake hannunsa ninkin baninkin,wani irin suya qirjinsa da zuciyarsa suke masa,baisan me zai tuna ba,bansan me zaiyi tunani akai ba,baya gane komai,shahida kawai yake hangowa a yanayin daya ganta a gabanshi,sai kawai ya zame ya kwanta a wajen. Ranar haka ya kwana nan wajen,kafin gari ya waye ya zubda jini mai yawa,takwas na safe abokinsa kuma babban amininsa yazo ya dinga bugun gidan bai tashi ya bude ba,yana da tabbacin yana ciki tunda gashi ba kwado a qofar gidan,daga qarshe dai da hankalinsa ya kasa kwanciya saiya haura gidan kawai. A lokacin ya samu a daddafe yayi sallah yana zaune wajen xazzabi nason rufeshi "Wannan wanne irin abune haka anwar?,ya zaka kulle kanka cikin gida ayita nemanka?" Ya fada yana son karantar yanayin da anwar din ke ciki,baikai ga bashi amsa ba sukaji ana buga gidan,miqewa muhsin yayi don ya duba mai bugun gidan. Minti daya sai gashi ya shigo riqe da envalope ya ajiye gaban anwar yana cewa "Hala ma dai baka da lafiya ko?"muhsin yayi tambayar yana qare masa kallo "bani da lafiya muhsin" "Subhanallahi,kasha magani?" Kai kawai ya iya kad'a masa "Ya zaka zauna haka?,bari naje wajen sule mai shayi na samo maka ruwan zafi kasha sai ka samu magani kasha,ko na rakaka asibiti a dubaka" bazai iya magana ba saboda shi kadai yasan me yakeji,yana kallon muhsin har ya fice daga gidan. Sai a sannan idanunsa suka sauka kan envalope din dake gabanshi *SAQON GAGGAWA MAI MATUQAR AMFANI GA WANDA SAQON YA SHAFA* ya gani rubuce baro baro a bayan envalope din bayan ya juyata,hakanan yaji hankalinsa ya karkata gason sanin meye a cikin envalope din. Ta sama ya farketa saboda yadda ta mannu,ya zazzage duk abinda ke ciki,hotom farko ya kusa tafiya da numfashinsa,shahida ce rungume jikin wani qato,wanda hoton an daukeshi ne jiya da sukaje siyan syrup sanda ta kusa faduwa ya tareta,hoto na biyu sanda sukaje gidan qawar fiddausi ta daga syrup tana sha,sauran duka hotuna ne na tsiraici tare da wani saurayi haihuwar mahaifiyarsu,kaf numfashinsa ya dauke saboda wani abu daya tokare kafar numfashinsa,ya tafi daga zaune zai kifa luuu,abu na qarshe daya ji kiran sunanshi da muhsin yayi cikin qaraji da razana,daga haka komai ya tsaya mishi cak.https://www.youtube.com/channel/UC4kJO342hmb_Pd2luKHBjFA/video *Alqawarin Allah* 1️⃣4️⃣ Ta bangaren shahida kuwa mahaifinta ne ya turo qofa ya tsinceta cikin wannan halin,wanda hakan ba qaramin kadashi yayi ba,bai gane a cikin maye take ba sai daya kamata zuwa cikin gida yaji tana surutai irin na wanda yasha wani abu ya bugu,saiya saketa suka zuba mata idanu shida ummanta suna kallonta,kasa tsaiwa tayi saita fadi luuu ta zube nata ci gaba da surutanta,wanda a nata tunanin anwar take kira ya tsaya tayi masa bayani,kuka umma ta fashe dashi yayin da abbanta cikin tashin hankali yace "Ina kika barmin 'yata taje mariya?" "Ina kuwa zan barta taje abba?,gaisuwar mutuwa suka je ita da qawarta" ta fada cikin tsananin tashin hankali da kuma kuka "Wallahi wallahi ki tabbatar da cewa indai wani mummunan abu ya samu 'yata toki kuka da kanki" ya fada cikin hargagi yana nunata da yatsa,a ranar dai umma babu bakin magana ta diyarta take,salati kawai take tana duba jikin shahida daya lalace da jini,bandaki ta kaita tayi mata wanka wanda shiya sanya bacci ya kwasheta bayan ta dawo da ita daki. 🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍 Da salati ta farka tana qarewa dakin kallo,ko ba'a fada ba tasan dakin ummanta ne,a hankali ta soma tuna me ya faru da ita,tun daga barinsu inda sukaje zuwa gidan qawar fiddausi,sauketa da saurayin yayi a qofar gidansu,daga nan zaren tunanin nata ya yanke,tayi tayi ta sake tuno abinda ya faru ta kasa,zuciyarta na gaya mata taga anwar,wata zuciyar tana ce mata bashi bane. Muryar umma ta jiyo tana kiranta cikin kakkausar murya wadda tasa hanjin cikinta kadawa "Shahida....ina kikaje jiya?" Saita kasa amsa mata,indai har a wannan yanayin ta shigo gidansu to tabbas bata da bakin kare kanta,kafin ta sake cewa wani abu umman ta zube dukka kwalaben da suka fado a jakarta wanda tuni ta gama karantawa ta kuma fahimci kayan shaye shaye ne a ciki,idanun umman jajur tace mata "Meye wannan shahida?" Kasa hada ido tayi da umman,hankalinta yayi qololuwar tashi,lafiyayyen mari umman ta sauke mata wanda ya gigitata,sannan yayi dai dai da shigowar abbanta dakin,wanda tunda ya fita sallar asuba daya daga cikin maqotansa ya masa jajen anga shahida an kawota qofar gida an yasar me ya sameta bai sake samun sukuni ba,yasan tabbas maganar akayita tattaunawa a jiya ana kuma sauya mata kamanni,yasan halin anguwar da 'yan unguwar kaf. "Ai kibar dukanta bari na gaya miki mariya,koma meye shahida ta zama laifinki ne,kin zaki baki kin kasa bawa diyata tarbiyya shine yanzu zaki zo kina wani hargagin banza da wofi?" Cikin bacin rai da shiga zafi biyu ta maida masa amsa "Indai shahida ta lalace ne kaima akwai laifinka,tunda kaima ubane ai ba'a dauke nauyin haqqin kula da ita daga kanka ba" "Au haka ma zaki ce?" "Eh na fada din,dame kakeso naji ne iye?" "To mariya nidai tsakanina dake saidai nace Allah ya isa ban yafe ba..." Cikin qaraji gana zubda hawaye tace "Nima Allah...." Qarar da shahida ta saki ita ta katse sauran magabar da umman tata taso furtawa,kuka take sosai hawaye wani yana bin wani "Ku dainawa juna Allah ya isa kune sila....dukanku ku kuka zama silar koma meye na koma a yau...ku ku kaini ga afkawa halin da nake ciki a yau,wannan abun da kukeyi shiya janyo komai,duk d'a na halak bazaiso yaga rana guda tak data zama ranar da mahaifansa sukai cecekuce ko jayayya ba a gabanshi,sai gashi ni nawa mahaifan a gabana suke xagin juna,a gabana suke aibata juna,a gabana suke debewa juna albarka,a gabana suke fada da junansu,duk yadda naso da ganin gyaruwar al'amarin hakan ya gaza,duk habyar da nabi ta ganin kun gyaru ba wadda ta bulle min,zafi da radadin haka yasa na nemowa kaina gurbatacciyar mafita,nake shan abinda ni a nawa tunanin bacci kawai zao sanyi ni,ban sani ba cewa ya shiga cikin abinda annabi ya haramta tunda zai gusar da hankali,zai saka maye,idan zanyi kuka bazanyi da d'aya saga cikinku ba,zanyi kuka ne sa dukkaninku,kun kasa fahimtata a sansa ya dace,kun kasa gane illar abinda kuke aikatawa a gabamu mu 'ya'yanku"daga haka ta miqe ta miqe jiri da kuma rashin qwarin jiki ya sanya ta dinga layi,amma bata dakata ba har sai data fice daga dakin zuwa nata dakin. Dukkaninsu sai jikinsu yayi sanyi,kowannensu ya shiga nazari da dogon tunani,bai sake cewa komai ba abban ya fice daga dakin,saiya zura takalmansa ma da niyyar ficewa daga gidan gaba daya. Yana sanya qafarsa a waje yaci karo da mutum uku cikin maqotansa "Yauwa malam nuraini...dama yanzu muke neman yaron da zai mana sallama dakai" qoqarin dai daita fuskarshi yayi ya basu hannu suka gaisa "Ashe haka abu ya faru?,wallahi sam bamuji dadi ba,yarinyar da kowa ke mata kallon hankali da nutsuwa" daya daga cikin maqotan nashi da ake kira da malam sallau ya fada "Wallahi kuwa malam sallau,amma nidai ina kyautata zaton sharrin qawaye ne tunda kowa ya shaidi nutsuwar yarinyar....amma cire ciki aiba qaramin abu bane,sanda haruna ke gayan qaryatashi nayi saida yatabbatar min da kunnensa yaji saurayin yana fada" a hautsine abban shahida ya dago yana musu wani bahagon kallo,kusan bai fahimci me suke fada ba gaba daya "Yata shahida ce tayi ciki harta cire?" Sai suka koma kallon kallo tsakaninsu,malam sallau ya dubi abban "Errrhmmm malam nuraini kodai mata sun maka irin halin nasu ne an boye maka bakasa me yake faruwa cikin gidanka ba?,banda haka wannan zancan ai ya karade unguwarnan daga daren jiya zuwa safiyar yau" "Innalillahi wa inna ilaihir raji'un" ya dinga maimaitawa yana dafe da kanshi,me yayi jama'ar unguwarsu haka sa cikin qanqanin lokaci zasu jefi diyar cikinsa da wannan sharrin,kansa ya dafe da yaji ya soma juya mishi sai kawai ya juya zuwa cikin gida "Allah ya tsare gaba ya kiyaye" ya juyo malam sallau yana fada cikin daga murya,dai dai sanda shahida data fito don shiga bayi ta kama ruwa ta saki butar hannunta cikin tsananin tashin hankali ta koma dakinta,dukka jikinta rawa yake,tana tariyar kalaman da saurayin ya dinga fada bayan ya saketa a qofar gidan,kenan duk abinda ya fada sun yarda dashi?,kenan yanzu kallon da kowa zai dinga mata?,innalillahi wa'inna ilaihir raji'un,Allahumma ajirni fi musibati wa akhlifni khairan minha"shine abinda ta dinga maimaitawa kenan. Cikin kwana biyu kacal ta rame ta fige ta fita a hayyacinta,bata taba tunanin akwai tashin hankalin daya wuce na fadan iyayenta ba saiga wanda ya ninkashi ya risketa,duk ta silar kaucewa wancan bacin ran ashe zata fada wanda yafi wancan tsanani rusa farinciki dama ruguza rayuwa gaba daya. Ba ita kadaiba gidanma gaba daya ya zama shuru,baya ga abinda ya faru abbanta ya kwanta ciwo sosai tun randa su sallau sukazo masa jaje,wanda ba komai bane ya taba ranshi irin maganar da suka furta,qarshe da aka aunashi jininsa ne yayi mugun hawa,hakan ya saga hankalin ummanta itama ta shiga wani sabon tashin hankalin da firgici. Kwana uku amma shahidar jinta take akwai ya babu,gata nan dai kawai amma komai ya fice mata aka,ranar kwana na ukun da yammaci wani yaro yayi sallama tsakar gidan nasu dauke da takarda wanda yace gashi a baiwa shahidan. Mubina ce ta bita har cikin daki a sannan tana kwance saman abun sallah ta miqa mata,saita saka hannu kawai ta amsa ta aje saman kanta tana ci gaba da lazuminta,wanda kusa fiye da rabi istigfari take da salatin annabi. Sai data idar sannan ta dauko envalope din,tana daga kwance ta farketa,takarda ce qwaya daya a cikinta ta fado,sai wata azurfarta guda biyu data siya ta baiwa anwar ajiya,da sauri tasoma warware takardar tana zumudin jin daga gareshi,don tunda abun ya faru taji dif daga bangarensa,tana zaton wala'alla yazo ance mishi bata da lafiya,don bata da maraba da mai lalurar,ita kuma wani kunya da nauyin kiranshi take,gani take kaman daga muryarta zai karanci komai,zai karanci halin data fada,wasiqace cikin rubutun anwar din mai tsari _Basai nayi miki sallama ba don baki cancanceta ba,saqo nake son isar miki dama ba wani mai tsaho ko yawa ba,shahida,sam baki dace dani ba,kuma sam bakiyi dai dai da rayuwata ba,tuntuni ina zaune dake ne kawai don bani da abinyi kuma bani da wata qwaqwaqwarar sana'a,gashi ina da buqatar macen da zan di ga rage dare a wajenta,to zuwa yanzu al'amura son suma yimin kyau,bana jin zan iya ci gaba da zama dake,ki sani ni muhammad anwar ban taba sonki ko qaunarki ba,na miki alfarma ne kawai a baya,kuma ki saka a ranki cewa baki taba soyayya da wani mai kama dani ko suna na bar har qarshen rayuwarki,wasiqar na tafe da guzurin sabuwar masoyiyita wadda nake da tabbacin ta fiki komai,idan nace komai ina nufin komai da komai da kikasan diya mace na mallaka_ Cikin rawar jiki ta miqe zaune dungurgur,sannan ta jawo envalope din ta sake lalubawa ciki,saiga hotuna guda shida rigis sun fado,dukkaninsu anwar ne cikin hotunan da wata matashiyar budurwa cikin kyakkyawar shiga ta alfarma,kana musu kallon farko zaka tabbatarwa kanka lallai masoya ne da sukayi zurfin cikin qaunar juna,saboda yadda kowanne ke kallon danuwanshi cikin fara'a da shauqi,sosai ta tsurawa fuskar yarinyar ido zuciyarta na wani qara gudu tamkar zata faso qirjinta,suya zuciyar tata take mata tanason yin kuka amma bataji koda alamarsa ba bare yazo,nazarin fuskar yarinyar take take ta tuno inda ta santa,ranar bikin umaima,ranar bikin umma zaune gaban motar daya amso don ya kaita ya daukota,saita saki hoton tana girgiza kai tare da laluben wayarta duka lokaci daya,tamkar tababba take zancan a fili ita kadai "Nasan wasa kake min ya anwar ba zamu taba rabuwa....nasan wani ya kaima labarin abinda ya faru dani,ranka ya baci ka furta min wannan kalaman saboda kishina da kake" maganar tata ta katse sanda wayar ta shiga ta soma ringing. Wata murya daban ta dauka,cikin matuqar sauri da zaquwa tace "Don girman Allah ka taimakeni ka bawa anwar" dan jimmm yayi cikin tunani,don a yanzun bayajin anwar din zai iya wata dogon magana,tunda Allah yasa suka miqashi asibiti yayi kwanaki biyunsa cur ya farfado yace a dawo dashi gida yazo ya dauke wata envalope dashi kansa muhsin baisan meye a ciki ba ya adana yake zaune waje daya,kana kallon yanayin fuskarsa kasan ya dulmiya cikin wani qunci,iein quncin dake kama zukata ya riqe tamau ya dinga yankarta a hankali yana saka rudani damuwa da baqinciki mai yawa a rayuwa,irin baqincikin dake tasiri kadan kadan daga ruhi zuwa gangar jiki ya illata mutum ta farat daya ba tare da an ankara ba. Miqa masa wayar yayi,sai daya daga idanunsa da suke nuna alamun gajiyawa da damuwa ya dubi muhsin sannan ya maida kan wayar,hannu ya saka a hankali ya masa,muhsin ya sakar masa yana tashi gami da cewa "Bari naje gida na dauko wayata na barta a chargy" kai kawai ya iya gyada masa yana kara wayar a kunnensa. Abu na farko da tayi kuka ta sakar masa,wanda yake bayyana rauninta qarara,gajiyawa da rashin samun madafa,idanunsa ya runtse yana jin zuciyarsa cikin wani inji ana hautsinata sama da qasa ko zata faso qirjinsa ta fito. *zafafa biyar na kudi ne,idan kika gani DON GIRMAN ALLAH karki sharing,idan kina buqatar siya ki tuntubi wannan number* 07067124863 *ko kuma* 09032345899https://www.youtube.com/channel/UC4kJO342hmb_Pd2luKHBjFA/videos *zafafa biyar na kudi ne,idan kika gani DON GIRMAN ALLAH karki sharing,idan kina da buqata ki nemi wadan nan numbers din* 07067124863 *ko kuma* 09032345899 *Alqawarin Allah* 1️⃣5️⃣ Tamkar ana hautsinashi shi kanshi,wani irin abu ya dinga ji mai kama da tsana qyamata da haushi cike fal a zuciyarsa,wannan runtse idanun da yayi ba abinda ke gilmawa cikin idanunsa sai hotunan daya gani kwanaki hudu baya da suka shude "Dama akwai wani wani lokaci da zaizo da zaka daina sona ka juyamin baya ya anwar?" Shuru yayi ba tare daya ce komai ba,duk sanda yayi yunqurin cewa wani abu sai yaji wani dunqulallen abu ya tare masa maqoshi "Ashe dama saboda wata qaddara ta fadawa rayuwata saika gujeni?" "Qarya kike!.....babu ruwab qaddara" ya fada cikin qaraji da daga murya,wanda har sai daya tashi daga kashingidar da yake yana fidda huci irin na wanda ransa yayi tsananin baci,daga gefan shahida tsoro ne ya kamata,tana daga zaune amma jikinta ya dauki rawa,cikin jarumta da dakiya tace "Amma yaya anwar....dare daya wannan abun har yayi girman da zai saka ka manta soyayyarmu?" "Soyayya?....soyayya kike fada shahida,daga yau ki sawa ranki nayi bikin bunne soyayyarmu,kisa a ranki baki taba soyayya da wani mai suna anwar ba" gabanta yayi mummunan faduwa,kalaman daya furta yanzu sunyi kama da wadanda ke rubuce cikin takardar dake qanqame yanzun a hannunta,da gaske anwar shi ya iya rubuta duk maganar dake kan takardar?,yana nufin ba bacin rai bane cikin hayyacinsa yake?,hakan yana nufin da gaske yana tare da wata?,ya sauyata da wata? "Sam baki dace dani ba bakiyi dai dai da rayuwata ba" kalaman suka sake saukar ba zata daga kunnuwanta zuwa zuciyarta,saqon ya isa kai tsaye zuwa qwaqwalwarta ya soma barazanar dakatar da aikinta "Nayi dana sanin saninki....nayi dana sanin kasancewa dake tsahon lokuttan dana diba a baya" ya furta cikin sanyi wanda hakan ya saba da ainihin abinda ke zuciyarsa na tururi da zafin da takeyi,idanunsa sun kada jazur dasu "Ya....yayya...kasanme...me kake fada kuwa?" Ta fada cikin harhada kalaman da suke niyyar qwacewa daga bakinta saboda tsananin dimuwa dataji ta afka lokaci guda "Shahida.....idan nace Allah ya yimin sakayya ba shakka banyi kure ba" qit ya katse kiran daga haka saboda numfashinsa da yaji ya soma yi masa tauri,kanshi ya kifa kan kujerar dake gabanshi yana fidda numfashi cikin wahala,ba shakka dashi ragon namiji ne kuka zai fashe dashi ko zai samu sassauci cikin zuciyarsa,domin a wannan yanayin da yake ciki kukan shine abunda yafi cancanta yayi. Daga fannin shahida kuwa miqewa tayi hannunta aka,sai kuma ta saukesu ta nufi qofa gadan gadan,komawa tayi da baya kuma saboda katsewa da tunaninta yayi,ta samu gefan katifarta ta zauna,lallai ba shakka koma meye zai faru a yau tana da buqatar ganin anwar ido da ido,zuciyata bata gamsu ba hakanan nata nutsu da cewa shi yake gaya mata wannan maganganun ba. Kusan wunin ranar gaba daya tsaho taga yayi mata,tayi sintiri sau babu adadi,takai ta kawo kaman wadda ta hadiyi tabarya,ko sha'awar zaman ma sam batayi har aka kirayi sallar magariba,magaribar tazo tadan gota sannan ta fito tsakar gidan sanye da hijabin sallarta. Ummantace kawai zaune saman abu sallar wanda suna hada idanu takau da kai,daga ita har abban nata ta fuskanci kamar suna kunyar hada idanu ne da ita ko yin wata doguwar magana tun maganar data gaya musu ta qarshe ta fito ta barsu a dakin,da alama yau abban nata ya samu ya lallaba ya fita masallaci sallah kenan,gefe ta samu ta tsugunna a takure "Zanje chemist din ado ya dubani"bata ce komai ba sai daga abun sallar gabanta da tayi ta ciro dari biyar ta miqa mata,sannan ta waiwaya ta kalli mubina dake zaune tana zane zanen 'yar tsana a paper "tashi ki rakata" tsam mubina ta aje takaddun,ta dauki hijabinta itama dake gefe wanda da alama tare da umman suka gama sallar ta saka tabi bayan shahida da tuni harta fara takawa zuwa waje,tuninta kawai ya zatayi da mubina. Dole ta fara zuwa shagon ado ta gaya masa qarya da gaskiya ya soma hada mata magani,sai tace masa tana zuwa,ta samu mubina zaune kan bencin dake aje a qofar shagon "Zauna mubina naje na amso wata allura da yace zaimin,karki sake ki tafi ki jirani na siyo na kawo yanzu zaiyimin"kai ta gyada abinta,tana ci gaba da kallo ta cikin qaramat tvn dake cikin chemist din. Sannu a hankali ta dinga tambayar gidan,karo na farko a rayuwarta data soma tunkarar gidanshi,bama gidan ba unguwar gaba daya. Sanda wani yaro ya nuna mata gidan saita tsaya cak zuciyarta na mugun bugawa kaman zata fito,addu'o'i ta soma karantawa tana neman agajin ubangiji,jin motsi daga cikin soron ya sanya tayi saurin matsawa ta rabe gefe tana kallon muhsin daya fito daga gidan ya miqe can layin nasu yana amsa waya. Sai data tabbatar ya qule sannan ta fito sosai,ta doshi gidan ta saka qafarta asoron da bismillah a bakinta. Dai dai lokacin yana zaune ne shuru,yayi nisa a duniyar tunani,gabanshi abinci ne aje,abincin da muhsin yaji haushin qin gaya masa damuwarsa da yayi ya tafi ya barshi yana mita. Bai ankara ba baisan ta shigo ba sai ganinta yayi tsaye bisa kanshi. Dubanta yake kaman yadda take dubanshi,kowanne da abinda qwaqwalwa da zuciyarsa take gaya masa,cikin hanzari ta isa gabanshi "Baka da lafiya ya anwar dama?,me yas....." "Dakata!" Ya fada a tsawace yana miqewa tsaye,ji yayi kamar ta dana mishi wuta a jikinsa,ganinta ita daya cikin wannan dare sannan kuma cikin gidanshi "Me ya kawoki me kikazo yi?" Idanunta fal hawaye take dubanshi,tunda suke dashi dai dai da second guda bai taba mata magana da irin wannan amon ba,har kullum shi mai tattalin kwanciyar hankalinta da farincikinta ne,yau daya anwar din gaba daya taga ya sauya mata?,tun daga lafazi zuwa kamanni "Na baki second biyar ki fita ki bani waje,idan ba haka ba saina baki mamaki wallahi" ya fadi idanunsa dake cike fal da kishi haushi takaici da baqinciki suka sake girma suka yo waje kaman zasu fado "Ya anwar....ka daina irin wannan abun kana bani tsoro wallahi....ya anwar wani ya baka labarin abinda na aikata ne yasa ka sauya haka?" Wani murmushin takaici ya saki,wanda shi kansa ba abinda ya qarawa fuskarsa face wani yanayi mai ban tsoro "Labari?,labari aka bani?labarin me?....shahida...ina cewa tun kafin kizo nan kinji me na gaya miki?" Kai take girgizawa kamar wata sabon tabi tana dubanshi,yayin da hawaye ya soma jiqa gaban hijabinta "Ka fada ne kawai amma ba kana nufin hakan har zuciyarka ba,ba zaka iya rabuwa dani ba,ba zaka iya gujemin ba" matsowa yayi dab da itar har suna musayar numfashi a junansu,idanunsa sun sake girma daja,ya sunkoya da fuskarsa saitin tata "So kike na maimaita miki abinda na fada a waya?,to ni anwar nayi dana sanin saninki da nayi,nayi dana sanin kasancewa da nayi dake a baya....shahida anwar bakya gabanshi a yanzu ki fita daga rayuwarshi,ya jima da yanke dukkan wata alaqa data taba hadaki dashi cikin tarihin rayuwarku keda shi" tunda ya soma maganar ta runtse idanunta tsam tana jin saukar hucin numfashinsa saman fuskarta,yayin da kaifi da dafin maganar ya dinga ratsa kowanne sashe na jikinta har ya isa ga zuciya ruhi da kuma qwaqwalwarta,duk da yadda idanunta ke a rufe hakan bai hana hawaye saukowa daga idanun nata ba kai kace lalataccen famfo aka bude,sanda ta ware idanunta itama akanshi sai yaja baya yana ci gaba da duban qwayar idanunta "Ya anwar....me yasa?,me yasa zaka yanke wannan kyakkyawar alaqar?,me yasa zaka yanke kyakkyawar dangantakar da aka ginata tun tana jaririya harta girma?" "Wannan kyakkyawar alaqar da kike magana akai ta dade da mutuwa,ta dade da juyewa zuwa mummunar dangantaka a wajena daga sanda na ganki kwance male male saman wa....." Sai ya kasa qarasawa saboda tuna mummunan ganin da yayiwa hotunan,wani abu mai tauri ya taho yaso ya toshe maqoshinsa,sabida haka cikin qaraji ya sake cewa "Ki fita shahida!. Ki fita nace!" Kai ta kada cikin tashin hankali tanason taji qarshen zancan daya dauko,daga sanda ya ganta me?,ya ganta ne sanda suka tafi siyan syrup?,koko yana tsaye sanda matashin saurayin ya fiddo ta daga motar? "Ba inda zani...kome zaka yimin ba inda zani" bata ankara ba taji ya damqi hannunta,karon farko a tarihin rayuwarsu,bai barta ba saida sukaje soron qarshe bakin qofar gidan sannan ya turata wanda hakan yayi sanadiyyar da tayi taga taga ta kusa faduwa Allah yasa ta turje "Bana sonki shahida" kalmar data hadu da qarar rufe qofar gidan garam da yayi ta bada wata tsawa tsakiyar kanta data sanya komai nata ya tsaya cak na wucin gadi,da taimakon ambaton sunan Allah data soma yi ne ta samu nutsuwarta ta dawo. A hankali ta dinga takawa kamar wadda tasha wani abun,kalaman anwar suka soma amsa kuwwa cikin kunnuwanta,wani irin bushewar zuciya taji,dukkan wani tashin hankali ta nemeshi ta rasa,ba abinda takeji sai kalaman anwar a kunneta,bata ankara ba taji ana "Subhanallahi....sannu...amma bakiji ciwo ba ko?" Sai a sannan ta daga kanta tana duban mutanen dake magana kamar wata doluwa,ashe qatuwar kwalbatin da ake haqawa unguwar ta fada,da qyar da taimakon wasu 'yammata da sukazo wucewa ta samu ta fito sunata mata sannu,taci gaba datakawa ba tare data tsaya duba ciwon data ji ba,burinta kawai ta isa gida,burinta Allah yasa ace mafarki take. Bata tabbatar da cewa komai da gaske yake faruwa ba saida dare ya tsala,taji idanunta tarwai kaman yanzu ta tashi daga baccin wata uku,siya zuciyarta ta dinga yi irin wanda bata tajin irinsa ba,cikin qaramin lokaci qirjinta ya soma ciwo,numfashinta ya dinga fita da qyar,haka ta tsinci kanta har asuba ta risketa,sanda ummanta ke yunqurin tadata tayi sallah a lokacin taga halin da take ciki,basuyi wata wata ba suka wuce da ita asibiti. Gwajin farko likitan yaga jininta yayi mugun hawa,don dab yake da yakai dari biyu,dole suka soma mata allurar bacci kafin sauran treatment su biyo baya,ba qaramin tashin hankali abba da umman suka shiga ba,don duk ga zatonsu iya halin da suka tsundumata ne kawai yayi sanadiyyar faruwar haka,duk da cewa shi dinma ya taka tashi muhimmiyar rawar. Daga bangaren anwar tunda ya maida qofar gidan ya rufe da qyar ya kaishi daki ya zube saman kujerar falon qwalqwalwarsa na daukan zafi,yana maijin ciwo da zafin dukkan wani abu daya faru tun daga kwanaki uku da suka wuce kawo yau,ji yake kaman ya budi idanun yaga mafarki yake,yana jin bugu wanda yasan bazai wuce muhsin ba amma bazai iya tashi ba,bashi da sha'awar ma kowa ya rabeshi,daga bisani wayarshi ta dauki qara,ya qura mata idanu yana kallonta hartayi ta gana ta tsinke,sannan ya miqa hannunshi ya daukota,ba tare daya damu da duba mai kiran ba ya bude bayan wayar ya ciro layin wayar ya karyashi ya watsa tsakar gida sannan ya cilla wayar da batiranta gefe guda,a ranar yadda yaga rana haka yaga dare,dukkan laifukan kuma na wuyan shahida ita ta haifar da komai,haka ya dinga sintiri yana zarya,gaba daya duniyar jinta yake sama ta koma qasa. Da qyar da sudin goshi ya samu bacci yayi awon gaba dashi. Cikin watanni qalilan yaji gaba daya rayuwar ta juya masa baya,baya jin dadin komai,komai ya daina burgeshi,komai kuma ya tsaya masa cak,duk yadda yayi qoqarin moving forward ga aje komai hakan ya gagareshi,dalili na farko da yasa ya tattara dukkan abunda ya danganci shahida wanda idan ya ganshi zai iya tuna mishi da ita ya killace a muhalli daya,duk yadda yaso ga qonasu ko zubarwa hakanan ya kasa,abu na biyu ya aje aikin kamfanin da yake,domin kuwa duk sanda zai tafin saiya tuna mishi da ita,abinda sam ko kusa ko alama baida buqatarsa. Ta bangaren shahida kuwa sanda ta farka kalamansa ne abu na farko da suka soma dawo mata aka,ji ta dinga yi kaman zatayi hauka,ta ina zata iya rayuwar da babu anwar,yadda ta koma din ya sake daga hankalin abba da umma,yayin da tarin damuwa da nadamar abinda suka aikata ya sanya ciwo ya shigi abban,ya dinga fama dashi shi kadai yana cinsa kadan kadan. Abubuwa sai suka taru suka yiwa umman yawa,ga shahida har yau bata gane kanta,ga abbansu ciwo nason kayar dashi,sannu sannu lamuran suka ci gaba da kwabe mata da tafi mata a haka,har zuwa rana mafi muni da tashin hankali a garesu,ranar da ciwo ya yiwa abbansu shahidan farat daya aka tadda gawarsa cikin daki,fadin irin tashin hankalin da suka tsinci kansu ma bata baki ne,shahida kam tunda ta suma bata farfado ba sai datayi kwana biyar,wata iriyar dakiya ta dinga shiganta,ta yadda tabbas wani tashin hankalin baida misali,yadda take jin kanta da rayuwarta ta zama wata mara gane komai,zaqi ko d'aci,baqinciki ko farinciki,murmushi ko kuka,ta koma kamar mutum mutumi,tana jin tamkar ita ta kashe mahaifinta,tana jin alhakin mutuwarsa na bisa wuyanta,abinda ta aikata ba shakka shi ya kashe mata mahaifi,awannan halin anty zubaida ta cimmasu,don dukkan abinda ya farun ya faru ne basa qasar ita da uncle hisham. Kuka umma ta zauna tayi sosai a gabanta,tana fatan ta samu wasu shawarwarin da zasu kawo silar warwarewar matsalarta,bata boyewa anty zubaidan komai ba,labarin dukkan abinda ya biyo bayan yayi masifar girgizata,tana qaunat shahida har cikin ranta,tasan kuma Allah ne ya sallada wannan qaunar a tsakaninsu "Ba shakka kun tafka kura kurai arayuwarku duk da cewa shi tashi ta riga data wuce kaman yadda kika shaidan yabar wasiyyar neman afuwa a gareku gaba daya saidai muyita masa addu'ar samun dacewa,cece kuce ko fada gaban 'ya'ya babu abinda baya haifarwa ku kunga irin naku sakamakon dayazo dashi,daga ciki yana haifar da qiyayyar uwa kota uba,saboda kan yara zai rarrabu,kowa da wanda yake goyawa baya,daga haka zakiga an samu jam'iyyu daban daban,wanda kowanne yaja tinga ne yana taya gwaninsa nashi fadan,walau yana taya uwa ko uba,wannan sai yasa hatta a tsakaninsu 'yan uwan junan ma basa jituwa saboda wani baya ra'ayin bangaren da wani yake,bugu da qari idan da namiji gareku kai uba kana koya mishi ko ya tara iyali haka zai mu'amalanci iyalinsa?,ke uwa kuma kin koyawa diyarki haka akewa miji,illoli ne masu tarin yawa da qalubake kala daban daban,yanzun kunyi silar jefa diyarku ga tafarkin shaye shaye sabida tashin hankalin da take shiga sanda kuke yaqar juna harta gwammace ta zama ko yaushe out of sense yadda ba zatasan meke faruwa cikin ahalinta ba..."dan shuru anty zubaida tayi abun na mata ciwo "Yanzu bazanyi kaffara ba cewa kun korarwa diyarku manemi...saboda halin data fada ya isa kunnenshi...wala'alla abaya yana mata kallon managarciya yanzu ya sameta kan wannan turbar,kowanne namiji burinsa shine zabawa yaransa uwa ta gari kun bata wannan kyakkyawar shaidar daga kan shahida...inajin ciwo...inajin ciwon abinda ya samu shahida...amma nayi alqawari bazan bar rayuwarta ta gurgunta ba" daga haka ta miqe zuwa dakin shahida cikin bacin rai amma kafin ta shiga sai tayi qoqarin dai daita yanayinta sannan ta daga labulen a hankali ta saka kai cikin dakin da babu kowa ciki sai shahidan qwal ita kadai.*Zafafa biyar na kudi ne,idan kika gani don GIRMAN ALLAH karki sharing,ga mai buqata ki tuntubi wannan numbers din* 07067124863 *ko kuma* 09032345899https://www.youtube.com/channel/UC4kJO342hmb_Pd2luKHBjFA/videos *Alqawarin Allah* 1️⃣6️⃣ Daga kai tayi ta dubi anty zubaidan maimakon yadda ta saba yi mata a baya duk sanda ta ganta,takan tashu cikin farinciki tana mata sannu da zuwa dama tambayarta yaushe ta iso,hadi da tambayarta su faruqu,a nutse anty zubaida itama take qare mata kallo bayan ta zauna dab da ita,cikin mintina qalilan ta gama karantarta "Shahida" ta soma kiran sunanta a sanyaye,sake tada kai tayi ta dubeta saita sake saukewa,shawarar da zuciyarta ta bata tabbas itace mafita,dole ne saita fara tayar mata da mikin dake zuciyarta don da ala zuciyarta ta riga data daskare,dab take da rasa feelings,dole ta sata tayi kuka ta rage radadin da yake damun zuciyarta wannan shine hanya daya na farkar da zuciyar tata,dole ta sakata da kan kanta ta nuna akwai ciwo a zuciyarta wanda ta wannan hanyar ne kawai zata dawo da feelings da emotion dinta na fushi,sannan asan yadda gyara zai iya yiwuwa,tana son maida zuciyarta ne matacciya idan ba'ayi gaggawar gyarawa al'amarin ba "Shahida!" Ta kirata wannan karon da mugun tsawar data taba zuciyar shahidan,ta kuma sanyata dago kai tana duban anty zubaida gami da zuba mata idanu,yadda ta kafeta da idanu shi ya sanya itama tsaiwa tana kallonta "Shahida bansan ke shashasha bace,ban kuma san ke wawiya bace sai yau,ban raina wayonki ba sai yau,ashe ke banza ce?!" Shuru tayi kaman wata sokuwa tana duban anty zubaida,qwaqwalwarta nason tariyo mata meta aikata haka?,ganin yanayinta ya baiwa anty zubaida qwarin gwiwa "Shahida....saboda namiji kikeson maida rayuwarki haka?,saboda wani da dacan baki sanshi ba?saboda wani daya nuna bai damu da rayuwarki ba?,wace iriyar shashasha ce ke wadda batasan ciwon kanta ba,shi din banza?...waye shi?,kina da 'yan uwa,kina da mahaifiya...mahaifinki ya rasu,waishin shi da mahaifinki wanne ne yafi miki muhimmanci,kin rasa mahaifinki ma ya tafi kuma har abada,kun rabu kenan da wanda yayi silar kawoki duniya,inaga wanda ya tsinceki rana tsaka da girmanki,shahida!....kisan me kikeyi,ki shiga taitayinki!" A hankali ta soma girgiza kanta,yayin da hawaye ya cika idanunta,zuciyarta ta soma motsawa,mikin dake danqare ciki ya tashi,kuka ta saka mai sauti qwarai wanda hatta mutumin dake tsakar gida zai iya jiyo gunjinta,sai anty zubaidan ta matso da ita jikinta,ba musu ta kwantar da kanta saman cinyar anty zubaidan taci gaba da gursheqen kukanta,bata ce mata komai ba hakanan bata hanata ba,shuru tayi tana sauraron yadda kukan nata yake fita,ta sani duk sanda hawaye daya ya sauka yana sauka ne da wani radadi daga cikin radadin dake danqare cikin zuciyarta,hannu anty zubaida ta dora saman kan shahidan ta dinga shafawa a hankali a hankali tana tayata jin radadin. Aqalla sun shafe awa guda cur a haka,harsai da kukan ya soma sassauta ta soma rage sauti ya koma sai hawaye,mintina talatin ta sake qara mata zuwa sannan hawayen ya sake raguwa "Me ya faru shahida?,garin yaya haka ta kasance?" Bata boyewa anty zubaida komai ba kanta na saman cinyarta ta warware mata dukkan yadda akayi ta soma shan wani abu da niyyar rage baqinciki da bacin ran dake damunta,sannan ta zarce da rabuwarta da anwar sannan ta dora da cewa "Baqinciki na shi ya kashe abbana anty,shaye shaye yabarmin tabon da har na mutu dashi zan mutu,na kashe abbana da takaicina!" wanda hakan ya sake bude sabon shafin kukanta,kai anty zubaida take girgizawa "Kuskurenki na farki shahida shine da kika saki Allah,kika manta da cewa babu wani babban abu dake yaye qunci da baqincikin a zuciyar bawa ya samu nutsuwa da kwanciyar hankali irin kusanta kai da Allah,babu wani abu da zai kawo miki farinciki da walwala irin karatun qur'ani,shan wani abu a wajen dan adam domin gusar da baqinciki bacin rai ko kuma damuwa bashi da wani tasiri a gareshi,baya haifarwa da bawa komai face sake sanyashi cikin damuwar,baya yaye damuwa ta har abada face ya sake sanyaka cikin wasu sabbin matsalolin,ya haifar maka da ciwuka masu kai d'an adam ga kushewa,Daga kai tayi ta dubi anty zubaidan maimakon yadda ta saba yi mata a baya duk sanda ta ganta,takan tashu cikin farinciki tana mata sannu da zuwa dama tambayarta yaushe ta iso,hadi da tambayarta su faruqu,a nutse anty zubaida itama take qare mata kallo bayan ta zauna dab da ita,cikin mintina qalilan ta gama karantarta "Shahida" ta soma kiran sunanta a sanyaye,sake tada kai tayi ta dubeta saita sake saukewa,shawarar da zuciyarta ta bata tabbas itace mafita,dole ne saita fara tayar mata da mikin dake zuciyarta don da ala zuciyarta ta riga data daskare,dab take da rasa feelings,dole ta sata tayi kuka ta rage radadin da yake damun zuciyarta wannan shine hanya daya na farkar da zuciyar tata,dole ta sakata da kan kanta ta nuna akwai ciwo a zuciyarta wanda ta wannan hanyar ne kawai zata dawo da feelings da emotion dinta na fushi,sannan asan yadda gyara zai iya yiwuwa,tana son maida zuciyarta ne matacciya idan ba'ayi gaggawar gyarawa al'amarin ba "Shahida!" Ta kirata wannan karon da mugun tsawar data taba zuciyar shahidan,ta kuma sanyata dago kai tana duban anty zubaida gami da zuba mata idanu,yadda ta kafeta da idanu shi ya sanya itama tsaiwa tana kallonta "Shahida bansan ke shashasha bace,ban kuma san ke wawiya bace sai yau,ban raina wayonki ba sai yau,ashe ke banza ce?!" Shuru tayi kaman wata sokuwa tana duban anty zubaida,qwaqwalwarta nason tariyo mata meta aikata haka?,ganin yanayinta ya baiwa anty zubaida qwarin gwiwa "Shahida....saboda namiji kikeson maida rayuwarki haka?,saboda wani da dacan baki sanshi ba?saboda wani daya nuna bai damu da rayuwarki ba?,wace iriyar shashasha ce ke wadda batasan ciwon kanta ba,shi din banza?...waye shi?,kina da 'yan uwa,kina da mahaifiya...mahaifinki ya rasu,waishin shi da mahaifinki wanne ne yafi miki muhimmanci,kin rasa mahaifinki ma ya tafi kuma har abada,kun rabu kenan da wanda yayi silar kawoki duniya,inaga wanda ya tsinceki rana tsaka da girmanki,shahida!....kisan me kikeyi,ki shiga taitayinki!" A hankali ta soma girgiza kanta,yayin da hawaye ya cika idanunta,zuciyarta ta soma motsawa,mikin dake danqare ciki ya tashi,kuka ta saka mai sauti qwarai wanda hatta mutumin dake tsakar gida zai iya jiyo gunjinta,sai anty zubaidan ta matso da ita jikinta,ba musu ta kwantar da kanta saman cinyar anty zubaidan taci gaba da gursheqen kukanta,bata ce mata komai ba hakanan bata hanata ba,shuru tayi tana sauraron yadda kukan nata yake fita,ta sani duk sanda hawaye daya ya sauka yana sauka ne da wani radadi daga cikin radadin dake danqare cikin zuciyarta,hannu anty zubaida ta dora saman kan shahidan ta dinga shafawa a hankali a hankali tana tayata jin radadin. Aqalla sun shafe awa guda cur a haka,harsai da kukan ya soma sassauta ta soma rage sauti ya koma sai hawaye,mintina talatin ta sake qara mata zuwa sannan hawayen ya sake raguwa "Me ya faru shahida?,garin yaya haka ta kasance?" Bata boyewa anty zubaida komai ba kanta na saman cinyarta ta warware mata dukkan yadda akayi ta soma shan wani abu da niyyar rage baqinciki da bacin ran dake damunta,sannan ta zarce da rabuwarta da anwar sannan ta dora da cewa "Baqinciki na shi ya kashe abbana anty,shaye shaye yabarmin tabon da har na mutu dashi zan mutu,na kashe abbana da takaicina!" wanda hakan ya sake bude sabon shafin kukanta,kai anty zubaida take girgizawa "Kuskurenki na farki shahida shine da kika saki Allah,kika manta da cewa babu wani babban abu dake yaye qunci da baqincikin a zuciyar bawa ya samu nutsuwa da kwanciyar hankali irin kusanta kai da Allah,babu wani abu da zai kawo miki farinciki da walwala irin karatun qur'ani,shan wani abu a wajen dan adam domin gusar da baqinciki bacin rai ko kuma damuwa bashi da wani tasiri a gareshi,baya haifarwa da bawa komai face sake sanyashi cikin damuwar,baya yaye damuwa ta har abada face ya sake sanyaka cikin wasu sabbin matsalolin,ya haifar maka da ciwuka masu kai d'an adam ga kushewa,Kana daukan cuta ne kana laftawa kanka,kana kashe kanka da kanka,Allah S W T da kansa yace kada ku kashe kawunanku,shan abun maye ba komai bane face kashe kai,don baka da maraba da mutumin daya dauki makami ya dabawa kansa,domin kuwa shaye shaye ba cutar da baya haifarwa,lalacewar qoda,lalacewar hanta,ciwon cancer,ciwon zuciya,yana nakasta hunhu,yana kuma lalata qwaqwalwa wanda hakan yake jagoranci zuwa ga haukacewa,dukka daya daga cikin wannan cututtuka idan aka bar mutum dasu sun isheshi azabar nan duniya,sun ishi mai hankali gujewa abun maye"ajiyar zuciya anty zubaida ta saki sannan ta dora "A duniyance shaye shaye bai haifar maka da komai sai zubewar qima da mutunci,mummunar dabi'a ce dako wanda yake yinta yake boyewa,kuma baiso a sani,dabi'ace dakan gusar da imani da hasken fuska,dabi'ace dake barin tabo cikin rayuwar wanda ya taba aikatata,sannan ba'a sanyaka cikin sahun managarta mutane ko mutane masu dattako har abada,saboda kowa kallon mahaukaci yake maka,sannan a addinance manzan rahama yace dukkan wani abu da zai saka maye haramunne,musulunci yafimu sanin cewa kayan maye abubuwane masu cutarwa ga lafiyarmu,shi kuma ko yaushe tattalin lafiyarmu yake,sannan addini ne dake kare mutunci da martabar dan adam,bambancin mutum da dabba hankali,kinsha abinda zai gusar da hankalin me sunanki kenan a wannan lokacin?,dalili kenan daya sanya aka haramta mana su,duk sanda kake cikin maye babu kunya tattare dakai,hakan na nufin ba alkhairi a tare dakai kenan,saboda ma'aiki ya gaya mana duk inda kaga kunya akwai alkhairi a wajen,sanda kuma babu kunya tare dakai zaka iya aikata dukkan komai ciki kuwa harda kisan kai!,tunda kike sha din damuwarki ta taba tafiya gaba daya?" Kai shahida ta girgaza,don da zarar ta farka dukkan wata damuwa take dawo mata sabuwa fil,harma tafi ta dazun "Zaki iya tuna sau nawa kikayi loosing sallah saboda tazo ta riskeki kina cikin bacci sanadin abinda kika sha?"shuru shahidan tayi tana tunani hawaye masu dumi nabin fuskarta har cikin kunnenta,kome take komai runtsi sallah bata taba wuceta ba sai a wannan karon,sai data shiga wannan mugunyar dabi'ar "Kina tunanin hujjace da zaki gayawa Allah ranar gobe qiyama na dalilin jinkirta sallahrki?" Ta jefo mata tambayar data sanya shahida fidda sabuwar qwalla,dana sani da nadama mara misaltuwa na sake shigarta,kaico da rayuwarta da haduwarta da fiddausi "Kina da yaqinin sanda kika farka kika ramata Allah zai amsa ya saka miki a mizanin ayyukanki wajen sallahrki na lokacin bazai tashi blank ba?,bayan kina baccin sabo ne bana ibada ba?" Sabon kuka shahidan ta sake saki,tsoron Allah na sake kamata,tana jin kaman yanzu Allah zai amshi rayuwarta,me ta tanada?,wacce amsa zata bayar?. "Allah yana karban tuban bayinsa ne matuqar ran bawa baizo gargara ba,sannan kuma rana bata fito daga mafadarta ba,bai halatta bawa ya jinkirta tuba kan wani aikin sabo da yake ba,yace har sai Allah ya shiryeshi,don haka yana daga cikin alamar 'yanwuta,kuma alamace dake nuna bawa ya tabe,sannan alamace ta toshewar basira,anaso koda yaushe bawa ya dinga gaggauta tuba saboda baisan randa ajalinsa zai riskeshi ba" "Astagfirullah...astagfirullah" shahida ta dinga maimaitawa a fili har na tsahon wani lokaci,sai data fuskanci ta samu nutsuwa sannnan ta dagota suna kallon juna "Shahida...maganar anwar....." wani abu mai ciwo taji ya tokareta,abinda yayi mata ya dinga yawo cikin idanunta kamar tariyar film,da sauri ta katsi antyn "Anty...don Allah ki daina kiramin sunanshi....don Allah anty ki dainamin maganarsa,yanzu bashi a gabana,yadda ya buqaci na barshi na barshi har abada...yadda ya nuna bai buqatata saboda wani kuskure dana aikata nima bana buqatarsa har abada" murmushi anty zubaida tayi tana karantar yanayinta da yadda maganar ke fita daga zuciyarta zuwa harshenta,kai ta girgiza tasan cewa wani bacin raine dake qonata tun daga cikin jiki zuwa zuciyarta,kowa ya shaida irin qauna da soyayya dake tsakanin shahida da anwar,koda baka sansu ba labarinsu ba shakka ya iskeka,bata da tabbaci ko yaqinin kan abunda shahidan ke furtawa saboda ta riga ta sani cewa soyayya ba qarya bace,ba qaramin dalili ne yake da qarfi da isar da zai karyata ba,karyawa ta har abada,karayar da ba zata doru ba "Duk wannan lafazin shahida ban buqatar jinsa daga bakinki,ba'a ciwa soyayya alwashi kuma ba'a cika mata baki....kiyi addu'a kawai a yanzun,ki tattara hankalinki waje guda,ki karbi qaddararki,kiyi moving forward,stop worrying about what u have to loose,and start focusing on what u have to gain,har yanzu yarinyace ke,shekarunki nawa?,me kika soma gani cikin rayuwa?,akwai abubuwa daya kamata ace kinyi achieving a rayuwarki,karki bari wani abu guda daya ya tsaidaki waje guda,ya ruguza dukkan wani kyakkyawan tanadi daya kamata kiwa rayuwarki,wannan abun daya faru ba komai bane cikin rayuwarki,daya daga cikin challanges kenan na rayuwa,ki godewa Allah kina da chance,kina da dama,kamar ya baki wata dama ne naci gaba da gina sabuwar duka rayuwar da kikaso kikaga dama,just choose tobe strong rather than letting it drown you" wadan nan sune ire iren kalaman da anty zubaida ta dinga amfani dasu tsahon shekara biyar don dawo da rayuwar shahida cikin nutsuwarta. Cikin qaramin lokaci taji anwar din ya wanke mata a rai tas,ya sire mata,ya fice mata daga ruhinta,taji zata iya rayuwa babu shi,taji abune mai sauqi hakan,saidai baizo mata da sauqi ba yadda ta tsammata,ta share darare da yawa bata samu bacci ba,ta ga wuninnika da darare masu tsaho da tsauri cikin rayuwarta a wannan lokaci,ta cika bangon dakinta da shafukan littafanta ta kalaman qarfafa kai da qarfafa gwiwa akaran kanta,ta siya littafi tayi rubutu mai tsaho da yawa kan rayuwarta har kawo bigiren da yau take kai,ta tattara duk wani abu da zai iya tuna mata da anwar ta ajesu waje daya,ta shiga tsara yadda rayuwarta zata kasance nan gaba,tun saga lokacin ko masoya ta gani sai taji tana tausayinsu,musamman mace idan taga ta zura jiki da yawa. Bayan umma ta fita takaba uncle hisham shi ya karbi ragamar daidaita musu duka al'amuran gidan,sannan suka yanke shawara dashi shahida zata koma hannun anty zubaidan,tunda har yanzu bata gama daidaita ba,saidai cikin kaso dari an samu sauyi na kaso shida,rabata da unguwar da duk wani tsohon memory dinta zai sake taimakawa wajen saita tunaninta,da wannan suka dauke shahidan ta koma wajensu. Makarantu daban daban anty zubaida ta sakata wanda zata qaru ta fanni da dama,wasu na koyon harshen larabci wani na koyon turanci bawai don bata iya ba,a'ah saidon ta maidata busy sosai wanda hakan zai sanya bata da lokacin zama ma ta tuna wani abu mara dadi daya faru da ita a baya,tayi hakanne kuma kafin wata shekarar ta zagayo su nema nata admission saboda wannan shekarar ta qwace mata. Rayuwarta ta soma samun sauye sauye,kullum kwanan duniya saitayi kukan dabi'ar shaye shaye data ta taba tsintar kanta a ciki,kullum sai tayi nadamar sanin fiddausi a rayuwarta,sai tayi nadamar sakin jiki ga duk qawar data kutso rayuwarki sama taka,abune mak wahala da idan ka sake ka jefa kanka da wuya ya fice daga rayuwarka salin alin ba tare daya haifar maka da nadama da danasani ba,bai kuma bar maka qatoton tabo ko baqin fenti a rayuwarka ba,ta godewa Allah da yayi gaggawar fiddata tun batayi nisan da ba zata ji kira ba kamat yadda tagani ta kuma ji labari da yawa akan wasu,wanda ta shiga bincike ne akai bayan ita Allah ya tsamota,gefe daya kuwa yaqi take tuquru da kanta game da lamarin anwar,wata irin tsana da bata taba tunanin tanawa wani dan adam ba ita ke taso mata,duk wani abu da yayi mata da yadda ya dubu qwayar idanunta ya gaya mata magana,fiddota daga gidanshi da sauransu,uwa uba hotunan yarinyar da yake gaya mata ya sake ya sauyata a madadinta,kullum qoqarin goge duk wani tabo ko abun tunawa daya barwa rayuwarta take,tanason ta nuna masa ta kuma nunawa duniya she can survive without him,tana son watan watarana yaga cewa shi din ba komai bane da ba zata iya rayuwa babushi ba. *Cikin rashin kunya murjewar ido dajin wannan karon dai dai take da kowa,zata iya karawa da kowa,a shirya take ta rabu da kowa saboda shi,bata jin akwai abinda ya isa yayi mata hijabi tsakaninta dashi,koda waye,koda mahaifiyarta data haifeta,koda mahaifinta da yayi silar zuwanta duniya* *"Allah ya isa ban yafe ba duk wanda yayi silar rabani da Zamab,ko wayeshi bazan taba yafe masa ba wallahi, dan an haifeka ai ba halittarka akayi ba, kai ma babu wanda yayi maka auren dole, haka a addinance babu inda Allah yace ayiwa mace auren dole"* *kalaman da suka fito kenan kai tsaye daga bakin Basmah zuwa ga mahaifinta Ya Mu'allim tana dubanshi kai tsaye ba kunya ko rusunawa* _SAKI RESHE KENAN littafin da zaizo muku daga jarumarku haziqar marubuciya HAUWA A USMAN JIDDERH_ *WANNAN WACCE IRIYAR DIYACE HAKA?,ME YAKE FARUWA ME KUMA YA FARU?,DON JIN CI GABAN WANNAN LABARI DAKE QUNSHE DA BADAQALA,SAKIN RESHE DA SAGEGEDUWA ZAKA BIYA NAIRA 300 KACAL TA WANNAN HANYA,BA TARE DA BATA LOKACI BA ZA'A SADAKA DA WAJEN DA ZAKA SAMU NAKA* Hauwa Auwal Usman GT bank 015325259310 *saiki tura shaidar biya zuwa ga wannan number* 07020489340 *katin waya kuma xaku tura 300 ta watsapp ta wannan number* 07020489340 _kar ayi babu ke,maza garzaya ki nemi naki_🏃🏾‍♀️🏃🏾‍♀️🏃🏾‍♀️🏃🏾‍♀️🏃🏾‍♀️ https://www.youtube.com/channel/UC4kJO342hmb_Pd2luKHBjFA/videos *zafafa biyar na kudi ne,idan kika gani don GIRMAN ALLAH karkiyi sharing,idan kina da buqata ki tuntubi wadan nan numbers din* 07067124863 *ko kuma* 09032345899 *Alqawarin Allah* 1️⃣7️⃣ Daga gefan anwar kuwa yaso barin garin ne gaba daya,saboda yadda garin yayi kishi zafi,yaji ya tsani komai,bashi buqatar duk wani abu daya sani,yana buqatar baqon muhalli,anty husaina ce ta kafe kai da fata kan bata yarda ba,ganin yadda ya dage kan son tafiya din ta sakar masa kuka,wanda ya sanya dole ya haqura shima yaci gaba da zaman. A wannan lokacin da nafisa taga dama tazo mata,taso ta gabatarwa da anwar kanta ne gaba gadi,taso anwar ya dawo cikin gidansu da zama qarqashin abbanta,ya bashi gida mota da kuma jari suyi aurensu,saidai yadda labari da halayyar anwar tazo mata ta tabbatar da cewa aikata hakan babban kuskure ne da zai janyo kwabarta tayi ruwa,wanda daga qarshe suka gama shawara da mima kan yadda zasuyi. Alhaji abba kabara mahaifin nafisa mutum ne mai yawan taimako da samawa matasa ayyukan yi,yana da kamfanoni hakanan yana da shagunan da yake sanya matasa a ciki,duk matashin da yayu shekara guda riqe da amanar shagon ba tare da an taba kuka dashi ba alhj abba yakanyi masa kyakkyawar sallama ta hanyar bashi jari mai tsoka,wani lokaci ma bai duba da abunda aka samu a shekarar,zamanka a shagon iya karantarshi da amanarka kawai ya nuna idan ya baka jarin ba zasu salwanta ba,wasunsu kuma yakan daukesu ne ya kaisu kamfaninshi,musamman masu takardun makaranta,dalili kenan sanya sanya ta samu abban nata "Uhmm...ya akayi nafi?" Cikin nuna yanayi najin kunya tadan sadda kanta "Abba dama...dama" sai tayi shuru "Dama me?" Ya tambayeta yana sauke medical glass dinsa "Akwai wani marayan matashi ne,abba yana da amana da duk halayen qwarai,ya kammala karatunsa baida aiki,abba yana shan wuyar rayuwa sanadiyyar haka,idan na masa magana abba da kaina bazai karbi duk wani abu ba,amma idan kaine da kanka abba zaifi amsar duk wani taimako" shuru ya danyi yana nazarinta "A ina ke kika sanshi?" "Abba...a unguwarsu qawata yake,ita take bani labarinsa,na tabbatar zaka yaba da halayenshi hakanan zaka tabbatar daya cancanci taimako" kai yake gyadawa sannan yace "Ba damuwa,ki turamin adress dinshi,zamu fidda sanarwar daukan ma'aikata a kamfanina zansa a duba takardunshi sosai" "To Abba Allah ya qara budi" amin ya fadi yana daukar jaridarsa yaci gaba da dubawa,yayin da nafisan ta fita cikin farinciki da walwala. Randa aka kira anwar aka shaida masa sunan kamfanin da sukeso duba takardunsa yayi mamaki qwarai,don iya yawon neman aikinsa bai taba bi koda ta titin da kamfanin yake ba,don bai taba sama ranshi cewa zasu daukeshi aiki ba. Qarfe taran safe na ranar da zaije kamfanin ya gama shirinsa ya fito yana kulle gidan yaga mota tsaye a qofar gidan,horn aka danna mishi kana aka jawo motar zuwa gabanshi "Daga kamfanin alhj abba ne akace muzo mu daukeka" ya kalli motar sosai yaga tambarin kamfani jiki,hakan ya sanya ba musu ya bishi suka shiga. Sam bai kula da itaba ashe tana zaune a bayan,sai daya waiwaya suka hada idanu ta sakar masa murmushi,sam bai ganeta ba,ita ta soma gaidashi sannan ta gabatar mishi da kanta a matsayin diyar alhj abba,mamaki day ayayi na wanne matsayine dashi da har za'azo har qofar gida a daukeshi cikin motar kamfani shi da za'a yiwa alfarmar bashi aiki,bashi da amsar wannan saboda haka shuru shi yafi masa,yana jin nafisan na bashi labarin abubuwan da suka shafi kamfanin kamar ma an daukeshi aikin ne,shidai nashi kunne ne,don yanzu baya ga anty husaina baya jin dadin hira da kowacce diya mace,hasalima bayaso su rabeshi. Bisa jagoranci da shigewar gaban nafisa ya gama komai cikin kamfanin,aka kuma bashi babban gurbi wanda ko a mafarki bai taba tsammata ba,koda wasa bata nuna ita ta roqa masa wannan alfarmar ba saboda tasan ba wani abu bane cikin aikinsa yaqi amsar aikin gaba daya. Lokaci kadan da fara aikinsa alhj abba ya tabbatar da duk maganar da nafisa ta fadi a kansa,yana da gaskiya yana da amana,hakanan yana da aiki tuquru,baya taba saba lokacin zuwa kamfani hakanan lokacin tashi,gwara ma lokacin tashin idan akwai wani aikin da kamfani zaici gaba yakan sarayar da lokacin nashi ya gabatar dashi,dalilin kenan daya sanya alhj abba da kanshi ya danqawa anwar qaramar motar hawa mai azabar kyau da tsada irin wadda bai kawo zai mallaketa ba nan kusa,sannan ya nemi daya dawo cikin gidanshi da zama,wanna ne kuma ya bawa alhjin haquri,saboda yadda nafisa ke shishshige masa sam baya masa dadi,yana karanta mata ne da daga mata qafa kawai saboda girma da darajar mahaifinta,motat ta sauqaqa masa sauran ayyuka da zuwanshi ma kamfani gaba daya,hakanan ya dinga barin motar a wani garage dake farkon layinsu wanda masu abun hawan da basu da muhallin ajesu suke ajewa a nan su biya wani abu ladan ajiyan. A sannan rayuwa ta soma mishi kyau,koma ya soma canzawa,kama daga sutura cima da sauransu,anty husaina ma kanta canji ya soma zuwa mata,a wannan lokacinne nafisa ta kasa shanye halin ko in kula da anwar ke nuna mata,duk wata alama da ake nunawa mutum ya gane ana sonshi ta nuna mishi amma a banza wai an mintsini kakkausa,hakan ya sanya tayi qundunbala taci alwashin sanar mishi wata rana da abbanta ya gayyatoshi cin abincin dare gidan. Abban da mamanta sun kammala sun bar wajen saura nafisan da tunda taji labarin zuwanshi ta kasa zaune ta kasa tsaye,ta tsara kwalliya ta a mutu,sannan ta aro duk wani salo da tasan zai iya tafiya da d'a namiji,saidai kuma har ya kusa gamawa bataga ya nuna wani abu game da ita ya burgeshi ba,hakan ya sanya tayi gyaran murya "Anwar....idan ba zaka damu ba don Allah...ina da magana dakai" "Uhmm...babu damuwa ina jinki" shuru tayi na wasu mintuna sannan ta daga kanta tana dubanshi sosai "Tun ranar da Allah yasa na soma ganinka anwar Allah ya dasa min qaunarka...na rasa ta yadda zan furta maka bansa ya zan gaya maka ka gane ba,wani irin soyayyarka nakejin har cikin jinina,anwar ina fata da roqon ka soni koda rabin yadda nake sonka ne" tunda ta soma maganar ya zuba mata idanu yana jin wani abu da baisan meye ba yana taso masa,ko kusa ko alama baison yaji wannan kalmar daga bakin kowacce diya mace gani yake duk yaudara ce,ba gaskiya bane qarya ce,yatsunsa ya dinga bugawa a saman teburin kadan kadan har ita sai data tsargu da kallon da yake matan ta soma kame kamen abunyi,da qyar ya iya hada abun fada "Nafisa" ya kira sunanta a kausashe,daga kanta tayi ta dubeshi sosai jin yadda sunan nata ya fito bilhaqqi daga zuciyarsa "Inason daga yau wannan tunanin yabar qwaqwalwarki,wannan kalmar ta fita daga bakinki,ina ganin qimarki data mahaifanki,kada ki jawo abinda bazai mana kyau da dadi ba ni dake gaba daya"daga haka ya miqe ya dauki maqullan motarshi ya wuce ya barta a wajen,kuka ta saki sosai,bata taba tunanin lamarin zaizo da haka ba,tayi tsammanin yadda yake nuna kulawa a gareta kaman qanwarshi zata samu soyayyarshi ta sauqi,haka ta miqe ta shiga bedroom dinta cikin tashin hankali ta dauki wayarta ta kira mima ta zayyane mata komai "Nafisa kenan,dama ke kina tunanin samun kanshi da wuri ne,to kinyi kuskure idan ma zaki zage damtse kiyi kaman kinayi to" ta jima tana juya zantukan miman a kwanyarta,inda daga qarshe ta zage damtsen kaman yadda ta bata shawara,saidai gogan ko a jikinsa wai an mintsini kakkausa,yadda ya saba mu'amala da ita haka yake babu abinda ya canza,naci kuwa babu kalar wanda batayi masa ba,inda daga qarshe ma ta matsawa dadynta ya bata gurbin aiki a kamfanin,ya bata din saidai tace matsayin secretary din anwar takeso,babu musu ya bata kasancewarta diya mace diya tilo dake gareshi,anwar din bashi da bakin cewa don me?,haka ya amsheta saidai kusan ba wani aikin kirki take ba,cikin qaramin lokaci kowa ya fahimci yadda nafisan ke bala'in so da qaunar anwar din,wannan labarin shi yakai har kunnen umminta,take ta saka abban nafisan ya karbe gurbin aikin daya bata aka maida shi da wani,fada ta dinga ma nafisan kan wautar da take nunawa na nunawa namiji irin wannan zallar son bayan shi baisan tana yi ba,kuka ta dinga duk da ta bata tausayi amma sam bata nuna ba,don tana sone idan anwar zasiso nafisan ya sota don karan kanshi,ya kuma sota da datajarta ba tare data zubda qimartata ba wajen neman soyayyarshi ba a matsayinta na diya mace. Wannan karbe aikin ya bata ran nafisa matuqa,tana ganin kaman ummin nata bata sonta ne,banda haka meye aibu a nunuwa anwar soyayya da take,hakan ya sanya ta sake maida akalar shawararta dai wajen mima,inda ta bata wasu shawarwari da take ganin anwar din bai isa ya tsallakesu ba dole ya furta mata soyayya da kuma kula koda ba haka bane har zuciyarshi. Cikin sa'a kuwa a lokacin aka maka wani gagrumin ruwan sama daya sanya gidan anwar rushewa,dama yana dab da soma aikinsa ne,dalili kenan daya sanya alhj abba ya sake nemanshi ya dawo gidanshi da zama har zuwa sanda zai kammala gyara nashin,tofa,abun nema ya samu wajen nafisa,nan ta zage damtse ta shiga shigewa anwar din haiqan,har abunma yana wuce gona da iri,don takan iya zamanta bangarenshi da sunan tayashi hira har tara ko goma na dare,duk wadda kuwa akayi katari cikin yammatan dake damunshi da kira ta kira nafisan ta samu nasarar dauka hara zata dauka ranar suyi kace kace da sunan matarshi ce,hakan ya sanya ya qaranta dawowa gida da wuri,ya qirqirarma kanshi guraren zuwa saiya daida daici sanda tayi bacci,wani bin ya dace wani bin kuma ya taddata dai tana zaman jiranshi. Ganin abun yaqi ci yaqi cinyewa tamkar cin qwan makauniya yasanyata amfani da shawarar mima,inda ta kwanta ciwo sosai suka hada baki da wani likita aka kaita can,ya dubata ya kuma ce lallai tana cikin damuwa ne,kuma tilas a sama mata abinda takeso idan ba haka ba za'a iya rasata. Randa ta farfado daga suman qaryarta anwar na dakin shida alhj abba da mahaifiyar nafisan,a sannan yana gefan daya gadon da babu kowa a kai yana charting da wani abokin kasuwanci da suka fara shirin saka hannun jari shi da shi su tashi nasu kamfanin,sunanshi ta soma kira wanda yaja hankalin dukkaninsu,saiya daga kai yana dubanta bayan ya amsa,ta wani lumshe idanu kaman gaske tana kallonshi,nauyin idanun alhj abba da mahifiyarta ya sanyashi barin abinda yake ya taso zuwa kusa da ita,sai ummanta tabar kujerar da take kai wanda ke gaban gadon ta masa nuni daya zauna ba musu ya zauna. Ba kunya ta kama hannunshi cikin dabara ya zame,saita saki kukan qarya "Don Allah anwar kace kana sona kaji" mummunar faduwar gaba ce ta sameshi yayi shuru yana jin yadda qirjinsa ke bugawa "Ina sonki" yayi qundun balar fada saboda ganin yadda take kuka gaban iyayenta "Zaka aureni?" Ta sake jefa masa tambayar data kusan sa jininsa hawa a take,tanason daureshi ne wato da jijiyoyin jikinsa. *zafafa biyar na kudi ne,idan kika gani don GIRMAN ALLAH karki sharing,ga mai buqata saita tuntubi wadan nan numbers* 07067124863 *ko kuma* 09032345899 *kuyi subscribing youtube channel dina don samun damar ganin shirye shiryenmu,subscribe kyauta ne!*👇🏽👇🏽 https://www.youtube.com/channel/UC4kJO342hmb_Pd2luKHBjFA/videos *Alqawarin Allah* 1️⃣8️⃣ Kanshi yaji yayi masa nauyi kaman an dora masa dutse,kafin ya ankara nafisa ta saki kuka tana roqonshi,dukkansu ya tabbatar hankulansu da kunnuwansu na wajen,haka yake,don dukansu fata yace ya amince,don sun yarda da hankali da nutsuwar anwar,sun tabbatar idan ya auri diyarsu ta fada hannun dako bayan ransu basa kokwanto ko shakka,saidai ta bangarin mamanta magiyar da take ta taba ranta ta kuma bata takaici "Meye haka kikeyi ne?,baki da hankali?" Cewar mamarta data matso kusa da gadon a fusace,ta rasa meye matsalar diyartata,kullum kwanan duniya cikin dorata hanya da gyara mata kurakurenta take amma a banza wai an tsikari kakkausa,cikin sauri anwar ya dakatar da maman,ko mutuwa ma tana kunyar idanun mahaifi,hakanan kara da alkunya ma wani abu ne,kuma shi alkhairi danqo ne baya faduwa qasa banza,nafisa diyarsu ce kuma fadinma suna sonta bata baki ne,saidai su wasu irin mutane ne masu kunya kara da kawaici,wanda soyayyar dansu bata hanasu ganin gaskiya "Qyaleta mama" hakan shi ya tsaida hajiya ta koma da baya tana sauke numfashi,duban nafisan yayi sosai sannan yace "To kuma meye na kukan?,ya isa kiyi shuru kinga ba cikakkiyar lafiya ce dake ba" "Indai kanason shuru na saika yarda kanasona zaka aureni ya anwar" alhj abba ne ya soma takawa don barin dakin ganin rashin kunyar nafisan na qara gaba "Zan aureki in sha Allah ki shuru" ajiyar zuciya dukkansu suka sauke wanda su kansu basu san ta fito sarari ba saida suka hada ido da juna suka tabbatar anwar din yaji sai kuma sukaji kunya,hakan shi ya tabbatarwa da anwar suma zancan na ransu,basason tararsa ko tauyeshi ko tilastashi kan abinda bashi da niyya ko ra'ayi. Wannan abun daya faru sai ya zama kamar wani lasisi nafisa ta samu na nuwa anwar soyayya ko a gaban waye,wanda hakan ya sanya babu shiri ya qara qaimi wajen gyaran gidansa,don yana ganin matyqar yaci gaba da zama a gidansu akwai matsala,don nafisan kaman ta soma fitsare sawayenta,duk da yadda hajiya bilkisu ke taka mata burki amma sam bataji,hudubar mima gani take itace dai dai don itace dai dai da ra'ayinta. Ta dage sosai wajen farauto zuciyarsa,da yake Allah shike sanya soyayya cikin zukatan bayinsa duk irin kulawa da kyautatawar da take masa bai taba jin wani abu mai kama da qaunarta ba cikin zuciyarsa,yana mata kallon qanwa tana kuma da qima a idanunsa darajar mahaifanta da yadda suke sonshi. Shekara biyu cur rayuwar anwar ta sauya,kai baka ce shine wannan anwar din ba,kamanni yanayin rayuwa da komai nashi,saida zuciyar nan na nan,zuciyar dai itace babu wani abu daya sauyata,a sannan alhj abba ya shirya bikin yaye wasu daga ma'aikatansa wanda su suka buqaci haka don suci gashin kansu,ciki harda anwar wanda tun dacan dama bai sha'awar zama qarqashin wani,yafison duk wahala yaci gashin kansa,a lokacin da alhj abba ya yayesu ya danqawa kowanne kudin sallama,saidai kudin anwar yafi na kowa yawa,ya zauna da alhj abban ya gaya masa zai amsa ya qara cikin kudadensa,amma in sha Allahu zai dawo da dukka kudin da aka bashi,aljh abba yace sam wannan kudin kyautane kawai saboda bauta da wahalar da suka yiwa kamfani, a nutse anwar ya fahimtar dashi manufarsa,shidai yace yaje kawai ya kafa kanshi din. Komai na rayuwa wato yana da lokacinsa,hakanan rabon kwado bai hawa sama,anwar ya tsaya tsayin daka,babu dare ba rana,babu lokacin bacci bana hutu sai daya tabbatar ya kafu,ya fidda kudin alhj abba ya maida masa,shi kansa alhj abban yayi mamakin yadda anwar din yayi kafuwar da aqalla kayi shekara goma sha bakayi irinta ba,saidai yasan komai yassarewace ta ubangiji,shi kansa anwar yasan cewa qarfin addu'ar iyaye tsayawa kai da fata kan gaskiya da riqe Allah da yayi shi ya kaishi fa wannan matakin,tuni ya tamfatsawa anty usaina gida,saidai a sanda yace ta zabi unguwa saita zabi unguwarsu shahida,farkon layinsu wasu gidaje da suka tashi suka saida,daya tambayeta dalili tace ba ruwansa,ba yadda ya iya haka yayi mata yadda tace tana so,saidai har aka kammala ginin bai taba taka qafarshi unguwar ba,data koma kuma sai zuwan ya zame masa dan zani shima,sai daya sanya aka sake fasa qofa ta bayan layinsu yake shiga ta nan. Ganin lokaci yana ja anwar yaqi soma maganar aurensu babban burin daya rage mata a duniya yasa ta soma masa shagube,qwarai ya fahimta saidai har yanzu baiji nutsuwar zama da nafisa a matsayin matar aurensa ba,duk da ya sani tunda ya furta dole ya cika amma har yanzu zuciyarsa taqi karban hakan,abinda yaketa yaqi akai kenan,ita kuma tasan cewa iyayenta ba zasu taba yi masa batun ba,mutum daya ce nan duniya zata ce yayi ya zame masa dole yayi anty husaina,dalili kenan da yasa ta wanki qafa bisa shawarar mima taje mata da batun,wanda a yanzu haka akan qadamin da suke kai kenan yanzu haka(idan baku manta ba a baya kunji inda anty usainan ke masa maganar kar suji kunya kan nafisan). Ta bangaren shahida ma kwanaki watanni zuwa shekaru sun soma tafiya,tuni ta kammala degree dinta wanda ta samu gamasu da qananun shekarun da kowa ya kalleta sai yayi mamaki,hakanan ta dora da masters shima Allah ya taimaketa ta kammalashi cike da nasara mai tarin yawa,a sanda sakamakonta ya fito uncle hisham yaso ta amshi tayin lacturing da jami'o'i suka yi mata tace sam bata ra'ayi,ya tura takardunta kamfanoni da dama ta samu aiki daga wajensu nanma tace ba zatayi ba ciki harda kamfaninsu,ba yadda ya iya hakanan ya qyaleta. Sanda tazo masa da zancan koyarwa a *NOOR INTERNATIONAL* sai daya cire gilashinsa ya kalleta don ya tabbatar da wasa take koda gaske,hakanan taji kawai bata da burin daya wuce itama yaran talaka su amfana da karatu ilimi da baiwar da Allah ya bata,ba haka yaso ba sam,saboda tayi karatu kai kyai wanda ya dace ta tsaya ta moreshi tayi amfani dashi ta hanyar yin aiki a gurbi da kuma bigiren daya dace,hanatayi kai tsaye yace maida kai baya ne,ta nace ta dage wansa ya sanyashi dole ya amince,amma bisa wasu sharudan. Duk sanda suka mata wani abu da bai gamsheshi ba to ba shakka ta gama koyarwa a makatantar,kai tsaye ta amince don bata ga ma abinda zai gamota dasu ba bare wani abun ya faru,kan wannan sharadin ta soma koyarwa cikin makarantar,ta kuma samu karbuwa daga wajen dalibai har malamai,zama cikin makarantar kuma yayi mata,hakanan yana mata dadi qwarai. Wannan shine labarin taurarinmu guda biyu da abinda ya zama sanadiyyar rabuwarsu ba tare dakowannensu yasan cewa MAQARQASHIYA CE ba. 🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍 Zaman bitar rayuwarsu ita da anwar din data tsaya yi daren jiya ba qaramin taba zuciya ruhi da kuma gangar jikinta yayi ba,tayi kuka irin wanda ta jima ta jefashi kwandon shara tare da yiwa kanta alqawarin ta daina har abada,dalilin daya sanyata makara kenan bata kwanta da wuri ba,hakan ya sanyata bata tashi farkawa ba sai qarfe bakwai na safe,ko sallar asuba ta qwace mata kenan,cikin hanzari ta sauko daga saman gadonta duk da yadda jikinta yake a matuqar mace,hakanan ya mata nauyi tun daga gangar jikinta zuwa kanta. Tana idar da sallar da ake binta tana cikin yin azkar dinta na safiya huda tayi knocking ta turo qofar,ta shirya tsaf cikin wankakku kuma gogaggun unifoarm dinta,kai kace yau ne zata soma zuwa makarantar,fuskarta qunshe fal da walwala da farinciki,saidai tana ganin alamun shahidan bata shirya ba ta turo baki kaman zatayi kuka "Anty...bakishirya ba,yaune fa?" Murmushi ta saki tana qarashe salatin annbi guda goma da takeyi ta shafa sannan tace "Banajin dadine yau huda" "Amman zaki ko?" Ta tambayeta da sauri cikin fargabar kada tace ba zata samu zuwan ba "Zanje huda...amma inajin zamu makara da yawa fa" qafa ta soma bubbugawa shahidan ta gane me take nufi "Kinga...ki shirya a soma kaiki,idan yaso in ya dawo daga kaiki ni saiya kaini,saimu hadu a hall din hakan yayi?" Kaita kada tana murmushi "Bari naje naci abinci to" ta fadi tana juyawa a guje ta fita a dakin,sai data bacewa ganinta sannan ta dauke kanta tana sauke nannauyar ajiyar zuciya,tanajin inama ace itace hudan,quruciya abu ne mai dadi,baka da matsala baka da damuwa,dukka ka tsere musu. A nutse ta cire kayanta ta shige bandaki ta tara ruwan dumi ta soma wanka,saboda yanayin jikin nata da batajin dadinsa yasa komai nata ma cikin nawaa take yinsa,hakan ya sanya ta kashe kusan awa guda a wanka da shiryawa. Ta jima gaban mudubi tana kallon fuskarta kaman yadda ta saba koda yaushe,dukda idanunta sun dan sauya saboda kukan da tayi daren jiya amma sai taga fuskarta tayi wasai,farar affaya mai taushi data nade jikinta ta amsheta qwarai,akwai adon golden jikinta,hakanan taji kaman ta cireta,me yasa ma tayi shigar ne?,batason dukkan wani abu da zai mata kyau a yanzu har yaja hankalin wani zuwa gareta,ta saka hannu ta soma cire lullubin laffayar dake kanta anty zubaida ta turo qofar ta shigo,wanda hakan ya tarwatsa abinda tayi niya "Me kike haka?,yau lafiyanku kuwa shahida?"koda ta boyewa antyn yadda take qare mata kallo tasan saita fahimceta,jin tayi shuru saita girgiza kai tana tabe baki " damuwa dai damuwa dai?,ina zakikai damuwa shahida?,wannan kuma da kike niyyar cireta fa?,don ta miki kyau?"dole yadda anty zubaidan tayi maganar ya baka daroya,saita murmusa tana maida lullubin gami da zarar jakarta "Ina kwana anty?" "Lafiya lau ni zan fita inason idan ya saukeni saiya wuce dake makarantar basai ya sake dawowa ya dauki wani ba" "Tohm anty" tare suka fito daga dakin shahida ta wuce saman dining ta soma tsakurar abinci,anty zubaida kuma ta koma dakinta don dauko mayafi da jakarta. Sam abincin ji take bazai ciwu ba,don haka ta hada tea kawai tasha anty zubaidan na fitowa suke fice tare. Sun dan sake bata lokaci a hanya saboda cunkoson ababen hawa da suja tarar a hanya wanda shahidan ta rasa na meye,titi ne da yake da wuya ka samu cunkuso akanshi,ita kanta data dubi agogonta sai da taga makarar tayi yawa,da qyar suka samu hanya suka wuce,ta sauke ajiyar zuciya sanda suka isa bakin katafaren ginin makarantar noor international academy "Yau ina tunanin zamu iya kaiwa biyu,saboda yaune hutu,idan mun tashi zan maka waya in sanar maka" "To babu matsala" ya fada yana tashin adaidaitan,tana tsaye kaman wadda aka dasa har adaidaitan data sauketan tabar gurin,sannan ta soma takawa a hankali kaman mai sanda zuwa cikin makarantar,haka kawai taji zuciyarta tayi mata nauyi,qafafunta kuwa kaman an sare su,bugun zuciyarta na daduwa duk sanda ta qara wani taku guda da zai kusantar da ita da cikin makarantar. Harabar makarantar fetal,sai ababen hawan wasu daga cikin malamai da kuma wasu baqin motoci guda uku da take kyautata zaton na baqonsu ne,shuru makarantar take,hakan ke nuna mata cewa duk an tafi zuwa hall din da za'a gudanar da taron da kuma hutun dalibai,ta dan tsaya tana shawarar ta soma kaiwa huda maganinta tasha kota bari sai sun hadu a dakin taron? "Malama shahida ya akayi haka?" Taji muryar kausar wadda ta fito daga can wani sashe wanda zai sadaka da dakin taron,murmushin yaqe shahida tabi kausar dashi saboda yadda takejin jikinta ba qwari haka kawai "An sallami kowanne aji saura naki,yau tsarin na daban ne,inviglating ya yiwa kowanne aji saiya gama dubaka sannan sai ku wuce kai da dalibanka dakin taron" murya qasa qasa tace "Yana naki ajin yanzu ku kawai ake jira a soma,kiyi sauri ki riskeshi donma yana da kirki,nima amakare na iso amma ina bashi uzuri ya karba" kai kawai shahida ta kada mata sannan ta soma takawa zuwa sashen azuzuwa. Bayanshi take iya hangowa saboda qofa da ya baiwa baya,tsaye yake gaban blackboard sanye da suits ash da suka zauna das a jikinsa,fuskanshi na kallon 'yan ajin da alama wani abu yake saurara daga garesu. Sautin fitar murmushinsa shi ya soma dukan kunnenta,bisa alama wani cikin daliban ya fadi abinda ya bashi dariya "To shikenan...next question....who is the best teacher in dis school?" "Anty rahama...aunty rahama!" Suka hada baki dukkansu suna fada,abinda ya sake sashi dariya qwarai,irin dariyar daya jima baiyi irinta ba,baisan wanne irinso yaran kewa malamar tasu ba,komai anty rahama anty rahama,wai wace anty rahama nan "Auntyyy" wasu daga cikin yaran da suka hango tsaiwarta bakin ajin suka fada cikin shauqi da nuna qauna tamkar sunji tambayar da yakewa kanshi,duban yaran yayi sannan a hankali ya waiwaya yana son yaga wace. Shahida....shahida ce dai tsaye cikin shigar kamala ta lafaya,jakarta rataye a kafadarta idanunta saye da farin gilashin daya zamto yana taimaka mata wajen gani,sakamakon matsalar idanu da taso gamuwa dashi tun shekarun baya saboda yawaita kukan da take,wani irin abu yaji yana zagayawa saman kanshi,tsigar jikinsa gaba daya ta zuba,zuciyarsa ta kasu kashi biyu,kowanne sashe na zuciyar tasa da abinda take ayyanawa. Gaba daya jin jikinta tayi tamkar an zare dukkan wata laka data yi saura,,nutsuwa tayi qaura daga jikinta a take,idanunta cikin nashi a hankali taga yana juye mata daga anwar data sani zuwa wani mutum daban,matashin saurayi mai kyau kwarjini kamala da haiba,matashin saurayi daya jiqu da hutu da naira,matashin saurayi mai cikar zati,tsayayyen namiji wanda tambarin ilimi nutsuwa da wata qasaita ta daban ta bayyana muraran kan fuskarshi,dukkan wani abu daya gani tattare da ita shekarun baya suka soma dawowa idanunshi daya bayan daya,hotunan da idan ya tuno dasu suke hanashi bacci duk dare,ganinta cikin halin maye,jinin zubda ciki na gangarowa daga qafafunta,yaci gaba da kallonta yana takowa inda take tsaye cak,sai yaga kaman a sannan ne abinda ke jikin hotunan ke faruwa,take cikin 'yan sakannin da bai wuce ka qirgasu da yatsunta biyu zuwa hudu ba idanunsa ya sauya launi,jijiyar kanshi ta motsa ta tashi,sai daya zo dab da ita sannan yace "Kina nufin a haka zaki baiwa yaran mutane tarbiyya?,a haka kike koyar da yaran jama'a?,na tambayeki ma me kike koya musu?,uhmmm gayamin,?,yadda zasu....." Sai kuma ya kasa qarasawa ya kaiwa iska wafta da hannunshi sannan ya dunquleshi tsam kaman zai tatse dukkan jinin dake cikin hannun nashi gaba daya,dai dai sanda shugaba kula da dukka sashen makarantar ya iso ganin shuru har yanzu bai iso ba,cikin girmamawa ya rusuna "Sir....." "Dakata!" Ya tsaidashi cikin tsawa "Dama irin wadan nan malaman kuke baiwa yara su koyar?" Cikin mamaki ya dubi shahida da yake nuna masa,wadda take tsaye qam a wajen kaman an dasata idanunta kan anwar,tana jin wani fushi na ratsata amma tana ta qoqarin hana hakan tasiri "Sir.....kodai wani akasi aka samu,amma malama shahida na daya daga cikin malaman da kaf makarantar nan babu kamarsu a kowanne sashe" "Sauraramin" ya kuma dakatar dashi wannan karon har yana daga mishi hannu,ya maida idanunsa cikin nata "Indai wannan ce malamar da babu kamarta tabbas bakusan abinda kuke ba,babu abinda ta iya!,bata iya komai ba!,daga yau na koreta!,na koreta cikin malaman makarantar nan.....kar qafarki ta sake tako mana makaranta,you are fired!" Dukkan wani qwarin gwiwa da taso tattarowa ya tarwatse da kalmarshi na qarshe saboda yadda sautin ya fito ya bada amsa kuwwa cikin ajin,qoqarin tattaro abinda zata fada take saidai bakinta ya gaza fidda sautin saboda karayar da zuciyarta tayi,idanunta suka hada qwalla fal suna shirin ga gangarowa,saiya sake saka idanunsa cikin nata cikin wani qwarin gwiwa da yake ji yace "Uhmm...kina da wani abun cewa ne?....say it....say it mana!" Ya kuma fada cikin hargagi yana dan dukan qirjinsa da yatsunshi gaba daya,jakar dake kafadarta ce ta sulmiyo saboda yadda jikinta ya soma rawa,gaba daya kayan ciki suka tarwatse a wajen ciki harda kwalaben magungunan huda,a kansu idanunsa suka soma sauka,wani tashin hankali da baisan na meye ba ya rufto masa,saiya daga kai da sauri yana kallonta,sam ko daya bata da nutsuwar da zata iya tsaiwa ta tattare kayayyakinta ko ta dauki jakar,hakan yasa ta juya da sauri ta soma takawa,fatanta da burinta kawai shine tabar makarantar,tabar wajen,tabar inuwar da anwar yake tsaye a cikinta,burinta shine ta nesanta dashi kawai,ta daina ganinsa ta kuma daina jin sautinsa "Ki dawo ki debi wannan kayan zatar naki" maimakon dawowar kamar yadda ya buqata saita qara sauri kamar wadda aka biyo,don burinta shine ficewa daga makarantar ta tserewa sautinsa,wannan sautin da ta jima da neman tsari dashi da mamallakinsa. Titi kawai ta miqa bata ko waiwaye,bata buqatar abun hawa don ji take kaman qafafunta zasuyi mata aiki fiye da abun hawan,sauri kawai take zubawa wani irin radadi na keta zuciyarta kamar ana yankarta da reza,anwar dai anwar dai?,tabbas da tasan akwai wata rana da zasu sake haduwa kaman haka da tuni ta yiwa kanta kandagarki da ita,wannan wace irin baqar rana ce a wajenta "Anty shahida...anty shahida" taji ana qwalla mata kira wanda sam bata tsaya ba har sai da akasha gabanta,shugaban sashe ne riqe da jakarta ya miqa mata "Don girman Allah kiyi haquri anty shahida,ya dauki hukuncin da dukkanmu bamu isa mu sauya shi ba" 👑 *zafafa biyar na kudi ne,idan kika gani don GIRMAN ALLAH karkiyi sharing,idan kina buqatar siya ki tuntubi wadan nan numbers din* 07067124863 *ko kuma* 09032345899 *kuyi subscribing youtube channel dina don samun damar ganin shirye shiryenmu,subscribe kyauta ne!* 👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽 https://www.youtube.com/channel/UC4kJO342hmb_Pd2luKHBjFA/videos *Alqawarin Allah* 1️⃣9️⃣ "sabon abune wannan a wajenmu,abinda bamu taba gani yayi ba tunda muke dashi,kowa ya shaidai wannan kirkin nasa....anty shahida kodai wani abu kika masa?,mutumin qwarai irin haka canzawarsa...."da sauri ta yanke masa hanzari "Na gode malam,haka Allah ya qaddara" gaba tayi da sauri don ita kadai tasan me take ji,ita daya tasan ya take ji,baifi taku biyar ba adaidaita sahu tasha gabanta tana tambayarta ina zata je?,sai data shiga sannan ta gaya mishi inda zai kaita,duk yadda taso daure zuciyarta ta bari saita isa gida saita kasa,ta tattakura ta rushe da kuka wanda har sai da dan sahun ya waiwayo "Hajiya...lafiya?,kiyi haquri komai yayi zafi maganinsa Allah" ita dai bata iya tanka masa ba illa kukanta data ci gaba dayi. Komao nata ta wurgar tsakar dakinta sannnan ta zauna dirshan tana risgar kuka,tanajin kaman ranta zai fita ne,duk wata nutsuwarta a yanzu babu ita,anwar dai shi idanunta suka gani?,anwar shine ya mata wannan tozarcin?,wanne abu tayi mai munin da har zaikai anwar ya kasa mantawa irin haka ya sake binta da mummunan shaida da wulaqanci?. Kusan haka ta dauki dogon lokaci,wanda ita din batasan wadanne awanni ta shafe haka ba,sai tsintar muryoyin anty zubaida tayi da huda,taso qwarai ta tashi amma ta kasa saboda wani mugun ciwo da kanta yake mata,da qyar take iya motsawa bayaga idanunta da suka zama tamkar fulawar da aka zubawa yeast,muryar saddiq taji yana cewa "Mummy...tana dakinta" a hankali anty zubaida ta turo qofar tana cewa "Alhmdlh,shahida kin daga mana hankali,ina kika shiga haka ke kuwa don Allah" ta qarashe maganar tana qarasowa kanta,zaro ido anty zubaida tayi ganin irin rawar darin da take yi "Subhanallahi,ashe bakyajin dadi" ta qaraso gefan gadon shahida ta zauna tana qoqarin yaye rufar da tayi,da qyar da taimakon anty zubaidan ta tashi ta zauna sosai,qarya tayi mata kan tana shiga makaranta zazzabi ya saukar mata shi yasa ta dawo bata kai ga zuwa dakin hutun ba ganin yadda duk suka damu daga anty zubaidan har su saddiq,farouq anty zubaida ta saka ya hada mata ruwan wanka,saddiq ya zubo mata abinci,ita taimaka mata ta shiga bandaki tayi wanka gami da daura alwalar sallar azahar da magariba da duka bata samu yinsu ba,bata bar dakin ba sai data ga taci abinci ta kuma sha magani sannan. Tana daga kwancen amma hawaye take sharcewa masu dumi,duk yadda taso ga kaucewa anwar da shafe duk wani abu daya shafeshi amma haka yaci tura?,wai sai yaushe?,sai yaushe zaibar rayuwarta zuciyarta da kuma ruhinta ya huta?wunin ranar gaba daya wani irin wahalallen yini tayi,ba shakka anwar ya zamewa rayuwarta babban qalubale,har zuwa dare tana cikin yanayi guda wanda da qyar da sudin goshi ta samu wani wahalallen bacci ya dauketa. ********* ********** A hankali ya daga cup din qarshe na coffe din da yayi saura ya kwankwade wanda shi kansa baisan kofi nawa yasha ba tsahon awannin daya kwashe zaune a wajen,idanunsa jajur suke kai kace an badawa idanunsa yaji ne a ciki,saidai yaqi yarda ko kusa ko alama a kira masa likita ya dubashi,bugu da qari dumin jikinsa ya qaru sosai har kana iya juyo hucinsa idan ya fidda iska daga bakinsa. Lumshe idanunsa yayi ya dora hannunsa saman sumarshi mai tauri saidai a gyare take matuqa yana yamutsata,buri yake inama ya iya kuka idan yana cikin tashin hankali ko tsanani,inama hawaye zasu fita daga idanunshi ko zai samu sauqin radadin da yake ji?,cikin sauri ya sake bude idanun shi wanda suka sake kadawa fiye da dazu,ko yaya ya runtsesu kwalaben da suka zubo daga jakarta yake gani,hakan yana nuna har yau bata bar dabu'arta ba?,waishin waye ne?,waye ya koya mata wannan dabi'ar?,babu shakka da zaisan waye shida ita duka saiya hadasu ya hukuntasu,dukan teburin gabansa yayi da hannunsa ko zaiji sauqin radadin da zuciyarsa ke masa amma a banza. Knocking katafariyar qofar falon aka somayi wanda yana ji yayi funfurus,saidai ya cika ya batse saboda koma waye yana son sake birkita masa lissafi ne,bayan kuma ya riga da yaja kunnen duka ma'aikatan gidan na kada wanda ya sake yako doshi sashensa. Knociking din jinsa yake har qwaqwalwarsa,hakan ya sanya ya miqe a fusace ya isa qofar ya budeta ya kuma bude baki don zazzagewa koma waye masifa,muhsin ne bayanshi likita ne tsaye cikin fararen kayan aiki,dole ya hadiye abinda yaso amayarwa ya saki qofar ya juya zuwa cikin falon ya zabi wata kujerar sabanin wadda ya tashi daga kai ya zube yana maida numfashi,kallo daya muhsin yayi masa baice dashi komai ba ya kalli likitan sannan ya maida idonsa ga anwar din "Zaka iya aikinka" yace dashi,saiyaka jinjina kai ya soma takawa inda anwar ke zaune ya aje akwatinshi kana ya bude,ya ciro abun gwada B.P ya daura a hannun anwar ya soma gwadawa,cikin sakannin da basu wuce goma ba ya warware abun daga dantsensa ya samu kujerar dake daura dashi ya zauna sosai idanunsa a kanshi "Yallabai....kasan yadda jininka ya sake hawa kuwa?" Ya tambayeshi kanshi tsaye "Na sani" shima ya bashi amsa bayan ya sake bude dukka idanunshi akan likitan,cikin mamaki likitan ya maida dubanshi ga muhsin,saiya masa alama daya rubuta magani kawai ya qyaleshi,hakan kuwa akayi ya rubuta maganin ya baiwa muhsin takardar sannan ya tattara kayanshi ya yuwa muhsin din sallama ya wuce. Sai daya tabbatar da fitar likitan sannan ya miqe riqe da takardar maganin ya qaraso inda anwar din ke zaune,idanu ya zuba masa yana kallonsa wanda hakan ya sanya anwar kau da kai "Tsahon shekaru kana fama da wannan damuwar,kaqi gayawa kowa dalilinta,kaqi gayawa kowa dalilin faruwarta,duk dai amma bazai wuce akan shahida ba,anya kuwa anwar anya?,me yasa kake shirye shiryen halaka kanka ne babu gaira babu dalili?" Zumbur ya miqe ya soma takawa don barin gurin "Kar sake cewa dominta ne,na riga dana shafe babinta kamar yadda na shafe babin komai daya faru dani a baya" qara sauri yayi ya wuce zuwa bedroom dinsa yanason baiwa kansa qwarin gwiwa don baison ma anty husaina taji cewa baida lafiya,yanzu dukkan tsofaffin matsaloli zasu taso,magana wata nabin wata har sai yaji kaman kanshi zai tarwatse. Kwananta goma sha hudu tana qoqarin saisaita kanta da maida kanta cikin yanayin daya dace,yaqi tayi ba dan qarami ba a kwanakin da kanta,ta rame qwarai saboda jinya tasha sosai,bata fita ko ina,hakanan hatta da wayarta ma a kashe take,daga daki sai daki,sam anty zubaida batasan meye ya faru ba,saidai dukkaninsu tattalinta suke har ta soma jin dadin jikinta. Ranar wata karaba qarfe hudu na yammaci ta fito daga dakinta,gidan yayi mata shuru haka yayi mata fadi,haka take ji duk sanda su huda suka wuce islamiyya saisu barta daga ita sai anty zubaida kawai,hakan ya sanyata tunanin samo islamiyya itama da zata dinga zuwa daukan karatu,don sanda ta fada din anty zubaida dariya ta dinga mata "Ohni zubaida,shahida bansan inda zakikai wannan son karatun naki ba" murmushi kawai tayi "Anty karatu fa baya yawa,indai ba mutuwa kayi ba ilimi bai yanke maka ba,ba zaka rasa cin karo da wani abun da baka sanshi ba" "Gaskiya ne" ta fada cikin nuna gamsuwa. Sanye take da atampha riga da zani wrapper,sai qaramin mayafi data yane kanta dashi,ta sake haske haka ta fada,a hankali take takawa har zuwa cikin ainihin falon,babu kowa kaman yadda ta zata,sabida haka ta juya ta nufi kitchen don tasan a wannan lokacin anty zubaida tana can. Da sallama a bakinta ta shiga da dashasshiyar muryarta irin ta marasa lpy,anty zubaida ta juyo tana amsawa fuskarta qunshe da murmushi "Patient an taso kenan" "Wallahi anty...na gaji da kwanciyar nan" ta furta tana jan kujera ta zauna akai "Ai gwara ki tattaka ko zakiji dadin jikinki" sama sama suke hira ita da anty zubaidan,inda tana daga zaune ta amshi wasu ayyukan tana tayata,a haka su faruq suka dawo daga islamiyya suka tarar dasu,zama sukai cikin kitchen din suma,saidai basu bar bakin anty zubaida ya huta ba,wannan ya buda wancan wannan ya buda wannan wai duka yunwa sukeji,sudai tunda anty shahida ta soma lalura kawai gidan sai a slow,waiwayowa anty zubaidan tayi "Kinga shahida...don Allah debe qannenkin nan ku bani waje na yafe taya aikin wallahi" dariya shahidan ta bushe da ita sannan ta miqe tana duban su huda "Oya....lets go" ta furta tana kada hannunta,ba musu suka bita a baya suka fice zuwa falon. Haidar ne ya soma canza tasha zuwa mbc bollywood faruq yace sam shi mbc action xai kalla,huda kuma ta tubure ita mbc three takeso "Dalla malama matsa kona kwada miki mari" faruq ya fada yana duban huda gami da zare mata ido "A'ah wallahi,dalili dame?,bani remote din gaba dayanku na raba gardama "please anty" faruq ya fada cikin langwabe kai yana miqa mata remote din,ta gane me yake nufi,saita basar tana cewa "Babu wanda za'a kamo zabinsa,zabina kowa zai kalla" gwalo kowa kema dan uwanshi,tana murmushi ta kamo TVC news kwana biyu tayi missing labarai bata samun kalla,tana jin haidar na gulmarta "Miss news" ta waiwaya ta kalleshi "Zamu hadu anjima" da sauri ya dawo ya fasa hawa saman da yake qoqarin yi "Sorry my aunty kar aji kanmu,niba dake nake ba,Allah kwana biyu dama da baki da lafiyar nan duk sanda ustaz zai karbi hadda fecewa nake kar 'yammatan ajinmu su min dariya...ki taimakeni" "Saika biya cin hanci" "Na yarda" ya fadi yana dariya,idnunta a kansu sanda suke wucewa dakunansu don sauya unifoarm dinsu,saida suka bace mata sannan ta janye idanun nata tana sauke ajiyar zuciya,duk sai taji kaman ita kadai keda matsala,takura da quncin zuciya,tana son ta rabu dasu amma ta rasa me yasa qoqarinta ya gaza?. Ganin cewa suma ba labaran suke ba saita sauya tasha zuwa FASHION TV,sabuwar tasha ce amma tana tashe kuma ta samu karbuwa wajen al'umma sosai,sukan nuna abubuwa kala daban daban,kama daga sutturu na zamani,bukukuwa,birthday,engagment da sauransu,wani lokaci tana son kallon tashar saboda takan debe mata kewa,wasu abubuwan da suke nunawa na burgeta. Yauma ta tadda suna hira da wata mai gyaran jiki shuwaarab cikin harshen turanci,shirin ya qayatar da ita sosai,ta bada dukkan hankalinta akai,sai suka yanke suka tafi talla,tallan farko da suka sako na engagment din wasu igbo ne,tsaki taja tana gyara zamanta saboda sam bata ji dadin tafiyarsu hutun ba,cikin ranta tana ganin rashin aikinyi ne kawai da zaka tsaya batawa kanka lokaci saboda an maka egage da wani,wai itama soyayyar nan gaba daya meye zaqi ko ribarta?,ta sake jan tsaki sanda aka nunosu suna bayyana yadda suke son juna da farincikinsu da kuma saqon godiya ga duk wadanda suka halacci bikin engage din nasu,remote ta dauka da niyyar sauya channel idan sun gama ta dawo,talla na gaba da suka fara haskowa sai yaja hankalinta matuqa fiye da komai,engage ne na wasu couple da za'ayi musulmai masu cikakken sunan hausawa,hoton farko na amaryar ne tayi kyau cikin shiga ta alfarma,wanda kallon farko idan kayi mata zaka tabbatar ta samu gata,hoto na biyu shi ya sanyata jin wani abu ya tsirga mata,a hankali kanta ya sara,hoton anwar ne a matsayin shine angon da za'a gudanar da bikin engage din nasu kwanaki goma masu zuwa,sosai ya fito tarwai,ya cika screen din tvn tamkar yana tsaye ne a gabanta,sanye da wasu shegun suit,daga sama har qasa shigarsa abar birgewa ce iya kallon mai kallo,miqewa tayi tsaye ba tare data shiryawa hakan ba,wani abu mai nauyi na danne zuciyarta kamar ana shirin riqe numfashinta ne,remote din taji ya mata kadan ta kauda fuskarsa daga screen din tvn,saboda haka bata tsaya ba har sai data dangane da socket din dake jone da kayan kallon ta kasheshi gaba daya,sannan ta juya da sauri don barin falon zuciyarta na wani irin gudu tamkar wadda taga wani abun tsoro. Sallamar uncle hisham ita ta tsaidata cak,tasan dole ya ganta bai kyautu kuma ta wuce ba tare data yi masa barka da zuwa ba,daidaita yanayinta taketa qoqarin yi,kafin afkuwar haka anty zubaida ta fito daga kitchen din,da sauri ta juya don batason taga fuskarta,ta gwammace ta fuskanci uncle hisham a haka akan anty zubaida,yanzu zata saka ayar tambaya kan sauyawar yanayinta lokaci guda bayan ba haka ta baro kitchen ba. "Sannu da zuwa abbu" ta fada a sanyaye idanunta na kallon qasa saboda tana ji a jikinta kamar qwayar idanun nata ba dai dai suke ba "Yauwa rahamatullah(ya kirata da ainihin sunanta),ya jikin naki" "Da sauqi abbu" ta amsa masa da sauri saboda wani abu dayake qoqarin shaqe mata wuya "Ma sha Allah" juyawa tayi da zummar barin falon yace "Shahida" sake juyowa tayi "Na'am abbu" "Anjima inason ganinki" "Toh" ta fada tana sake juyawa zuwa dakinta. Takai ta kawo tayi hakan yafi sau babu adadi,hawaye keson fita daga idanunta amma ta hana kanta hakan,tanason lalubowa kanta dalilin da zai sanyata kuka "Enought is enought shahida,kinyi kuka a rayuwarki da yawa...ya isa haka,ya kamata ki kawo qarshen komai,ya kamata komai ya qare" take fadawa kanta da kanta bayan ta tsaya gaban mudubin tana duban qwayar idanunta da kanta gaba daya saika zaci zararriya ce,kallon kanta da kanta take tana bawa kanta qwarin gwiwa,saidai ina hawaye ba'a masa shamaki,saida daya ya ziraro mata wanda ya baiwa dukka sauran damar samun hanya,ta fashe da kuka sosai cikin sassarfa ta isa saman gadonta tayi rub da ciki tana cusa kanta qasan filo tana kokawar hana kanta ci gaba da kukan. Kaman ba zata falon ba amma dole ta qarfafa jikinta ko don saboda abbu da yace yanason ganinta,ta gyra fuskarta gaban mudubi ta zizara kwalli bayan ta shafa powder,batason kowa ya fuskanci tayi kuka,a kasalance take kawowa har ta iso cikin falon,wanda a al'adar abbun dama bayan cin abincin dare yana zama ne cikin yaran nashi su taba hira kafin ya tattara ya wuce dakinshi. "Rahama,meye ya faru ranar hutun noor international?" Tambayar da abbun ya jefo mata kenan bayan ta gama dubawa su farouq haddarsu da wajibul manzil da aka basu kan tajwidi,a hankali ta dago idanunta ta dubi abbun,daita sunkui da kanta qasa,tana tuna duk wani cin fuska da anwar yayi mata,tanq tuna kalamanshi akanta daya bayan daya,wani daci na tasowa daga qirjinta zuwa harshenta,saidai ta dake zuciyarta,batason ko daya ta sake zubda qwalla a rayuwarta saboda anwar "Uhmmm..." Abbu ya sake bata dama ganin tayi shuru "Abbu sun koreni ne" "Kora kaman yaya?,me kika musu?,wannan wanne irin cin fuska ne?" Anty zubaida ta fada a hasale,yayin da abbu yayi shuru har sai da anty xubaida takai aya "Dazu gamayyar malaman makarantarku sun sameni har wajen aikina,sun bani haquri kan abinda ya faru,na gaya musu banda masaniyar abinda yafarun,sun bayyanamin cewa mai makarantar ne gaba daya ya sallameki,dukkansu basu da masaniyar ainihn dalilin daya sanya ya koreki ba,duk da kina daya daga cikin haziqan malaman da suke alfahari dasu,idan don kamarace bake daya kika makara a ranar ba,amma suna so na baki haquri in sha Allahu zasu magana dashi master din,kuma sunsan yana da sauqi zai fahimta,to,duka dai sun gama bayanansu,na kuma ari bakinki naci musu albasa cewa kema ba zaki koma ba,idan baki manta ba dama kan yarjejeniya na barki koyarwa a makarantar,yanzu kuma abinda muka gina yarjejeniyar akai ya afku,saboda haka yanxu kinga nayi winning,dole ki karbi duk aikin dana samo miki kenan" ya qarshe yana murmushi,don bashi da ra'ayin tursasa dan adam ne,amma dama tun asali ta yaya shahida me matakin karatun irin wannan zata tsaya koyarwa a primary?,wanne irin maida kai baya ne "In sha Allahu abbu,nima bani da sha'awar komawar har abada" "Shikenam faduwa tazo daidai da zama,Allah yasa hakan shine yafi alkhairi" "Amin abbu na gode" ta furta idanunta har yanzu na kallon qasa,nan ta yimusu saida safe da zummar zata sha magani ta kwanta. Sai data raba dare tana gayawa kanta ya kamata ta motsa gaba,ta watsar da komai,ta ciyar da rayuwarta gaba,ya kamata ta shafe komai kaman yadda take gayawa kanta a 'yan kwanakin nan,idan bata manta ba,idan kuma zata iya tunawa,anwar din data gani dazu da anwar din data gani satin daya gabata ba shine anwar din data sani shekaru goma baya ba,lallai ba shakka bashi bane,ya kamata aga wata shahidan ta daban ba wannan ba "Yes!" Ta fada tana baiwa kanta qwarin gwiwa da tabbacin zata sauya komai. Washe gari da qwarin gwiwarta ta fito,hakanan tayi yaqin maida murmushi da fara'arta gaba daya,koda bata samu duka ba taji a jikinta ta maida kaso hamsin cikin dari,wanka ta soma yi sa'annan ta fito ta shirya cikin kwalliya madaidaiciya a riga da skert na atamfa don kusan tafi son atamfa saboda tana son kaya cottoon kasancewarta mutum da batason zafi,feshe jikinta tayi da turarenta na din din din,ta tsaya gaban mudubi tana kalli kanta,ita kanta tasan tayi kyau,kwalliyar data jima bata bari ta rabi koda fuskarta ba,murmushi ta sakarwa kanta da kanta tana sake baiwa kanta qwarin gwiwa,sai taji gaba daya hankalinta ya karkata ga aikin da abbun yace zai sama mata,batason ci gaba da zama haka "I need to make my self busy,so i can forget dat am deeply hurt and broke" ta qarshe maganar tana juyawa cikin hanzari ta dauki wayarta ta fice daga dakin. A tunanin anty zubaida zata ganta sukuku ko cikin damuwa saboda maganar jiya amma sai taga sabanin hakan,itama hakan yayi mata dadi sosai,ranar alhamis ce babu islamiyya,haka ta sake sosai cikinsu huda sukayita buga games bayan sun gama karatu,ta kira mutanen data jima bata kirasu ba,ta kira zunnurarta sun jima suna hira,har ita kanta ta dinga tambayarta yau da alama ranar ta musamman ce. Koda noradden yazo shima yazo yau a sa'a,ta tanqwara zuciyarta ta fita ta saurareshi ba tare da wani dogon turanci ba,ba laifi kuma ta dan jima wajensa,don ta dauki mintuna aqalla ashirin abinda bai taba faruwa ba a tarihin zamantakewarsu,ita kanta yau taji zuciyarta sakayau kaman ta rage mata nauyi daga cikin nauye nauyen dake takure da ita. *zafafa biyar na kudine,idan kika gani don GIRMAN ALLAH karkiyi sharing,idan kina buqatar siya ki tuntubi wannan number* 07067124863 *ko kuma* 09032345899 *ga mai buqatar littafina da zanyi bayan kammala alqawarin Allah,yaje youtube yayi searching SAUTIN HIKIMA,zaiga SUBSCRIBE da jan rubutu ya dannan zai koma black,yayi screenshoot ya turo zuwa ga number da zatazo a qasa,zan sakashi group din da yardar Allah SUBSCRIBW KYAUTA NE BA'A DAUKAN KO SISI* 07038670166 *Alqawarin Allah* 2️⃣0️⃣ Zaune yake shi daya cikin dan qaramkn garden din dake bangare raban na gidan nashi,wanda yasa aka masa shi sannan aka qawata masa,yakan yawaita zama lokaci zuwa lokaci musamman a sanda yake buqatar kebewa ko yin wani gagarumin aiki da bai buqatar surutu ko takura,snye yake da t.shirt mai gajeran hannu gami da trouser light and dark brown,tray ne dan qarami aje a ganshi da butar shayi hadi da qananun kofuna guda biyu akai,daya kofin yana hannunsa,idanunsa zube kan laptop din dake kunne gabanshi tana aiki yana kallon wani aiki daya soma tsarawa,inda yake fidda duk wajajen dake da kura kurai,yayi. Da wani sashen kuma ranshi ke a bace saboda sanarwar da nafisa ta fitar a fashion tv,baisan ya akayi ba sai saqonnin taya murna ya tashi dashi fal email dinshi,watsapp dinshi da twitter,angage din ma da ba'akai ga tabbatar dashi ba. Qarar bude gate din gidan da mai gadi yayi ya shiga kunnuwansa,sai yayi tsai yana sauraro,iyakar saninsa yasan dai ya gaya masa kar yabar kowa ya shigo masa gida idan ba muhsin ba,saboda yana son ya hada hankulanshi waje daya,zuciya da qwaqwalwarsa ta samu cikakken hutu. Ba'a wuce minti biyar cikakke da budewar ba ya juyo taku,kamn ya juya saiya basar yaci gaba da abinda yake,don qamshin turarenta daya rigashi isowa ya gaya mishi ko wacece. Ta dauki minti biyar tana tsaye a bayanshi,hannayenta harde a qirji tana qare masa kalla,ba shakka ta jarabtu da son anwar irin soyayyar da bata tsammaceta ba,har kwanan gobe kuma bata ji a jikinta zahiri da badini ta samu irin soyayyar da take kwadayi daga gareshi,haka ta gaji ta saki hannayenta tana fidda ajiyar zuciya ta taka har inda yake,gabanshi ta zagayo ta tsaya tana dubanshi,fuskarta a narke haka ta karyar da wuyanta,sai daya mula don kanshi sannan ya dago ya mata kallo daya,haka kawai yakeji wasu abubuwa marasa dadi akanta,har yanzu baisan a wanne aji zai sanya nafisan ba,ta kuma qi ta gane taqi ta fuskanceshi "Baki iya sallama ba?" Sai tadan sassauta kwabw fuskar da tayi,tana son ta koyi sallama duk sanda ta iskoshi kaman yadda ta fahimci tsarinsa ne amma takan yawaita mantawa,kuma mima ta gaya mata dole ta siffantu da duk wani yanayi da tasan yana so yana kuma cikin tsarinsa "To salamu alaikum" amsa mata yayi duk da har yanzu bai daga kai ya sake dubanta ba "Ba zakace na xauna ba?" Ta fada cikin shagwaba,ture kofin dake gabansa yayi "Sai nace ma?,ai ga kujera nan kina gani ko?" Kai ta gyada a hankali taja kujarar dake fuskantarsa ta zauna. Hannayenta ta hade waje guda,ta sake sassauta murya "Dear...don Allah me nayi maka?,me yasa kakeson sanya zuciyata cikin rudani,kasan ya nake ji duk sanda na kiraka baka daga ba,ko na turo maka saqo baka karanta ko ka turamin reply ba?" Idanunshi ya daga ya dubeta sai ya sake kautar dasu yaci gaba da abinda yake,tunu qwalla ta cika mata idanu,ta tsani wannan miskilancin nashi ya motsa,wahala takesha,tana ji a ranta duk sanda ya soma shariya irin hakan kaman dai ya tuna tsinanniyar yarinyar da yanzu tsanarta ta ninku a zuciyarta wato shahida,data sani baya ga rabasun da tayi ta nakastata yadda ko da wasa ma bazai sake kawota cikin zuciyarsa ba,amma data taba masa zancan ya tunata ne ranar taqa zallar bacin rai,ya gaya mata karta sake mishi wannan zancan don ba huruminta bane,sannan kuma karta sake masa maganar wata shahida,abinda ma yasaka ranta ya danyi sanyi kenan,ta cika da fatan Allah yasa tabar ranshi kenan har abada. "Meye laifina dear..." Ta fada cikin son fashewa da kuka,saiya tattara dukkan abinda yake gefe guda ya rufe system din sannan ya daga kai yana dubanta duba na kai tsaye,yana fata Allah ya yaye mata wannan son da take masa,sam ko kadan shi hakan baya masa dadi "Ni na aikeki kona bada daman ki bada sanarwar engage dinmu rana ita yau?" Kai ta girgiza tana dubanshi hawaye na sake cika idanunta "Wannan wacce irin banzar dabi'a ce,mu yahudawa ne nafisa?" Nan ma kai ta gyada saidai cikin ranta tana jin dadi da sauqin radadin da take ji,ta zaci wani babban laifi ne ta aikata,koya ganta ne ranan nan da saddam randa sukaje dinner din abokinsu,wanda basu dawo ba sai sha biyu da rabi na dare,ita a ganinta wannan sam ba laifi ne ba,hasalima saika isa ka qasaita ka amsa sunanka wani sannan za'a ga wani abu daya shafi event dinku a gidan talabijin din "Kayi haquri,kuskure ne,bani na biya bama siyama ce tace lallai a saka" "Siyama....ita tace rana ita yau din kiyi wani bikin engage namu kenan?,ohk tunda haka ne rana ita yau din ita saita tabbatar da abun kota tursasani" ya qarashe fada yana janyo wayarshi dake gefe,da sauri ta riqe hannun nashi don tafison a kawo qarshen komai,bata jurewa fushinsa,jinsa take har zuciyarta,kallonta da yayi ya sanyata saurin janye hannun nata,yasha mata kashedin tabashi ba sau daya ba ba sau biyu ba "Don Allah dear don Allah,wallahi na fasa ba za'a yi ba" yana da tausayin mace hakanan mutum ne shi da tun asali yake tausaya raunin 'ya mace ko wacece "Kome mutum xaiyi ya kamata ya dinga duba da abinda bai sabawa addini da al'adarsa ba,sannan ka dinga dogon nazari da tsinkaye a duk lamarinka kafin aiwatar dashi" "Kayi haquri" "Ya wuce" ya fada a taqaice "Yanzu daga ina kike?" Kame kame ta soma yi,don tun dazun suka fito gantali ita dasu mima,yanzu haka suna cikin mota su suka rakota bashi haquri,ko hajiya bilkisu ma batasan tazo ba,ganin ta rasa qwaqwqwaran abun fada guda daya ya dakatar da ita "Is ok...yanzu ki wuce gida" "To yaushe xakazo?,kwana biyu ma gaba daya ka daina zuwa ko cin abinci,mama nata complain" ta fada cikin shagwaba "Zanzo da zarar na samu dama" "Can i call you anjima?" Ta sake tambaya,idanunsa ya lumshe kana ya bude,don maganar ta soma isarsa "Allah ya kaimu anjima" miqewa tayi ta masa sallama cikin salon nuna qauna sannan ta juya ta fice daga gidan,ajiyar zuciya ya sauke sanda yaji fitarta,saiya hada kayanshi gaba daya don zaman gun har ya fita akanshi kuma. Bacci ya samu yadanyi,qarfe hudu ya tashi,yayi alwala ya fice masallaci,daya dawo ya shiga wanka ya shirya tsaf cikin dogayen kaya wanda bai fiya sakasu ba,ya dauki wayoyinshi da maqullin motarsa ya fice,ya yiwa mai gadin sallama ya wuce. Tafiyar mintuna qalilan ta sadashi da gidan anty usaina,suka gaisa sosai da mai gadin qofar da yake shiga,saidai qofar ana gyaranta ne saboda gate din yana masa tauri bai buduwa da sauri,tilas yayi rivers ba don son ranshi ba ya zagaya ta daya layin. Idanunshi fes yana iya hangen qofar gidan daga qofar gidan anty usainar,a hankali ya dauke kanshi yana fidda zazzafar iska daga bakinsa,horn daya yayi aka bude masa don tuni ya zagayo mai gadin,ya saka motar tashi yayi parking sannan ya kasheta ya fito. Anty usainan ya tadda da yaran ta zaune cikin valcony din dake gefan matattakala hudun da zata sadaka da babban falon gidan,assigment sukeyi,dukansu suka hada baki suna masa sannu da zuwa cikin girmamawa ya amsa,har ta miqe zasu shiga ciki taga yana zare sau cikinsa "Barni daga nan anty na zauna cikinsu nima,sati biyu kenan bamu hadu ba" da d'aya da d'aya ya dinga bibiyar karatunsu,yammata masu kimanin shekara sha hudu sha biyar da sha shida,sai namiji mai shekara sha uku,yaji dadin yadda yadda ya samu karatun nasu na tafiya daidai,wansa daga qarshe ya sallamesu da kyautar dari biyar biyar suka shige cikin gida suna murna,wajen ya rage daga shi sai anty usainar. "ya jikin naka?"anty usainar ta tambayeshi bayan sun gama gaisawa,dubanta yayi "Waye yace bani da lafiya?"gajeran murmushi ta saki "kana tunanin zaka iya boyemin ne,tun zuwan da kayi cikin wancan satin nasan baka jin dadi" "Don dai karkice na musa miki ne...amma da nace lafiyata qalau,kawai stress ne na wajen aiki" kai ta kada kawai,tasan dama bazai taba yarda ba,baisan tsohon abu bane wannan a wajenta,ta karanceshi ciki da bai "Hakane....Allah ya taimaka to" "Amin" ya amsa yana ciro wayarsa da tayi qara alamun shigowar saqo,nafisa ce,ya karanta ya maida mata da thanks sannan ya maida wayar idonsa kan anty usainan "Dama inason muyi wata magana ce da kai" "Toh anty,Allah yasa ta samu" "Eh to.....zancan nafisa,munyi magana da ita ta sanarmin kace rana ita yau kakesan suje su sami alhj abba,amma saga bangarenka banji kace komai ba har yanzu,ya kamata fa anwar ka maida hankalinka jikinka,da da yanzu ba daya bane,kullum shekaru qara yawa suke akan mutum,baya ga haka ma ya kamata mu fita kunyar yarinyar nan da iyayenta" shuru yayi yana saurarenra idanunsa na kallon carfet din da suke kai,har sai data kammala sannan ya dubeta cikin nutsuwa da jeranta kalamai "Anty,har yanzu banji nutsuwa da gamsuwar nafisa ta zama mata agareni ba,har yanzu ina qoqari da tsarawa kaina yadda zan amshetq,bana son ayi abinda daga qarshe zai xama wani batu na daban,ina matuqar ganin qimar mama da abbanta,ina ganin mubi komai a sannu har zuwa sanda komai zai dai daita,zuciyata ta amshi abun dari bisa dari yadda ya dace"fuska anty usaina ta canza,har cikin ranta tana jin anwar din zai aikata ba dai dai bane kawai "Anwar,idan ka sauya ra'ayi ne kawai ka furta,har xuwa yaushe kakeson yarinyar tayita zaman jiranka?,tun tana kara har takai ga tana takowa ta sameni da maganar,waishin ma idan bakayi aure ba yanzu sai yaushe xakayi anwar?" Ta jefa masa tambayar tana tsareshi da idanu "Duka anty ba wannan maganar bace" "To wacce ce gaya min?" "Kamar yadda na gaya miki ne a baya,har yanzu zuciyata ta kasa nutsuwa da yadda da soyayyar kowacce yarinya,da nafisa zata haqura dani da nafi kowa murna,saboda zanso mata ta auri wanda yake sonta ba wanda takeso ba" "Maganata ta tabbata kenan,kawai anwar ka fasa auren nafisa kakeson cewa,ka shirya butulci wa mahaifanta" cikin bacin rai ta qarashe maganar "Banason ranki ya baci anty,za'ayi duk yadda kikeso,zanje da kaina na samu kawu abdulkarim na shaida musu,Allah yayi mana jagora" ajiyar zuciya ta sauke sannan tace amin Allah yasa ayi a sa'a,ko kadan batason iyayen nafisa su kallesu amatsayin butulu marasa cika alqawari,marasa kuma rama alkhairi da alkhairi,daga wannan magana ya miqe "Har zaka wuce?" "Eh...ina da aiki da yawa kwana uku ban samu shiga company ba" "To Allah ya taimaka....amm dama inason gaya maka,cikin satin nan nakeso na shiga katsina mu gaisa dasu baba furai'ah,ya dace kaima ka ware lokaci kaje ku gaisa,don ba qaramin jimawa kayi rabonka dasu,tun suna qorafin kayi kudi ka watsar dasu sai aike har sun haqura ma sun daina" bawai zuwanne wajensu baya sonyi ba,katsinarce baya son shiga,shi duk wani abu daya jibanci tuna mishi da ita baya qaunarsa "Zanyi qoqari in sha Allah" tana zaune daga nan har ya isa inda ya aje motarsa tana kallonsa,ya bude ya shiga ya tayar da ita yabar gidan. Ajiyar zuciya ta sauke bayan ya bacewa ganinta,ta fada dogon tunani,abinda yake dojewa dai yake nuna tsantsar qinsa shine ke wahalar dashi,lamarin da yake qaryatawa shike dawainiya dashi,itakam a duniya kaf bataga matar data dace dashi irin shahida ba,har yau yaqu furta nata meye sanadi?,meye dalilin rabuwarsu,har cikin zuciyarta tana qaunar yarinyar,ta zabi gida kusa dasu ne don tana saka ran wataran ta dawo mishi da ita cikin rayuwarshi,tarihin soyayyarsu,yadda tayi tambari ta kuma yi suna bai kyautu ace ta qare a haka a banza ba,ta sani cewa ko yaqi ko yaso koya nuna koya boye shahidan wani bangare ce na rayuwarshi,ta jima tsahon shekaru tana addu'a tare da fatan Allah ya shige mata gaba yasa taci galaba duk sanda ta tasamma tunkarar lamarin,domin cire qiyayya daga zuciyar da ada take cike da soyayya ba qanqanin abu bane,saidai a jikinta da xuciyarta duka tana jin lokaci yayi daya dace ta tashi ta gwada tabuka wani abu,koda zaiyi kuka da ita gaba tana da tabbacin zaya gode mata,duk da batasan meye yayi silar ruguxa wannan kyakkyawar alaqar da aka ginata cikin fahimtar juna ba. 🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍 Cikin lokaci kadan ta soma jin cewa zuciyarta ta karbi canjin da tazo mata dashi,ba'a dauki dogon lokaci ba uncle hisham yazo mata da upper ta daukan aiki a companyn *TRIPLE R GEM* kamfanin dake sarrafa duwatsu masu daraja da tsada zuwa kayan ado da qawa na mata ,irinsu sarqoqi,dan kunnaye,zobuna,abun hannu,munduwa da sauransu,mallakin *RAYYAN* miji ga *RUMANA DA RAIHANA* (DANGANTAKAR ZUCI). Sun bata matsayin accountant na wajen gaba daya saboda yarda da amincin uncle hisham da rayyan yayi yasa ya bashi cigiyar wanda zai riqa masa wannan matsayin,matsayin da aka bata sai taji yayi mata girma,har taso tace ba zata amsa ba,uncle hisham ya zauna yayi mata bayani da kyau ya kuma nuna mata Allah ne ya bata,fatanshi kada ta bashi kunya ta kumayi aiki tuquru,tace in sha Allah. Duk wani abu da ake baiwa sabon ma'aikaci mai matsayi irin nata sun bata,saidai taqi amsar gida da mota da suke bayarwa,tace bata da ra'ayinsu,ganin haka sai suka qara mata kudi kan wanda ya kamata a bata. Uncle hisham da kanshi ya kaita gidan shugaba kuma mamallakin kamfanin gaba daya don tayi musu godiya,gida mai dauke da matan aure biyu kuma aminan juna,gida na farko data ji yanayin rayuwarsu ya burgeta bayan gidan anty zubaida,haduwar farko jininta ya hadu dana raihana,yanayin rayuwarta nutsuwarta da komai nata,haduwar farko ta karanci yadda ta iya tattalin miji cikin wani yanayi mai sanyi da kuma mu'amala,rumana uwargida,mace mai fara'a da saurin sabo itama sunsha hira da ita,wanda daga qarshe ta tattara kan yara tace zasuje siyayya ne ta barsu da raihana,yaran da shahida ta kasa tantance wanne ne yaran rumana wanne ne na raihana?. Cikin qanqanin lokaci ta kama aikinta sosai,ta kama mutuncinta haka nan tsakaninta da ma'aikatan sai gaisuwar mutunci da girmama juna,ita kanta idan ka kalleta zakaga sauyi mai yawa tattare da ita sabanin baya,ta sake fresh hakan fatarta ta qara kyau da gogewa,kwanciyar hankali da nutsuwa sun samu tare da ita,ta soma shimfida sabuwar rayuwa,tayi wancakali da dukkan wani qalubale da bacin ran rayuwa. _yanzu aka soma,muje zuwa masu karatu_ *Alqawarin Allah* 2️⃣1️⃣ *BAYAN SHEKARA DAYA* Komai na duniya baya ga qaddara yana tafe ne da lokaci,wanda wannan lokacin shike qunshe da komai,yake tattare da faruwar komai,shike bayyana komai hakanan shike haifar da komai din,cikin shekara guda shaheedan ta samu sauyi da canje canje masu tarin yawa,tayi qoqarin binne duk wani qalubale data taba samu cikin rayuwarta,ta kaucewa dukkan wani abu da zai tuna mata dashi fiye da baya,ta fannin rayuwarta kuwa shahidan ta sake zama wata mace mai aji,irin macen da kana mata kallon farko zakasan ta goge,bawai gogewa ta budewar ido ba,gogewa ta kyau,gogewa ta iya ado da mu'amala sakamon mu'amala da take da mutane kala daban daban daga sashe daban daban na qasashen afrika,ta qara wani kyau da kwarjini,hakanan ta murje,ta gefe guda kuwa a yanzu nuraddeen ya samu kanta babu laifi,aduk sanda ya kirata zata daga su taba hira,hakanan duk sanda yazo wajenta a gida takanyi qoqarin fita,wani lokaci ma yakan bita wajen aiki da niyyar daukota,anan ta dakatar dashi,don babu abinda ta tsana a duniya a yanzu irin shiga motar wani d'a namiji,duk sanda ta saka kai zata shiga sai abun ya fado mata,wannan moments din ya kasa barin qwaqwalwarta,shine kuma abu mafi muni cikin dukkan abinda ya faru da ita,tana mamakin me ta yiwa wannan mutumin daya watsota qofar gidansu cikin cin mutunci da wulaqanci?,me ta yiwa fiddausi wadda har yau bata bi ta kanta ba ko neman inda take,hasalima bata sake ganinta ba,to me zatayi mata?,me zata buqata daga gareta?,koma meye tana roqon Allah yayi hukuncin daya dace. To ko cikin company ma da baqin dakanzo siyayya kamfanin masoyane suka mata rubdugu,wani lokaci har haushi kan kamata na yadda ba'a cikakken kwananki uku wani bai ganta yace yana so ba,ta rasa meye a jikinta haka?,me take dashi wanda yake jan hankalinsu?,da tasan wannan abun ba shakka data cireshi ta jefar kota huta da shegen binbinin da suke ma rayuwarta "Kin hadu ne shahida,kina da komai Allah ya miki baiwar komai,ba zaki gane abinda nake nufi ba shahida,amma kinyi tako ina,ki bani dama don Allah" ta tuno kalaman wani alhj wanda tunda yazo kamfanin siyawa matarsa sarqoqi gift na birthday dinta ya dafewa shahidan,a sannan ta sauko zata je cin abinci,baima san ma'aikaciyarsu bace. Gefe daya ta sake yalwata rayuwar ummanta da qannenta,hakan ta yiwa gidansu gyara ta sake qawatashi,ita kanta a yanzu jin dadin rayuwarta take,abu daya ne data fuskanci umman nata ta tsiro dashi shine son shahidan tayi aure,don zancan da ake mubina na ss two ne,kuma ta samu wanda yake sonta,dama yakeso a bashi yaje can wajen dangin mahaifinsu dake katsina ya gabatar da kanshi. 🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍 Qarfe hudu suka tashi daga aiki yau,cikin sauri saboda kar lokaci ya qwace mata ta shiga adaidaita sahun da yake nata ne yake kaita aiki ko wata unguwa da takeson zuwa,a sanda kuma ya ajeta yaje yayi haya dashi. Saloon din da take zuwa kitso ya sauketa,ta dubeshi "Ka dan jirani yau ba dadewa zanyi ba" "To hajiya" ya fadi yana kashe adaidaitan,ta juya cikin takun nutsuwa zuwa bakin saloon din. Yanayin wajen kaman tsarin ciki da falo aka yi masa,duk da qofar cikin mai fadi ce sai aka saka labule mai shara shara,falon kuma kujerun zaman custumers ne da kuma kayayyakin siyarwa na kwalliya kamansu ribbom,man kitso man shamfo,beads da sauransu. Shagon akwai mutane saidai ba sosai ba,a falon ta tadda mai saloon din tsaye da wasu mata suna siyan ribboms,cikin fara'a da muntuntawa ta tarbi shahidan,saboda tasan duk sanda tazo din ba qaramin qaruwa takeyi da ita ba,suka gaisa sannan tace mata "Kitso nakeso madam,amma manya nakeso yau ayimin ibra nakeso" cikin juyayyar hausarta tace "Ohk madam babu damuwa..saidai akwai wasu da za'a wankewa kai,amma bari na soma sallamarka su sai su jira" "A'ah madam,aisun rigani zuwa sallamesu tukunna" "Ohk maa" ta fada tana juyawa ta duba wani waje da take aje magazines ta zubewa shahidan sannan ta sallami wadanda suke sayen ribbom ta koma ciki inda take wankin kan. Daya daga cikin kujerun dake wajen shahida ta zauna,ta aje jakarta gefe daya sannan ta cire glass dinta da take amfani dashi lokaci zuwa lokaci saboda ado ta dorashi saman jakartata ta bude magazine din ta soma dubawa. Hayaniya da hirar dake tasowa daga ciki ta cika mata kunne har tasa ta daina fahimtar abinda take dubawar,sai kawai ta rufe magazine din ta riqeta a hannu,hirar yammatan dake ciki na shiga cikin kunnenta "Ya hadu iya haduwa,daa wlh ni bai dameni ba saboda a sannan baida wani abun burgewa,amma yanzu har wani kishi kishinta nakejin yana kamani wallahi,anya nan gaba kuwa ba za'ayi juyin mulki ba kuwa?" Dariya suka kece dashi "Mima baki da kyau,daga daukanki sojan haya saiki fadi haka?" "Ke qyale shegiya,shekara nawa ina mata bauta?,don tana biya na aiba halitta ta tayi ba" hirar sam bata wa shahida ma'ana ba,saboda haka ta zaro wayarta kawai tayi kiran ummanta,bayan sun gaisa tace "Umma don Allah ki saka mubina ta soyamin wainar fulawa ina nan zuwa,na tsaya yin kitso ne,ta saka min albasa da yawa,ta manja nakeso" "Toh shikenan,amma saita saukemin tuwona" "Eh kafin sannan ma na qaraso" "Allah ya kawoki lafiya" "Ameen umma" bayan ta kashe kiran noradden ya shigo,ba yabo ba fallasa ta daga "Yallabiya kin hanani sukuni sai naji muryarki" murmushi ne ya subuce mata ba tare data sani ba,ita mamaki ke kamata idan nura na nuna yadda yake tsananin qaunarta "Dariya ma na baki?,don bakiga yadda na gaji tubus ba saboda tunaninki,shahida har yau kina daukan son da nake miki da sauqi" "Ba haka bane,kawai dai haka kai ka fahimta" "Koma yaya ne dai yanzu kin wuni lafiya?" "Lafiya qalau,kaifa?" Sosai yaji dadin yadda ta tambayeshin,daga haka ya shiga janta da hira,ta biye mishi kodan ta ragewa kanta lokacin zaman jiran da takeyi. Minti ashirin 'yammatan da akewa wankin kan daya ta soma daga labulen ta fito,tana sanye da riga dinkin straight gown wadda tafitar da duk wata sura tata,shahidan na shirin dauke kai dayar ta biyo bayanta,itama sak irin dinkin dayar ne a jikinta,har shahida ta dauke kai yadda taga ta zuba mata ido ya sanya itama ta maida idanunta kanta,da sauri taga ta juya ta koma ciki tana cewa "Au...madam na manta qawata tace muyi jiranta a nan" "Ohkey to babu damuwa" ta bata amsa sanda shahida tayi sallama da nooradden ta maida wayar jakarta sannan ta cire rolling din kanta,ta zare ribbom dinta ta soma taje kanta. A gaggauce nafisa tayi parking na motarta a qofar shagon,cikin hanzari da sassarfa ta nufi qofar shiga wajen kai tsaye. A sannan anyi rabin kitson da akewa shahida,labulen kawo sukaga an bankado hakan ya sanya shahida daga kanta ita da madam tawakkaltu dake mata kitson gaba daya,idanunta ne ya sauka cikin na shahida tana mata kallon fes,itama shahidan kallonta take,tasan fuskar,fuskace da ba zata taba manceta ba,fuska ce da anwar ya turo mata da hotunansu a tare yana bayyana mata ita a matsayin masoyiya a gareshi,ta yaya zata manta wannan fuskar,amma saita dauke idonta ta maida kanta qasa tana ci gaba da danne danne a wayarta,saidai wani abu yazo ya tsaya mata cak a qahon zuciyarta. Madam tawakkaltu ce ta amsa mata tana ci gaba da yiwa shahida kitson,saidai idanunta na akanta tana neman jin abinda ya kawota wajen,don bata santa ba "Amm,akwai friend dita mima da tazo wankin kai nan ko?" Nafisa tayi qarfin halin furtawa,ranta da zuciyarta gaba daya a jagule "Eh sunaa ciki aeke sukee jira" ta amsa mata cikin gurbatacciyar hausa,kafin takai ga isa wajen mima ta fito da qawarta lima "Gani...mu wuce ko?" Ta fada tana karantar fuskar nafisan,kaita jinjina yanayin fuskarta na sake sauyawa yana nuna rudani a ciki qarara,har sukaje bakin qofar da zasu fita tana duban shahida wadda bata ma san tanayi ba,saidai jikinta ya bata hakan "Madam ko kinsansu ne?" Tawakkaltu ta tambayeta ganin yadda suke kallonta "Ba wadda na sani a cikinsu" ta amsa mata a taqaice "Allaho ya kyauta" ta fada tana mamakin irin kallon da sukewa shahidan su duka. Duka sai komai ya tsayawa shahidan cak,ba bacin rai takeji ba amma ranta da jikinta sam babu dadi,wayar ta maida cikin jaka ta ciro carbinta ta maqala a yatsanta ta soma jan HASBUNALLAHU WA NI'IMAL WAKIL,wansa babu jimawa taji komai na koma mata dai dai. Dukan sitiyarin motar tayi da qarfin gaske har lima na zaro ido kada fa kan motar ya lalace "Ba haka nakeso na ganta ba mima,ya akayi na ganta a cikin kyakkyawan yanayi?,so nake ta dilmiya ta lalace,so nake tayi nisa cikin shan kayan maye karta waiwayo komai nisan kiran da za'a mata,kudin dana biyaki bai kamata wasan ya tsaya iya nan ba,ya akayi haka?" Ran mima yadan sosu kadan sabida yadda nafisan koda yaushe taqamarta nakan kudin data bata,amma abinka da bariki saita danne "Abinda ya bani mamaki ya girgizani kenan yasa har nayi kiranki" shuru ne ya ratsa motar abun na kaiwa nafisa ko ina,maganar mima ta katse mata zaren tunaninta Ba wannan nakeson jiba,meye mafita?" Ajiyar zuciya mima ta sauke "Toh....a yanzu dai babu batun saka wani kota bar wani ya shiga jikinta,na tabbatar ba zata sake barin haka ta faru ba a gareta...amma dai duk da haka,ba'a rasa nono a riga,ki fidda kudi,zansan aikin daya dace muyi a kanta,amma....kece zakiyi rabin aikin,ke kike tare da anwar kuma zakici gaba da kasancewa tare dashi,dole ki sake cusa masa tsana da qinta cikin zuciyarsa,kisan yadda zaki ki mamaye tunaninsa ki shiga lungu da saqo" "Kudi ba damuwa bace,successful aiki shine damuwata" "Karki samu damuwa,kinsan wace ni,nayi kin gani ai" locker motarta ta bude ta ciro kudi ta irga ta miqa mata,tasa hannu ta cafesu tana sakin murmushi "Koma sit dina ki jamu,don bazan iya driving ba a yanzu" "Ohkey" miman ta fadi,sukayi musanyan seat ta kunna motar ta figeta,wata ta sanya musu nafisa taja tsaki "Ina cikin irin wannan mode din zaki kunnan waqa,kashe malama ki barni nayi tunani da kyau" "Daqiqiya wanne tunani gareki?,bayan duk wani tunaninki nice nake miki" ta fada a zuciyarta tana cire waqar,yayin da a fili tace "Am sorry,komai fa zai dai daita". Qarfe shida ta shiga soron gidansu bakinta dauke da sallama,tsakar gidan nasu babu kowa sai mubina dake zaune saga qofar kitchen tana suyar wainar fulawarta,fes gidan yake kamar kullum,cikin gajiya ta qarasa inda mubina ke zaune "Sannu da zuwa yayaa" "Yauwa mubi...ashe kin soma?" Tayi maganar sanda take duqawa ta bude flask din dake gaban mubina ta gutsiro wainar takai bakinta "Da tunima na gama ai,maqociyarmu ce ta shigo umma tace a zuba mata shine nake tara miki wata yanzu" "Ummmm....amma fa tayi dadi sosai" ta nemi waje kusa da mubinan tana zama ta janyo yaji ta soma gutsira tana dangwala,mubina na bata labarin bikin wata cousin dinsu dake matsowa,shirin da akeyi anko da dai sauransu "Kowa shiri yake yaya sosai,kinsan wanda zata aura din yana da kudi ba laifi" murmushi kawai shahida ta fitar,wato duk wadda akace yau zata auri me danshi murna ake mata "Allah yasa abokin zama ne,ya sanya alkhairi" "Ameen yaya,naga umma ma tasa an kawo mana ankon,amma bandake" harararta tayi "Ce miki akayi ni cima zaune ce da za'a min anko?" Dariya mubina ta qyaqyace da ita "Waya isa yace miki cima zaune,hajiya accountat da kanta"sai data ci ta qoshi sosai sannan ta isa bakin famfo ta wanke hannunta ta daura alwala ta wuce falon umma. Da sallama ta shiga,su biyu ne zaune suna hira,ita da wata baquwar fuska da batasan wace ba,saidai kallo daya ta yiwa matar taji gabanta yayi mummunar faduwa,itama matar idanunta kan shahida,murmushi kan fuskarta tana amsa sallamar tata,dauke idanunta tayi ta samu gefen kujera ta zauna "Sai yanzu kika shigo?" "Haba tun daxu umma,na tsaya naci waina ne" "Ashe takice amma umma ta bamu muka cinyeta" cewar matar cikin fara'a,sai shahida ta juya ta dubeta itama fuskarta ba yabo ba fallasa tace "Ina yini?" "Lafiya qalau,mun yini lpy shahida ko?" Ta amsa gaisuwar gami da jeho mata tambaya daga qarshe,kai ta gyada tana mamakin yadda akayi matar ta san sunanta,bayan umma bata furta sunan a gabanta ba "Tunda nake zuwa ban taba ganinki ba sai yau,Allah dai yayi yau zanga yaya shahida" ta kuma fada tana murmushi,itama murmushin shahidan ta maidata mata,ganin kaman bata saki jiki ba ya sanya umma cewa "Maqociyarmu ce nan gaba kadan gidanta yake,tayi wajen wata shida da tarewa sai yanzu Allah yayi ta leqo mana,gidan nan da faruq yake gaya miki ana sadaka duk juma'a?" Sai a sannan ta fahimci gidan da take nufi,kai ta gyada tana sake fadada fara'arta,don mubina tasha bata labarin kirkin matar,daki ta wuce daga haka tana jiyo hirarsu da umma. Har ta gama zamanta ta soma shirin tafiya matar tana nan,a nan taci abincin dare tare dasu umman,mamaki take sosai shahida,a ina suka santa ne?,wace ita?. A falo tana rataye da jakarta ta dubi mubina "Cikin kayan da antyn katsina ta kawo miki daukomin na zabi style zankai dinki,yi sauri ki daukomin,sa'id yayi anguwa mai nisa yace ya barshi basai ya dawo dakata ba tunda kusa da anguwarsu yake,motar haya zanbi kar dare ya sake yimin" "Wallahi duka na sakasu yaaya suna wajen wanki" goshinta ta dafe tana jan dan tsaki cikin rashin jin dadi "Halinku daya ai indai mubina ce,kowanne kaya da an saka an cire duk kyanshi sai ruwa,saiki haqura ai har sai ta karbo itama da dan banzan sanabe,ki kama kayanki ki wanke amma saikin kai wankau" murmushi matar tayi har fararen haqoranta suka bayyana kan idanun shahida,gabanta ya sake faduwa,matar tana mata kama da wata,kaman ta taba ganin fuskar "Kinga qanwata zo muje ki zabi style wanda kikeso kinji"tayi maganar sanda ta miqe tsaye ta dauki hijabinta dake aje gefe tana sakawa,kallonta shahida tayi,sai taji tana jin nauyinta sosai,banda haka ce mata zatayi a'ah ta barshi,amma saita kasa fada,don ita gaba daya ta jima rabonta da sake amincewa da wani a rayuwarta,duk wata baquwar fuska da zatayi kutsewa rayuwarta kaffa kaffa take da ita. "umma...ina kuka samota newai?,ni gaskiya ba wani gidanta da zan bita" shahida ta fada dai dai saitin kunnen umman cikin nuna rashin yarda "Babu komai matar sananniya ce,hakanan mun dan jima tare,kije kawai" hakanan jiki ba qwari ta fito ta sameta bakin famfo tana daura alwala,ta kammala ta yiwa umma sallama suka fice. Ko a tafiyarma bata yarda sun hada kafada ba,tana gaba ne tana binta a baya,duk da haka takan juyi jefi jefi ta sako ma shahidan hira,nata eh ko a'ah ne har suka qaraso gate din gidan,tsaiwa shahidan tayi tana kallon gidan,kaman taso ta taba ganin anwar tsaye bakin gate din sau daya,saidai bata tabbatar dashi dinne ko bashi bane,kawai dai tun daga ranar ta tsani kallon qofar gidan ma "Muje ciki mana shahida saiki zaba a nutse" murmushin yaqe ta saki "Nan ma ya isa,idan da yara saiki turo su miqo min na wuce,yau nayi dare sosai a waje takwas ta kusa" "Yanzu zaki wuce ai,ki shigo ko kuma nace mubina ta fiki kirki dason mutane" murmushi tayi saita bi bayanta kawai. Sosai falon ya burge shahida,komai a kammale a tsaftace yana fitar da qamshi "Zauna gu waje nan shahida" tana nuna mata kujera da hannu,a darare ta zauna din tana bin falon da kallo mai gwanin sha'awa da burgewa,sanda yake fidda hijabinta wata 'yar budurwa ta sauko daga sama ta matakalar benan dake falon "Sannu da zuwa ummi kin dade yau" ta fada tana duban maman tata "Wallahi sa'ida...yauwa shiga dakina ki bude wardrobe dina,inda na aje dinkunan da aka kawomin din nan shekaran jiya ki cirosu gaba daya" "Toh" ta amsa tana shirin juyawa idanunta ya sauka kan shahida,saita sake juyowa da sauri ta kalleta ta kalli ummin nata,sai kuma ta juya ta sake hayewa saman. "Ina zuwa shahida kinji" ta fadi tana nufar wata qofa dake nuna alamun kitchen ne,wayarta dake jaka ta dauki kuka alamun kira ke shigowa,ta cirota tana dubawa,noradden ne,saita latsa tana karawa a kunnenta "Ranki ya dade,ya akayi sa'idu yabarmin ke a waje da daren nan?,naje gida baki nan,na kirashi yace wajen umma yabarki,kuma kince basai ya dawo ba" "Eh uzuri nayi masa ne" ajiyar zuciya ya aje "Ni gaki kin fiddoni,kema kinsan ba yadda za'ayi na iya kwanciya kina waje,fito gani a qofar gida" "Na fito daga gidan ai" "Ina kika je?" "Ina maqota" sai tayi mishi kwatancen gidan yace gashinan,babu jimawa ta fito dauke da wani dan qaramin faranti da aka dora ruwa da lemo,gefe daya dambun nama da meatpie ta aje gabanta "Ga ruwa kisha" murmushin yaqe ta danyi don har yanzu a darare take,hakanan taji ta kasa sakewa "Na qoshi wlh anty" "Da alama dai da gasken shahida baki da kirki" dariya maganar ta bata,saita kuma sakin murmushi sosai "Ba haka bane anty,kina gani kusan ma tare mukaci abincin" "Eh...amma ko albarka kyasa" bata sake cewa komai ba ta gutsuri meatpie din kadan,dai dai sanda ta qwalawa yarinyar kira "Sa'ida me kike ne?,kiyi sauri sauri fa take gida zata wuce" "Gani nan ummi" tana maganar ne sanda take sakkowa daga saman cikin sassarfa rungume da kayan a qirjinta,a gaban ummin ta zubesu "Riga daya ce ban gani ba ashe ta shiga cikin wasu kayan "ok...gasu ki xaba wadanda zasu miki" a nutse take daga dinkunan,duka sun mata hakanan sunyi bala'in kyau,tana son yace xata dauka duka tanajin nauyinta,saita zabi uku daga ciki "Wadan nan ma sunyi,na gode" tura mata sauran tayi "Jeki dasu gaba daya,mai yiwuwa telan yaga wanda zaifi miki kyau akan wanda ke kika zaba" haka ta tattara duka kayan ta zuba mata a wata 'yar jaka mai kyau,ta mata sallama ta fito. Yana tsaye jikin motarsa wayarsa na hannunshi yana danne danne,ganin fitowarta ya sanyashi maida wayar aljihu,ya tarbeta cikin fara'a ya amshi ledar hannun nata sannan ya bude mata gaban mota,dubanshi tayi sosai "Kaima kariga da kasan qa'idata ko,mu taka zuwa titi ka tsaremin napep" kai ya langwabar mata yana dubanta "Kar muyi haka dake don Allah,yau dai daya kiyimin wannan alfarmar na kaiki,tunda muke dake shahida ko kara babu baki taba shiga motata kosau daya ba,koda batan hanya" maganar tashi ta bata dariya amma ta maze,ita bata da ra'ayin hakan kwata kwata,ganin yadda yaketa roqarta gashi dare nayi yasa tayi bismillah gami da addu'a ta shiga ya zagaya ya rufe ya tada motar. Farinciki yau fal zuciyar nuran,haka ya dinga sako mata hira,suna tsaka da tafiya taga ya dauke hanya,idanu a waje zuciyarta na gudu ta kalleshi "Ina zaka dani malam" dariya yayi "Karki damu shahida,duk sanda kike tare dani cikin aminci kike,wani waje kawai zamu shiga,ki rakani zanwa mama siyayya"shuru tayi tana sauke ajiyar zuciya,duk da haka hankalinta bai kwanta ba har sai data ga sunyi parking qofar wajen ta bude murfin motar suka shiga. A tsaye yake wajen biyan kudi da yake dab da qofar shiga da fita,yana saka pin dinshi jikin p.o.s machine da ma'aikin wajen ya turo gabanshi,yana gama sawa ya tura musu donsu ciri kudinsu wanda hakan yayi dai dai da ganin gilmawar wata da zuciyarsa hakanan ta afu da sanin wacece,suna miqa masa resit ya karba ya soma takawa don ficewa daga wajen,saiya tuna ya yiwa sa'ida alqawarin turare,tace tana son irin turarenshi randa yaje gidan,yace mata ba lallai a sameshi qasar nan ba,amma zai siya mata copy dinshi,yana da wuya yayi alqawari ya saba banda haka da bazai sake komawa ba,a gajiye ya sake juyawa zuwa ciki ya soma laluben sashen turaruka. Tunda ya shiga side din daga nesa yake hangowa kamar shahidan,tana tafe yana biye da ita a bayanta kaman wani bodyguard,taku kadan zai qara ya hade tazarar dake tsakaninsu,tana zaban abu tana zubawa a cart din da nuradden ke turawa,ya bata dama ne ta zabarwa maman komai,da fari taso zuqewa yace indai tayi hakan bata dauki maman mamarta ba,dole tayi yadda yakeso. Sanda ta waiwayo don dawowa daya side din fuskarta ta bayyana fes cikin idanunshi,tana murmushi ne gami da hararar nuradden daya tsokaneta da "Iyee,ashe madam din tawa an iya siyayya,irin wannan siyayya me aji haka?,gaskiya idan mukayi aure ke xaki dinga min shopping" dauke kanshi yaso yayi tare da aiwatar da abinda ke gabanshi amma sai ya gaza hakan kamar wanda aka haneshi,haka kawai yaji idanunsa na masa yaji yaji,wani abu mai zafi ya sauka a qirjinsa,suna dab da cimmasa ya juya ya soma takawa don barin shagon gaba daya. Kallon bayanshi kawai ya haifar mata da mummunar faduwar gaba,duk da batasan waye ba bata ga fuskarshi ba,haka kawai ta dinga kallon bayanshi har ya bacewa ganinta nuradden nacan yana zaben zobe,yanayin tafiyarshi da bayanshi kaman anwar "And so what koda ya kasance anwar dinne?" Zuciyarta ta gaya mata wanda hakan ya sanyata tabe baki da daga kafada. Tun kafin ya qarasa ya bude motar,yana zuwa ya shiga ya maida murfin ya rufe,saiya samu kansa da kasa tafiya,ya sauke glass din side dinsa gaba daya qasa abinda ba dabi'arsa bace,numfashi yake fitarwa dai dai idanunsa kan qofar fitowa daga wajen,shi kansa baisan zaman me yayi ba me yake jira oho duka bai sani ba,saiya duba agogon hannunshi,tara saura,tara saura fa na dare?,sake maida idanunsa yayi qofar shagon dai ya kafeshi da ido. Minti goma ya sake duba agogo,tara na dare saura kadan,har yanzu dai shuru?,ya tambayi kansa "Lafiyanka kuwa anwar?,wai shin ma me kake jira ne?" Ya tambayi kansa da kansa,tuna hakan da yayi yasa ya dage gilasan motar da gaggawa ya zura key zai tasheta,dai dai sanda ya sake duban qofar kanti,sai gasu sun fito fuskokinsu cike da murmushi,yana riqe da ledojin siyayyar,yayin da ita kuma take riqe da iya tata jakar. *Ga mai buqatar littafin da zan fara bayan kammala alqawarin Allah,ya shiga youtube yayi searching SAUTIN HIKIMA zaiga an rubuta (subscribe) dajan rubutu,ya danna sau daya zai koma black,yayi screenshoot ya turo zuwa wannan number zanyi adding dinsa a grpup din in sha Allahu 07038670166* https://www.youtube.com/channel/UC4kJO342hmb_Pd2luKHBjFA/videos alliya: *Alqawarin Allah* 2️⃣2️⃣ Fasa kunna motar yayi ya tsaya cak yana dubansu ta cikin gilashin har suka isa bakin motar nuradden din,shi ya bude mata qofar motar ta shiga sannan ya sanya ledar daya a baya,saiya dora dayar saman cinyarta,runtse ido anwar yayi ganin haka yana jin wani abu ya dunqule masa a wuya. Hannu nuradden ya saka cikin aljihun wandonshi ya ciro wani dan qaramin akwati,ya budeshi yana murmushi ya ciro qayataccen zobe a ciki ya miqawa shahida yana murmushin,kallonsa tayi sannan ta kalli zoben "Da zaki miqo min hannunki na saka miki sai nafison haka,ki saka da hannunki shahida....amma shahida,don Allah zaki aureni?" Maganar ta shiga kunnenta a bazata,daga idanunta tayi ta kalleshi "Me ya kawo wannan maganar nuradden?" "Ban cancanci nayi wannan maganar bane shahida?,kina tunanin akwai wani namiji da zai kalleki yaji ba burinsa bane ya mallakeki?,ko tsahon zamanmu tare bai kamata ace na nemi mu zama miji da mata ba?" Bayyananniyar ajiyar zuciya ya saki,gaba daya ya rusa mata lissafi da plan dinta "Hakane....amma kayi haquri zamuyi wannan maganar daga baya,kaga yanzu dare yayi naga kiran anty xubaida ma" "Shikenan" ya fada yana maida zoben akwakunsa sannan ya miqa mata,ta saka hannu ta amsa ya zagaya seat dinsa ya shiga ya tayar da motar. Kashi anwar ya jingina da kujerar da yake kai idanunsa kan motar tasu har suka fice daga wajen,hakanan yaji ya kasa zama shima ya tada motar tasa ya figeta yabi bayansu da hanzari,ba jimawa ya cimmasu,haka ya dinga bin bayan motar har zuwa cikin unguwarsu qofar gidan,gotasu yayi yayi parking din motarsa daga gaban tasu ya kasheta yana kallon abinda ke faruwa,motar ta bude ta fice ta tura gate din gidan ta shige sannan nura ya tashi motarsa ya fice daga layin. Ya kusa a qalla minti goma a tsaye a wajen "Wanne abu kake ne haka anwar,kana cikin hayyacinka kuwa?" Yaji maganar daga sama,wani sashe na zuciyarsa na tuhumarsa "Ya Allah" ya fada shima cikin jin haushin kansa,gami da tuhumar kansa na me ya kaishi aikata haka,saiya kunna motar yana duban agogon dake gaban motar,qarfe tara harda minti goma sha shida,yana jin da qyar idan zai iya zuwa gidana anty usaina yanzu duk da tana can tana jiranshi,kawai saiya wuce gidanshi,zuciyarsa na masa wani irin zafi haka kawai. Baiyi nisa a tafiyar ba wayarshi ta dauki qara,ya kalli wayar da ido kawai,sa'ida ce ke kiranshi,saiya danna sannan ya maidata handsfree yace "Ya akayi sa'in(shi yakan kirata dashi wani lokaci)" "Uncle,zaka zo ne?" "Me ya faru?" "Uncle wani abu na gani,wata na gani tazo wajen ummi uncle kasan dawa take kama?" Kai ya kada "A'ah,dawa take miki kama?" "Uncle kaman anty shahida nidai haka na gani,amma wannan ta dan fita girma ta kuma dan fita kyau" gabanshi ne yafadi baisan sanda yace "Yaushe?" Ba "Dazu dazu suka shigo gida tare da ummi" dan shuru yayi na dan wani lokaci sannan ya sauke boyayyar ajiyar zuciya "Shikenan...yau bazan samu shigowa ba,amma ki bari gobe idan nazo sai muyi maganar" "Toh uncle,ka siyomin turaren?" "Zan kawo miki karki damu,ki gaida ummin naki kice mata wani dan uzuri ya riqeni" "Toh uncle" daga haka dukkansu suka kashe kiran,tunani ya shiga sosai,sai salon tuqin nasa ya koma slow kaman bazashi gida ba,tunaninta ne ya dawo masa sosai tun farko alaqarsu irin wanda bai taba tsintar kansa a ciki ba. Sai daya kashe wasu mintoci kafin ya isa gida,a gajiye ya isa falonshi ya fada saman kujera yana lumshe idanunshi kafin ya budesu,yanason manta komai amma abubuwan nata zarya bisa qwaqwalwarsa,sai kawai ya miqe zuwa bedroom dinshi,ya cire kayanshi ya daura towel ya shige toilet ya sakarwa kansa ruwan sanyi sosai. Ya jima zaune gefan gadonshi yana neman bacci ya sureshi amma abun yaci tura,saiya miqe zuwa wani safe na musamman dake dakin,ya saka lambobin sirri ya budeshi,envalope din daya tsani gani yau da kanshi ya daukota,ya bude abubuwan dake ciki gaba daya,hotunan ciki suka bayyana,take kanshi ya soma daukan zafi,idanunsa suka kada jazur dasu,saiya kasa ci gaba da kalla ya soma tattaresu yana tuhumar shahida cikin ranshi "Me yasa shahida me yasa?,me yasa za k iyi haka,me yasa kika tarwatsani,me yasa kika tarwatsa duk wani buri da fata na?" Ya qarashe maganar yana cilla envalope din cikin abun ya maida ya rufe,saiya fada saman gadonshi yana maida numfashi gami da ambatar "Hasbunallahu wa ni'imal wakil" *WASHEGARI* Qarfe goma da minti arba'in ya isa gidan cikin dinkin shadda wadda tayi masifar masa kyau da fito da kyawunshi. Dukkansu suna falo suna karyawa "Uncle sannu da zuwa,ina kwana" suka dinga fada daya bayan daya,fuska a sake yake amsa musu yana tambayar lafiyar kowa suna amsa mishi "Ina ummin taku?" "Tana sama tana wanka" sa'ida ta bashi amsa bakinta fal da zance,turarenta ya ciro ya miqa mata tasa hannu biyu ta amsa cikin Murna "Uncle na gode,na gode" "Yauwa" ya amsa yana duban tashar da suke kallo,hijra tv waqoqi suke sanyowa na mawaqa daban,sa'ida ce ta tashi daga cin abincin da take ta dawo kan kujerar da anwar yake kai "Uncle" ta fada qasa qasa,waiwayo yayi yana kallonta "Uhmmm" "Maganarmu ta jiya...." Shuru tayi ta ganin saukowar anty usaina,suna hada ido tahau rarraba idanu,miqewa tayi tsaye kafin ta iso,ta jefa mata harara "Ku kwashe farantan nan kukai kitchen,munaya ki hadasu ki wanke,ke kuma uwar zance ki bita ki daura abincin rana,kafin ki gama laqaqin naki kin gama" duka suka miqe falon ya zama daga ita saishi,ta zauna tana dubanshi "Jiya sai kuma na jika shuru,sa'ida tace ba zaka samu shigowa ba" yana shafa kanshi yace "Wallahi,jiyan na taho wani uzuri ya tsaidani" "To Allah ya rufa asiri" a mutunce ya gaisheta ta amsa masa cikin kulawa sannan daga bisani tace "Ko a hado maka abincin kari?" "Eh to...amma bada wani yawa ba" dauke idanunta tayi daga kanshi ta mayar qofar kitchen din ta kira sa'ida tace ta hado mishi. Yana karyawan suna taba hiran,a hankali shurunsa yafi maganarsa yawa,hankalinsa ya karkata kan hijra tv da suka sako waqar jarumar mata,saita dinga taba ranshi kadan kadan,tana tuna mishi wani lokaci can baya,a nutse ya dauki remote din dake aje kusa dashi ya sauya tasha,dai dai sanda anty usaina tace "Anwar....ya kamata fa ace ka soma shiri,biki saura sati hudu amma banga alamun hakan tattare dakai ba"sai daya hadiye abincin bakinsa sannan yace "to me zanyi anty bayan wanda nayi" "Kamar ya me zakayi?,haka zaka aurar musu diya babu maganar lefe babu komai?" Aje cokalin hannunsa yayu sannan yace "Nifa anty,da zaki yadda da maganata ayi haquri a qara min wasu watanni" "Saboda baka da gidan sakata ko baka da kudin yi mata lefan?,ko sadaki ne baka dashi?" Murmushi ne ya subuce masa ba tare daya shirya ba "Au dariya ma nake baka ko anwar?"kai ya girgixa dariyar na kubce masa "ni na isa antyna,kawai dai....naga kina yin nafisa ne da yawa" zamanta ta gyara sosai,alamun maganar da zata masa nada muhimmanci "Ba haka bane anwar,ka fahimceni,mutanen nan suna da kawaici da dauke kai,basu da son zuciya ko tilasta mutum,da wasu ne su yadda suke ganin sun isa dakai dinnan kawai zasu baka umarnin ka auri diyarsu ne,su saka kuma ranar biki da komai baka data cewa,uwa uba ina gudun halayyarku ta maza kafa kazo ka murje ido kace ka fasa ka barmu da kunya" murmushi yayi yana kallon qasa,shikam dama bayajin zai dauki irin wadan nan abubuwan,dalili kenan da tun farko ya zabi yaci gashin kansa,bai qasan wani bare ya tilastashi koya tauyeshi,rama halacci dai wannan yasan abune mai kyau,kuma shine hujja daya,dalili daya da zai sakashi ya haqura ya auri nafisa "Anty kiyimin kyakkyawan zato,ba abinda zai faru da yardar Allah indai daga bangarena ne,abinda kawai yasa na buqaci qarin shine,akwai wata 'yar tafiya da zanyi ta wata uku,kinga zaifi kyau naje na dawo,hankalina ya hadu waje guda,duk abinda za'ayin ma sai ayin,zan baki kudin da zai isa a hada lefan kafin wucewata da sauran abubuwan da aka sabayi na al'ada" ajiyar zuciya ta saki "Shikenan,yanzu ya za'ayi ka shaida musu?" "Wannan duk ba damuwa bace,zan samu alhj da kaina,baida matsala,yasan da tafiyar tawa dama" "Shikenan,Allah yayi mana jagora ya bada sa'a" "Amin anty" daga haka suka shiga hirar data shafesu,sai wajejen shabiyu na rana ya baro gidan shima ganin haduwar hadarine,baya n ya tambayesu ya tabbatar basu da wata damuwa. 🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍 Cikin harabar gidan yake zaune cikin motarsa,murfin motar side din da yake a bude yake,hakanan ya ziro qafarsa daya waje,iska mai dadi dake kadawa tana shigowa har inda yake,iskar na masa dadi qwarai,,dalilin kenan daya sanya idanunsa lumshewa yana shaqarta har tsakiyar kanshi,knocking glass din motar yaji anyi,ya ware idanunsa a hankali suka sauka kan fuskar nafisa dake tsaye cikin kwalliya tana dubanshi daga sama har qasa,duk da fuskarta qawace take da kwalliya amma annurin cikinta kadan ne,shigarsa take kallo,yayi kyau cikin qananun kaya baqaqe qafarshi saye cikin wani booth mai bala'in kyau,quruciyarshi da kyanshi muraran suka bayyana,sai taji sonshi na sake shigarta,baqinciki da bacin ran daga bikinsu ya sake mamayeta har hakan ya bayyana kan fuskarta "Whats wrong with you" ya tambayeta idanunsa qyar a kanta,saitayi narai narai da idanu,qwayar idonta cike da qwalla,,da alama gab take da sakin kuka,shuru tayi ba tare data amsa ba,fitowa yayi gaba daya daga motar ya rufe sannan ya jingina da ita hannayensa shima harde a qirji "Me ya sameki kuma?" "Au..baka ma sani ba zaka cemin?" Hannayensa ya watsa yana harde qafafunsa sannan ya soka hannayensa a aljihun wandonsa "Eh to,xai iya yiwuwa ni abinda nake tunanin shi zai saki kuka ke a wajenki bashi bane" "Me yasa anwar me yasa har qarin watanni uku bayan wata gudan dake gabanmu" girarshi biyun ya dage yana murmushi "Au,kice ke kukan aure kike,to saurin na meye?,wata hudu kawai saiya zama damuwa?" Langabe kai tayi tana dubanshi "Ni sai ya zama damuwa mana a wajena idan har wajenka bai zama damuwa ba,dama ni na damu dakai ai na sani" murmushi ya kuma saki,yadan tafa hannunshi kadan "Abinda ya faru ya riga ya faru,sai a jira zuwan lokaci" "Ai shikenan,yana iya"agogo ya kalla sannan yace "Zan wuce" idanu ta zaro "Duka duka yaushe kazo?,haba ya anwar mana don Allah,hajiyama fa tace ka shigo kaci abinci" "Sauri nake nafisa,amma idan na samu chance anjima zan dawo,idan ban dawo ba kuma sai gobe" ya qarashe maganar yana bude motar,sai daya shiga sannan ta mayar masa da murfin ta rufe ta daga masa hannu "Allah ya kiyaye" shima hannu yadan daga mata,har zai tada motar tayi hanzarin tsaidashi "Sorry...don Allah ka yimin alfarma mana" "Allah yasa batafi qarfina ba" murmushi tayi "Bata fiba,saidai idan ba za'a min ba" dan qaramin murmushi yayi "Fadi muji"sai data danyi shuru na sakanni sannan tace "Kamfani triple R Gem nakeso ka rakani don Allah" shuru yayi yana dubanta "Me zakiyi a can" hannu ta yarfar "Kai ya anwar,da banso gaya maka ba Allah,amma..." "A'ah,riqe cikinki" yayi maganar sanda ya tada motar,da sauri ta zaburo "Bafa wani abu bane,wasu sarqoqi nakeson saya a can" kallonta kawai yake,burin nafisa yayi girma da yawa,duk sarqoqin garin nan amma sai taje har triple R ta saya?,iya saninshi wajene dake da babu abun qaramin kudi a can,dutse ne masu daraja da tsada suke sarrfasu,wanda ba kowa ke iya siyan abun kwalliya ba acan,bayason ya fiya gwasaleta har taji kaman ya tozartata,sai ya gyada kai "Alright..amma gaskiya bani da lokaci cikin satin nan gaba daya,saidai ko zuwa next week" "Well,yayi indai zaka rakani din" da haka sukayi sallama ya fice daga gidan yabarta tsaye awajen sonshi na shawagi da ita,sai kuma ta tuna yau akwai partyn da zata saboda haka da sauri ta juya zuwa cikin gida. 🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍 Qarfe biyar ta fito daga kamfanin kaman yadda qa'idar lokacin tashinsu yake,saidai gaba daya hankalinta ba'a kwance yake ba saboda baqin hadarin daya hado yake kwance a sama yana shirin zub da ruwa. Kusan mutum uku ne sukayi mata tayin sauketa a gida amma ta doje don kare mutunci da qimarta,ciki harda alhajin dake nacinta wanda ta lallaba ta fito abinta ta baroshi a office din rayyan mai kamfanin gaba daya suna lissafin wasu sarqoqi da sukayi masa,haka ta fito cikin ranta tana addu'a Allah yasa ta isa gida lafiya qalau. Titin babu wadatar motoci sai jifa jifa,ko dama can titin bashi da wadatar wucewar ababen hawa musamman ma na haya,yawanci saina gida,hakan ya sanya ta ku sa kashe minti goma tsaye ba tare da taga gilmawar wani abun hawa na haya ba,cikin abinda bai gaza minti biyar ba hadarin ya taso sosai,iska ta shiga kadawa ko ina sama ta sake duhu,fargabarta ta dadu,ta runtse ido tana jin saukar ruwan saman bisa fuskarta,Allah dai yayi saiya daketa. A hankali yake tuqin saboda yanayin ruwan dake sauka din,uwa uba yanajin kaman yayita shawagi saman titi ba tare daya koma gida ba,yakan kasance cikin kewa da kadaici duk sanda ruwan sama irin haka ke zuba yana cikin gidan shi daya,yakan tuna masa wata hira da suka tabayi da uta,duk da yadda yakeson bunne komai nata amma duk lokacin da ake ruwan sama kaman haka sai hirar ta fado masa "Nafison damina akan kowanne yanayi,tana saka nishadi cikin zuciya,komai yana wankewa yayi fes,tsirrai zaka ga sunyi kyau ya anwar sunyi kore shar,kosu kasan suna farinciki da zuwanta,qamshin qasa iska mai dadin da babu kamarta" tayi maganar ne idanunta na alumshe,saita budesu tar cikin nashi a lokacin da ya zuba mata ido yana tayata murmushin da takeyi na tuna yanayin da tayi "Kasan me yaya anwar?" Ta tambayeshi wanda bata kai ga fadin abinda takeson fada din ba kiran nafisa a sannan ya katsesu,dai dai sanda shima nashi tunanin ya katse yana hango tsaiwar wata matashiya cikin ruwan saman da har hazo hazo yake,tsurawa wajen ido yayi yana ci gaba da tuqin a mugun slow kai kace motar na dab da mutuwa ne,baikai ga qarasawa ba wata farar mota ta yanko daga layin da yake kusa da ita,dab da ita ta tsaya na cikin motar ya fito riqe da lema ya iso gabanta ya matsar da lemar zuwa kanta da alamu magana yake mata,idanu ya runtse yana tsaida motar duk da a tsakiyar titi yake,idanunsa qur akansu,alokaci shahida ta sake ja baya "Ka wuce kawai,bani da damuwa nasan ko ban samu mota yanzu ba ruwan daya tsagaita zan samu" "Haba yallabiya,ke kuwa yau dai kawai,uzuri ne fa,kiga yadda ruwa ke dukanki ke daya atsaye anan,uwa uba tsaiwarki a titi irin wannan lokacin hatsarine ga rayuwarki"kai ta girgixa "ba komai Allah zai kareni" "Duk da haka amma kiyi...." Ta gaji dajin kalaman bakinsa,saboda haka kaman adan hasale tace "Don qaunarka da mahaliccinka kayi tafiyarka" ya fuskanci kaman tanason hasala ne don haka yace "Allah ya baki haquri,naji zan tafi,amma kema don qaunarki da mahaliccinki ki karbi wannan lemar" batason dogon zance saboda haka tasa hannu ta amsa,ya koma ya shiga motar ya tasheta ya wuce,ajiyar zuciya ya saki ganin tafiyarsa,duk da haka saiya kasa tafiya yaci gaba da tsaiwa kaman me gadinta. Ganin ruwan yadan fara sauqi saita soma takawa don canza wani titin ko zata dace,shima saiya tashi motar yaci gaba da binta sannu sannu,yana kallon yadda take digar ruwa har cikin zuciyarsa,saidai bazai iya daukarta amotarsa ba,yanajin wani abu cikin zuciyarsa,kallonta na tuna masa da ganinta da yayi,fitowarta daga motar wani,wanda ba qaramin suya yake masa a qirjinsa ba. *ga mai buqatar littafina da zan fara bayan gama alqawarin Allah,zaije youtube yayi searching SAUTIN HIKIMA,daga qasa zaiga an rubuta SUBSCRIBE da jan rubutu,ya danna sau daya zai koma black,yayi screen shoot ya tiro zuwa wannan number,za'ayi adding dinsa agroup din in sha Allah* 07038670166 *zafafa biyar na kudi ne,idan kika gani don girman Allah karki sharing,idan kina da buqata ki tuntubi wadan nan numbers din* 07067124863 *ko kuma* 09032345899 *Alqawarin Allah* 2️⃣3️⃣ Gab da zata tsallaka daya titin mai adaidaita ya taho,ta tsaidashi da sauri,babu kowa a ciki ta gaya masa inda zata ya dauketa suka wuce,sai da yaga tashinsu sannan ya saki ajiyar zuciya "Wai anwar meye damuwarka ne haka?" Wani sashe na zuciyarsa ya jeho masa tambaya,sai a sannan ya dinga tuno abinda ke faruwa,sam duka baisan yana abinda yayin ba,kamar wani umarni yaji ana bashi,kai ya girgiza yana jin haushin kansa,yana ganin ya tsaya ne kawai ya bata lokacinsa,motar ya bawa wuta sosai cikin gudu ya figeta ya harba titi. Su duka suna zaune a falon suna kallo,da sallama ta shiga,dukkansu sannu da zuwa suke mata,anty zubaida na cewa "Wai wai,sannu rahamatullah" murmushi tayi tana zuge lemar hannunta,huda ta tashi da hanzari zata tarbeta ta dakatar da ita "Tsaya huda karki jiqe,don ni da kika ganni yau jalaf nake a kaina ruwan yau ya qare" tayi maganar sanda take aje jakarta "Ahto...haka kawai za'a baki mota kika qi,da kinga yanzu ba ruwanki da ruwa ko rana" "Wallahi anty to ya za'ayi....faruqu don Allah zazzagemin jakarnan ka duban wayata ka shanyan abinda kaga ya jiqe" da sauri huda ta amshe cikin shagwaba "Anty gani sai kice ya faruq kuma?"hararta faruq yayi "To kishiyata" Dariya shahida tayi "Auto auta yi haquri,gyaramin bari naje na sauya kayan jikina sanyi sanyi nakeji" "Idan kin saukoma ga dinkunanki nan an kawo" waiwayowa tayi "Yauwa,yaushe ya kawo?,jiya fa mukayi waya dashi yace bai gama ba" "Dazu ya kawo" "Ya kyauta,don kayan matar data bani aron style nakeson maida mata,kar taga rashin hankalina...bari naje na dawo saina gani" "Uhmmm" anty zubaida ta fada. Sai data soma kunna qwan dakin data kashe dazun da zata fita aiki,haske ya gauraye ko ina,ko.ina tsaf yana fitar da qamshi kaman yadda ta saba masa,ta kalli agogo,shida harda rabi na yamma,an kusa kiran magariba kenan,kayan jikinta ta fitar ta shiga bandaki ta hada ruwa mai dumi sosai tayi wanka hade da alwala sannan ta dawo daki ta shirya cikin wasu kaya masu dan kauri,sai datayi sallar magariba sannan ta sake fitowa. Yanzun ma a zaune ta samesu,saidai da alama faruqu da haidar sunje masallaci sun dawo,anty zubaidan ma wannan karon da hijabi jikinta,huda dake duqe gaban socket ta dago tana cewa "Yauwa anty,yaa nuradden ne ya kiraki" "Uhmmm" ta amsa tana dubanta,saita ciro wayar ta kawo mata ta karba tana dubawa,Allah ya taimaketa ba abinda tayi ruwa bai tabata "Na gode hudallahi" shahida na murmushi ta fada. Saida sukaci abinci sannan ta duba dinkunan,sunyi masifar kyau ko ba'a fada ba tasan zasu zauna mata a jiki,saita yanke kawai ta barsu saida bikin da zasuyi,ta ninke kayan ta kwashesu ta haura sama dasu,don yau da wuri takeson kwanciya har yanzu kuma yayyafi ake,saboda gobe sammakon fita zatayi akwai ayyuka da yawa. Tana shirin jan abun rufa kiran nura ya shigo wayarta,ido ta lumshe sannan ta waresu,ba yadda ta iya haka ta daga "Ranki ya dade....yau an manta dani kwata kwata ko?,koda yake dama idan ban nemeki ba saidai na shekara ina jajenki" "Ba haka bane...ayyuka ne yau sai hamdala" "Ina fatan dai basu gajiyarmin dake ba?"ajiyar zuciya ta sauke "Gajiya kam akwaita,don yanzu ma shirin kwanciya bacci nake" "Da wuri haka?,da qorafi nakira nayi,amma tunda haka ne kiyu baccinki dakyau,ki gayan yaushe zanzo mu hadu?" Kanta ta juya daya sashen,ta danyi nazari kadan "Kasan yanayin aikin nawa,wunin office ne,idan na dawo kuma na gaji bacci kawai nake buqata" tsaf ya gama ramfota,haduwar tasu ne bataso,ita kuma takurawa da zancan aure da yake a 'yan kwanakin da yadda yake marairaice mata ya sanya bata fiya son haduwar tasu dashi ba,sakata yake kawai a corner "Duka ba damuwa bace,ni idan anmin izini saina riskeki har office din lokacin break mu tattauna abinda zamu tattauna din,karki damu bazan jima ba zan tafi,daga nan har zuwa next week ina jiranki" numfashi ta sauke,ya gama kamata kenan iya wuya,amma itama bari ta qure haqurinsa "Saidai nan da sati daya rana ita yau" "Allah ya kaimu" ya amsa hakan bisa ga mamakinta,da haka sukayi sallama ta kwanta tunani fal ranta,tana mamakin yadda nuradden yake iya shanye duk wani hali nata,bata taba kamashi da rashin yi mata uzuri ko hanzari ba,tanajin nuran na hawa wani mataki fiye da wanda yake kai a baya,ya kamata ta sake bashi wata damar ko yaya take,da wannan tunanin bacci yayi awon gaba da ita. *BAYAN SATI DAYA* Turare ta dauka ta fesa abu na qarshe cikin shirin fitarta office,ta kalli kanta sosai ta tabbatar komai yayi mata,shiga mai kyau da tsari,riga da skert na swiss atampha wanda suka mata cas da mayafi yalwatacce wanda ta dorashi saman daurin dankwalinta data dan turoshi gaban goshi,hannunta agogo ne kaman yadda tafi son sakashi fiye da awarwaro,wuyanta sarqa ce da dan kunnayensu masu azabar kyau qirar kamfaninsu,wanda gwaji ne akayisu aka bawa masu manyan matsayi a kamfanin,takalmanta ta jawo rufaffe na mata wanda ya dace da shigarta,tana zuge jakarta da zata fita da ita taji shigowar saqo a wayarta,saita dakata da abinda take ga zatonta mudassir ne daya daga cikin abokan aikinta wanda yace zai tura mata wasu bayanai kan lissafin da suke tayi na wasu siyayya da wani kamfani yayi na sarqoqi,ga sabanin tunaninta saita tarad da nuradden ne _Da fatan wannan kyakkyawar halittar ta tashi lafiya cikin amincin ubangiji,yau sati guda cif cif,Allah yasa banyi azarbabi da yawa ba_ Kyawawan idanunta masu kyau da haske ta juya gabanta yadan fadi,sam ta manta da zancansu wanda yace ya bata sati guda,saita sauke numfashi data tuna cewa bai taba zuwa kamfanin nasu ba,asalima bata taba gaya masa inda yake ba,hakan na nuna baisan office dinta ba,bazai kuma iya zuwa ba har sai ta bashi adress,tuna hakan ya mata dadi,don idan yazo din bata jin zaya samu amsar da yake da muradi,saboda haka ya kashe wayarta ta jefa a jaka tana murmushin nasara,ta duqa ta qarasa saka takalminta ta dago tana rataya jakarta huda ta shigo cikin shirin makaranta itama,gaida shahidan tayi ta gaya mata sun fito "Muje hudallah...wannan makaranta anaji da ita" dariya ta saki "Sosaima anty,kinga randa me makarantarmu yazo,ya bamu labarin wahalar da yayi saboda karatu,yace mu dake muyi karatu sosai muma donmu zama irinshi" yatsine fuska shahida tayi saboda yadda zancan ya tuna mata da ranar "Allah ya kiyaye" shahidan tayi subul da bakan fada wanda yasa buda ta juyi da sauri "Allah ya kiyaye kuma anty?,yana da kirki fa,sannan yana da karatu,ya iya turanci da larabci,gashi kyakkyawa,shiyyasa ranar banji dadi ba da kika koma gida baki ganshi ba.....kinsan me?,uncle fa muke ce masa,yace duka mu yayanmu ne..." "Hudaa....a'ah" shahida ta fada tana kallonta,itama sai ta saka ido kawai tana kallon shahidan "Oya muje karki sa muyi late dukanmu" dariya ta saki tana tafiya sauri sauri "Mu yanzu ai ba'a dukan late comers,uncle ya hana" goshinta ta dafe da tafin hannunta,wato dai hudan ba zata daina mata zancan mutumin nan ba. Tana mamakin yadda suke ganin kirkinsa haka da yawa,basu san cewa macijin sari ka noqe bane shi?. Agurguje kuma a tsaye ta hada tea dan kadan ta kurba,duk yadda anty zubaida tayi kan ta tsaya tayi break sosai cewa tayi sauri take yau suna da aiki da yawa,haka ta fice bayan ta musu sallama,aka dauki huda itama ta shiga tata adaidaitan suka wuce. A cikin company ya ajeta kaman yadda suka saba ya juya ya fice ita kuma ta shige zuwa cikin ainihin kamfanin,a sashen kula da baqi na musamman zata wuce cikin hanzari tajuyi muryar mudassir "Kin kusa makara fa" waiwayowa tayi fuskarta babu yabo ba fallasa ta dubeshi "Wallahi,amma na gode Allah da ban makara ba,ina fatan komai ya zama ready" kafadarshi ya daga yana dubanta,yana da muradin shahidan sosai tana burgeshi,komai nata abun sha'awa ne amma kame kai da jan ajinta yasa ta masa wani irin kwarjini daya sanyashi ya kasa kwatanta mata bare ya furta "Eh tuni ma" ya qarashe maganar yana miqa mata daya daga cikin file biyun dake hannunshi,hannu ta saka tana buda shafukan farko tana dubawa sama sama,daga kai tayi sai suka hada ido yana kallonta,hakan ya sanyata dan tsare gida "Ka sameni a office dina muyi acan inaga zaifi" ta juya abinta ta isa bakin elevator da xata kaita zuwa bakin ofishinta. Da sallama ta shiga duk da cewa ya sani babu kowa ciki,a nutse ta qarewa office din kallo,ko ina tsaf yake yana fidda sassanyar qamshin da ita ta yiwa kanta zabin kalar freshner din da takeso wadda ta banbanta data kowa,wadda ke mata shara din ta qwarai sosai,sannan kuma tasan aikinta,hakan yasa takejin dadin aikin da take mata,tasan ra'ayinta da tsarinta,jakar hannunta da file din ta dora saman teburinta sannan ta taka a hankali ta isa bakin windows din office din ta bude kowanne,iska mai dadi da sanyaya rai ta soma kunno kai,irin iskar damina mai taushi da sanyi,tana son irin wannan iskar,sabida banu iska mai dadinta,fresh ce daga indallahi,sai data tabbatar ta gauraye office din sannan ta rufe windows din,ta sauke labulayen ta kunna AC,hakan ya qarawa office din wani dadi da yanayi na musamman. Tana zama mudassir ya shigo,yaja kujera ya zauna yana qarewa office din kallo sanda take kiciniyar futo da system dinta wadda a office din ta kwana bata je da ita gida ba jiya "Kai masha Allah,duka kamfanin nan ba office din dake burgeni nakejin dadin shigoshi irin wannan,komai neat masha Allah" ya qarashe maganar yana sauke idonshi a kanta,dan qaramin murmushi ta saki sannan ta soma dai daita cumputer din gabanta,ba tare data sake bashi wata qofar sako wani zancan ba ta soma gabatar masa da abinda ya zaunar dasu. Tun tara da rabi suke abu daya har qarfe daya da rabi na rana kafin su kammala,ta gaji matuqa tayi tubus,ga 'yar banzan yunwa dake damunta,kujerarta taja baya bayan ta rufe system din tana hamma idanunta lumshewa wanda sam bata kula da yadda mudassir ya zuba mata ido yana kallonta ba cikin burgewa,tunda suka zauna qamshinta ke burgeshi "Yadai madam?" Ya tambayeta har yanxu idanunshi na kanta,sai a sannan ta juyo ta dubeshi,fuskarta adan hade kaman yadda ta saba idan ta fuskanci kana da shiga sharo ba shanu "Da akayi me?,ai mun gama ko?,sauran aikin ya rage naka da nawa,kowa yaje ya tsara abinsa cikin system dinsa,duk randa zamu gabatarwa da boss kowa yasan me zai fada" kai ya rausayar "Ba haka nake nufi ba,naga kaman bakijin dadi ne" miqewa tayi tsaye tana gyara yafen mayafinta,bandaki takeson shiga sabida fitsari ya matseta gashi yaqi fita ya bata waje "No,ba komai gajiya ce kawai.." Ta tura kujera baya sosai yadda zata samu damar fita daga tsakanin kujerar da teburin. Gab da zata shige bandakin aka nemi izinin shigowa office din ta bayar,masinjarta ce cikin girmamawa tace "Kinyi baqo ne anty(haka take kiranta saboda yadda take ganin qimar shahidan" cikin mamaki tace "Baqo kuma?,custumer ne?", ta tambaya duk da tasan bashi bane,don yawanci ba'a ganinta ita idan ba wata matsala bace akan pyment da custumer zaiyi,koda kuma zai ganta ma za'a rakoshi ta qarqashin wani office dake kula da shige da fice da kuma siyayyar kaya a kamfanin " a'ah,yace yana son ganinki ne personal"tayi tsammanin cikin mutanen dake takura mata ne,abun saiya qona mata rai,batason abinda zai shafi mutuncinta a wajen aikinta,sabida haka taja tsaki "Jeki ce masa lokacin aiki ne yanzu,ya nemeni ta waya ko waye idan na tashi daga nan" "Toh" ta fadi tana juya ta fice daga office din,tsaki taja ta dawo don daukar ruwa ta soma sha tukunna "Sai haqurifa,kinsan kowanne mutum da yadda Allah yake masa baiwar jama'a" waiwayowa tayi ta kalleshi,shaf ta mance dashi cikin office din,saita dauke kai tana sake hade girarta ba tare datace masa komai ba,batason a dinga zama mata cikin office tafison kuna gama aiki ka kama gabanka,wayarta dakw cikin jakar hannunta wadda ke saman teburinta tayi qara,a nutse ta qarasa ta zugeta ta cirota,sai taga number nuradden,fuska tadan yamutsa saboda yadda taji gabanta yadan fadi,ta daga ta kara a kunnenta "Allah ya baki haquri gimbiya nine fa,ko nima ba za'a samu damar ganina ba bayan alqawari aka yimin?" Mamaki ya cikata,ta yaya akayi yasan kamfanin da take aikin,banda abinki wannan wajen kina tunanin zai xama boyayye ne?,shahararren waje irin wannan? Wata zuciyar tace da ita,murmushi ta qaqaro "Ayyah bansan kai bane,minti daya ina xuwa" kiran nashi ta katse ta soma neman wata number cikin ranta fana dana sani da Allah wadai da kunna wayarta data yi,data sani tun daxun ta barta a kashe kawai,wani sashe ta kira na kamfanin ta bada umarnin a rakoshi,daga haka ta kashe wayar,duka sai jikinta yayi sanyi taju qafafunta kamar an bubbuge mata su,sai ta zauna saman kujerun cushion dake gefe daya na office din. Sanda ya turo qofar lokacin saddam ya miqe yana fadin "Bari na samo miki wani abun,na fuskanci kaman yunwa kike ji" bata iya amsa mishi ba yayin da sukayu clashing da nuradden sanda yake shigowa,suka kalli juna saddam ya sanya kai ya fice nuradden ya bishi da kallo,sai daya bace masa sannan ya dauke idanunshi ya qaraso yana rufe office din idanunshi a kanta "Waye wannan din?" Ya tambayeta kai tsaye,tasan akan wa yake tambaya saita saki murmushi "Abokin aiki,aiki muka gama dashi yanxu" dan shuru yayi kishi na cinsa,ji yayi kaman ya maqure saddam din sabida ya karanci irin kallon da yakewa saddam din shima irinsa yake masa,kansa kawai ya jinjina yana qarasowa "Kin kashe wayarki kin tsammaci bazan iya laluboki ba duk inda kika shiga ko?" Boye dariyarta tayi,batasan ya dagota ba "A'ah,kasan idan ina aiki banason yawan amsa waya,dalili kenan daya sanyani na kashe" inda ta tashi ya koma ya zauna yana kallon office din nata,kaman yadda ya saba burge jama'a shima ya burgeshi sosai "Sannunka da zuwa" saiya kalleta "Allah yasa har zuci" qaramar dariya ta saki "Da ba har zuci ba da tunu na koreka ai" maimakon ya amsa saiya jefo mata wata tambayar "Wanne babban baqo haka kukayi a companynku yau?" Dan tunani tayi kadan sannan tace "Gaskiya ban sani ba,saboda ba bangarena bane" kishi yakeji sosai da fargabar kar shahidan ta subuce masa saiya sanya idanunsa cikin nata sanda take za a wata kujerar da take kallon tashi "Haka manyan mutane ke zuwa wajenku?" Kafada ta dage "Wajensu dai,abune mawuyaci ni nasan zuwansu ko fitarsu,tubda ba sashe na bane saidai idan wata matsala da buqatar zuwa wajena ya zama dole" "Ina kishinki shahida" cak ta tsaya tana kallonsa,kalamansu sunyi shigen kama dana juna,ya tuna mata dashi dole saboda yanayin yadda yayi furucin,hakan ya sanya ta miqe kawai ba tare data samu abun fada ba "Kinsan sonki yake?" Ya jefa mata tambayar sanda take bakin dan qaramin fridge dinta tana ciro masa ruwa da lemo,saita waiwayo tana dubanshi,murmushi ya qwace mata "Wani abu makamancin haka bai taba shiga tsakanina dashi ba,kar ka saka komai a ranka,kai kanka shaida ne na wace shahida,abu mai sauqi ne samun hanya zuwa zuciyata kai tsaye har haka?" Maganar tata ta bashi qwarin gwiwa,sai yayi shuru yana nazarinta,harta dawo ta aje masa lemon da ruwan a gabanshi,yayin dashi kuma ya dire mata ledar daya shigo da ita "Ga abinci nan,inajin kamar kina da buqatarsa shi yasa dana tsaya naci nayo miki naki takeway din,don nasan ko xuwa nayi nace kizo muje muci taren ba zuwa zaki ba" ya fada cikin jefanta da magana,tasan yana jin haushin hakan,ita kuma ra'ayine sam bata dashi,sabida haka tayi murmushi kawai,ko yanzun ma ba zata iya cin abinci yana kallonta ba shina ya sani,amma duk da haka saiya soma bude mata ledar yana cewa "Kiyi haquri yau dai daya kici a gabana,saimu tattauna abinda ya kawonin,kada lokacin break dinki ya qare na shiga haqqin company",bai gama budewa aka sake bude qofar aka shigo,dukansu suka maida hankali ga qofar,saddam ne hannunshi dauke da ledar gidan abincin dake daura dasu,wanda shahida tafi order abinci acan,fuskarsa cike da murmushi ya nufosu kai tsaye ba tare daya dubi nuradden ba ya iso gabanta,dora abincin yayi saman na nuradden daya bude mata yace "ga favourite dinki nan", wani abu ne ya takorewa nuradden wuya,ya daga kai ya kalli saddam cikin fushi "Wanne irin rashin hankaline malam?" Dubansa saddam yayi "Da akayi me?" "Ta yaya zaka shigo kai tsaye ba tare daka nemi izni ba,sannan ka samemu zaune zata ci abinci ka dora wata ledar a sama?" A dage saddam yace "Matarka ce?" "Koba matata bace ina zaton tare ka ganmu" cikin halin ko in kula yace "Auto da sauqi abun,kaga kenan allurar cikin ruwa ce,mai rabo ka dauka" ran nuradden saiya kai qololuwar baci,hakan ya sanya shahida ta dubi saddam "Banason tashin hankali saddam,meye haka?" Baison nuradden ya gane cewa bai taba furta mata kalmar soba bare ya sake samun qwarin gwiwa,hakan ya sanya ya dubeta "Ba manufata na bata miki rai ba,sai anjima" ya juya ya fice. Sosai yake jin babu dadi cikin ranshi,saiya dubi shahidan "Shahida...tsorona da fargabata ta sake daduwa,inajin har cikin raina bani da tabbas idan har baki amsa min cewa ni kikeso ba kuma ni xaki aura ba" gaba daya sai lissafinta ya nemi dagulewa,batason ta dauki alqawarin da zai zame mata ciwo ko nauyin da wuya ta zaiyi wahala ya iya dauka,saboda haka cikin sanyin murya da kwantar dakai tace "Tsoron meye haka nuradden,ka kwantar da hankalinka don Allah". Duban nafisan yayi fuskarshi a hade" me kikayi haka kenan?,me yasa tun farko baki duba lafiyar atm din naki ba saida kika gama siyayyar?,bayan kinsan accnt din aya samu matsala sai xuwa gobe zai soma aiki?"langabe mishi kai tayi "Please anwar...don Allah kayi magana da mai kamfanin gaba daya,na tabbatar ka sanshi tunda naji kace bakason yasan ka shigo kamfanin,tunda ka bada rabin kudin yanzu zai amince ka aiko da saura idan ka koma office,Allah wannan sarqar nasha wahala na dade ina nemanta,kuma kanaji suma sukace dsign dinta kadai yayi saura,ba lallai idan na ajeta naje na dawo na sameta" idanunsa ya lumshe kaman bazaice komai ba,haka kawai yakejin kasala tunda ya tashi yau,hakanan zuciyarsa da jikinsa sam babu dadi,baice komai din ba ya fita daga wajen da kanshi ya taka zuwa sashen biyan kudi,suka tarbeshi don tunda ya shigo kamfanin suka gane waye,hakan ya sanya suketa nan nan dashi,daya daga cikin ma'iakatan ya yiwa magana yana son ganin rayyan "Ranka ya dade,oga bai shigo ba,amma babu damuwa zaka iya ganin rahama" dan shuru ya sake yana fidda wayarsa daga aljihunsa ya duba lokaci,sannan ya lalubo wata number ya kira,bata shiga ba,duka lambobin rayyan din basa tafiya,saiya sake kiran wata number din,ba jimawa aka daga,ya ambaci adadin kudin da yake buqata ya gaya masa inda zai kawo masa "In sha Allah yallabai ina hanya" daga haka ya maida wayar aljihunsa "Ai...ranka ya dade basai ka zauna jira ba,rahaman kawai zaka yiwa bayani shikenan zata shigar ne cikin kundin bayanan shiga da fitar kudi na kamfanin" lokaci ya kuma dubawa,shi kansa baison zaman,saboda jiransa da ake,banda ya riga da yayiwa nafisan alqawari kuma baison rashin cika alqawari da baiga abinda zai zaunar dashi har haka ba "Ba damuwa,bani number din office din" "To ranka ya dade" ya fada yana gaya mishi cikin sauri kai tsaye ba tare da an sanar da mai office din ba saboda sanin wayeshi baida buqatar sai sun hadashi da mai masa iso,a nutse ya juya ya soma takawa "Ina zaka?" Nafisa dake addu'ar Allah yasa su gama lafiya su fita lpy karya hutsance mata ta tambaya "Ki jirani" kawai ya fada yanayin gaba. Kallon number office din yayi sosai sannan yaja da baya ya kalli qofar,ya dora hannunshi saman handle din ya tura a hankali wanda hakan ya sanya basuji alamun bude qofar ba. *zafafa biyar na kudine,idan kika gani don GIRMAN ALLAH karki sharing,idan kina da buqata ki tuntubi wannan number* 07067124863 *ko kuma* 09032345899 *Alqawarin Allah* 2️⃣4️⃣ "Hankalina bazai taba kwanciya ba idan ba ganinki nayi a gidana a matsayin matata ba...shahida" ya kira sunanta yana miqewa zuwa gabanta,gab da ita ya zauna akwai kusanci sosai tsakaninsu,tanason sake ja baya ta kasa,ya saka hannunshi cikin aljihunsa ya ciro zoben rannan daya siya ya bata tabar masa abinsa cikin mota,ya bude gidan xoben ya ciroshi "Ki yarda mu qulla wanna yarjejeniyar tsakanina dake yanzu yanzu shahida,ita kadaice zata dan kwantar min da hankalina" bata ankara ba ya kama yatsanta yana ci gaba da roqonta,wani abu anwar yaji ya dakar masa tsakiyar kai,yayu yunqurin juyawa ya fice daga office din salin alin kaman yadda ya shigo,saidai ya gagara haka,ji yayi kaman an kafeshi idanuwanshi a kansu,ya gaza daga qafarshi bare ya juya ya fita din,da hanzari shahida tace "Sakemin yatsa nuradden...basai ka saka..." Bata qarasa kaiwa ba ya soma zura mata zoben,bansan ya akayi ba,baisan ta yaya ba ya tsinci kanshi da furta "Stop it!" Cikin tsawa da hargagu,idanuwanshi na sauya kala,wanda yayi sanadiyyar rashin shigar zoben yatsanta,dukkansu waiwayawa sukayi don ganin waye,ga tsammanin nuradden saddam ne ya dawo,amma sai yaga bashi bane,matashin saurayi ne da shekarunsa suka tasamma talatin da biyar,mai kyau kwarjini da cikar zati tsaye yana dubansu,idanunshi qyar kan nuradden din,yayin da idanun shahida ke kanshi,mamaki yaso daskarar da qwaqwalwarta,me yake nan?,me ya kawoshi?,yazo ci mata mutunci ne?,koko yazo tozartata cikin mutane ne kaman yadda yayi mata wancan karon,anya ma shine kuwa?. Idanunsa har yanzu nakan nuradden suna kallon kallon har zuwa sanda ya soma takowa zuwa cikin office din hannayensa soke a aljihunsa,cikin wata izza da taqama,qarfin gwiwa da qarfin halin da sam baisan yana nunashi ba muraran. Kafin ya qaraso shima nuradden din ya miqe tsaye yana dubanshi gami da jiran isowarsa,a qalla kusan minti daya sukayi suna duban juna,taqin dake tsakaninsu kadanne,cikin wata murya dake cike da ginshira isa da bada umarni yace "Kar ka sake gangancin aikata haka,idan ba haka ba?...." "Idan ba haka ba me?" Nuradden ya maida masa cikin zafi "You will regret it!" Ya qarasa cikin tsawa,murmushin baqinciki da kishi nuradden yayi,wai me yasa yayi saken da har yanzu bai mallaki shahida ba?,me yasa yayi bacci har akeson kawo masa farmaki? "Ina tunanin kana cikin masu sonta ko?" Ya fada yana waiwaya ya dubu shahida dake tsaye tana dubansu kaman wadda ta zama bebiya "To ka makaro,don kuwa shahida tawa ce,mallakina ce,hakanan baka da wani hurumi na shiga sabgata da ita,idan ma kace zakayi gigin shiga kunyace da nadama a qarshe zata riskeka,yadda ka ganmu haka zaka barmu,kayi kadan ka shiga tsakaninmu,baka da qarfi iko ko izzar rabamu,tarayyata da shahida ba muhallin shigarka bane,bama kaiba,har wani ma dake iqirari ko gigin cewa yana sonta" idanunsa ya lumshe kalaman nuradden na sauka cikin kunne da kwanyarsa,yau shi ake furtawa kalaman nuna iyaka akanta?,wani abu mai nauyi ya sauko saman zuciyarsa,ya bude idanunsa dai dai lokaci da shahida ke cewa "Please noor,wannan baikai abunda zaka bata ranka akai ba,nida kai mutu ka raba ne,qaramin dalili ko qaramin abu irin wannan yayi kadan ya raba tarayyarmu nida kai" tayi maganar kanta tsaye,direct daga zuciyarta ta hada kalaman,idanunta akanshi,sai ya qarasa bude idanun nashi gaba daya ya watsasu a kanta,ta kauda nata idon da sauri tana baiwa kanta qwarin gwiwa dason yin ramuwar gayya ko sau daya ne kafin wannan damar ta kubce mata,tana son ko sau daya ne yaji ciwon rai ya kwanta yana tuna kalamanta "Me kakeyi ne anwar?" Yaji tambayar tsakar kansa,kaman an sake doka masa wani abu,yadan runtse idonsa kansa na sarawa daya tuna ainihin abinda ya kawoshi office din "Assalamu alaikum,ranka ya dade...yallabai din ya shigo,ya nemi ma yin magana dakai" wata murya ta ratsasu duka su ukun,ya waiwaya yana dubanshi,ma'aikacin daya baro dazu ne a daya sashen,sai ya jinjina masa kai ya juya ma'akacin shima cikin girmamawa ya fita. Kallonshi ya maida kan nuradden ba tare daya dubi shahidan ba,ya murtsa yatsunsa sosai kaman mai neman attention dinsa,ya sakar masa murmushi sannan ya juya cikin wani irin sauri ya bude qofar office din ya fice. "Wash" shahida ta fada tana dafe kanta tare da duqawa kadan kaman mai ciwon ciki bayan fitar tashi "Subhanallah" nuradden ya fada da sauri yana nufota,da sauri ta daga masa hannu ta koma da baya ta zauna kan kujera,gabanta ya qaraso ya duqa yana tambayarta,ta nuna mishi kanta "Sannu,kiyi haquri don Allah,banzo nan da niyyar wani abu mara dadi ba,nazo ne muyi magana dake ta qarshe kuma ta fahimtar juna,bansa ya akayi duka hakan ta faru ba" "Ba komai,gida nakeson tafiya" "Muje na kaiki" ya fada cikin nuna kulawa yana miqewa,da gaske kan nata ke mata ciwlo sosai,saboda haka taja wayar office din,ta bada uzurin barin office dinta ba tare da lokacin tashi yayi ba. Cikin girmamawa rayyan ya tarbeshi,ya bashi hannu suka gaisa sannan yaja masa kujera ya zauna "Yallabai kai da kanka?,a maimakon kayi tafiyarka kawai saika tsaya bada excuse?" Murmushi anwar ya saki yana shafa kanshi dake masa ciwo "Doka ce bai kamata ace mune muke karyata ba" "Kasan yanzu tsarin ya canza,account dinka idan ya zamana kudi na yawan shiga da fita suna saka ido akanshi saboda yadda barayin gwamnati ke bude account kala kala suna aje kudaden al'umma da suka diba,qasarmu saidai addu'a kawai" "Wallahi yallabai,abubuwan kullum qara dagulewa suke,saidai fatan dacewa" hira suka shiga yi data shafesu,wanda bai jima ba sukayi sallama dash ya fito. A reception ya tadda nafisa yana kai kawo,tana ganinshi ta qaraso inda yake "Inata neman inda ka shiga...."bai amsata ba ya ciro waya da aljihunsa yayi kira yana buqatar qarin mota guda daya,sai daya kammala sannan ya dubeta "Zasu zo su daukeki,ni xan wuce inda da baqi,ki tafi da duka kayan da kika zaba babu matsala" Da ido ta bishi sanda yake takawa don ficewa daga katafaren wajen,tana mamakin sauyawarshi lokaci guda,iyaka tunaninta ka gaza ganowa,tilas ta samu waje ta zauna,lokaci lokaci tana duba lokaci gami da bin jama'ar dake kai kawo a wajen da kallo. Gefanta ta kalla kamar wadda aka baiwa umarni,take idanunta suka sauka a kanta tana takowa a hankali cikin nutsuwa nuradden na binta a baya,cak ta miqe tsaye tana ci gaba da kallonta har zuwa sanda ta fice daga ginin gaba daya,duk data ganta da wani amma sam hankalinta da zuciyarta sun kasa kwanciya,yanayin anwar daya sauya lokaci daya shi ya fado mata a rai,ko ita ya gani?,gabanta ya sake faduwa hankalinta ya tashi,itakam ta shiga uku,bata qaunar duk wani abu da zai hada anwar da shahida koda na bacin raine bare na mutunci,lallai tana buqatar qarin bayani,hakan ya sanya ta taka har zuwa reception "Sannu malam" ta fadi tana duban daya daga cikin receptionist din "Yauwa,kina da buqatar taimako ne?" Ya fada yana karantarta a nutse ganin kaman hankalinta bai jikinta,yaga kuma da wanda sukazo din tun dazun "Eh...don Allah tambaya gareni"kai ya gyada "yi tambayarki" duban hanyar da shahida tabi ta wuce tayi kaman har yanzu tana wajen sannan ta maida dubanta gareshi "Don Allah malam wannan matar data fita yanzun nan ita da wani,ma'aikaciyarku ce?" Shima qofar ya kalla sannan ya kalleta "Eh" yace yana gyada kai "Yauwa,don Allah ina take?,sannan tana da aure ne ko tayi aure?" "Kiyi haquri madam,gaskiya bama bada imformation haka kai tsaye game da duk wani ma'aikacin wannan kamfanin,idan kana buqatar ganinsa ne ka iya samunshi a nan"gyara tsaiwarta tayi,tana son sanin wani abu game da rayuwar shahidan,zataso qwarai ace a shekarun nan tayi aure kodon tabar mata anwar din ta samu nutsuwa ita kanta,ta daina fargaba kullum dare game da ita ko dawowarta rayuwarsu "Kaga ba wani abu bane,childhood friend dina ce,na jima ina nemanta ban samu ganinta ba sai yau,kuma nayi qoqarin na tareta muyi magana amma ta kubcemin bansan ina tayi ba" "Kiyi haquri doka ce ta kamfani" ba yadda batayi ba amma bata samu komai akanta ba,hakanan ta juya a sanyaye tana jaddadawa ranta dole ta sake nemo mima,tana shirin zama driban da anwar ya turo ya qaraso yayi mata magana kan ta taso su wuce,haka ta fita daga kamfanin jiki babu qwari tana danasanin rakiyar data roqi anwar yayi mata. *12:45 pm* Idanunsa qyar bisa rubutun dake kan screen din computer dinsa,ya gama tsara duk wata yarjejeniya ta kwangilar da zasu amsa,amma ya kasa fahimtar meye gyara meye daidai cikin rubutun bare ya tura,dogon tsaki yaja wanda kana ji kasan akwai abinda ke tafasa zuciya da tunzurashi,maimakon ya tura sai kawai yayi serving dinsa a draft,ya rufe cumputer da qarfi har screen din ya bada qass da alamu ya masa lahani. Miqewa yayi yakai ya kawo sau biyu tsakiyar dakin nashi,sannan ya sake juyawa ya isa bakin window din daki,ya zuge labulen gami da budesu gaba daya,iska mai sanyi irin ya daren daya soma nisa,darenma na damina ta soma shigowa,ya furzar da iska mai zafi daga bakinsa yana kallon sama da yau tayi fresh da taurari tare da fatan zafin da yake ji cikin zuciyarsa zai samu ya ragu,runtse idanunsa yayi karo na barkatai _ina tunanin kana cikin masu sonta ko,to ka makaro,don kuwa shahida tawace,mallakina ce,hakanan baka da wani hurumi na shiga sabgata da ita,idan ma kace zakayi gigin shiga kunya ce da nadama a qarshe zata riskeka,yadda ka ganmu haka zaka barmu,kayi kadan ka shiga tsakaninmu,baka da qarfi ko iko ko izzar rabamu,tarayyata da shahida ba muhallin shigarka bane,bama kaiba,har wani ma dake iqirarin ko gigin cewa yana sonta_ Kalaman nuradden suka dawo masa fes kamar ma a sannan yake furta masa su,kalaman da yau wuni sur su suka dinga qona mishi rai,suka hanashi dukkan wani sukuni da walwala,baya tunanin tsahon rayuwarsa bayan labarin mutuwar mahaifansa akwai kalaman da wani ya gaya masa da suka hanashi sukuni irin wannan,bai tabajin anci mutuncinsa ko anci masa fuska ba kamar haka "Shashasha,zaka ganne koni waye,zaka ganne qarfina isata da kuma izzata"ya fada afili zuciyarsa na yanke masa shawarar abinda ya kamata yayi. _please noor,wannan baikai abunda zaka bata ranka akai ba,ni da kai mutu ka raba ne,qaramin dalili ko qaramin abu irin wannan yayi kadan ya raba tarayyarmu nida kai_ Girgiza kansa sosai yayi zuwa hagu da dama,kalaman shahida na sake amsa kuwwa cikin kunnensa,ware idanunsa yayi murmushi ya subuce masa shi kadai "Zaki fahimci cewa nidin ba qaramin dalili bane keda shashashan masoyinki"ya furta sanda yake qoqarin rufe windows din dakin jin yayyafi ya soma sauka,yanajin bai kamata ya qyale nuradden ya furta masa wadan nan kalaman ba ya kuma ci bulus,bai kamata ya qyale shahida taci gaba da rayuwarta yadda taga dama ba,yadda ta tsaida duk wani aiki na zuciyarsa ya kamata itama tata zuciyar ta tsaya,bai kamata ace zuciyarta taci gaba da aikin da har xata karbi wani a matsayin masoyi ba bayan ta quntata tashi,ta kuma barta a rufe ruf,ta sanyata ganin baqi da baiken soyayya. A nutse ya hada abincinsa yaci sosai,don ya gama yankewa kanshi shawara,kuma shawarar ta karbu dari bisa dari cikin ransa,hakanan yaji duk wani nauyi dake qirjinsa ya sauka,walwalarshi ta soma dawowa,hakan kuma yana jin bai rasa nasaba da nunawa nuradden kurensa da illar lafazin da yayi a gareshi da zaiyi. 🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍 Kofin kunun hannunshi ya aje yana duban anty usaina "katsina zan wuce,ko kina da wani saqo wajensu inna?" Cikin mamaki take kallonshi "Katsina kuma anwar?" Kai ya gyada yana murmushi "Mamaki kikayi anty irin wannan kallo haka?" "Ai dole nayi mamaki,idan zaka katsina ba haka muka saba yi dakai ba,hasalima saina tursasaka kafin kaje,wani lokaci ma saika zabi lokaci da kanka,baka taba cemin zaka katsina haka katsaham ba sai yau,kodai wani abu ya faru acan ne kake boyemin?" Sai ta bashi dariya ganin yadda duka ta damu,har yanzu bata daina damuwa dashi da lamuransa ba "Anty na,babu wani daya faru,shikenan Allah baya shiryar da bayinsa duk sanda yaga dama,da da nake qin zuwa yanzu Allah ya shiryeni shikenan?" Kai ta kada "Allah yasa" "Yasa ma" ya amsa yana murmushi "Atamfofi ne kawai zan baka ka kaiwa innan kayan sallarsu dana saba basu,sai kuma sannu da jiki da zakace ina yiwa basira" "Gsky banjin zan samu zuwa gidansu basiran,saboda ayau nakeso na dawo" "Shikenan,mayi waya" ta fadi tana miqewa don shiga ciki ta debo masa saqon. Zuwa qarfe sha biyu na rana ya gama duk wata siyayya da yakanyi musu a sanda zaije katsinan waje kakanninsa wadda ta haifi mahaifinsa,kasancewarsu masu qaramin qarfi sosai,daya na raina ya dauki hanya,ya saki ajiyar zuciya yana qissima yadda abubuwan zasu kaya idan ya isa can.*zafafa biyar na kudine,idan kika gani don GIRMAN ALLAH karki sharing,ga mai buqatar siya zaki tuntubi wadan nan numbers din* 07067124863 *ko kuma* 09032345899 *Alqawarin Allah* 2️⃣5️⃣ Tafiyar awa biyu cif ta shigar dashi garin katsina,tuqi yayi lafiyayye cike da nutsuwa da kuma tunani kala kala,kai tsaye unguwar kakanninsa ya nufa. Yana qoqarin parking motarsa kawunshi modu ya fito da alama masallaci zashi saboda yadda yake dan hanzari,bai ganshi ba hakan ya sanya anwar kirayenshi,saiya waiwayo yana dubanshi cikin murmushi "Ikon Allah,yau kaine a garin da kanka?" Yana murmushi gami da kashe motar yace "Wallahi kawu,mun sameku lafiya?" "Lafiya qalau...mu shiga daga ciki" "A'ah kawu,gwara na soma yin alwalar tukunna" "To...to,shiga daga mana saika daura" "Ah ah kawi,kar naje su tsaidani mu rasa jam'i,idan mun idar ma shuga tare" daya daga cikin yaran da sukazo wucewa kawu modu ya qwalawa kira ya sashi ya shuga ciki ya debo musu ruwa a buta "Dan kuwa yau inna ta samu nayi,kazo yau zuwan ba zata sanda ba'a tsammaci ganinka ba" murmushu anwar yayi "Wallahi kawu,Allah ne ya kawo tafiyar haka"mintuna kadan yaron yafito dauke da 'yar matsakaiciyar buta,anwar ya karba suna dan taba hira da kawu madun harya gama alwalar suka rankaya zuwa masallacin. "kaine yau kuma?" Inna ta fada sanda yake qoqarin zama kan daya daga cikin kujerun dake falon,murmushi ya saki yana dubanta,sun riga da sun camfashi baisan dalili ba "Nine inna,kaman wanda bai zuwa?,kodai rikicin tsufa ya soma samunki ne kike zaton na jima sosai banzo ba?" Baki ta tabe tana rufe kwanon shan data gama shan ruwa a ciki "Idan ina rikicin tsufa na kasa lissafi ai kawunka ahmadu baiyi tsufan da zai kasa lissafi ba ko?" Dariya ta bashi sosai har sai daya danyi sannan yace "To shikenan yanzu Allah ya shiryeni,saime kuma?" Harararshi ta danyi "Allah yasa" "Amin inna" gaisheta yayi cikin mutuntawa ta amsa tana tambayarshi su anty usaina "Lafiya lau take,tana gaisheku dakyau" "Muna amsawa" daidai lokacin rashida 'yar kawu ahmadu ta shigo da kwanon abinci guda biyu,cikin girmamawa ta isa gaban anwar ta aje tana gaidashi "Duba cikin dakina ki dauko kwanon sha ki debo masa ruwan a randa idan zai iya sha" dariya ta sake bashi,ya fuskanci rikici yau take ji da gaske,saboda wancan zuwan da yayi tace ya zabi daya cikin yammatan 'yan uwa dake katsina ya hada da wdda zai aura a kano duka ya aura,yasan yau zai kashe bakin tsanya ne gaba daya shi yasa bai tada maganar ba ya barta take rikicinta "Sha kuwa harda shaye shaye...amma ba yanzu zanci abincin bane,zanje wata unguwa ne na dawo,saqonku na tsaya saukewa don na ragewa motar nauyi" duban rashida yayi dake zaune gefe tana kallonshi,ji take daman a gidansu yake "Inasu abdurrashid?" "Suna qofar gidan malam" "Maza jeki kiraminsu" da hanzari ta miqe ta fice kawu ahmadu ya sako kai hannunsa dauke da ruwan roba da lemon roba ya aje gaban anwar yana cewa "Garin yau ana zuga rana da zafi,ko rashin saukar ruwan sama ne kwana biyu ya saka haka oho?" "Ba mamaki kawu,kasan ko yaya hadari ua hadu ba ruwa sai gari ya bada zafi" daga haka kawun ya samu waje ya zauna suka shiga taba hira kan harkar noma da abinda ya shafi damina har yaran suka shigo. Cikin girmamawa suka gaidashi kowa na murnar ganinsa,ya amsa musu cikin kulawa ya dubi kawu da inna "Kawu xanje wata unguwa na dawo,Allah yasa zan sameka idan na dawo din,akwai maganar da nakeso mu tattauna" "Eh nima inason dan fita in duba shago na yau aike akemin,dalilin ma daya sanya ka ganni gida ban fita kasuwa ba kenan,amma ba jimawa zanyi ba,zan sallami yaranne na dawo" "To ma sha Allah,kafin sannan na dawo,inna zanje na dawo" "Allah ya tsare hanya" ta fada tana aje carbin hannunta sannan suka fita da yaran ya bude motarsa ya fito da duka kayan da yake nasu ne,yace sukai cikin gidan,sai daya tabbatar sun shige sannan ya tada motar ya fice daga layin. Sassanyar ajiyad zuciya ya fitar sanda yake gab da isa unguwar,qwaqwalwarsa na masa bitar abinda xaije ya aiwatar din,jiki da zuciyarsa tana gaya masa abinda zaiyi din shine dai dai,a nutse ya kutsa motar cikin layin,bai tsaya ba sai daya rage daura gida daya ya isa qofar gidan sannan ya kashe motar,zamansa yayi ciki yana tunanin ta yadda zai soma shiga gidan,daada zata ganeshi kuwa?,zata karbi zancansa?,zata yarda da qudurinsa?. Idonsa ya bude sosai sanda yaga saurayin daya saba aike zuwa gidan lokaci xuwa lokaci ya leqo ya koma da sauru,addu'a yake Allah yasa ya sake fitowa. Da hanzari sulaiman ya koma zuwa cikin gida da sauri yana kiran "Daada,daada" dattijuwar da ake kira da daadan wadda ke zaune cikin rumfarta tana daura busashshiyar kubewa ta daga kai kawai tana kallonshi har ya iso rumfar tata "Haba sule,wannan wacce iriyar dabi'ar banza ce haka?" "Daada wallahi saurayin nan da yake bani saqo lokaci lokaci nake kawo miki wanda kikace bakisan waye ba kema shi na gani a tsaye a qofar gida,kince duk randa ya sake zuwa na tsaidamiki shi shi yasa nake sauri na gaya miki kar yana bada saqon ya tafi" "Miqo min mayafina....duk abinda ya baka kada ka amsa kace masa lallai lallai ya shigo inason ganinsa" "To" sulaiman ya fada yana bata mayafin sannan ya sake fitowa da hanzari. A nutse yake nufo motar anwar,wanda shima ganinsa yasanshi sauke glass dinsa har sanda sulaiman din ya qaraso bakin window bakinsa a washe,anwar ya miqa masa hannu kaman yadda suka saba,yana Murmushi sulaiman ya miqa masa hannu sukayi musabaha,yana bala'in son musabaha da anwar din,koba komai zai gogi qamshinsa dake burgeshi yaji laushin fata sannan kuma hannunsa ya shaqi sanyin acn dake cikin motar kamar yadda sulaiman din ke cewa "Kwana biyu yallabai?" Sulaiman ya fada yana sosa kai,murmushi anwar din yayi sannan yace "Ko zaka yimin iso gurin mutanen gidan?" "Me zai hana?,dama daadan nason ganinka,ta roqeni ma kan don girman Allah yaudai ka shigo taga me mata aiken nan" murmushi ya kuma saki yana cire belt din jikinsa sannan ya maida glass din motar sama ya bude murfin ya fito,sai daya rufe motar sosai sannan sulaiman yayi gaba anwar din na biye dashi a baya. A bakin qofar gidan anwar ya coge yana duban soron gidan yana tuna wani abu daya taba faruwa a wajen shekaru shida baya,a shekarun baya da suka wuce idan aka ce masa zai sake taka soron saiya qaryata,amma dattako mutunci da qaunar da dattijuwar ta nuna masa a baya ya dawo dashi yaci gaba da nuna mata nashi karamcin,sulaiman ya dubeshi "Ka shigo mana,bismillah" kai ya kada "Shiga tukunna ka gaya mata zan shigo" anwar din ya masa kwarjini da yawa don haka ya kasa musa masa,ya saka kai zuwa cikin gidan karo na biyu. "Tace ayi maka iso" sulaiman din ya fada yana duban anwar,a nutse ya sanya qafafunsa soron yaci gaba da takawa bisa jagorancin sulaiman. Qarqashin bishiyar dake gefe daya na tsakar gidan tabarma ke shimfide,nan sulaiman ya nuna ma anwar,ya sabule saucikin dake qafarsa ya ajesu sannan ya isa saman tabarmar ya zauna,dai dai lokacin da daada ke fitowa daga rumfarta hannunta dauke da kwanon sha wanda ke cike da ruwan randarta mai sanyi,idanunta akan anwar din harta qaraso,duk da ganinta dashi sau biyu ne tak a rayuwa,a lokacin da yafi haka qarancin shekaru da rashin cikar xati da kamala. Hannu yasa ya amshi kwanon sanda take shirin xama ya ajeshi gabanta,saida ta zauna sosai sannan ya soma gaidata "Mun sameku lafiya?" "Lafiya qalau alhmdlh....yaro kaike hidima damu haka tsahon shekaru uku amma baka taba tsayawa na ganka ba ko wani cikin 'ya'yana ya ganka ba bare yayi maka godiya" murmushi yayi har fararen haqoransa suka bayyana idanunsa a qasa,sai taga ya sake koma mata anwar din sak,anwar din da har kwanan gobe takeson tasan ina yake?,meya rabashi da jikartata,amma har yau idan zata tambayi shahidan sau dari bazata tada kai ta bata amsa ba,harsai ta gaji tayi shuru "Amma saurayi....sai naga kamar anwaru ko?,anwarun shahida" daga kai yayi yana duban dadan tare da jinjina ma qoqarinta data iya ganeshi "Shine daada" gaba daya fuskarta ta washe da fara'a sosai,wani irin farinciki ya mamayeta,tunda taga anwar din a wancan shekarun Allah yasa mata qaunarsa,ya shiga ranta sosai,dai daikun ranaku ne da zasu zo su shude bata tuna dashi ba "Ma sha Allah,Allah abin godiya,kana nan dama anwaru?,har kana iya zuwa guna ka aikomin da saqo amma ka kasa shigowa na ganka mu gaisa ko sau daya ne?,haba anwar,me muka yi maka haka?" Murmushin dai ya sakeyi "Kawai haka Allah ya tsara mana daada,shi ya raba ganawarmu sai yanzu daya qaddara haduwar tamu" "Wannan haka yake" ta fada tana jinjina kai cike da gamsuwa,har yanzu bakinta ya kasa rufuwa "Ashe daada baki manta dani ba?" Baki ta kama tana cewa "Ta yaya zan manta dakai anwar,bani bama hatta da qannen mahaifin shahida sun kasa mantawa dakai,kaiba irin mutumin da za'a manta dashi bane anwaru,gashi shekara kusan uku kanamin alkhairi ba tare daka bari nasan cewa kai bane....kai sule,zo nan zoka amsowa anwaru damammiyar fura da nono" tafada tana qoqarin kunce daurin habar zaninta dake daure da kudi,da sauri anwar ya dakatar da ita "A'ah daada,don Allah karki wahalar da kanki" dakatawa tayi da abinda take "Karka tsaidani anwaru,nasan yana daya daga cikin abinda kafison sha rahama ta gayamin tun lokacin ban manta ba,wannan shine kadai abinda nakejin zan iya maka" saiya qyaleta ta kunce kudin ta baiwa sulaiman ya amsa ya fice. "Wanne laifi muka yi maka haka anwaru daka gujemu haka?,ka bace mana bat,ina tsaka da murnar jikata ta samu nagartaccen miji,tunda har naji isma'ila Allah ya jiqan rai na yawaita maganarka na tabbatar da nagartarka,dana ganka kuma saina sake tabbatarwa lallai nagartaccen ne kai,ita kuma waccar almurar koxan kwana kwana tambayarta ba zata cemin kanzil ba" gyara zamanshi yayi sannan a nutse yace "Dukkan abinda ya faru a rayuwar bayi ba shakka muqaddari ne daga Allah,kisa a ranki hukuncin ubangiji ne bacewata daga rayuwarku..." "Gaskiya ne" ta amsashi tana gyada kai,sadda kanshi qasa yayi sosai "Zuwa nayi ki bani aurenta daada" kyakkyawan murmushi ya subuce kan fuskar dattijuwar,cikin ranta tana godewa Allah tare da hamdala,tayi tsammanin shahidanta ta rasa nagartaccen anwar din nan,sai gashi ya dawo a sanda basu zata ba "Wannan ai tsohon zance ne anwar,shahida ai taka ce" wani abu ya tsaya masa a wuya,zayafi kowa farincikin jin hakan da ace a baya ne sanda shahidan take shahidan anwar ba yanzu data zama ta kowa ba "Na sani daada,amma wannan karon nazo ne a bani auren shahida da gaske ba kamar a bayan ba" "Indai wannan kake da buqata kana iya komawa da aurenta,bamu da haufi kanka anwaru,koda mahaifin shahida na raye nasan haka zai fadi" hakanan yaji wani sasauci a ranshi da zuciyarsa,wanda ya danganta hakan da nasarar da zai samu ce ta nunawa shahida da saurayinta cewa shiba sa'ansu bane takowanne fanni "Amma duk da haka,ka jira zuwa gobe zan kira kawunnanta na tabbatar musu da aurenka da shahida" "Na gode qwarai da gaske daada da wannan karamci,amma inason kimin wata alfarma guda daya" "Ba zata gagara ba insha Allahu anwaru"sassauta muryarsa yayi "mun samu sabani da shahida wanda shi ya zama silar rabuwarmu na wadan nan shekaru,na dawowa shahida saidai yadda ta dauki zafi fiye dani ta tabbatarmin ba zata taba karbata a matsayin miji ba..." Yadan dakata a ranshi yana istigfari kan qaryarda yayi "Inason don Allah dada a boyewa shahida gaskiyar wanda ke neman aurenta,inason na gaya mata da kaina mu sasanta kuma kanmu ba tare da kowa ya shigo ciki ba" qanqan da ido daada tayi cikin masifa tace "Wato ja'ira tasan komai shi yasa ko zaka kwana tambayarta saita dinke bakinta ko?,yoni aida ka barni da ita don dakalin qofar gidansu mu gauraya da ita,ja'ira tana tafe kaman daben masallaci kai kace ba ita bace..." Duk yadda yake jin ransa saida fadan dadan ya bashi dariya,ya danne yana cewa "Ki haquri daada karki tasarmin ballina"qwafa taja "Don dai kace haka ne amma da goben zan gaya mata da kaina,idan yaso ta iskoni katsina ta hukunta ni" daada na tsaka da fadan dake baiwa anwar dariya yake kuma sakashi nishadi sabida nasarar daya samu sulaimanu ya dawo da damammiyar fura mai sanyi data sha suger,sosai anwar ya sake ya dinga sha suna hira da dadan tana bashi labarai wanda anan yaji labarin rasuwar abban shahidan,sosai jikinsa yayi sanyi qwarai,ya dinga jin babu dadi har cikin ransa,ya dinga tuno abubuwa da dama tsakaninsa dashi,yana qaunarshi sosai hakanan yana ganin girmansa,kaman dan cikinsa ya daukeshi ba suruki ba,yayiwa daada ta'aziyya sosai. Bata barshi ya tafi ba saida tayi masa irin danwaken da yakeso,wanda ta taba yi masa zuwansa ziyara wajenta na farko,baici da yawa can ba saboda tuna wani lokaci da yayi a baya,hakan yasa yaji cikinsa ya cushe,sai bayan la'asar sannan yayi mata sallama ya wuce. Daga nan gidan wani abokinsa ya wuce,bashi ya baro wajensa ba shima sai gab da magariba,koda ga koma unguwar kakannin nasa yana aje motarsa ya wuce sallah masallaci,acan suka gamu da kawu modu suka rankayo gida bayan an idar. Inna na zaune cikin rumfarta iskar fankar solar da anwar ya hada duka gidan na kaiwa da kawowa a falon,bata qure fankar can ba hakanan batayi qasa da yawa ba,hakan ya sanya iskar ke kadawa dai dai "Ina ka tsaya haka daga cewa yanzu zaka ka dawo?" Sosai yakejin gajiya da kasala yadan motsa fuska "Wallahi inna..nima ban zaci zan dade haka ba" dauke kai tayi ta kalli jijarta bushira dake xaune tana kallo falon inna tace ta miqawa anwar tuwon darenshi da mamarsu ta aje masa,cikin sabbin fulasai kaman da plates masu kyau harda ruwan sha a jug kaman yadda suka saba masa duk sanda yazo. Qasa ya sauko ya soma zubawa da kanshi duk da cewa ba wata yunwa yakeji sosai ba,amma saboda innar kar tava dazu baici ba yanzun ma haka taji ba dadi "Naje gidan daada ne,kakar shah....." Saiya kasa qarasa fadin sunan "Rahama" ya qarashe fada da ainihin sunanta,wanda baya jin tsahon zamanin da yayi da saninta ya taba ambatar ainihin sunanta "Wacece haka?" "Yarinyar da zan aura..na taba baki labarinta shekara shida baya,wadda ta kasa zuwa gaidaku?" Murmushi inna ta saki "Shahida wai?,yarinyar da usaina ke bamu labari wadda ta damu kan rabuwarku?" Kai ya gyada yana ci gaba da ci tuwon "Ma sha Allah,amma saidai wani hanzari ba gudu ba,ina maganar yarinyar can nafisa 'yar wajen alhajin nan?,ina cewa duka duka watanni aurenku ya rage?,don dama zuwan naka nake jira naji ainihin sati nawa ya rage" "Maganar nafisa tana nan,kuma watanni uku suka rage" "Anya anwar?,kana nufin auren mata biyu lokaci guda?" Inna ta fada tana kallonshi,kai ua gyada "In sha Allah inna,tunda Allah ya hore saidai a tayamu addu'a" shuru ta danyi kadan kafin daga bisani tace "Shikenan...Allah yayi jagora,ubangiji ya kore abinqi" "Ameen"sai daya hadiye lomar bakinsa sannan ya sake cewa "Na shaidama kakartata gobe su kawu zasu je su tambayamin izini a wajensu,to gashi ban samu na sanarwa kawun ba,kuma a goben nakeson na koma saboda na baro ayyuka,ban tsammaci ma yau din zan kwana ba" "Aiba wata matsala bace,ai ado kawai za'a yiwa waya(qaninta kenan)a sanarwa,shehu da dahiru suna kan hanya yanzu muka gama waya,sunje duba ta'annabi,idan suka shigo sai kuyi maganar". Bashi yabar gidan ba sai qarfe goma na dare,sai daya tabbatar komai ya kammala ya kuma tsaru sannan ya nufi masauki,yana fitowa daga wanka yana shirin kwanciya wayar nafisa ta shigo,ya gaji tubus duk da yaga tarin miscal dinta niyyarsa saida safe zaya kirata saboda bacci yake da buqatar yi,dole ya daga bayan ya kwanta sosai saman gadonshi "dear,ina ka tafi ne?,muhsin yace min baka gari" "Katsina" "Me kuma kajeyi can dear?" "Kin manta ina da dangi ne a can?,naje gaida su inna,sannan kuma na gabatar da wani dan aiki" "Au haka ne,me yasa baka hadani da ita ba na gaidata?" "Idan kin matsu kina iya karbar lambarta tunda tana da waya,da can baki gaidata ba saida nazo zakice na baki?" A shagwabe tace "Am so sorry dear,ka turomin number din nata saina kirata" "Saidai gobe idan Allah ya kaimu,yanzun kam na gaji bacci nakeson nayi" da haka ya samu ya sallameta ya aje wayar tunani nakai kawo cikin ranshi,kenan yanzu idan lamarin ya tabbata mata biyu zai aure kenan?,juya lamarin yayi cikin zuciyarsa,koda wasa bai taba kawowa kanshi xai auri mata biyu ba,sai kuma tunaninsa ya juya kan shahida da nuradden,zayaso yaga fuskar kowannensu a sanda labari ya isa kunnensa,murmushin mugunta ya saki yana mirginawa hannun damanshi ya soma karanto addu'ar bacci bayan ya kunna suratul baqara cikin wayarshi ya rage mata sauti sosai. *ga mai buqatar littafin da zan soma bayan kammala rubutun alqawarin Allah,zaije youtube yayi searching SAUTIN HIKIMA,akwai jan rubutu na SUBSCRIBE daga qasa,zaka dannan sau daya zai koma baqi,sai kiyi screenshoot ki turawa wannan number da zataso daga qasa,za'a sakaki a group din littafin da yardar Allah* 07038670166 *zafafa biyar na kudi ne,idan kika gansu don GIRMAN ALLAH karki sharing,idan kina da buqata ki tuntubi wannan numbers din* 07067124863 *ko kuma* 09032345899 *Alqawarin Allah* 2️⃣6️⃣ 🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍 Washegari qarfe tara na safiya ya gama shirinsa tsaf cikin yadinsa na maza mai kyau da tsada,yayi masifar kyau yadda hularshi ta zauna kanshi sosai kawai ya isa ya gaya maka ya hada jini da kanawa,hakanan yake jinsa wani sawai kuma fayau dashi,ya qarasa reception yayi maida musu key din dakinsu ya sallamesu ya wuce zuwa gidan inna. Falon inna ya wuce kai tsaye bayan ya isa gidan,ya tadda kawu dahiru da kawu modu suna rumfar innar suna hira da alama anan sukari karin safe tare,cikin girmamawa ya gaida inna sannan ya gaidasu yana zama daura da ita,ita ta yunqura da kanta ta hada masa lafiyayyen kunun tsamiya da sukayi da wainar gero,cikin marmari yake ci suna ci gaba da hira dasu kawu dahirun,yana kammalawa kawu shehu ya iso,basu wani jima ba suka miqe gaba daya zuwa gidan daada,shi yaja motar,kawu shehu da yake shine babbansu yana gaba,kawu dahiru da kawu modu kuma suna baya. Sanda suka isa gidan sha daya na safe har ta dan gota,hakan yasa suka tadda kawun nan shahida sun riga da sun iso,sulaiman shi ya musu jagora kamar ko yaushe zuwa cikin gidan "A'ah....shehu,kardai kacemin yaron dake neman shahida dan wajenka ne?" Kawu ummaru wanda yake yaya ne ga mahaifin shahida ya fada yana dariya sanda sukayi musabaha da kawu shehu "Yaro na ne,dan wajen qanina ne mai rasuwa" " "Kai ma sha Allah,amma naji dadin abun nan qwarai,to ai abunma duk na gida ne,ita kanta daadan ma bata sani ba,inaga basai anje anata kaiwa da kawowa ba,ayi komai kawai a gama lokaci guda" "Kana ganin babu wata damuwa ko matsala?" "Haba shehu,kaine fa,babu wata damuwa wallahi,dama meye burinmu banda muga yaranmu sunata aurensu". A ranar gaba daya kawu ummaru suka amshi kudin auren shahida harda sadaki,aka kuma tsaida lokacin biki ko ince daurin aure a wajen maza watanni uku masu zuww,wanda yayi dai dai da watannin da aka tsaida a farko na daurin aurenshi da nafisa. Yana tsaye jikin motarshi qafafunshi amatuqar sanyaye,irin wannan lokaci ya jima yana mafarkin zuwanshi shekara shida baya,ya qiyasta yanayin farinciki da zai samu kansa a duk sanda Allah ya tabbatar masa a wancan lokaci har baisan sau naya ya qiyasta din ba,sai gashi abun yazo a bahagon yanayi,yanayin daya kasa tantance wani iri ne,farinciki ne ko baqinciki?,kansa ya daga a hankali sanda ya soma jiyo muryoyin su kawu dahiru da alama suna sallama ne dasu kawu ummaru. Ranar kasa shiga yayi wajen daada duk da yaso suyi sallama,haka ya sake dibansu kawu shehu ya sauke kowanne a gidansa sannan suka wuce wajen inna shida kawu modu. Murmushi ne kawai ke fita a fuskar daada sanda 'ya'yan nata ke gaya mata yadda komai ya kasance "haba,ba banza ba nutsuwar yaron ta yimin,naji ya shiga raina sosai,ashe jinin gidan malam usman ne(sunyi zama na maqotaka ne tun iyayensu da kakanni,zaman da sukaji dadinsa,kunsan mutanen daa akwai riqo da zumunci da kuma girmama alaqa da dangantaka komai qanqantarta),na godewa Allah,Allah yasa albarka ya kuma tabbatar da alkhairi" "Amin daada" dukkansu suka amsa suna jin dadin hadin "Yanzu daada za'a sanar dasu kenan?"kai ta girgiza "qwarai kuwa,ka shaida ma ita uwartata,sannan kuma ka kira can gidan hishamun a shaida musu,duk da cewa shi ya sani amma sai a gaya masa an karba harda kudin auren da sadaki,gobe idan ka dawo kai ummaru ka kiramin rahamar ka hadani da ita" "To shikenan daada" ya fada yana lalubar wayarshi dake aljihun rigarsa. *_GUDUN QADDARA guzurin taddata....._* Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke wadda ta fito tun daga zuciyarta,ta sauke idanunta kan tafin hannunta tana bitar maganganun nuradden daya gama furta mata ayanzu,dauta dauko na anty zubaida data gama gaya mata jiya,kusan maganganun nasu sunyi kamanceceniya da juna,a yanzu bata da wata mafita bata da wani uzuri kaman yadda anty zubaida tace mata,imma dai ta baiwa nuradden dama wa imma ta sallameshi hakanan ya daina wahala,ko ga ummanta madai wannan karon ta matsa qwarai kan ya kamata ta tsaida manemi tayi aure,tunda dai abinda ya farun da ita bawai qarshen rayuwarta ya kawo ba,saima sabon babin rayuwa daya sake bude mata,idan ta sallami nuradden bata jin akwai wani qwaya daya cikin samari dama masu auren dake kara kaina akanta da zata iya kwatanta rayuwarta ta wanzu tare da tashi "Na amince nuradden....Allah ya zaba mana abinda yafi alkhairi" hannayensa gaba daya ya hada ya rungume a qirjinsa yana lumshe idanunsa,wani farinciki da baisan a wanne mizani zai dorashi ba ya shiga dawainiya dashi,sai kawai ya zame saman gwiwoyinsa a gabanta "Shahida,ki fadamin me kikeso na baki ladan wannan kyakkyawan albishir din naki?" Kai ta kada kawai qwalla na taruwa a idanunta,murmushi mai cakude da alamun son yin kuka na kubcewa saman fuskarta "Babu abinda zaka bani face nace kayi qoqari karka sa na sake yin nadama da dana sani a rayuwata karo na biyu" "Koda baki roqi haka ba wannan duty na ne" da ido kawai ta dinga bishi yadda ya rasa inda zai tsoma ranshi ya dinga bata mamaki,harta daina mamaki ma abun ya soma bata dariya,sai daya tabbatar ta dan saki ranta sannan yace "Yanzu yaushe za'a kai maganata katsina?,shine abu daya da zai sake sawa in samu nutsuwa a raina,in kuma tabbatar na yiwa duk wani dake da buri ko hanqoran mallakarki na masa fintikau din da dole ya haqura" murmushi ya qwace mata,tasan cewa burinsu daada kenan,tana da tabbacin indai nuradden ya isa katsina to magana ta qare,don ba wani lokaci zasu ja ba ba tare da sun bashi ita ba "Karka damu duka abun bana sauri bane,next month za'a dauki azumi,sai kayi haquri mu barwa salla" fuska yadan bata "Gaskiya yayimin nisa,saidai idan har kin yarda ne ni zan kaiki,qafarki qafata"hannu ta daga tana murmushi "Shikenan naji,sai kuma me?" "Aikin gama min komai nikam,yau nafi kowanne namiji dake fadin duniyar nan sa'a" yayi furucin a sanda yake kallon sararin samaniya cikin madaukakin farinciki. Qarfe tara ta shiga gida don bata wuce hakan a waje,duk da dama ba fita take wajen kowa ba,kusan nuradden din ne kawaima yaci qwallo da har take fita ta saurareshi,ga mamakinta saita tadda anty zubaida zaune saman kujerar falon hannunta daya tallafe da kanta,gwiwar hannunta saman hannun kujera,ba kowa falon sai ita kadai,kallon wani series da suke haskowa a mbc take,sallamar shahidan ya sakata dagowa da sauri tana dubanta "Anty,yau yana sameki a nan?" Qoqarin daidaita kanta tayi "To ya zanyi,uncle dinki yace lallai lallai naga shigowarki na tura masa ke" murmushi tayi tana zama hannun daya kujerar dake daura da anty xubaidan "Hala anty kinkai masa qarata ne kan nuradden?,to kisha kuruminki,na riga na baiwa nuradden dama,zuwa nan da qaramar sallah xai isa gasu daada in sha Allahu" ta qarashe tana duban anty zubaida,don tasan ta gama mata abinda ranta keso kenan,sai taga ta murmusa kadan "Ya za'ayi nakai qararki?,koda nakai dinma ai Allah abinda ya hukunta dole shi zai faru ko?,yanzu dai kije yana falonshi yana jiranki" sai data miqe sannan tace "Anty muje tare mana don Allah" "Ba ruwan zubaida" ta fada da hanzari,dariya ta baiwa shahidan yadda tayi maganar kamar wata baquwar uncle hisham din,saita juya ta wuce tana cewa "Ai shikenan anty". "barka da dare uncle"shahida ta furta sanda ta nutsu a gaban uncle hisham,ya sauke takardar da yake dubawa ya kalleta "barka kadai shahida,sai yaushene zakuyi hutun naku kamfanin?" "Eh to uncle gaskiya ina zaton sai sai dab da sallah,saboda wannan season ne na yawaita da kuma cunkoson custumers" kai ya jinjina sannan ya danyi shuru kamar mai nazari kafin daga bisani yace "Daada ce keda buqatar kije,to ban sani ba ko xaki samu ko weekend ne kije kiji kiran nata na meye?" "Shikenan uncle babu damuwa,yau alhamis ranar juma'a tunda da wuri muke barin kamfani saina shirya naje,idan yaso ran lahadi da yamma saina dawo" "Hakan yayi,shikenan dama kiran" "To uncle saida safe" ta fada tana miqewa "Allah ya bamu alkhairi". A inda tabar anty xubaida nan ta taras da ita,saita daga kai tana kallon shahidan,ganin babu sauyin fuska tattare da ita ya tabbatar mata uncle din bai gaya mata komai ba,zai turata ne kaman yadda dada ta buqata,sallama anty zubaidan tayi mata ta wuce wajen uncle din,tabar shahidan na sake sabon xaman ganin maimaicin wani shiri,tana mitar baccin wuri da yau su faruqu sukayi suka barta ita daya,don bata jin dadin zaman falon ita kadai. A nutse yake murza motarsa tamkar wanda baison barin titin har zuwa sanda ya isa unguwarsu anty usaina,cikin nutsuwa ya faka motar sannan ya kasheta ya fito,cikin wani irin karsashi yake takawa zuwa cikin gidan,haka kawai yake jinsa kaman mai yawo cikin farin gajimare wanda shi kansa baisan dalilin haka ba,yana shirin saka qafarsa kan step qwaya daya da zai sadashi da falon gidan ya jiyo muryar sa'ida na kiranshi,a nutse ya waiwaya,sai ya tsaya hannayensa zube a aljihun wandonsa yana dakon qarasowarta. Aladabce ta rusuna tana gaidashi ya amsa yana dubanta "Daga ina kike?" Sai data dan waiwaya sannan ta dawo da dubanta wajensa "Uncle....gidansu anty shahida,ummi ta aikeni na amso mata saqo?,kasan me uncle?" Kai ya girgiza yana dubanta "Na ganta mafa tazo wajen mamansu,uncle kaganta kuwa kaman ba ita ba...."takun data jiyo ya sanyata tsuke bakinta,cikin minti daya anty usaina ta bayyana,akwai 'yar tazara tsakaninsu kadan,ya juya ya dubi sa'idan "Wuce kafin tazo ta fara miki jajayen idanuwa" maganar ta baiwa sa'ida dariya har sai data qyalqyale da dariya sannan ta soma takawa don wucewa ciki "Wato kin dawo shine kika samu waje kika tsaya kina masa wannan dan banzan surutun naki ko?"kai ta gyada " a'ah ummi,nima fa yanzu na shigo"harararta tayi cikin ranta tana qissima lallai ya zama dole ta kwabi sa'ida,donta fuskanci kanta yana rawa tanason ta lalata mata plan "Wuce,saura kuma naga qafarki a wajen" da hanzari sa'idan ta wuce,anty usaina ta bita da kallo harsai data shige sannan ta dauke idanunta,dai dai sanda anwar yake tsaye daga inda yake,a nutse yana karantar duk wani motsi na anty usaina,murmushi ya kubce masa,ya gama ganeta tsaf,ya gama karantar tsoronta,ya kuma gane me take boye masa,saidai baisan nata shirin ba,koma meye nata shirin shi zai mata ba zatan da bata tsammata ba,idonta ta sauke a kanshi,tana tsaye har ya isketa "Yaushe kai kuma ka dawo?,daga wuni daya sai kwana har biyu?" "Tun jiya na dawo,wasu sabgogi ne suka riqeni,duk yadda naso in shigo baiyiwu ba" bata ce komai ba ta bude qofar falon ta shiga yabi bayanta. Bayan sun gama gaisawa suka shiga hirar mutanen garin daya baro ya gaya mata kowa lafiya sannan yace "Kin tambayeni lafiya na tashi zuwa katsina ba yadda na saba ba" ya fada yana duban anty usainan dake yankan farcenta "Eh ai dole,koma waye daya sanka yadda kaqi jinin zuwa katsina dole yayi mamakin tafiyar taka" "Neman aure naje,na nema kuma sun bani" saita dakata da abinda take tana kallonshi sosai,saidai bata ga alamun wasa tattare dashi ba,hakan ya sanya ta gyara zamanta "Auren wa kuma anwar" "Shahida" ya fada kai tsaye kuma a taqaice,wani abu taji ya tsarga mata gaba daya ilahirin jikinta,saita aje rezar gefanta ta zauna sosai tana kallon anwar,tana jin wani farinciki na ratsata,da gaske ko mafarki take,shahidan da take tayi masa farautarta?,sun shirya kansu ne koko yaya abun ya faru?abinda ya shiga tsakaninsun dama baiyi girman da zasu kasa daidaita tsakaninsu ba amma har ya zama silar rabuwarsu na tsahon shekaru?,ya zama silar lalacewar soyayyar da kowa yake sha'awa,duka cikin lokaci kadan ya karanci tarin tambayoyin dake yawo a idanunta,qaramin murmushi yayi yana jin wani ciwo cikin ranshi,inama ace yadda kowa ya kalli lamarin hakan yake "Karki damu anty,na rage miki aikin da kiketa yunqurin yine" ya qarasa fada yana son ganin yanayin fuskarta,ajiyar zuciya ta sauke ta zauna sosai zaman dake nuna ta soma samun nutsuwa "Zuciyata ta kasa karbar rabuwarka da ita ne anwar,inaji a jikina bai cancanci ku rabu ba" "Shikenan ai....yanzu dai anty abinda nakeso kici gaba da zama a yadda ta sanki har zuwa lokacin da komai zai daidaita" sai yanayin fuskarta ya sauya "Komai zai daidaita kamar yaya?,kana nufin baku daidaita ba ka nemi aurenta a haka?" Kai ya gyada mata "Eh kusan hakanne" "Me hakan ke nufi anwar?" "Babu komai,kema hakan kikeso mu kasance tare fa?" Eh...amma zanso ace hakan ta faru ne a lokacin da duk wani sabani dakw tsakaninku ya zama babu shi" "Karki damu anty" shuru tayi tana nazari,yayin da zuciyarta taji ta mata sanyi sosao,ta dinga jin farinciki na shigarta,tana ji babu shakka abune mawuyaci anwar ya samu soyayya irinta shahidan,abune mai wahalar gaske yaso wata kwatankwacin nata son koda shi yana qaryata hakan tasan wani dalili ne nashi na daban daya rufe masa idanu har yake qaryata hakan "Nafisa fa?" Ta sako mishi zancan da take ganin kamar ya manta ne "Ba abinda ya sauya tsakanina da ita" "Tasan da wannan maganar?" "Zata sani anty,zata sani idan lokacin daya dace ta sani yayi" "Shikenan,Allah ya shige gaba ya kauda dukkan abunqi"mai makon ya amsa saiya soko wani zancan "cikin satin nan ne tafiyata,ina ganin ki lissafa duk abinda kuke da buqata don bazan dawo ba saina gama wata biyun gaba daya,aiki ne mai muhimmanci a gabana" "Babu wata matsala,don bana tunanin zamu buqaci komai harka dawo din" 🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍 Ranar juma'a qarfe biyu na rana suma gama shirin tafiya katsina,ga mamakinta sai uncle hisham ya hadasu ita da haidar da faruqu,ganin haka huda itama ta turje saita je,hakan yasa ta hada kayanta duka suka bar gidan sai anty zubaida kawai. Tafiyar tayi mata dadi sosai saboda su faruq,har Allah Allah ta dinga yi su isa,basu jima sosai saman hanya ba suka isa katsina. Sosai daada tayi farincikin ganinsu su duka,ta rasa inda zata sanyasu,kowannensu haba haba takeyi dashi,saida suka ci suka sha suka nutsu qarfe uku na yammaci,a lokacin su faruqu sun fita kewaya 'yan uwa dake nesa,shahida tace ta gaji ba zata iya fita ba sai gobe,jin haka yasanya huda itama cewa bazata bisu,nan tayi kwanciyarta saman cinyar daada suna hira abinsu. Duban shahida daadan tayi bayan ta maida nutsuwarta sosai "Rahama" ta kirayi ainihin sunanta,saita daga kai daga danna wayar da take ta dubi daada "Yau kuma sunan nawa kike sha'awar kira" maimakon ta maida mata yadda suka saba sai tace "Maida hankalinki jikinki ki aje wannan wayar" jin hakan yasa ta sauke wayar saman cinyarta tana kallon daadan "Abinda yasa nace a turomin ke,inason gaya miki cewa mun bada ke kuma mun karbi kudin aurenki" *KIYI SUBSCRIBING,KI TURA WANNAN NUMBER DON SAMUN DAMAR SHIGA GROUP DIN SABON LITTAFINA DA ZAN SOMA RUBUTAWA BAYAN ALQAWARIN ALLAH IN SHA ALLAH* 07038670166 SAUTIN HIKIMA https://youtu.be/H7M7h6l6wNM *zafafa biyar na kudi ne,idan kika gani don GIRMAN ALLAH karki sharing,ga mai buqata zata tuntubi wadan nan numbers din* 07067124863 *ko kuma* 09032345899 *Alqawarin Allah* 2️⃣7️⃣ Murmushi shahida tayi tana kada kai "Haba tsohuwa,wai gajiyar da kukayi dani yasa har kin soma min irin wannan wasan?,toki kwantar da hankalinki idan ma bugun cikina kike,ana gama azumi aka sallace zan kawomiki dandasheshen angona" "Ni banga miji ba kamar anwar" daada ta fada cikin ranta,amma a sarari saita sake hade fuskarta sosai,ta yadda shahidan zata fuskanci bada wasa take mata ba "Ki dakatar dashi,don hatta sadakinki yana hannu,kuma watanni uku ya rage daurin aurenki" cak ta tsaya ta nutsu sosai tana son karantar maganar daadan,ta fidda gaskiyar dake cikin maganar "Sadakina fa daada kike cewa kun karba?" "Idan baki yarda ba tunda ni sa'ar wasanki ce,saiki jirayi wadanda kike yadda da nasu zancan anjima suzo su shaida miki" tana kaiwa nan ta yunqura ta miqe ta nufi qofar fita,hakan yasa shahida ta miqe zumbur cikin tashin hankali harta manta da wayarta dake seaman cinya ta cimma dadan ta ruqo hannunta,muryarta na rawa tace "Daada....wa kuka baiwa ni?,nidai nasan ba wanda na bawa dama,da nura mukayi magana shi kuma sai bayan sallah mukayi dashi zaizo" juyowa tayi ta kalleta "Mai rabo muka bawa,zama zamuyi mu zuba miki ido sai sanda kika ga damar aure sannan kiyi?,to sakalcina baikai nan ba...idan zaki nutsu ki fahimceni ki nutsu idan ba zaki nutsu ba kuma kici gaba da shiriritar saina qyaleki cikin duhu" dakiya da dukkan juriya ta gayyato,ta soma kokawar maida qwalla da abinda ya tare mata maqoshi tana cewa "Na nutsu,ki gayamin don Allah" komawa tayi ta zauna inda ta tashi,itama shahidan ta koma ta zauna idanunta qyarr kan daadan,kamar ta fiddo zuciyar daadan ta karanta komai haka takeji "Yazo yana neman aurenki,dan mutunci ne yaro da mai mutunci kirki da karamci,bashi da wani aibu ko abun qi,hakan ha sanya ya turo magabatansa,kawunki ummaru ya sanshi kawun nashi gaba da baya,hakanan muma din akwai wata 'yar alaqa tsakaninmu duk da bamai qarfi bace,babu wata matsala hakan yasa aka amshi harda sadakinsa,karki damu karki daga hankalinki zaki sanshi zaizo ya sameki kuga juna,ke kanki kinsan shekarunki a yanzu sun isa ace kina gidanki harda albarkar zuri'a ma,idan baki aure ba shahida yanzu sai yaushe?" Kuka ta fashe sosai dashi,don tana ganin itace hanya guda daya da zata iya samun mafita da ita "Don shekaruna sun soma tafiya wanda har yau basu rufa ashirin da biyar ba kawai daada saiku amshi kudin aure harda sadakin wanda ban sanshi ba?,bansan daga inda yake ba?,bani na turoshi ba?,ba soyayya ko sabo tsakaninmu?,wallahi wannan zubarmin da mutunci kawai da ajina kukayi" ta qarashe cikin kuka wanda yasa huda ta tsaya sak tana kallon shahidan,daquwa daada ta watsa mata "Kinci qaniyarki,makaranta muka zubar miki ba aji ba,wanne aji kike nema bayan na gidan aure?,ba gata muka yi miki ba?" Haushi ya ciyota,saita sake saka kuka "Wanne irin gata daada haka ake gata tsakani da Allah?,kaman na rasa mashinshini?,kawai sai mutum yazo muku sama taka ku karbeshi?" "To yanzu aisai ki hadamu ki zanemu uwarmu,mun miki laifi ko?" Ta fadi tana fiddo idanu tana kallon shahida,wani tashin hankali takeji da bacin rai qwarai,idan taci gaba da magana batasan me zai fito daga bakinta ba,daboda haka ta gwammace ta barwa daada falon kawai,haka ta miqe ko gabanta bata gani ta shige dakin. Wani irin tashin hankali ta tsinci kanta ciki,saitakejin kaman da wasa daadan ke mata zata dawo tace tsokanarta take,saidai har akayi magariba su faruqu suka dawo shuru daadan bata bi ta kanta ba,sanda suka dawo suma suka leqo dakin da take,dukkansu tambayarta suke me ya sameta da suka sameta a kwance,saidai ba wanda ta baiwa amsa,tana jiyo muryar daada daga falo tana cewa su fito suzo ita ta basu amsa,haka suka juya suka fita,faga haka basu sake dawowa dakin ba suma. Har qarfe goma na dare tana kwance ita daya cikin dakin cikin wani yanayi,nuradden ya jirata yafi a qirga ta kasa dagawa saboda tashin hankalin da take ji cikin zuciyarta,saida goma ta gota daadan ta shigo dakin da kanta ta taddata,ta aje kwanon abincin hannunta sannan ta samu gefan gadon da shahidan ke kai ta zauna "Tashi ki dauki abincinki kici" shuru tayi mata kaman bata ji me take cewa ba,ta sani sarai taji din,tsohon halinta keson motsawa saboda an mata zancan an bada ita "Saboda an hadaki da miji nagari za'a miki aure shine kika yiwa abinci yajin aiki?,kusan ni natsaya tsayin daka kan maganarnan saboda ganin nagartar da yaron yake dashi,sannan kuma ina da yaqinin cewa bamuyi miki zaben tumun dare ba,uwa uba nasan ko ba dade koba jima sai kinyi dariya kin godemin da irin mijin dana zaba miki" tana ganin daadan tazo gabar da zatayi magana saboda haka ta miqe ta zauna sosai tana gyara rigarta data sabule "Duk naji dada na fahimceki,amma daada ina ake irin wannan auren?,ban sanshi ba bansan waye ba,bance ina sonshi ba bani na aikoshi ba kawai sai a daukeni a bashi ni?,ta yaya za'a karbi sadakina abawa wani aurena ban sani ba?" "Saboda mun isa dake" lallabawa take ta samu a kwanceta daga tarkon da aka sakata,sabida haka tayi qasa da murya "Na sani daada,amma don Allah ina roqon alfarma ku maida masa kudinsa,nuradden ya jima yana tare dani,ya dade yana bibiyata,sannan kuma shima yana da dukkan nagartar da za'a iya baiwa mutum aure saboda ita" "Duk nagartarsa bazai kama qafar wannan ba" mamaki duka ya cika shahidan,wai waye wannan da daada ta kafe kai da fata taketa faman yabo da kodashi haka?,taqi ji taqi gani saboda shi?,ko wani cikin 'yan uwanta nanan dake qwaqwar sonta dai daadan ta baiwa ita? "Taya kika sani?,bafa sanin nuran kikayi ba?" "Eh ban sanshi ba kuma bana son na sanshi,bazamu zama qananun mutane ba magana an riga da an gamata,ki sauko ki dauki abincinki kici" daga haka daadan ta miqe tayi ficewarta,alamar dake nuna cewa ba qaramin abu bane zai saukar da ita daga kan bakanta ba. Ajiyar zuciya ta saki cikin tashin hankali idanunta na tara sababbin hawaye,ta zurafafa tunaninta tana neman dukkan hanyoyi da take ganin zati ba don sauke daada daga qudurinta,tunaninta yakai ya kawo,babu wata qofa guda daya,tunda kowa kusan da umarninta yake aiki,mafita daya ce ta dage da nacin roqonta kawai kafin nan da ranar lahadi ko Allah zaisa ta janye tun maganar batayi qarfi ta watsu a dangi ba. Ba irin tunanin da bata kawo ranta ba kafin bacci yayi awon gaba da ita. Koda ta idar da sallahr asuba wani baccin ne ya sake kwasheta,saboda rashin samun isashshen bacci da batayi na daren jiya. Cikin baccin taji kamar muryar huda na tashinta,ta bude idanunta da qyar wadanda sukayi nauyi ta zubesu kan huda "Anty shahida,kizo inji kawu ummaru" tuni ta nemi sauran baccin idanunta ta rasa shi,saita zauna dangwargwar saman gadon tana duban shahida "Yaushe yazo" "Bai jima da zuwa ba,muna cikin cin abincin safe" "Kice masa ganinan" ta fada cikin fargaba,miqewa tayi ta dauki hijabinta dake saman jakarta ta zura,ta tsaya gaban mudubi ta kalli fuskarta gabanta na faduwa,tasan halin kawu ummarun sarai,yafi kowa zafi cikin kawun nan nata,Tana dage labulen tana addu'ar Allah yasa koma da meye yazo ya zamana mai sauqi ne. Cikin girmamawa ta gaidashi ya amsa,shuru yadan biyo baya kafin daga bisani ya ciro kudade daga aljihunsa ya zube kusa da ita "Nasan tuni daada tayi miki bayanin cewa mun karbi kudin aure da sadakinki,to gasu,inaso nayi magana da mahaifiyarki kan meye ya dace ayi da kudin" da sauri ta dago kai tana duban kawun idanunta ya cika taf da qwalla sannan ta sauke qasa,ya karanci me takeson cewa,don tuni daada ta gaya masa "Rahama,karki wani ce zaki damu,yaron ya cancanta,banda haka babu abinda zai saka mu bashi ke,muma muna sonki fa" cikin muryar kuka tace "Kawu,wallahi bansanshi ba,bani bace na turoshi,akwai wanda muka riga mukayi alqawarin aure dashi,harma yana shirin zuwa gaidaku" murmushi kawun yayi "Rahama,indai cancanta take sa a baiwa mutum aure wannan yaron ya cancanta,matar mutum kabarinsa,Allah baiyi shi wancan din shine mijinki ba,saboda haka kiyi addu'a kawai,Allah yasa hakan shine alkhairi a gareki" kai ta sadda kawai qwalla na silalo mata,tana jin kawun harya gama maganganunshi yayi sallama dasu yayi gaba,miqewa tayi kawai ta fita daga falon zuwa tsakar gida ta wuce bandaki,ta tara ruwa tayi wanka sannan ta sake zuwa ta wuce daada zuwa daki. Cikin minti talatin ta gama shirinta gami da hada kayanta tsaf,daidai lokacin daada ta leqo dakin tana mata magana ta fito ta karya,saita ganta saqale da jaka tana shirin fitowa,binta tayi da kallo "Ke kuma meye hakan?" "Gidan zan wuce,tunda nazo na karbi saqon naki" baki ta tabe tana dubanta "Allah ya raka taki gona,dadin abundai bake kadaice jikata ba,kuma su bayau zasu tafi ba,saikin dawo" duban daadan tayi,zuciyarta na mata zafi matuqa idan ta tuna abinda suka mata,yanzu kamar ita da hankalinta da wayonta da komai amma ace an baiwa wani ita?,waninma da batasan waye ba?,tsabar qarfa qarfa kota bakinta ba'a jiba aka amsa harda sadakinsa?,ranar daurin aure kawai suke jira kenan?,saita juya da kayanta ta koma cikin daki ta zube gefan katifa,tana jin wayarta na rurin shigowar kiran nuradden amma bata da qarfin gwiwar dauka. Dole ta haqura da tafiyar sabida wani zazzafan zazzabi daya saukar mata wunin guda,ba ita ta samu sassauci ba sai washegari da safe,kafin sallar azahar ta sake shirin tafiya,wannan karo daadar bata hanasu ba,suka shirya tsaf suka wuce,saidai tafiyar bata musu dadi ba kamar yadda tayi musu a zuwansu,saboda gaba daya hankalin shahida bai kansu,sosai ta shiga tunani mai zurfi ita daya,har suka qaraci surutansu suka haqura. 🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍 Kwana biyu da dawowarta tana gaban system dinta tana tura saqon daukar uzurin ba zata samu damar komawa office bakin aikinta ba anty zubaida ta shigo dakin,saita samu gefan shahidan ta zauna sanda ta gama tura saqon ta soma kashe system din,cikin qaramin lokaci gaba daya shahidan ta sauya ta wani sukurkuce kamar wadda akace an daura auren nata,ta sauya gaba daya ta auri zaman daki,duk wata hira da walwala data dawo da.ita cikin gidan yanzu ta janyeta,kamar wadda ke shirin komawa 'yar gidan jiya,anty zubaida batace da ita komai ba saidata gama ta ture computer din gefe sannan ta kira sunan shahidan,daga kai tayi tana dubanta "Yanzu shahida daga maganar karbar kudin aurenki saiki ki tsangwami kanki haka?,kina neman maida kanki 'yar gidan jiya?" Kamar mai jira sai kuwa ta soma hadiyar zuciya,idanunta suka soma yaji tare da tara qwalla,ta bude bakinta tana jin wani abu ya tokare mata wuya cikin muryar kuka tace "Haba anty,ko waye aka yi masa haka anty ba'a kyauta masa ba,ta yaya za'a badani kamar an gaji dani,yanzu an siya min mutunci kenan?,kina gani fa shi wanda akace an bawa din bansan ko waye ba,uwa uba yau kwanaki nawa shi dinma bai nemeni ba,qafa da qafa kiran waya ko text,me kike tunanin sun jawomin kenan anty?" Ta qarashe maganar da sigar tambaya idanunta kan anty wanda gab suke da ziraro da qwallar dake cikinsu,kai anty zubaida ke kadawa,ita kanta abun bai mata ba amma uncle hisham ya dakatar da ita kan babu ruwanta,duk wata hanya da zata bi tasha cikin uncle din ya gaya mata na ko waye donta gayawa shahidan ta samu dan relief ya tosheta "Haka zaki haquri shahida,qaddara ta riga fata,amma sai nake ganin idan da laifinsu kema da naki laifin,kinyi wasa da damarki qwarai,shekara nawa nuradden na bibiyarshi ki bashi dama kikaqi,idan da ace kin bashi dama da tuni yanzu wani zancan ake ba wannan ba,nidai bani da wani abunyi bani kuma data cewa saidai ince kiyi haquri kiyita addu'a kawai,nima kuna zan tayaki" kai kawai ta kada,ta bude baki zata ce wani abu wayarta ta sake kadawa karo na barkatai,tare idanunsu yakai kan wayar,nuradden ne,sai anty zubaida ta kalli shahidan "Babu hujja ko alfanun boye masa komai,kawai ya kamata ace ya sani ni a ganina" tana kaiwa nan ta miqe don ficewa ta bawa shahidan damar amsa wayar. ******* ****** ********* A hankali ya miqe daga gaban qaramin akwatin mai lambobin sirri yana sauke nannuyar ajiyar zuciya,duk sanda ya budeshi koda wani abu zai ciro daga ciki saiya tayar masa da wawakeken mikin dake danqare a zuciyarsa,cikin nutsuwa wadda ta cakudu da kasala ya isa gaban akwatinshi ya jefa abinda ya dauko daga ciki ya rufe zip din akwatin sannan ya saukeshi daga saman gadon ya soma janshi har zuwa falonshi. Saman dining ya isa ya zauna a nutse ya soma duba abinda aka dafa din,rabin hankalinsa nakan wayarshi da haka ya zuba abincin ya soma ci,knocikin din da akayi shi yaja hankalinsa,saiya dan daga kanshi yana duban qofar,kafin yace komai aka turo aka shigo,nafisa ce,sanye cikin doguwar riga ta atamfa da madaidaicin mayafi,idanunta bisa kanshi yayin daya dauke nashi idanun ya maida kan abincinsa,hakan yasa tayi hanzarin tunawa da batayi sallama ba,saita dan koma da baya tayi sallamar sannan taci gaba da takowa cikin falon a hankali tana nazarin falon,falon ya jima yana burgeta,duk da wannan shine ganinta dashi na uku,saboda haidar din bai lamunci ta dinga zuwa masa gida ba bayan shi kadaine cikin gidan. Bata tsaya ba har sai data isa dining din,fuskarwa a washe take kallonshi,ta dora jakarta saman teburin tana kallon abincin da yake ci,saita zari spoon ta saka cikin farantin nashi tana cewa "Goodmorning boss" idanunshi ya daga yana janyewa daga cin abincin yana cewa "Morning...me kika fito yi yanzu?" Zama tayi saman kujerar dake daura da ita,ta langabe wuya tana kallonshi bayan ta aje cokalin hannunta "Rakiya mana dear....uhmm....ji nake kaman na bika wlh,kaika janyo mana kaga da tuni tare zamuyi tafiyarmu babu me tuhumarmu" saiya yagi tissue yana goge bakinsa,ya cilla dan qaramin dust bin dake gefanshi yana miqewa daga saman kujerar "Amma dai kinsan akwai wadanda zamu fita tare,kuma duka maza ne,bai kuma kamata ki shiga cikinsu ba ko?" Itama tashi tayi tana daukar jakarta,cikin hanzari harta cimmasa tasha gabanshi "Amma dear,tafiyar wata biyu fa banan kusa bane,ni a wajena ba laifi bane don nayi maka rakiya" *ga mai buqatar sabon littafina da zan fara bayan alqawarin Allah,sai yaje youtube yayi searching SAUTIN HIKIMA,da zarar sunan ya fito akwai rubutun SUBSCRIBE da jan rubutu,ki danna shi sau daya zai koma black,saikiyi screenshot ki turo zuwa number dake qasa,za'a saki a group din in sha Allah* 07038670166 *Ziyarci tasharmu ta youtube don samun qawatattun litattafan hausa,masu qunshe da zallar soyayya darasin rayuwa da kuma nishadi* 👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽 https://youtu.be/H7M7h6l6wNM *Alqawarin Allah* 2️⃣8️⃣ Bata tsaya ba har sai data isa dining din,fuskarwa a washe take kallonshi,ta dora jakarta saman teburin tana kallon abincin da yake ci,saita zari spoon ta saka cikin farantin nashi tana cewa "Goodmorning boss" idanunshi ya daga yana janyewa daga cin abincin yana cewa "Morning...me kika fito yi yanzu?" Zama tayi saman kujerar dake daura da ita,ta langabe wuya tana kallonshi bayan ta aje cokalin hannunta "Rakiya mana dear....uhmm....ji nake kaman na bika wlh,kaika janyo mana kaga da tuni tare zamuyi tafiyarmu babu me tuhumarmu" saiya yagi tissue yana goge bakinsa,ya cilla dan qaramin dust bin dake gefanshi yana miqewa daga saman kujerar "Amma dai kinsan akwai wadanda zamu fita tare,kuma duka maza ne,bai kuma kamata ki shiga cikinsu ba ko?" Itama tashi tayi tana daukar jakarta,cikin hanzari harta cimmasa tasha gabanshi "Amma dear,tafiyar wata biyu fa banan kusa bane,ni a wajena ba laifi bane don nayi maka rakiya". Bai amsata ba saida ya ciro wayarshi ya amsa kiran dake shigowa sannan ya maidata ya daga kai ya zuba mata idanunsa da kullum kwanan duniya ke sanya nafisar sake dilmiya cikin so da qaunarshi,kallonsa kawai yakansa taji wani sanyi da sassauci cikin ruhinta,taji tamkar an mata rahama "Waye ya kawoki?"wuya ta noqe tana jefa masa wani kallo da take fata ko yaya yayi tasiri a zuciyarsa "da kaina na taho"hannu ya miqa mata,ta kalleshi tana son qarin bayani "Bani muqullin motar"ba musu ta zuge jakar tata ta dauko muqullin ta miqa masa,saiya sakashi a aljihunsa sannan yace mata muje. Tana gaba yana bayanta,a hankali yakai idanunshi kanta,saiya lumshe idanu yana tuna wani lokaci can baya,lokacin da yake mata rakiya zuwa gida,lokacin da take sadakar shinkafa da wake,ya tuna randa ta zura da gudu tabar mishi botikinta saboda ya furta mata kalaman soyayya,murmushi ya sube masa cikin qiftawa da bismillah kuma murmushin ya bace bat,bacin rai ya maye gurbinsa,ya hadiyi wani abu mai tauri yana girgiza kai,hotunanta ita da saurayin suna yawo a idanunshi,fuskar saurayin daya ajeta a mota har yau taqi barin idanunshi,ya dunqule hannunsa daya yana jin wani abu mai dumi na zagaya jikinsa,har kwanan gobe takaicin dukan da baiwa saurayin yake ba,amma yaci alwashi...yaci alwashin dashi kadai ya barwa kansa sani...... Inda yaje aje motocinsa ya nufa,ta bishi a baya,ya bude daya daga cikin motocin ya mata alama da hannu kan ta shiga,wani dadi ya kamata,yau din taga kamar wani dama dama yake da ita,ta rabeshi ta shiga ta zauna,maimakon shima ya shiga sai taga ya maida murfin motar ya rufe,ya duqa bakin window din idanunshi cikin nata,wanda hakan ya sake narkar da ita ya kashe mata jiki,qamshinsa ya cika mata hanci,kamanninsa suka fito sosai,cikin daddan muryarshi yace "ga driver nan zai kaiki gida,karki sake irin wannan fitar da sassafe haka,zamuyi waya kafin na tashi,motarki kuma zansa a kawo miki ita,sai Allah yayimin dawowa?" Kai kawai ta gyada,ta kasa cewa komai saboda gaba daya jikinta a mace yake dakyau da kwarjinsa,baya yaja ya miqawa drivern muqullin,yana tsaye har suka fice daga gidan,ya saki ajiyar zuciya yana duba agogon hannunsa,da yana da yadda zaiyi ya ragewa nafisa sonshi ko yadda ta damu dashi da yayi,sam baiso ta zura kanta da yawa kamar yadda yayi,shi a ganinsa wannan shine babban kuskure ko gangancin da mutum zaiyi a soyayya. ***** ****** ******** A hankali take takowa zuwa qofar gidan nasu,sanye da dogon hijabi har qasa mai hannu,kallo daya zaka yiwa fuskarta kaga yadda ta fada,ta dashe hakanan tayi fayau,duk yadda anty zubaida taso ga kwantar mata da hankali kan lamarin hakanan taji hankalinta ya kasa kwanciya,tana ji ba auren dole za'a mata ba,a'ah nata ya xarce wannan ya koma auren qarfa qarfa. Tunda ya hangota ya fito ya tsaya yana jiran qarasowarta,ji yake kamar ya isketa ya tarbeta,tana isowa suka hada idanu sai taji zuciyarta ta karye gaba daya,tausayin nuradden din ya kamata fiye da ita kanta,don dama ita tuni ta sallamawa soyayya bare tayi mata kamun da zata jigata aduk sanda ta tashi gwada izzarta,saidai ko babu komai sabo mugun abu ne hakanan turken wawa ne,da hanzari ya zaga ya bude mata daya seat din ya kalleta "Shiga ki zauna,kar tsaiwar tayi miki yawa" karon farko ba musu cikin kasala ta zagaya ta shiga din,saidai duka qafafunta na waje,shima saiya zagaya ya shiga mazaunin direba yabar qofar a bude. Idanu ya zuba nata gaba daya yana hasaso ta ina zai soma daukar rashinta,sam yana jin bazai iya ba,a hankali ta bude baki zatayi magana ya daga mata hannu ya tsaidata "Karkice komai shahida,maganar gaskiya bazan iya rabuwa dake ba,bazan iya rabuwa dake ba shahida matuqar ba aure aka daura miki ba,zanci gaba kuma da yaqi tuquru don ganin na sameki,koda hakan na nufin zanje wajen daada da kaina na roqeta tabarmu tare ne" da hanzari ta bude baki "Ina nan ina gwada sa'ata,kuma ina saka ran samun nasara,idan hakan ya cimma tura zan sadaka da ita daadan taci daga bakinka" ajiyar zuciya ya sauke yana kallon shahidan,wani qaunarta yake sakeji,baya fata ko sau daya ya sakejin kalmar rabuwa a tsakaninsu. Tsahon mintina ashirin suna tare suna baiwa juna baki kafin yayi mata sallama yace zai wuce amma ta dakaceshi a waya,hakanan suka rabu kowa jiki babu qwari musamman nuradden din. 🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍 Cikin satittikan da suka biyo baya suka fara zama watanni shahida tayi dukkan iya yinta don ganin daada ta janye qudirinta,an maidawa koma waye kudinsa da suka amsa amma abun yaci tura,bata taba ganin daadar ta dage kan abun haka ba irin wannan,sannu a hankali taji ta soma tsanar kona waye wannan,da wanne irin abu haka yazo da tashin farko za'a dauketa sukutum da guda a bashi ita?,sannan ta kowanne fanni kowa ya cije yace sai anyi?,hatta da anty zubaida ma yanzu ta soma bin layi,balle ummanta data ga kamar ma tafi kowa murna da farincikinda abun,don ko rannan data je gida bacin rai da baqinciki ya hanata wuni,wai umman har tarin biki take mata,hakanan su mubina har sun fidda anko,ita bata ma sani ba,sai 'yan uwanta 'yammatan dake sa'anninta daketa kiranta kan zasu sayi anko akwai a gida wajen umma?,ko sau daya ta kasa amsa musu saidai taja tsaki ta kashe wayar. Batun ya tsaya mata qwarai a rai,harta lura ta soma ramewa,bacin ranta da har zuwa lokacin wanda ake budurin a kansa bai gabatar da kanshi a gareta ba barema tasan waye,hakan ke nuna ma bata da wani daraja ko muhimmanci a wajensa kenan?. A haka aka shiga azumin ramadana,Allah ya taimaketa batayi sake da kwanakin ba,ta tsawaita ta kuma nace da addu'ar neman mafita wajen ubangiji babu dare ba rana,duk ta zama wata sukuku da ita,sauqinta daya wurin aiki sun bata hutu data tura cewa bata da lafiya,ba zata koma ba har sai bayan sallah,ko daya taqi samun nutsuwa cikin ranta,bacin rai fargaba da qunci da batasan na meye ba gaba daya sun cikata. Da sallah kuwa tana ganin su mubina dasu faruqu suka shirya tafiya katsina tace saisun dawo bata zuwa,ita lallai sai daada ta fuskanci fushi take da ita,daadan dako a jikinta wai an mintsini kakkausa,hakan na sake qona ran shahida,an shiga wata na biyu har ya cimma qarewa a yadda ma taji suna fada biki saura sati biyar amma bata yaba sashi a qwayar idanunta ba?,itakam taga yadda za'ayi wannan abu haka take yawaita fada cikin ranta,saitakejin ma abun kamar wasa,kamar bamai yiwuwa bane,hakan ya sanya ta sake baiwa nuradden qwarin gwiwa da kyautatan zaton lamarin bazai dore ba. 🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍 *_SO DANGIN MUTUWA_* Satu guda cif cif da sallah ranar litinin daada ta buqaci shahidan tazo ranar juma'a mai zuwa,qememe tace bata zuwa ba inda zata,mubina ce 'yar isar da saqon data ji abinda tace bata ce komai ba harta gama wuninta tayi tafiyarta gida. Qarfe tara da rabi na dare suna gama waya da nuradden ta maida wayar chargy ta dawo tana cire hijabin jikinta don taji dadin kwanciya tana son saurarar littafin JARRABI na huguma (littafin da nan gaba kadan zaizo muku a SAUTIN HIKIMA TV dake youtube,idan baki subscribe ba ki hanzarta zuwa kiyi don kar a fara babu ke) ta gyara daurin dankwalinta don tafijin dadin kwanciya,sosai salon labarin ya qayatar da ita shi yasa da an dora sabon shiri a sautin hikima bata missing. Anty zubaida ce ta turo qofar dakin ta shigo itama da hijab har qasa a jikinta,da alama kayan baccine a jikinta "Baki kwanta ba?" "Shirin kwanciyar nake dai,jarrabi nakeson in saurara kafin na kwanta din" murmushi kadan anty zubaida tayi "Kin ganni nima kundin qaddarata nake saurara,ya zamemin jiki kullum saina saurari sabon episode idan sukayi updating" "Na koya miki ko anty?" Shahida ta fada tana dariya "A'ah,ai littafanne idan kika fara saurara baki da zaman lafiya saikinji qarshen kowanne labari" "Gaskiya kam", zama anty zubaida tayi kan kujerar mudubin shahidan " dazu mubina tazo tace miki daada tace kije daga ran talata zuwa juma'a shine kika ce ba zakije ba?"yanayin fuskar shahida yadan sauya,sam ita yanzu ko zancan katsjna ma bataso ayi mata "Anty to me zanje nayi mata kuma?,bayan ta gama tsara duk yadda ranta yakeso?" "Amma bai kyautu ta kiraki kiqi zuwa bako?,tunda kinsan cewa koma meye daada ba maqiyiyarki bace masoyiyarki ce,kome zata yi zatayishi ne sabida tana sinki ba don ki cutu ba" shuru sukayi gaba daya,anty zubaidan na karantar shahida,yayin da shahidan ta shiga tunanin me zata je ta yiwa daada?,amma tana ganin kuma wannan kamar wata dama ce da zata kaimata nuradden ya gwada sa'arshi ko Allah zaisa haqarsa ya cimma ruwa,kai ta kada "Shikenan,zanje ran alhamis" "Yauwa,dadai yafi" ta fadi tana miqewa "Anty don Allah idan kin fita ki cewa faruqu yayimin transfer din data,data din nan satinta daya da ita nakejin littafin,donma ba cirar data din ake ba ai da tuni ta qare" "Yana falon uncle,zan masa magana" ta amsa mata tana fita a dakin. _kuyi manage da wannan_ https://youtu.be/_XVqJSBXVPI *Alqawarin Allah* 2️⃣9️⃣ Da hanzari ta koma jikin wayarta ta cirota,ta koma gefan gado ta rubuta saqo ta tura masa,saita kashe wayar don ta tabbatar ta barta akunne nuradden bazai barta tayi barci ba,tunda damar da yake nema kenan gashi ya samu. Washegari tana kunna wayartata kuwa kiransa ne abu na farko daya soma shigowa,yadda taji muryarshi ya kasa zaune ya kasa tsaye kaman ance masa an bashi ita dinne,tun a ranar suka shirya yadda tafiyar zata kaya,ya nemi su tafi tare tace sam,ya sameta kawai a can ran alhamis din,murmushi ya saka mai sauti "Bakison hawa motata kwata kwata shahida,don know why....koda yake babu komai saura qiris in sha Allahu,Allah yakai damo ga harawa dai" murmushi kawai ta saki tana yanke kiran,bazai gane bane,baisan irin illa tabo da masifar da shiga motar wani ta sabbabawa rayuwarta bane,tabon da har yanzu bata daina jin dacinsa ba yana zaga jiki da rayuwarta gaba daya. 🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍 Qarfe sha biyu da minti arba'in da biyar tayi sallama falon daada,hasina 'yar gidan qanin abbanta ce zaune ta daga kai cikin mamaki da farinciki ta amsa sallamar "Mutan kano,yau a gari?,ni har nayi fushi fa,wai shahida kizo har garin nan kwanaki amma ki kasa leqani,gaba daya kin watsar dani kaman wadda ta miki wani mugun laifi?" Murmushi shahida tayi tana zama kan daya daga cikin kujerun gami da cire mayafinta ta aje gefe,iskar fankar da aka qurewa gudu cikin falon tana kadata gami da shigarta tako ina sakamakon zafin da ake zabgawa da kuma uwar rana "Kiyi haquri hasina,ba'a son raina ba wallahi,wannan tsohuwr ce ta min laifin daya shafeku,amma kiyi haquri zanzo in sha Allahu" cikin murmushi hasina ta tabe baki "Kedai bansan me ya dameki ba,koda yake an auna arziqi da aka samu ma kika ci gaba da zuwa katsinar da kika yiwa yajin aiki wajen shekaru hudu" murmushin da baikai har zuci ba shahida tayi tana cire agogon hannunta "Yanzun ma mawuyacine idan ban koma muku yajin aikin ba ai" ta qarshe fada wani abu na takore mata wuya idan ta tuna kasassabar dasu daada suka aikata mata,saidai takanji sassauci idan ta tuna tana da hope a yau,qasa qasa da murya hasina tayi "Hala ta kusa kwatanta miki abinda taso yimin kenan?" Kallonta shahida take ba tare da tace komai ba tana son jin qarin bayani "Wai in gaya miki matarnan daga zuwa mata hutu shikenan tasa aka mata kiran saurayina qafa da qafa wai ya kamata ya fito hakanan,wannan shekarar ta shirya aurar da jikokinta,wai basai ya dorawa kanshi wata dawainiya ba yayi abinda addini kawai yace masa ya wadatar Allah ya sawa auren albarka" tagumi da haba shahida tayi kawai tana jin wannan bayanin,ita kenan ta mata dakyau ma data amshi kudin aure,amma gwara hasina da ita sau dubu "Hasina kukan dadi kike,kinsan me daada tayimin?" Kai ta girgixa tana duban shahida "Kudin aurena da sadakina suka amsa gaba daya ba tare da na sani ba,kuma ba tare da nasan waye zan aura din ba,kawai don bincikensu ya basu managarcine suke ganin ya dace dani" idanu waje hasina ta fito dasu tana duban shahida,kafin tace wani abu suka jiyo maganar daada daga tsakar gida wadda ta fito da wanka ne tana fadin "Da kika shigo kika bar akwatin naki rana na duka waye zai dauke miki" dole kowanne yaja bakinsa yayi shuru harta iso falon,saita kalli idanunsu na 'yan sakanni kana ta tabe baki "Magulmatan banza da wofi" daga haka tayi wucewarta daki donta saka kaya,yayin da shahida cikin dacin rai da baqincikin daya taso mata ta fito tsakar gida ta shiga bandaki tayi fitsari sannan ta daura alwala nan bakin famfo ta shigo da akwatin nata. Qarfe daya da minti ashirin na rana tana tashi daga saman abun sallarta wayarta ta dauki tsuwwa,hasina ta miqo mata ta duba,nuradden ke kira ko bai fada ba tasan ya iso ne,gabanta taji yayi mummunar faduwa ta daga idanunta ta kalli daada data qarawa fura da nono ruwa take sha,saita kalli hasina,suka hada idanu ta mata signa sannan ta fita tsakar gida,ba jimawa ta biyo bayanta,janta tayi bakin kitchen ta gaya mata abinda ke faruwa "Tabdi,kina tunanin akwai abinda zai sauya dada?,amma arashin tayi akan bar arha,bari na gaya mata baqo zai shigo" ta juya tana komawa,kafin takai ga shiga falon yaro ya tamfatsa sallama yana rangada fadin wai ana sallama da shahida,daada dake zaune a rumfarta tayi katsu tana jiran taji wanda zaiyi magana cikinsu,shuru sukayi ba wadda ta amsa,sai daadan ta kira yaron ya qaraso bakin rumfar "Waye yake sallama da ita?" "Wani ne,wai nuradden daga kano" "Kano?" Ta sake tambayar yaron,saiya kada kai alamun eh,shuru na sakanni sannan tace "Jeka ce masa ya shigo" juyawa yaron yayi ya fice ita kuma ta kira shahida da hasina gaba daya "Xauna nan" ta nunawa shahida gefanta,ba musu ta zauna jiki a sanyaye,ta dubi hasina "Bude firinjin can ki ciro ruwa da lemo" ba musu hasinar tayi yadda tace,dada ta nuna mata shimfidar daddumar data gama salla akai bata kai ga daukewa ba tace ta dora saman nan. Cikin minti biyu kacal nuradden ya bayyana cikin falon,yaci manyan kaya yanata qamshi,bashi kadai bane shida wani abokinsa ko kuma ince amininsa ne,duk da dan uwanshi ne,cikin girmamawa suka zauna saman shimfidar suna gaida daada,ta amsa musu kadaran kadaham,yayin da idanun nuradden ke kan shahida. Tayin ruwa da lemon tayi musu,Sayyid abokinsa ya bude ya zuzzuba musu a kofi,kusan shi kadai yasha,yana sha suna dan taba jira jifa jifa da daada tana tambayarshi kano,kasancewar ta dauki shekaru masu dama rabonta da ita,tun kafin rasuwar babansu shahida. Sai da suka kammala tasa hasina ta zuba musu abinci,saidai sunce a qoshe suke,tilas ta rufe ta maida kitchen din,shuru ne ya ratsa na dan wani lokaci sannan sayyid yace "Am...daada,abinda yake tafe damu dama magana ce game da shahida da kuma abokina nura,duk da nasan bata sanar miki da zuwanmu ba" "Haka yake" a nutse sayyid ya fayyacewa daada komai,tayi gyaran murya tana dubansu "Nasan cewa kuna da labarin an bada shahidan harma an karbi sadakinta,idan ma ta boye maka bata gaya maka ba ni ya zama wajibi na gaya maka gaskiyar abinda ake ciki" "Ta fadama bata boye ba daada" "Yauwa...an riga da an karbi sadakin yaron,kuma a shekarun da Allah ya bamu bai kamata kuma ace muna magana biyu ba,uwa uba sanin kanka ne cewa haramunne neman aure akan nema,koda ciniki akan ciniki ne haramun ne bare nema kan nema,matar mutum kabarinsa,Allah ya qaddari haka tun farko shi yasa ya hukunta jinkirin zuwanka garemu,saboda haka ina mai yaba maka bisa soyayyar daka nunawa jininmu,ina kuma mai maka fatan samun dacewa da wata matar data fita,sannan ina mai dorawa da baka haquri,kayi haquri,Allah ya sawa zuciyarka dangana" sayyid ne kawai ke amsawa da amin,yayin da gaba daya jikin nuradden ya mutu murus,zufa ta dinga yanko masa tako ina "Mun gode sosai da karamcin da akayi mana" sayyid ya fada sanda suke miqewa bayan sun ajewa daada kudi "A'ah yaro...nifa bazan karba ba,zoka dauka ku wuce Allah yayi maka zabi mafi alkhairi" qememe suka qi dauka haka suka fice,daada ta juya ta kalli shahida dake zaune gefanta tana sharbar qwalla "Saikije ki sallamesu" daga haka ta miqe ta tayi wucewarta daki,sanda ta cimma qofar gidan tuni su nuradden sun wuce,sai tex daya turo mata na anjima zai kirata don yanzu baida nutsuwar tsaiwa,sulalewa tayi ta zauna gefan gadon,tana qoqarin hadiye kukanta. Shigowar daada dakin ya sanyata daga kai tana kallonta,tana daga tsaye ta soma magana "Kin kyauta sosai da kika sanyashi yazo kika toxarta mu,daa can kinsan yana sonki baki bashi dama ba har saida muka yanke hukunci a kanki?,ko kina tsammanin mu warware maganar da mukayi kaman qananun mutane?,to idan ma zaki kwantar da hankalinki ki nutsu waje guda shiya fiye miki alkhairi,ki shirya kuma ki dakaci zuwan gobe,mijinki da yardar Allah zaizo kuga juna,idan kinga dama kuma idan yazo din ki watsa mana qasa a idanu" daga haka daadan ta juya tayi ficewarta,sai kawai shahidan ta bita da kallo ranta na quntata,koma meye shi ya janyo mata,kuma shima saiyaji a jikinsa da zuciyarsa yadda ya janyo mata bacin rai tsakar rana ba tare data shiryawa hakan ba. ***** ****** ****** ***** Tunda ta tashi washegarin take kwance abinta kamar ruwa taqi yin komai,saidai daga nan ta koma can,hasina tayi tayi ta tashi tayi wani abun ko taji qwarin jikinta amma ta qeqashe qasa,ko kallo bata ishi daada ba sangar gabanta kawai take,tana daga kwancen tana kallon daada,yadda ta cika fridge dinta da fura da nono mai kyau,lemuka da kuma ruwa,tasa hasina tayi total na kayan fulawa aka siyo komai hasina tayi dan dai dai aka adana komai,baki ta tabe ta dauke kai bacin rai na cinta sanda daada ta fito da sabuwar daddumarta da kawu ummaru ya bata sanda ya dawo daga umara ya fesheta da turare ta baiwa hasina taje ta shimfida a dakin soro. Saida komai ya kammala hasina ta isketa kwance cikin kujera tana saqa da warwara ta zauna gefanta "Ya kamata ki tashi ko ruwa ko watsa kyaji dadin jikinki?" Idanunta da suka sake girma saboda kwana biyu data yi bata saka musu kwalli ba ta watsawa hasina cikin salon tambaya "Me kikeson cewa?,kice kawai na tashi na yi masa kwalliya saboda zaizo,mutuncina ya qara zuba a idanunsa ko?" Murmushi hasina ta saki tana kada kai "Niba haka nake nufi ba,kawai nasan yadda kikeson wanka wuni guda kuma ace tun safe ga azahar ta shiga baki watsa ruwa ba bare kici wani abun ai babu dadi,a qalla kodon tsaftar jikinki ko?" Saita maida kanta ta kwantar gami da rufe ido sannan ta amsa mata "Share kawai" dubanta hasinan tayi na wasu mintunan sannan ta miqe tana cewa "Allah ya kyauta,ya kamata dai ki sawa ranki salama,tunda kinsan cewa aikin gama ya gama,kada madai azo gaba kina jin kunya yazo kiga ya miki ki kamu da sonshi,kinsan wallahi daada ba raga miki zatayi ba"da sauri ta sake bude idon ta dubi hasina "So,bakisan nayi bikin binneshi ba?" Dariya ta qwacewa hasina ta kama baki tana kallonta "Shi kuma wannan da kika kawo fa?,mutunci kuke kenan?" "Nuradden?..inason in rama halaccin da yayi minne shekaru kusan hudu" "Tabdi,kice gwara da Allah yasa daada ta zaba miki miji,ashema ba soyayya kuke ba kenan" kofin dake gefanta shahida ta wafto ta jefi hasina dashi Allah yasa ta kauce bai sameta ba,har ga Allah taso ta sametan don bata da bakinma ce mata ta fita saboda wani abu dake takore da wuyanta "Na rantse da Allah na tashi hasina saidai daada ta fiddaki daga gidan nan" cikin dariya ta fice tana cewa "A'ah,a'ah,bani nakar zomon ba,ratayarma kuma ba'a bani ba". Qarfe uku na rana da 'yan mintina daada ta shigo ta sameta "Tashi kiyi wanka ko yanzu nasa akaimin ke bandaki na sabeki" ta furta tana nuna da gaske take,saida ta gama taurin kanta ganin da gaske daadan take sannan ta shiga bandaki tayi wankan. Sanda ta fito mai kawai ta shafa sai turarenta oily data gogawa fatarta,tasaka wasu riga da skert na atamfa ta zura dogon hijabinta daya sauka har saman qafafunta ta soma da nafila kafin ta gabatar da farillar sallar la'asar. sanda ta kammala saman abun sallar ta zauna tana jan hasbunallahu wani'imal wakil,saboda faduwar da gabanta yaketa yi wanda batasan dalili ba. 👑 https://youtu.be/H7M7h6l6wNM *xafafa biyar na kudi ne,idan kika gani don girman Allah karki sharing,ga mai buqatar siya zai tuntubi wadan nan numbers din* 07067124863 *ko kuma* 09032345899 *Alqawarin Allah* 3️⃣0️⃣ "Kana nufin kaine mutumin daya kawo sadakina da mudin airena ba tare da sani ko yardata ba?" Ta furta wani bala'i na cinta,maimakon ya bata amsa da baki saiya daga mata dukka girarsa biyun yana dubanta kai tsaye ya kafeta da idanunshi,wani tashin hankali taji ya rufto mata irin wanda bata taba jin irinsa ba tunda maganar aurenta ta bullo,tashin hankali da ba'a saka masa rana,ko zata yarda da kowa ba zata yarda da anwar ba,ko zata amince da auren kowa ba zata taba amincewa da auren anwar ba koda su biyu kadai suka rage a duniyar,murmushin takaici ta saki wanda qasan zuciyarta ji take kaman zata fashe "Kaima kasan ka dauko abinda bazai taba yiwuwa ba har abada,tamkar wanda ya mutu ya dawo ne,kai bakaji kunya ba anwar?,kana tunanin akwai abinda yayi saura?,kana tsammani akwai wani sauran abinda ya rage tsakanina dakai?,to bari kaji na gaya maka,ba zaka taba samun yardata ba,ba zaka sake samun soyayyata ba,har abada aure tsakanina dakai,har abada...." Qawataccen murmushi ya saki,da alamun kwanciyar hankali kwance kan fuskarshi,sai daya sauke qafarsa ya sauya jinginar da daya sannan ya rungume hannunsa daya dayan kuma yana shafar sajensa idanunshi a kanta,fara'ar fuskarshi ta bace bata "Hajiya shahida....dukka tunaninki bai baki dai dai ba,baije inda ya kamata yaje ba" sauke qafarsa yayi ya soma takowa inda take tsaye,sai daya rage tazarar dake tsakaninsu sosai sannan ya tsaya ya soke hannayensa cikin aljihun rigarsa "Kina tunani ko tsammanin soyayya ce tasa na nemi aurenki?,ko kina tunanin neman yardarki nake kafin na aureki?"sai ya sake takowa gab da ita kamar zai hadeta da jikinsa,ya nunata da yatsa "Zan aureki don na nunawa wancan wawan cewa nidin na girmi qaramin dalili babban dalili ne ni,sannan nayi isar da zan yanke guntuwar soyayyar da yake taqama da ita,soyayyar da bai iyata ba,bai gama saninta bama bare ya iya,baisan kanta ba baisan mece ita ba!" Ya qarasa fada yana dan daga muryarsa gami da nuna qofa da yatsa kai kace nuradden ne ke tsaye a wajen,saiya sauke hannun nashi yana maidashi aljihunsa kana yaja baya kadan har yanzu bai dauke idonsa daga kanta ba "Yana tunanin ya sanki?,yana tunanin yafi kowa saninki koya riga kowa saninki?,ya gayamin magana yayi tunanin yaci bulus?,inaso yaji ciwo ya kuma ci gaba da jin ciwo a ransa duk sa'a daya da zata wuce da tunanin wani mai suna anwar ya haramta masa auren wadda yake iqirarin yanaso,wadda yake iqirarin ba wanda ya isa ya shiga tsakaninsu" yana kaiwa nan ya juya mata baya,yana jin kamar ana yankar zuciyarsa "Baki cancanci na qyaleki kici gashin kanki ba,baki cancanci na barki kiyi zabin da kikaga dama ba,bayan kin cutar da zuciyar da bata cancanci sakamakon da kika bata ba,kin bata rayuwar da alokacin ya kamata ki tattaleta kodon iyaye da qannenki,kin bada jikinki ga wani har yayi ajiya a wajen daba muhallin......" Saiya kasa qarasawa saboda wani dunqulallen abu daya tokare masa maqoshi,ya dinga jin wani turari tun daga zuciyarsa zuwa fuskarsa,bakinsa yaji ya dauki zafi ya fitar da iska zazzafa,yana jin wani irin ciwo da qunci duk lokacin daya tuna da lokacin da kuma abinda ya faru,hotunan dake wajensa da ganin da yayi kaya ido da ido sun kasa gogewa daga qwaqwalwa da zuciyarsa,yana jin wani irin ciwo mara misaltuwa,tabbas da yana da iko daya dawo da lokacin ya goge duk wani abu daya faru ko xai samawa zuciyarsa salama. Tuni hawaye ya soma wanke mata fuska tana tuna lokacin da abinda ya faru alokacin daya bayan daya,sai a sannan ta dinga tuna kaman ta ganshi,kaman a gabanshi aka sauketa,hakan na nufin ya ganta cikin maye?,ya ganta a lokacin da jini kebin qafafunta?,yaga sanda aka cillo mata pant dinta da kwalabenta?,amma me yasa ya zama mai qaramin tsinkaye?,mai yasa ya zama mai gajeran nazari?,me yasa ya yanke mata wannan danyen hukunci farat daya,haka soyayya take?,haka masoyi yakewa masoyinsa?,sai taji ya sake sireta,daya zama mai dogon nazari da dukka abubuwan da suka faru yanzu basu faru ba Ranta ya ninka bacin da yayi,hankalinta taji ya tashi,da qyar ta bude baki cikin muryar kuka tace "Mugu azzalumi,ba ruwanka da kowa sai kanka,ba ruwanka da damuwar wani sai taka,ka tanadi mugun nufi akaina kan abinda baka da cikakkiyar hujja a kai...." "Wacce huja nake nema baya ga wanda na samu....!" Ya juyo a fusace ya fada idanunshi da suka kada zuwa jaa suna kanta "Ba hujjar kake nema ba,kanayin komaine don ka wulaqantani dama,ka shirya komai ne donka tozartani,to Allah ya fika,ba zaka taba samun nasara a kaina ba,nuradden kuma idan Allah yaga dama kai baka isa ka rabani dashi ba"itama ta fada cikin tunzura fushi da bacin rai "kome zaki fada dai dai ne,duk yadda kika fassara lamarin a ranki ko a bakinki kisa a ranki haka ne,any ways ma ni nasan na taimaki rayuwarki ne,ko kina tunanin wancan wawan idan yaji wace ke a baya zaici gaba da haukan da yake a kanki?,kinga 'yammata....koki sawa ranki sauqi ko kar kisa duk uwar ubansu daya" kai take gyadawa bacin rai na cinta,idanunta fes cikin nashi,ji take kaman ta shaqe anwar din,a yanzu babu halittar data ji ta tsana sama dashi "Zan saka salamar duk da bakayimin fatanta ko burin samunta,amma ka sani....tsugune bata qare ba,don babu abinda zanyi da masoyi irinka nawar!,ka shirya tarbar duk wani abu da zai tunkaroka!" Tayi lafazin da alama wani abu ya motsa ranta qwarai,duk da murta na a raunane amma amma fuskarta da qwayar idanunta na bayyana jarumtarta,wani malalacin murmushi ya saki ya sake matsowa inda take,wannan karon har qamshin turarensan nan data sanshi dashi yana busowa zuwa hancinta,ya kafeta da idanunsa,muryarsa can qasa kamar mai shirin furta kalaman soyayya a gareta yace "A shirye nake,kece zan gayawa ki shirya zama dani idanma ba'a shirye kike ba,yaushe kikeso wasan ya fara?" Ya fadi cikin halin ko in kula,ganin kallon da yake mata bacin rai ya sanya ta fashewa da kuka sosai ta zube saman kujerar tana rufe fuskarta da tafin hannunta,saiya tabe baki yana isa inda hularsa take yasa hannu ya dauka yana cewa "Ashe raguwa ce ta gaske,tun yanzu?,wasan namu kuwa zaiyi iri qarkon da nakeso?" Ya dora hularshi saman kansa sanda ya qarashe maganar,saiya sanya hannunsa cikin aljihunsa ya ciro kudade sabbabi masu dan yawa ya aje hannun kujerar da take kai yana cewa "Ga kudin zance nan,kuma bance a sayi abunda za'a bugu da kudina na,idan aka siya Allah ya isa na" sosai maganar ta doketa,tana niyyar daga kai ta dubeshi ta fuskanci ya juya zai fita ne,har yakai bakin qofa sai yasake cewa "Ammmm..." Yana dawowa da baya,kanta yazo ya tsaya hannunsa daya a aljihun wandonsa dayan kuma yana duba agogon dake daure a tsintsiyar hannunsa "Karki manta da sadakina akanki,shaidu kawai za'a tara a daura,ban lamince ki kula kowanne dan iska ba,ciki harda wannan looser din,idan kuma kikayi hakan shima Allah ya isa ban yafe ba" saiya sassauta murya ya sauko da kansa qasa qasa gab da ita "Ina fata har yanzu wasu daga halayen anwar basu bace miki ba daga kanki,mutum ne mai kishi,ina da kishi kan mace koba wadda ban biya sadakinta ba bare wadda na cire halalina sa nasha wahalar nema zafi da sanyi nabiya" a fusace ta bude fuskarta saboda yadda maganganunshi suka isheta,saita ganshi dab da fuskarta,cikin bacin rai da muryar kuka take cewa "Sadakinka din banza da wofi,idan kana son nunan kudinka wata tsiya ce kaje ka karbi sadakinka idan har ka isa cikakken namiji" tsaf ya karanci bacin ran dake kwance muraran saman fuskarta,saidai yadda yake jin quna yana tunanin bata jin haka,duk sanda zai kalli fuskarta yana tuna sanda aka sauketa ne a gabanshi,cikin maye,cikin jini,pant dinta a gabanshi aka cilloshi,wani ya riqe zuwa jikinsa gaban idanunsa,saiya runtse idanunsa kana ya bata baya ya soma takawa "Idan kin isa ke kije ki karbo kin kiga idan ban amsa ba,dama taimako nayi kuma na fuskanci ke bakiga hakan ba" daga haka ya qarasa ficewa daga dakin,sake rushewa da kuka tayi,ta tsani kalmar taimakon nan,wannan wanne irin cutace?,ita zai taimaka. Cikin gida ya qarasa,daada na rumfarta a zaune ita da hasina,saiya cire takalmansa ya zauna saman tabarmar dake shimfide qasan inuwar bishiyar dake tsakar gidan,daadan tayi tayi dashi ya shigo amma yace wucewa zaiyi,dole ta fito ta zauna daga gefan tabarmar itama "Zan wuce daada,ina tunanin rana ita yau za'a kawo lefe,to bansan inda za'a kai ba,can wajen umma,ko nan garin ko kuma gidan uncle hisham?" "Babu damuwa akai can hidan hashimun tunda acan za'a yi duka bikin,muma can zamu tattara ai mu tafi" "To daada,Allah ya saka da alkhairi ya qara girma" ya furta yana dan sadda kanshi qasa alamun girmamawa "Ina kuma ta shiga?" Daada ta tambaya,ya fuskanci shahida take magana,saiya saki murmushin daya qwata fuskarshi duk da baikai masa qasan ranshi ba "Tana daki tana kukan bata sona can na barota" kama baki daada tayi tana salati harta baiwa anwar dariya,harya miqe ya aje mata kudi ma sam bata kula ba tana ta jajjabi tare da sillewa shahidan hasina na dariya,sai daya sanya takalmansa sannan ya kalli hasina "Taimaka kije ki fito da ita daga dakin karta rube" dariya hasina ta saki sosai,abun saiya qayatar da ita,ya yiwa daada sallama suka fice zuwa soron gidan shida hasina. Bakin qofar dakin ya coge ya yaye labulen bayan hasina ta shiga dakin,ta isa inda take dunqule tana gursheqen kuka "Saikace yau akace za'a kaiki?,taso da Allah karki tara mana jama'a" hannun hasina ta buge tana jin takaici yana cikata,duk maganganunsu da daada tana jinsa,tamkar ma ya raina mata wayo ne,ko yana tunanin 'yar qaramar shahida daya sani a baya ce wannan? "Matsa hasina barta,bari na rage miki aikin na dauketa zuwa qofar soro saiki qarasa shiga da ita ciki,da sauri ta bude fuskarta,idanunta da sukayi jawur zuwa fuskarta ta kalleshi dasu "wallahi wallahi ka sake ka tabani sai kayi dana sani!" Ta fada a kausashe "Meye hakane shahida?" Hasina ta tambayeta tana dubanta cikin mamakin kausasa lafazin da tayi,dubanta yake sosai,yana son yace shine farau?,amma idanun hasina yasa ya maida amsarsa "Wallahi wallahi kinji nima na rantse matsawar baki tashi kin shige ba ko abinda yafi danasani zanyi saina dangana dake har rumfar daada" saiya maida dubansa ga hasina dake tsaye tana kallon dramer "Ina cikin mota a qofar gida,minti biyar na bata idan ta dara hakan bata tashi ba ki fito ki gayamin" kai ta gyada ya saki labulen ya taka a sannu ya fice daga soron. Bata buqatar duk wani abu da zai kawo wani kusanci tsakaninta dashi,so take ya tafi yabar gidan saboda haka ta miqe tana hada hanya,hasina ta dauki kudin dake aje inda ta tashi ta bita dasu a baya,ko kallon dada dake tsakar gida tana mita batayi ba ta shige rumfar daadan ta zube saman kujera,saita dora hannu aka ta fashe da ihun kuka ko zataji salamar radadin da take ji cikin ranta,hasina kallonta take idanu a waje cikin rudewa tace "Meyw haka ne shahida kike kamar wata 'yar shekara goma,ya zaki tara mana jama'a?" Takai qarshan maganar sanda daada ta runtumo cikin dakin tana tambayar ba'asi "Au ihu kike?" "Wallahi daada bana sonshi,shima daada ba sona yake ba bazai gaya muku gaskiya bane kawai" baki ta tabe tana mata duban sakarya "Au Allah ko?,ashe tun farkon saninmu dashi mu muka jajibo miki shi ko?,ashe qiyayya ce ta hadaku a baya ba soyayya ba?" "Daada baya sona yanzu bana sonshi!" Ta sake fada cikin kuka "Eh naga alama,shi yasa bai bar kakarki ba yaci gaba dayi mata aike a boye bai bari nasan wayeshi ba,kuma qiyayyar ce tasa ya tasl qafa da qafa ya nemi aurenki hannun iyayenki" "Wallahi daada kinji na ra ntse miki da manufa a lamarinsa" "Dama akwai auren da babu manufa?,shirme kenan" ganin duka taqi fahimtarta saita sauko gwiwoyinta qasa tana kallonta "Daada,don girman Allah ku maida masa kudinsa,ko bazaku bani nuradden ba na amince ko zabamin ko waye a lokacin da kuka saka na bikin nawa ayi dashi" nazarinta daadan tayi na wani dan lokaci sannan ta kamata ta miqar da ita tsaye "Naji,zauna muyi magana" sanyi taji yana ratsa zuciyarta,ta soma jin qamshin nasara,saita miqe din kamar yadda daada ta buqata suka koma saman kujera suka zauna. Saidata bata 'yan mintuna ta nutsu tukunna sannan tace "Komai da kika gani a rayuwa yana da dalili,inason ki gayamin dalilinki na duka wadan nan maganganun da tsallen badaken qin auren mutumin da kowa ya shaida kuma yana da labarin soyayyarku" shuru tayi kawai tana qiyasta ta yadda zata gayawa daadan komai bayan basusan komai ba akan rayuwar data fada a baya,sannan uwa uba shi kansa anwar din ta fahimci ba wanda ya taba gayawa ko bashi labarin komai,idan ta aikata hakan kamar ta dabawa cikinta wuqa,kamar ta yaye mayafin asirin da Allah ya rufa mata kenan?,ganin tayi shuru sai daada tayi tsammanin ko batason magana ne a gaban hasina,saboda haka ta korata waje "Ki gayamin dalilinki,indai matuqar na gamsu,toba shakka a yau basai gobe ba zamu maida masa komai nashi" tofa ga qoshi ga kwanan yunwa,ta ina zata fara ya zatayi?,batason tona komai,batason kowa yaji komai,tana ganin kamar ba muhallin kowa bane ba hurumin kowa bane Kai ta kada "Daada baya sona ne,nima yanzu na daina sonshi,kinga babu amfanin aurenmu" murmushi ta saki tana kada kai "Banda abinki shahida ta yaya masoya haka siddan zasu daina son junansu?,ai ruwa baya tsami banza" cikin nuna dagiya da qarfin hali tace "Hakanan nidai daada muka daina son junanmu,don Allah karku qulla auren qiyayya" hawaye ta siraro daga idanunta muryarta ta soma rawa,saita sake murmushi tana kallonta "Shahida,anyi auren hadin da baki taba ganinsa ba bai taba ganinki ba sai hadi kuma an zauna lafiya harma yafi na soyayyar qarko,kin ganni nan gani da ran Allah?,to sanda na auri kakanku sai randa ya shiga dakina nasan shi na aura,saboda haka indai rashin soyayya ne hujjar fasa aurenki da anwar indai kikaga an fasa to la shakka mutuwa nayi bana raye,ko bana raye zanbar wasiyyar a tabbatar an daura,don anwar din ya cika dukkan siffa da kamalar da annabi yace a baiwa mutum aure" daga haka sai daadan ta miqe ta qyaleta,tashin hankalin data ji a sannan yasa taji zuciyarta ta bushe gaba daya,hawayen idanunta sun bushe tas,saita miqe itama ta shige daki tayi rub da ciki tana sakin ajiyar zuciya ko zataji sanyin tuquqin da ranta yake. Ta shafe a qalla minti talatin a haka kafin daga bisani ta janyo wayarta,ta lalubo number nuradden ta kira,bugu daya tak ya daga,ajiyar zuciya ya soma saukewa da alamu hankalinsa shima ba'a kwance yake ba,duk sai taji bacin rai ya sake shigarta,shi ya janyo komai,shine silar komai "Ka dawo ka sake neman aurena karo na biyu nuradden,bazan iya aurensa ba" ta fada kai tsaye ba tare da tayi sallama ba ko tace komai,kafin taji yace wani abu taji an karbe wayar,da sauri ta daga kai don ganin waye,daada ce,bata ce komai ba ta kara wayar a kunnenta "Nura kana jina?" Ta fadi sanda take ficewa daga dakin,saita miqe ta zauna sosai saman katifar tana bin qofar da kallo. *muna muku fatan alkhairi tare da fatan zaku gudanar da bukukuwan sallarku lafiya cikin amincin ubangiji,Allah ya karba mana ibadunmu,ya gafarta mana zunubanmu,yaji qanmu ya jiqan mamatanmu,yasa mu cikin 'yantattun bayinsa amin umma amin,ZAFAFA BIYAR na muku fatan alkhairi* *_karku manta,ku kasance da tashar SAUTIN HIKIMA TV don sauraren littattafan da zasu debe muku kewa yayin ayyukan sallah a gida* *kundin qaddarata* *daurin boye* *mutuncin mace* Duka wadanda na rubuta *fatan alkhairi a gareku* #zafafa biyar #sautin hikima tv #team anwar #team shahida #team nafisa 🏃🏾‍♀️ _ma'assalam_🤝🏽🤝🏽🤝🏽 _ziyarci tasharmu ta youtube don sauraren tsaffin litattafanmu dama sababbi da zamu fara dorawa nan gaba kadan in sha Allah_ https://youtu.be/H7M7h6l6wNM *Alqawarin Allah* 3️⃣1️⃣ Minti goma kyawawa daadan ta dawo,ta miqa mata wayartata tana dubanta,sannan ta miqa mata kudin da anwar ya bata tana cewa "Tunda kin zabi zubar mana da qima rahama mu zuba nida ke" daga haka ta juya ta fice,a sannan ji shahidan take kamar ta dora hannu aka tayita zunduma ihu ko xata ji sanyi cikin zuciyarta,me yasa ba zasu fahimceta su bata uzuri ba?,me yasa ba zasu haqura ba?,wai da anwar da itama wa sukafiso ne?,waye nasu a ciki?,kira ne ya sake shigowa wayarta,ta daga ta duba da sauri sai taga nuradden ne,muryarsa kadai ta gaya mata cewa ya karaya bashi da wani sauran fata "Shahida,na rasaki shahida,ta ina zan iya jurewa rashinki?,zan iya tsira daga hukunci da horon rasaki da zuciyata zata yimin?,ki tayani addu'a bansan ya zata kayamin ba" daga haka ya yanke kiran,me daada ta gayawa nuradden?,shikenan ta rabata dashi?,dole ta zauna da mutumin da sam bata ra'ayinsa ne wai?,irin wannan masoyin zata rabata dashi?,kalamansa kawai sun tabbatar da tsantsar qauna da soyayyar da yake mata,saita kifa kawai rubda ciki tana lalube da binciken meye abunyi a qwaqwalwarta,mecece mafita?duk wata dabararta ta qare,wayonta duka ya qure,daada ta yanke komai. 🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍 Qarfe bakwai da rabi ne na daren ranar,yana zaune a harabar gidan saman daya daga cikin fararen kujerun roba dake wajen,shi ya zabi zama a wajen saboda yadda iskar damina mai sanyi ke busawa gabas da yamma,hakanan qwayayen lantarkin dake harabar gidan sun haske ko ina harda korayen tsirran dake harabar wajen,sai yake jin zuciyarsa wasai,hakanan babu nauyi qunci ko wani abu da yakejin ya dameshi a yanzu,shaqar iskar yake sosai yana fesarwa har cikin huhunshi qamshin iskar da sanyinta na sake sa zuciyarsa cikin wani shauqi da walwala,fuskarsa fes take a washe. A hankali take takowa cikin gayunta,tayi kyau don ba qaramar kwalliya ta dauka ba,don yau din na daya daga cikin ranakunta na musamman,saboda bako da yaushe take samun dama irin wannan ba,ace yau anwar din yazo zance takanas saboda ita,zata iya irga sau nawa hakan ya taba faruwa a tarayyarsu,shi yasa duk ransa zaizo din ba qaramin tanadi takewa ranar ba. Gabansa ta tsaya sannan tayi sallama tana kallon yadda yayi masifar kyau cikin qananun kaya sai kace wanda ya dawo daga europe,ya daga kai yana dubanta sannan ya amsa,cikin shagwaba shigarsa da yadda yayi kyau yana dada burgeta tace "Ya bakaci komai ba dear?" Ta qarashe fada tana jan kujerar dake kallonsa ta zauna,duban tulin kayan ciye ciyen dake gabanshi yayi sannan ya kalleta,shi sam a ra'ayinsa ba mutum bane mai yawan son ciye ciye,kusan ma babu cimarshi ciki sai kadan,kafada ya daga "Karki damu,duka basu da muhimmanci,zuwankin da ganinki ya fisu muhimmanci" wani farinciki data jima bataji kamarsa ba ya tsirga mata,ta lumshe ido tana sakin murmushi,ta jima bata ji kalmar data mata dadi matuqa daga anwar din ba irin wannan,sannan ta budesu idanun nata a kanshi "Ya gida yasu momy" "Kowa lafiya suna ma gaidaka" ta fada tana zuba masa lemo sannan ta tura masa,bai musa ba yaja yadan kurba tana binsa da kallo,batasan wane irin qauna takewa anwar din ba,jifa jifa take sako hura yana tayata kana ta sako masa zancan bikinsu,lissafin events da zatayi da sauran abubuwa,yana kurba yana saurarenta sai daya shanye sannan yace mata "Next week za'a kawo lefen idan Allah ya kaimu....saidai kuma kafin sannan inason nayi wata muhimmiyar magana dake,duk da na riga na shaidawa su momy amma naga kece yafi cancanta ki sani,kuma ni yafi dacewa na sanar miki da kaina" dukka hankalinta ta bashi ganin yadda ya tara shima nutsuwarshi waje guda gamida soke yatsunsa cikin na juna yana dubanta sosai "Uhmm,ina jinka" "Komai da kika gani a duniya muqaddarine daga Allah,hakanan ba wanda ya isa sauya tsarin Allah,yadda ya tsarawa bawa haka zai karba,naka kawai ka gode masa,zaka iya tsarawa rayuwarka abu amma idan baiyi dai dai da tsarin Allah ba zai sauya maka ne da wanda yake ganin shine daidai da rayuwarka kuma shine mafi alkhairi,to...ina tunanin ku biyu za'a daura mana aure dasu lokaci guda,na nemi aure watanni biyu baya da suka wuce Allah ya qaddara kuma an bani,yanzu haka cikin satin da za'a kawo naki kefen suma za'a kai,lokacin daurin aurenma kusan daya ne,rana ce kawai aka bambanta,kinga ya kamata ace kin sani saboda kina da haqqin ki sani din,nasan mai yiwuwa hakan zai bata miki rai saboda halin kishi irin na mata,saboda haka ina mai baki haquri tare da shaida miki haka Allah ya qaddara dama tun fil'azal shi yasa ya hukunta faruwar hakan,ina fata hakan bazai dameki ba don kowacce cikinku matsayinta daban" wani irin abu taji yana mata yawo tsakiyar kaa kamar ana yamutsa qwaqwalwarta,wannan wacce iriyar mummunar rana ce?,wanne irin mummunan labari kunnuwanta suke dauko mata?,saita cije lebanta da kyau ga zatonta mafarki take ko zata farka,saita fuskanci da gaske ne,wani abu ke niyyar toshe mata numfashi,ta fahimci idan bata bari tayi kuka ba wani mummunan abu na iya faruwa da ita,saboda haka kawai ta saki hawayen da take qoqarin tarewa suka soma zuba "Wanne irin abu kake gayamin haka anwar?,kana gayaminne fa kishiya zaka yimin tun ban shiga gidanka ba,anwar kana gayamin zaka hada soyayyata data wata ne fa,kana gayamin zamu hada miji da wata,zaka raba soyayyarmu,wai shinma yaushe ka ganta harkaji kana sonta kaji zaka iya aurenta?" "Karki damu,ba wata sabuwa bace cikin rayuwata,mun jima tare,rabuwarmu da ita qaddarar haduwarki dani ce" "Shahida?!" Ta fada cikin razana da kuma salo na tambaya,saiya zuba mata idanu yana kallonta tare da mamakin kama sunanta farat daya da tayi kafin daga bisani yace "Eh,ya akayi kika santa?" Sam batabi takan tambayarshi ba saboda ji take kamar alqiyamarta ta tsaya,a ina ya tono shahida?,a ina ya ganta?,ya akayi suka daidaitawa?,ya akayi ta aminta zata aureshi?,ya akayi yaci gaba da kulata?,dama soyayyarta bata mutu cikin ransa ba?,inaa,har abada ba zata taba yarda ta hada anwar da shahida ba qarqashin inuwa daya,kuma ta kasance a tsakiyarsu?,ashe data cika shashasha "Kacemin kawai ka koma wajen tsohuwar masoyiyarka donka samu damar wulaqantani idan ka aureni,har abada anwar bazan hadaka da wata ba,bazanyi zaman kishi da kowa ba,bazan zauna da kishiya ba" ta fada tana miqewa tsaye,cikin hargagi,hannunshi ya daga mata a nutse "Ki nutsu nafisa ki samu waje ki zauna" "Bazan nutsu ba,bazan zauna ba,ka daina kiramin nutsuwa a wannan yanayin,saidai ka zaba koni ko ita" furucin ya fito hade da kuka mai cike da tashin hankali "Ba wanda zan zaba hakanan ba wanda zanqi zaba" ya amsa mata kai tsaye tana dubanta cikin yanayin dake nuna jarunta da mazantaka na jajirtaccen namiji,kai take jinjinawa hawaye na zuba daga fuskarta sosai yana hadewa da majina,ji take kaman ta cire ranta,ji take kama ta dauki numfashin shahida da bata tashi dawowa rayuwarta ba sai sanda ta sakankace take saka ran ta mallaki anwar,tana ganin da tayi faduwar baqar tasa,data shiga ta zama 'yar kallo gwara ta haqura dashi har abada "Anwar!...kaje ka auri shahida bazan aureka ba,bazan aureka ba har abada" tana kaiwa nan ta juya da gudu gudu sauri sauri tayi cikin gida,yayi niyyar dakatar da ita amma sam bata tsaya ta saurareshi bama bare taji me zai sake fada,saiya furzar da numfashi,kana ya ture kujerar baya ya miqe yana daukar muqullin motarsa gamida da handkherchief dinsa dake aje saman teburin ya saka cikin aljihunsa ya nufi qofar fita,sai daya shiga parking space sannan ya dauki motarsa yayiwa mai gida horn ya bude masa gate ya fice daga gidan cikin nutsatstsen tuqi. Yana tuqin yana furzar sa iska mai dumi daga bakinsa,wai me yasa mata dukka harkarsu matsala ce?,don kawai yace mata ba ita daya za'a daurawa aure dashi ba shine xata masa wannan jinnun?,to xaya zuba ido yaga iya nata gudun ruwan. Wayarshi dake aje gefe ta dauki rura,yadan juya ya kalleta,ganin number anty usaina ce ya sanyashi dagawa,ya saka handsfree ya aje gefansa "Kana wajen ta ina ne?" "Ina hanya anty" "To shikenan saika iso"bai amsa ba ya katse kiran ya aje wayar ya maida hankalinsa ga tuqinsa,duka hannayensa na zube saman sitiyarin,yayin da rabin tunaninsa ya tafi ga abinda nafisan tayi yanzu,me take tunani?,zaita binta ne yana lallashinta?,ko yace ta taimaka ta aureshi?. Yana fitowa daga motar su sa'ida suka shigo gidan,dawowarsu kenan daga makarantar dare dake can daya bangaren na unguwarsu,ba yadda anwar din baiyi ta qyalesu ba amma tace sam batason zaman banza,zaman kallon bayan sallar magariba daga waccar tashar a koma waccar,dukansu suka iso suna masa sannu da zuwa ya amsa ya shiga cikinsu suka shige cikin gidan. Qaramin falon anty usaina suka shiga suka bar yaran a babban falo,idanunsa nakan tauraruwa tv anty usaina ta shigo ta aje masa abinci,kallon abincin yayi " banajin yunwa anty"tana shirin zama tace "Kaci a gidan abinci kenan?,gwanda dai kayi auren nan suma sa huta da ganinka" murmushi ya saki yana shafa kanshi,zama tayi suka gaisa "Ya za'ayi da kayan lefen?,na ina za'a fara kaiwa?" Tsaki yaja can qasa sannan yace "Ni kaina ban sani ba,ina tunanin iya nasu za'a kai,don nafisa tace ta fasa" idanu anty usaina ta fiddo "Ta fasa kamar yaya?"hannayenshi ya watsa sannan yace "Oho,na shaida mata kawai su biyu ne dalilin da yasa tace ta fasa kenan" saita sauke ajiyar zuciya tana dubanshi "Don tace ta fasa bawai yana nufin ta fasa dinne ba,kishi ne kawai da bacin rai,lokaci qanqani zata sauko,saboda haka ba za'a fasa shirin komai ba,zuwa gobe ka kirata ka bata baki duk yadda kukayi saika sanarmin" kai kawai ya gyada yana mita qasan zuciyarshi,yadan jima anan suna tattaunawa sannan daga bisani yayi mata sallama ya wuce. A guje nafisa ta shiga falon gidan nasu ta wuce momy dake zaune tana kallo ta haye sama dakinta,da kallo momyn ta bita harta shige,saita dauke kai tana sauke ajiyar zuciya,dama ta sani za'a rina wai an saci zanin mahaukaciya,yadda nafisan ta dora burinta da rayuwarta duka kan anwar din tasan za'a sha gwagwarmaya duk sanda labarin ya shiga kunnenta,qyaleta tayi bata bi ta kanta ba,ta barta ta gama kukan zuciyarta ta huce tukunna. Tamkar zata zauce haka taji,ta kai ta kawo ta kasa zama kamar wadda ta hadiyi tabarya,wannan wacce iriyar masifaffiyar shahida ce?,wanne irin mayen anwar ne?,ace duk yadda takai ga rabasu haqanta ya gaza cimma ruwa?,iya abinda ya kamata tayi don rabasu tayi amma ace bayan shekaru shidda sun sake dawowa sun jone?,idan ma kisa ba batasan me zatayi don rabasu ba,wayarta ta rarumo ta kira number mima,saidai hartayi quginta ta katse bata daga ba,haka ta dinga kira ba qaqqautawa amma bata daga ba,cillar da wayar tayi cikin muryar kuka mai cike da bacin rai da qunan zuciya tace "Shegiya mahaukaciya,wai ina kika shiga ne?!" Ta qarasa fada cikin qaraji wanda banda sautin tv dake aiki ba abinda zai hana momyn jiyo sautinta. Haka ta dinga qaramin hauka ita kadai cikin dakin har sha biyu saura na dare sanda wayarta tahau kuka,ta daukota da hanzari tana tsammanin mima ce,maimakon mima anwar ne,aje wayar tayi kawai tana kallonta harta qaraci kukanta ta gama,sai daya kira sau uku bata daga ba tana zaune da kallon wayar ruwan hawaye na fita daga idanunta,tana ganin hakan da zatayi kawai shine zaisa anwar din ya janye qudurinsa ya haqura shahidan. Washegari qarfe goma na safe tana gaban mudubi a zaune tana kallon yadda fuskarta ta qojale saboda kukan data kwana tana yi wayar ta sake burari,wannan karonma anwar ne a maimakon mima,bata da mafita tilas ta daga wayar ta sake gaya masa kalaman da zasu tabbatar masa da cewa ta rabu dashi kp hakan zai tsoratashi ya janye nufinsa "Karka sake kirana matsawar kana kan qudurinka na hada aurena da wata macen daban,na gaya maka tun jiya nikam nafisa bazan aureka ba anwar muddin kana a matsayin mijin mace biyu,na haqura dakai har abada" daga haka ta yanke kiran,saiya furzar da numfashi daga bakinsa ya baiwa banza ajiyarta,ya aje wayarshi yaci gaba da shirinsa,shikam ya yankema ransa babu sauran wata mace da zata sake bashi wahala,bazai sake son wata ba bare ta gasa mishi zuciya yadda ya faru dashi a baya,ya saki qaramin murmushi sanda ya tuna cewa da sonta yake da tuni yanzu yana cikin tashin hankali da dimuwa a sanda tace bata sonshi,yanzun kam hankalinshi kwance yake jinsa,saidai kuma wani bari na zuciyarsa yana dan jin damuwa,musamman idan ya tuna da mahaifanta yadda zasu dauki maganar,da wannan tunanin ya gama shirinsa ko abinci yau bai saurara ba ya dauki muqullinsa ya fito,kafin ya tashi motarsa ya tsaya ya turawa anty usaina yadda sukayi da nafisan,don baison kiranta ma bare ta bijiro da wani abun da zai hanashi uzurinsa nayau. ***** ****** ****** ***** "Wannan sakarcin banza ne ai sakarcin wofi,ta isa ta haramta abinda Allah ya halatta?" Alhj abba mahaifin nafisa ya fada cikin fushi da bacin rai yana duban mummy mahaifiyarta,kai ta gyada itama,sau tari tana mamakin halayen nafisan,ta rasa inda take debo wasu baqaqen halayen,abubuwa da yawa ita dai ta sani ba halayyarta bace kota mahaifinta ba "Atoh,nayi mata magana daxun da safe ta nunamin tana kan bakanta" mummy ta baiwa alhj abba amsa,shikam anwar yana daga gefe kanshi a qasa cikin girmamawa yana saurarensu,baice komai ba sai a sannan "Kuyi mata uzuri,duba da yadda zancan ya sameta a qurarren lokacin da bata zata ba,ni kaina bani da masaniyar abun zai kasance haka sai gab da zanyi tafiya,sai naga yafi kyau idan na dawo na shaida mata mu fahimci juna,to sai kuma aka samu sabanin fahimta" "Qarancin hankali da tunani dai,ita zata zauna maka da ita?,ko ita haqqin kula da ita yake kanta?,bilki....kiramin ita maza" a nutse hajiyan ta miqe ta fice zuwa dakin nafisan. Kwance take rub da ciki tana aikin kuka,tana son anwar tana tsoron rabuwa dashi,tana tsoron yaqi janye qudurinsa,don itakam ba abinda zai sata ta sauka daga kan bakanta,matsawar ta yarda ta aureshi to yaqin da tayi shekara da shekaru tana yi,kudinta data kashe,lokacinta data fansar duka sun tashi a babin badinuhu bataci riba ba kenan "Kin hadu da aiki kuma kin gama kanki da wahala wallahi,tunda kin daukama kanki aqidar banza da wofi,ki tashi kije mahaifinki nason ganinki" cewar mummy daga haka bata qara ba ta juya tayi ficewarta. Sanda ta isa falon anwar ta soma gani,kishinsa ya sake lullubeta ganin yadda kamar ma sake kyau da fresh yayi abinsa tsakanin kwanakin da ita take fama da quncin zuciya,gefan abban nata ta zauna ya dubeta "Nafi,wanne irin shashanci da sakalci kike shirin aikatawa haka?,saboda Allah ya halatta masa auren daga daya zuwa hudu saikice ba zaki aureshi ba saboda haka?,zaki sauya hukuncin Allah kenan?,koke kikayi kanki?to kar naji karna gani,banason wannan shirmen banza,yana da damarma yace biyu zaiyi kece ata uku" Kuka ta saki sosai "Abba...wallahi bazan aureshi ba,bazan iya zama dashi da wata ba"baki bude alhj abba ya watsa mata daquwa "Kinci gidanku,kajimin fitinanniyar yarinya?,to saikin aureshin naga wanda ya isa ya hana" miqewa tayi cikin kuka "Wallahi abba zan gudu,zan barku idan aka aura min shi" mummy na shirin kai mata duka saboda takaici ta fice a guje daga falon. Shuru ne ya ratsa falon,kunya da takaici na kama alhj abba da hajiya bilkisu,sai suka rasa ta inda zasu kama zancan,sunsan halin nafisa sarai sai addu'a,karta aikata wani abu da zai zama musu illa nan gaba,anwar ya fahimci shurunsu saboda haka yace "Alhj,karka damu,Dukkaninmu ni da kai da mummy bamu da ikon da zamu sauya mata ra'ayi,sannan duk yadda mukaso abin itace zata zauna,dole saida gamsuwarta sannan komai zai tafi yadda ake buqata"ajiyar zuciya suka saki dukansu kusan a tare cikin bacin rai da takaici "Yarone ka haifeshi baka haifi halinsa ba,kayi haquri anwar" cewar alhj abba yana jin babu dadi har cikin ransa,yana jin kaman ya muzanta "Haka Allah ya qaddara" anwar din ya furta kanshi a qasa,shima yana jin babu dadi saboda yadda sukejin laifin kaman a kansu yake. Tana zaune har yanzu inda ta zauna tana rusar kuka a haka mummy ta tura qofar dakin ta sameta,da hanzari ta daga kai cikin fargaba da razani tare da taraddin furucin da zai fito daga bakin mummyn,tana son anwar tana fata ace ya karbi muradinta "Shikenan ko?,burinki ya cika?,saikije ki samo wani mijin wanda yafi anwar" daga haka ta juya abinta ta fice tabar mata dakin,cikin tashin hankali ta miqe kaman zata bi bayan mommy don samun qarin bayani,sai kuma ta dawo da baya qwaqwalwarta na gaya mata ma'anar maganar mummyn,anwar ya barta?,anwar ya zabi shahida akanta?,wahalarta ta tashi a banza kenan?,kai ta shiga girgizawa tana fadin bazaiyiwu ba,ta dauki wayarta ta soma kiran layin mima ba qaqqautawa don tana da buqatarta a yau fiye da kullum,saidai amsar dai daya ce wayar a kashe take. A qalla ta kwashi awa kusan biyu a haka,bata da wata mafita ayanzu banda ta kira anwar,ta soma laluben number dinsa ta kira. Fitowarsa kenan daga kitchen dauke da cup na coffe wanda ya shiga ya hada da kansa,cikin mamaki yake duban mai kiran,saiya samu daya daga cikin kujerun falon ya zauna yana amsa wayar "Ni zaka yiwa haka anwar?,ni nafisa zaka gujewa saboda wata banzar shahida da bata kama qafata wajen qaunarka ba?,idan baki sani ba bari yau na fada maka,ni nafisa nice silar duk wani arzqinka,nice silar duk wani matsayi daka taka a yau,nice silar zamantowa abinda kake a yanxu,amma sakayyar da zaka yimin kenan?,ka zabi wata akaina?" "Kin gama?" Ya furta a nutse yana saurarenta,jin batace komai ba yasa ya dora "Na farko ba wani bawa daya isa ya azurta wani bawa dukkaninmu muna cine cikin taskar ubangiji,abu na biyu banyi zabe ba hakan ban fifita ba,kece wadda kika zabarwa kanki haka,ko a yanxu kika yarda da abinda nazo dashi,kika amince da cewa qaddararmu ce gaba daya ina maraba da hakan,saboda haka zabi ya rage game shiga rijiya" daga haka ya datse kiran ya aje wayar gefanshi,yadda yake tsammanin zai damu ko zaiji ciwo saiyaga duka ba haka bane,abu daya cikin daruruwan daya sanya ya kasa baiwa nafisa koda digo daya cikin dari na so ko qauna a zuciyarsa kenan,bata da lafazin magana,bata da tarbiyya yiwa kai waigi a duk sanda rai ya baci,ya godewa Allah daya sanya ya maida dukkan kudaden da kamfani da kuma alhj abba ya bashi a wancan lokacin ya zabi yaci gashin kanshi ba tarema da yasan waye yayi silar zuwanshi wajen ba,saiya dauki coffensa a hankali ya soma kurba ba tare daya ji wata gagarumar damuwa ba. Kira ya sake shigowa wayar tashi,ya dauka itace dai sai yaga anty usaina,ya amsa wayar bayan sun gaisa ga gaya masa komai ya kammala kuma jibi ne zasu miqa lefan "Shikenam babu damuwa,Allah ya nuna mana,saidai na nafisa ki ajesu wajenki,zan shigo gobe zamuyi magana" "Allah ya nuna mana" ta amsa masa. Wayarsa ya dauka yana duba jerin numbers din dake cikin wayar,kaf wayar babu number dinta,ba abun mamaki bane don yasan dama da zaman hakan,rabonshi da number dinta ta rabi wayarshi cikin xamanin da yake amfani da waya keypad,wayar da har yanzu bai rabu da ita ba,hakanan baisan dalilin qin rabuwa da ita ba,saiya koma neman number wayar sulaiman,bugu uku ya daga,suka gaisa ya gaya masa ya kaiwa daada wayar,ya shaida masa yana kusa da ita,sabida haka ya miqa mata wayar,bayan sun gaisa cikin mutunta juna sun dan taba wasa irin na jika da kaka da suke lokaci zuwa lokaci,don jin anwar din take kamar jikanta na jini "Jibi xasu miqa kayan daada,na nemi number dinta ban samu ba,ko zaki nemi wani cikin gidan a shaida masa" "Karka damu,sule nada lambar zubaida,yanzu zansa ya kirata ya gaya mata" hira suka dan qra tabawa kadan yana tsokanarta sannan sukayi sallama. Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke yana kurban coffensa idanunsa saman tv da aka ragewa volume sosai,tunani nason fisgarsa yana jefashi wata duniya can,zamanin da dukkaninsu shida shahidan keda buri da fatan mallakar junansu,zamanin da kowannensu yake kwana ya kuma tashi da marari soyayya da begen dan uwanshi,a sannan dukkan mafarkinsu da fatansu ya ta'allaqa ne akan lokacin da zasu zama mallakin juna,lokacin da dukansu shida ita quruciyarsu ta ninka ta yanzj qwarai,bai mantawa wani lokaci daya je hira suna hirar qawar shahida da aka kaiwa lefe,ganin yadda yake nuna buri da fatan yiwa shahidan lefe mai yawa na kece sa'a yasa tace "Nifa yaa anwar,basai ka takura kanka ba,nifa ba wani lefe da zakamin,ni ba kaya nakeso ba..." "Me kikeso...?" Ya fada yana tsareta da ido cikin wani salon kallo da baisan yana mata ba saboda shagwabarta data tafi dashi,yasandai cewa sanda yake kallonta din soyayyarta da qaunarta na narkewa tana sake kwaranya cikin magudanan jininsa,kallon da yake mata ya sanyata jin kunya harta rufe fuskarta da tafukan hannayenta tana dariya "Kai nakeso ni" "Na sani shahida,amma kullum burina shine na daga darajar shahida cikin mata,kullum burina shahida tafi kowacce mace a duniya,indai ina dashi dole shahidana ta fita daban,kita min addu'a shahida,idan na tashi zan miki lefe irin wanda kowacce mace xatayi burinsa" idanunta ta zaro tana kallonshi "Ya anwar?,ranar kuwa zanyi bacci?,ya anwar dina yayimin kaya irin haka ranar kowacce mace saidai ta biyo bayana" "Qwarai kuwa,wannan dan qaramin bakinkin ya iya furta kalmomi masu zaqi da tsayawa a rai" dariya sukayi a tare tana kife fuskarta akan cinyarta. Yana kawowa nan wani qaramin murmushi da bai shirya ba ya subuce saman fuskarsa,saiya aje cup din,lokaci guda wani abu yayi kutse cikin farincikin daya tsinci kasa,ya soma juyawa zuwa bacin rai,da sauri ya soma furta la'ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minazzalimin,saiya miqe ya dauki cup dinsa ya haura sama inda bedroom dinsa yake dashi. ***** ******* ********* "Ina kwana anty" shahida ta fada sanda take sanya kanta cikin kitchen tana daura agogon hannunta,anty zubaida ta amsa hankalinta na wajen siyayyar da akayi mata tana dubawa,sai data gama daura agogon sannan ta daga kai,turus tayi yadda taga kitchen din ga kacame da kayyaki "Anty,wadan nan kayan kuma fa?" Ajiye dan qaramin botikin butter din data duba tayi "Kayan aikin abincin masu kawo lefe ne" wani mummunar faduwar gaba taji ta ziyarceta,duk wani dan kuzari data samu ta sauko dashi yau ya soma yin nashi waje,saita dan dafe kujerar dake kusa da ita "Lefe kuma?" Kai anty zubaida ta kada tana karantarta "Eh,jiya da dare daada ta gayamin" sai kawai ta kada kai tana qoqarin hadiye wani abu,ba tare data ce komai ba ta juya ta fice a kitchen din,ko abincin break dake saman tebur bata saurara ba ta fice daga gidan,ta samu mai adaidatanta na jiranta ta shiga ta zauna yaja suka bar gidan. Ko data isa office rufe kanta kawai tayi ba tare data bar kowa ya shigo ba,ta rasa shin kuka zatayi ko kuwa,idan tayi kuka babu mai sauraren kukanta,idan bore zata ci gaba dayi wanda zatayiwa borenma bata ganshi ba,wannan wanne irin cin zaline anwar ya shiryawa rayuwarta?,me yasa zai bibiyi rayuwarta da irin wannan sakamakon na daban,tunda bai ra'ayinta ya barta tayi rayuwarta cikin salama,irin rayuwar da zata samu nutsuwa mana,saiya shigo don ya rusata?,ya rusa dukkan walwala da farincikin data jima tana tattalinsu da rainonsu?. Kusan haka ta wuni cikin kamfanin babu cikakkiyar madafa ko mafita,don haka suna tashi ta yanke shawarar zuwa gida,donkarta koma ma ta tadda su anty zubaida na aikin kayan masu kawo lefe,lefen da takeji kamar ta cinnawa mai lefen da lefan kanshi wuta.*AA* 3️⃣2️⃣ Sallama tayi a tsakar gidansu,khadija dake qofar kitchen tana tankadewa umma dake cikin kitchen garin tuwo ta amsa,a matuqar kasalance kamar wadda tayi aikin shekara ta tsaya da qofar kitchen din tana gaida umman,ta waiwayo ta dubeta sannan ta amsa tana karantar yanayinta,khadija na gaidata ta amsa mata tana shigewa falonsu,jakarta ta aje waje daya sannan ta cire mayafinta ta dora akai,ta samu daya daga cikin kujerun falon ta kwanta tana sauke numfashi a hsnkali,saita tashi ta sake qaro gudun fankar dake sama tana juyawa ta sake dawowa ta kwanta a riginginen dai,haka kawai zuciyarta tayi wani rauni,hawaye ya soma bin kumatunta yana zirarowa gefan fuskarta,ta dinga shareshi akai akai,duk sanda ta tuna anwar zata aura sai taji zuciyarta ta quntata,a ganinta bata dace dashi ba,bata cancanci mutum kamarsa ba,tunda a baya ya iya guje mata a gaba babu abinda zai hanashi aikata hakan,bugu da qarima gaba daya auren manufa zaiyi da ita,yayi ne don kawai ya rusa walwalarta ya rabata da nuradden. Umman ta dan jima tana kallonta ba tare data sani ba kafin tatako zuwa cikin falon,ta samu kujera daya ta zauna sai a sannan shahidan ta ganta,miqewa tayi daga kwanciyar kuka na balle mata sosai,baki ta sake umman tana dubanta sannan tace "Saikace qanqanuwar yarinya zaki tasani gaba kina kuka?,meye hakan?" Zamowa tayi daga saman kujerar da take kai tayin kneeldown a gaban umman ta kama hannayenta "Don girman Allah umma ki dakatar dasu,ke daya ce burina na qarshe,wallahi umma bana sonshi shima baya sona,ku aura min koma waye umma amma banda anwar?" Idanu ta saka tana kallonta,a iya saninta abinda ya faru tsakaninta da anwar ma laifi nata ne,iya abinda ta saninma baiyi zafin da zata rikice hakan ba harta rasa sukuni da walwala ba,Yayin da khadija wadda shigowarta kenan ta tsinci xancan ta dafe baki gami da zare ido cikin mamaki,har batasan sanda tayi subutar bakin cewa "Yaaya?,ya anwar ne fa?" Daga kai umma tayi tayi mata nuni data fice,haka ta fita cikin dimbin mamaki,ta zaci antyn tata zatayi farinciki da dawowar anwar rayuwarsu fiye da yadda su sukayi,amma ga sabanin hankalinta sai taga ba haka bane sam. A nutse umma ta zuba mata idanu,cikin sanyin murya wanda ke nuna har jikinta ma a sanyaye yake tace "Ashe so kike ki tona mana asiri shahida bayan lullubin sutura da Allah yayi mana?" Ta qarasa maganar wani abu na taba zuciyarta wanda ya bayyana har a muryarta "Shahida ashe baki qaunata?,ashe ba rufin asiri Allah yayi miki ba damu kanmu daya dawo miki da anwar?,meye a zuciyarki shahida?,bakison farincikina ashe da walwalata?"kai shahida ke girgizawa kuka na qwace mata "ba haka bane umma,umma bana sonshi kiyi haquri umma,wallahi banajin sonshi kwata kwata" "Shahida indai nice na haifeki ina....." "A'ah,karki qarasa don Allah umma" sukaji wata murya da sako kanta kenan dakin ta tsinci zancan shahida na qarshe da lafazin umman ta fada,dukkansu suka juya suna kallonta,anty usaina ce,ta qarso inda suke zaune,wajen shahida ta nufa kai tsaye ta kama hannayenta sannan ta zauna gab da ita,hankalin umma yadan tashi kadan don ba zataso shahida tacigaba da magana kan anwar ba,don tana da tabbacin batasan wace ita a wajenshi ba "Idan kika fadi haka kamar kin mata qarfa qarfa ne ai" tana kallon umman tayi maganar,wani sanyi shahida taji cikin ranta,tana fatan Allah yasa zuwan matar ya zame mata haske "Idan kuma tana da hujjarta fa wadda tafi taku qarfi?,ki barta aji hujjarta da dalilanta tukunna". Miqewa umma tayi " bata da wata hujja ko dalili usaina" "A'ah bari naji ta bakinta tukunna" "Koda kinji ta bakinta na riga na yanke matuqar nina haifeta ina bata umarnin auren anwar" daga haka umma ta fice daga dakin tana mamakin wauta da sakarcin da shahidan takeson tafkawa,kamar batasan meya wakana cikin rayuwarta a baya ba,bata taba tsammanin ma anwar zai sake waiwayar shahida yace zai aureta ba sabida abunda idanunshi suka gane masa a zahiri ba labarj,dama tazo mata tanason tayi wasa da ita?,koda taqi anwar din batajin zata samu kamar anwar din,mutumin da tun wancan lokacin ya samu karbuwa cikin kaf danginta na uwa da uba,badon komai ba sai kyawun halayyarsa da kyawawan dabi'un da Allah ya huwace masa. Maido dubanta kan shahida tayi bayan ficewar umma,suka hada idanu,hakanan shahidan taji gabanta ya fadi,ta dauke nata idanun tana matsar qwalla,cikin taushin murya ba tare data saki hannunta ba tace "Shahida....inason naji meye matsalarki dashi wannan din da umma tace saikin aura,indai naji dalilanki masu qarfi ne nayi alqawarin tsaya miki harsai an warware komai" shuru na 'yan sakanni ya ratsa tsakaninsu,batajin zata iya furtawa wani komai,yin hakan kamar ta dabawa cikinta wuqane,tana ji ceqa wani sirri ne agareta ga duk wanda baisan meye faru ba,a hankali ta motsa labbanta sannan tace "Kawai bana sonshi,shima kuma baya sona,hasalima mun rabu dashi a qalla shekara shida kenan,ba wanda keda muradin wani" shuru anty usaina tayi tana nazarin kalamanta,ba shakka akwai wani abu,amma dukkansu amsa kusan guda ce,jiya jiya ta titsiye anwar din kan meye sanadin rabuwarsu da shahida amma ya kasa bata amsa daya qwaqwqwara,kowannensu bayason fallasa asirin dan uwanshi,hakan na nufin akwai ragowar wani abu da yayi saura game da zukatansu qarqashin zukatansu kenan koda su basusan da hakan ba? "Amma shahida....ya akayi kikasan baya sonki?,kuma dama an taba rabuwa hakanan babu wani dalili?"tambayar taso kaita maqura saboda rashin amsa "Miji da mata ma kan iya rabuwa haka kawai ya saketa badon ta masa komai ba,saidon qarewar wa'adin zamansu da Allah ya qaddara musu" saitayi shuru tana hadiyar zuciya tana neman amsa ta biyu da zata bata wadda zata gamsar da ita,da qyar ta iya hada abun fadi bayan anty usainan tace "Uhmmm,ya akayi kikasan baya sonki?" "Duk wani abu na nuna kulawa ko xiyara da zai nuna saurayi yana son budurwa babu shi tattare dashi,sau daya ya taba zuwa wajena,shima bamuyi ganawar dadi dashi ba,ta yaya zance yana sona?" Ta qarasa maganar badon abinda ta fada ya dameta koya dadata da qasa ba,a'ah,ta fada ne kawai donta riqeshi hujjar da anty usaina zata taimaka mata ta rana wannan auren da take kallonsa a matsayin qarfen qafa mai wuyar kwantuwa a gareta. Lallai ya zama dole ta shiga alaqar shahida da anwar,tana fata nan gaba dukkansu suyi dariya,tana fatan ko meye silar shiga tsakaninsu nan gaba ya zama tarihi,rayuwarsu ta koma kamar yadda take a baya "Naji dadi da kika kasance yarinya mai biyayya wa iyayenta,ina mai miki kyakkyawan fatan ba zaki toxarta ba in sha Allahu,biyayyarki zata kai miki da ixinin ubangiji" da wannan kalaman sukayi sallama,ta fice daga gidan bayan ta samu umma ta roqeta kan karta gaya mata dangantakarta da anwar,donta tabbatar hakan zai baiwa shahidan kunya. Tun a kan hanya ta soma gwada number anwar din,saidai bata sami wayarshi ba akashe take,da alama yana muhimmin wani abune,dole ta katse kiran ta isa gida,saidai lokaci lokaci tana gwada number tashi ko xata dace ta shiga. Tana idar da sallar magariba ta soma shirin barin gidan,umma ta dubeta "Amma da kin dan jinkirta tafiyar tukunna,saboda garin a dinke yake da hadari ga iska ta soma kadawa" "Idan ya sauko bansan ranar da zai dauke ba,anty zubaida kuma zataji shurun yayi yawa,don ban gaya mata ma ina nan ba" "Shikenan,Allah yayi miki albarka,yasa albarka a rayuwarku" "Ameen" ta amsa tana maida qwallar dakeson fitowa,haka ta baro gidan tana tafiya kamar wadda batason taka qasa,wanda bai sani ba sai ya zaci salo ne ko tana sane,amma ba komai bane sai tsabar damuwa dake cinta a rai,tana jin yadda hadarin ya taso sosai sanda takai tsakiyar layin nasu,iska ta dinga kadawa tana ratsa jikinta,saidai sam bata damu ba,bata damu da ruwan ya sauko ya daketa ba,hakanan bata damu data koma gida donta samu mafaka ba. Daidai lokacin da motarsa ke tsaye qofar gidan anty usaina wadda ta buqaci ganinsa a yau basai gobe ba,yana zaune cikin motar baikai ga yiwa mai gadi horn ba bare ya bude masa,ya tsaya ne amsa waya,dukka gilasansa a rufe suke ruf kamar yadda al'adarsa take yawanci idan yana cikin mota,bugu da qari kuma ma sabida iskar dayaga ta taso sosai,wanda yasan ba za'a rasa qura ba cikinta,gefansa ya kalla kamar wanda aka fisgi hankalinsa,sai yaga kaman itace ta wuce,yaci gaba da amsa wayar yana kallon bayanta,tabbas ita dince,amma me take har war haka duhun magariba ya mamaye gari bata koma gida ba,idanunsa suka ci gaba da kallonta har lokacin data dan bada tazara daga inda yake,yana shirin janye idanunsa yaga yayyafi ya soma sauka ta gilashin motarsa,yaso ya dake yaso ya dauke kai ya saka motarsa cikin gidan anty usaina amma saiyaji kaman umarni,a zafafe yace "Oh god" yana zare belt din jikinsa,cikin zafin nama da kuma jin haushin kansa da kansa ya bude murfin motar ya fice. Yana kuzari da halittar ba daya bace,hakan ya sanya cikin qididdgaggun taku ya cimmata "Daga ina kike haka?" A nutse ta waiwayo tana dubansa sanda take gab da qarasa bakin titi,saita juya da niyyar ci gaba da takawa ba tare data amsa shi ba "Wai sanda zaki fita ma kin tambayeni ne?,saboda tsabar rinton zunubi?" Kalaman sun mata ciwo,wato tun yanzu yake nufin xai mulkata kenan?,hakan yasa ta tsaida tafiyar tata ta juyo ta dubeshi "Kai waye da don zan fita saina tambayeka?" "Kinfi kowa sanin ni waye ai ba buqatar na maimaita miki,banason dogon zance wuce muje na taimaka miki na saukeki,amma kafin sannan idan kina da niqab ki saka a fuskarki kar mutanen unguwa su ganmu tare su zaci nima dan harka ne" ya kai qarshen zancan yana dage girarsa duka biyun,wanda hakan ya masa kyau ainun duk da fuskarshi a murtuke take,sosai kalaman suka fusatata wanda hakan ya sanyata ta juyo gaba daya ta watsa masa idanunta da suka sake budewa saboda bacin rai,hakan ya tilasta masa dan qanqance nashi idanun gami da damqe hannayensa dake zube a aljihu "To hell with your taimako...Allah suturu buqui,har abada bana son taimakonka,sannan kuma aikin banza kake harara a duhu,da kake gudun kar a ganmu tare me ya kaika neman dauramin igiyarka,idan da gaske kake qyamata aiya kamata ka gujeni da gaske ta yadda ko qasa daya ba zaka hada dani ba bare inuwa daya,indai ka cika kai anwar ne ka aikata hakan" qaramin murmushi ya saki daya sake fitar da kyansa,ya dage dukka kafadunsa "Ba zaki taba samun yadda kikeso ba,niba qaramin yaro bane bare kalamanki su tunzurani nayi miki yadda kikeso,abu daya kawai na sani shine,na riga dana biya sadakinki,saboda haka ina da power a kanki ko kinqi ko kinso...saboda haka ki wuce muje" dogon tsaki taja wanda ya ratsa kunnuwansa,sannan ta watsa masa harara ta juya taci gaba da tafiya,bai fasa binta ba shima har suka isa titi. Adaidaitan farko data tsaida ya sallameshi da dubu daya yace yane abinsa,na biyu ma haka,na uku kuwa da yame dattijone yace masa baba kaje matata ce yaji takeson yi,na bata haquri taki haqura,nan yasa bawan Allahn ya tsaya yana mata nasiha,inda daga qarshe ya sallameshi da dubu uku ya amsa yana godiya,ta hudu kuwa ya samu sauayi maiji da tashen girma yaso masa gardama.kan saiya dauketa tunda itama tana son shiga "Kana sha'awar xaman gidan kaso kenan?" Harya karkata baki zai masa diban albarka saiya nutsu ya qarewa shigarsa kallo,tun daga takalminsa,kayan jikinsa zuwa agogonsa,aibabu shiri yaja abun hawansa ya fece,bacin rai ya taru ya rufeta ruf sanda ta kalli titin ta ganshi fayau ba wani sauran abun hawa na haya kuma nan kusa,ta waiwayo zata gasa masa magana ko xataji sanyi,kadan ya rage fuskarsu ta gwaru,sam batasan yana bayanta ba a tsaye,da alama kuma duk tsahon lokacin kallonta yake,baya yaja yana bata fuska "Ke baki da kunya ne?,akan titi kike neman ki rungumeni?,toki maida qwalamarki,ni ba naki bane" kawai saita fashe da kuka ba tare data shirya ba,saboda ya gama cutarta,bata ga wani kalma da zata fada masa ba wadda zata rama abinda ya gaya mata,minti biyu kacal ruwan sama ya soma sauka,ya kalli sama sannan ya kalleta "A karo na qarshe nake gaya miki ki wuce mu tafi" baya taja saman wasu tayoyi da masu faci suka tashi suka barsu a wajen ta zauna,ta gwammace ruwan yayi mata koma meye data bishi kota shiga motarshi,ganin ta zauna dafa'an ya sanyashi juyawa ya koma cikin layin don dauko motartashi zuwa nan bakin titin dukda yadda ruwa yake dukansa. Yana isowa wajen yaga tashinta cikin adaidaita sahu,qaramin murmushi ya sube masa,wato dama tana da taurin kai kenan?,saiya sake baiwa motar wuta harsai daya je daya side din na adaidaitan,ya tabbatar ta ganshi sannan ya barsu suka wuceshi,a baya yaci gaba da binsu har xuwa sanda yaga shigarta gida sannan ya karya kan motar ya koma gidan anty usaina. Sanda ta shiga gida baqinciki da takaici ya sake cikata ganin yadda gidan har baqi yadan samu,hakanan ga kayan amsar lefe a kammale gobe kawai suke jira,hasina ma ba'a barta a baya ba,ganun zata saka mata ciwon kai da tsokanarta yasa tayi zarcewarta daki ko tsayawa a wajen batayi ba bare ta zauna,gaban mudubinta ta tsaya tana kallon yadda ta jiqe gaba dayanta,haushinsa ya sake cikata,taji kaman ta sake fashewa da wani kukan,duk shi yaja mata,da ta shiga adaidatan a lokacin daya dace da duk hakan bata faru da ita ba,haka ta ringa cire kayanta daya bayan daya ta daura babban towel ta shige bandakinta ta hada ruwa mai zafi tayi wanka. https://youtu.be/alR4jOvvQUc *Alqawarin Allah* 3️⃣3️⃣ Washegari da wuri tabar gidan fiye da yadda ta saba fita,ko a kamfaninma masu gadi kawai ta taras,ta bude office dinta ta shiga ta zaun donko mai maita shara ma bata iso ba. Sanda aka tashi ta tsaya tunanin inda zata,don tasan wala'alla dai dai lokacinne ma gidan yake a cike,yankewa kawai tayi ta tafi gidan oga rayyan,ba bata lokaci ta gayawa mai adaidaitanta ya wuce can da ita. Sosai taji dadin zuwa gidan,a rayuwa gidan yana burgeta qwarai,yanayin mu'amalar jama'an gidan,nan wajen raihana ta zauna suka sha hira sosai,sai bayan sallar magariba sannan tayi haramar tafiya,nan ta cikata da turaruka tana cewa "Gashi amarya,naji oga yace kin kusa shiga daga ciki,ki fara amfani da wadan nan kafin lokacin xan kawo miki na amare" "Hmmm" kawai tace tana dan fitar da murmushin da baikai zuci ba daga fuskarta. Tun daga harabar gidan zaka san cewa ansha baqi a gidan,bata yarda tabi ta qofar falo ba saita bi ta qofar baya tayi shigewarta dakinta,kayan hannunta ta aje ta rage kayan jikinta ta shiga wanka,bayan ta fito ta murza manta mai qamshi ta saka riga mara nauyi,ta ciro wayarta daga jaka kenan taga miscal din zunnurah,sai fuskarta ta washe da fara'a,ba bata lokaci tabi kiran,bugu biyu ta daga,abu na farko data fara shine guda ta sakar mata,bacin rai ya bijirowa shahidan,wato kiranta tayi donta tsokaneta kenan?,sai kawai ta yanke kiran,ta nufi gadonta ta hau ta kwanta rub da ciki tana lumshe idanunta,dai dai nan hasina ta turo qofar "Au yaushe kika shigo?" Banza tayi da ita kamar bata ji ba,hakanan taqi bude idanunta,don tasan qarshenta itama tention xata qara mata kawai "Shahida" hasina ta sake fada tana matsowa dab da gadon,ta dora hannunta saman filon tadan daka,sai a sannan ta ware idanunta tana dubanta "Bacci nakeji,don Allah ki barni na huta" murmushi hasina ta saki "Amma na miki jaje da zaki kwana bakiga kayanki ba wallahi,kallo ya barki" qur ta mata da idanu kafin taja qaramin tsaki ta maida kanta daya barin tana rufe idanunta,dariya ta sheqe sosai da ita sannan ta juya ta fice tana waqar amarya. Da sauri ta diro daga saman gadon ta isa bakin qofar ta saka key ta kulle sannan ta sake dawowa ta kwanta,tana gyara kwanciyar tata tana mita ita daya gami da jan tsaki lokaci lokaci,rigingine ta kwanta tana kallon roofing din dakin,idanunta a kulle gam tanason tilasta kanta tayi bacci. Haka aka dinga mata knocking tana ji ta share,donko hasina yau saidai ta kwana wani dakin amma ba nata ba,kadaitaka kawai yau take da buqata. Sai sha daya da wani abu na dare sannan bacci ya soma fisgarta,qarar wayarta yasa ta bude idanunta ahankali kan wayar dake aje saman cikinta,ta daga wayar tana dubawa,lambace babu suna,kaman ba zata daga ba sai kuma ta daga kana ta kara a kunneta gamida yin sallama,can qasa taji an amsa sallamar har bata tantance muryar waye,shuru ya ratsa da wasu sakanni "Nuradden" ta canki sunan "Shahida,na rasa ta ina zan fara koyawa kaina haquri dake" idanunta ta lumshe tana jin bacin rai na ratsata "Kayi haquri noradden,duk ni na jawo mana komai,da ace banyi jinkirin hanaka zuwa gidanmu ba da guni hakan duka bata faru ba" "Ki tayani addu'a kawai,Allah ya yayemin,don ba lallai bane na daina sonki" daga haka wayar ta katse,a sanyaye ta ajiye wayar ta mirgina daya barin nata,harga Allah bata tausayin kanta kamar yadda take tausayin nuradden din,ya riga ya fada da yawa,ta kuma son ciwo da radadin soyayya,musamman a sanda ka rasa abinda kake tsananin so ka kuma saka ranka dashi,a hankali kalamanshi suka fado mata,baya neman yaradarta,bata cancani ta rayu cikin farinciki ba ta zabi wanda takeso,zai aureta ne don ya nuna mata ya isa,lebanta na qasa ta cije tana rarrabe maganar da abinda yake nufi,auren manufa zaiyi da ita kenan?,zaiyi ne don cimma wani boyayyen nufi nashi?,lallai zata nuna masa yayi ganganci,akwai banbanci tsakanin da da yanzu,ta jima ahaka tana saqa abubuwa da yawa tare da tunawa da al'amura masu yawa kafin bacci yayi nasarar saceta. Washegarima kusan fitar wuri tayi,tana tsaye a kitchen tana shan ruwan dumi anty zubaida ta taras da ita "Ba zakiga kayan ba kenan zaki fita" agogonta ta kalla sannan ta sauke hannu "Sauri nake anty" "Hakan yasanya jiya nace a tasoki ki gani ai" baki ta tabe a fakaice tana tuna haushin da hasina taso tura mata ajiyan da yadda ta matsanta mata,kayan da bataga abinda anwar zai zuba a ciki da zasu burgeta ba "Idan na dawo na gani,saina dawo anty" ta fada cikin hanzari bayan ta dauki jakarta data aje ta rataya tana ficewa da hanzari,kasa cewa komai anty zubaida tayi sai binta da kallo kawai da tayi harta fice sannan ta girgiza kanta tana tadi ita da zuciyarta,ko ba'a fada ba tasan ganin kayanne bata sonyi. Kwana uku tana cewa anty zubaidan zata gani amma bata yarda taje inda sukebama bare ta gani,dole ta gaji ta zuba mata idanu,a haka har akaci kwana goma sha biyu,ga tsammanin anty zubaida shahidan zata dauki hutu wajen aiki,saidai taga ko ajikinta bata fasa fita aikin na,sake qara mata kwana biyu tayi taga ko zata dakata da fitar,saidai ranar daya rage biki saura kwana bakwai cif da safe anty zubaida ta sameta a falo tana karyawa ta gama shiryawa tsaf,kallonta sosai take taga da gaske take fita aiki zatayi?,kallon harya sanya shahidan itama yin sak tana kallon anty zubaidan,saidata soma dan tsuke fuska sannan tace "Ina zaki haka da safe?" Tambayar tadan baiwa shahida mamaki,ko maqota sunsan inda taje zuwa daga safiya zuwa yammaci bare anty zubaidan,don ita bata kawo tambayar tata nada alaqa da aurenta ba "Office mana anty" ta fada cikin son gamsar da ita,kai anty zubaida ta girgiza "Bakisan aurenki saura kwanaki bakwai ba ko lissafi ne ya qwace miki?,ko kuma duka kina sane saboda kinha na zuba miki ido ne?"wani abu ya taba zuciyar shahidan,ba zancan data tsana a yanzu irin zancan aurenta,tana sane saura kwanaki bakwai su qullashi to amma ita meye nata a ciki?,me zata zauna gida tayi " to anty,ni menene nawa a ciki?,me zan zauna nayi a gida?" "Eh babu komai naki a ciki tunda zubaida ce zatayi aure,so kike duniya ta zagemu ko?,tunda kike kin taba ganin amarya budurwar da aka aurar salin alin?,to banason sakarci,babu ruwana da wani abu daya taba gittawa tsakaninki da anwar ni aikina zanyi kawai,rawata zan taka,saboda haka ki koma ciki daga yau zansa abban huda ya dauka miki excuse,su baki hutun sati uku" kaman ta zunduma ihu haka taji sanda anty zubaida ke maganar,abinda ta dauka wasa ne gashi yana neman tabbata,ba damar musu da ita saboda yadda ta tsare gida sosai,haka shahidan ta soma takawa don komawa dakinta "Eheennn...jimana" anty zubaida ta sake fada,saita tsaya gami da waiwayowa tana dubanta,sai data kallo agogo sannan tace da ita "Qarfe sha daya na rana zamu fita dake,ki zauna cikin shirin" kai ta gyada kamar kazar da qwai ya fashewa cikin cikinta,haka ta dinga tafiya harta isa daki,ta watsar da duka kayanta kanta na daukar zafi,me yasa anwar yake son ya soma da nasara da sa'a a kanta?,me yasa anwar ya dawo cikin rayuwarta bayan bata da buqatarsa?,haka ta dinga yiwa kanta tambaya ranta na zafi. Sha dayan da 'yan mintina suka fita ita da anty zubaidan kawai,bata tambayeta ina zasuje ba har saida suka isa gidan sannan ta fahimci wajen gyaran jiki ta kawota,tamkar wata doluwa haka ta dinga bin anty zubaida da kallo har suka gama gaisawa da matar da gabatar da shahida wajen matar a matsayin amaryar da za'a yiwa bikin "Kai tubarkalla masha Allah,wannan badon hausawa suna cewa idan kana da kyau ka qara da wanka ba ai bata buqatar komai,saida nasan gyaran ba qaramin hawanta zaiba zubaida" tana jinsu harta gama surutunta ta soma hada kayayyakin gyaran jikin ta buqaci shahida ta sauya wani zani na daban data dauko.mata,fuska ta bata tana duban anty zubaida ranta na baci ta wani gefan,yanzu saboda anwar ne aka kawota nan wajen "Anty,don Allah abar abunnan,batamin kaya kawai zaiyi" dago idonta tayi daga wayarta da take dannawa ta watsawa shahidan harara,hakanan tana ji tana gani ta sauya zanin aka shiga mata gyaran,bakinta gum tana bin matar da kallo kaman ta mangareta saboda yadda takebin fatarta da kayyakin tana shafeta dasu. Tana ganin kawai bata lokaci da bata kudi ne. A qalla sun kusa kashe awa biyu cur ana abu daya,bin jikin nata take da kallo yadda ya soma wani santsi sulbi da sheqi na musamman,tabe bakinta tayi data tuna saboda me akayi mata,sai taji gyaran sam bai burgeta ba,tana maida kayanta wani qamshi na tashi daga jikinta duk sanda ta motsa,turarukan qarshe da aka murje mata jikinta dasu. Basu jima ba suka isa gida,a falonta zauna cikinsu huda wadanda ke kallo,faruq ya kalleta "Anty harkin fara canzawa,kaman bakeba akan dazun da kuka fita'binsa tayi da ido kawai ba tare datace komai ba,kafin ta gama tunanin da take ta jiyo muryar huda "anty...zamuyi kewarki,tafiya zakiyi yanzu ki barmu?"ta qarasa fada a shagwabe kaman zata saki kuka,nan take ran shahida yaso ya sake baci da tuna hakan da tayu,anty zubaida ce ta katse komai tana tambatar faruq me suka dafa musu,yace white rice ne bazai iya miya ba,hararsa tayi "Daga kai har haidar din a rasa wanda zaiyi miya?" Huda na gefa na musu dariya,kai ya langabar "Allah ummi shi yasa nace ki samo mai aiki fa" tsaki taja sai shahida ta miqe "Bari na hada" tafurta tana yin gaba zuwa kitchen. Kayan miya ta diba ta soma gyarawa sannan tayi blending,dukka rabin hankalinta da nutsuwarta nakan tunani,data hada miyar saita zauna cikin kitchen din tana duban agogo,tasan zuwa sanda zata gama hudu tayi saita da alwala kawai gaba daya. Miyar na soyuwa haidar ya shigo yana shaida mata tazo inji anty zubaida,saita rage wutar can qasa yadda ba zata kama ba kafin ta dawo ta fito zuwa falon,a zaune ta sameta da tulin kaya a gaba da alama sabbabi dinkuna ne tana dagawa tana kalla gami da ware wasu gefe "Kije waje kinyi baqo"gabanta yadan fadi,tadan bata fuska " waye haka da la'asar din na" "Ban sani ba nima,idan kinje zaki gani" hakan yadan kwantar mata da hankali jin ba wanda ta tsani ganin bane,nan kan kujera ta dauki mayafinta data dawo dazu dashi ta yafa sannan ta fice. Matashin saurayine mai kyau da aji tsaye jikin motarsa,sanye yake da shadda riga da wando dinkin tazarce,hankalinsa duka nakan wayarshi a haka ta kusa cimmasa,bata sanshi ba amma sai take ganin tasan fuskar a wani waje daban ko can da dadewa,sallama ta masa ganin baisan da isowarta ba,ya daga kai da hanzari yana amsawa fuskarsa ta fadada da fara'a "Barkanki da yamma kin wuni lpy" "Lafiya alhmdlh" ta amsashi a taqaice "Ya mutanen gidan kowa da kowa lafiya?" "Lafiya qalau" ta sake amsawa tana mamaki ina ya santa tare da zurfafa tunaninta ko zata iya tuna a inda ta sanshi,murmushi ya saki "Nasan baki sanni ba,ni sunana muhsin,aboki kuma aminin anwar" lokaci daya maganar ta sauka a zuciyarta,sai yanayin fuskarta ya soma sauyawa,fuskarta ta soma tsukewa,duk da haka tadan dake hadi da qoqarin sassautawa,shima dubanta yake yana karantar sauyawar yanayinta lokaci kadan,bai sake cewa komai ba ya bude murfin motar da yake jingine a jiki ya zura hannu ya ciro wata babbar envalope da qarama ya miqa mata,kallon envalope din tayi sannan ta dawo da kallonta kanshi alamun neman ba'asi "Katin gayyata ne na dinner ko zaki gayyaci qawayenki,wannan kuma kudine ko zaki buqaci wani abu" kai ta girgiza tana danja baya,a fuska tana ganin mutuncinsa amma baya ga haka so take taci masa mutunci ne shida wanda ya aikoshin,amma duk da haka ba zata kasa bashi saqo ba "Ka maida masa dukkan kayansa,ka gaya masa aurensa baya buqatar wani shiri tunda a shiryensa aka qulla shi,kudi kuwa baiyi kudin bani ba a yanzu har zuwa nan gaba,ka gaida na gode" daga haka ta juya zuwa cikin gidan tana takawa a nutse,da kallo ya bita qwaqwalwarsa cunkushe da tunani da mamaki,kullum kwanan duniya sake mamaki yake kan meye haka mai girma daya raba kwanunansu ya tarwatsasu haka zuwa pieces suka kasa kuma daidaita tsahon shekarun?,amsar daya kasa samunta kenan haryau daga wajen anwar duk da sanda rabuwar ta afku shine mutum na farko daya sha wuya da anwar din kafin rayuwarshi ta daidaita,saiya xagaya ya bude murfin motar tasa ya shiga yana tuna yadda sukayi da anwar sanda zai ya shirya kudin da katin yace zai kaimata da sunanshi,har kusan haurawa sukayi kan koda zaikai din yakai amma bada sunanshi ba. Iska ya furzar daga bakinsa lokacin da muhsin ke zaune kan daya daga cikin kujerun office din yana sake tambayarsa wanne laifi ya aikatawa shahida haka?,ya dubi envalope din daya fita dasu ya dawo dasu kamar yadda suke,hakan na nufin bata karba ba kenan "Bata karbi kayan daka kai din ba kenan?" Anwar ya tambayi muhsin kai tsaye yana dubanshi,kai ya kada "Ni duk ba wannan na tambayeka ba,inason gyara wannan barakar ne shi yafi damuna,banason alaqar taci gaba da tafiya a haka" "Me ta gaya maka sanda kaje?" Ya sake jeho masa tambaya ba tare daya damu da nashi bayanan ba "Batace komai ba" murmushin yaqe ya saki,takowa yayi kusa dashi kujerar dake fuskantarsa ya zauna "Ta fadi maganganu a kaina,takuma ce ba zata karba bata buqata right?" Idanunsa cikin na muhsin ya fada,kauda idonsa muhsin yayi saboda shi kansa wasu lokutan anwar na masa kwarjini da yawa "Kaga malam nidai bance maka haka ba,banason tone tone" miqewa yayi yana jijjiga kai "Ta fada,na santa kamar yunwar cikina" gaban envalope din ya qarasa,ya farke dayar ya cire kudaden ciki ya janyo locker din office din nasa ya zubasu ciki,sannan ya janyo daya locker ya ciro wasu ya musanyasu dasu ya maidata ya manne muhsin na kallonsa,ya kwashesu duka ya aje masa key saman teburinsa "Idan ka gama ka rufe ko ina" daga haka ya juya yana takawa sannu sannu zai fice daga office din "Wait mana malam,ina zaka je?" Murmushi ya jefa masa ya fita ba tare daya amsashi ba. Gidansa ya soma isa ya bude sashensa ya shiga,ya aje kayan hannunsa,bandaki ya shiga ya tara ruwan wanka mai dumi ya sake wanka sannan ya nemi abinci yaci ya qoshi,wardrobe dinsa ya bude ya zabi kayan da yaje gani sun dace da irin wannan lokacin ya sanya,ya tsaya gaban mudubi yana taje kansa gami da kallon kansa yadda kayan suka amsheshi,tuna abinda ya faru tsakaninta da muhsin yayi,saki yaja,wato ita mai taurin kai ko?,har yau bata kallon laifinta sai wani take dorawa alhakin faruwar komai ba tare data duba nata laifin ba,aikawa yaso yi direct inda dole ta karba saqon,amma hkanan yaji yana son yaje yaga hawayenta ya takaleta ya kuma tsone zuciyarta,saiya aje cumb din yana daura agogon fata sannan ya zauna ya daura takalmansa ya feshe jikinsa da turare ya dauki key din motarsa ya fito. A hankali yake tafiyar kaman bazaije ba,karon farko da zai fara zuwa gidan anty zubaida kenan,yadan yi nauyi a hanya hakan yasa bai isa ba sai qarfe shida mintina hamsin suka rage kenan a yi sallar magarib. Maigadin gidan anty zubaida ne ya iso ya bashi hannu don suyi musabaha,cikin tantama yadanyi jim don yana ganin bai kamata suyi hannu da hannu ba "Mu gaisa mana abokina,bakason ladar ne" da sauri ya miqa masa suka gaisa "Inason magana da wata yarinya shahida a gidan nan ne" cikin washe baki yace "Au,kaddai kaine angon?" Murmushi kawai yayi sannan ya sake cewa "Idan ka shiga matar gidan zaka sanarwa zuwa na,sannan ka turomin faruqu ko haidar" "Toh...toh" ya fada yana juyawa zuwa ciki. Sanda saqon kiran ya sameta tana daki tana shiryawa bayan ta gama mitar wankan turaren da anty zubaida ta kafa nata dokarshi,turaren na nata dadi da qamshi amma tuna dalilin yinsa ke qona mata rai da dagula mata lissafi,tsaki taja sanda huda ta gaya mata ana kiranta,ta shiga mita "Wai wanne irin kirane da baqi haka tun dazu ba za'a bar mutum ya huta ba?,haka kawai kana zaman zamanka daada ta tada zaune tsaye cak,ni wallahi na gaji da wadan nan abubuwan,daga wannan sai wancan?" A haka ta shirya ta zari hijabi ta fito "Baqon na waje ai" anty zubaida tace da ita sanda taga ta tsaya ta mata turus,haka ta juya ta fita kaman zata fashe. Faruq ta soma hangowa cikin dakin saukar baqi na gidan baki na motsi da alama hira yake zubawa,harara ta zabga masa duk da bai ganta ba,a haka ta isa ta yaye labulen,tare idanunsu suka sauka cikin na juna,yawun bakinta ya tsaya kowannensu na kallon dan uwanshi ba tare daya dauke ido ba,gani yayi kamar ba ita,fatarta ta sake sauyawa kyanta kaman an matso shi,qamshinta ya soma cika wajen,shima kwarjini taga yayi mata,shigar ta amsheshi,yayi kyau ya sake zama cikakken mutum da hankali da ilimi suka ratsashi,ita ta soma janye idanunta,ranta a hade tsaf ta taka zuwa ciki tana duban faruq,saiya miqe,anwar yace "Zan nemeka kafin na wuce kada kayi nisa" "To yaya" ya fada yana ficewa,sai da taga fitarsa sannan ta zauna hannun kujerar dake a dab da bakin qofar fita,tanason tsareshi da ido donta karanci me ya kawoshi amma batasan me yasa takejin rashin qwarin gwiwa ba,ta maida idanunta kan tafin hannunta tana murzawa ba tare data ce masa uffan ba,hakan ya bashi damar kafeta da ido,ya soma kallonta tun daga yatsan qafarta zuwa saman kanta,yana jin wasu tagwayen abubuwa na fada cikin zuciyarsa,daya nason yaqar daya gami da rinjayarsa,inda daga qarshe dayan yayi galaba,saiya runtse idanunsa yabar kallonta saboda wani bacin rai dakeson shaqeshi,kullum kwanan duniya yana son sasautawa kanshi,yana son ya daina ganin baqinta da baqin abinda ta aikata,yana son abinda idanunsa suka gane masa da hotunan daya gani su bace daga idanunsa ko zai samu salama da rangwame amma hakan ya faskara,sai komai yayi kaman zai goge saiya sake dawowa sabo fil a ransa. Walwalar da yake jin kaman zata samu a ruhinsa ta dusashe,sauran faragar fuskarsa ta bace bat. Zaman kurame ne yaci gaba da wanzuwa tsakaninsu harna tsahon wasu mintuna,sai daya gama zamanshi don kanshi sannan ya miqe,cikin wani taku ya isa dab da ita ya tsaya akanta,kana ya ranqwafa gefanta har tana iya jiyo qamshin ya aje envalope din hannunshi,ba tare daya dago ba yace mata "Baki iya gaisuwa ba saikace a gidan mashaya inda kowa yake ogan kanshi,karki tsammaci xaki gidana da wannan dabi'ar ki tsira,ga saqon da muhsin ya kawo miki daxu kika maidashi nina dawo dashi,idan kin isa karkiyi amfani dashi yadda ya dace kiga yadda zata kaya mana nidake,tunda na fahimci cikin halayen da kika koyo kala daban daban harda taurin kai ko?,good....inason wannan sabon halin naki,idan kin tashi gayyatarki karki sake ki kwaso min tarkacen 'yan maye,ko tarkacen qazaman tsaffin samarinki" daga haka ya dago yana shirin wucewa zuciyarta taje iya wuya,ta kasa daurewa "Idan ba haka bafa?,me zakayi?" Ta fada a tsiwace cikin fushi da fusata,saiya sake dawowa gabanta ya tsaya,ya dubeta na wasu mintuna sannan ya saki murmushi "Ki aikata din sai kiga sakamakon" miqewa tsaye tana masa kallon tara saura kwata sannan tace dashi cikin salo na masifa dake cin zuciyarta "Baka isa ka sakani abinda banyi niyya ba,baka isa komai ba idan ma kana tunin ka isa" murmushi ya sake saki wannan karon mai sauti,yadan buga qafarsa sannan yace "Ko a haka aka tsaya ai inga irin tawa isar ko?,hukuncin da zan miki ba isata kawai zai nuna miki ba,izzar aure da izzar anwar namiji" "Namiji shine zai tsaya takara da abokan adawarshi ya kuma samu nasara,ba wanda zai wafta koya biyo ta bayan gida ba,koya taka wani tsani don kaiwa wannan bigiren,ka daina batawa kanka lokaci wajen kiran kanka da namiji,ba namiji bane kai saidai mata maza" idanunsa ya qura mata qir sanda take maganar cikin dakiya da rashin nuna tsoro,hakanan bilhaqqi da gaske,ganin takai aya saiya soma takowa inda take tsaye,ta tsaya cak don ganin iya gudun ruwanshi,saidai harya iso gab da ita bai daina takowa ba,hakan na nufin zai hade gap din dake tsakaninsu kenan,don haka ta soma ja baya ga zatonta zai tsaya amma ina,bai barta ba sai daya tabbatar ya hada bayanta da bango,qafarshi dake saye da takalmi saman tata qafar wanda yana iya jin zafi zafi na tudun takalminsa daya take mata qafa,kusancin dake tsakaninsu yayi yawa,tana iya ganin fuskarsa tarwai wadda kyau ya cikata gamida iya gyara,idanunsa sai suke juye mata irin na anwar dinta na wancan lokacin sak,janye qwayar idanunta tayi gabanta na bugawa da sauri da sauri,tsoro da fargabar me zaiyi mata na shigarta,saitaga ya daga hannu kaman yana shirin marinta,ta runtse idonta da sauri tana wassafa me zata masa ita bayan ya gama marin nata,ji tayi yaja baya da sauri cikin kaushi yace "Sai na saki kinyi nadamar lafazinki,tsautsayi kuma yasa bakiyi yadda nace miki ba" daga haka ya juya da sauri sauri ya fice daga dakin,cikin hanzari ta daga murya "Idan ka isa ka tsaya mana ka dakenin kaga yadda akeyinta" gab da zai fice ya waiwayo yace "Aiba a gidan syrup muke ba" kalmar ta tsaya tana fassarawa,take wani abu ya cushe mata maqoshi,cikin qanqanin lokaci hawaye ya ballewa idanunta,tana jin zafi a zuciyarta duk sanda yayi wani lafazi dazai iya tuna mata da abinda ta aikata a baya,sulalewa tayi ta zauna a wajen,ba shakka ba'a bari a kwashe duka,shaye shaye ashe wani tabone da tambarinsa bai barin jikin maishi?,koda kowa ya manta ba'a rasa burbushi,ta jima a wajen tana jin ciwo kala kala kafin ta miqe ta fice daga dakin,ko kallo envalope din basu isheta ba bare ta dauka. A falo anty zubaida tace ta tsaya ta duba dinkunanta na biki wanda ita batasan ankai bama,don ko kayan har yau bata kalla ba bare ta gane me takeso a ciki har tayi tunanin kaiwa dinki?,bata cikin yanayin da zata iya zama cikinsu saboda haka tabawa anty zubaidan uzurin kanta na ciwo zata duba zuwa safiya da haka ta wuce dakinta. Washegari sun fito da anty zubaida zata koma gidan gyaran jiki tanata kumbure kumburenta da mita cikin ranta na yadda aka takura mata ba gaira babu dalili faruq dake sharar dakin da uncle hisham ya sakashi sabida zaiyi baqi ya fito da envalope din yana miqawa anty zubaida "Anty wannan a dakin na gansu,kaman na anty shahida ne don jiya na gansu a hannun uncle anwar" hanu tasa ta karba sannan ta waiwaya tana duban shahidan "Me yasa kika barsu a dakin?,abinda kikayi dai dai kenan?" Saita langabe kai,ita abun goma da ashirin,komai tayi batayi dai dai ba,saita saka hannu kawai ta amsa suka wuce,suna shiga mota ta kasa daurewa ta saki kuka tana kife fuskarta saman cinyarta,anty zubaida batace komai ba saidai ta dora hannunta saman bayan shahidan,saida tayi kukan na wani lokaci sannan anty zubaida tace mata.......*Alqawarin Allah* 3️⃣4️⃣ "Abubuwa da yawa da mukeso muke qwallafa rai a garesu ba alkhairi bane ga bawa,kiyi qoqarin rage wannan kaifin qiyayyar kamar yadda annabi yayi umarni saboda kada ta juye miki zuwa soyayya mai zafi daga baya,kiyita addu'a Allah yasa abinda zai faru dake ya zama shine mafi akhairi a rayuwarki duniyarki da lahirarki" da ire iren wannan nasihar suka isa wajen gyaran jikin. Anty zubaidan ita ta karbi envalope din ta bude taga abunda ke ciki,saita amsa ta aje tana jiran hasina tazo ta raba cikin 'yan uwa,don shahidan a yanzu bata da wata qawa banda zunnurah da take sokoto,tunda abun ya faru gaba daya ta cure qawa daga tsarin rayuwarta,saidai gaisuwa kawai ta mutunci,sabida card din bashi da wani yawa sosai,da alama dinner ce da akayi selecting iya adadin mutanen da zasu shiga. 🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍 Gaba daya ta susuce cikin kwanakin ta fita hayyacinta,idan ka ganta saika dauka ba ita bace ba,gashi daga mummy har abban nata ba wanda ya sake bi ta kanta koya tanka mata dangane da hukuncin data yanke na ba zata auri anwar ba bare ta fadi abunda yake ranta ko zataji dadi,kullum kwanan duniya kamar ibada kuwa saita kira number mima sau babu adadi amma tana a kashe amsar kenan kullu yaumin,ko fita yanzu ba kasafai take ba,kishin anwar da sauran kwanakin daya rage ya zama mallakin shahida su take lissafi,sanda taga kwanakin na qaratowa kuma bata da madafa ko makoma saita soma dana sani da nadama tana tuhumar kanta anya kuwa batayi kuskure ba?,anya bata aikata ba dai dai ba?,da wannan tunanin ne a yau daya rage saura kwanaki hudu biki ta sake jan wayarta tana gwada lambar mima karo na wajen dari biyu da wani abu. Kaman a mafarki taji ta shiga,saita miqe zumbur tana kaiwa da kowawa ita kadai tana fadin "Ki daga mima,ki daga ki daga don Allah" gab da zata katse ta daga din kuwa "Ina kika shiga don Allah?,ina kika tafi?,don Allah duk inda kike ki dawo a yau" "Lafiya?" "Ba lafiya ba mima,nace na fasa auren anwar saboda zai aureni nida shahida mima kina ina,ina buqatar taimakonki" "Shahida kuma?" Ta tambaya cikin mamaki "Eh ita dai" wani malalacin murmushi mima ta saki sannan tace "To ai kinyi dai dai da kika ce kin fasa,hukuncinki shine dai dai" "Kaman yaya mima,nifa ina qaunar anwar har yanzu ina jin soyayyarsa cikin raina,ina jin bazan iya rabuwa dashi ba" dan bata rai mima tayi sannan tace "Duk da haka dole kiyi haquri ai yanzu bake ba shiga gidan saikin shirya,sabida haka kici gaba da walwalarki har zuwa sanda zan dawo karki damu komai zai gyaru yadda kikeso" "Ina cikin damuwa mima,burina yanzu kawai shine na mallaki anwar,sai zuwa yaushe zaki dawo" "A'ah fa,aikina kinsan babu gaggawa sai biyan buqata,saboda haka idan gaggawa kike kawai ki nemi wata mafitar bani ba" "Shikenan saikin dawo" "Yauwa...am idan ba damuwa kimin transfer mana,ina da buqatar wasu yan kudi" "Babu damuwa,kaman nawa kike da buqatar?" "Dubu dari uku ma sun isheni in jalauta" "Ohk,accnt dina ya samu matsala bazaiyiwu inyi miki trasfer ba,amma zanje banki na tura miki" "Shikenan saina jiki,karki wuce la'asar" "Ba case" daga haka suka aje wayoyin,duk sai taji salama na shigarta tamkar matsalarta ma ta yanke kenan tunda sukayi magana da mina,saidai kuma har yanzu zuciyarta cike take da kishin anwar da tsanar shahida,da kuma jun babu dadi duk sanda ta tuna kwanaki qalilan ya rage su zama ma'aurata,amma idan ta tuna mima tasan cewa data dawo komai yazo qarshe,don so take kafin ita ta shiga gidan ta fara yin waje da shahida. Kai tsaye ta sauqo qasa don zuwa kitchen ta samu wani abu da zata ci,yunwar data tarawa kanta tsahon satittika sai yanzu take taso mata,a falo taga mummyn tata,saita bi nafisan da kallo ba tare data ce mata komai ba harta shige kitchen din,lokaci daya ta fada ta rame,yarinyar Allah ya zuba mata taurin kai da kafiya,duk sunsan tana son anwar amma ba yadda suka iya sabida ta nuna ba zata aureshi ba,sun fita jin zafin rabuwarsu sabida sun shaida nagartarsa,basu da sauran abunyi bare su tursasata tunda basu zasuyi mata zaman auren ba. Sai data ci ta qoshi sannan ta shiga tayi wanka,tayi 'yar kwalliya sama sama ta dauki muqullin motarta da kudaden da mummyn ce ta bata ajiya ta irga dai dai yadda mima keso ta fita bankin donta tura mata. 🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍 File na qarshe ya qarasa dubawa ya rufe yana fadin wash gami da miqar da bayansa jikin makarin kujerarsa da yake kai yana cire agogon hannunsa gamida ajeshi gefa,duban muhsin yayi "Uhmm ina jinka" ba tare daya ce komai ba ya ciro wata 'yar guntuwar takarda ya tura gaban anwar din,sannan ya aje wata a tsakiyarsu,wadda ya tura masan ya dauka yana dubawa,sai daya gama karantawa sannan ya kalli muhsin alamun yanason qarin bayani "List na kudin dinkin kayan angwancinka ne,bazan biya wannan ba kai zaka biya" qaramin murmushi ya saki,gaba daya muhsin din ya hana kanshi sakat kaman shi zaiyi auren,hatta shi kansa sabbin kayan daya dinka saboda auren suna da yawa "Ni malam dama bannce maka ina buqatar sabon kaya ba,saboda haka kayi sadaka" shima murmushin ya saki yana hararshi "Baka isa ka sani sadakar da babu niyya ba,nadai ranta maka kuma zaka biyani" dariya ya dan saki yana daukar ruwan da muhsin din ya zuba baisha ba ya soma sha a hankali daidai sanda muhsin ya sake tura masa daya takardar daya aje a tsakiyarsu,aje ruwan da yakesha yayi yana sake dubanta "Oh god,muhsin wai kana nufin da gaske dinner zakuyi?"a kaikaice ya kalleshi "au...kai da kana nufin an buga katinne kawai saboda burga ko wani abu?,dinner ne na gama tsara komai ka duba gashinan ka gani,ka saka mana sunayen qawayen amarya" aje takardar yayi yana furzar da iska daga bakinsa "Sai kaje ka tambayeta ai,nikam ban sani ba,ina zaman zamana lafiyar Allah zaka tayarmin da zaune tsaye ka tsiri hada dinner" "Aikin banza aikin wofi,qaryar banza,ina cewa duka kwanakin nan saboda auren nan gaba daya ka canza,walwarka da fara'arka,duk wanda ka gani bakinka har qeya yake" tilas muhsin din ya sanyashi sakin dariyar da bai shirya ba "Bakasan dawar garin ba muhsin,kasan auren dole?" Ya tambayeshi bayan fara'ar fuskarsa ta ragu "Qwarai kuwa" "Toshi zanma kaina" dariya sosai muhsin ya fashe da ita yana kallonsa "Gayawa qaramin yaro da baisan abinda yakeyi ba...waima don Allah,ka gayamin meye ya hadaka haka da shahida,shahidan da a baya duk duniya baka da kamarta?" "Tsarin Allah ne" ya bashi amsa ba tare daya dubeshi ba,fuskarsa na bayyana akwai radadi da ciwon dake cikin zuciyarsa,sai muhsin yayi shuru yana dan karantarsa kafin daga bisani yace "Duk abinda zakayi kabishi a hankali anwar,ba dukka zatone yake zama gaskiya ba,daukan hukunci cikin zafi yana haifar da dana sani,ka dauki komai da sassauci karka yarda ka tsaurara dayawa,don tsauri bai har da komai sai cakudewar lamura da rashin samun gyara ko ci gaba" baice komai ba ya miqe yana rufe sauran takardun gabanshi sannan ya nufi toilet dake cikin office din. 🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍 Duk wani abu dake faruwa ganinsa take tamkar mafarki ne bawai gaske ba,tuni ta sare taci gaba da zubawa sarautar Allah idanu kawai,cikin kwana biyu da suka biyo baya gidan anty zubaida ya soma samun baqi 'yan biki,komai tana yinsa ne kan tsari da shirin anty xubaida,saura kwana biyu a fara biki akaje akayi mata jeranta,sanda su hasina suka dawo suna yaba kyan gidan tsarinsa da kyansa,itadai nata ido ne da kunne,shiri sukewa bikin sosai takowanne fanni,baga gidansu ba baga gidan anty zubaida ba,ba daga katsina ba,kaman dama kowanne jiran lokacin auren nata yake,hakan baya rasa nasaba da yadda take mutum mai kirki ga kowa,sannu a hankali kuzarinta ya dinga raguwa,karsashinta ya dinga raguwa,bata sake sallamawa ba sai ana ya gobe za'a fara gudanar da bikin sanda ta dawo daga qunshi,wani irin qunshi ne da aka shimfidawa hannu da qafarta kai kace zanene saboda kyau da haduwarsa,ba lallen ba gaba dayanta ta canza,duk wanda ya kalleta saiya kuma,gyaran kuma ya hadu da kwarjinin amarci saita zama kamar wata zara cikin wata,duk da yadda take fama da rashin kuxari da walwala. Ranar da za'a yi kamu da wuri anty zubaida tasa ta koma a qarasa gyaran jiki na qarshe,itada hasina da wata coursin dinta suka je,daga can suka biya gidansu saboda daada data sauka a can tace tana son ganinta. Gidan nasu ma baqine kota ita kasancewar wannan shine karo na farko da ummantata zata aurat da diya,tun daga soro aka soma sakin mata guda,wanda hakan yasa taji kanta ya sara,tadan tsuke fuska suka wuce ciki,a rumfa suka samu dadan,duk da tsufarta ita dinma amma sai data lallaba jan lalle wanda yayi mata kyau,tana zaune cikin matan 'ya'yanta da jikokinta shahida da hasinan suka shiga,guri daya ta samu ta zauna don ba zata iya maida tsokanar da ake mata ba da kiranta amarya da ake faman yi,tana jinsu har sukayi suka gama suka qyaleta. Da daya da daya kowa ya fice ya barta a rumfar daga ita sai dadan,ta dubeta sosai gami da gyara zamanta tana kallonta "Abinda yasa nace a turomin ke tun yanzu saboda bani da tabbas din xamu samu zama kamar haka idan kuka fara wadan nan bidi'o'in naku" baki shahida ta tabe,su waye a gaba idan ba goshi ba da zata ce haka,duk basu suka tada aurenba,suka tayar da zaune tsaye,sosai daada ta zama cikim seriouse ta soma magana tana duban shahida "Kafin rasuwar mahaifinki Allah shine shaida cewa ya baki tarbiyya bakin gwargwado ya baki duk kulawar data dace,hakanan mahaifiyarki itama ta baki tata tarbiyyar bakin gwargwado,abinda nakeson cewa shine,kinar gani ko karki duba cewa anwar mun lanqwasaki ne kan dole kin aureshi,ba ruwan Allah da wannan,yi masa biyayya ya zama miki wajibi,dole kiyi idan yace dole ki bari idan yace,sauke dukkan haqqinsa ki sani ya rataya a wuyanki babu fashi,ruwanki ne kije ki masa tsiya ruwanki ne ki kyautata,koma meye kikayi abinda za'a soma fada shine tarbiyyar gidanku ce ta uwa da uba kenan,idan kinso kija musu yabo,idan kuma kinso kija musu zagi,Kiyi biyayyawa mijinki sauda qafa,yi nayi bari na bari,anwar ya riga ya zama mijinki Alqawarin Allah ne wannan daya cikashi"a fakaice ta sake tabe baki sannan ta miqe tsam tana cewa "To,na gode" ta soma yin gaba zata fice daga falon,a tsakar gida ta samu hasina tana tsakiyar mutane suka kwasar cafta,da hannu kawai tayi mata inkiya ta fice,hasinan ta tashi ta bita bayan ta yiwa su umma sallama. Qarfe hudu na yammaci harabar gidan maqotan anty zubaida ta cika ta tumbatsa da jama'a,wanda shahida dake zaune cikin dakinta anty zubaida ta kasa ta tsare mai kwalliya na mata takejin surutun jama'a da hayaniyarsu har tsakiyar kanta,babbar harabar gida ce wadda aka qawata da decoration me kyau da tsari wanda ya dace da sutturar da amarya zata saka,kota ina mutane ne dangin shahidan na uwa dana uba,manya da yara da yammata,wajen a tsare yake duk da yawan mutanen da suka halacci kamun. Anty zubaida ita ke riqe da ita har mazauninta inda aka tanada saboda ita,bata barta ba sai data duqa ta mata gargadin karta sake ta bata musu taro ta hanyar yin wani abu na daban,hakanan cikin mayafinta da aka lullubeta har saman kanta ta dinga hadiyar wani abu mai tauri a maqogaronta,ta dinga kokawar maida kukanta,duk wanda yazo a haka zai mata liqi ya wuce taqi ta daga kaima bare ta tantance su waye a wajen,a haka har lokacin soma kamu yayi,tana jin sanda dangin mahaifiyarta dana mahaifinta suka iso inda take zaune,aka buqaci dangin ango su matso "Ga turaren da za'a yiwa amarya kamu dashi inji angonta" taji wata murya wadda kamar ta santa tana fada,aka saki dariya gaba daya,wata mai azabar murya ta rangada guda wadda shahida taji kaman ana sakatar qwaqwalwarta,ta runtse idonta hawayen da take boyewa suka gaza riquwa,sai suka silalo suka zubo har saman tafin hannunta dake aje saman cinyarta,feshin farko na turaren da aka mata gabanta yayi mumunan faduwa,tabbas wannan qamshin anwar ne,turarensa ne,sake rintse idanunta tayi tanajin radadi a zuciyarta,waishin me yasa kowa ya kasa fahimtarta ne?,basa ganewa ne?,me yasa kullum kwanan duniya suke jawo abinda zai sake kusantata dashi ne?,a haka har aka qare fesheta akayi addu'a sannan akaci gaba da saka kidan qwarya,dangin ago suka buqaci yi mata liqi,haka anty zubaida tazo ta dagata zuwa amma ba tare data bude mata fuskarta ba suka shiga mata liqi,kowa sai daya tsaya ya kallesu ya qara. Qarfe sha daya da rabi na daren ranar bayan taron kamu ya watse tana tsaye gaban window din dakinta dake bude iska na shigowa sosai mai sanyi na alamun dare ya soma nisa,iskar dake shigowa cakude take da turaren da aka yi mata barinsa daxu a jikinta wanda duk da wankan da tayi kusan aikin banza ne qamshin bai rabu da jikinta ba,kusan a yanzu ba wannan ne ya dameta ba,saqon anty zubaida data gaya mata kafin shigowarta dakin shine babban abinda ya hanata sukuni a yanzu,dinner da za'ayi gobe tsakanin ango da amarya da abokansu,ta yaya zata zauna bigire daya da anwar din a matsayin amarya da ango?,yadda anty zubaida ta tsume take ja mata kunne kan goben ta tabbatar kome tayi a laifi yake,ranta a bace yake sosai,ga mari ga tsinka jaka?,itakam me anwar zaice da ita?,ya jima da rusa dukka wani farinciki nata yanzu gashi ya sake dawowa yasa hannu ya takwabe wanda yayi saura,bata da wata mafita gashi ta gaji da tsaiwar,saboda haka ta saki labulen ta dawo cikin dakin wanda su uku ne duka duka a ciki don tace ba zata kwana da kowa ba,tsallakesu tayi wanda tuni sun fara barci ta shiga bandaki ta daura alwala sannan ta dawo ta kwanta tana fatan bacci ya dauketa. 🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍 Duk yadda taso ta taushi kanta ta kuma qwararawa kanta gwiwa donta fita ga motoci hudu na anwar dake jiranta a qofar gidan hakan yaci tura,a dakin baqi na uncle hisham dake dab da qofar fita ta shiga ta zauna. Ran hasina ya baci it hankalinta ya tashi na kada ta bada su,ga zunnurah tayi gaba tuni a motar mai gidanta da yace bai yarda tahau motar kowa ba bare ta mata magana ko shahidan zataji maganarta,irin kudaden da aka kashe mata kawai a ranar donta fito ba kadan bane,ta kuwa fita din tayi kyau,irin amaryar da duk wanda ya kalleta sau daya saiya maida kanshi ya mata duba na biyu,gashi dukka wanda ya dace hasinan ta yiwa magana kan yasa shahidan ta fito sunyi gaba,kusan su suka rage kawai,bata da wata dabara dole daga qarshe ta fita ta shaidawa muhsin da suke zaman jiran fitowarsu. Kai ya jinjina kawai sannan ya juya ya nufi daya daga cikin motocin datafi kowacce kyau da girma,bude gidan baya yayi ya shiga inda anan anwar ke hakimce,cikin dan bacin rai yace "Wai zaman me muke muhsin,haka kawai ka kawoni cikin mota ka aje bayan kasan inada abunyi da yawa" "Kaga saurara....wayarka zaka dauka ka kira mana amarya ka lallabata ta taimaka ta fito" cikin rashin gane me yake nufi yace "Kaman yaya?" Girarsa muhsin ya dage "Eh to....qila sarautar tasu ce ta motsa,tana ciki taqi fitowa" dan jim yayi na wani lokaci sannan ya saki wani tsaki da qarfi "Koma meye kaika jawa mutane wallahi" ya qarasa fada yana kokawar cire babbar rigar shaddar dake jikinsa wadda taci aiki tayi bala'in yi masa kyau,ko ba'a fada maka ba kana kallonshi kaga ango "A'ah,meye na cire babbar riga kamar me shirin dambe?" Sai daya bude murfin motar ya saka qafarsa daya a waje sannan yace "Damben zanyi" ya qarasa fita yana rufe murfin motar,yanajin muhsin din na cewa nifa kiranta nace kayi a waya ka fiddota fa ba wani abu ba,ko kallonshi baiyi ba ya wuce abinsa,dukka 'yammatan dake tsatstsaye suna jiran fitowat amarya donsu wuce dakin taron sai dayaja hankalinsu,kowacce idanunta bisa kanshi,b wadda bai burge ba cikinsu,a hankali yaci gaba da takunsa harya shiga gidan ya nufi dakin baqin kai tsaye ya tura qofar. _ku ziyarci tashar SAUTIN HIKIMA dake youtube,don sauraron litattafanmu tsaffi da sababbi,dama wadanda zasu muku nan gaba wadanda babu su a duniyar watsapp,karku manta kuyi subscribe don sanin cewa mun dora sabon shirinmu_ *Alqawarin Allah* 3️⃣5️⃣ Tana kwance saman doguwar kujera ta juyawa qofar shigowa baya,hakan ya sanya sanda taji an bude qofar ta waiwayo ta saddaqar da cewa anty zubaida ce,saidai wanda ta gani din yana shigowa ya sanyata bude manyan idanunta da suka sake qawatuwa da kwallin da me makeup ta sanya musu tana dubanshi,fuskarta a yamutse alamun tambaya tacj gaba da kallonshi sanda shi kuma yake takowa cikin dakin,yayin da wani sashe na zuciyarta ya karkata wajen kallon adonshi cikin shaddar jikinsa mai azabar kyau da daukar ido,ta zauna masa das kai kace saboda shi kadai aka yita,shima ita yake kallo,duk yadda yaso kwabar kansa da hana kanshi yabata saida zuciyarsa ta zarme ta gano kyawun da tayi masa,tayi wani kyau na musamman,duk da ramar da tayi amma hakan bai hana kyawunta fitowa ba. Nesa da ita kadan ya tsaya ya harde hannayensa yanaci gaba da kallonta,yace da ita sanda ta waiwaya tana niyyar sake juya baya ta koma kwanciyarta abinta "Mudin kin tsammaci abokan wasanki ne?,ko ce miki akayi bamu da abunyi?,sauko maza ki wuce mu tafi tun ban aikata abinda nayi niyya ba" idan ta tanka to sauran kujerun dakin sun tanka,saima sake gyara kwanciyarta data yi kamar bada ita yake ba,hakan ya bashi haushi,shi zatama kunnen uwar shegu tana jinsa?,saboda haka bai sake ce mata komai ba ya taka har inda take kwancen a hankali ba tare data sani ba,ya isa bayanta ya ranqwafa gaba daya ya sanya hannunsa ya soma ciccibarta,cikin matuqar mamaki tayi yunqurin tashi gami da zillewa cikin zafin nama,ta zauna sosai fuskarta cike da bacin rai take dubanshi "Me hakane?,karka kuma kuskuren tabani malam kaji na gaya maka"girar sama data qasa a hade ya maida mata amsa idanunshi cikin nata "wannan sharadinki ne ba nawa ba,baki isa kuma ki kafamin shi ba,a banza ma wani ya taba bare ni?mema kike gudu ne?,meye abun killacewar?"ya qarashe furucin wannan karon yana tuna sanda nuradden ya kama hannunta a office yana niyyar sanya mata zobe,idanunta ta daga ta kalleshi cikin mamaki,kamar yaya wani ya tabata?,shi wai abu nawa ya gani?,abu nawa ya sani dangane da ita wanda ita bata da masaniya akan ya sani din?,ba abinda ya fado mata a rai sai sanda ta fada jikin mutumin da fiddausi ta kaita siyan kayan maye,anya bai wajen koya ganta ne yake mata gugar xana?,wani bacin rai ya sauko mata a take fiye da wanda take ciki,tsaki taja qasan ranta zuciyarta na mata suya,ta kwashe qafafunta da garin sauri ta saukesu qasa bata ma sani ba,yabi qafafun nata da suka sha lalle da kallo harta tanqwashe su tana niyyar sake kwanciya "karki kuskura...wannan karon idan na iso inda kike banga abinda xai dakatar dani daga fitar dake ba da hannuna"baki ta tabe karon farko ta jefa masa harara,ji take kaman ta tashi tayita dukansa ko xataji sassaucin haushi da zafinsa da take ji,kansa ya nuna da yatsa "Ni kike harara?" "Saime don na harareka,kai waye?" Tayi furucin tana son ta tunzurashi ko hakan zaiyi sanadin da zaiyi zuciya ya fita ya qyaleta,don itakam ko daya bata da muradin zuwa ko ina,hannun nasa dake harde a qirji ya sauke yana sake takowa inda take idonsa akanta,kafin ya qaraso tayi zumbur ta miqe tsaye gami da kaucewa gefa "Na gaya maka babu inda zani,ko ana dole ne?idan ka aureni dole baka isa kamin dolen zuwa wajen taro ba" "Haka kika ce?" "Eh" ta bashi amsa kai tsaye,wannan karon qwaqwalwarta bata gama bata shawarar abinda zatayi ba caraf taji ya sureta gaba daya ya fice da ita,sosai ta tsorata,kunyar jama'an da zasu tarar haushi da takaicinsa suka cikata "Ka cikani malam,ka saukeni,wannan wanne irin wulaqanci ne haka?,baka ganin mutane?,a haka zaka fita dani har waje?" Bai saurareta ba harsai da sukaje daf da gate din sannan ya direta,hakanan ya babbake qofar ya tsareta da ido yana son yaga iya gudun ruwanta,daidai sanda wayar hannunta ta soma ruri,tana hadiye bacin ranta ta duba sunan mai kiran,anty zubaida ce ta daga ta kara a kunnenta "Wai me kuka tsayane kuna ina har yanzu baqi sun gaji da jiranku?" Bata da wata dabara saita yanke wayar ta gyara tsaiwarta,takalman qafarta takeon gyarawa amma batason duqawa,ya tsareta da ido dole ta sunkuya a hankali da niyyar sake daure igiyoyin jiki,daidai nan shima ya duqa goshinsu ya gwaru,ta miqe tsaye da sauri dage da goshin nata tana jin zafin gwaren da sukayi,bai dago ya duqa,ya sanya hannunsa a nutse ya tattara igiyoyin ya soma daure mata su idanunsa kan farar qafarta data sha jan lalle har saman qafar,qoqarin qwace qafar ta shiga yi amma a banza sai daya gama sannan ya miqe,yaja da baya fuska a matuqar tsuke,sai data kalleshi sannan ta soma takawa ta fice daga gidan ya mara mata baya. Dukkansu xaman kurame sukayi shida ita cikin motar,kowa ya kama owners corner ya hade fuska kaman zasu masgi juna,ta cikin glasa muhsin ya qare musu kallo,dariya ta cikashi,ya girgiza kai kawai,shikam wannan abun yafi masa kama da fadan masoya,sai shine daya gaji da shurun ya soma sako musu hira don gudun xaman shuru,ba wani hadin kai ya samu daga wajensu ba na tayashi hirar ba,har gwara ma anwar akan shahidan ta takejin wani abu ya tokare mata wuya,tunda suka shiga motar sai kace bai santa ba,kai bakace shine a daxun ke shirin mata daukan amarya ba. Sanda duka isa muhsin shiya fara ficewa a motar,tana shirin budewa itama ta fita anwar ya danna lock,waiwayowa tayi ta dubeshi,batason wata magana ko gajerace bare mai tsaho saboda haka ta kalleshi kawai daidai sanda shima ya kalleta "Saurin me kikeyi?,kina gudun jerawa ne dani,saidai ni na fiki gudun na jera dake don kar a dauka nida ke Ali yaga Ali ne" "Ai baka cika wanda yake gudun jerawa da 'yar maye ba tunda zaka iya aurenta" ta maida masa amsa idanunta akanshi,saiya dauke kanshi yana cire belt din jikinsa,hakanan ya samu kansa dajin zafin kalmar 'yar maye data fada din. Sanda suke shiga wajen babu wanda basu burge ba,duk wanda ya dora idonshi akansu saiya shagala da kallonsu,perfect martch da yawa suke fada,yayin da duka jama'ar dake wajen suka miqe don nuna girmamawa a garesu,da yawa wadanda sukasan tsohuwar alaqar dake tsakaninsu kuwa irinsu anty usaina zunnurah da maqota fuskokinsu sunqi gushewa da murmushi "Lallai *ALQAWARIN ALLAH BAYA TASHI* ba wanda ya isa ya canza alqawarin Allah" zunnurah take fada a bayyane tana kallon maigidanta sanda shahida da anwar suka zauna a muhallin da aka tanadar musu,tana tuna tsahon zamanin da suka dauka basu tare,tana tuna yadda kowanne yaqi dan uwansa yake nesanta kanshi dashi,dai gashi cikin qanqanin lokaci ubangiji ya nuna buwayarsa,ya sake dawo dasu cikin rayuwar juna duk da yadda kowannensu ke tsaye kai da fata akan qudurinsa amma Allah yayi nasa hukuncin. Sanda aka fara gabatar da komai akayi kiran dangin ango anty usaina ta fito sai abun ya baiwa shahida mamaki,ruwan kudin data musu yasa ta sanya ayar tambaya a kanta,wace anty usaina?ta tambayi kanta lokacin data tsaya gefan anwar suna magana qasa qasa yadda shahidan bataji,gabanta ya fadi cikin ranta tana addu'ar Allah yasa ba abinda take zato bane. Saidai kuma addu'ar tata batayi tsaho na aka ware fili na musamman saboda babbar yayar ango aka bata dama,cikin qananun hawaye da suka kasa riquwa a idanunta ta miqe ta isa inda anwar da shahida ke zaune,tasa hannunta ta tashesu tsaye gami da dan matso dasu gaban step din da suke kai kadan yadda kowa zai iya ganinsu,ta karbi abun magana tayi taku biyu gaba kadan dasu sannan ta tsaya "Yanzu da zan tambaya cewa suwa kuke gani a tsaye a nan wasunku zasuce amarya da ango,wasu zasuce masoya,eh....masoya ne saidai ba ordinary masoya da kowa ya sani ba,masoya ne da kalar soyayyarsu ta bambanta data kowa,masoyan da Allah zai cika alqawarinsa a kansu koda ba wanda yaso hakan,nasan zaku yarda dani idan kukaga wannan" saita juya ta kalli masu gabatarwa,cikin sakannin da basu wuce goma ba majigin dake kafe a bango daban dake hall din ya soma haske wanda hakan yaja hankalin kowa,ciki harda anwar da shahida,cikin qanqanin lokaci hotuna suka soma bayyana kansu daya bayan daya,hotunan anwar da shahida shekara biyar zuwa shida baya,mamaki ya kama anwar ni na a ina anty usaina ta samo wadan nan hotunan?,hotuna ne da sukan dauka lokaci zuwa lokaci shida shahidan idan yaje zance sanda ya siyi waya torching ya siya mata itama,tana ainihin shahidarta yana ainihin anwar dinsa,nan fa murmushi ya cika fuskokin al'umma kowa nabin hotunan daya bayan daya da kallo,abokan tsokana suka samu nayi,yayye da iyaye suka dinga dariyar hotunan,wasu da hijabai a jikinta,wasu ta sunne kai,shi kuwa yana dan tsirit dinsa babu wata cika ko kumari tattare dashi,a hankali hotunan suka dinga shiga zukatansu suna tuna musu wani lokaci can baya,lokutan da sukafi kowanne dadi cikin rayuwarsu,hoto na qarshe ya soki zuciyarsa shida ita,dukkansu basu manta ba,wannan shine hoto kusan na qarshe da suka dauka tsakaninsu dab da mai afkuwa zata afku,idanunta ta runtse hawaye nason saukowa tana hanashi,turota da anwar yayi daga gidansa shine abinda yazo mata a rai,daidai sanda shima ya dauke kanshi daga kallon hotunan,suna qarewa gurin ya rude da hayaniya da kuma tafu gami da sowa,saida mc ya daidaita komai sannan anty usaina taci gaba da magana "Zuwa yanzu nasan kowa ya gasgata maganata ko?" "Eh..." Duka hall din ya amsa,kaita jinjina sannan ta sake komawa gabansu tana dubansu har yanzu abun magana na hannunta "Inason ku sake tabbatarmana da cewa zaku kula dakanku,zaku kula da amanar juna,ga shaidu nan suna kallo" ta qarashe maganar tana fidda murmushi gami da fatan hakan ya kawo sauyi tsakaninsu komi qanqantarsa,anwar ta fara miqawa abun maganar tana tsareshi da ido,dole ya amsa yakai bakinsa,sassanyar muryarshi mai cike da mazantaka ta cika hall din wanda hakan ya taso da tsohon mikin dake danqare zuciyar nafisa dake maqale ita da mima a wani sashe na hall din,ji tayi kaman zuciyarta zatayi bindiga,sonshi da qaunarshi ya sake narkewa cikin zuciyarta,taji inama tun farko batayi sakin bakin cewa ta fasa aurenshi ba? "In sha Allah zan kula da ita,zan sauke duk wani haqqi nata dake wuyana..." "Kayi mana qwange....zaka bata soyayya da kulawa?" Anty usaina ta tari numfashinsa ta fada cikin sauri ta sigar tambata,kasancewar ba abun magana a hannunta yasa wadanda ke zaune gaba gaba abokanshi su kadai sukaji me tace sai kuwa su,idanu ya fiddo yana kallon antyn ya tabbatar qure takeson yi masa,cikin qasa qasa da murya yadda su kadai zasuji yace "Idan naga ta cancanta ba" yana miqawa antyn abun maganar,duka takai masa wanda ta manta ma a inda suka saboda jin haushi ya goce yana dariya,abun ya baiwa mutanen dake wajen sha'awa suka saka dariya gami da sanya musu tafi,harara ta jefa masa sannan ta juya ta miqawa shahida abun maganar "Uhmm...uwar gidan anwar,ina naki alqawarin" murmushi ta qaqalo sannan ta jefawa anwar harara wanda har cikin zuciyarta ita tayi hakan,yayin da sauran mutane suka tsammaci soyayya ce "Alqawarin daya dauka baiyimin ba anty,ba abinda ya iya,baisan haqqin soyayya ba baisan mutuncin masoyi ba,baisan komai ba a soyayya bai iyata ba" tsit kowa yayi yana saurarenta cikin mamaki,gaban anty usaina ya shiga faduwa,hasina da zunnurah dake zaune cikin mutane ji sukayi kaman su rugo da gudu su qwace abun maganar daga hannunta,yayin da nafisa ta tsaya cak farinciki na ratsata,me zai farune?,ba hadin kai tsakaninsu kenan ko jituwa "Haka kikeso anty na fada irin kalaman da wata amarya da aka yiwa auren dole ta fada?,idan ban yabi masoyi kamarshi ba me zance?,bashi da buqatar yabo ko daukan alwashi a kansa,shi yasan komai,duk alqawarin da zan dauka anan na fallasa sirrin soyayyarmu ne,alqawarin daya dauka duka namu ne mu biyu basai nayi maimaici ba,ni dashi duka abu daya ne" ta qarashe fada tana murmushi saman fuskarta can qasan ranta kuma tana jin ciwon lafazinta,sowa da ihu wajen ya kaure dashi,ba wanda ya fuskanci me take nufi daga anty usaina saishi uban gayyar,sai zunnurah da hasina,kowa ya zaci cewa abinda ta fada din zallar soyayya ce da qauna,miqawa antyn abun maganar tayi,tana juyowa suka hada idanu dashi saita dauke idonta gefe guda. Sosai dinner din ta qayatar ta sanya farinciki cikin zukatan al'umma da dama,takuma burgesu,komai ya gudana yadda anty zubaida tayi fata shahidan bata bada matsala ba,tayi qoqarin kula da duk wani motsi nata da action nata. *Alqawarin Allah* 3️⃣6️⃣ 🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍 Daurin auren da za'ayi sha daya na safe amma tun takwas na safe gidan ya soma cika da 'yan uwa,a sannan tana kwance daga saman gadonta tana kallon yammatan nata hada hadarsu abinsu suna breakfast,ko sha'awar abincinma batayi bare takai gaci,babu yadda hasina batayi da ita ba amma ko kallonta batayi ba bare ta tashi,sai juyi take daga nan zuwa can,ji take kaman zazzabi zai kamata,har goma saura tana kwance tana kallon masu wanka nayi masu kwalliya nayi. A sannan ne anty zubaida ta shigo tana dubanta "Wankanne yau baki da niyyaryi ko kuwa?" Bata amsa mata ba illa miqewa da tayi ta zauna sosai saman gadon tanajin jikinta a matuqar mace,haka zuciyarta a cunkushe,kanta a qasa anty zubaida ta aje ledar hannunta "Ki tashi kiyi wanka ki shirya,mai kwalliya zata shigo tayi miki" "Anty.." Ta kira sunan anty zubaidan zuciya a karye,juyowa tayi tana kallonta "Don Allah ki qyale mai kwalliyar nan yau,don Allah" dan shuru tayi sannan tace "Shikenan zata koma,hasina ta shafa miki ko powder ne" daga haka ta fice daga dakin. Dariya hasina tayi sosai tana qarasowa inda shahida ke zaune tana tare qwallar idonta,idan da hali yau batason ko sau daya tayi kuka "Hajiya shahida,nikam na rasa me kike nufi,don Allah yammata ba kukan dadi wannan matar take ba?" Ta tambayi sauran yammatan dake dakin tana watsa hannaye,dariya aka sanya sannan ta dora "Allah ya baki miji irin wannan da yaji komai da komai amma ki tsaya kina wani nuna qiyayyar banza,ke idanunsa kawai aka kallah Allah ansan dan soyayya ne na qarshe,baku lura da yanayin kallonsa bane?" Ta sake jefawa 'yammatan dakin tambaya "Ashe bani kadai na gani ba,nida daada ta fadamin tun farko aini zan sako kai akwai amanta da batunki" daya daga cikin cousin sis din shahida ta fada,muryarta kamar ta mutumin daya tashi yanzu a bacci tace "Yanzu ma lokaci bai qureba,da zasu taimakeni da sun maida daurin auren kanki,don Allah ki shaida musu" daya daga cikinsu ta saki dariyahatda qyaqyacewa "Kuna ganin idonta kunsan qarya take,wannan aka qwace miki shi idan baki kuka ba yanzu gaba sai hawan jini ya kamaki" dukka suka sheqe da dariya,abun ya bata haushi ganin wai basu yarda da ita ba "Nikeson anwar?,amma kun yaudari kanku" daga haka ta zira takalmanta ta shige bandakin ganin suna sake turata. Kafin sha daya na rana layin ya dinke tsaf da jama'a,hayaniya ta kowanne sashi,yayin da fargaba da faduwar gaban shahida suka dadu duk sanda wani minti ko sakan ya shude,idanuwanta kan agogo,duk surutan da ake cikin dakin bata jinsu bare ta fahimci me suke fada. Sha daya da minti goma sha biyar qanwar ummanta ita da wasu yan uwan babanta su uku suma shigo dakin suna sakin guda wadda ta firgita shahida gamida saka zuciyarta gudu da matsanancin sauri,inda take zaune suka qaraso hannun daya daga cikinsu na dauke da turare ta dunfarota tana cewa " *Alqawarin Allah* ya tabbata,yau Allah yayi,shahida ta zama matar anwar"wadda ke tsaye a bakin qofa qanwar abbanta tace "Allah ya jiqan habibu,Allah baiyi zaiga aurenki ba shahida,duk qaunar da yake miki Allah bai nufa ba,Allah ya jiqanka habibu yakai haske kabarinka" kalaman da suka sake tunzura zuciyar shahida kenan sanda suke fesheta da turaren,ta saki kuka sosai mai sauti wanda ya tunawa da abbanta yasa taji auren ya sake fice mata daga kai,karo na biyu tun bayan lokacin da al'amarin ya faru da taji ba zata iya yafewa fiddausi ba wadda ita ta zama sila kuma jagorar afkuwar komai a rayuwarta,me ta yiwa fiddausi haka dataso tarwatsa mata rayuwa?. Daada ce ta shigo dakin jin hayaniya da gudar dake tashi a cikin dakin,yawan kukan da taga shahidan nayi yasa daadan ta fitar da kowa daga dakin taja mata qofar,tayi hakanne donta bata damar yin kuka sosai ko zataji sanyi a ranta. Daidai lokacin da nafisa ke kaikawo kaman wadda ta hadiyi kunawa tana zufa,bata tabajin cewa tayi kuskure ba sai yanzu da labarin tabbatuwar auren shahida da anwar ya ratsa kunnenta "Anya banyi ganganci ba kuwa mima?" "Gaganci kuma na nawa?" Ta fadi a zuciyarta,amma a fili saits iso inda take ta dafa kafadarta "Babu wani ganganci da kikayi,badai gani na iso ba?zaki shiga gidan anwar a sanda ya dace dake,ki sawq ranki kamar kin sameshi kin gama" sanyi ya ratsa ranta ta saki ajiyar zuciya "Please mima,duk wani shiri da zakiyi karkiyi na dogon lokaci,kiyishi a gajeran zango,don zuciysta ba zata iya jurar tunawa da zan dinga cewa anwar nacan ya kebe da wata macen ba bayan ni" "Baki da damuwa fa hajiyata,kisa ido kisha kallo" mima tayi lafazin tana daukan jaka da dan yalolon mayafinta ta fice daga falon. *5:00 pm* Qarfe biyar na yammaci cikin dakin nata da aka gama kwashe komai nata take zaune saman kujerar madubi,da kanta a yanzu take shiryawa don tasan me afkuwar ta riga data afku,komai ya qare mata,babu sauran wani abu da zai tasiri koya hanata shiga gidan anwar,ta gama yankewa kanta gwara ta sassautawa zuciyarta,ta yadda da hakan ta kuma sallama,taci alwashin samawa kanta walwala da nutsuwa,saidai hawayen da har yanzu ta kasa cin galaba akanshi gaba daya duk da ya ragu,amma lokaci lokaci yakan sako kai tasa hannu ta daukeshi. Tsaf ta gama shirin nata hasina da anty xubaida na gyara mata wasu abubuwan har komai ya kammala,lallai amarya amarya ce,gaba daya kaman sauya shahidan akayi da wata sabuwar halittar,tayi wani kyau na musamman gami da kwarjini,anty usaina ta zauna daga bakin gado tana dubanta "Za'a soma kaiki wajen umma,daganan kuma akaiki gidan yayarshi,za'a barki a nan shi zaizo ya daukeki ku wuce,munyi magana da ita ta gayan dalilanta nayin hakan kuma na gamsu,shahida,zamana dake zamane mai dadi wansa nake alfahari dashi,kuma dukkan abinda ya kamata na gaya kiki koki sani kin riga dakin sani na kuma sake miki tishinsa,abu na qarshe kawai da zan rufe dashi shine ince miki,shi aure bautar ubangiji ne,hakan ya sanya dadinsa bai rufewa mace ido ta manta da mahaliccinta,haka dacinsa ma bai sanya mace ta manta da cewa bautar Allah take,Allah yasa kin shiga a sa'a,ya sauya zukatanku da manufofinku cikin qanqanin lokaci,ina maraba da tambaya daga gareki duk sanda wani abu ya shige miki duhu,amma ki sani,dole ki zama jaruma,dole ki koyi hadiye wasu abubuwan ba tare da kowa ya sani kokin gayawa kowa ba,ciki badon tuwo kawai aka yishi ba,Allah ya sadamu da dukkan alkhairinsa" daga haka anty zubaida ta miqe don batason tayi qwalla ko daya don karta sake karyawa shahida gwiwa tunda ta fuskanci kamar ta aro dakiya da juriya,daidai sannan huda ta shigo da sauri,ta isa gaban shahida ta rungumeta,zata fara kuka anty zubaida ta zare mata ido gamida korata don karta karyawa shahidan gwiwa,a haka aka fita da ita zuwa gidansu. Can dinma gidan cike yake da jama'a 'yan yinin biki,uwar dakan ummanta aka ajeta,'yan uwa suka dinga shigowa aka dinga gaisawa ana yi mata Allah ya sanya alkhairi,tayi qoqarin tarbar kowa cikin mutuntawa,tunda kusan dangin ummanta ne duka,ba wani bare ko baquwar fuska. Sai gab da magariba sannan umma ta zauna da ita ita da sauran yayyenta,fadane dai irin wanda uwaye kewa diyarsu,daga bisani kuma umma ta taba nata,ta nemi yafiyarta cikin kuka tana tunawa da abbanta "Bakiyimin komai ba shahida,saidaima ni nace ki yafe mana nida mahaifinku" kukan da bataso ba a yanzu shi take haiqan,kaman ba zata fita daga gidan ba haka ta tako suna riqe da ita aka fito da ita,saitaji wani qauna da kewar mahaifiyarta na ratsata,taji kaman karta tafi,taji kaman taci gaba da zama dasu,a yanzu bata buqatar anwar sam,bata da buqatarsa cikin rayuwarta. Tun daga harabar gidan anty usainan zaka gane wata walima ake ta daban saboda yadda harabar ta qawatu,uwa uba ankon da yake jikin duk wanda ke farfajiyar dama cikin gidan cikin wata atamfa mai azabar kyau da tsari. Sabon shagali na walimar da dangin ango suka hada aka bude,nan aka zaunar da shahida suka dinga mata barin liqi tako ina,ba'a tashi ba saida akayi sallar magariba,anty usaina bata bari an shiga da ita cikin gidan ba,can wani babban falo dake da daki da bandaki aka kaita,babu kowa wurin da niyyar ko zatayi sallah,aka aje mata abinci aka barta ita daya donta sake,tuni 'yan uwanta suka koma gida ba wanda ya zauna,fashin sallah take hakanan abinci bata sha'awarsa,kuma batajin zai iya wucewa ta maqoshinta,saboda haka ta zauna kawai idanunta kan tv din dake aiki ita daya,volume dinta can qasa don ba'ajin ma me ake cewa,sam ba tv dince a gabanta ba,sabuwar rayuwar da zata fuskanta itace a gabanta,abu na gaba tsakanin kunyar anty usaina,ta yaya zata kalleta?,idan ta tuna kalaman data gaya mata na batason dan uwanta sai taji duk nauyi ya sauko mata,batasan itace wannan yayar tashi qwaya daya da bashi da kamarta ba,da duk yadda take qin abun ba zata yarda bakinta ya fada ba,addu'a take cikin ranta Allah yasa kada ta shigo. Bakwai da rabi zuwa takwas na dare taji hayaniyar gidan ta ragu sosai,da alama masu tafiya sun tafi kenan,masu shigewa cikin gida sun shige,turo qofar da akayi shi yaja hankalinta,ta dan dage mayafinta kadan tana kallon mai shigowar,sa'ida ce saidai ita batasanta ba,fuskarwa a washe ta qaraso falon tana takowa a hankali tana waigawa,da alama ba'asan tayo.nan ba,dab da shahida ta zauna tana kallonta "Anty,saike kadai?,nayi nayi da ummi tabarni nazo tace a'ah zamu takura miki kina hutawa ne,da qyar na samu na sallabo" murmushi shahida tadan saki tana duban sa'ida "Ina yini anty,ya gajiyar biki" "Lafiya lau,me sunanki" "Sa'ida,'yar anty usaina ce ni,kuma qawar uncle anwar" girarta shahida ta dage duka biyun tana dubanta alamun tambaya,dorawa tayi "Wallahi kun dace sosai anty keda uncle,uncle ya samu mata me kyau" tana murmushi sosai ta fada tana kuma sake kallon fuskar shahidan data ji tana burgeta,murmushi shahidan ta kuma saki "Ko?" Tace cikin sigar tambaya,kaita kada "Qwarai kuwa,amma anty,don Allah ki kularmin da uncle dina,wallahi inason uncle anwar,yana da kirki sosai,yana sonmu shima,yana kula damu sosai da sosai,don Allah anty" saita tsaya tana sake dubanta kafin ta kuma sakin murmushi,ta dora hannunta saman hannun sa'ida "Uncle din naki nima zai iya kula dani ne sa'ida?" Dariya ta saki "Tabdi,sosai kuwa anty,kinsan uncle anwar kuwa?,ai matarshi ta caba" saitayi qasa da murya "Na zaci fa zai iya aurena harna cewa ummi ina sonshi,ranar saida na daku sosai,ashe babana ne" dariya ta kubcewa shahida da sa'idan duka,da sauran dariya a fuskar shahidan tace "Babanki ne sa'ida,amma kita addu'a Allah ya baki wanda ya fishi nagartar halaye" "Akwai wanda yafi uncle dina kuwa?" Ta fada cikin tantama da tunani,kaita jinjina "Qwarai kuwa,duk wanda kika gani kome kika gani a duniya akwai wanda ya fishi akwai wanda baikaishi ba akwai dai dai dashi" "Tohm shikenan......" Bata qarasa maganar ba suka jiyo taku ana nufowa wajen,saita fiddo idanu "Na shiga uku anty,Allah yasa ba ummi bace" riqe hannunta tayi "Karki damu,zance nina kiraki ki tayani hira" shuru sukayi suna jiran ganin wanda zai shigo din. Sallamar mutum biyu ce,ummin sai muryar anwar daga bayanta,mummunar faduwar gaban data sanya shahida maida kanta cikin mayafi ta saukar mata,ummi anty usaina ce a gaba sai anwar din daga bayanta,idanunta akan sa'ida nashi idanun nakan shahida da kanta ke sunkuye lullube da mayafi,kama baki tayi "Na shigesu ni usaina,sa'ida...sa'ida ki shiga hankalinki da wannan rawar qafar taki,dama da akacemin ba'a ganki ba nan kikayo?,to tashi ki wuce ki bama mutane guri" da sauri ta zame hannunta cikin na shahidan sannan ta miqe,duk da haka da zata gifta anwar din saida tace "Uncle,kayi kyau sosai yau,amma wallahi in gaya maka gaskiya?,anty shahida ta fika kyau ashe" anty usaina batasan sanda dariya kubce mata ba,yayin da murmushi ya subuce masa shima ya bita da kallo harta fice daga dakin,ba ruwanta hakanan take,idan taga gaskiya saita fada,kusan halayenta suna kamanceceniya dana mahaifiyarsu,duk cikin yaran anty usaina tasu tafi zuwa daya,kusan sanda aka haifi sa'ida tare sukayi rainonta shida anty usainan tun lokacin mahaifansu suna raye,idanunsa ya sake saukewa akan shahidan a hankali duk da bai ganin fuskarta,yana tsaye a wajen har anty usaina ta zauna "Zauna daga can" ta fada tana masa nuni da inda takeso ya zauna din,kujerar da shahida ke kaine,duk da cewa mai yalwa ce amma saiya zauna a hannun kujera,cikin hikima da nutsuwa ta soma magana dasu "Alhamdulillahi rabbil Aalim,komai na rayuwa a tsare yake zuwa daga wajen ubangiji mai kowa da komai,basai na tsaya wani tambaye tambaye ba don nasan ba amsa zan samu daga gareku ba,abunda nakeson na fada shine,wannan auren naku ya isheku dama sauran mutane ishara,kun rabu da juna kun guji juna ba tare da dayanku ya sake tunani Allah zaiyi ikonsa ku sake haduwa a wannan bigire ba na aure,wannan kadai ya isa ya nunawa bawa yana tashi ne Allah yana tasa,ta Allah kuma itace dai dai,saboda haka ku sanyawa zukatanku salama,ku zauna da juna cikin aminci da bin umarnin mahalicci,kada ku yiwa Allah butulci wanda ya baku aron rai da lafiya ya kawoku wannan lokacin koda cikin zukatanku bason hakan kuke ba,dubunku na nan na fatan samun kamar takun,ya sake hadaku a sanda kowannenku rayuwarsa ta sauya ta samu ci gaba,ta yuwu hikimar rabuwar daku dama don kowanne ya cimma gacinsa ne,wanda wala'alla idan kuna tare da zaku cimma wannan abun ba,ku kauda hayaniya da tashin hankali ku ajeshi idanma kun daura azamar hakan,kuyita addu'ar Allah ya baku mafita ya sanyaya zukatanku" saita waiwaya ta dubi anwar "Kai kaine babba sannan kaine shugaba,kai keda hankali fiye da mace,sabida haka fiye da rabin nauyi da yanayin yadda zamanku zai kasance ya ta'allaqa a wuyanka ne,kasan komai basak na fada maka ba,iyayenmu kafin su rasu makarantace a gareka,ka dauki matarka ku tafi daga kai sai ita,ina muku fatan alkhairi,shahida...Allah ya bamu alkhairinsa kinji" kasa magana tayi kunya na kamata,ta fuskanci hakan sabida haka tayi murmushi taga bari kawai ta murje mata kunyar a wuce wajen "Ki daina kunyata,don kincemin bakison anwar wallahi banga laifinki ko daya ba,hasalima burgeni kikayi,donko nice kw abinda zanyi kenan,kawai saika rabu dani tsahon wasu shekaru ka zagaya ta bayan fage ka aureni haka akeyi?" Ta qarashe maganar tana duban anwar gamida harararsa "Kuma ka nemi yafiyarta kukan daka sa ta dinga yi da aurenka data yi bayan bata shirya ba bata amince ba" murmushi ya qwace masa mai dan sauti,itama antyn tana murmushin ta fice ta barsu. Shuru ya ratsa dakin na wasu mintina masu dan dama,idonsa akanta da yake lullube,zuciyarsa na masa bitar wasu shekaru can baya,yasha kwana idanunsa biyu yana wassafa yaya zai kasance duk randa shahida ta zama mallakinsa,yasha raba dare yana tsara ranar da irin abubuwan da zasu faru a lokacin,ga komai yazo ga lokacin yazo saidai cikin bahagon yanayi da dabaibayi,ajiyar zuciya ya saki a bayyane sannan ya furta cikin sanyin murya "Tashi mu tafi" yi tayi kaman batajishi ba,yayi tsai yana dubanta,ya tabbatar taji,har tsahon minti guda sannan yace "Kin sani sarai tun da can banason musu da taurin kai ko?,indai zaki dauki wannan dabi'ar zakisha wuya a wajena" daga haka ya miqe yayi gaba,tasan idan ta bari yafice batasan hanya ba,dole ta miqe itama ta bishi". Bangaren ajiye motocin gidan suka isa,yasa muqulli ya bude motar ya shiga,saita soma qoqarin bude gidan baya da zummar zata shiga,lock ya sakawa qofar ba tare daya waiwayo ya dubeta ba,hakanan ta gaji da tsaiwa ya yunqurin budewar ta matso gidan gaba ta bude,a hankali ta shiga ta zauna sosai sannan ta kame jikinta waje daya bayan ta sake jan mayafinta ta rufe fuskarta,karon farko bayan wasu shekaru masu tsayi ta sake hada mazauni dashi cikin mota,gaba dayansu jinsu suke banbarakwai,kowa yanaji kamar yana tare da baqonsa ne,ya dage dukka gilasan ya kunna ac dukda sanyin dake dan kadawa a garin,ya tashi motar suka fice daga gidan. Wani tuqi yake kaman bazasu gida ba ko kuma yana lallaba kwalta,duk da titin da sukabin fetal yake babu yawaitar jama'a sai haske fitilun titi tako ina,shuru ya ratsa motar babu me cewa komai har suka isa wani waje da sukeda saida kayan ciye ciye,kama daga ice cream,burger shawarma kaza da tsire da sauransu,saida yadanyi gaba kadan inda babu mutane sannan yayi parking,ya kashe motar ya fita. Bai jima ba ya dawo hannunsa dauke da leda ya sakata a sit din baya,sannan ya tashi motar sukayi gaba,hannunsa ya saka ya kunna rediyo freedom wanda minti biyar ya rage su fara shirin siyasa na kowanne gauta,waqar jarumar matace ta soma plying,waqar tana taba zuciyarsa sosai,yana son ya kashe amma saiya samu kanshi da barinta tana ci gaba da tashi,sautin na karade motar yana shiga kunnuwansu cikin sauti madaidaici gami da haifarwa da kowa yanayi na daban. Ta gefan ido ya saci kallonta,tayi laqwas cikin sit din motar,idanunta a lumshe,zara zaran gashin idanunta sun fito sosai,juyawa yayi duka yana kallonta sosai,daidai sanda ta bude nata idanun,saiyayi hanzarin dauke kanshin ya maida ga titi yaci gaba da tuqa motar cikin nutsuwa da qwarewa. _zaku iya jina shuru gobe saboda wani uzuri daya tasomin,amma idan na samu dama zaku jini in sha Allah_ 😊 _kuci gaba dai dayi mana uzuri,kana taka ne Allah na tashi,ta Allah itace dai dai,har kullum burinmu mu sauke nauyinku dake kanmu,muna godiya_ 🙏🏽*Alqawarin Allah* 3️⃣7️⃣ _ziyarci tasharmu ta youtube SAUTIN HIKIMA,don sauraren littafanmu sabbi dama tsofaffi_ https://youtu.be/H7M7h6l6wNM A maidaidacin qawataccen wajen ajiyar motocin gidan ya ajeta kusa da 'yan uwanta biyu qasan wata rumfa,ya kashe motar can qasan ranshi yana furta "Alhamdulillah Ala kulli haal" sai a sannan shahida ta bude idanunta tana duban gabanta "Ki fito" ya furta yaba bude side dinshi ya fita,cikin kasala da fargaba ta bude ta fito ta soma bin bayanshi sanda yake takawa ta wata qawatacciyar doguwar hanya mara fadi sosai wadda kai tsaye ta sadasu da falon gidan. Ci gaba yayi da tafiya bayan shigarsu falon,saita tsaya cak cikin baqunta tana qarewa falon kallon,ba wani mugun qato bane,amma wadatacce ne sosai,wanda jeran ciki ya bala'in birgeta tare da fito da kyawunsa,komai na ciki yayi kyau ya dace dashi hakanan ya dace da gidan. Mintuna biyu ya dawo idanunsa a kanta ya mata nuni da wata hanya wadda zata sadaka da farfajiyar da dakunan baccin gidan suke "Dukka qasan nan mallakinki ne,ga hanyar dakinki nan,duk abinda baki fahimta ba kina iya tambaya,zaki iya tafiya ki kwanta" a hankali ta soma takawa zuwa direction din daya nuna mata ba tare data bashi amsa kotace wani abu ba. A nutsewa takebin yalwataccen dakin da kallo mai dauke da seat din gado dressing mirrow da wardrobe,sai wasu kujeru qwaya biyu masu dogon makari,daga dan qaramin carfet xuwa labule zuwa teburin mahadin kayan gadon duka dark purple ne da light ash,shima dakin ya qayatar da ita matuqa,komai ya tsaru yadda ya kamata,qamshi kawai yake fitarwa da sanyin raba,ta taka a hankali ta zauna kan daya daga cikin kujerun dake jere gefe daya zuciyarta nason soma rawa tana hana kanta,qofar dakin aka turo ta daga kai ta dubeshi sanda yake shigowa da leda a hannunsa,baice komai ba harya shigo ya aje ledar kan dan teburin wanda yake daura da ita ya fice daga dakin hadi da jaa mata qofar. Ta jima zaune a wajen tana saqa da warwara,ta dade tana tunanin wanne irin dama zasuyi?,ta dade tana wassafa yadda zata mu'amalanci anwar din ta ina zata soma kallonsa a matsayin miji?,yaya zamantakewarsu zata kasance?,sai da jikinta ya soma gaya mata irin gajiyar da yayi ya soma gazawa sannan ta bude toilet din dake cikin dakin,shi kansa abun kallo ne,ta dinga amfani da komai na ciki yadda ya dace ta sauya pad din jikinta ba tare data nemi ta sauya kayan jikinta ta dawo ta nemi waje ta kwanta tana sauke ajiyar zuciya. Duk da gajiyar da yakeji saidaya kammala komai nashi daya saba kafin yin bacci,ya nade saman nashi gadon yana sauke nannauyan ajiyar zuciya idanunshi a lumshe kafin daga bisani ya budeshi,hakanan yakeson gidan,duk da bai kama qafar girman wanda yake ciki ba da haduwarshi gami da cin kudi ma baki daya,fili ne daya siyeshi a zamanin da yake hada kudi da qyar,a zamanin daya tara kudin tun daga qananu zuwa manya,gininsa ne kawai yayishi sanda yake cikin wadata,yanayin yadda aka tsara gidan yakan burgeshi shi kansa,ba yadda anty usaina batayi ya zauna a wancan ba tunda yafi girma amma yace a'a yafison wannan,yabi dakin da kallo a hankali idanunsa ya sauka kan ledojin daya shigo dasu,ci gaba yayi da kallonsu yana tuna wani lokaci can baya,lokacin da yake anwar din take shahidanshi,a lokacin yakan tsokaneta da cewa awara zai siyo mata duk randa aka kawota gidansa ranar farko tunda mayyar awara ce,dariya take ta sunne kanta a hijabi sannan tace "Ko haka ka shigomin ya anwar bazan damu ba,saboda kaidin da aka bani yafi komai da zaka shigomin dashi" ajiyar zucuiya ya sauke idonshi ya sauka kan safe dinshi daya daukoshi daga gidansa ya dawo nan dashi,zuciyarsa na gargadarsa amma sai daya sakko,ya saka lambobin sirrin ya budeshi,a hankali ya ciro envalope din da har yau yadda aka kawota haka take,ko takardar bayan ba'a canza ba bare saqon ciki,har rubutun jiki yana nan baro baro kaman yadda aka rubuta din. Zaman dirshan yayi qasan tiles din dakin,zuciyarsa na masa zafi tun bai fito da hotunan ciki ba,ya daga ya zazzagesu duka suka zubo,dai dai sanda wani abu ya tokare masa maqoshi,idanunsa suka soma sauya launi zuciyarsa na suya,haka ya dinga daga hotunan daya bayan daya yana kalla abinda ya jima baiyi ba donko sashen da suke ajiye bai fiya son kalla ba,kowanne hoto yayi a qalla minti biyar yana qare masa kallo kamar maison sanin dai dai lokacin da aka daukeshi,haka ya gama kalla baiga wani abu da zainuna akwai kuskure koba dai dai ba game da hoton,kowanne ya fito tas ya fita kar hakanan komai na jikin shahidan ya bayyana baro baro,gudun zuciyarsa yaji ya sake daduwa kansa ya soma daukan dumi,haka ya janyo envalope din ya soma maidasu ciki jin alamun hawan jininsa na neman tashi,yasan shiya jawa kansa daya kalla hotunan,amma hakanan kawai yaji kaman an tsunkulinsa kan ya jawosu ya duba,saiya miqe a daddafe ya shiga bandakinsa ya saje daura alwala ya fito ya tada sallah. Kamar yadda ya saba kafin ya idar sanyi da nutsuwa sun saukar masa,ya daga hannu yayi addu'a sosai sannan ya shafa,saman abun sallar yaci gaba da zama,kwanan da baiyi ba kenan kan gadonshi a darensa na farko cikin gidan aurenshi,sai akan abun sallar ya kwana,wanda bai sake farkawa ba saida ya rage mintuna kadan a tada sallar asuba sannan ya sake wata alwalar bayan yayi wanka,ya bare wata jallabiyyar ya saka bayan ya feshe jikinsa da turare masu sanyi da taushin qamshi. Har zai fice saiya tuna da ita,ya tabbatar haqqinsa ne ya kula da addininta,koma meye a yanzun tana wuyanshi,saboda haka ya sauya akalar tafiyar tashi zuwa sashen dakunanta. A sannan itama ta farka tana gefan gado tana shirin shiga bandaki ta sauya audigar jikinta taji knocking,tasan ba kowa bane saishi,tana ji amma tayi banza kaman bata ji ba,saida yayi a qalla wajen sau goma sannan tadan ja gyaran murya kadan,hakan yasa ya gane ta tashi sai kawai ya juya ya fice zuwa masallaci. Sanda ya dawo kashe wayoyinsa yayi baki daya ya haye saman gadon sosai bayan ya cire jallabiyar jikinsa daga shi sai gajeran wando,ya kwanta dai dai saman gadon yana sauke gajiyar da jiya bai samu saukewa ba. Duk da gajiyar datayi qarfe tara saura taji baccin ya fita a kanta,saboda haka ta miqe ta fada bandaki ta tara ruwa mai dumi sosai tayi wanka ta dawo cikin dakin ta shirya cikin atamfa riga da zani simple mara ado,bayan mai sai powder da kwalli kawai data zizara a fuskarta,tayi daurinta sosai ta feshe jikinta da turare,dakin tadan kakkabe tayi goge goge ta sake shareshi ta dame gadonta sosai,sai a sannan ta bude qofar dakin nata tabi 'yar hanyar data sadata ta falon. Daga tsaye take sake kallon falon,sai yanzu ta sake ganin kyau da tsaruwarshi,komai yayi mata perfect daidai da ra'ayinta,ta daga kanta ta kalli saman wanda da alama anan dakunan baccinsa suke,saita tabe baki ta juya zuwa qofar da kitchen take,can dinma komai yayi mata a tsare,gidan gaba daya babu fariyar kashe dukiya hakanan babu qaranta,karon farko tun bayan da suka sake haduwa da yayi wani abu data ji abun ya burgeta,duster ta dauko ta dawo falon shima ta saitashi yadda takeso,daga nan kitchen ta shiga,store dinsu babu komai a ciki,amma taga kayan tea da qwai,saboda haka ta tafasa shayi mai kayan qamshi ta zuba a flask,sannan ta fasa qwai ta soya,sai a sannan ta tuna da ledar jiya,ta kyabe baki ko tabata batayi ba bare ta duba meye a ciki,saita debi ruwan zafin tasha,sannan ta fito da flask din da wainar ta jera saman madaidaicin dining dinta mai kyau wanda keda kujera shida tana cewa "Ba don halinka ba" saidata aje sannan ta koma dakin,ta janyo ledar ta duba,kayan qwalama ne irin na kowacce amarya daren farko,kazar ciki kawai ta cire ta koma da ita kitchen,ta sake mata dan hadi cikin kayan qamshin da aka kawota dashi ta jona ovean dinta ta sake gasata da kyau sannan ta cireta taje ta hadata da 'yan uwanta saman table din,ta gyare wajen ta juya ta fice,bata tsaya a falon ba ta wuce dakinta don tana tunanin ba zata rasa abunyi ba a ciki. Cikin baccinsa ya soma jin qamshin kazar da take gasawa,bai gama farkawa ba wayar muhsin ta tadashi,ya farka yana ware hanci yana shaqar qamshin wanda yasa tsohuwar yunwarshi motsawa,saida kiran ya katse ya sake shigowa sannan ya samu damar dagawa "Haba malam,da ba zaka daga kiran nawa ba wato tunda mun gama namu aikinko?" "Kai bakasan haqqina ka dauka ba?,ina tsaka da baccina ka tadani?" Murmushi mai kama da dariya muhsin ya saki "Lallaikam,su bacci manya,ai dole kayi bacci tunda ka mallaki abinda rai keso ruhi ke muradi,barcin shekara shida zakayi ai...." "Wannan ne dalilin kiran daka yimin?" Ya katseshi gami da jeho masa da tambaya kai tsaye "A'a a'ah,so nake ince maka ka haqura hakanan fito muje gaisuwar surukai,idan muka dawo ka dora daga inda ka tsaya" "Ban fara bama bare na dora shaqiyyin banza,ni zaka yiwa iskanci?,dadin abundai aiba haram bane ko?" Dariya ya qyalqyale da ita "Dama waya ce haram ne?,banda kai dakeson haramtawa kansa,kayi sauri ka fito don Allah don nikam bazan shigo gidanku ba" "Kai ka sani" ya katse wayar ya ajeta gefe sannan ya yaye bargon da yake lullube dashi ya sauka daga gadon ya shige toilet. Tsaf ya shirya cikin manyan kaya,yayi masifar kyau daka ganshi ango xam,saidai babu wata walwala ko qyallin goshi da hausawa ke fada. Har yakai bakin qofar falon xai fita saiya tuna da ita,ya sake komawa ya doshi qofar dakin nata,sau hudu yana knocking bata amsa ba sannan bata bude ba duk da tana jinsa,ganin lokaci kaman zai qwace saiya juya ya fito,idanunsa suka sauka kan dining ya hangi flask akai,ya qarasa ya bubbude yaga meye a ciki,hankalinsa ya kwanta da alama taci abinci kenan,dama damuwarshi ya sauke nauyinta daga kanshi,kada ya fita ya barta bai sani ba ko bataci komai ba. Qaramin tsaki taja tana dauko wayarta ta soma danne danne,wani saqo data gani yadan ja hankalinta saita bude,nuradden ne ya tura mata shi,yana nuna yadda yayi rashi da kuma yi mata fatan alkhairi a aurenta,data duba date din sai taga tun ranar daurin aurenta ne,reply ta masa na godiya sannan ta fita ta laluba number anty zubaida tana son kiranta,duka yau babu wanda ya kirata kamar wadda tayi baqin jini ta raya haka a ranta. Kafin takai ga kiran kiran mubina ya shigo,ta daga ta kara a kunneta,gaidata ta soma yi ta amsa tana tambayar umma "Anty 'yan katsina zasu koma gobe da sassafe,zan rakosu zasu miki sallama" "To shikenan,idan kun tashi tahowa mubina,ki biya ta wajen anty zubaida ki taho min da laptop dina dana bata ajiya,zan kirata na gaya mata" "Tohm" ta amsa mata sannan ta sata ta kaiwa umma suka gaisa,tana ji tana cewa ga daada ta katse wayar tana sane,me daadan zata gaya mata kuma bayan tayi yadda takeso da rayuwarta me kuma yayi saura?,gwara a kawo mata laptop dinta don ko aiki zata koma abinta,bata ga kuma zaman da zatayi a gidan ba,aure ne dai sun daura bashikenan ba kuma?. Daga bakin qofar falo taji knocking,ta tashi ta saka hijabinta ta bude,dattijon dake musu gadi ne,ta gaidasji cikin girmamawa sanda shima ke qoqarin gaidata "Alhaji ne ya aiko dasu,amma yace yaron karya shigo masa gida yana waje,zan debosu yace a aje a qofar falo idan yazo zai shiga dasu" "Toh baba,ba damuwa" ta fada tana kaucewa tabar masa qofar a bude,koda ta dawo don rufe qofar bayan ya gama saita tadda kayan abinci ne,babu nau'in abinda babu naci da sha,hatta dasu maggi da curry,ba zata iya kwashewa ba saboda haka ta maida qofar ta rufe ta koma dakinta. Awa biyu sai gasu mubina sun iso,matan yayyen babanta biyu dana qannen babanta uku,sai su hasina mubina da khadija,sosai ta ware cikinsu aka shiga sabgogi,suna hira da matan kawunnan nata su hasina ana gyare gyaren indai takega ya kamata a gyara din,duk suka shigar da kayan abincin store suka jera,abinda ba zasu iya dauka ba kaman manyan buhunhunan shinkafa suka barshi a falon a gefe daya da zummar idan mai gidan ya dawo ya shiga dasu tunda ya hana wani ya shigo masa bare a shiga dashi,tunda suka zo hasina minti daya biyu sai tace amarsu ta ango tana mata dariyar shaqiyanci,tana sane da ita amma tayi banza da ita,bata tanka mata ba sai qarfe biyu na rana suna shirin yin sallar azahar bayan sun gama cin abincin rana "Amarya amarya,aina tsammaci zanzo na tadda angon naki" harara ta balla mata "Au da kika shiga dakina baki ganshi cikin handbag dina ba?" Sosai tasa su rafi'a cousin dinta da sukazo su dukka kwashewa da dariya,har ita hasinan da aka baiwa amsa "Banson wulaqanci,duk take takenki ina sane dashi,idan kika cikani kuwa zaki gane shayi ruwa ne" "Allah ya baki haquru,kawai na tsammaci sai munzo mun miki ruwan zafi ne" "Yanzu ma bata baci ba"tana amsata ta miqe ta shige bandaki donta daura alwala,tana jiyo dariyarsu,ita abunma saiya bata dariya,hasina duk yadda zata qular dakai ta iya,ina ita ina wani anwar,abinda hasinan ke hasashe akai bata tsammanin yiwuwarsa har abada a tsakaninsu,don masoyi akewa wannan halaccin,ita kuwa ta jima da cire anwar daga layin masoyanta can wani zamani daya jima da shudewa. Tana idar da sallah mubina data barsu a falo ita da matan kawuna nanta ta shigo tana gaya mata an kawo aike,cikin mamaki tace aike kuma?,ta amsa mata da eh,saita miqe kawai tabi bayanta. Manya manyan baqaqen ledoji ne data duba ciki nama ne da kifi danye "kai kitchen ki saka cikin freezer dake kusa da sink"ta fada tana juyawa sama abinta,qarfe uku hasina tace bari a dorawa ango,tasan tsokanarta take,don haka ko kallonta batayi ba,tana zaune suka shige kitchen din kuwa itadai tana cikin baqinta suna hirarsu. Qarfe biyar suka kammala lafiyayyen abinci,hasina ta bude sabbin warmers din shahida ta zuba komai ta tsarashi saman table,sannan suka gyare kitchen da gidanma duka suka soma haramar tafiya. Ta rasa me zata basu,saita tuna salary dinta na watan nan da company ya biyata duk da batakai qarshen watan ba biyu ta raba ta saka rabi cikin jakarta,jakar ta bude ta dauko musu ta hada musu da snacks na gararta,kamar kada su tafi haka taji,hakanan ta rakosu har farfajiyar gidan,daidai sanda wasu baqin katsinan suka shigo cikin motar gidan anty usaina bisa jagorancin sa'ida,suka gaisa dasu hasina su suka wuce su kuma suka shigo ciki. Cikin girmamawa da mutuntawa suka gaisa da juna,taja sa'ida kitchen ta hada mata kayan abinci tace takai musu,idan takai ta dawo ta dauki ruwa da drinks,sanda ta dawo shahida na ta gama shirya cups din da komai sa'ida ta qaraso tana murmushi ta dubi shahida "Anty,baki tambayi uncle ba,yana gidanmu wajen ummi,kinsan me yacemin?" Kai shahida ta kada tanadan murmushi badon hirar ta mata ba,kawai sa'idan na burgeta hakanan "Wai idan munje mu duba masa ke,ko kunyar ummi dake wajen fa baiji na anty,wai ki bashi abun dadi nakai masa" wato sai zaiwa siyasa kenan saboda yaga anty usaina a wajen?,lallai kam to su zuba,saita saki dan murmushin yaqe don kada yarinyar ta gane "Nikam inajin kunyar ummi,qyaleshi zai dawo gidan ai" daga haka yarinyar ta dauki ruwa da lemo,ita kuma shahida ta dauki kofuna suka fito. Ba laifi sun dan taba hira dasu suma,babu ruwansu kaman anty usaina,hakanan suna da girmama mutum kuma suna d sauqin kai. Gab da za'a kira magriba don har sun soma daura alwala motar anwar ta shigo gidan,shahida na tsaye tana shimfida musu manyan abun sallah ya shigo,donsunqi shiga dakin data ce su shiga suyi sallar a can,idanunshi akanta,karo na farko a rayuwarsa daya soma ganinta a haka gayarta,ba hijabi babu mayafi,cikin riga da skert na atamfa da suka xauna mata das a jikinta,suka fidda shape dinta sosai,wani kishinta yaji ya sake kamashi sosai fiye da baya,saiya dauke kansa yana son hana bacin ranshi tasiri,duk sanda zai ganta hotunannna dawo masa,abun ya zame masa kamar jarraba,bai taba zaton yana da halittar kishi ba haka,bai tama tsammanin yana kishin wata halitta a bayan qasa kamar yadda yake kishin shahidan ba,a yanzun da take cikin gidanshi sai yake jin yayi wani abu daya dace,yake jin hankalinsa yafi kwanciya da samun nutsuwa a hakan koda ba zaman dadi bane akan tana waje ba tare dayasan me take yi kuma aina take ba,tare dawa take,duka yanzu ya samu aminci game da wannan. Ita ta soma yi masa sannanu da zuwa,yadan tsaya suka sake gaisawa dasu,yace bari ya shiga ya daura alwala kada a kira sallah,daya daga cikinsu data ke zaton qanwar babansa ce tace "Ai muma muna idar da sallahr xamu wuce don zamu koma mu shirya kayanmu gobe sai ta dikko dakin kara" murmushi ya saki "Dakin kaara ko dakin kara?" Dariya suka saki ta maida masa amsa da alama akwai dan wasa haka a tsakaninsu "Oho kai ka sani,koma dai dakin meye ta maka komai,tunda gashi sun baka mata da nan kanon suka kasa baka saida kayi kamun qafa damu,kai din kanka su suka samar dakai" "Gaskiya ne,kin gama magana" ya fada yana dariya dariya gami da gyada kai "Kafin ku wuce na fito in sha Allah" "Toh babu damuwa" ta amsashi,saiya juya da dan sassarfa ya soma hayewa saman. Tsaiwa tayi ta rasa abunyi,duk saita tsargu taga kaman kowa idanunshi a kanta yake yanason yaga ya zatayi,duk da cewa ba haka bane kowa sabgar gabanshi yake "Jeki mana shahida?,mu ai ba baqi bane karki damu" anty aminan dake shirin tada sallah ta fada,saita miqe cikin jin kunya ta soma takawa a hankali ta isa inda hasina ta shirya kayan abinci,ta dauki jug data hada lemo ya fara qanqara shi yasa ta fito dashi,tasan wai kafin lokacin cin abincin ya huce yadda za'a iya sha,ta dauki cup daya cikin mutuwar jiki ta nufi saman ta soma taka step din,xataso ta sanya koda mayafine,amma batason tayi wani abu da zai bar alamun tambaya game da ita akan baqin,fatanta daya Allah yasa taje ta taras dashi a bandaki,shine kawai zatayi saukowarta ba tare dashi yasan taje ba,hakanan suma ba tare da sunsan cewa bata je din ba. Qaramar varender mai kyau itace zaka soma taddawa bayan ka gama tsallake matattakalar benen zuwa qarshenta,wadda aka qawata da tiles da kuma shukes shuke na roba wanda idan ba tabawa kayi na zaka rantse da Allah rayayyu ne na gaske,cikin qananun kwandunansu masu ado suma,sai qofar glass wanda ta mamaye gabanka,daka tura zaka tadda wani ni'imataccen falo,wanda iskar dake kaiwa da kawowa ma daban take,komai na falon farine sol idan ka debe kayan kallon dake ciki,don hatta da frames masu sunayen Allah dake jikim bango farare ne,qofofine guda uku a saman kowacce tana dan nesa da 'yar uwarta. Bata gama wannan nazarin ba taji motsi daga gefanta,ta juya saita ganshi tsaye yana cire agogon hannunshi wanda dorashi da yayi saman teburin gilashin ya bada sautin daya jayo hankalinta,ya dan dosana gefan kujerar ya cire takalmanshi hadi sa safar gaba daya ya hadesu waje daya,safar agogon takalmin da muqullin motarsa,sau daya ya daga kai ya kalleta,saiya dauke ya taka zuwa inda ya aje remote na ac ya dauka ya soma rage sanyin da take kwararowa sannan ya ajeshi. Takawa yayi kaman zai shigeta ya wuce bedroom,sai kuma ya dakata saitinta,sunyi kusanci da yawa,tanason jan baya amma batason nuna masa tsiawarsa ta wani dameta kota dadata da qasa,idamunshi cikin nata ya sanya hannu ya dauki jug din ya daga cup daya ya zaunar dashi saman tray din dake riqe a hannunta tunda ta shigo,ya tsiyaya lemon a ciki ya aje jug din sannan ya dauko cup din yakai bakinsa,har ya gama shanyewa idanunsa na kanta,yayin da ita kuma taqi duban sashen da yake,sai daya shanye tas sannan ya aje cup din ya wuceta,sai daya dora hannunshi saman handle din sannan yace "Baiyi dadi bama" ya tura qofar zai shige,sarai ta jishi,haushi ya cikata,takaici ya qumeta "Dama badon kai na kawo ba,albarkacin wasu kaci,idan ka isa kuma ka amayomin da abina mana,aiba matse bakinka akayi akace sai kasha ba dama" fasa shiga dakin yayi,yayi taku uki da baya sannan ta juyo gaba daya,cikin takun nan nasa dai ya iskota,kaman xai hadeta cikin jikinsa har yanzu idanunsa na narke cikin nata yace "Zan amayoshi,amma nima ba zakimin asarar ruwan jikina ba,saidai idan zaki shanye amanne tas" ba shiri ta ware duka idanunta tsakiyar nashi ta watsa masa harara "Allah ya kiyaye ya sawwaqe,in sha amanka ni shahida?" Kafe juna sukayi da idanu,fuskarta na nuna bacin ranta muraran,yayin da nashi yanayin ya kasa nunawa,bacin rai ko walwala?,yaci gaba da duban qwayar idanunta,yana tuna wani lokaci can baya da ya taba zuwa mata yana zazzabi,kwananshi uku baida lafiya amma yaqi yarda ta sani don karta tashi hankalinta,duk da haka ta fahinta,ta kuma nuna rashin jin dadinta na yadda ya boye mata,tace da shine da baida zaune saiya tabbatar ta samu lpy donme ita zai boye mata?,da qyar ya lallasheta kan ya samu sauqi aisuna tsaka da fira yaji bazai iya daurewa ba amai na taso masa,ya sanar mata kan zai wuce gida,cikin damuwa ta tsaidashi tasha gabansa tana duban yadda yanayinsa ya sauya,aman ya taso masa,yasa hannu da hanzari don ya kaudata gefe amma taqi ta matsa din,da haka ya soma wanke mata jiki dashi,daqyar ya matsar da ita gefe ya qarasa a qasa,yana ta jikinta daya bata mata amma ita sai yaha ba damuwarta bane,qarshe ma dayaqi tsaiwa ta gyara wajen tace "Idan baka bari ba wallahi kana kallo xan shanye aman gaba daya" cikin mamaki yake dubanta,qaramin murmushi ya subuce masa,ya zaci da wasa take "Toh shikenan bismillah,amma dai ni bazan barke ki wanke wajen nan da kanki ba alhali gani a tsaye" bai ankare ba ta durqusa,cikin zafin nama ya riqe gefan hijabinta gam da mamaki yake cewa "Kina hauka ne shahida?!,amaine fa qazanta" rai ta bata sosai "To matsa gefe idan ba haka ba na aikata" haka ya matsa din yana kallonta ta gyara wajen. Tunaninsa ya yanke sanda shahidan dake gabansa ta soma motsawa da alamun barin wajen dauke da farantin lemon "Kin makaro tunda ada kinsha ai" da hanzari ta dago ta dubeshi suka hada idanu,ta tuna lokacin da yake nufi din itama,amma saita yatsina fuska kamar bata gane ba "Kama zancan xamanin jahiliyyar shahida,kuma da ana maida hannun agogo baya da sai na maidashi na kuma goge wajen don baka cancan......" Bata kai ga qarasawa ba ta tsinci bakinta cikin nashi,ya riqe fuskarta da dukka tafin hannuwansa,ta tsorata sosai don bata zaci haka ba,garin yunqurin qwacewa ta saki jug da cup din duka suka zube anan qasa suka tarwatse,sai daya tsotse duk lips dinta da cikin bakin iya son ranshi sannan ya saketa,bacin rai a sannan ya bayyana qarara a fuskarta,ta bude baki xatayi magana cikin fushi ya rigata "Tunda wancan xamanin ya shude ba zaki iya gogewa ba saiki goge wannan ai na sabon zamani dake wanzuwa a yanzu,ki saku reza ki yanke bakin kiyar ki canzashi da wani" daga haka ya juya abinshi,rasa amsar bashi tayi ga kuka nason qwace mata kuma bata son tayi a gabansa,saita juya da sauri zata fice,tana bude qofar yana sake shan gabanta,fuska a turbune yace da ita "Wannan zaqin da bakinki yake ina fata ba syrup kika sha ba ko?,don nan gidan ba'a haka ciki" yakai qarshen zancan yana dage mata girarsa qwaya daya,kukan da take riqewa ya qwace mata,hawaye suka soma layi,duka girarsa biyun ya kuma dagewa "Au....shi kika sha kenan?,sauka ki tafi to kafin ya fara aiki" ya fada yana matsawa gefe gamida kafeta da ido "Allah yasakamin ban yafe ba" kawai tace tana ficewa cikin sassarfa,wata dariya ce taso qwace masa sanda ta fice din ya maida qofar ya tura,saiya tuna shahida 'yar 16 shekaru shida baya da suka wuce,bata da tsiwa amma bata iya bacin rai ba,baiji dadin kukanta ba amma yasan wannan ce kawai hanyar da zai sata tayi magana,tunda can mutum ne shi da bai iya gaba ba sam,duk da har yanzu bacin ranshi game da ita na nan danqare cikin ranshi amma bazai yarda ayi xaman maqiya dashi ba. Yana kwashe fasassun gilasan yana tuna abinda ya farun,yakai tatsunsa saman lips dinsa ya shafa,yadan cije lebansa na qasa kadan,tabbas yaji zaqi a bakinta,saidai yasan ba kayan maye bane,don tunda ya bada sadakinta ya zuba ido akanta sosai amma bai taba ganin wani abu da zai sashi ya zargeta ba,ko da shahida nakan halayenta nada da idanunsa suka gani,koda bazai dore a zaman aure da ita ba zaiyi qoqarin ganin ya maidata saitinta kodon soyayya da amanna da mahaifinta ya bashi a baya,duk da hakama baiga wani mummmunan abuba game da ita har yau daga sanda ya soma sanya idanu a duk motsinta. _gashinan yau na muku,amma har gobe sai jibi idan Allah ya kaimu_🙏🏽🙏🏽 *Alqawarin Allah* 3️⃣8️⃣ Kafin ta sauka qasa ta dan jima a tsaye saman step na kusa da qarshe tana dai daita yanayinta sannan ta sauka a hankali. Ana qwala kiran sallahn ya sauko cikin jallabiya mai gajeran hannu fara sol da ita,bisa dukkan alamu sabuwa ce,jikinsa na tashin qamshin turare mai sanyi kaman wanda yayi wanka dashi,zuciyarta taso yadan fisgeta ta kalleshi amma tayi ta maza ta dake kaman bata ganshi ba har ya fice masallacin. Ba'a jima can da idarwa ba ya dawo,ya zauna saman kujerar falon suna dan taba hira da anty amina kafin su kammala kintsawa,da suka tashi tafiya saita rasa me zata basu,qarshe data shiga dakinta wajen akwatunan lefanta ta isa ,karo na farko data budesu ta kuma kalla abinda ke ciki,guda biyu ne masu dauke kayan sawa taf daqyar aka rufesu don ba abinda aka taba a ciki,ta dinga daga kayan daya bayan daya tana kalla,kan wata shadda lace ta tsaya,ta kalleta sosai,tun daga colour har design din choice dinta ne,tasan duk duniya kuma babu wanda yasan hakan sai anwar,hakan ya saka ta sanya hannu ta cirota,ta kalleta sosai,iya kyau ta mata kyau qwarai,kuma kana ganinta kasan babbar ce,saidai ba zata iya sanyata a jikinta ba,tasan anwar ne ya zabeta,ta yanke ta baiwa anty amina ita,sauran manyan su uku ta zaba musu atamfofi,yan yaran da yan matasan kuma ta diba musu kayan kwalliya,ta zaba kayan gararta da yawa ta hada musu. Anwar yana tsaye ta miqawa kowa,ta miqo ledar anty amina yafi kusa da inda take tsaye,saboda haka ya zira hannu ya karba ya buda yana gani sannan ya rufe,daga kai yayi tasan ita zai kalla saboda haka ta dauke kai,ilai kuwa itadin ya kalla,haka kawai yaji kyautar ta masa ciwo,bawai saboda kudin abarba,a'ah,yafi qarfin kudinta hakanan anty amina a wajenta tafi qarfi wannan,yasan cewa da biyu tayi kyautar itama ta san da hakan,abinda ya bata ranshi kenan. Har bakin mota tayi musu rakiya,anwar yace a matse sukazo hala,su ragu wasu su shiga motarsa ya kaisu,ta musu sallama ta koma cikin gida,harsun gama shiga yace yana zuwa,ya buda murfin motar ya koma cikin gidan. Tana tsaka da tattare wajen taji shigowarsa,ta daga kai ta dubeshi saita basar taci gaba da abinda take kaman bataga shigowarsa ba,bayanta kadan ya tsaya,kaman bazaiyi magana ba sannan daga bisani yace "Duk yadda kikeji a zuciyarki game dani kusan nima haka yake koma fiye,amma,karki sake gangancin da kikayi yau,duk kayan dana siya nasan wa na siyawa shi,idan da buqatar bada kyautar irinsu a siyo daga waje ba daga cikin akwati ba" idanunta ta watsa masa sannan tace "Ina ruwan wani?,ina cewa kayana ne ko?" "Alright,hakane fa,amma keda kayan qasan wa kuke?" "Oho" tace tana ci gaba da aikinta,shuru yayi yana kallonta,saiya jinjina kai sannan yace "Zaki gane kurenki" ya juya ya fice saboda tunawa da yayi yabar mutane a mota,tsaki taja taci gaba da aikinta tana cewa "Na dade ban gane kuren nawa ba" A gurguje ta gama duk abinda zatayi ta dauki duk abinda take buqata ta shige dakinta,wanka ta soma yi sannan taci abinci,ta jawo wayarta ta fara amfani da ita,kama daga kiran waya,da duba saqonnin wayarta ta watsapp,bataji shigowarsa ba sai wajen qarfe goma na dare,dai dai sannan ta miqe ta kashe qwanta ta koma gado tayi addu'ar bacci tayi kwanciyarta. Shika koda ya shigo dakinsa ya wuce abinsa,baibi kota kan abincin dake kan tebur ba. 🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍 Washegari ma ta samu baqi ba laifi duk da basu kai na jiya ba,abinda ya debe mata kewa kenan har wata washegarin,saidai randa ta cika kwana na hudu dif kakeji,duk sai taji gidan babu dadi,haka ta wuni ita kadai,daga kwanciya sai kallo sai latse latsen waya,har zuwa dare data kammala abinda take tayi shigewarta daki. Tunda ta gama yin baqi bai kuma sakata a idanunsa ba,kafin magariba ta gama komai tayi shigewarta daki,bata fitowa sai washegari shima idan ya fita a gidan,zatayi abincin safe haka na dare ta aje masa,saidai shima bai bata taba abincin ba,yadda ta jera haka zata kwashe abinta,kusan hakan na faruwa ne saboda ya koma aikinsa gadan gadan,bai samun damar dawowa gidan dawuri,hakanan da wuri yake fita. Sati biyu cur aka suka kwashe a haka,idan ya dawo bai ganinta,hakanan idan zai fita ma haka. Zaman taji ya isheta,kadaicin ya mata yawa,tayi kallo har ta gaji,tayi chart ya isheta,saita yanke shawarar ta sameshi tayi masa magana kan komawarta office don tana da buqatar hakan. Sai data idar da sallar magariba yau sannan ta shiga tayi wanka,ta shirya cikin wani cotton material baqi da aka yiwa adon purple wanda yadan ciza,ta gyara gyara gashinta sannan ta feshe jikinta da turaruka yadda ta saba,duk da ko batasaka turaren ba qamshi kayan suke bayarwa na turaren wutar da take turare kayan nata dashi,nan bakin window din dakinta dake fuskantar harabar gidan ta tsaya,ta yaye labulen tana kallon harabar gidan kawai,duk da babu kowa sai mai gadi dake zaune can bakin qofar gidan,amma ko ina gauraye yake da haske tarwai kaman rana,haka gidan yake da wuta 24hrs. Ta jima tsaye tana saqo tana warwara,har ta soma gajiya da tsaiwar ta saki labulen da niyyar komawa ta zauna taji horn,saita tsaya tana ci gaba da kallon qofa sanda baaba ya tura gate din anwar ya sako motarsa cikin gidan,tabi motar da kallo har zuwa harabar da yake ajesu,tana kallo baban ya qarasa bakin motar bayan ya maida qofar ya rufe,ya tsaya daga bakin window din da alama magana suke sannan ya juya ya tafi. Tayi zaton bazai fito daga motar ba jin shuru na wasu mintuna,kana daga bisani taga ya bude murfin motar ya fito,sanye da mens blazzer ruwan blueblack da baqin takalmi sau ciki,yanayin takunsa kawai zai gaya maka a gajiye yake,idanunta akanshi har ya bacewa ganinta sannan ta saki labulen tana sauke ajiyar zuciya,hannunta saman kanta tana son tuna wani abu tana tursasa zuciyarta kan kada ta tuna mata. A qalla sai data bada minti talatin kyawawa sannan ta yafa mayafinta ta fito,sam bata ko sha'awar hawa samansa amma dole ce xata kaita,taso ace yana zama a falo ta cimmasa a can. Yauma da zata gota table din sai data kalla,komai yana nan akai kamar yadda ta dora,saita tabe baki tayi gaba cikin zuciyarta tana cewa "Kai ka jiyo,nidai na sauke haqqina ko". Yana zaune saman kujera one sitter,sanye da boxer da short sleeve shirt farare qal,fitowarsa kenan daga wanka,yayi relaxing bayansa a makarin kujerar,idanunsa na lumshe ya hada yatsun hannanunshi cikin na juna,haka kawai yakejin gidan ya masa shuru tamkar shi kadaine a cikin gidan,yunwa da gajiya suna damunsa,yana buqatar abubuwa da yawa amma ya rasa wanne zai fara tunawa cikin zuciyarsa,cikin haka yaji kaman an buda qofar falonsa,da mamaki ya ware idanunshi da suka dan kada saboda yadda ya jima da rufesu yana kallon qofar,qwarai yayi mamakin ganinta,amma ya shanye mamakin yana ci gaba da dubanta sanda take takowa ciki,bazaiyi qarya ba ta masa kyai cikin yadin jikinta,saiyaji wani bangare daya cunkushe a zuciyarsa yana budewa,tunanin da yakeson yi ya soma dawowa,kwanaki yau kusan goma sha uku kenan bai sanyata a idanunsa ba,ko motsinta bazai iya fadin yaushe rabon daya ji ba,tana sake matsowa qamshin jikinta na shiga ta qofofin hancinsa,qamshin daya sanyashi lumshe idanunsa ya sake budesu a kanta sanda ta samu hannun daya daga cikin kujerun dake can nesa dashi ta dosana ta zauna kan wuta,shuru ya ratsa dakin bayan sallamar data yi na wasu daqiqu sannan tace "Inason magana dakai" idanunshi ya daga ya kalleta na wasu sakanni kafin ya janye duban nashi daga kanta ya maida idanun nasa ya rufe kaman yadda suke dazu,don shine mafita kawai a wajensa "Uhmmm" yace da ita a taqaice "Inason na koma aiki idan Allah ya kaimu ranar monday" da sauri ya bude idanun nasa ya zubesu fes a kanta,saitaji ya mata kwarjini saboda haka ta janye idanunta daga kanshi "Labari kike bani ko umarni?" Ya tambayeta kai tsaye,yanayin tambayar daya mata yasa dole ta kuma kallonshi,tadan sake tsuke fuska "Shaida maka nake"sai ya maida idanun nashi ya rufe sannan yace "Tunda ba umarni bane ba zaki koma ba,kin gama aiki a triple r gem,bama nan ba kawai,kin gama kowanne aiki ako ina idan ba cikin gidan nan ba" haushi takaici da baqinciki suka cikata,me yake nufi kenan?,yana nufin ya rabata da aikinta,cikin hasala tace "Me kakeso kace?,bayan duka qarfa qarfan daka yimin bai isheka ba har saika qara da wannan?,toni ban yarda ba in gaya maka gaskiya,ai bamuyi haka dakai ba" miqewa tayi tsaye ta soma tafiya "Dama na gaya maka ne donkar kazo ka tarar bana nan kace ban shaida maka ba". Tana dab da fita ta tsinceshi a gabanta,suna hada ido ta kauda kai saboda yadda qwayar idanunshi ta sauya launi "Bazan taba lamunta ki fita wani waje mahada jama'a maza da mata ba da sunan aiki,ki gogayya da maza kiyi magana dasu,ki fita da safe ki dawo da yammaci,idan na barki kika koma lallai na tabbata wawa,kuma abinda nayi baiyi riba ba,kina nufin komawa office din danaga wani ya kama yatsarki zai saka miki zobe?,Karki soma gigin aikata kuskure irin wannan,idan ba haka ba zaki gane baki da wayau,idan kuma baki yarda ba bismillah" daga haka ya kauce daga hanya ya bata waje yana komawa mazauninsa,da gudu gudu ta fice daga falon ta soma sauka qasa,tayi nasarar riqe kukanta batayi agabansa ba sai data danga da dakin gadonta,wani irin tuquqi takeji cikin qirjinta da zuciyarta,sam bazata yarda ba,ba zata lamunci ya sake cin galaba a kanta ba bayan wadda yaci,idan yayi haka aiya tauyeta da yawa,tayita zama kenan cikin wannan gidan da zaman cikinsa harya soma gundirarta,zaman da bai mata ma'ana ba sam?,gobe kam saidai ayi duk wadda za'ayi,idan yaso yace ta wuce gidansu. Iska yake furzarwa daga bakinsa mai dumi bayan fitarta yana murza tafin hannunshi kan hannun kujerar da yake kai,yanajin bacin rai nason taso masa yana danneshi,ta yaya zai barta ta koma aiki?,aikin da tun ranar daya ganta cikinsa bai sake samun nutsuwa ba sai daya tabbatar ta daina zuwa ta sanadin aurenshi,randa yaga nuradden din cikin office dinta da qyar ya samu ya saisaita kansa,ji ya dinga yi kaman hawan jininsa zai tashi,sannu sannu ya dinga ambaton sunan Allah har ya samu zafin da yakeji ya sauka,yunwar da yakeji ta dawo masa sabuwa fil,bashi da mafita illa slipper dinshi daya zira ya sauka zuwa qasan. Karon farko da zauna kan dining din,ya jawo warmers din ya soma budewa daya bayan daya,take qamshi ya cika wajen wanda ya qara qaimin yunwar tasa,tun kafin ya soma ci a ido abincin yayi masa,sanda ya soma ci kuwa saiya samu kansa da lumshe idanunsa,dadin girkinta ya ninka fiye da wanda ya sani a baya,a nutse yaci abincin,ya kuma yi qoshin daya manta rabonshi da yayi irinsa,baibat abincinba sai daya diba wani yayi guzuri ya haura sama dashi. 🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍 Bayan ta idar da sallar asuba bata koma ba ta soma gyara dakinta,sannan ta fito falo,ga zatonta zata dauki fulasan abincin kamar yadda ta saba kowanne lokaci amma saita tarar anci fiye da rabin abincin,harara kwanukan abincin tayi kaman su suka mata laifi "Dan rainin hankali,nina kwana ina baqinciki,shi kuma ashe zuwa yayi ya cika cikinsa,bacin raina dadi ma kenan yake masa,bai taba cin abincina ba sai yau daya fuskanci a bacin rai nake kenan,aikuwa bazan yadda ba nima" da wannan tunanin ta gama komai na gidan,ta kuma shirya abincin safe ta jera yadda ta saba sannan ta shiga wanka. Tara saura ta gama komai,ta shirya tsaf cikin laffaya data nade jikinta fes da ita,qafarta sanye take da takalmi me tsinin dunduniya,ba qaramin kyau tayi ba,kana kallonta kasan sabuwar amarya ce. Tana tsaue bakin dining tana break don ko zama batasonyi bare ta makara taji takun takalmi da alama ana saukowa ne daga sama,tasan shine don haka taqi daga kanta bare ta dubeshi,daga saman step din ya tsaya yana dubanta cikin mamaki,tana nufin fita kenan zatayi da gaske?,a ina shahida ta sauyo hali ta koyi musu da kafiya?,bari ya zuba ido yaga iya gudun ruwanta,dole ya nuna mata shine mijin itace matar,zata ga qarfin qwanji yau kuwa idan batayi wasa ba. Bai qara taku daya ba yana tsaye yana kallonta harta gama,ta ciro paper daga jakarta tayi rubutu ta ninke ta aje anan sannan ta tattara jakarta ta zuge ta riqe a hannunta ta soma takawa don ficewa. *Alqawarin Allah* 39 "Karki kuskura ki fita" ya fada yana daga tsayen yana dubanta,kamarma bada ita yake ba haka taci gaba da takawa. A nutse ya gama saukowa sannan ya saka hanzari irin na ingarman namiji,kafin kace meye wannan ya cimmata,yasa hannu ya maida murfin qofat falon ya rufe idanunshi cikin nata ya bata umarni kai tsaye "Wuce ki koma ciki" dubansa tayi itama "Kaman yaya?,bayan na gaya maka tun jiya aiko?" "Ki koma ciki kawai nace" saita dubeshi na tsahon minti daya,ta karanci da gaske yake,ita kuma na zata yarda yaga lagonta ba bare yaci gaba da sanyata yin abinda batayi niyya ba kuma bata shirya ba,saita sake dora hannunta kan handle din qofar da niyyar budewa,caraf ya riqe hannun nata,tana shirin masa tsiwar ya saketa bata ankara ba taji an sureta gaba daya daga ita hat jakar hannun tata,ya juya ya soma taka matakalar da zata sadashi da sama,sosai ta soma qoqarin zillewa ranta na quna na yadda ya maidata kaman wata karmami,ya dagata ba komai bane a wajensa kamar ba mutum ba?,sai kace wata 'yar baby "Meye haka ne?,ka saukeni don Allah bana son irin haka,ka saukeni,ka saukeni bana so" abinda ta dinga fada kenan tana qoqarin qwacewa daga daga hannunsa,baiko bi ta kanta ba hakanan bai fasa hawa saman ba har sai daya dangane da bedroom dinsa sannan ya cillata saman lallausan gadonshi yana maida numfashi,fuskarshi a daure,ranshi a matuqar bace wanda ko ba'a gaya maka ba zaka fuskanci haka ta idanunsa da suka soma sauya kala,nunata yayi da yatsa cikin bambami dake nuna ranshi ya baci "Na fuskanci cewa sassauci na yana neman kawo raini a tsakaninmu,barinki kiyi yadda kikeso yasa kikejin kece mijin nine matar ko?,to daga yau komai zai sauya,zaki gane wane shugaba tsakanin ni da ke" daga haka ya maida muqullin dakin ya rufesu shida ita gaba daya,cikin hanzari take saukowa daga saman gadon nashi tana cewa "Ka budemin qofa,ya zaka rufeni anan,wai me yasa ka fiya son kanka ne da yawa?,me yasa kake zalunt...." Maganar tata ce ta katse sakamakon yadda ta sauko qafafunta qasa da hanzari da cogenta,sai akayi rashin sa'a qafar tata ta turgude da tsinin takalminta,maimakon ta qarasa maganar da take saita buge da sakin qara,ta koma tayi zaman dole bakin gadon tana duba qafarta. Towel din dayake daukowa ya rataya a wuyanshi sannan ya waiwayo yaga me ya sakata yin qarar,idanunsa ya sauka a qafarta da take dafe da ita,a hankali ya qarasa ya duqa gabanta,ya saka hannu zai taba qafar ta janyeta baya da sauri tana ci gaba da dafe wajen,ya gane me take nufi,tana nufin batason ya taba nata qafa kenan,saboda haka ya qyaleta ya juya abinshi yayi shigewarsa wankansa. Azabar data dinga ji cikin qafar ya tabbatar mata mawuyacine idan ba targade tayi ba,batasan ya zatayi da qafar taya ba,hakanan ita daua cikin dakin ta dinga dafe qafar tana jin zugi na ratsata. Sai daya kwashe awa guda cur sannan ya fito,a shiryensa kaman ba shine ya shiga wanka da towel da jallabiya ba,ya isa gaban mudubi ya dauki turarukansa ya fesa,ta cikin madubin yaje dan kallonta yadda ta soma hada gumi,tuni harta cire yafen lafayar jikinta,idanunsa ya sauka kan lallausar t.shirt din dake jikinta fara sol mai dogon hannu da rufaffen wuya,wadda ta lafe sosai a jikinta ta fidda shape din albarkatun qirjinta,saiya dauke idanunsa daga kanta da sauri,ya gama fesa turarensa ya taje kansa sannan ya juya ya sake takawa inda take ya tsugunna gabanta karo na biyu,zata sake janye qafar yayi caraf ya riqeta sosai,ta saki ihun azaba sanda ya gama zare takalmin ya soma mammatsata,take ya gane targade ne,ya kuma gamo wajen,sai daya faki numfashinta ya kama wajen sosai wanda babu shiri ta qwalla wata irin qara tana qoqarin tureshi,saidai ko gezau baiyi na yaci gaba da gyara wajen,tun tana masa masifa tana jin girman kan ta roqeshi ya qyaleta harta soma roqon nashi tana hadashi da Allah,ta hada gumi jagaf kafin ya gama,yana sakinta ta saki ajiyar zuciya,sai kuka ya qwace mata,dama zuciyar na akusa,gani take kaman yana sane ya taba ciwon da yawa yayine kawai saboda mugunta. Baiko dubeta ya juya ya isa bakin qofa yabude zai fice,taso yunqurawa ta miqe ta bishi a baya da hanzari ko xata samu nasarar ficewa amma ina babu damar ta taka qafar,tana kallo yaja qofar,saidai wannan karon bai rufeta ba,abinda ya sanyata sakin ajiyar zuciya kenan,ta maida kanta jikin filo ta jinginar tana lumshe jiqaqqun idanunta da duka jiqe da ruwan hawaye. Tun tana sauke ajiyar zuciya tana shaqar qamshinsa daya kama dakin har bacci ya soma fisgarta,ta dinga dagewa don bata son yin bacci saman gadonshi amma ina yafi qarfinta. Qarfe biyu na rana ya sake dawowa saman,duka yau ba inda ya fita,duk da yaso yayi fitarsa ya qyaleta amma saiya kasa,sanin cewa mawuyacine ta iya tabuka komai saboda targaden data ji din ba kadan bane. A hankali ya turo qofar dakin,yayi tsammanin samunta zaune,sabanin hakan saiya sameta a kwance a rigingine tana bacci sosai,ya qarasa a hankali ya tsaya kanta hannunsa rungume a qirji ya zuba mata ido,irin kallon daya jima baiyi mata irinsa ba,abubuwa biyu na kokawa cikin zuciyarsa,ya samu ya kauda su,ya isa gefan kanta yadan bubbuga filon da take kai a hankali,bude idanunta tayi sannu sannu,saita tuna inda take,saboda haka ya ware idanun nata da sauri gami da miqewa zaune sosai tana masa wani kallo da yafi kama da harara "Ki tashi ki sallah" ya fada yana aje mata takeaway,sannan ya goya hannunsa a baya ya tsaya yana kallon yadda take kokawar miqewa cikin dabara,da alama tana shan zafi amma taqi nemon taimakonsa,data gaji da kanta ta koma ta zauna tana lumshe ido saboda zafin da wajen yake mata,gami da sauke numfashi "Ki tashi na taimaka miki badon halinki ba" "Banaso" ta fada da hanzari,sai ya daga kafadunsa alamun bai damu ba ya soma takawa zai fice,ta kalli agogo ta tabbatar idan ya fita da matsala,lokaci zai iya qwace mata,ita kuma idan tace zata tashi da kanta zata sha wahala,saboda haka kaman wadda aka yiwa dole tace "Dawo ka tayani,amma karka soma tabamin jiki don zaka rakani alwala" "Riqe jikinki na riqe taimakona" ya bata amsa sanda ya tura qofar kamar xai fita,tana kallo ya sake ficewa,sai wani abu ya tokare mata maqoshi,ita zaiwa wulaqanci?. Sau uku tana gwada takawar amma zafi da tsoro ya hanata,dole ta koma ya zauna tana kallo lokacin sallah na sake wuceta,baqinciki kamar tayi yaya. Turo qofar da aka sakeyi yasata daga kanta,shine dai ya sake dawowa dauke da wata roba dake fidda tururin ruwan zafi,hannunsa dayan riqe da towel,gabanta ya iso saitin qafar ya aje robar sannan ya jawo wani qaramin qawataccen stool dan gajere ya dora robar akai,bai kalleta ba ya kama qafar ya dora saman robar,zafi yasa ta saki 'yar qaramar qara zata riqe hannunsa sai kuma tayi saurin janyewa,tana ji ya dinga tsoma towel din yana matsewa gami da danna mata wurin,tun tana jin ciwo harya soma sake mata,radadin ya ragu,tunda ya soma aikin bai daga kai ya dubeta ba,lokaci lokaci idanunta kan fada kansa ba tare data shirya ba,amma ko sau daya taci sa'a basu hada ido ba,tsahon mintuna sannan ya miqe ya dauki towel da robar ya fice dasu. Sake gwada miqewar tayi wannan karon saita dan taku,a daddafe ta samu ta tura qofar da zata sadaka da falonshi don dakinta takeson tafiya,sam bata qaunar zaman dakin nasa,a bakin qofar falon wadda zata sadaka da matattakalar benan suka kusa karo yana dawowa tana shirin sauka,fuskarnan a tsuke kaman baisan meye dariya ba yace "Ina zaki haka?" "Inda nafi wayo" ta amsashi tana duban ta inda zata rabashi ta wuce "Koma ba inda zaki,kin dawo nan kenan harsai kin gane kece matar nice mijin,don na fuskanci baki banbance tazarar dake tsakaninmu ba" wani kallonsa tayi "Ba inda zan koma,dakina xan koma" girarshi ya dage "Ashe?,tunda kin yarda dakinki ne can ashe nine mai gidan ko?" "Oho?" Tace tana juya masa baya gami da turo baki,anwar din yakai mata ko ina,ya soma quret,ta fuskanci duk abinda zaiyi ya qureta ya iya,saita soma qoqarin rabeshi,qyaleta yayi harsai data raba tsakiyarsa sannan ya cukukikuyeta gaba daya cikin qirjinsa ya mata wani kyakkyawan ruqo,karon farko shida ita a rayuwarsu,ihu ta saki kaman wadda taga abun tsoro tana qoqarin qwacewa,daukarta yayi cak kamar yadda ya saba mata,abinda tafi tsana kenan,saboda idan yayi hakan gani take kaman ya raina mata wayo,bai sauketa ko ina ba bandaki,ya ajeta saman toilet sit,ta bude baki zatayi magana yasa yatsa ya dalle mata bakin gami da cewa "Shshshs,karki sake ki mana surutu a bandaki" yana maganar yana zaro ido kaman wanda yakewa qaramin yaro,bacin rai ya hanata magana,saita qyaleshi tana kallonsa ya daura mata alwalar,zai sake sungumota ya fito da ita ta zille,ta tashi tana dingisawa ta fito,fafur taqi zama a bedroom dinsa sai a falo,a nan tayi sallarta. Daidai sanda ta idar wayarta tayi tsuwwa,lokaci daya idanunsu suka sauka kan jakar,ya rigata saka hannu ya dauki jakar ya zuge ya ciro wayar,zai daga ta dubeshi "Karka daga min waya,bani abata" fuska a tsuke ya daga kai daga daga wayar da yayi niyya yi "Saboda baki da gaskiya?" Saita ware ido tana kallonshi "Eh bani da gaskiyar,duk abinda zakace kace,ka fadima abinda yafi hakan idan kaso,bakinka rayuwarka kuma zuciyarka ba tawa ba" ta qarashe cikin hasala,yana tsaye cak yana kallonta saiya saki murmushi ya dauke idanunsa daga kanta "Ko baki fada ba dama ai haka yake,dama ai zuciyata ce ba taki ba,haka rayuwata vata taba zama taki ba ki rubuta ki aje" daga haka ya daga wayar ya kara a kunnesa,hakanan taji kalaman sun samata ciwo,saita jefa masa harara ta dauke kanta wani sashe daban "Lpy qalau....eh,to" kawai taji ya fada ya latse wayar,yana shirin maidata wayar jakar aka sake kira "Triple R company" ya furta a fili,ta waiwayo da sauri ta dubeshi,da alama kira ne daga kamfaninsu,saita samu kanta tana addu'ar Allah yasa ba daga cikin maza abokan aikinta bane,bata gama wannan tunanin ba tajishi yana bada amsa "Maigidanta zaishigo ya samu boss dinku,zamuyi magana dashi" daga haka itama ya yanke wayar,tana kallo ya juya wajen da layi yake ya ciroshi,ya fidda layin saiya soma lanqwasashi "Karka karyamin layina" ta fada cikin hanzari,saidai ina tuni ya karyashin ya watsashi cikin dan qaramin abun sharar dake kusa dasu sannan ya dubeta "Namiji ne ya kiraki yana tambayar ba'asin rashin zuwanki aiki yau,baisan kina da aure ba?,ko baya ga haka dole ki rabu da wannan layin,bazan lamunci kici gaba da amfani dashi ba" ya qureta matuqa ta kasa daure bacin ranta ya bayyana muraran "Wai me ya dameka da rayuwata ne?,ina ruwanka dani?,me yasa kakeson shishshigema rayuwata bayan ni bayan ni gana shigewa taka?,bayan ni ban damu da taka rayuwar ba?,me na tsare maka?,ohk....alwashinka kakeson ka cimma ko na quntatawa rayuwata shine kake aiwatarwa yanzu?" Tsaf ya xuba ido yana kallonta ba tare daya motsa ko yace wani abu ba,mamaki take bashi idan tana masifa wanda ko iyawa ma batayi ba,batasan me yake ji cikin zuciyarsa bane,batasan wanne hali yaje ciki ba,da yana da ikon maida bara bana daya dawo da ita ya goge dukkan wani tabo da aibu,ba zata fahimci komai ba,ba zata gane komai ba,tanata amfani da zahiri ne ba tare data binciki me badinin ta haifar ba,saiya saki hannuwansa kawai gami da fidda qaramin murmushi,indai ba tunzurata yayi ba bazai taba jin muryarta ba,idan bai tunzurata ba yasan halinta sarai ba zata taba yin magana dashi ba ko zasu shekare a haka,yasan halinta tsaf,baijin baya ga mahaifanta akwai wanda yasan halinta sama dashi "Donke baki damu da rayuwata ba saime?,akwai dubbai da suka damu da ita,don na taimakeki ma na rabi rayuwar taki shine kike wani zaqalqalewa kina zaton ke watace a wajena?" Ido da baki duka ta saka tana son tantance me yake cewa,daidai lokacin da qararrwar dake nuna akwai baqi can falon qasa ta soma kadawa,saiya miqe kawai yana tabe mata baki ya fice ya sauka qasa. Daada ce ita da mubina da khadija,su sukayi waya dazu kan zasu rakota,tun bikin daada bata koma ba umma tace saitayi sati uku,sai yanzu ta soma shirin komawa,zuwanshi gidan wajen daada hira babu adadi,ta fuskanci abubuwa da dama game da zamansu ba tare daya gaya mata ba,da batayi niyyar zuwa gidan ba sam,amma taga ya kamata ta danyi gyara ko yaya ne kafin ta wuce karta tafi tabar baya da qura,don tasan umman shahidan koda wasa ba zata taba taka gidan shahida a yanzu ba,donko hira ake bata sanya baki,yaji qishin qishin din zata zo din yau dalili kenan dayasa ya tsare shahidan a sama don kar daada ta ramfo komai,don hausawa sunce babba babba ne,abinda zai gano ko kahau bishiyar rimi ba zaka hangoshi ba. Shi ya tarbesu daada tahau baza ido "Ina ita waccar ja'irar,kaine kake tarar baqin ita kuma tana me?" Murmushi ya saki "A'ah a'ah,kawai yaune na karbata,tana sama batajin dadi ne,ta samu targade a qafarta" "To ce mata ta sauko,don tayi targade saboda tsabar son jiki shine zata hau sama ta nade?,oh ni habiba,yaran yanzu saidai abarsu,kamar wadda ta karye" "Yi haquri daada karki rudamin mata,kin manta ke mai laifi ce dama?" Ya fada cikin tsokana,da ido ta bishi baki sake "Iyeeee....au wato harka soma bin bayan matarka?" Murmushi ya saki sosai sannan yace "Yi haquri daadarmu,so so ne amma aisonkai yafi ko?" Kasa amsashi tayi,cikin zuciyarta tanajin sanyi da dadi na yadda ta fuskanci.yana kulawa da jikarta,ta cika da fata da addu'ar Allah yasa itama haka take masa kada ta basu kunya,kada kuma ta watsa musu qasa a ido,mubina yasa ta shiga kitchen ta hada musu abin motsa baki,sai dayaga ta shirya musu komai sannan ya zqri muqulli don zuwa ya sama musu abinci "Ku hau saman daada ku sameta kafin na dawo" "Kaga nifa ba zama zanyi ba,mai motar daya kawomu ma yana qofar gida yana jira in fito ya maidani,don yau ni kam kwanan garinmu zanyi" qememe taqi barinshi ya fita,tace saidai yahau sama ya sauko mata da shahida "Kiyi haquri daada ki hau,ba zata iya saukowa ba" "Ita sabon qashima taqi saukowa bare ni tsohon qashi za'ace nayi tattaki nahau,tunda goya mata baya kake tayita narkewa kaga tafiyarmu" daqyar ya lallaba daadan tahau saman,inda mubina da khadija sukayi xamansu nan falon suna kallo. Har yanzu tana zaune saman abun sallah a haka daada ta shigo,sai taji dadin zuwan daadan,tana ganin tazo a daidai,ita ta qulla komai saboda haka dole ta yiwa anwar magana ya barta ta koma bakin aikinta,ba yabi ba fallasa ta gaidata,ta amsa tana qare mata kallo,bawani sauyi data gani tattare da shahidan na mace me aure,saita tabe baki,zata fara magana shahidan ta rigata cikin sautin wanda keson fashewa da kuka "Daada ki masa magana ya barni na koma aikina,kinga tun asali da aikina ya ganni,sannan kuma baice min bazanyi ba sai jiya da nake gaya masa zan koma yace waina gama aiki,daxun nan kan ku shigo ya dauki wayata ya ballamin layina waina daina amfani dashi" rashin sani yafi dare duhu,wani kallo daadan ke mata akaikaice,sai data gama tsaf sannan tace "Yo ai ni banga wani abun azo a gani dakika tabuka ba daxai nuna kinsan ma kina da aure,daga ke harshi banga wani sauyi tattare daku ba" "Kai anwaru" ta kira sunanshi tana zare ido,ya amsa mata ta masa nuni da kusa da shahida "Xauna nan" ba musu ya zauna yana qunshe dariya,daada sarkin rigimammu,da alama akwai magana a bakinta "Tunda kuka tare ta taba maka kwanan turaka?" Ta jeho masa tambayar kanta tsaye,take qwaqwalwarsa ta gaya masa abinda take nufi,kunya ta rugo ta rarumeshi,bai taba tunanin tambayar da zata masa kenan ba,cikin hanzari yace "Daada ai.... "Aime?,idan baka da amsa to bari na amsa maka,bata taba ba,kalli qafafunta da wuyanta,idan tace ma eh to qarya take,oh la'ilaha illallahu muhammadarasulillahi sallallahu alaihi wasallam" ta debo salati tana tafa hannuwa _afwa masu karatu,kunsan yadda sabgogi ke kutso kai cikin rayuwa_🙏🏽 *Alqawarin Allah* 39 "Karki kuskura ki fita" ya fada yana daga tsayen yana dubanta,kamarma bada ita yake ba haka taci gaba da takawa. A nutse ya gama saukowa sannan ya saka hanzari irin na ingarman namiji,kafin kace meye wannan ya cimmata,yasa hannu ya maida murfin qofat falon ya rufe idanunshi cikin nata ya bata umarni kai tsaye "Wuce ki koma ciki" dubansa tayi itama "Kaman yaya?,bayan na gaya maka tun jiya aiko?" "Ki koma ciki kawai nace" saita dubeshi na tsahon minti daya,ta karanci da gaske yake,ita kuma na zata yarda yaga lagonta ba bare yaci gaba da sanyata yin abinda batayi niyya ba kuma bata shirya ba,saita sake dora hannunta kan handle din qofar da niyyar budewa,caraf ya riqe hannun nata,tana shirin masa tsiwar ya saketa bata ankara ba taji an sureta gaba daya daga ita hat jakar hannun tata,ya juya ya soma taka matakalar da zata sadashi da sama,sosai ta soma qoqarin zillewa ranta na quna na yadda ya maidata kaman wata karmami,ya dagata ba komai bane a wajensa kamar ba mutum ba?,sai kace wata 'yar baby "Meye haka ne?,ka saukeni don Allah bana son irin haka,ka saukeni,ka saukeni bana so" abinda ta dinga fada kenan tana qoqarin qwacewa daga daga hannunsa,baiko bi ta kanta ba hakanan bai fasa hawa saman ba har sai daya dangane da bedroom dinsa sannan ya cillata saman lallausan gadonshi yana maida numfashi,fuskarshi a daure,ranshi a matuqar bace wanda ko ba'a gaya maka ba zaka fuskanci haka ta idanunsa da suka soma sauya kala,nunata yayi da yatsa cikin bambami dake nuna ranshi ya baci "Na fuskanci cewa sassauci na yana neman kawo raini a tsakaninmu,barinki kiyi yadda kikeso yasa kikejin kece mijin nine matar ko?,to daga yau komai zai sauya,zaki gane wane shugaba tsakanin ni da ke" daga haka ya maida muqullin dakin ya rufesu shida ita gaba daya,cikin hanzari take saukowa daga saman gadon nashi tana cewa "Ka budemin qofa,ya zaka rufeni anan,wai me yasa ka fiya son kanka ne da yawa?,me yasa kake zalunt...." Maganar tata ce ta katse sakamakon yadda ta sauko qafafunta qasa da hanzari da cogenta,sai akayi rashin sa'a qafar tata ta turgude da tsinin takalminta,maimakon ta qarasa maganar da take saita buge da sakin qara,ta koma tayi zaman dole bakin gadon tana duba qafarta. Towel din dayake daukowa ya rataya a wuyanshi sannan ya waiwayo yaga me ya sakata yin qarar,idanunsa ya sauka a qafarta da take dafe da ita,a hankali ya qarasa ya duqa gabanta,ya saka hannu zai taba qafar ta janyeta baya da sauri tana ci gaba da dafe wajen,ya gane me take nufi,tana nufin batason ya taba nata qafa kenan,saboda haka ya qyaleta ya juya abinshi yayi shigewarsa wankansa. Azabar data dinga ji cikin qafar ya tabbatar mata mawuyacine idan ba targade tayi ba,batasan ya zatayi da qafar taya ba,hakanan ita daua cikin dakin ta dinga dafe qafar tana jin zugi na ratsata. Sai daya kwashe awa guda cur sannan ya fito,a shiryensa kaman ba shine ya shiga wanka da towel da jallabiya ba,ya isa gaban mudubi ya dauki turarukansa ya fesa,ta cikin madubin yaje dan kallonta yadda ta soma hada gumi,tuni harta cire yafen lafayar jikinta,idanunsa ya sauka kan lallausar t.shirt din dake jikinta fara sol mai dogon hannu da rufaffen wuya,wadda ta lafe sosai a jikinta ta fidda shape din albarkatun qirjinta,saiya dauke idanunsa daga kanta da sauri,ya gama fesa turarensa ya taje kansa sannan ya juya ya sake takawa inda take ya tsugunna gabanta karo na biyu,zata sake janye qafar yayi caraf ya riqeta sosai,ta saki ihun azaba sanda ya gama zare takalmin ya soma mammatsata,take ya gane targade ne,ya kuma gamo wajen,sai daya faki numfashinta ya kama wajen sosai wanda babu shiri ta qwalla wata irin qara tana qoqarin tureshi,saidai ko gezau baiyi na yaci gaba da gyara wajen,tun tana masa masifa tana jin girman kan ta roqeshi ya qyaleta harta soma roqon nashi tana hadashi da Allah,ta hada gumi jagaf kafin ya gama,yana sakinta ta saki ajiyar zuciya,sai kuka ya qwace mata,dama zuciyar na akusa,gani take kaman yana sane ya taba ciwon da yawa yayine kawai saboda mugunta. Baiko dubeta ya juya ya isa bakin qofa yabude zai fice,taso yunqurawa ta miqe ta bishi a baya da hanzari ko xata samu nasarar ficewa amma ina babu damar ta taka qafar,tana kallo yaja qofar,saidai wannan karon bai rufeta ba,abinda ya sanyata sakin ajiyar zuciya kenan,ta maida kanta jikin filo ta jinginar tana lumshe jiqaqqun idanunta da duka jiqe da ruwan hawaye. Tun tana sauke ajiyar zuciya tana shaqar qamshinsa daya kama dakin har bacci ya soma fisgarta,ta dinga dagewa don bata son yin bacci saman gadonshi amma ina yafi qarfinta. Qarfe biyu na rana ya sake dawowa saman,duka yau ba inda ya fita,duk da yaso yayi fitarsa ya qyaleta amma saiya kasa,sanin cewa mawuyacine ta iya tabuka komai saboda targaden data ji din ba kadan bane. A hankali ya turo qofar dakin,yayi tsammanin samunta zaune,sabanin hakan saiya sameta a kwance a rigingine tana bacci sosai,ya qarasa a hankali ya tsaya kanta hannunsa rungume a qirji ya zuba mata ido,irin kallon daya jima baiyi mata irinsa ba,abubuwa biyu na kokawa cikin zuciyarsa,ya samu ya kauda su,ya isa gefan kanta yadan bubbuga filon da take kai a hankali,bude idanunta tayi sannu sannu,saita tuna inda take,saboda haka ya ware idanun nata da sauri gami da miqewa zaune sosai tana masa wani kallo da yafi kama da harara "Ki tashi ki sallah" ya fada yana aje mata takeaway,sannan ya goya hannunsa a baya ya tsaya yana kallon yadda take kokawar miqewa cikin dabara,da alama tana shan zafi amma taqi nemon taimakonsa,data gaji da kanta ta koma ta zauna tana lumshe ido saboda zafin da wajen yake mata,gami da sauke numfashi "Ki tashi na taimaka miki badon halinki ba" "Banaso" ta fada da hanzari,sai ya daga kafadunsa alamun bai damu ba ya soma takawa zai fice,ta kalli agogo ta tabbatar idan ya fita da matsala,lokaci zai iya qwace mata,ita kuma idan tace zata tashi da kanta zata sha wahala,saboda haka kaman wadda aka yiwa dole tace "Dawo ka tayani,amma karka soma tabamin jiki don zaka rakani alwala" "Riqe jikinki na riqe taimakona" ya bata amsa sanda ya tura qofar kamar xai fita,tana kallo ya sake ficewa,sai wani abu ya tokare mata maqoshi,ita zaiwa wulaqanci?. Sau uku tana gwada takawar amma zafi da tsoro ya hanata,dole ta koma ya zauna tana kallo lokacin sallah na sake wuceta,baqinciki kamar tayi yaya. Turo qofar da aka sakeyi yasata daga kanta,shine dai ya sake dawowa dauke da wata roba dake fidda tururin ruwan zafi,hannunsa dayan riqe da towel,gabanta ya iso saitin qafar ya aje robar sannan ya jawo wani qaramin qawataccen stool dan gajere ya dora robar akai,bai kalleta ba ya kama qafar ya dora saman robar,zafi yasa ta saki 'yar qaramar qara zata riqe hannunsa sai kuma tayi saurin janyewa,tana ji ya dinga tsoma towel din yana matsewa gami da danna mata wurin,tun tana jin ciwo harya soma sake mata,radadin ya ragu,tunda ya soma aikin bai daga kai ya dubeta ba,lokaci lokaci idanunta kan fada kansa ba tare data shirya ba,amma ko sau daya taci sa'a basu hada ido ba,tsahon mintuna sannan ya miqe ya dauki towel da robar ya fice dasu. Sake gwada miqewar tayi wannan karon saita dan taku,a daddafe ta samu ta tura qofar da zata sadaka da falonshi don dakinta takeson tafiya,sam bata qaunar zaman dakin nasa,a bakin qofar falon wadda zata sadaka da matattakalar benan suka kusa karo yana dawowa tana shirin sauka,fuskarnan a tsuke kaman baisan meye dariya ba yace "Ina zaki haka?" "Inda nafi wayo" ta amsashi tana duban ta inda zata rabashi ta wuce "Koma ba inda zaki,kin dawo nan kenan harsai kin gane kece matar nice mijin,don na fuskanci baki banbance tazarar dake tsakaninmu ba" wani kallonsa tayi "Ba inda zan koma,dakina xan koma" girarshi ya dage "Ashe?,tunda kin yarda dakinki ne can ashe nine mai gidan ko?" "Oho?" Tace tana juya masa baya gami da turo baki,anwar din yakai mata ko ina,ya soma quret,ta fuskanci duk abinda zaiyi ya qureta ya iya,saita soma qoqarin rabeshi,qyaleta yayi harsai data raba tsakiyarsa sannan ya cukukikuyeta gaba daya cikin qirjinsa ya mata wani kyakkyawan ruqo,karon farko shida ita a rayuwarsu,ihu ta saki kaman wadda taga abun tsoro tana qoqarin qwacewa,daukarta yayi cak kamar yadda ya saba mata,abinda tafi tsana kenan,saboda idan yayi hakan gani take kaman ya raina mata wayo,bai sauketa ko ina ba bandaki,ya ajeta saman toilet sit,ta bude baki zatayi magana yasa yatsa ya dalle mata bakin gami da cewa "Shshshs,karki sake ki mana surutu a bandaki" yana maganar yana zaro ido kaman wanda yakewa qaramin yaro,bacin rai ya hanata magana,saita qyaleshi tana kallonsa ya daura mata alwalar,zai sake sungumota ya fito da ita ta zille,ta tashi tana dingisawa ta fito,fafur taqi zama a bedroom dinsa sai a falo,a nan tayi sallarta. Daidai sanda ta idar wayarta tayi tsuwwa,lokaci daya idanunsu suka sauka kan jakar,ya rigata saka hannu ya dauki jakar ya zuge ya ciro wayar,zai daga ta dubeshi "Karka daga min waya,bani abata" fuska a tsuke ya daga kai daga daga wayar da yayi niyya yi "Saboda baki da gaskiya?" Saita ware ido tana kallonshi "Eh bani da gaskiyar,duk abinda zakace kace,ka fadima abinda yafi hakan idan kaso,bakinka rayuwarka kuma zuciyarka ba tawa ba" ta qarashe cikin hasala,yana tsaye cak yana kallonta saiya saki murmushi ya dauke idanunsa daga kanta "Ko baki fada ba dama ai haka yake,dama ai zuciyata ce ba taki ba,haka rayuwata vata taba zama taki ba ki rubuta ki aje" daga haka ya daga wayar ya kara a kunnesa,hakanan taji kalaman sun samata ciwo,saita jefa masa harara ta dauke kanta wani sashe daban "Lpy qalau....eh,to" kawai taji ya fada ya latse wayar,yana shirin maidata wayar jakar aka sake kira "Triple R company" ya furta a fili,ta waiwayo da sauri ta dubeshi,da alama kira ne daga kamfaninsu,saita samu kanta tana addu'ar Allah yasa ba daga cikin maza abokan aikinta bane,bata gama wannan tunanin ba tajishi yana bada amsa "Maigidanta zaishigo ya samu boss dinku,zamuyi magana dashi" daga haka itama ya yanke wayar,tana kallo ya juya wajen da layi yake ya ciroshi,ya fidda layin saiya soma lanqwasashi "Karka karyamin layina" ta fada cikin hanzari,saidai ina tuni ya karyashin ya watsashi cikin dan qaramin abun sharar dake kusa dasu sannan ya dubeta "Namiji ne ya kiraki yana tambayar ba'asin rashin zuwanki aiki yau,baisan kina da aure ba?,ko baya ga haka dole ki rabu da wannan layin,bazan lamunci kici gaba da amfani dashi ba" ya qureta matuqa ta kasa daure bacin ranta ya bayyana muraran "Wai me ya dameka da rayuwata ne?,ina ruwanka dani?,me yasa kakeson shishshigema rayuwata bayan ni bayan ni gana shigewa taka?,bayan ni ban damu da taka rayuwar ba?,me na tsare maka?,ohk....alwashinka kakeson ka cimma ko na quntatawa rayuwata shine kake aiwatarwa yanzu?" Tsaf ya xuba ido yana kallonta ba tare daya motsa ko yace wani abu ba,mamaki take bashi idan tana masifa wanda ko iyawa ma batayi ba,batasan me yake ji cikin zuciyarsa bane,batasan wanne hali yaje ciki ba,da yana da ikon maida bara bana daya dawo da ita ya goge dukkan wani tabo da aibu,ba zata fahimci komai ba,ba zata gane komai ba,tanata amfani da zahiri ne ba tare data binciki me badinin ta haifar ba,saiya saki hannuwansa kawai gami da fidda qaramin murmushi,indai ba tunzurata yayi ba bazai taba jin muryarta ba,idan bai tunzurata ba yasan halinta sarai ba zata taba yin magana dashi ba ko zasu shekare a haka,yasan halinta tsaf,baijin baya ga mahaifanta akwai wanda yasan halinta sama dashi "Donke baki damu da rayuwata ba saime?,akwai dubbai da suka damu da ita,don na taimakeki ma na rabi rayuwar taki shine kike wani zaqalqalewa kina zaton ke watace a wajena?" Ido da baki duka ta saka tana son tantance me yake cewa,daidai lokacin da qararrwar dake nuna akwai baqi can falon qasa ta soma kadawa,saiya miqe kawai yana tabe mata baki ya fice ya sauka qasa. Daada ce ita da mubina da khadija,su sukayi waya dazu kan zasu rakota,tun bikin daada bata koma ba umma tace saitayi sati uku,sai yanzu ta soma shirin komawa,zuwanshi gidan wajen daada hira babu adadi,ta fuskanci abubuwa da dama game da zamansu ba tare daya gaya mata ba,da batayi niyyar zuwa gidan ba sam,amma taga ya kamata ta danyi gyara ko yaya ne kafin ta wuce karta tafi tabar baya da qura,don tasan umman shahidan koda wasa ba zata taba taka gidan shahida a yanzu ba,donko hira ake bata sanya baki,yaji qishin qishin din zata zo din yau dalili kenan dayasa ya tsare shahidan a sama don kar daada ta ramfo komai,don hausawa sunce babba babba ne,abinda zai gano ko kahau bishiyar rimi ba zaka hangoshi ba. Shi ya tarbesu daada tahau baza ido "Ina ita waccar ja'irar,kaine kake tarar baqin ita kuma tana me?" Murmushi ya saki "A'ah a'ah,kawai yaune na karbata,tana sama batajin dadi ne,ta samu targade a qafarta" "To ce mata ta sauko,don tayi targade saboda tsabar son jiki shine zata hau sama ta nade?,oh ni habiba,yaran yanzu saidai abarsu,kamar wadda ta karye" "Yi haquri daada karki rudamin mata,kin manta ke mai laifi ce dama?" Ya fada cikin tsokana,da ido ta bishi baki sake "Iyeeee....au wato harka soma bin bayan matarka?" Murmushi ya saki sosai sannan yace "Yi haquri daadarmu,so so ne amma aisonkai yafi ko?" Kasa amsashi tayi,cikin zuciyarta tanajin sanyi da dadi na yadda ta fuskanci.yana kulawa da jikarta,ta cika da fata da addu'ar Allah yasa itama haka take masa kada ta basu kunya,kada kuma ta watsa musu qasa a ido,mubina yasa ta shiga kitchen ta hada musu abin motsa baki,sai dayaga ta shirya musu komai sannan ya zqri muqulli don zuwa ya sama musu abinci "Ku hau saman daada ku sameta kafin na dawo" "Kaga nifa ba zama zanyi ba,mai motar daya kawomu ma yana qofar gida yana jira in fito ya maidani,don yau ni kam kwanan garinmu zanyi" qememe taqi barinshi ya fita,tace saidai yahau sama ya sauko mata da shahida "Kiyi haquri daada ki hau,ba zata iya saukowa ba" "Ita sabon qashima taqi saukowa bare ni tsohon qashi za'ace nayi tattaki nahau,tunda goya mata baya kake tayita narkewa kaga tafiyarmu" daqyar ya lallaba daadan tahau saman,inda mubina da khadija sukayi xamansu nan falon suna kallo. Har yanzu tana zaune saman abun sallah a haka daada ta shigo,sai taji dadin zuwan daadan,tana ganin tazo a daidai,ita ta qulla komai saboda haka dole ta yiwa anwar magana ya barta ta koma bakin aikinta,ba yabi ba fallasa ta gaidata,ta amsa tana qare mata kallo,bawani sauyi data gani tattare da shahidan na mace me aure,saita tabe baki,zata fara magana shahidan ta rigata cikin sautin wanda keson fashewa da kuka "Daada ki masa magana ya barni na koma aikina,kinga tun asali da aikina ya ganni,sannan kuma baice min bazanyi ba sai jiya da nake gaya masa zan koma yace waina gama aiki,daxun nan kan ku shigo ya dauki wayata ya ballamin layina waina daina amfani dashi" rashin sani yafi dare duhu,wani kallo daadan ke mata akaikaice,sai data gama tsaf sannan tace "Yo ai ni banga wani abun azo a gani dakika tabuka ba daxai nuna kinsan ma kina da aure,daga ke harshi banga wani sauyi tattare daku ba" "Kai anwaru" ta kira sunanshi tana zare ido,ya amsa mata ta masa nuni da kusa da shahida "Xauna nan" ba musu ya zauna yana qunshe dariya,daada sarkin rigimammu,da alama akwai magana a bakinta "Tunda kuka tare ta taba maka kwanan turaka?" Ta jeho masa tambayar kanta tsaye,take qwaqwalwarsa ta gaya masa abinda take nufi,kunya ta rugo ta rarumeshi,bai taba tunanin tambayar da zata masa kenan ba,cikin hanzari yace "Daada ai...." "Aime?,idan baka da amsa to bari na amsa maka,bata taba ba,kalli qafafunta da wuyanta,idan tace ma eh to qarya take,oh la'ilaha illallahu muhammadarasulillahi sallallahu alaihi wasallam" ta debo salati tana tafa hannuwa _afwa masu karatu,kunsan yadda sabgogi ke kutso kai cikin rayuwa_🙏🏽 *Alqawarin Allah* 40 "Ni habiba naga abinda ya isheni.....rahama?!" Tayi kiranta da sunanta na ainihi,daga ita har anwar din sai sukayi tsuru tsuru suna kallon daada yadda ta dauki abun,kunya da daurewar kai duk suka cikasu "Kinason ki gama lafiya kuwa?,kinsan tsinuwar mala'iku kuwa akanki?,so kike ki shiga wuta da qafafunki?,to wallahi kishiga taitayinki karki jawowa kanki masifa ki jawo mana,rahama!" Ta sake kiran nata cikin kambama abun,yadda daadan ke magana da yadda shahida ta soma turo baki fuska a hade cikin bacin rai saiya so baiwa anwar dariya,shi tuni a nasa shekarun ya fahimci tayine tana sane donta tsorata shahidan,ta kuma sake kawo gyara a zamansun gaba daya "Yanzu daada fisabilillahi waya gaya miki wannan maganar?,shi yace miki haka?ko kuwa ni?" Daquwa ta watsa mata "Kinci gidanku,don gyatumarki a tsufana ni akwai abinda za'a boyemin?,to wallahi wallahi tun muna shaida juna ni dake ki gyara duk abinda na gane da wanda ma ban gane ba,duka kin fini sani ai basai nayi filla filla ba,kin ganni nan bana daukar sakarci,ba abu bane me wahala na miki dukan tsiya cikin gidan nan kibar ganin kina da igiya a kanki,girma kuwa ban ganshi ba bare ya hanani dakarki,aiki kuma ba zakiyishi ba haihata haihata...." "A'ah daada....ba'ace haihata haihata ba" anwar ya dakatar da daada yana boye dariyarsa wadda shahidan ta fuskanci hakan,ta sake qulewa sosai,wato ita tako ina bata da nasara,bata da rinjaye kenan? "Zatayi aiki idan tanaso....amma ba bisa qarqashin kowa ba sai qarqashina,zatayi aiki a nawa companyn kuma a office dina" ya qarashe zancan yana duban daada ba tare daya dubi shahida ba,don yasan kai tsaye cewa zatayi ba zatayi ba,amma ga mamakinsa sai yaji ta amsa da "Na amince zanyi" ta amsa masa idanunta qyar a kansa,tasan yayine don ya qureta yayi da manufa,ita kuwa tacu damarar takura masa itama tunda har ya bullo ta wannan hanyar,sai daya gama karantarta ta qwayar idanunta sannan ya girgixa kai "Well,hakan yayi,daga yau daga yanzu ma na daukeki aiki,za'a dinga kuma baki salary kamar na kowanne ma'aikaci dai dai da matsayinka,salary dinki shine salary na farko dayafi na kowanne ma'aikaci yawa duba da matakin aikin dana baki" kaita juyar tana hadiyar bacin ranta,cikin ranta ba haka taso ba "Shikenan ma,shine daidai,kaga kuna tare ko yaushe,tuwona maina,yamafi tsari" daada ta fada tana ware hannaye,daga haka daadan ta miqe bayan ta sake kwakkwafar shahidan,ba yadda anwar baiyi ta zauna ba tace sam,daqyar shahida ta iyayi mata a sauka lafiya,ya fita rakata. Cikin kwanakin hakanan shahidan naji na gani ta zauna saman nashi,saidai kwana uku rak tayi wanda ta jita kaman akan wuta take,a falo duka tayi xamanta,sai shima ya shareta kawai ya shiga sabgarsa,randa taji dama dama a qafarta ranar ta sake tarkatawa ta koma dakinta. 🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍 A hankali take takowa zuwa bakin dining din donta samu tadan dumama cikinta,bayan ta gama shirinta tsaf kamar yadda ta saba duk lokacin da zata je office,madaidaiciyar kwalliya tayi wadda ta qawatar da ita matuqa,ta sake fidda kyawunta,kallo daya xaka mata kasan macace mai aji tako ina,wannan itace ranar farko da zata soma zuwa office din anwar da sunan ma'aikaciya. Shi dinma yana tsaye daura da teburin yana kurbar tea gami da jefa soyayyen chips a bakinsa,kacokam idanunsa nakan wata takarda dake saman teburin kusa da farantin chips dinsa,wanda ke dauke da zanen taswirar wani gini da gwamnati ta basu kwangilarsa da xasu soma yinsa cikin satin. Takun daya soma ji shi yaja hankalinsa,har yakai kofin bakinsa ya janye ba tare daya kurbi tea din ba,daga sama zuwa qasa ya qarewa kwalliyar tata kallo cikin taqaitattun daqiqa ya kauda kanshi yaci gaba da shan tea dinsa. Qarasowa tayi itama ta fara hada nata ba tare data dubeshi ba tace "Gd mrng" fuska a tsuke "Mrng" ya amsa mata a taqaice shima yana juya fasalin takardarsa ba tare daya dubeta ba,wani abu ke tsunkulin zuciyarsa,shigarta sai yaga ta bayyana ado da yawa,duk da ko ina a jikinta rufe yakr ruf ba wani abu nata daya bayyana,amma sai yake ganin kamar kallonta za'a yita yi idan suka je,dana sanin cewa tayi aiki a kamfaninsa ya kamashi,inama ace cewa kawai yayi ba zatayi aikin ba gaba daya,gashi ya ruga ya furta babu damar ya canza,yin hakan zai nuna qarantarsa ne kawai. Sai daya gama tas ya dire cup din yana cewa "Wannan shigar batayi ba,kije ki canza wata ki sameni a mota,idan kuma kika makara to cikin albashinki" daga haka ya juya ya soma takawa,ya dauki handkherchief dinsa da muqullin mota dake aje saman daya daga cikin kujerun falon,ta bishi da kallo galala baki sake harya fice,sai daya bacewa ganinta sannan ta dauke idanunta tana lumshe ido,takaici nason kamata amma tana daurewa. Yana daga xaune cikin motar,ta baqaqen gilasan da batasan yana kallonta ba ya xuba mata ido,karo na biyu kenan daya sake maidata ta sauya shiga amma shi har yau baiga wani abu na kyanta daya buya ba,bayyananniyar ajiyar zuciya ya sauke,tunda can yasan cewa haka take halittarta ce,duk kayan da zata saka suna mata kyau gami da dacewa da ita komai rashin kyau ko tsadarsa,agogon dake daura a hannunsa ya kalla,dole ya haqura ya qyaleta su tafi hakanan,zuwa yanxu ya cinye sauran lokacin da suke dashi. Tana zuwa gidan baya ta shiga,baice mata komai ba yaja motar suka fice daga gidan,suna dab da ginin kamfanin ya tsaida motar,ba tare daya juyo ya dubeta ba yace "Dawo gaba" jim tayi sai kuma ta fito don batason ma ta yawaita magana dashi. Tun daga harabar kamfanin ta karanci yadda suke ganin qima daraja da mutuncinsa,wannan karon baiyi parking inda kowa yake ba,sai dayaje gaban ginin sosai sannan ya tsaida motar suka fito,basu shiga ta gaban ginin ba saita bayanshi. Kallon office din babu abinda ya tuna mata dashi face nata office din,kusan tsari yanayi da kuma zubinsa kamar nata office din,take kewarsa ta kamata,ta lumshe idanunta sanda take zaune kan cushion din office din tana jira ya kaita nata ofishin. Abinda ya bata haushi da mamaki shine bai wuce yadda taga yayi zamansa kan tashi kujerar ba ya shiga ayyukan daya taras kan teburinsa ba,yayin da take zaune shuru bata wani aiki. Ganin sun cinye awanni biyu cur a haka ya sanyata gyara zama sannan ta dubeshi "Ban gane manufar ajeni cikin office dinka ba,ka mantane aiki nazo yi?" Sai sannan ya daga kai ya dubeta,saiya maida kan cumputer dinsa yana cewa "Na fiki sanin ai aiki kikazo yi,gaggawar me kike?,zakiga aikin naki ai" daga haka ba wanda ya sake tankawa wani,saidai sau uku tana daga kai sai taga kaman kallonta yake,daga kanta yasa ya kauda nashi kan,saidai har yanxu bata kamashi dumu dumu ba shi yasa bata tabbatarwa da ranta hakanne ba. Minti talatin bayan nan yace "Hadamin coffee,ki bude can ki ciromin cake guda uku" duk yayi maganar ne ba tare daya dubeta ba,karon farko daya fara bata umarni irin haka tunda sukayi aure,saita miqe din tayi yadda yace ta dawo ta zauna. Ba'a jima ba sosai ya sake cewa ta dauko mishi ruwa,ta dauko ta aje masa saman table din,saiya daga kansa ya kalleta sannan ya maida kan computer dinsa yaci gaba da aikinsa,awa biyu tsakani yace ta dauko mishi lemo a fridge,idanunta ta juya cikin nuna qosawa,ta sauke numfashi sannan taje ta bude ta dauko masa ta aje "Ba wannan kalar nakeso ba,ki duba akwai wani daban shi zaki dauko min" hadiyewa tayi ta juya din ta maida ta dauko masa ta aje,saiya dubeta ya kauda kai "Waishin haka ake bawa mutum abu,a dire masa kaman dutse,baza'a bude masa ba bare a zuba masa?" Hannayenta ta goya a qirjinta ta zuba masa ido "Wai na tambayeka?,aiki nazo yiwa kamfani ko kai nazo yiwa aiki?" A nutse ya dubeta sannan ya ture cumputer din gefe kadan ya hada yatsunsa cikin na juna "Bakisan cewa nine kamfanin ba gaba daya?" Ido ta fiddo alamun bata gane ba,girarsa ya daga mata "Eh,aikin kamfani xakiyi,kuma nine kamfanin gaba daya,babu aikin dayafi nawa aikin,wannan aikin shine aikinki a office dina,zan biyaki albashi kamar kowa albashinma daya fi na kowanne ma'aikaci,ba shikenan ba?" Idanu kawai ta zuba masa tana kallonshi yana fidda qaramin murmushi,tsantsar raina mata wayon da yayi kawai ya isheta bacin rai,saita juya kawai ba tare data tanka masa ba ta nufi qofar fita. Gabanta yasha ya tsate hanya "Ina zaki?,lokacin tashi baiyi ba madam" "Aikinne na fasa bazanyi ba gaba daya" duka kafadunsa ya daga,hakan ya masa shima,don baisan ta yaya zai dinga barin mutane na shiga masa office ba alhali tana ciki "Fine and good....saiki jira sai lokacin tashi yayi saimu wuce gida" daga haka ya juya zuwa wajen wayarsa da tunda suka fara taqaddamar ta soma ringing,daga wayar yayi yana dubawa,wannan shine kira na dari da biyu daya samu da lambar daga farkon satin xuwa yau,tunda ya daga yaji muryar nafisa bai sake daga wayar ba,don baisan me kuma zata ce masa ba,me yayi saura tsakaninsu?. Wayar ta wurgar a gefanta ta fada saman kujera tana yamutsa gashinta,sam ta kasa jurewa da rashin anwar kamar yadda mima ta shawarceta ta jira sai zuwa wani lokaci da ita miman ke shirya mata,ta rasa ta yaya zata iya jurewa,daga qarshe dole tabi zabin ranta ta soma neman khalipha baji babu gani,tana neman hanyar da zata gyara kurenta,kullum ranta soyuwa take ta gaza sukuni idan ta tuna yanzu haka fa yana can suna rayuwarsu shida shahidan?,me yasa kishi ya rufe mata ido haka ta tauyi rayuwarta?,ta yaudari kanta akan ba zata iya aurenshi ba?,bayan tasan cewa ka ta kawai ta yiwa qarya,ta ina zata soma gyara wannan babban kuskuren data tagka,tasan cewa abune ba mai sauqi ba musamman idan ta tuna da yadda ta samu soyayyarshi a baya,saidai koma meye tanajin zata jure harsai haqarta ta cimma ruwa,sai taga abinda ya turewa buzu nadi,zata aje mima a gefe wannan karon,zatayi yaqi ta samawa zuciyarta abinda takeso kota yayane ma,idan yaso ta nemi miman daga baya su dora daga inda suka tsaya. Dirowa tayi daga saman gadonta ta shiga bandaki ta dauraye fuskarta sannan ta yafa qaramin mayafi saman kanta ta fito. Dakin mahaifiyarta ta wuce,ta sameta zaune tana waya,saita samu waje tana jiranta garta kammala,kusan tunda abun ya faru ta sake dauke mata wuta,a baya ta sani amma ta nuna kamar abin bai dameta ba,tunda tana tsammanin abinda ta aikata shine dai dai "Mommy,zuwa nayi na baki haquri" dubanta tayi sannan tace "Akanme?" Shuru tadanyi sannan daga bisani kanta a qasa tace "Nasan na bata muku kan qin auren anwar da nayi,amma a sannan idanuna ya rufe,don Allah momy kuyi haquri,ki tayani baiwa daddy haquri" tabe baki mommyn tayi tana miqewa "Aike za'a baiwa haquri,name zaki bamu haquri tunda kin aikata dai dai,rayuwarkice fa kuma kika zaba mata abinda kike ganin yafi davewa da ita" daga haka mummyn ta bude qofar dakin nata ta fice,da kallo ta bita kafin daga bisani ta janye idanunta tana sauke ajiyar zuciya,lallai aikine ba qaramiba a gananta kafin ta soma shan kan iyayenta,wanda sune tsaninta na nasararta Wajen anwar,saita miqe kawai tabi bayan mummyn,sai inda qarfinta ya qare kam. Lokacin sallar azahar taga ya sanya rigarshi ya fita,hakanan ta miqe itama ta shiga bandakinsa dake nan cikin office din ta shiga tayi alwala tazo ta tada sallah kan abun sallarsa dake cikin office din. Bai wani jima ba da yawa ya dawo dauke da takeaway,ya aje mata nata ya bude nashi ya wanke hannunsa ya soma ci,ta gefan ido take satar kallonsa,wato har yau halinshi nacin abinci da hannu dai yana nan. Ranar haka suka wuni har lokacin tashi,yana aikinsa tana zaune waje daya,saidai sam taqi zama saitin da zata ga fuskarshi koshi yaga tata,tayi danasanin karbar tayin aikinsa da biyoshi kamfanin datayi yafi sau shurin masaki,kome za'ayi kam ba zata taba iya aiki dashi ba,ta gwammace tayita zaman gidan akan zamansu qarqashin inuwa daya,suna musayar numfashi daya kusa da juna sosai har kamar haka,ta saurari muryarsa data wulaqantata wulaqancin da har yau yaqi gushewa yabar zuciyarta,duk sanda ta nutsa duniyar tunani saita tuna kalamansa da har yau bataji kalaman da suka yiwa kunnuwanta muni kamarsu ba. 🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍 Qarfe shida da minti ashirin da biyar na yammaci ya shigo gidan. ,yana zaune a falon yana sauke gajiyar daya tarawa kansa yau,ji yake kaman bazai iya hawa samanshi ba,da ido yake bin kowanne sashe na falon da kallo,ko ina fes yake ba alamun datti ko qura,hakanan yana fitar da sassanyan qamshi mai ratsa zuciya,amma saika rantse ba wani dan adam cikin gidan,sai qarar na'urori kawai dake fita kadan kadan,ya janye idanunshi kenan yana shirin miqewa yaganta tana fitowa,sanye take da doguwar rigar atamfa mai gajeran hannu,wadda tafitar da shape dinta sosai,kama dafa damammen cikinta,qirjinta da yake das cikakku,zuwa mazaunanta da suka dace da qirar jikinta,kanta babu kallabi sai gashinta dake daure waje daya,tayi kyau kamar wata 'yar tsana,fatarta ta sake fresh na zama waje daya,da alama ta fito daukan wani abune,suna hada idanu tayi turus kamar zata juya,sai kuma ta maze taci gaba da takowa,dab da zata giftashi tace "Sannu da zuwa" ciki ciki kamar wadda aka turawa tsumma a baki,wanda banda kunnuwansa dake dukka wajen ba bazai iya jin me tace ba,hakanan yaji yana da sha'awar ya takaleta,kwana biyu da bai ganta ba saiyaga kaman ya jima bai ganta din ba,saboda haka ya hade rai qyam sannan yace "Zonan" yadda ya kirata cikin gadara da bata haushi,amma saita tuna koma meye itace a qasanshi,saboda haka ta sassauta ranta ta tako inda yake zaune ta tsaya gefanshi,saiya daga kai yana kallonta "Me haka?,zaki samin ciwon kai rage tsahonki" dubansa tayi sosai kaman zata tanka saita shareshi,ta zauna hannun kujerar da take daura dashi,samun kanshi yayi da qare mata kallo,idanunsa suka tsaya kan qirjinta kamar wani mayen qarfe ke janshi,idanu ta zaro data fuskanci inda yake kalla,saita goye hannayenta a wajen abinda ya fargar dashi cewa kallonshi ya zarme da yawa,saiya maze yana sake hada rai "Haka kike zama dama idan bana nan?" Ya jeho mata tambayar,mamaki ya kamata,ta kasa gane me yake cewa? "Kamar yaya?,ban gane ba?" Ta tambayeshi itama tana kallonshi bayan ta kalli kanta "Wannan shigar gaskiya bata dace ba" mamaki ya sake kamata "Waini da waye cikin gidan?"ya gane sam maganarsa bata da makama saboda haka yace "tunda haka kika zaba shikenan,bani ruwa nasha tunda baki iyaba har sai mutum ya roqa" ta gane sarai neman abun fada yake,saboda haka ta miqe kawai ba tare datace masa komai ba ta wuce kitchen din,saiya waiwaya ya bita da kallo,karon farko da yaji wani abu yana ratsashi tun daga tsakiyar kansa zuwa tafin qafafunsa,ya lumshe ido yana ambaton sunan Allah,baqon feelings yakeji sosai wanda har yaso danne gajiyar da yakeji. Idanunsa ya bude sanda take aje masa ruwan,idanunsa kuwa sukayi kyakkyawan gani,saiyaji kaman yakai hannunsa kamar ana janshi ne,ya samu da qyar yayi controlling kansa sanda qamshin turarenta ya soma rarraba mishi hankali,yana kallon tasoma takawa don barin wajen ya kasa magana sai binta da idanu,da qyar yasamu cewa "Nace ki tafi ne?" Waiwayowa tayi tana kallonshi fuska a turbune "Zo nan" ya sake fada,ba yadda ta iya don batason ta saba da dabi'ar musu da gardama data soma masa ya zame mata jiki "Zubamin" ya fada yana nuna mata ruwan,haka ta sake duqawa tana zuba masa,ta gama ya amsa yana nuna mata wata leda daya shigo da ita "Kaimin dakina" ya dora qafarsa daya kan daya ya soma shan ruwan,baki take turowa ciki ciki,ya soma kaita bango,ta dauki jakar ta soma hawa saman,nan ma da kallo ya bita yadda mazaunanta ke juyawa kai kace tana sane takeyin hakan,ajiyar zuciya ya sauke bayan ta bacewa ganinsa,ya dire cup din da hanzari ya miqe ya rufa mata baya. *Alqawarin Allah* 41 _ku ziyarci tasharmu ta youtube don sauraren tsofaffi dama sabbabin littafanmu,da sababbin ma da bakusan dasu ba wadanda zasu fara zuwa muku ta tashar nan gaba kadan da ixinin ubangiji_ https://youtu.be/-tPtW9YtNpU Tana shirin fita yana shirin shigowa sukayi kacibus,tadanja da baya tana neman hanyar wucewa "Waye ya miki karatun yadda ake zama da mijine?" Yayi tambayar yana dubanta,dagowa tayi cikin mamaki ta kalleshi,saiya dage mata gira guda daya "Eh,gaskiya bata iya komai ba kaman yadda na lura,saboda bangani a qasa ba" ya fada yana takowa zuwa inda take tsaye,yanajin bazai iya barinta yadda ta rikitashi taci bulus ba ba tare da shima yau yadan taba koda fatarta ba yaji yadda akeji,baya ta soma ja tana kallonshi,bata fahimci me yake shirin aikatawa ba saida ya kusa qureta jikin madubin dakin,idanunta cike fal da tsoron da takeson boyewa tace "Meye haka kakeyi?" "Abinda kika gani" ya bata amsa bai fasa nufota ba,cikin dan tsoro tace "Karka tabani" cak ya tsaya yana kallonta "Tunda kwartone ni?" Ya amsa mata ta sigar tambaya,bai kuma bi ta kanta ba yaci gaba da nufarta,don baijin zai iya haqura din shima bai d'aana ba,ko ina ta kalla ya riga daya kangeta,a haka ya hade gap din dake tsakaninsu,ya zagaya hannunsa ta qugunta ya janyota sosai cikin jikinsa,fuskarsa ya sauko da ita dokin wuyanta yana kai hancinsa,ta soma juye juye tana son ta qwace daga hannunshi "Banaso,meye haka,ka sakeni" "Ni kuma inaso" ya fada yana fidda numfashi saboda yadda abun ya soma masa dadi,wayarsa dake saman mudubin ta dauki haske da qara,wanda hakan yaja hankalinsu gaba dayansu,a tare idanunsu ya sauka a tare kan screen din wayar,sunan NAFISA ya bayyana saman screen din,dauke idanunshi yayi yaci gaba da abinda yake,hakanan taji wani abu yadan sosa mata rai kadan,amma saita dauka yadda ya tarfata ne yake yadda yaso da ita,sosai yake shinshinar kowanne lungu da saqo na jikinta yana fitar da numfashi,ko ina jikin shahidan rawa yake itama,karon farko da irin hakan ya soma faruwa da ita a rayuwarta,tsoro da haushin anwar din ya cikata ganin da gaske yake yau ba wasa bane,kaman wanda aka tsikara ya saketa da sauri gami da turata baya shima yaja baya da hanzari yana zama gefan gado ya dafe kanshi dayaji ya sara masa lokaci daya "Ya Allah" ya furta yana ci gaba da dafe kan nashi,hanqota kawai yayi sanda take rungume jikin wani,bayaso ire iren wadan nan tunanukan su dinga dawo masa kwanya,saboda haka saiya dinga maimaita "Hasbunallahu wani'imal wakil" tana zuge zif din rigarta tana mamakin yadda lokaci guda yasaketa haka,yanayin da taga ya shiga din,saidai itama ba'a nutse take ba saboda haka tana gama jan zip din nata ta soma tattaki cikin hanzari zata fice "Dawo nan!" Ya fada cikin kakkausar murya,ba musu tadawo din ta tsaya cak saidai bata dubeshi ba,fuskarshi a dinke take tsaf babu fara'a ta sisin kwabo "Shiga ki hadamin ruwan wanka" jikinta a mace take takawa zuwa bandakin,ta hada mishin ta fito ta shaida masa,saiya miqe kawai ya zari towel "Karki tafi saina fito" ya fada yana shigewa cikin bandakin,tsayawa tayi cak,ta jingina da madubi tanajin yadda qafafunta suka mutu,jikinta babu qwari sam,ta soma tuna yadda taji daxun da yadda abun ya kasance,saita lumshe idanunta tana tuns komai,qamshin jikinsa daya goga mata yana zarya cikin hancinta har zuwa qwaqwalwarta,kasala na sake saukar mata,qarar da wayar tashi ta sakeyi ita ta katse mata duk tunaninta ta sanyata bude ido,bata tabata ba sai dubanta data kai kan wayar,sunan nafisa ne dai again,saita ci gaba da kallon wayar harta katse,tana shirin dauke idanun nata wani kiran ya sake shigowa. Ci gaba tayi da kallon wayar har kiran ya sake katsewa,duk kiran daya shigo din kan idanunta ya dinga shigowa yana katsewa,wanda a qalla kafin ya fito din an kira yakai sau goma sha biyar,kuma ba'a fasa kiran ba,bata dauke idonta ba itama saida taji ya soma qoqarin bude qofar bandakin sannan ta kauda kai tana tunanin wace wannan haka?,meye ya faru take jero kira haka ba qaqqautawa?,bakin mudubin ya tako saita matsa gefe tana sake dauke kanta wani sashen,towel ne daure a jikinsa iya qugu,sai wani daya ratayo wanda duka duka bai gama rufe jikinsa ba gaba daya,wani nauyi da bata taba jin irinsa ba ya saukar mata,gabanta ya dunga faduwa sosai,ta sake dauke kanta yadda ko inuwarsa ba zata gani ba,baice mata komai ba ya daga wayar ya duba mai kiran,duka nafisan ce,cikin zuciyarsa yaja tsaki yana tambayar kanshi me zata masa?,ya aje wayar yana cewa "Kije ki shirya,zamuje duba anty usaina batajin dadi" waiwayowa tayi cikin faduwar gaba da fargaba,bala'in kunya da nauyin anty usainan takeji,yanzu kuma zai kaita gidanta?,saidai a kamatance ma bai kamata ta musa masa ba kodon karamci irin na anty usainan da qaunar da take gwada mata. Tana shiryawa amma kiran wayar ya tsaya mata arai,ta rasa dalili,kiran sai takega kamar yayi yawa,a haka ta gama shiryawa tsaf cikin wani lace,ta yane kanta da yalwataccen mayafin daya dace da shigar tata,saidata dubawa anty usainan abinda zata kai mata ta saka cikin jakar hannunta sannan ta fito,a falon qasa suka hadu,saita tsinci kanta da satar kallonsa duk da bata shiryawa hakan ba,anwar badai wanka ba,tunda can tun lokacin da bashi da komai mutum ne mai tsafta da kwalliya ma gaba daya,yayi kyau cikin yadin kufta na maza,dubanta yayi sosai wannan karon kanshi tsaye babu boye boye "Wannan qamshin yayi yawa" yana takowa zuwa gabanta,tuna abin daxu daya mata tayi saitayi hanzarin jaa da baya kada ya maimaita,don har yanzu jikinta a mace yake,tsayawa yayi cak saiyayi murmushi cikin ranshi,ya gane me take gujewa,itakam ba wani turare ta saka ba bayan na jikinta,juyawa yayi ya fice ta mara masa baya. Zata shiga baya kamar yadda ta saba masa taji qofar taqi buduwa,haka tayita qoqarinta na budewar amma taqi da alama lock ya saka,dole ta dawo gaba ta bude ta shiga. Horn biyu maigadin ya dage masa gate din ya saka motar,ya qaraso suka gaisa da anwar din sanda yake fitowa daga motar,suka soma takawa zuwa cikin gidan,suna gab da valcony din da zata sadasu da qofar falon tana fitowa cikin doguwar riga da yalolon mayafi,hada idanu sukayi da anwar,saita kasa dauke idanunta daga kanshi,gabanta na faduwa qaunarshi na sake ratsa zuciyarta fiye dada,sai taga kaman an qara masa kyau da haske,ga wani kwarjini na musamman da gake fitarwa,shi ya soma janye nashi idanun ya soma yin gaba,suka hada idanu da shahida dake bayanshi,kowacce nata idon cikin na 'yar uwarta,sake kallon shahidan nafisa take sama da qasa,kishinta na ratsata,ta sake kyau da aji fiye da daa,duk da cewa ba zata taba mance fuskarba,duk da cewa ta ganeta amma saita janye idonta daga kanta ta rufawa anwar baya,tana jin wani abu na sukar zuciyarta,da kallo tabi bayan shahidan har suka wuce,sannan taja qwafa ta wuce,tanajin a zuciyarta wannan karan kam ba zatabi shawarar mima ba,zuciyarta takai maqurar da bazata iya jurewa ba. Yana gaba tana binsa a baya cike da kunya har cikin babban falon anty usaina,gaba daya yaran suke miqe suna musu sannu da zuwa,sa'ida ta soma tare shahida ta rungumeta "Oyoyo anty,uncle,amma bakacemin zakuzo da anty ba yau" "To ai gata kin ganmu" ya bata amsa yana zama saman daya daga cikin kujerun,yayin da maibin sa'idan ta haura sama donta shaidawa anty usainan zuwan sun tana cewa "Yanxu ma tahau saman,anty nafisa ce tazo dubata" cikin shi da shahidan ba wanda yace komai ba,itakam nunawa ma tayi kaman bata santa ba bare ta ganeta,sunata taba hira da sa'idan,yayin da shi kuma ya shiga tunanin me nafisan tazoyi gidan anty usainan?. Dawowa tayi ta shaida musu tace su hau saman,shine dai a gaba tana binsa a baya har suka bayyana wani falon dake daman,anty usainan na zaune qasan carfet suka shiga da sallama,fuskar anty usaina wadace da fara'a takewa shahidan lale kota anwar ma bata biba,a kunyace ta zauna gefan anty usainan tana jin anwar na tambayar antyn fitilun harabar gidan da wasu suka mutu "Ka qyalesu hakanan tunda dai gidan da haske ai shikenan" saita sake maida kanta ga shahida wanda kanta ke sunkuye a qasa,gaidata tayi a kunyace anty usainan ta amsa cikin kulawa,Shahidan ta mata sannu da jiki ta amsata "Aina warware alhmdlh,shine sai daya tattagoki" qaramin murmushi ta saki kanta a qasa cike da jin kunya da nauyinta,daidai lokacin sa'ida ta shigo dauke da tray wanda ta cikashi da kayan ciye ciye,kai tsaye ta aje gaban shahidan,ta durqusa tana zuba mata duk abinda ke cikin farantin,qasa qasa shahidan ke kallonta tana dariya idanu a waje yadda su anty usaina bazasujiba tace "Sa'idah,wannan duka?,aisai cikin antyn taki ya fashe" "A'ah anty kici wallahi,yauke baquwarmuce ta musamman" "Mu kuma aisai a koramu ko?,yauni aka yiwa danwaken zagaye saboda kin ganta ko?" Tana dariya sa'idan ta daga kai daga shiryawa shahida cake da take cikin plate ta kalleshi cikin dariya "Ba haka bane uncle nina isa?,kawaidai nasan ka gayamin cewa kaida anty abu guda ne,kaga idan na bata kamar kai na baiwa" murmushi yayi yana daga mata hannu yana satar kallon shahidan,shi sam ya mance daya gaya mata hakan,ya fada ne a gaban anty usaina don sake kwantar mata da hankali da amintar mata tunaninta,saidai ya manta sa'idan bata mantuwa,ta kammala zubawa shahida komai ta miqe tana duban anty usaina "Na gama ummi" "Shikenan,idan kin sauka ki shiga kitchen ki tafasa min maganin nan,ki samu botiki mai murfi ki xuba a ciki kidan sabashi yasha iska kafin na sauko shi xansha" "Tohm" tajuya ta dubi shahida "Anty kici sosai don Allah ki cinye duka" murmushi kawai tayi tana dubanta,sosai yarinyar take sonta da burgeta. Inda shahidan ke zaune ya sauko,ya zauna sosai a gabanta,farantin dake tsakiyarsu ne kawai ya raba tsakaninsu,idanunsu suka shiga cikin na jina,kowanne ya zare nashi idon daga cikin na dan uwanshi yana jin yarrr cikin jikinsa saboda kusancin da sukayi da juna yayi yawa,saiya sanya hannu ya dauki kofin gabanta yana cewa "Tunda niba wanda yayimin tayi bari nayiwa kaina" "A'ah..ban yarda da wannan juyin mallakar ba,aje mata,kaidin baqo ne da bazaka dauka da kanka ba?" Murmushi ya saki yana tsaida kofin da yayi nufin kaiwa bakinsa "To ai anty itama ba zata sha ba idan bansha ba" ya qarshe maganar yana waiwayawa ya dubi shahidan yana kashe mata ido,sadda kanta qasa tayi saboda wani abu dataji ya saukar mata saman zuciyarta mau nauyi,yakai bakinsa ya kurba lemon ya miqa mata suna magana da anty usaina,qin amsa tayi har ya gama maganar ya juyo yana dubanta "Karbi mana,kosai na baki da kaina?" Harara ta cilla masa a fakaice ta saka hannu takarba ganin yana kai kofin bakinta,ya xuba mata ido sanda takai kofin nata bakin,tana sane ta juya daga wajen daya sha ta sauya gurbi,murmushin mugunta ya saki ya waiwaya wajen anty usaina yana tambayarta "Me yarinyarnan tazoyi gidan nan?,na ganta sanda muke shigowa" "Nafisa?....waitaji banji dadiba shine tazo dubani,amma tazomin da wata magana da nace saikazo naji ta bakinka tukunna" ta fada tana dan dubam shahida,batason yin maganar a gabanta,amma kuma tana ganin yin maganar a gabantan kamar xai bada wani alfanu game da kawo gyara kan yanayin mu'amalarsu da anwar,don har yanzu bata gamsu da yanayin zaman nasu ba,tana ganin yadda suke abu kaman baqin juna "Tace na baka haquri akan kuskuren datayi a baya,tana son idan da hali ka dawo ka....." Daga kai anty usaina tayi tana duban shahida wadda ta miqe tsaye "A'ah,ki zamanki shahida mana?"murmushi tadan saki,don tunda aka ambaci sunan nafisa zuciyarta ta gaya mata ba kowa bace illa wannan wadda suka gani dai sanda zasu fita,fuskar da anwar ya aiko mata da ita cikin envalope din data baiwa suna da baqin saqo,hotunan da har yau ta kasa rabuwa dasu dukda yadda suke qona ruhi da zuciyarta duk sanda ta tuna dasu,ko kuma duk lokacin data kallo gefan da suke aje "Zan saukane wajensu sa'ida" "To shikenan,nima ganinan zuwa,ai bamu gama hirar ba" "Toh anty" ta fada ta juya tana fice daga dakin,anty usaina ta bita da kallo farinciki na ratsa zuciyarta,tanason karanto wani abu game da shahidan,saita maida dubanta ga anwar,wannan karon shiya soma magana "Don Allah anty karki shiga maganar nan,an riga da an wuce wajen tuni,na godewa Allah da bani na soma gudunta ba bare aga butulcina,ta ruga data gayamin manufarta tun rannan,kuma kullum kwanan duniya saita aikomin da saqo kan hakan" ajiyar zuciya anty usaina ta saki,itakam a duniya yanzu ba abinda ya rage mata illa taga kan shahida da anwar din ya hadu kawai,ta tabbatar idan hakan ta faru babu kuma sauran wata matsala "Shikenan Allah ya zaba abinda yafi alkhairi,nikam yanzu bani da burin daya wuce naga kanku ya hadu yadda ya kamata kaida shahida,yarinyar tana da nagarta anwar,kayi qoqarin gyara zamanku,gashi kuna qoqarin cinye wata na biyu amma a karatuna banga hadin kan da nake buqata ba,ajiyar zuciya ya saki yana dan kashingida kadan,cikin zuciyarsa yana fadin antyn ba zata gane ba,shi kadai yasan me yakeji kullum kwanan duniya,a raye yake amma zuciyarsa matatta ce,ya gaza gano dalilin daya sanya shahidan aikata dukkan abinda ta aikata a rayuwarta,meye sila?,meya janyo haka?. Shahida na qasa suna hirarsu dasu sa'ida anty usaina ta koro anwar qasan takuma ce ya turo mata shahidan,sanda taje kusan karatun xama da miji tayi mata sosai ba kunya ko nauyi tsakaninsu "Shahida...kiyi haquri da yadda rayuwar aurenku taxo muku ahagunce kuma a kaikace,farinciki gamida walwalar gida a hannun matar gida take,tana da ikon maida gidanta aljannar duniya ko kuma akasin haka,duk yadda namiji keda taurin kai,taurin zuciya da kuma kafiya abune mai sauqi matarsa ta canzashi matuqar tayi karatu mai yawa akanshi da halayyarshi,kiyi haquri kiyi qoqarin canza gidanki,ki zama mace sosai,kiyi amfani da hikima da basirarki,kaf dinmu makusantanki dana anwar ba wanda yake fata ko burin rabuwarki dashi,kinga kenan babu ranar da zaku rabun,tome zayasa abinda babu ranar yankewarsa maimakon ka gyarashi kaji dadinsa ka amfaneshi saika zabi dawwama cikin karkatacciyar rayuwa maras dadi?,duk lokacin da rayuwar auratayya ta kacame ta lalace babu wanda yafi cutuwa a ciki,yafi quntata,yafi zama cikin wahala baqinciki da bacin rai irin MACE,namiji nada tarin hanyoyin da zai debewa kansa kewa ya ragewa kansa baqinciki da bacin rai,ba kamar ke mace ba da taki damar qwaya dayace wannan mijin da kike aure,kome anwar ya miki,duk da bansan girman cutarwar da yayi miki ba abaya,ina mai qasaqantar da kaina da roqa masa alfarmar ki yafe masa,ki tashi tsaye ki gyara gidanki,ki masa kyautatawar da girmanta zaisa yayi nadama yayi danasani,ya kuma ji kunyar aikata miki dukkan abinda ya aikata mikin,ita mace tana da wannan power,zuciyar namiji a wajenta ba komai bace horewa ce ta ubangiji,nasan zaki iya din ina kyautata miki wannan zaton,ina roqar alfarma zakiyimin shahida?"cikin jin kunya da nauyi gamida gasgata kalaman anty usaina ta gyada kai "Xan miki anty,zanyi in sha Allahu" ajiyar zuciya ta saki tana lumshe idanu "Na gode qwarai,amma kafin sannan,ki nutsu ki mu'amalanceshi ta yanayi da sigar da yake mu'amalantarki gudun kadda kisha wahala,ina fatan kin fahimceni?" Kai ta gyada mata alamun ta gane,hakan ya yiwa anty usaina dadi sosai,da kanta ta bude cupboard dinta ta ciro mata wasu rigunan bacci masu shegen kyau da sulbi guda shida,ta hada mata da turarukan bedroom suma guda hudu masu kyau da tsada,ta amsa tayi mata godiya sosai,saita danyi jim,anty usainam ta fuskanci akwai maganar da takesonyi,saboda haka tace da ita ta fada kada taji nauyi ko kunya "Anty aron sa'ida zaki bani don Allah tayimin ko sati guda ne" baki anty usaina ta bude "Keda zaki shiga yaqarmin tunanin dan uwa na hadaki da sa'ida ta hana ruwa gudu?" Kunya ta sata sadda kai tana dariya "Shikenan,amma ba zata wuce kwana uku ba" "Don Allah anty ki barta tayi sati" daqyar ta yadda da hakan,sa'ida murna kaman me ta hada kayanta ta bisu. *11:30 pm* Doguwar rigar bacci ce a jikinta mai sulbi wadda takai har qasa da dogon hannu,sai baby hijab data sanya wanda iyakarsa saman kafadunta,duk motsin datayi qamshi ne yake tashi harta iso matatattakalar qarshe wadda daga ita sai qaramar baranda da zata sadaka da falon samanshi,cak ta tsaya tana ajiyar numfashi,shida kanshi ya mata magana kafin su shigo gidan kanta taho samanshi saboda sa'ida kada ta karanci yanayin zamansu,baiso anty usaina ta fahimci komai,baisan yayi sara bane kan gaba,ta riga data gama shirinta dukda ciwo da takeji a qirjinta da nauyin alqawarin data dauka,anya zata iya saukewa?,takewa kanta wannan tambayar,duk sanda fuskar nafisa ta gilma mata a idanu,yadda ya cillota da girman kalaman daya sossoka mata saitaga gaba daya yayi mata baqi a ido,koren shaidan tayi sannan tayi bismillah taci gaba da takawa ta tura qofar falon ta shiga. *Alqawarin Allah* 43 Wani irin murdawa mararshi tayi wanda hakan ya sanyashi duqawa riqe da cikinsa,ya tako a haka a hankali zuwa gefan gadon,idanu ta zaro jikinta ya dauki rawa,ta tako ta tsaya daga bayanshi amma ta kasa cewa komai,da qyar cikin rawar murya tace "Sannu,baka da lafiya" kallonta kawai da yayi da qwayar idanunsa da suka kada zuwa launin jaa ya tabbatar mata da bashi da lafiyar kenan,ta juya zata futa da niyyar ta kira anty usaina ta shaida mata,saiya dakatar da ita "Jirani na shirya,zanje naga likita". Hannu likitan ya saka ya cire abun abun awon jini daya sanya a dantsen anwar din yana kallonshi "kamar yadda na tsammata ne,jininka yahau sosai,kamarma yahau fiye da kowanne lokaci,gaskiya anwar bazan boye maka ba,wani lokaci sai naga kamar kana wasa da lafiyarka ne,bansan meya hanaka kwantar da hankalinka ba ka samu jinin nan ya sauka gaba daya,sai yayi kaman ya sauka saiya sake hawa,bansan daga inda matsalar take ba" murmushin qarfin hali yasaki,ya lumshe idanunsa kana ya bude "Share kawai khalid" likitan mai sunan khalid ya waiwaya ya dubi shahida wadda ke zaune wata kujerar daban,hannayenta rungume a qirjinta,ta zubawa anwar ido ba tare da yasani ba,kallon mamaki take masa na bayanan da taji daga bakin dr khalid,wanne irin hawan jini?,yaushe anwar din yasamu hawan jini?,iya saninta dashi kaf tarayyarsu anwar baida hawan jinin,yaushe ya gamu da wannan matsalar? "Madam" ya kirata wanda hakan yaja hankalinta zuwa kanshi "Bayan hawan jini gaskiya abokina na buqatar kulawa,don Allah ki kulamana dashi,nasan kinfi kowa sanin mutumin kirki ne,lalurarshi ba zata yiwa mutane da yawa dadi ba" kai ta gyada likitan ya miqe yana cewa "Ruwa naso indan saka maka,amma nasan hali ba zaka taba yarda ka zauna ba,bari na rubuta maka wasu magungunan na bayar a karbo maka,madam sai a kula da bashi akan lokaci" kai ta sake gyadawa tana duban anwar din,saita kauda kai sanda taga ya waiwayo suna shirin hada idanu. Suna tafe a hanya motar ta dauki shuru,kowa da abinda yake saqawa cikin zuciyarsa,tambayar ta yiwa shahida tsaye a rai na hawan jinin anwar,yayin data gefan anwar din maganganun dr khalil suka dinga kai kawo a qwaqwalwarsa,tabbas ba shakka shine mutum na farko da zaifi kowa son rabuwa da cutar,zaifi kowa son ganin ya cire kome cikin ransa,zaiso ace ya goge kome dake damunsa,amma saidai shi kansa yasan hakan bame yiwuwa bane,shahida ce,idan da wata macen ce daban ha tabbatar da tuni ya cireta daga rayuwarshi irin fitar da mai rai kanyi daga duniya wanda har abadan bazai dawo cikinta ba,amma akan shahidam hakan ya gaza,ya sani cewa koda zai fada a baki koda zai nuna a aikace shahidan bata dameshi ba yayiwa kanshi qarya,karon farko dayakejin inama inama,inama ace bai kalli hotunan ba,inama ace ranar baije gidansu zance ba bare yaga abinda ya gani,inama ace shahidan bata fada halin data fada ba a baya,da wannan tunanin suka isa gida,da kanshi wannan karon yasha maganin sannan ya shiga bedroom dinsa ya kwanta kozai samu relief. 🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍 A kasalance yake shiryawa cikin farar shadda,riga iya gwiwa mai gajeran hannu da dogon wando,kana ganin yadda yake shiryawar kasan cewa ba wani dadin jikinsa yake ji sosai ba,yana daura agogon hannunshi ta turo qofar dakin da sallama,hannunta riqe wata butar shayi me kyau,da mamaki take dan dubanshi saidai bata tanka ba ta aje butar "Ya jikin?" Ta tambaya a taqaice,daga kai yayi ya dubeta yadda ta juya baya ya maida kansa yaci gaba da daura agogonsa sannan yace "Alhamdulillah" tadanyi taku biyu sannan ta sake tsaiwa,ya fuskanci akwai magana a bakinta saiya amsa "Tun jiya akwai alqawari. Haduwarmu dashi,jiya banjin dadi,so yau nakeson nacika" yana gama fadi ta taka ta sauka daga saman,dama tanson jin fitar zaiyi amma tanajin nauyin tambaya. Tun jiya take zuba idanun ganinsa,ta kasa zaune ta kasa tsaye,tun bakwai na dare take zirya tsakanin harabar gidan,falon abbansu zuwa nasu falon da dakinta ma gaba daya,ganin goma na dare tayi hankalinta yayi mummunan tashi,Allah yasa abba bai gane ba,Allah yasa anwar bai kira abba ba ya sanar masa yaji yana nemansa ba abba kuma yace bashi bane,daga daren zuwa safiyar ranar ji tayi kaman ta zare,duk motsin shiga da fitar mota a gidan yana kan idanunta,saida dare yayi ta tabbatar babu wani sauran wanda ka iya zuwa a wannan lokacin sannan ta haqura. Da safema haka ta dasa abun zama cike da fata da kuma buri,qarfe goma da rabi da minti takwas aka saki horn mai gadi ya doshi qofar don ya bude,gabanta wani mugun faduwa yake haka tamiqe tsaye tana duban qofar gidan,kusan shidewa tayi sanda taga fitowarsa daga motar,idanunta qur akanshi yana sake burgeta duk wani motsi da yayi,tana kallon aka masa iso cikin falon daddyn,cikin wani mugun hanzari ta diba tayi cikin gida kai tsaye ta wuce dakinta,hijabi ta lalubo ta zira saman kanta sannanta sake fitowa da hanzari don kada lokaci ya qwace mata. Sanda ta shiga mummynta na tare da daddyn,hakan yayi masifar yi mata dadi,sait tayi qoqarin daidaita nutsuwarta ta taka zuwa cikin falon da sallama. Dukkaninsu suka amsa mata,ta isa gefan daddyn inda anwar ke zaune qasan carfet saboda girmamawa suna gaisawa,nan ta duqa kan duka gwiwoyinta,ta saki kuka sosai wanda ya karade ilahirin falon,duka sakin baki sukayi suna kallonta,mummy ce cikin hade rai tace "Kewai meye haka?,wanne irin shashancine wannan kawai zaki shigo kisa mutane a gaba da kuka?" Cikin muryar kuka tace "Don girman Allah mummy ku yafemin,ku yafemin,ku roqamin ya anwar shima ya yafemin" "Me ya dawo da wannan maganar data riga tawuce kuma nafi?" "Gafarar ya anwar nake nema" gaba daya kanshi ya kunce,shi sam.bai dauki abunda tayi a matsayin wata matsala ko abun bacin rai ba,tuni ya riga daya wuce wajen,tun a lokacin da abun ya faru shiya tattara komai daya shafi wannan fannin ya ajeshi a gefe,baison zancan yayi tsaho saboda haka yace "Ya riga ya wuce har abada" ranta taji yayi,wani mugun sanyi,alamun nasara na tabbata kenan a gareta,saita sake sunkuyar da kanta qasa sosai sannan tace "Bansan cewa nayi wauta ba kuma nayi kwaba saida na rabu dakai,nakai kukana ga abba da mummy amma kowannensu yaqi mara min baya ka dawo cikin rayuwata,sunce idan ka amince suna murna da hakan,saboda sunsan cewa idan sukayi maka magana ko bakaso zakace eh,gani a gabanka anwar don girman Allah inason ka sake dawowa rayuwata karo na biyu,ka yiwa iyayena dake shauqin son ganin haka alfarma wanda alkunya da kawaici yasa suka kasa gaya maka" "Ke nafi!" Abbanta ya dakatar da ita ta hanyar daka mata tsaw,a,bataji komai ba don idanunta da zuciyarta sunyi nisa wajen son ganin cikar muradi da burinta,saita daga kai ta dubi abban sannan ta sake sunkuyarwa "Abba na fadi masa gaskiyar abinda yake faruwa ne,na tabbatar da zaka iya da kaine xaka nemi ya aureni karo na biyu....anwar,ka duba wannan alkunya da kara ta iyayena gami da girman soyayyar da nake maka" baqinciki ya kama mummy na yadda sam halayen nafisan suke wadansu irin mabanbanta daban,ta kawo mata duka anwar ya dakatar da mummyn cikin sauri "Rabu dani na mata duka,baki da kunya nafisa ko kadan?,a gabanmu kice kin fasa aurensa,sannan ki dawo a gaban namu dai kice ya aureki?,wace iriyar yarinya ce ke?" Cikin kuka sosai nafisan tace "Kuskure ne mummy yanzu kuma na gane kuskuren da nayi,wallahi idan babu anwar rayuwata ba zata taba dai daita ba,mummy ku tayani bashi baki" "Ce miki akayi baida zuciya da zaki gujeshi yanzu ki dawo masa saboda rashin ta ido?,kema kinsan bazai taba yiwuwa ba" mummy ta amsa mata tana jifanta da harara,so take kawai ta samu dama ta daki bakin nafisan ya fashe ko zata samu sassauci takaicin dake cikata "Na amince zan aureta" anwar ya furta,lafazin daya girgizasu dukka su ukun,basu taba zata ba sam ko a mafarki,sunyi tsammanin bazai taba yarda ba,cikin hikima yake karantar yanayin fuskar alhj abba da munny bilkisu,ko basu fada masa ba ya gama karantar yanayin da zukatansu suka shiga,alhj abba da mummyn suna da daraja a idanunshi,ya sani cewa tsantsar kara kawaici da alkunya ne dasu,amma da qauna kowa ya sani suna matuqar qaunar nafisa,me yasa shi bazai iya musu kara ba ya auri diyar su wanda yasan shine cikon muradinsu,ba shakka da nafisan diyar wani ce da ya barta kenan har abada,amma ko a lahirama wani yana cin albarkacin wani bare nan gidan duniya. "Bazaiyiwu ba anwar,ka tashi kawai kayi tafiyarka" cewar alhj abba,don harga Allah bayason su xama sila na yiwa anwar din dole,wani tashin hankali ya saukowa nafisan,ya ga qoshi ga kuma kwanan yunwa tana shirin yi?,me yasa abban nata zaiyi mata haka?,girgixa kai anwar yayi cikin qarfin hali "A'ah abba,ba za'ayi haka ba,nafisa qanwa take a gurina idan da kara da kawaici,abinda ya wuce ya riga daya wuce tunda ta gane kuskurenta,Allah ya yafe mana gaba daya ya kuma kiyaye gaba" murna farinciki kaman ta taka rawa a gabansu,saidai yanzu ba lokacin hakan bane,sake kwantar dakai tayi sosai ta sake neman afuwa gamida nuna tsantsar nadamarta,itakam hajiya bilkisu miqewa tayi ta fice tabar falon,tana jin ciwo cikin zuciyarta sosai duk lokacin da nafisan ke roqar soyayya,ta rasa wacce irin diya Allah ya bata?,zataso ace nafisan ta auri wanda shi yake mutuwar sonta ba ita take mutuwar sonshi ba,ta rasa meye matsalarta meye damuwarta?,ba kalar saurayin da bata dashi wanda kowa neman yardarta kan ya aureta yake amma sam ita ta qwallafa rayuwarta kan anwar,eh anwar ya isa mutumin da za'aso a zama mata a gareshi,amma duka hakan a ganin mummyn xaifi kyau idan har shine yazo da kanshi ya nemi hakan. Tunaninsa ne ya dinga kasuwa kashi kashi,abinda ya faru yanxu cikin gidan alhj abban,tabbas shi shaidane kan irin son da nafisan ke masa wanda sautari hakan yakan bashi mamaki qwarai,karbar aurenta da yayi yasani shi kadaine abunda zaiwa alhj abba ya saka masa dimbin alkhairin da yayi masa da kyautatawa a rayuwa,da yadda yake kallonshi tamkar danshi,saidai ko daya zuciyarsa babu nutsuwa ko jin dadin karbar da yayi,bayajin wani daidaito ko daya kan batun nafisan,duk da agefe guda ya sani yana da buqatar kulawar mace,amma,ta yaya wata zata sanyo kai cikin rayuwar gidan alhali ga yadda take?,ta yaya zai kawo gyara?,tuninsa ya sake tafiya kan hotunan dake aje har yanzu suna yankawa gami da qona zuciyarsa duk daqiqa ko sa'a daya da zata shude,duk lokacin da idanunsa suka kai kai,yaha shahidan tsirara tare da wani sai yaji kaman mai shirin haukacewa,duk sanda ya kallo hoton yaga shahidan rungume qirjin daya daga cikin masu saida kayan maye sai yaji dama makaho ne shi,Allah ne kadai da qarfin addu'a suka sashi ya rayu har yakai bigiren da yake kai a yanzu. Sassanyar ajiyar zuciya ya saki sanda yake kashe motar shi,ya daga hannunsa ya kira maigadin,cikin girmamawa ya qaraso "Baqi indai ba 'yan uwa bane na jiki duk wanda yazo kace musa bama nan"ya qarashe maganar cikin muryar dake nuna jiki da zuciyarsa duka babu qwari "To ranka ya dade" ya wuce ya koma bakin qofa yayin da shi kuma ya fito,ya dinga takawa a hankali zuwa cikin falon. Shuru yake kaman koda yaushe,saidai ya hangi abinci a shirye saman dining,hakanan yayi sha'awar xama a falon,idonsa kan wata tasha da suke nuno fasahar zamani da qere qere,suna wani shirin kan na'ura mai qwaqwalwa,tsohon mintuna idanunsa nakan allon talabijin din,wani bayani da baqon nasu yakeyi ya dauki hankalinsa matuqa,yadda ci gaban xamani yazo da sauye sauye,yadda za'a qirqiri abu a idanunka kaga haka yake,amma da za'a sanyashi a na'ura sai kaga abun ba haka yake ba,tsahon minti ashirin yana bayanin wanda yayi matuqar daukan hankalinsa. A hankali tunaninsa ya karkata ga abunda zuciyarsa keson tuna masa tun daxun,saiya miqe da hanzari ya soma haurawa saman cikin sassarfa,bai tsaya ko inaba sai bakin safe din nashi,cikin sauri ya tsugunna,ya soma saka lambobin sirrin ya budeshi,envalope din ya ciro kaman ko yaushe ya zazzage hotunan ciki duka suka fado "Hasbunallahu wa ni'imal wakil" ya furta kaman yadda ya saba sanda yake binsu da kallo daya bayan daya,duk sanda zai gansu yakanji kaman duniyarshi sama ta kona qasa ne,kullum yanajin kamar ranar ya soma ganinsu,saiya zauna sosai zuciyarsa na fata da kuma burin samun mafita,xuciyarsa ta cika da fatan dama ace ba haka bane,dama ace ba ita bace,dama ace ba shahida bace a jiki shine bai ganin dai dai duk sanda zai kalla,saiya sake gyara zamanshi sosai,ta ina zai fara?,bashi da wani qarfin sani ta wannan fannin,idan kuma yi masa za'ayi duk duniya bayajin akwao wani mahaluki da zai iya bari yaga hotunan,koda mahaifiyarshi data haifeshi ce inda tana raye. Sake miqewa yayi da sauri saboda tunawa da yayi da makarantar computer da sa'ida ta mishi xancan ummi ta musu register xasu fara zuwa,idan bai manta ba ta gaya mishi akwai online classes da special classes da za'azo har gida a koya maka,system yayi nufin kunnawa,sai yaga kamar ba zata masa sauri ba,ya ciro wayarshi daga aljihunsa ya kunna data sannan ha fada google ya soma rubuta sunan makarantar,bai manta sunanta ba saboda kusan ma'abocin siyayya ne a shagonsu na yanar gizo wato www.rahamalls.com,bakin gado ya koma sannan ya rubuta sunan makarantar *RAHA COMPUTER INSTITUTE* ,cikin qaramin lokaci ya samu dukkan bayanai,kuma tsarin ya gamsar dashi,ya dauki number dake cikin bayanan ya kira. Cikin sanin daraja da mutuntaka tadan adam ya sake samun bayanan da yake buqata,cikin abinda bai gaza awa guda ba yayi register dasu da komai da komai,ajiyar zuciya ya sauke sanda komai ya kammala,ya duba agogo yaga lokacin daya kwashe,ya miqe a hankali yana fidda kayan jikinsa,ya sauya wasu marasa nauyi,wando iya gwiwa sai jallabiyya daya fitar ganin lokacin sallah ya kusa,ya shiga bandaki ya daura alwala,sanda ya fito wayarshi na ruri,gab da zai isa gareta ta katse,saiya duba mai kiran,nafisa ce,miscal na shida kenan daga sanda ta fara kiransa zuwa yanzu,sai a sannan ma zancan ya dawo masa,ya duba saqon data tura masa wanda na godiya ne da kuma ya yaje gida,aje wayar yayi ya isa inda magungunansa suke ya cira yasha,sannan ya fesa turare ya qarasa bakin gado ya dauki jallabiyyarsa ya saka,hakanan yakejin kaman wani nauyi ya ragu daga zuciyarsa. Cikin mamaki ta dubi table din sanda ta fito daga dakinta,taji kaman ya shigo amma bataga alamun hakan ba,kaman zata share sai kuma taba hakan bai dace ba,kodon jikinsa takega ya kamata ta duba,idan lafiya lau shikenan babu buqatar sake damuwa ko saka ido. Zai fita ita kuma zata shigo,kusan lokaci daya suka murda handle din,baya tadanja kadan bayan ta dubeshi ta dauke idanunta,sai taga kaman ya fada kadan daga jiya zuwa yau da kuma fitar daya sakeyi da dawowarsa,ganin alamun fita zaiyi sallah saita juya ta soma sauka tana cewa "Sannu da zuwa" "Yauwa" ya amsa yana tsaye cak yana dubanta sanda take sauka din,yanajin kaman ya rintse ido ya bude yaga duk abinda ya farun da wanda ke faruwa a mafarkine,bai taba kwana ya kwatanta a ranshi ko sau daya rayuwar zata iya zuwa musu da wannan salon ba,dai gashi lokaci daya komai ya canza,komai ya tabarbare,komai yazo da cikin wani bahagon yanayi. Karon farko tun bayan rabuwarsu dayaji wani abu mai kama da tausayi tausayi akanta saboda tuna cewa nan gaba kadan nafisa xata shigo gidan a matsayin kishiya a wajenya,ya tuna yadda mata ke komawa duk sanda zance makamancin haka ya shiga kunnensu yatuna yadda nafisa ta birkice a sanda labarin wanzuwarta qarqashin inuwa guda ya shiga kunnenta,a sannanma bata zama qarqashin ikonsa na,basu taba kwana qasan rufi guda ba,inaga ita?,duk da bashi da tabbacin cewa zataji wani abu ko zata damu,saboda dukkan dalilin dake sawa mace tayi hakan babushi tattare da ita. "Kidan samu kifi ki dafaminshi idan ba damuwa,zanje sallah na dawo" ya fada cikin laushin murya wanda har hakan yaso bata mamaki,saita juyo tana kallonshi,suka hada idanu ta sake dauke kai ganin yadda ya kafa mata idanu,taji kallon nata har cikin jikinta,sai taba baiken kanta data sanya kaya irin wannan ta zauna haka ko mayafi babu bare hijabi,amsa masa tayi da to tana ci gaba da sauka daga benan,har sai dayaga bacewarta sannan ya sauko shima yawuce masallacin. Sai data soma shiga daki ta samu dan qaramin hijabi ta saka sannnan ta wuce kitchen din har yanzu tana mamakin irin salon da yayi mata magana dashi,ta ciro kifi ta gyarashi,ta kauda wancan tunanin na farko ta fada tunanin yadda zata sarrafashi ta yadda zai dace da yanayinsa,wani gashi ta tuno mai kama da romo romo da takanga anty xubaida bayi,ba bata lokaci ta soma hadashi,wanda cikin mintuna qalilan ta kammala,qamshi kuwa ya cika gidan ko ina,ta gyara komai a kitchen din ta gogeshi sosai yadda ta saba sannan ta fito don barin kitchen din. Tunda ya dawo yana falon a zaune yana shaqar qamshin kifin har cikin zuciyarsa,da mamaki tadan dubi sashen da yake din,don iya zamanta a gidan batace ga sanda ta ganshi zaune haka sosao cikin falon ba,kamar yasan da tsaiwarta shima ya waiwaya yana dubanta,yabi hijabin jikinta da kallo,shima hakan yayi masa don tamkar gata tayi masa,baisan me yasa takeson ta zame masa tamkar wani maganadisu ba ko mayen qarfe aduk sanda ya ganta?,baisan me yakeson sauyashi haka ba,bayan a baya yasan bai damu da dukka shigarta ba,amma cikin abinda bai gaza sati biyu ba yanason sauyawa gaba daya?. *Alqawarin Allah* 44 Komawa tayi da baya kitchen din ta shirya komai ta dauko kan tray sannan ta sake fitowa "A'ina za'a aje maka?" Nuni yayi kata da gabanshi,ta qaraso nan ta aje ta shirya komai ta dauko sauran na wajen dining shima ta shirya masa,tayi sarving dinsa sannan ta yunqura zata miqe saiya dakatar da ita yace ta zauna,ba musu ta koma ta zauna din,saidai duka bata jinta dai dai,baiyi magana ba harya qare cin abincin sannan ya soma da cewa "Da can kafin aurenki ina tare da wata yarinya nafisa wadda har an saka mana rana lokacin biki ya rage saura sati uku,to wasu abubuwa suka biyo baya wanda ya zama silar fasa auren namu a wancan lokacin,a yanzu maganar ta dawo wanda ina tunanin duka ba za'a wuce sati uku ba nan gaba" bata taba tunanin zataji irin abinda taji a zuciyarta ba'a yanzu,tunda ya ambaci sunan zuciyarta da idanunta suka haska mata ita,saita dinga binsa da kallo kawai sanda yake bayanansa,gaba daya saita daina fahimtarsa,duka bayanan da yake kawai tana ganin yana yine saboda radin kanshi,yarinyar daya aiko mata da hotunanta sanda take tsaka da radadin rashin mahaifinta?,yarinyar daya turo mata da fuskarta sanda take tsaka da jimami da alhinin rabuwa dashi?,yarinyar daya kawo mata hotonta ta gani cewa ya samu wadda ta fita?,ya sauya wata a madadinta,a yanzu ita zai aura ya kawo gidan?,shine yake wani rufa rufa dason yiwa zancan kwaskwarima?,tana ganin abu mafi sauqi kawai ya fito ya gaya mata zai cika muradi da burinsa ne,yanzune manufar da yasa ya aureta zai bayyan muraran baro baro,me yayi saura?,me xata xauna taji daga bakinsa,ai komai ya qare hakanan komai ya fito fili,sai kawai ta miqe sanda yake tsaka da bayanin nashi,binta yayi da kallo ganin ta soma tafiya zuwa hanyar dakinta ba tare data ko waiwayeshi ba,kiran sunanta ya soma yi abinda ya jima rabonshi dayin hakan,saidai ko daya bata saurareshi ba bare taji me yake fada,da hanzari ya miqe ya bi baya,taji takun tafiyarsa,saboda haka tana shiga dakin ta saka key,ta samu gefan gadonta ta xauna ba tare datasan me zata tuna ba,wani kuka ne mai sautu ya qwace mata wanda ta kasa tsaidashi,hannunsa saman kanshi yana yamutsawa jin sautin kukanta dake ratso har inda yake tsaye "Hasbunallahu wa ni'imal wakil" ya furta yana kallon qofar dakin da yayi juyin duniya ta bude taqi,bai taba xato ko tunanin xata damu ba ko sau daya,me yasa ta damu?,me yasa ranta yw baci?,bayan ta gaya mishi cewa bata qaunarshi ko kadan?. "Me yasa kike kuka shahida?,kukan me kike?,kins kukane saboda mutumin da kika dainaso xai qara aure?,ko kina kuka ne saboda mutumin daya daina sonki xai auro wadda yakeso?,muradin zuciyarsa?,haske rayuwarshi?,meye abun damuwa a ciki shahida?,har yanzu anwar na cikin zuciyarki ko kuwa?" Tambayoyin da zuciyarta ta dinga mata kenan wanda yasa ta soma tuhumar kanta da kanta. 🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍 Duban nafisan mima takeyi sosai da wani irin banzan kallo,cikin ranta ji take kaman ta tashi ta shaqe nafisan,cikin ranta tana ala wadai da sakacin da tayi har ta bari tunanin nafisa yakai gata nemi anwar karo na biyu,tabbas da tasan da irin wannan ranar da tunu ta saka almakashi ta datse alaqar da tayi saura tsakanin anwar din da nafisan,koda yake a yanzu ma bata baci ba,saidai kuma ba haka taso ba,dole ya saka taka tsantsan da nutsuwa dinta wargaza tsakaninsu,don a yanzu bata da burin daya wuce ta ganta itama gidan anwar din a matsayin matarsa,sake duban nafisan tayi a karo na biyu yadda taketa faman fara'a,bakinta kamar zai hade da kunnenta,irin kallon da miman ke mata yasanya jikinta yadan soma sanyi "Ko bayi dai dai bane hajjaju?,bafa zan iya haqura da anwar ba matuqar ina raye shima yana raye" baki miman ta tabe tana ci gaba da dubanta "Dama aida kin jira ni nidin xan miki wannan aikin,abinda yasa kika ji shuru ba'a kai gabar bane,naso mu gasashine harsai ya kawo kanshi da kanshi ta yadda koda kin shiga saikinfi daraja da qima a idanunsa,amma a yanzun yadda kikayi wallahi qimarki ta zube qasa warwas,kuma haki da wata fuffuka da xakiyi idan kin shiga gidan,hasalima ba baiyi matsuwar shigowarki gidan ba kinga baki da abun cewa sawa ko hanawa koda kin shiga gidan" sai jikinta ya danyi sanyi,taji maganar mima tabbas tana kan hanya,shigen maganar da mummynta ta gaya mata kenan,ita kuwa a rayuwa yanzu burinta na gaba shine ta shiga gidan anwar ta zama ita ke fada aji,ita zata sa ayi ta hana kuma a hanu,wanda daga qarshe take fatan shahidan ta fita tabar mata gidan gaba daya taci gaba dayin yadda takeso. "Gaskiyar magana mima banason nayi rayuwar da bani zance ayi ba cikin wannan gida,saboda har yau ina tsoro kuma ina shakkar soyayyar dake tsakanin anwar da wannan mayyar yarinyar" abun nema ya samu wajen mima,hanyar da zata wargaza rayuwar auren nafisan cikin sauqi,duk da haka saita sake tsuke fuska ta kuma gum da bakinta harsai da nafisan ta sake magantuwa cikin mitar tayi mata shuru,fuska ta yatsina "In sake shiga sabgarki ki watsamin qasa a ido?,ina qoqarin fiddo miki da daraja da martabarki amma ke baki gani,gwara kawao na qyaleki kici gaba da samawa kanki mafita" harara ta watsawa miman "Banason wulaqanci wallahi mima,haba don Allah,sau daya dai don nayi amfani da shawarar kaina saiya zama matsala?" Sai data gama shan qamshinta sannan tace "Shikenan,zaki samu yadda kikeso,zaki mulka anwar ki kuma juyashi shida waccar yadda kikeso matuqar zaki jure ki kuma bi doka da qa'ida,zan dawo next week randa kikacemin zaki fara rabon IV zakiji sauran qarin bayani" kamar ta goya mima haka nafisa taji,kudade masu yawa ta baiwa miman sannan ta rakata. Dariya mima ta saki bayan ta gama irga kudaden,mota takeson sauyawa,kuma ba shakka lokacin da zata sauya motar da takeso din yayi,a jikin nafisan zata hada kudinta tsaf,daga qarshe kuma ta tashi a tutar babu,ba anwar din ba kuma kudinta,daga haka ta tada motarta taci gaba da tafiya tanabin waqar dake tashi cikin motar cikin nishadi gami da tsara yadda zata mallaki anwar ita kadai bayan ta fitar da shahida da nafisan ma daga gidan dukkansu. 🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍 Kaman a mafarki take jiyo sallamar anty xubaida cikin falon nasu,da sauri ta sauko daga gadon wanda ta maidashi wajen rayuwarta,idan kaga ta fito tota tabbatar anwar ya fita baya gidan sannan zata fito tayi aikace aikacenta a gaggauce ta koma,sam bata qaunar haduwa dashi ko daya,Suna shirin yiwa kansu mazauni ta fito fuskarta a washe "Anty yau a gida na?,ashe xakixo?" "Kamawa ai take,gashi ta kama shahida naxo" cikin walwala da farinciki ta tarbesu. ,sun jima sosai ranar,sunata hira dasu huda,duk sai yaji kewar gida ta sake kamata,kaman ta koma gidan haka takeji. Saida suka dan kebe sannan anty zubaidan ta gaya mata abinda ya kawota,zancan auren anwar,kebe fuska shahidan tayi cikin nuna halin ko in kula,saidai can qasan ranta wani abu ke tsinkulinta,maganganu sosai anty zubaidan tayi mata,gami da jan hankalinta,suna gama cin abincin rana tace zasu koma,kaman shahidan tayi kuka amma hakan ta haqura,taso sosai antyn tabar mata hudan amma qememe taqi,haka suka tattara tanaji tana gani suka tafi. Zuwan antyn yasa tadan sake ranta,ta koma sabgoginta kamar baya,saidai ta sake janye sosai daga anwar din,sati biyu da faruwar hakan anwar ya shigoda set din manyan akwatina guda hudu,da farko tayi burus amma daga bisani tayi tunani kada ya tsammaci kishinsa take saita karba ta masa godiya,yayin daya bita da kallon mamaki,da gaske bata jin kishinsa? Hakan na nufin bata sonshi?. Cikin kwanakin ka'in da na'in ya maida hankalinsa ga koyon abinda yasa gaba daga raha computer instute,ya ware lokaci har gida yake iskeshi malamin,baisan me yasa abun ya tsaya masa a rai ba,bai san me yasa ya maida hankali fiye da yadda ya xata ba,wanda yake da tabbacin cewa cikin wata uku ya cimma abinda yakeso ya cimma din,ta bangare guda guda kuwa yayi qoqarin kawo sauyi ko yaya yake tsakaninsa da shahidan,don ko kusa baida burin nafisa taxo ta fuskanci komai dangane da zamansu,duk da qoqarin nasa sau da yawa yakan cimma tasgaro,saboda rashin samun cikakken hadin kai daga shahidan. Ta bangaren amarya nafisa kuwa shirye shirye sun kankama ka'in da na'in,dukkan wani abu da aka sani na bidi'ar biki ba wanda bata tsara xatayi ba,harda ma wanda ba' saba gani ba,ko sauraren abinda anwar din zai bayar batayi,sha'aninta kawai take. Qarfe shida saura malamin da suke karatu tare ya tafi,yarage saura shi kadai a dakin,ya shiga cumputer din sosai yayi shige da fice wanda ya tabbatar masa lallai ya soma nisa,hakanan yana cimma abinda ya nufa din,saiya kasheta yana sakin murmushi wanda yayi dai dai da shigowar kira a wayarshi,duban wayar yayi sai yaga nafisa ce,ya manta shaf cikin satin zasuxo jeran kaya,bai daga ba harta katse,saiya janyo wayar yana laluba inda ya aje numberta,cikin sauyin da aka fara samu wanda ada bashi da ita. Har tayi ringing sau biyu tana katsewa ba amsa,sai ana ukun sannan ta daga,shuru tayi tana sauraren muryarsa wadda ko mutuwa tayi ta dawo ba zata kasa gane muryar waye ba "Bakisan ina cikin gidan bane?" Ya tambayeta ganin tsahon zamansu baiji motsinta ko gilmawarta ba,shuru babu amsa saboda haka ya kautar da wancan zancan "Ki sameni a dakin karatuna....am yana nan daga baya kaman zaki shiga qofar kitchen ta baya" ya sake mata bayani don ya sani bata sani ba,tunda bata taba zuwa ba. Wayar ta sauke tana jin wani haushinsa na kamata,tome zaiyi mata,kiran me kuma yake mata?. Har sai daya zaci ba zata zo ba yaci gaba da aikinsa sannan yaji an murda murfin qofar,ya daga kai yana kallon bakin qofar,itace cikin jar doguwar riga wadda ta yane kanta da qaramin mayafinta,idonsa ya dauke wani abu na tsirga masa,ba kwalliya a fuskarta amma tayi masifar amsarta rigar wanda ya kasa kubuta daga qyasata da zuciyarsa tayi. Daga sallama bata sake cewa komai ba,ta samu gefansa ta zauna,saiya kashe wayar tashi da yake dannawa,ya juyo gaba daya suna fuskantar juna sosai yatsunshi sarqafe da juna idanunshi cikin nata,fuskarsa na nuna zancan da zaiyi mai muhimmanci ne,sai taji kallon da yamata nauyi,ta kauda kanta gefe guda "Gobe jibi gata masu jeren amarya zasu zo...." "Me zanyi musu to?,meye amfanin gayamin din?,Allah ya kawosu lafiya" ta fada cikin zafi zafi wanda ita kanta batasan ta aikata hakan ba,idanu ya zuba mata har takai aya sannan yace "Babu abunda xaki musu,kawai inason ki kwashe kayanki xaki koma dakunan sama" waiwayowa tayi tana dubanshi,me zataje samanshi tayi masa,dai kawai ta miqe ta soma takawa tana cewa "Na barwa amarya,inda nake nan ya isheni na qarasa kwanakin da suka ragemin" bai fuskanci me kalmarta ta qarshe ke nufi ba,amma ganin zata fice sai yace da ita "Umarni na baki ai ba shawara bace bare ki gayamin naki ra'ayin" daga haka shima ya juya abinda shida kujerarsa,saita waiwayo tadan dubeshi kadan sannan taci gaba da takawai ta fita daga dakin. Tana shiga nata dakin taji kuka ya qwace mata,duk yadda taso hana kanta abun yaci tura,batasan me yasa takejin bacin rai da damuwa ba,kuka tayi sosai kafin taji zuciyarta tayi sanyi. *BAYAN KWANA UKU* Tana kwance rub da ciki saman gadonta,sanye da wata doguwar riga na wani yadi me sulbi wanda yake kama da yadin satin,hakan yasa yabi jikinta ya lafe,gajeran hannu ne dashi gami da wuyan half shoulder wanda ya fitar da wuyanta da wani sashi na qirjinta sosai,kanta babu dankwali kana a tsefe yake,hakan yasanya gashinta da bata kamashi da ribbom ba ya biyota shima ya kwanta saman filon da take kai,gama wayarta kenan da ummanta tana nazarin maganganun data gaya mata taji an murda qofar dakin,wanda hakan yaja hankalinta zuwa kallon qofar,yana shigowa idanunshi cikin nata,mamaki ya sanyata miqewa ta zauna sosai saman gadon,tama mance da irin dinkin da yake jikinta,idanunta fal da alamun tambaya,jingina yayi daura da qofar ya goye hannayensa a qirji yana qare mata kallo,sai a sannan ta tuna da rigar jikinta,tabi kanta da kanta da kallo saita daga kai tana hade fuskarta tsaf,miqewa tayi ta nufi wardrobe dinta ta soma lalubar mayafi,yana tsaye still yana kallonta har yanzu baice komai ba,harta gama yafa mayafin ta dawo gefan gadonta ta zauna "Ki shirya gobe qarfe tara na safe xamu fita tare xan saukeki gida" fuska a tattare ta bishi fa kallo har ya fice,saita ja qaramin tsaki ta koma ta kwanta tana tunanin ina zai kaita?,kuma me zata fita tayi. Tara saura tana tsaka da shirinta wayarta ta shiga ruri,ta qarasa inda take aje ta daga tana duba mai kiran,anty usaina ta gani,a ladabce ta daga suka gaisa sannan tace "Na kasa samun layin anwar,inata kira busy,taimaka don Allah ki gaya masa idan zai fito ya fito da wadan nan takardun" "Toh anty" ta amsa mata a ladabce tana aje wayar,qarasa shiryawa tayi sannan ta fito ta haura saman nashi,tana shiga yana aje wayar gami da miqewa ya tura qofar toilet ya shige,bata masa magana ba don qyashin hakan takeji,saita barshi ta samu saman kujerar mudubi inda ya tashi ta zauna tana dakon fitowarsa. Wayar daya aje saman mudubi wanda take dab da ita ta dauki ruri,idanunta kai kan me kiran,nafisa ta gani,ta riga data haddace sunan,saita dauke kai saidai hankalinta ya kasa daukuwa daga kai,tana jin sautin ringing din har cikin kanta harta katse,aka sake kira ta sake katsewa,ba jima wani kira yasake shigowa,batasan sanda taja wani mugun tsaki ba ta finciko wayar ta kasheta gaba daya ta dangwarar da ita awajen,tana tuna sanda ta shigo waya taga ya gama,wala'alla ma shi yasa anty usaina ta gaza samunshi wayama yake kenan "Ina ruwana da wayarshi" ta gayawa kanta tana sake tsuke fuska ita kadai,daidai lokacin daya fito daga bandakin jikinsa jiqe da lema,da alama wanka yayi,fuskarta a dinke tsaf cikin kaushi tace dashi tana miqewa "Anty tace karka manta ka fito da takardun nan" daga haka tayi gaba,binta yayi da kallo,tana gab da ficewa yasha gabanta,ya murza key ya rufe qofar,saita danja da baya tana dubanshi,kuka takeson tayi amma batasonyi a gabansa,don tasha alwashin ta daina yi din yana gani yana jin dadi "Ka budemin na fita na qarasa shiryawa" ta fada cikin sanyi,wanda ba haka taso,taso tayi maganar ne cikin kaushi da zafi,saiya kada kai yana duban idanunta wansa hakan yaso mata tasiri,saita zare nata idon gami da kauda kanta wani sashen daban. tokare _Dadai zakuyi haquri harmu cimma manufar labarin,don kowanne labari yana da manufar da akeso a cimma,idan kuma kunason shortcut shikenan_🤷🏽‍♀️ Mai yiwuwa gobe kujini shuru,idan kuma Allah ya bada dama to. *karku manta kuyi wekend dinku da tashar SAUTIN HIKIMA dake youtube,ku saurari littafanmu ba tare da kunsha wahalar karatu ba kuna daga kwance*💃🏻 *Asha weekend lafiya*🤝🏽 *Alqawarin Allah* 45 "Zuwa yanzu ya kamata ki fara koyan wasu abubuwan,saboda karta shigo ta rainaki" ya fada yana son dawo da salon tsokanarshi. Wani kallo ta watsa masa da idanunta sanda yake komawa zuwa bakin mudubi,wani abu ya tokare mata wuya "Wace zata shigo din?,bani ya kamata ka gayawa wannan maganar ba,don ni ba kallon mijina nake maka ba" saiya waiwayo yana zare idanu "Da gaske?,lallai kinci tuwo da yawa,wait....waima kallon me kike min?" Harara ta sake watsa masa ganin yanason maida abun shirme kamar yadda ya saba,baisan yadda ranta ke tafasa ba "Oho,koma meye ba damuwarka bane,ka budemin qofa kawai na wuce,abu daya na sani shine,daga kai har ita kada wanda ya sake yashiga hurumina" baki ya kama yana kallonta,sau tari yakanso yaga tana rashin kunya,sai dan qaramin bakinta yayita burgeshi,don a tsahon xamansu na baya bai taba ganin tana tsiwa ba sai yanzu "Idan kuma akaqi fa?" "Raine zai baci" ta amsashi kai tsaye,qaramar dariya ya bushe da ita "Kinga...kawai ki fito kice kishi ne yake damunki ko?,to kiyi haquri,na miki laifi" sake hararshi tayi,tanajin kaman ta makeshi ko zataji sauqi "Ni na gaya maka duka wannan na damuwata bace,bama kallon miji nake maka ba bare nayi kishinka,ka budemin na fice kawai" "Aiko kin makaro,dakin yadda kawai da hakan yanzu zan bude miki qofar salin alin,amma tunda kika musa to sai na gama shiryawa tsaf sannan zan bude ki mu sauka tare" tanaji tana gani yayi funfurus yahau shiryawa a gabanta ko kunya baiji,haka ta zauna ta kallo bango harya gama ya budeta. Har daki yabita ta gama daukar abinda zata dauka kaman wani body guard,tana kumburi tana komai amma bai kula ba ta fito suka fita. Gidansu ya soma kaita,ta cika da mamaki sanda suka isa taga ya sake cikinsu sosai kaman yadda suka saba a baya,sai taga kamar ma sunfi zumudin zuwanshi akan nata,hira suke abinsu da umma kamar danta,baqinciki yasa ta kasa sakewa ma bare tayi hira,basu bar gidan ba sai qarfe daya da rabi na rana bayan yaje masallacin layinsu yayi sallah sannan yace ta taso,kaman ba zata tashin ba,don ita sam lokacin bai isheta ba,amma yadda umma ke jifanta da harara yasa dole ta miqe tabi bayanshi. Daga nan gidan anty zubaida sukayi,can dinma haka suka gaisa da antyn cike da sabo,sannan ya yiwa anty zubaidan sallama kan zaije anjima zai dawo ya dauki shahidan. Kusan fiye da rabin hirarsu ya ranar jirwaye me kama da wanka anty zubaidan ta dinga mata da gugar zana,ta kuma fahimceta sarai saidai tayi kaman bata gane ba,duka dai kan zamantakewarsu ne da nafisa dake shirin shigowa gidan,wanda duka ita tana ganin wannan ba matsalarta bace,dubanta anty zubaidan tayi sanda suke tsaye cikin kitchen tana tayata yanka cabbage zata hada coleslow "Ranar yaushe zaki yinin naki ne banji kince komai ba,yaufa alhamis,lahadi kuma daurin aure" baki ta tabe bayan ta dubi anty zubaidan "Ko nawa bikinma ban tsaya wani tsara wuni ba bare bikin wasu" ta fadi cikin qunquni,murmushi ya subucewa anty zubaida saita kada kai,lallai yaro yaro ne,ga zallar kishi na bayyana kan fuskarta da kalamanta amma taqi yarda da cewa kishi take "Wancan daban wannan daban,bakyace ba zakiyi ba kodon idon mutane,kuma kema zaki buqaci wadanda zasu tayaki karbar amarya" "Waini zan karbeta ma?" Ta fada tana nuna kanta da wuqar hannunta "Eh mana,haka akeyi ai" saita jijjiga kai tana ci gaba da yankanta "Lalllai kam" anty zubaida ta fuskanci zancan ciwo yake mata ba tare datasan da hakan ba,sai kawai ta shareta suka shiga wata maganar daban. Bayan sunyi sallar la'asar anty zubaidan tace tazo ta rakata kitso,ba musu ya dauki mayafinta suka fita a motarta,huda tace zata bisu antyn yace sam tayi zamanta,suna tafe a motar antyn na nuwa shahidan wasu robobi masu dauke da gumba ta kwakwa da dabino,wanda idan kanaci zaka xaci an hada kayan qwalamane kawai sai aiki a jiki,wadda takan jima jikin mace bata bar jikinta ba,ta dinga mata dabara kanta dandana mata taji,haka ta dinga ci suna hira,antyn tana tuqi a hankali har sai dataci da yawa,ta sake nuna mata wata roba wadda ke cike da tsumi tace "Sha kiji wannan fa"dan bata fuska shahidan tayi "Wainikam anty wadan nan ba irin kayan nan naku bane na matan aure?" Harara ta jefa mata "Ke matar shika ce?" Sai zancan ya bawa shahidan dariya,ta bude robar ta ta soma sha,zaqinsa da dadinsa yasa sai data sha rabi,abun har ya baiwa anty zubaida dariya tace "Ya haka?" "Wannan kam yayi dadi sosai shima" "Tsumin maman farida ne,jiya aka aikomin shi daga zariya"tana rufe robar tace "Amma yayi dadi wlh ya tsumu" dariya ta sake baiwa antyn. Bata gane inda sukazo ba saida anty zubaida tayi parking,wajen da aka mata gyaran jiki ne na aure,saida suka shiga ta gane wai ita antyn ta kawo ayiwa,narke mata tayi don ita sam bata sha'awa,hasalima tasan cewa asarar kudi kawai za'ayi "Don Allah anty,iya qunshinma kawai ya isa" daga qarshe dai da qunshi kawai aka tsira ja da baqi,itama antyn aka mata jaa sannan sukayo gida,zuwa lokacin har anyi sallar magariba,saboda haka tana shiga salla kawai tayi,ko abinci bata ciba ya iso suka wuce. Tun daga falon qasa taga gidan gaba daya kamar ba nata ba "Sama zaki wuce" ya furta mata yana zama saman daya daga cikin kujerun,bata kulashiba ta shige,saidai tayi tayi qofar dakin nata ya budu amma sam yaqi,haka ta dawo falon tana raba ido zuciyarta fal qunci,da gaske kenan ya maidata saman ya saka nafisan a nata dakin?,zuwa yanzu baya falon,haka ta gaji da zama a falon bacin rai na sake cikata,tilas ta haura saman. Dakin da yake kallo nashi ta tura,komai na dakin sabo ne kaman yadda kayan falon saman ma suke sabo dai dai dana qasan,abu daya yasa ta gane dakinta ne takacen kayan makeup dake jere saman mudubinta gasunan jere saman sabon mudubinta,ta jima tana qarewa dakin kallo yadda yatsaru yayi wani kyau,dukka colours din ciki masu kyau da kwantar da hankaline,sai data gaji don kanta sannan ta cire kayanta tafada wanka,tana wankan tana kallon lallenta wanda yayi kyau sosai ita kanta ya burgeta. 🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍 Kallo daya zaka yiwa fuskarta ka tabbatar da cewa yau din rana ce ta musamman a wajenta,hakanan farincikin da take ciki ayau din shima farinciki ne na musamman. Ta kasa boye duk wani jin dadi da walwalarta,duk da cewa yadda taso ba duka haka anwar yayi mata ba,dinner daya yaje mata a gaggauce,hatta yau da yake daurin aurensu tana da labarin a makare ya iso wajen,bai kuma jima ba ya koma,saidai duka wannan ba damuwarta bane,da taimakon mima tasan cewa komai zai daidaita,zata kuma samu yadda takeso. "Qawata jimana" mima dake tsaye dankwali gaban goshi ta fada bayan ta gama yiwa duk yarinyar dake madaidaicin falon nafisan kallon tara saura "Kowa zaici uwasa" ta fadi a ranta,shigowarta kenan ita dinma batazo da wuri ba,ta jima tsaye daga waje tana kallon yafda nafisa ke wani rawar kai kamar zata taka kan shege "Gani,ta samu ne?" "Eh kusan hakanne,amma qawata,bayan sauran event da ango baizo daurin aurenma ance a makare yazo ko?" Tabe baki nafisa tayi da alama tadanji haushin abun "Hmmmm,wallahi in gaya miki mima,ban sani ba ko waccar matar tashice ta tsaidashi Allahu a'alamu" Sake tabe baki mima tayi "Waxai hanashin idan ba ita ba?,kinga abinda nake gaya miki aiko?" Sanyin jikin nafisa yayi,saita zubawa mima ido kawai tana kallonta,da alamun neman mafita take,hakan yayi dai dai da tsarin miman,saboda haka tasa hannu cikin jikirta ta fito da wani qullin baqar leda ta soma warwareta,layune tafka tafka guda biyu wanda jikinsu yake wani iri babu kyan gani ta nuna mata "Wannan,ki tabbatar ayau ko gobe idan an kaiki kin maqalata gefan gadonki" ta ajeta ta dauko wasu baqaqen garin magunguna da wani mai kama da man shafawa saidai kore sharr yake "Wadan nan kuma kin gansu?" Tafada tana duban nafisan sosai,alamun maganar da zata gaya mata babba ce "Kin gansu dakyau ko?"ta sake jaddada mata,gyada kai nafisan tayi tana kallonsu tana kallon mima "qananu ne amma amfaninsu yawa ne dashi,wadan nan da kike gani idan kikabi doka da tsarinsu to rayuwar gidan aurenki zata inganta ta tafi yadda kike fata,idan kika tsallake doka daya ko sharadinsu to kuwa babu shakka kjn wargaza komai,kuma komai zai iya biyo baya" cikin nuna zaquwa da qaguwa ta gyara tsaiwarta tana cewa "In sha Allahu ba abinda zai faru,gayamin ya amfaninsu yake" sai data daure ta miqa mata sannan tace "Daga randa za'a kaiki gidanki zaki jiqa kowanne kiyi tsarki dashi,mai kama da man shine na shafawa,zakiyita amfani dasu har tsahon watanni uku cif cif,sharadinsu sune,idan kika soma amfani dasu babu maganar kwanciyar aure harsai kin kammala,kinga kenan daga randa xaki shiga gidanki harki kammala amfani dasu ba zaki bawa anwar kanki ba harsaikin gama amfani dasu,ammafa daga randa kika gama amfani dasu yasanki a 'ya mace ko?" Sai tayi shuru tana juya idanunta sannan tace "Uhmmm.....abun ba'a magana kawai" ta furta murmushi na qwacewa fuskarta,shuru nafisa tayi tana nazari,da alamu ta shiga damuwa,cikin zuciyarta tana jin babu dadi,ba qaramin buri ta cuwa first night dinta ba,tayi alqawarin saita hana shahida bacci a ranar saboda tayi tayi anwar ya kaita gidansa na alfarma data sani wanda da yake zaune a ciki amma yaqj,gidan da xai kaitan sam yayi mata qanqanta "Yanzu har watanni uku kenan ba wani mu'amala tsakaninmu?" "Eh...indai kinanson samun yadda kikeso,idan kuma ba haka ba,kina iya bani maganina na juya dashi,saiki shirya fuskantar duk wata rayuwa da zaki gani" da sauri ta janye maganin ganin mima ta miqo hannu tana cewa "A'ah,Allah na tuba don dai wata uku kawai?" "Ah to nima shi na gani,kuma gidan nan bake kadai bace bare kice akwai matsala,idan ya matsu ya tafi wajen dayar" harara nafisa ta watsa mata cike da kishi "Tabdi,lallai ma,to bari kiji,nijin kaina nake ni kadai nake wallahi" dariya mima ta kwashe da ita harda tafa hannu tana duban nafisan,yayin da nafisan ta taka tayi gaba ta koma cikin mutane yana yiwa miman godiya,juyawa tayi mima ta fice daga gidan tana sakin murmushi don tace mata ba zata zauna ba akwai inda zata,amma anjima da ita za'a kai amarya. 🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍 Sake dawowa yayi jikin qofar karo na babu adadi,tun kafin ya fita daurin aure take cikin dakin kuma taqi fitowa,yayi juyin duniya amma taqi tabude mishi,ko bata fada ba koda bai sani ba jikinsa ya bashi kuka take,dalilin daya sanyashi makara baije akan kariba kenan,bayan yaje ya dawo kuma nanma ko reception din da aka shirya bai tsaya ba yayo gida saidai jiya iyau,daga qarshe badon yaso ba ya yanke tilas ya kira anty xubaida ya gaya mata. Sakin ajiyar zuciya tayi tana aje wayar bayan gama doguwar waya da sukayi da anty zubaida da kuma zunnurah,ita kanta tanason tayi controlling kanta amma ta kasa,wani irin bacin rai da baqin ciki ke taso mata,tadan dauki wasu mintuna a zaune a wajen sannan ta miqe ta shiga bandaki,ta hada ruwan wanka mai dumi sosai tayi wanka,already ta riga data sauko ta gyare gidan tun sanda taji fitarsa,shi kadai dinne kawai batason gani,amma dole ta haqura ta dauki maganar anty zubaida da zunnurarta,donta wuce komai a wajenta. 'Yar madaidaiciyar kwalliya tayi cikin wani sabon coffe lace me adon silver pink da golden,sosai ta dinkin ya tsaya mata,hakanan lace din yahau fatarta qwarai,ta saka awarwaro dan kunne da sarqa duka silver ta wadata jikinta da turare. Dai dai nan taji ana sake knocking,ta kalli qofar ta dauke kanta,sannan ta soma takowa ta bude ba tare data tambayi waye ba,anwar dinne yana tsaye qofar dakin sanye da rigar da wando na shadda blue ruwan sararin samaniya,fuskarsa sam babu walwala,hannunsa goye a qirji ya zubawa qofar ido,wanda tana bude qofar idanunshi suka sauka a kanta,rabon daya sanyata a idanunsa tun ranar dinner din nafisa data matsanta mishi sai yazo,sanda ya shirya zai fita tana falon qasa tana kallo,abinda kusan ba dabi'arta bace,zai mata magana bata tsaya saurarenshi ba ta tattare wayoyinta da kayanta ta haura saman ko waiwayoshi batayi ba,sai yaji sam baiji dadi ba,tunda ba dabi'arta bane zaman falo mai yiwuwa yau tayi sha'awa ne gashi ya bata mata yanayi,koda yaje a gurguje ya dawo,amma saiya tadda ta garqame kanta,tun ranar rabonshi da ganinta sai yau. Bata ankara ba har ya iso gabanta,saiki tayi ta riqe dukka hannayenta cikin lallausan tafin hannunshi,runtse ido tayi tana son zamewa amma ya riqe gam,saita soma qoqarin ganin ta qwace din,gaba daya ya janyota sai gata cikin jikinsa,saura kadan numfashinta ya dauke,ta dinga qoqarin zuqoshi hadi da shaqar qamshin daddadan turarenshi "Babu dadi ko?,kiyi haquri" ya gaya mata muryasa qasa qasa,tsigar jikinta ta zuba sosai,saita soma kokawar cire jikinta tana tureshi da dukka hannayenta "Ina ruwana?,meya dameni?,ka sakeni don Allah bana son irin haka" "Ko baki taba sona ba shahida dole kiji haushi,dole kiji kishi,nasan halin mata fa" yayi maganar yana sakinta daga jikin nashi,saiyadan jaa baya kadan "Kije qasa kina da baqi" daga haka ya juya ya nufi dakinsa,yayin data gyara daurin dankwalinta sannan ta sauka zuwa qasan. Mubina ce khadija da huda sai sa'ida da qanwarta ,fuskarta a sake ta karbesu,nan suka sake sosai abinsu cikin gidan,sa'ida ta gaya mata anty usaina na gaidata,can gidan anty usainan dole ta hada wuni saboda 'yan katsina da sukazo duk da basu da yawa,amma wannan karon harda inna kakar anwar,wanda ta manta rabonta da kano,shi yasa wannan karon anwar din ya matsa sai tazo,tunda ta fuskanci shahidan bata da ra'ayi hada wani taro sai ita ta hada a gidanta,saidai sa'idan ta gaya mata anjima zasuzo karban amarya. Kaman babu abinda yake damunta haka suka dinga sabgoginsu da yaran,anwar din yana daga sama,wani lokaci ya leqo yayita kallonsu bata sani ba,wani lokaci kuma yana daga daki yakejin motsinsu,shi ya aika akaje aka dauko yaran yasa aka kawo mata,yasan koba komai zasu hanata zaman dakin daya tsira,ta kuwa ji dadin zuwan nasu,duk wata damuwa da take jinta liqe da ranta sai takejin ta ragu. Ko data gama abinci iya ita da yaran suka zauna sukaci,bayan sun gama tasa suka kwashe suka kai mata kitchen zata wanke,tana tsaye a kitchen din ta soma dauraye kwanukan ya shigo,ta waiwaya ta dubeshi ta dubeshi sai kuma ta dauke kai tana ci gaba da wanke wankenta "Ni ban taba ganin ango irin wannan ba,ba abokai ba komai,ka dawo gida ka samu waje ka zauna?" Take tadin ita da zuciyarta,wanda harya iso bayanta dab da ita bata sani ba,kallonta yake hakanan qirarta da shape dinta yake daukan hankalinsa fiye da qima,saiya dinga tuna baya can da bai taba ganin komai nata ba,saboda a sannan ma'abociyar sanya hijabi ce,a lokacin da yake cike da buri da fatan Allah ya bashi kudin da zai aureta ya mallaketa a matsayin matarsa,yanzu gata a matsayin matarsa,amma wani abu ya ma rayuwarsu karan tsaye,saiya kauda wannan tunanin yace "Ni ba za'a bani abincin ba?" Gocewa tayi gefe jin maganarsa dab da ita,da alama tsaye yake kenan a bayanta "Ban dafa dakai ba" ta amsa masa tana ci gaba da wanke farantan ba tare data juyo ta dubeshi ba,shuru yayi yana dubanta,bata taba hanashi abinci ba sai yau,sai baice komai ba ya matsa gefe kusa da inda tukwane suke,ya dauki daya ya dauraye ya ya tari ruwa a fanfon dake kusa da ita,ya hada kayan qamshi ya dora ruwan shayi,ya jingina da jikin kwabar kitchen din yana kallon ruwan yana jiran ya tafasa,duk abinda yake tana kallonshi ta gefen ido,ta rugashi gamawa don haka ta fita tabar masa kitchen din,suna falon yazo ya wucesu da ruwan shayin,harya soma hawa saman saiya waiwayo yana dubanta,hankalin yaran duka nakan arewa24 yace "Banfa ji haushi ba,wanda ma aka dinga bani a baya Allah ya amfana ko?" Ya qarashe maganar yana daga mata gira,kauda kai tayi yadda ta saba kaman bata ganshi ba,yayin dashi kuma yaci gaba da hawa saman. Da yammaci suka sake gyare gidan tsaf suka cikashi da qamshi tako ina,har turarukan da bata taba amfani dasu ba sai ranar,kama daga na labule carfet da wanda kebin iska,sun gama kenan sai gashi ya sauko cikin shadda brown sabuwar qarr,kyau uya kyau yayishi,sai taga kamar wannan shigar ta musammance,duk da dama shidin koda yaushe cikin saka sabbin sutura yake,hakanan taji wani abu ya tokareta sanda suka hada ido ya dage mata gira guda,saita aje pillow din hannunta ba tare data bari ya iso inda suke ba ta shige kitchen,tana jinshi da yaran suna uncle kayi kyau,ya gama dan hirarsu dasu ya fice daga gidan bayan ya dauki daya daga cikin motocinsa.