Hamshakiyar uwa book 3 Ban an kara ba kawai sai ji nayi ya jani jikinsa, na fara mitar dan Allah a yi sauri kar Umma ta tafi yana faɗin "Haba Baby babu inda zataje." Nace bazan so ta gane me nayi ba fa kamar rashin kunya ne, ɗan Allah nikam kayi saur.... Bakinshi ya saka ya datse surutu na, wanda haka ya tilasta min yin tsit. Bayan ya samu kanshi na uzzira mishi ya yi wanka ya shirya amma dole na zura mishi ido ya yi salla saboda an riga anyi a masallaci. Ni kuwa ko wakan banyi ba burina dai ya fita. Kafin ya kammala na ɗauki jakarsa na rataya a kafaɗa. Yace "Yau a haka zan tafi bazan saka turare ba?" Nace E yau a haka zaka tafi, domin dama ai danni ake sakawa ko?" Yace haka ne amma ayi haƙuri a ɗan yarfamin ko ba yawa." Na ɗauki wanda hannu na yakai na feshe shi,sannan na ce mu tafi. A falo Hajiya ce kaɗai take yin salla a gurin salarta,na shiga waige waige ina faɗin to ina ummana ta shiga kuma! Na kalleshi, cikin kukan shagaɓa nace kaga ka gani ko? Gashinan ta tafi ina ta cewa ka yi sauri amma ka ƙi gashi kuma ta tafi ko ɗakina fa bata shiga ba... Da leɓen shi ya nuna min bayana. Cikin sauri na waiwaya sai naga Umma ta fito daga ɗakin Hajiya tana faɗin Baby kukan me kuma ki ke yi haka kamar wata ƙaramar yarinya? Na saki dariya ga hawaye nace na zaci fa ko har kin tafi ne. Tace "Shi ne ki ke yin me?" Shamaki ya ce "Shi ne ta ke kuka dan shagwaɓa." Umma tace Shagaɓar gaske kuwa banda shiririta ina ke ina kukan na tafi tunda ba tare zamu tafi ba.Ta zauna agurin zamanta na aje jakar nace Umma bari in saka miki abincin ko? Tace "Kaɗan zaki sa min don banajin yunwa. Na sa mata kaɗan na loda mata nama, da da hali saina kwashe mata naman ta kaiwa su Jafar, amma gudun zargi ko maganar Hajiya dale dai na haƙura. Hajiya ta idar Shamaki dama ita ya ke jira, domin in ta fara salla sai mutum ya jira dan wani lokacin na kan tambayi kai na ko dai Hajiya sai an amshi sallar sannan take idarwa. Yace "Hajiya na gama shirin zan fita kasuwa. Ta dafa kanshi kamar yadda ta saba. Tace Allah ya yi maka albarka ya bada sa'a ya tsare gabanka da bayan ka." Yace Ameen ya kalli Umma yace Umma a gaida su Jamila da Abba. Tace zan faɗa musu Allah ya bada sa'a da rabo mai amfani. Yace Ameen Umma na gode. Na bishi da jaka ina jin takaicin banga ya ba Ummana komai ba har yana wani zai jira su gaisa, a zuciya ta nace sai na roƙe shi yau koda zai hana ni. Sai da mukaje falon da nake tsayawa, na haɗe girar sama da ƙasa, ya sa hannu ya ɗago fuskanta yace "Me kuma aka ce ya faru Baby?" Nace ce ina son in bawa Ummana wani abu na tsaraba koda kuɗi ne ta saya wa ƙanne na ,amma na kasance bana maganin ko sisi. Cikin shagwaɓa na yi maganar. Ya kwaikwayi muryata yace, "Na ba Hajiya saƙo zata ba Umma shike nan?" Kai masa ɗan dukan wasa nayi ina faɗin na gode. Ya saki fuska ta ya amshi jakar na ɗaga hannu nayi masa bye bye. Na dawo Umma ta aje abincin tana shan ruwa,na kalli naman kamar ma bata ci ba, nace Umma to ya baƙi ci naman ba kuma? Tace na ci Baby Allah ya amfana. Hajiya tace "Nima dai naga kamar bata ci ba, nan dai kamar gidan ki ne bakya yi fulako ba." Umma tace Alhamdulillahi ai na ci. Hajiya tace "To ko kuma dai a juye ta kaiwa yara dan kinga karnuka za'a baiwa?" Umma tace "Haba dai bazan ɗaukii abinci ba ga shi can a gidan, zuwa zanyi ma in tafi,ƙarfe biyu Abbansu y ace in dawo. Gashi naga ɗaya da rabi ta gota. Hajiya tace "To kuma baki shiga ɗakin nata ba, ga mamakina sai naga Hajiya ta miƙe tana faɗin "Muje in raka ki, nima ban taɓa shiga ɗanikinsu ba, me zakaje ka yi a ɗakin yaro." Umma tace gaskiya dai, bare ko yaushe suna dabdala a nan gurin ki. Tace haka kuwa. Mamakin Hajiya ya hana ni magana ina biye da su ina tunanin. Hajiya dai ƙila dan kar mu tattauna wata maganar da Ummane ta yi wannan katan katan ɗin ta ƙi bamu fili ko kuwa kulawa ce da mutuntawa ta yi wa Umma.? Bani da amsa dan haka naci gaba da binsu. Ta nuna wa Umma ko ina tun daga banɗaki har saura ɗakunan Umma dai tana ta addu'a da fatan alkhairi Sannan suka zauna a kan kujera,na zauna a gaban su kamar mai nema gafara,Umma ta fara magana. "To Hajiya masan dai kuna ta haƙuri da ƙuruciya,yaran yanzu sai anyi haƙuri, a daure ana tsawata mata in tayi ba daidai ba a sata a hanya na hukunci kuma a yi mata ba sai an sanar da mu ba,. Allah ya sa mutu ka raba tsakanin su." Hajiya ta amsa da Ameen, ai ita Rabi'atu bata da matsala yarinya ce mai biyayya laifin ta da nii ɗaya ne. Na zaro ido cikin faɗuwar gaba domin inji laifin nawa. Taci gaba da fadin Duk yadda yarinyar nan zata so mijinta ba za ta yi ya ni Uwar da na haife shi ba Haka ne?" Umma tace "Ko alamar ƙafar ki bata kama ba." Hajiya tace madalla, to wai yarinyar nan nace ta shirya za'a kaita gidan wani malami wanda zai bata taimako Allah cikin ikon sa sai yadda ta yi da mijinta, kina kallo gata dai a cikin irin wannan gida amma bata maganin kwabo ɗaya,ko kina da shi?" Na girgiza kai tare da faɗin bani da shi. Tace yanzu dubi ke ba surukarsa bace, da fatar baki yace miki ki gaida gida,zancan gaskiya hakan ya kyautu?" Umma dai bata yi magana ba. Hajiya ta ci gaba da faɗin. Nasan har maƙota da wasu a dangi sai sun yi da ku,suce 'yar ku tana aure a gidan Alhaji Baita amma har yanzu kuna nan jiya i yau. Koma ace laifita ne ta yi aure gidan daula ta mance da ku, wasu ma cewa za suyi ana baku kun ƙi nunawa ne dan kar ku sammusu, maganar haka take?" Umma tace haka ne. Hajiya ta nuna ni da yatsa tace, "To kinganta nan fir taƙi zuwa gidan malamin har da ɗauke min ƙafa ina hankalce da ita,in ba mijin ta ne a gurina ba ta daina zuwa tunda ta san ba yadda za a yi in yi mata maganar a gaban sa. Ita bazata gurin Malami ba,ba kyau ba sai an mallake shi ba. Jifa sokonci. Kuma ita hakan zai wa amfani,nima kuma ta ɓangare na wani abin in zai min gaddama sai in bi ta hannunta kin san dai ɗan yau." Mamakin Hajiya ya sa na kasa daina kallon ta, ko dai so take Shamaki ya fara yi mata sujjada. Mutumin da kara in ta aje ba zai taɓa tsallaka shi ba. Muryar Umma ta katseni, tayi gyaran murya sannan ta ce, Wato Hajiya ni ma dai a nawa ganin sam bai kyautu Baby ta kai sunan mijinta gidan malami ba koda baya iya sauke hakkin da Allah ya ɗora masa nata na aure. Balle duk maganar nan ana yinta ne game da wata kyautatawa wadda in bai yi ba Allah ba zai kamashi da wani laifi ba. Babu shakka ban goyi bayan wannan abin ba. Kuma wai ma Hajiya dan mutane za su ce ko maƙota za su yi damu, Allah na tuba zaka hana bawa ya ɗauki zunubi ne, kace dole sai ya yi aikin lada? Kinga kuwa bamu isa mu hana a yi munafircinmu ba, kuma ko da me kuka bamu Hajiya wannan ba zai hana mai magana ya yi magar shiba. Dan haka don Allah Hajiya kar a nuna mata wannan hanyar, kinsan yaran zamani wataran sai ta tafi da kanta neman wata buƙatar da zata ɓatawa kowa rai. Munriga mun ɗora ta a hanyar sallar dare,in wata damuwa ce ta faɗawa Allah,kuma ta ke yi wa mijinta addu'a Allah ya tsare shi. Ta dubi Hajiya wadda ta zuba mata ido tace, ki yi hakuri in na faɗi ba dai dai ba. Amma shawara ta ƙarshe ku barshi ya ji da masu jiran shi na waje,kinsan 'yan kasuwa ba'a raba su da magauta, a gida sai a tsananta addu'a bare ta ku Hajiya, bakin Mahaifiya ya sha gaban bakin duk wani malami." Hajiya ta sauke ajiyar zuciya ta ce "To ai shikenan tunda kin goye mata baya, na kyale ku ,yanzu ita ko dan kishiyoyin da suka fita ko wasu da zasu shigo bakya bata ƙwarin gwiwa ta amshi taimako ba?" Umma ta yi 'yar dariya tare da faɗin mijin mace huɗu kuma a tauye shi da mace ɗaya Allah ya rufa masa asiri. Ai Hajiya duk namiji da burin aure ya ke mutuwa saidai in Allah bai ƙaddara mishi ba. Dan Allah ina neman alfarma Hajiya a bar zancan gidan Malamin nan, Abbasu in yaji ba ita ba har ni zai saɓa min ƙwarai. Juma ta ƙwanƙwasa ƙofa da sallama . Hajiya tace ta shigo , ta miƙo wayar Umma da ta aje a inda ta zauna a falo, tace "Ana ta kiran wayar ne." Umma ta amsa da sauri tana faɗin Abban su ne.Daidai lokacin kiran ya sake shigowa. Ta ɗaga tana faɗin yi haƙuri wayar tana can sitirum ne mu kuma gamu a cikin ɗani. Muna jiyo murya Abba kasancewar wayar Umma ta samu matsala ko yaushe murya a buɗe ta ke. Yace "Kenan shantakewa ki ka yi a gidan yarinyar ke da na baki ƙarfe biyu yanzu saura mintina ko baro gidan nakiyi ba." Tace yanzu zan taho muna 'yar hira ne da surukarta kaga gata ma ku gaisa. Yace to bata, suka gaida shima dai ya bada haƙuri akan cewa su yi haƙuri da ni in har na yi ba daidai ba. Suka yi sallama yace da Umma ta gaishe ni, kuma ta taho domin gashi nan zai koma gidan yanzu. To haka dai muka sake fitowa gaba ɗaya,domin Hajiya bata da niyyar bamu guri, muka dawo Falon Hajiya. Umma ta miƙo leda mai layi layi tace ga tafarnuwa da kayan ƙamahi Hajiya, tsarabar ce sai na rasa me zan kawo muku tunda Allah ya sa kuna da komai. Hajiya tace "To muna godiya Allah ya saka da alkhari. Hajiya ta dube ni, "Shiga ciki kan gado ki ɗakko mata Envelope ta sayawa yara alawa a hanya. Ta dubi Juma da ke kwashe kayan abinci tace "Je ki faɗawa direba zai maida baƙuwa gida. Har mota na raka Umma sai da naga motar ta bar harabar gidan sannan na dawo ciki. Hajiya ta kalle ni, ke ce "'yar fari ko?" Nace E. Hajiya. Tace. "Naga itama yarinya ce mahaifiyar ta ki. Nayi Murmushi tace "Gurinta ki ka samo wannan shegen baƙin wayon ko?" Nayi 'yar dariya nace bari in shiga ciki. Na yi wanka na yi salla naji daɗin zuwan Ummana duk da Hajiya ta hana mu sakewa. To wai ita Hajiya domin kar in faɗawa Umma cewa Shamaki zai ƙara aure shine ko kuwa dai tana zaton zan faɗawa Umma cewa bata min yadda kamata ne? Bani da amsa don haka sai na tashi na ce bari in kira Umma inji ko sun isa gida. Na faɗa kan gado na, na ɗauki wayata na kira layin Umma, ta ɗaga tace "Yanzu fa na ke shirin kiran ki in faɗa Miki cewa Dubu Hamsin ne a 'yar takarda nan da Hajiya ta bani." Na ja dogon numfashi nace amma angode Allah ya saka da khairan. Gashi bamu samu minti hira ba. Tace "To wace hirar ma zamuyi ko kina da wata matsala ne?" Nace "To ba dai wata ƙatuwar matsala bace amma dai an saka mishi ranar aure da wata yarinya 'yar uwarshi, tana nan a gidan ko da kika zo tana ciki bata fita ne hatta makaranta ta daina zuwa. Umma tace "Tofa! Amma kin san abinda nake so da ke?" Na ce A a,Tace ki kama kanki ba ruwanki da auran sa. Sannan hanyar da da maganar gidan malami da Hajiya ke yi duk yadda aka yi so take ta gwada ki, ko dai wani abu mai kama da haka. Nima baki ga ta latsa min basira ba, kar nake kallon ta. Wata uwa ce zata ce a kai ɗanta gidan malami ki kiyaye sosai wata kitimirmira take haɗawa. Kuma ki ke nazari ko magana zaki furta domin na lura cewa 'yar shan loga ce, ga ta da alaye. Sannan karki taɓa damuwa da abinsu. Baki gani ba,naman nan ina son inci shi amma ina jin tsoro kar in bar miki abin faɗa dan haka na kauda kai daga gare shi na haɗiye kwaɗa yi na. Nayi dariya nace zan kiyaye Umma, tunda ga kuɗi nan kin samu sai ki siyo muku mama ku dafa. Tace wannan kuɗin zan ciri jari a ciki in ba Abbanku dubu goma shima. In sai wa Jamila tukwane, ba zan bari in maimaita kuskuren da nayi a baya ba a bikin ki. Nace haka ne Allah ya rufa asiri. Tace "Ameen dan Allah kar ki saka maganar aurannan ya dame ki, ke dai kiyi ƙoƙari ki iya allonki. Nace Insha Allahu. Muka ɗanyi shiru can tace ina ganin fa kamar kin ƙara ramewa, anya babu wata matsala bayan wannan?" Nace babu, ai nayi zazzaɓi ne kwanaki harna kwanta a asibiti amma nayi ƙiba, sosai. Tace Allah ya ƙara lafiya, yanzu dai ki kwantar da hankalinki. Nace to Umma. Bayan mun yi sallama na yi shiru ina tunani, yaushe kuwa zanyi wata ƙiba a gidan nan tunda nayi kuskuren duba wayar mijina. Kuma gashi abin ya zame min masifa ko na ce bazan duba ba sai na duba. Gashi dole in haɗiye duk abinda na gani a cikinta tunda bani da damar fadawa wani domin in samu salama. Duk da cewa ina bukatar shawara amma bansan wa ya kamata in nema shawara ba, wanda asirina zai rufu. Zan ci gaba da miƙawa Allah kuka na shine mafi girman wanda zai bani mafita. Azumi ya gabato bai fi sauran kwana tara ba, Shamaki baya samun zama yawanci sai na jima da bacci ya ke shigowa. Suna ta fama da lissafi za su cire Zakka. Za su tafi Umara,ita Hajiya acan zata yi Idi shine zai dawo kafin lokacin salla, amma sai an fara azumi da sati biyu zasu tafi. Sun fara rabon zakka ina zaune ina jin su ana lissafin, masallatai da za'a kai miliyoyin kuɗi. Sai kuma wasu marasa ƙarfi, sai dangin su da za a baiwa dubu ɗari ɗari a Envelope da kayan abinci. Yayinsa kowa ta zo ta kawo list na mutanen da take son a taimaka. Ni kuwa matar gida ko oho,ina zaune bana maganin ahu, ko kitso da ƙunshi ko wanke kai saidai direban ya kai ni in turawa Hajiya account ta turo musu kuɗin. Ɗinki kuwa da yace in bada kayan cikin lefena duka a ɗinka da na faɗa mata zan kai ɗinki Unguwar mu sai tace a a,ta sa Maman Iman ta kawo tela har gida ya gwadani ya kwashi kaya, sai dai ɗinki na gani bani da wata hanya da kwabo zai shigo min duk wani abu da nake buƙata za a kawo min. To irin wannan uƙuba ta rashin kuɗi dan ma dai dama can ban saba riƙewa ba bare in damu sosai. Ina kwance sai ga Juma wai inzo inji Hajiya. Na same ta a hakimce kamar kullum da carbi tana ja, ta bini da kallo har na fara tunanin ko nayi wani abu ba daidai ba. Na tsugunna nace Hajiya gani. Ta nuna gefen ta da yatsanta, "Ki ƙirga min wannan Envelope ɗin guda nawa ne." Na ce To. Na ƙirga guda ashirin ne. Tace "Dubu ɗari ɗari ne a ciki ina son ki rabawa mutum irishin ma su buƙata ciki harda su Juma, sannan yanzu zan saka Juma ta je ta rakaki can baya inda kayan abincin zakka su ke, na azumi , ki raba su ga masu buƙata. Na zaro idanu ina faɗin Hajiya bazan iya ba." Ta ɗago ta dube ni cikin gimtsewar fuska,tace kina auren Shamaki amma baki san yadda ake raba taimako ba? Na kalli Juma wadda ta min alamar inyi shiru da ido. Na maida dubana ga Hajiya wadda ta kuma tattara hankalinta ga carbin da take ja. Na miƙe na ce Juma muje ki nuna min..... .... Muka fita can wata haraba ta bayan gidan ina ta tunani yadda zan bigi cikin Juma. Nace wai kuwa Baba Juma a ina ake rabon kuma suwa da wa ake baiwa.? Tace "To kowace mace dai da yadda ta ke rabon ta wata ta yi a cikin gida wata kuma a waje amma can da dai a cikin gida ake yi kuma ba a taruwa, yanzu dai naki sai yadda ki ka yi da shi." Nace kina nufin duk sauran matan sun yi irin wannan rabo? Juma ta ja baya ta riƙe ƙugu sannan Tace "Babu wadda ba ta yi irin wannan rabon ba." Nace ni damuwar ban san su wa zan baiwa ba. Kuma yaushe zan bayar? Tace "wannan duk yadda ki ka yi Hajiya bata da matsala da haka, in kina so ma zaki iya bari sai sun tafi Ummara sai ki yi yadda ki ke so." Na kalli Baba Juma tabbas tana min wani irin kallo mai kama da shurin jeki ki mutu. Muka ƙarasa wani ƙaton store narke da shinkafa 'yar gwamnatin ga taliya da makaroni Suger Indomie da sauran kayan abinci na azumi. Na kalla nace taɓɗi gaskiya in wannan aikin yana cikin jarabawar Hajiya ba shakka dole a faɗi. Muka dawo ni dai ranar haka na yini ina nazari Na ɗauki waya na kira mijina Shamaki ya ɗaga cikin sauri yace "Menene yi magana meeting zan shiga yanzu." Nace to dan Allah ina son magana da kai in ka fito. "Ki kira ni ƙarfe Shidda na yamma." Bai jira amsa ta ba ya kashe wayar. Na ce kai nima fa ina da uwa,duk Duniya ita ce take min son da ba wanda ya ke min makamancin shi, dan haka ita ce zata bani mafita kamar yadda ya ke tutuyar ta shi uwar tana sama mishi mafita. Na ɗaga waya na kira Umma, Muka gaisa nace Umma dama wani yanayi na samu kaina ina buƙatar wanda zai tsaya min har komai ya yi kyau "To kuwa wake gare ki bayan mu Baby?" Ta katse ni. "Menene faɗa min. Na kwashe komai na sanar wa Umma sannan na tsaya sauraron ta. Tace abu na farko yanzun ki je ki samu Hajiya ki ce abaki list na mutanen da za su amfana da wannan zakkar in ta baki sai mu sake yin magana." Na zo bayan la'asar na samu Hajiya tana kallo na zauna na gaishe ta,sannan nace Hajiya dama list za a bani na waɗanda aka saba baiwa wannan taimakon. Hajiya ta ɗago ta dune ni kamar zata yi magana sai kuma ta kauda kai, sannan ta ɗaga wani fayal ta ciro wata doguwar takarda mai ɗauke da sunaye a jere tace "Gashi." Na amsa,nannan na nace yawwa Hajiya dama su waɗannan kuɗin na cikin... Ta ɗaga min hannu duk yadda ki ke buƙata haka zaki yi abida ya sa na baki list ɗinnan saboda kin tambaya ne,da baki tambaya ba bazan baki ba." Na ce To na gane. Na koma ɗaki ina me alfahari da uwata na zauna na duba list mutum ɗari harda uku. Na kalli kuɗin aka durowar gefen gado na, nace gashi kuɗin na mutum ishirin ne. Naira miliyan biyu ne ta riga ta raba kuɗin bare ince a rage su yadda kowa zai samu. Na sake duba takardar sosai ko a kwai sunayen da zanga anyi musu alama amma bangani ba,na kuma kiran Umma na faɗa mata ga halin da ake ciki. Tace "To abinda za ki yi ƙoƙari ki gano shine waɗanda za a baiwa wannan dubu ɗari ɗarin domin tabbas na wasu ne daban kuma ana haɗa musu da kayan abinci sauran mutanan kuwa sai ki kira su tunda akwai suna da kuma lambar waya sannan ki tabbatar ba ki ba wani naki ko mu wannan kayan abinci da kuɗi ba." Nace Haba Umma hauka ake, duk yadda za ayi dole in cire muku kuma,shirme kenan zan yi cewa fa aka yi duk yadda nayi daidai, banda ma tsoron Allah harni sai na ɗauki kashi ɗaya. Umma tace "Baki da hankali, ko ƙwayar gero kar ki sake ki aiko mana da shi. Ki bi list ɗin da ta baki, abinda za kiyi kawai shine ki ki fara da kiran lambar farko kiji waye a haka sai ki ware waɗan da zaki ba kuɗin, amma ki bari sai ranar lahadi tunda kince baya fita da wuri." Nace to zan yi haka amma zan kira su kafin ranar in sanar musu Da safe da naje gaida Hajiya bayan na gaishe su har zan miƙe sai tace "Ranar yaushe za ki yi rabon zakka?" Na sunkuyar da kai nace ranar Lahadi. Tace "Nan da kwana hudu kenan me yasa ki ka kai shi har wannan kwanakin?" Nace ina son in gano suwa za a ba wannan kuɗin ne. Ta ɗan yi jim sannan tace shike nan Allah ya taimaka. Shamaki ya matso kusa da kunne na "Jiya me ki ka sha ne na yi miki tashin duniyar nan amma ki ka kasa tashi?" Na rage murya nace na yi shaye shaye jiya irin su ruwa da lemo.muka sa dariya. Nace na jira ka har kusan ɗaya baka shigo ba,bacci mai nauyi ne kawai. Yace "Dama maganar da kika ce za mu yi ce na so in tashe ki." Da gefen ido na kalli Hajiya kuma na gane hankalinta yana gurinmu. Nace ba fa wani abu bane,kawai ina so ne inji muryar ka, ko zanji sanyi a zuciya ta. Yace "Zafi ta yi a lokacin?" Nace ƙunar sonka ba. Ya ɗan kai min dukan wasa,yace Me wayo zaki faɗa min gaskiya bari in shigo. Na tashi na koma ciki. Na ɗauki takardar ina ƙara kallon ta. A fili nace banda Hajiya ta so wahalar da ni, ai da sai tace kawai da sai ta faɗa min cewa kuɗinna wane da wane ne. Na kira lambar farko Na miji ya ɗauka kuma da alama dattijo ne. Muka gaisa, nace daga gidan Alhaji Baita ne don Allah da wa nake magana? Sai aka ce "Da liman ne mai jan salla a masallacin gidan. Nace to ranar Lahadi za ka karɓi saƙo. Yace to Allah ya kai mu." Bayan mun gama waya nace ina ruwa na Allah duk wanda yake sahun farko shi zan ba kuɗi kuma in haɗa masa da abinci. Na kira na biyu shima na tambaya kamar yadda na yi na farko. Akace wacece baki gane da wa ki ke magana ba? Nace Matar Shamaki ce. Sai yace auto Babanku ne ƙanin Hajiya. Nace Baba ranar Lahadi za a bada saƙo, yace to "yar nan mu zamu zo mu karɓa? Nace Baba ya ake yi muku ne kawowa ake yi ko ku ke zuwa? Yace "To shekarun baya dai can kafin rabon ya koma hannun matan Shamaki direba ke kawo wa Bama sanin cewa za a bamu amma daga baya sai ace mu zo mu karɓa." Cikin zumuɗi nace acan baya ɗin me ake baku ne Baba? Yace "A can baya dai dubu dari da buhun shinkafa da suga da gero. Nace to Baba bana ma ba sai ka zo ba, za a kawo maka kamar yadda ka lissafa. Yace to Allah ya yi albarka. Nace Ameen yace akwai wani ƙanenmu a ƙauye shi an daina bashi ma gaba ɗaya,kuma da har shi Hajiya ke bamu. Nace to za 'a bashi ya zo ranar lahadi ko shima kauyen ake kai masa da? Yace A'a gidan yake zuwa. Nace to. Wato ashe dai lissafin Umma haka ne da nayi ta bin lambar har shi na ƙauyen nan na samu lambar ɗansa, sannan sai ga su Juma na kira ta ɗaga tana cewa wacece? Na ɗauki murya nace Baba Juma ce tace e, sai kawai na kashe domin na gane. Munan duk makusantan su ne 'ɓangaren Alhaji Baita da ita Hajiya Zeena, sannan 'yan aiki. Bayan na gama da ishirin ɗin nan sai na koma in gano sauran me za a basu, nace irin dai wancan tsarin zan bi innaji a bakin mutum ɗaya shike nan. Na kira wayar na ishirin da ɗaya. Muka gaisa mace ce, nace an kirata ne daga gidan Alhaji Baita,tace to Hajiya ce ina yini,ta sake gaida ni cikin girmamawa. Nace na san kin sani zakkar abinci ce ko? Tace e nace me ake baku ki faɗa min gaskiya domin akwai waɗanda za a soke sunan su in sun faɗi ba daidai ba. Tace tsakani da Allah da dai can ana bamu shinkafa gero sai suga mu biyu buhu ɗaya ni da wata itama 'yar uwarmu ce, kuma ana bamu taliya. Nace kuma 'yan uwan Hajiya ne? Tace a a mun yi aiki shekarun baya can tare da Hajiya Gwamma mahaifiyar Alhaji Baita lokacin muna ƙananan yara, shine Hajiya Zeena ta riƙe alƙawari ake bamu, duk shekara sai anzo har gida an karɓi lamba. Amma 'yan shekarun nan gero ake bamu da shinkafa. Wannan lambar ki ce? Tace ta jika ta ce. Nace ku zo ranar Lahadi tace sai dai in turo jikata Dan ni sai bakin da kunne ba ido ba ƙafa, Nace Kaka ya sunan jikar ta ƙi? Tace "Mairamu zan turo ita mijin ya mutu ya bar ta da 'ya'ya." Nace ki faɗa mata in tazo tace tana son ganin matar Shamaki. Tace to zan faɗa mata, inaha Allahu 'yar nan ke ce matar Shamaki ɗin?" Nace E ni ce Kaka. Tace Ikon Allah ɗannan tun yana goye rabon da in gashi. Na yi dariya muka yi sallama. Haka nayi ta kira ina sanar da su suzo ranar Lahadi har na gaji na yi makin ɗin inda na tsaya. Washe gari sai da na gama komai mijina ya fita sannan na koma na ɗora, zuwa washe gari duk na gama sanar da kowa. Ranar asabar na idar da sallar azahar ina kan sallaya ina danna waya na ga ansani a wani group na duba admin ɗin sai na ga wata 'yar ajinmu ce ta boko Basira Ashiru na sake duba sunan group ɗin sai naga an saka Gandu 2019 nace la group ɗin 'yan makaranta, gaskiya na ji daɗin domin za a sada zumunci. Wayar gida ta katse min tunani da ƙara, na san Hajiya ce, na daga na gaishe ta. Ta amsa, sannan tace, "Kina ji na ko?Ki fito ga waɗanda zasu taya ki aikin gobe sun zo, ki zo ki basu Umarni yadda za su miki aikin." Nace To. Na samu maza majiya ƙarfi su biyar. Suka gaishe ni cikin girmamawa har naji kunya. Hajiya tace ki je ki basu abinda za suyi su fara tun yanzu, bana son sai gobe a cika mana gida kamar kasuwa fatan kuma ki fidda tsarin da wani ba zai amsa so biyu ba. Nace Insha Allahu. Na dube su nace muje can gurin da kayan abincin suke. Suka fita dan su zagaya. Dama da hijabi na na fito sai na koma ciki na ɗakko takardar sannan na ɗakko wata takardar da biro na dawo na bi ta kicin na ce da Baba Juma ta zo muje... 🖊️🖊️🖊 ️Na nuna musu abincin nace ina son su ware min buhun shinkafa guda tamanin, ko wanne su saka taliya da makaroni da gero sannan ina son su ware min suga buhu arba'in. sannan su cire min ashirin, shima su ware su sa taliya da makaroni da gero da buhun suga in sun gama ina son su faɗawa Juma ta sanar da ni. Juma ta kalle ni. 'yar nan jiran su zan har su gama kafin in koma ciki?" Nace kije za su sanar da ke in sun gama. Tace "Ko da dai bari in tsaya in yi gadi domin kar ace ba wani buhun lissafi ya sha banban." Ɗayan ciki yace tsohuwa nan da ki ka ganmu duk ciki babu ɓarawo, da sana'ar mu inda halin mu ke nan Hajiya ba za ta ce Alhaji ya turo mu ba, duk shekara mune ke yin wannan aiki. Kuma ko a kasuwa mu ne 'yan dakon kayayyakin Zeena. Tace to naji Allah ya baku haƙuri amma dai ina nan sai kun gama. Na tafi ina dariya. Nace Baba Juma ho! Ina sako ƙafa falon Hajiya naji tana waya dan haka na dawo na tsaya tsam ji nayi tana faɗin. "Saurara kiji Aminiyata, ni dai na gama yanke nawa hukunci kuma dai kinsan dole duk yadda na dama a gidannan dole kowa ya sha shi haka,har yanzu ina kan bakana in yarinyar nan ta faɗi jarabawar nan ba zan ji nauyin sawa a sake ta ba. Duk ba wanda ya san dalilina. Taɗan yi shiru tana sauraron wancan ɓangaren sai ta yi murmushi mai sauti. Tace "Ya za 'ayi in daɓawa cikina wuƙa to kinsan halin kishi watarana ai gora mata zata yi,ban bari ta san maganar Azima ba,ita ma Juma na ja mata kunne shikuwa ai ba yadda zai yi duk da bashi bane ai dole ya aureta a haka. Ina ba so nake kimata ta ragu ba na gama cika baki ta baɗan ƙasa a ido ai ba yadda za a yi in fidda wannan zancan. Yanzu tunanin da nake kar inyi tafiyar nan ta ke sa ƙafa tana fita ta ƙara ɗakko min wata maganar ko iyayen ta fa banbari sun ji maganar ba, na cika baki akanta da yawa sai gashi ta kunyata ni. Abin ya min ciwo da yawa." Ta yi shiru tana sauraro sai tace "Haba Hajiya Zaliha ki na yi kamar baki sanni ba ne, ai ba batun jarabawa akan Azima me zan jaraba kuma baya ta riga ta faɗi warwas na faɗa masa dai ya zauna da ita 'yar uwarsa kuma matar sa, banda a gidana take abinnan ya faru wallahi ke kinsan ni sarai bazan taɓa bari ya aureta ba." Ta kuma yin shiru can tace Ke kinsan itama akwai maatuƙar wahala ta tsallake ta wannan jarabawar ko ta tsallake komai ba zata iya tsallake ta ƙarshe ba, har zuwa yau ni kaɗai na san dalilin jarabawar, shi kuma dole ya sake ta, domin dai shekara guda in suka kwashe kinsan lokacin namiji ya fara gajiya da mace, yadda ya saki sauran ko a jikin sa haka ita ma zai mata. Daɗi na ɗaya ita ko cikin har yanzu shiru. Amma na kula ita wannan har yanzu bai kawo min ƙarar ta ba,duk da hakan baya cikin sharuddan jarabawa ta amma dole in bata makin su." Sai ƙaran ɗaya wayar ya shigo na ji tace Hajiya Zaliha sai mun sake magana bari in ɗaga wata wayar. Nayi tsam jikina duk ya yi sanyi ba shakka ba zan tsallake tarkon Hajiya ba, gashi ina son mijina tunda shi har zuwa yanzu banda maganar neman matan shi bani da wata matsala da shi. Ba dama in wuce, dole in bari ta ɗanyi nisa a wannan wayar, sai in fito kar ta gane cewa ni ɗin nayi mata laɓe. Da alamu suna magana da Shamaki ne aka batun tafiyar su,dan haka sai kawai na fito sai da na zo kusa da ita sannan nayi mata sannu, da kai ta amsa na wuce ɗakina. Sukuti na yi a kan gado yanzu zamu rabu da Shamaki da gaske! A fili na furta gaskiya bazan iya ba, ya yi min alƙawari ba so ɗaya ba, amma ya kamata inke tuna masa da wannan alkawarin da ya ɗaukar min akai akai. Kamar awa ɗaya da shigowa ta ɗaki na kira shi,ya ɗaga na soma ɗan kukan shagwaɓa yace "Wai me akayi ne kuma zaki ɗaga min hankali?" Nace Dan Allah wai zaka sake ni? Yace "Injiwa kuma?" Nace bacci na yi yanzu sai na yi mafarki wai Hajiya tace sai ka sake ni. Yace "To na sake ki ɗin a cikin mafarkin na ki?" Nace 'a 'a kana ta bata haƙuri ne sai tace me yasa zaka yi mata gardama shine kace ka ɗaukar min alƙawari tun kafin aurenmu har ka fara tuna mata girman alƙawari, shine ta ce ta janye. Sai naji ya sauke ajiyar zuciya,yace ba abinda zai sa in sake ki Baby." Nace Alƙawari yace "Alƙawari." Sai kusan ƙarfe biyar Juma ta zo tace sun gama na fito naje na gani yadda nace haka suka yi, abin al ajab sai gashi wani abu guda ɗaya bai rage ba, wannan ya tabbatar min haka rabon nan ya ke. Nace dube su nace ku menene sallamar ku? Suka ce sai abinda aka bamu. Nace to ku zagaya mu haɗu a gurin Hajiya. Na tsugunna agabanta nace sun gama menene sallamar su? Hajiya ta dube ni, wannan baya cikin huruminki in dai sun gama miki aiki to ki turo min sunan. Namiƙe dai-dai lokacin da suke shigowa. Su Juma su uku ne mata masu aiki a gida da haka na basu kuɗin su sannan na nuna musu kashin da za su ɗauka wato mai suga buhu ɗaya. Juma tace 'yannan kin gaji Hajiya, wannan shine rabon da Hajiya ta ke bamu kafin zuwan matan Shamaki, insha Allahu zaki lashe jarabawar ki, ke ce mandiya matar gida, jinki ya fi ganin ki,ga ki ƙarama sai tarin basira. Ta yi ƙasa da murya 'yata saboda jin daɗi zan miki wani taimako guda ɗaya,kina jina?" Na tattara hankali na gare ta. Tace" ranar ƙarshe ta jarabawar ki da baki Hajiya zata yi muku tambayoyi anan duk wata ƙullaliya ta ke, ina son ki tabbatar kin san waye Shamaki kafin wannan rana." Wannan gudunmawa ta ce nima zuwa gare ki,amma karki tambaye ni waye Shamaki domin bansani ba, kar ki kar ki tambaye ni wanda zai sanar da ke." Na yi shiru ina mamakin irin wannan abu, ni ko lokacin da na yi karance karance ban taɓa dubo irin wannan almarar ba. Tace kin ji mamaki ko? To kar ki tsaya mamaki kiyi ƙoƙari ki samu wannan bayani. Ta wuce na bita da kallo a fili nace kai jama'a Ni kuma irin tawa ƙaddarar ke nan. Washe gari tun bakwai na fito bayan mun gaisa da Hajiya nace zan fita gurin rabon nan in sake bin sunayen in tabbatar kowa ya samu kashin sa. Tace min, hakan yana da kyau, Juma ta faɗa min abinda aka basu Allah ya saka da alkhari. Na sunkuyar da kai nace Hajiya ku za a yi wa godiya, Allah ya sa a ɗauka a gidan Aljanna. Tace "Ameen, amma me yasa ki ka haɗawa su Juma da kuɗi? Nace to ni dai a ganina su makusanta ne,kuma duk da ana biyan su hidimar da suke mana an so ka fara zakka da makusantan ka,sannan ka kyutata musu shine kawai dalilina. Tace "Allah ya amsa." Nace Ameen. Haka mutane suka yi ta zuwa kujera na saka na zauna duk wanda ya kira waya sai ince ya shigo ya faɗi suna da lambar waya,kafin ya ɗauka kuma zaije ya yi wa Hajiya godiya a falo wannan shima tsari na ne.Direba kuwa ya kai na bashi na Liman da na Kawu, kuma bayan ya dawo na kirasu su suka tabbatar min da cewa an basu wannan kuɗi. Na ce to su kira Hajiya su yi mata godiya. Rabo dai bai tashi ba sai ranar Litinin muka gama, matar da tsohuwar nan ta turo tace min dan Allah tana son ganin matar Shamaki, sai na tuna ni nace ta neme ni. Na tambaye ta unguwar su tace min a Fage suke ta min kwatance na yi godiya muka yi sallama. Bayan ta kwashi kayan ta. Bayan an gama komai kashi uku ya rage biyu masu kuɗi ɗaya mara kuɗi na samu Hajiya na sanar mata cewa ga kashi uku ya rage kashi ɗari kuma kowa ya ɗauka ga jerin sunayen su da lambobin su da kuma saka hannun su cewa sun amsa. Na bata tsohon list ɗin da ta bani da sabon da na yi da sauran kuɗin dubu ɗari biyu. Tace "Iyayen ki fa kin ba su?" Nace ai ba sunan su a list. Tunda kuwa basu ai maganar ba su bata taso ba. Hajiya tace to wannan uku sai ki ba su shine dama na su. Na sake durƙusawa ina godiya,nace to sai a baiwa Ya'yan Abban mu ɗaya shima Abban mu ɗaya,ɗaya sai a baiwa dangin Umma su raba hakan ya yi?" Tace duk yadda kika yi dai dai ne ni bansan 'yan uwanku ba. Na kira Umma ina murna na faɗa mata.nace Umma an gama rabo lafiya,ga naku ya za ayi rabon na faɗa mata niyya ta. Tace ba haka za a yi ba, shi Abbanku ya hi ɗau ɗaya,ɗayan Abban zuhra ya ɗauki kayan abinci kuɗin kai Annan ku ya rabawa sauran ƙanan sa, maza da mata kowa ya sheda ya shi albarka, sauran kayan abincin suma 'yan Kurna su sheda. Nace to zan aiko direba gobe duk yadda ku ka yi dai dai ne. Ranar azumin farko a falon Hajiya muka sha ruwa duk gidan domin a nan muka bi salla dan haka kawai nace Juma ta barmin abinci na a nan,haka su Anisa sun kasance da mu duk da su ba azumin suka yi ba. Azima ana idar da salla ta koma ciki. Abin ya birge ni banya da muka gama sallar asham na koma ɗaki dan in yiwa su Umma sannu da shan ruwa. Cikin satin Shamaki ya zama cikin yi musu shirin tafiya. Ana jibi za su tafi Hajiya ta kira ni. Tace min nauyi ya hau kanki na kwanakin da zanyi kafin in dawo, duk wani abu da ake bukata ke zaki samar da shi a gidan nan. Ta ciro ATM kati ta bani,ga wannan katin duk wata hidima ta gidan nan a cikin wannan asusun ake yin sa, yau sha biyar ga watan bature zaki biya dukkan ma'aikatan gidannan kuɗin su a ranar ashirin da biyar ga wata. Hidimar salla da abincin salla duk ke zaki samar, haka duk wanda ake ba goron salla zaki bashi, 'yan uwan Shamaki wadda duk bataje Ummara ba,nan zata yini da yaranta. Dan haka ki kula sosai ki mu'amalanci kowa da kyau bana son in dawo in samu wani ƙorafi ko da na mutum ɗaya ne. Nace To Hajiya insha Allahu zan yi bakin ƙoƙarina. Tashin magariba za su yi ranar Shamaki bai fita kasuwa ba, na gama shirya masa komai na tafiya. Yace "Na so ace tare zamu tafi Baby." Nace Allah bai kawo lokacina a yanzu ba, in kaje ka saka ni cikin addu'o'in ka, Allah ya amince inje wata shekarar. Yace haba Baby ai ya amince insha Allahu. Ni addu'a zanyi ina dawo wa in samu in baki cikin Zeena 'yar mitsila." Nace wai kuwa in tambaye ka mana. Yace "Ina jin ki." Nace meyasa duk yaran sunansu ɗaya ko Hajiya ce ke zaɓa musu? Ya kama kunne na ya riƙe da ƙarfi har sai da na yi ɗan ƙara yace, bansan ko so nawa zan baki wannan amsar ba, amma in na kama kunanki zaki fi riƙewa, ni na zaɓa musu wannan sunan in zan haifi yara mata guda ɗari duk sunan su Zeena in kuma maza ne duk sunan su Aliyu." Na ƙwace kunne na daƙyar, nace na haddace amma fa ka handame da yawa. Kenan bani da damar saka sunan Umma da Abbanmu? Yace baki da hurumin haka, wannan hurumin su Jafar ne." Yin hakan laifi ne? Na jefa masa tambaya cikin harar wasa. Yace Babba ma kuwa amma fa a gurin Shamaki." Nace To Allah ya bamu masu albarka." Yace kinji batu. Haka dai suka tafi har ina kuka ranar lokacin da zasu wuce. Hajiya tace, "Ba kuka zaki yi masa ba, addu'a zaki yi masa dan ga su Anisa nan bye bye suke yi masa ." Nace Hajiya kewa ce harda ta ku nake yi. Tace "Au to muna godiya. Ashe abin harda mu." Na dai koma cikin gida bayan sun suka wuce. Ni sabo ne da ni,ko ina naje in zan tafi sai na yi kuka. Na shiga ɗaki na zauna nace ni Baby wai gidan nan a hannu na yake sai yadda na yi da shi. Gashi babu wani cikakken bayani na sosai da Hajiya ta yi min bada kuɗin albashin ma'aikata. To kayan sallar ya zan samar da su,? Na miƙe. bari dai in kira Umma inji shawara sannan in samu Ba Juma in kallaɓa ta. Lokacin da zan kwanta na kira Juma na faɗa mata cewa ayi duk yadda aka saba,a bawa kowa abincin asbahi in ba wani abu a yimin magana. Tace "To Hajiya." Na kalle ta da sauri nace Kul Hajiya ɗaya ce a gidan nan bana son in kuma ji... ...... Da safe na kira Umma na ke faɗa mata hali da ake ciki game da gida da aka bar min, tace to ki yi komai tsakanin ki ga Allah sannan wannan katin na kuɗi kar ki kuskura ki taɓa ko ficika, duk abinda zakiyi ki ke rubuta an ciri kaza an sai kaza, ko naira hamsin ce ki tabbatar kin rubuta da kwanan wata da komai, domin in ta dawo zata buƙaci kiyi mata bayani, sai kawai ki ɗako ki karanta. Sannan duk wani mai aikin gidan ki keɓe da su ɗaya bayan ɗaya ki yi masu tambayoyi game da albashin su da kuma abinda ake masu a salla. Yaran nan nashi ki yi musu kayan salla da duk wanda ake yi wa." Nace to Umma sai dai abinda ke damuna wata magana da Juma tamin kwanan baya,tace wai Hajiya zata tambaye ni wanene Shamaki wai kuma in har ban sani ba,na faɗi gwajin ta, to ni da ba Allah musu su gare ni ba,yaya za'a yi in san wani sirri na su na ɓoye. Sai dai akwai wata mata a cikin waɗanda ake bawa sadaka da tace sunyi wa kakar Shamaki aiki wato uwar Alhaji Ali Baita, sai naji ina son inda tarihin asalin su,shine na tambayi kwatance sai kuma Juma ta yi min wannan maganar. Umma tace "Iko sai Allah, ni lamarin na ku kamar almara, to ai kuma akwai wata shekara da wani marubuci ya rubuta tarihin Alhaji Ali Baita har aka yi taron lancin na littafin a gidajan Radio aka yi ta sanar wa,me zai hana ki nemi littafin ki karanta,ba za a rasa shi a wannan gidan na ku ba." Amma ki bincika maganar kafin ki nemi littafin amma ba shakka na ji wannan da kunnen na. Na yi wa Umma godiya sannan na fita domin in tabbatar da komai na tafiya daidai. Kasancewar azumi ne kowa na bacci kuma yaran dama an basu hutu dan haka na ɗakko makullin ɗakin Mijina na nufi can na tabbatar in har an buga littafin nan to dashi a gidan, in kuma tabbas akwai shi a gidan to ɗakin Shamaki yana ɗaya daga cikin ɗakunan da ya kamata a ganshi. Ban wani wahala ba na ganshi a cikin wasu littattafai a durowar gefen gadonsa. WANENE ALHAJI ALI BAITA? Wannan shine sunan da ke manne a bangon littafin. Na kalli sunan marubucin Aminu Sani Takai. Na rufe durowar na dawo bakin gado na zauna na buɗa shafin farko an rubuta Babi na ɗaya. Na fara karanta wa kamar haka.. Alhaji Baita wanda Asalin sunan shi Aliyu ɗan asalin ƙasar Sudan ne ya shigo Nigeria a lokacin yana matashi ɗan ƙasa da shekara ashirin,ya zauna a gidan wani malami inda yake karatun ƙur'ani,daga nan sai wani attajiri mai suna Alhaji Sani Aliyu ɗan kasuwar kwari maƙocin Malam ya ɗauke shi a matsayin yaron shago bayan Malamin ya nemi alfarmar hakan saboda shi Aliyu ya faɗawa Malam cewa ya na sha'awar kasuwanci. Alhaji Sani shine ya sawa Aliyu suna Baita saboda irin sunan mahaifin shi ne ba zai iya faɗin sunan sa ba. Biyayya da gaskiya da amana ita ta sa Alhaji ya maida Baita babban yaron shi wanda ya san dukkan sirrikan shi kasancewar shi duk 'yayan shi mutuwa suke yi sai guda ɗaya tak Amina suna kiranta da Gwamma . Saboda ya ƙara ƙarfafa zumunci sai ya wanke 'yar shi Gwamma ya bai wa Baita auren ta ya ci gaba da gudanar masa da kasuwanci har tsawon shekaru goma sannan ya fitar da shi ya yi masa sallama wato ya yi masa nasa Katin. Cikin ikon Allah sai kuma Allah ya sa masa albarka kafin shekaru biyar sunan Baita ke yawo a sassan Najeriya da maƙwafta. Sai dai Allah bai bashi haihuwa ba, ya yi ta neman aure yana yi amma ba wadda ta haihu sai a shekarar su ta sha takwas da aure sai Gwamma ta samu ciki, ta haifi yaro na miji wanda ya ci sunan Aliyu ana kiranshi Ali. Haka ya taso a cikin gata. Allah ya yi wa Alhaji Sani rasuwa mahaifin Gwamma inda ta samu gado mai yawa da ƙadarori da kuɗi tsaba sai ta bi ta sa sunan ɗan ta Ali a matsayin mamallaki dukiyar ta. Shima Ali ya taso da cikin son kasuwanci shima tun kafin ya kai wani mata har sunan Ali ya doke na mahaifinsa Baita sunan Ali Baita ake ji domin shi ya yi karatun zamani. Wannan ya sa Hajiya Gwamma ta fara tunanin matar da ya kamata Ali ya aure ta saboda mutane sai kyautar 'ya'yansu suke bashi yana cewa baya so.haka kuma Hajiya Gwamma tana bincike a hankali, sannan ta baza malamai suna mata addu'a Allah ya haɗa shi da mata tagari. Ganin yanda idon matan birni ya tsayu aka Ali Baita kuma ya gane dan kuɗinsa ne sai ya koma in yaga Yarinyar da yake so sai yaje gidansu da shiga irin ta talakawa, amma sai yarinyar ta wulaƙanta shi, washegari kuma sai ya yi shiga ciki ƙasaita yaje a Ali Baitan sa, sai ka ga yarinya ita da iyayen ta sun hau rawar jiki. Shi kuma sai ya zo ya faɗawa Hajiya cewa ya fasa, anyi haka ba bu adadi dan haka ya haƙura. Wannan ya sa ya ja lokaci bai yi aure ba abin yana damun Hajiya Gwamma har ta hakura kan cewa zuwa yanzu duk wadda ya samo ita ce alkhairi. A Shekarar 1950 yaje wani taro na 'yan kasuwa na ƙasa wanda aka gudanar a jihar Lagos da yaje ya haɗu da wata 'yar kasuwa da ta zo daga jihar Zamfara. Ali Baita ya kamu da son wannan mata bayan sun tattauna hira akan kasuwanci kuma ya fahimci tana da basira da kuma nasibi a harkar kasuwanci sai kawai ya yi mata ta yin soyayya kuma ta amince ya dawo ya faɗa wa mahaifiyar shi Hajiya Gwamma, ta yi murna amma tace sai ta saka anyi mata binciken wacece Zeena Amadu Shinkafi. Na ɗago kai tare da sauke ajiyar zuciya. Babi na ɗaya ya ƙare na miƙe naje na ja durowar na maida littafin na nufi ɗaki na. Na hau gado na kwanta lamo. Kafin in ci gaba da karatun ina buƙatar in yi nazarin abinda na karanta domin in rike shi kuma in haddace..Yanzu dai naji tushen Shamaki tun daga Kakansa labarin ya faɗo kan mahaifinsa wanda shine dama ake bada tarihinsa ko ince aka rubuta littafin domin minsa. Zai zama dole akwai iya inda labarin zai ƙare ba bu cikakken bayani akan Shamaki. Sai dai zanbi labarin a hankali har zuwa inda ya ƙare sanna in nemo sauran labarin in ɗora. Na tashi na fito zuwa kicin na samu su Juma suna ta goge goge. Nace Juma ta min bayanin abinda ake buƙata na buɗa baki, sannan yara a tabbatar an ba su abinci da wuri tunda basa yin azumi. Ta ce "Dama yanzu nake faɗawa Laure ta ɗora musu Indomie zanje gunki in tambayi abinda za ayi,sai kuma in faɗa miki abinda ake buƙata. Nace babu damuwa ki sanar da ni yanzu. Kuma tace yau ranar kunun tsamiya ne da ƙosai sai farar shinkafa da kayan ciki, sai lemon zoɓo sannan akwai fura da kilishi." Nace to duka akwai su ko sai an nemo? Tace Nono ne za ayi waya a kawo. Nace to ina lambar? Tace bani da ita, sai dai ki kira Hajiya ta baki. Nace to na fita na koma falo na duba in da Hajiya ke zama akwai wani ɗan littafi da na fahimci tana rubuta lambobi. Na ɗauke shi ina dubawa, ɗauke ya ke da suna da kuma lambobin waya. Tabbas zan gani tunda ga sunayen masu kaji da nama. Boɗejo mai nono, take na kira lambar wani namiji ya ɗauka muka gaisa yace gidan Alhaji Baita ko? Nace e yace to zan faɗa mata za a kawo ne? Nace E . Ƙwarya ɗaya aka kawo nace nawa take bayar wa? Suka ce dubu ishirin nace to ina lambar akawut ɗin su, sukace Hajiya na dashi a rubuce. Nace to ba damuwa. Sai lokacin na tuna ai ba amshi lambobin sirrin ba. Na sake ɗakko ɗan littafi tabbas ga account ɗin su. Lambobin shirin sune matsala yanzu koda na saka direba ya kai ni banki ai babu su, sannan wani ƙalubalen ban taɓa zuwa banki ba tunda uwata ta haife ni. Na shiga kai mari ina kai gauro, ina ganin dai Hajiya tana sane bata bani number ba. Na sake zuwa ɗaki na kira Umma na faɗa mata. Tace " Ki samu nutsuwa Baby duk lambobin sirri suna zama na musamman ne, haka kuma zasu kasance ɗayan biyu, kodai wasu daga cikin lambar waya ko kuma ya kasance ranar haihuwa. Zai iya kasance wa ranar haihuwar ɗa ko miji, wani abu dai da ba'a manta shi. Nace to, sai dai ya zanyi in gwada. Nace wa Juma ta faɗawa direba zamu fita zuwa banki. Har na hau mota sai na tuna da Azima na sauka da sauri na cewa direba ina zuwa. Na je na shiga ɗakinta. Tana zaune tana kallo. Ta bini da kallo nace Azima zo muje banki mana. Tace Hajiya ta ce kar in sake in fita zuwa wani guri. Na zauna bakin gadon nace kin taɓa zuwa ciro kuɗi da Hajiya? Ta dube ni. Ta sake mai da kanta ga kallon TV kamar ita ce Hajiyar sannan tace, ki duba jikin katin zaki gani. Na kalli katin da kyau banga wani rubutu ba, na miƙa mata nuna min. Ta amsa ta kalla tace wannan ba katin da na sani bane, kije ku duba gurin da take zama, ko kuma ki kira ta mana. Na fita na koma na duba bangani ba. Na kira Shamaki a Video call, ya ɗauka suna Madina yace min "Yi haƙuri Baby ina ta son in kira ki in na samu nutsuwa. To ya gidan ya kowa da kowa?" Nace duk muna lafiya . Kaga dama zan tambayi Hajiya ne bata bani lambobin sirri na katin ba, kuna tare ne? gashi masu nono sun kawo za ayi musu Transfer. Yace "Gaskiya ban sani ba,amma tana yawan amfani da 1950 ki gwada ki gani. Sai dai kuma kada ki ce mata ni na baki,domin tsawon shekara ɗaya ne bazan shiga wata magana da ke tsakanin ke da Hajiya ba, ƙa'idar shi ne in an cika shekara zata bani umarni." Nace Umarnin saki na ko? yace "Bana fatan haka. Ke dai kiyi ta ƙoƙari duk da bansan me take dubawa ba ina yi miki kyakkyawan zato. Nace direba zai kai ni banki zan tura kuɗi in ciro wasu in aje a gida saboda buƙatar gaggawa. Yace "To amma dai ki sani Hajiya ce zata karɓi alert. Nace Karka damu. Yace ki kula da Azima in tana bukatar wani abu ki mata. Nace ." To. Sannan ban taɓa zuwa banki ba yaya za ayi in gane yadda zanyi amfani da katin? Yace ki samu ma'aikacin gurin gurin guda ɗaya sai ya nuna miki, kar ki yarda da kowa fa." Nace to. Cikin sa a da naje banki ashe ita ce lambar da na faɗawa ma'aikacin. Ya nuna min yadda zan tura kuɗi da yadda zan cire da kuma yadda zan duba ragowar kuɗin. Da ya tafin na shiga gurin duba ragowar kuɗin ban gane ko nawa bane sai tarin ziro. Na ciri dubu ɗari na koma mota. Washe gari Rahin ta same ni tace za a yi wa yara kitso." nace To ayi musu. Na je har lambu inda ake yi musu kitso na tambayi mai kitso kuɗinta ta faɗa min nace in an gama Rahin ta zo ta amsa, na ɗauki takarda na rubuta. Su kuma nace ta ba su cakuleti su daina rigima. Haka nayi fama ina iya kacin ƙoƙarin ganin komai ya tafi daidai. Har kwanaki tara na gana duk ma'aikata da masu gadi jani albashin kowa kuma na biya su. Kuma ce ta sanar da ni cewa Hajiya tana ba su atamfar salla kala biyu maza shadda. A shagon Zeena na sa su Ahmad yaran shagon Shamaki suka kawo na biya su kuɗin. Yaran kuwa a mota na zuba su muka je Zeena Supar market na zaɓa musu 'yan kanti masu kyau. Azima kuma tace Jallabiya take so, ta faɗi tsayi da kala muka zo mata da shi. Ni kam ban sai wa kaina komai ba,sai kuɗin kitso ne a lissafina da kowa sunan shi na saka. Sai kuma batun mama da kajin salla. "Shanu biyu raƙumi biyu kaji hamsin ake amfani da su." Inji Juma. Na zaro ido tare da faɗin wa zai je siyan waɗannan? ...... *HAMSHAƘIYAR UWA🧕🏻* *NA* *HALIMA ABDULLAHI K/ MASHI* _PAID BOOK_ _Kuɗin karatu ₦600_ _Account number 0700549935 Halima Abdullahi Access Bank a turo shaidar biya ta wannan number 08140004302 ko katin Mtn_ _Phone 08140004302_ *DOKA* _Ban amince wani ya ɗora littafin nan a wani Social media ba,ko a maida mini shi Audio ba tare da iznina ba yin haka daidai yake da fuskantar fushin hukuma. A kiyaye_ *Masu son a Tallata masu hajarsu suyi magana ta wannan number 09068032427* *Page 40* Allah cikin ikon sa a na sauran kwana huɗu salla sai ga Shamaki ya kira ni yace sun sauka a Abuja zasu hau jirgi zuwa Kano, nace shine jiya fa mun yi waya amma baka faɗa min ba. Yace "Bazata ce." Don haka na tashi na shiga shirin tarbar mai gida. Ranar kuwa mai ƙunshi ta zo ta yi mana jan lalle, ita kuma mai kitso sai washe gari. Nayi murna sosai da dawowar mijina, kasancewar Hajiya bata nan a gaban kowa na rungumi mijina ina murna. Shima ya ƙanƙame ni sannan yace "To ga yaranki bari suma in ba su runguma." Ya ɗauke su ɗaya bayan ɗaya, sannan ya miƙawa Rahin wata leda, yace a ba su chocolate kowa ya sha. Ko suna azumi?" Anisa tace bamayi Dady.Nace Kince min ki na yi fa Anisa Baby. Tace Mommy ai na karye shi fa. Muka sa dariya. A ranar dai kam na tabbatar cewa na yi kewar shi na tsawo kwanakin,. ,amma shi ya fi kewata ya kasance kamar zai cinye ni. Dawowar Shamaki ya taimake ni sosai domin sai dai naji an kawo shanu da raƙuma. Kaji kuwa haka aka yi ta rabon su, kamar in tambayar wa su Umma, amma sai nayi shiru tunda na san suna sane da su. Juma ta same mi tace "Hajiya tana nemo wasu masu aikin su taya mu kamar uku sai kuma aikin cincin da duk kayan fulawa bamu ke yi ba Zeena ake kaiwa wanda suke cewa ko batiri ko me?." Nace ko dai Factory? Baba Juma tace "Yawwa haka." Muka yi 'yar dariya. Nace to zanyi masa magan. Sannan ina zani neman masu aiki ukun da ki ke magana? Tace "In kuma in samo su sai in samo, domin da akwai su." Nace ki samo. Haka ta samo mata ta faɗi abinda za a ba su agaban su na sallama in an gama salla. Ranar Idi na matsawa Shamaki don Allah zamu je sallar idi yace , "Ba wadda ta taɓa zuwa in tsoro kar Hajiya ta ga cewa an kawo wani abu daban." Nace amma wata ta taɓa cewa zataje Hajiya ta hana? Yace "A cikin su babu wadda ta ambaci zuwa Masallaci." Nace bana zaton Hajiya zata hana ibada. Yace Haka ne." Haka dai ya kwashe ni da yara mukaje sallar Idi duk mun sha hijabai waɗan da na saya mana a kasuwa domin amfanin yau ɗin. Haka aka ci gaba da bikin salla, nace yaushe zamu gida? Yace in jira "yan uwanshi su zo. Sai uku ga salla suka zo, muka sha yini. Shine ya kawo min sabbin kudi 'yan ɗari biyu wai goron salla na shi kuma inzo in bashi nashi. Na zata wasa yake sai naga ya maida makullin ɗakina ya murɗa, yana faɗin yau a ɗakin nan nake shi'awarki, ga ƙamshin ɗakin ga ƙamshin mai ɗakin zan rufe ne saboda yaranki da zasu zo suna kiran Momy."Ni dai Nayi murnar kuɗi ina ta godiya har sai da ya fara nuna rashin ya ɓaci. Nace amma dai ka bari su tafi zuwa dare sai in baka goron sallar ka ɗin. Yace har yau kin kasa gane cewa mu maza in shi'awar mu ta taso bata komawa ko?"Na faɗa jikinsa,a zuciya ta ina faɗin kar a kaita wajen matan banza. Bayan na fito sai na koma gurin su,Maman Nana tace "Wai ina ki ka shige bacci ki ka yi ne ki ka share mu ana hira." Maman Umar ta ce "kai! Ke kuwa kin cika bincike, agabanki Shamaki ya kira ta f." Sai ta ce "O haka na manta,sai suka sa dariya. Na yi ɗan murmushi tare da faɗin kai Anty ba wani abu bane fa, saƙo ya bani. Maman Umar tace "E ai mun sani." Cikin kunya Na ja Naman Iman gefe nace Anty Maman Iman dan Allah Hajiya tace duk abinda ake yi muku da salla in kuzo a yi muku,shine nake son ki faɗa min abinda ake muku? Tace ba a mana komai ai kin mana komai anci ansha anyi wasa da dariya ai shine abin daɗin. Karki damu. Yara dai take bawa ɗan goron salla na sabbin kuɗi." Nace Nawa nawa? Tace duk yadda ya zama rabon su." Haka na ɗauki kuɗin na rabe musu dubu ishirin ɗin,amma da niyyar zan ciri kuɗina a wancan account ɗin tunda Nima ai zanje gida. Washe gari na tambaye shi yaushe zanje gida? Yace "inje, duk lokacin da na shirya. Na fara murna sai ya ce, "Amma kina ganin ya dace ki tafi Hajiya bata dawo ba? Kinga gidan nan a hannun ki yake,in Hajiya ta dawo baki nan fa?" Nace ai zata faɗa in zata dawo ko? Yace "Inji wa? Hajiya sai dai a ji kiranta tace aje a jirata a filin jirgi ƙarfe kaza zata sauka. Ni ina zaton ma yau zata dawo." Nace to shike nan,na haƙura zan jira.Yace Kama gefen kumatuna yace, "Daga cikin abinda ke ƙarawa mace daraja a idon miji shine rashin gardama." Na ɗora tafin hannu akan nasa nace Insha Allahu zan riƙe wannan karatun. Ya sunbaci goshina kin haddace wannan Baby." Nace To ina godiya Malam. Yana fita na tafi ɗakin shi domin ci gaba da karatun littafin nan Babi na gaba na shiga. Wanda ya ke magana akan Hajiya Zeena Amadu Shinkafi. Hajiya Gwamma ta sa anje har Shinkafi ta jihar Zamfara an yo mata bincike akan Zeena. Tamkar dai shi Ali Baita Itace 'ya ɗaya tak da Ubangiji ya baiwa maihaifinta kuma ya bata ilimin zamani dana addini. Sai dai kullum yana cikin damuwar rashin samun ɗa namiji wanda zai hutar da shi in ya kai matakin wasu shekaru. Zeena ta fuskanci damuwar da mahaifinta ke ciki don haka sai ta sawa zuciyar ta cewa zata share masa wannan kuka. Ta kuma nuna masa a zahiri ta karanci fanin kasuwanci. Dan haka data ƙare taci gaba da jagorantar wani ɓangare na kasuwanci sa. Abinda ya ba ni mamaki shine daga daidai nan gurin sai aka sa wani abu mai kama da farin fenti aka goge rubutun aka ɓata shi har zuwa Babi na uku wanda yake magana akan cewa an Ɗaura Aure Zeena da Ali Baita kuma an kawo ta garin Kano. Me aka rufe a can? Na tambayi kaina baya na buɗe shafu kan na koma baya na duba,hakan dai suke ba ido na bane. Dole za a samu kwafi mai kyau a gidan nan koda babu a ko ina za a same shi a gurin Hajiya. Na buɗe shafukan gaba duk dai bayani ne akan dukiyar da ya mallaka da tallafi da yake bayarwa sai hotunan karramawar da ya yi ta samu daga ƙungiyoyi da jam'i o'i sai hotunan su Shamaki da yayinsa an rubuta 'ya'yan Ali Baita. Na kasa ci gaba da karanta wannan littafin ina bukatar mai kyan. Na maida shi na aje. Ilai kuwa a ranar sai ga kiran Hajiyan Shamaki a waya, yace min a sanar da direba yaje filin jirgi ya jira Hajiya suna Lagos. Nace to na fita da kaina na faɗa masa. Na kira wayar Juma kwanan ta biyu taje gida. Nace Hajiya na hanya ta dawo domin ita ce tasan wanne irin girke girken da za a yi domin tarbar Hajiya. Cikin rawar jiki sai ga Juma ta dawo,tace don Allah in Hajiya ta dawo karki in ce mata taje cikin gari saboda zata yi faɗa, tace min kar inje tunda bata nan. " Nace ba komai karki damu bazata sani ba..Ni dai burina ki shirya mata abinci wanda ki ka san tafi so zata yi marmari. Ni kuma zan shiga ɗakinta da kaina in gyarra mata shi, amma ina son ki Kunno turaren da ya fi yi mata daɗi ki biɗe gidan da shi lungu da saƙo. Cikin mamaki tace 'Yannan ke ta daban ce sauran in Hajiya taje wani guri zata dawo sun dinga takaici kenan wai takura zata dawo. " Nace Ni kam ina farin ciki da dawowar Hajiya wallahi Baba Juma ina son Hajiya har cikin zuciya ta, kin san dalili? Tace "A'a. Nace ta haifa min Shamaki wanda nake masa wani irin so mara misaltawa. Kullum ina mata addu'a Allah ya sa ta gama da duniya lafiya tare da mu gaba ɗaya. Juma ta saki baki tana kallo na, nace yaya dai Baba Juma? tace, 'yannan ashe Kema kikan taɓa rashin kunya ashe. Na yi dariya wuce na nufi ɗakin Hajiya. Ta biyo ni har ɗakin tace "To zan baki wata shawara, komai nata ki barshi a inda yake karni canza masa guri." Nace Juma zan gyara ɗakin nan kamar yadda zan gyara ɗakin mahaifiya ta ne zan iya canza komai zuwa inda ya dace. Tace To shikenan. Na canza zanin gado da labulaye. Na wanke banɗaki na share na goge komai na kuma canza mata shirin wasu abubuwan. Na duba durowoyin ta ina neman kwafin littafin nan ban samu ba, zan fita sai na kula da wata durowar ta ƙarfe ina ganin irinta a finafinai. Wandda ake buɗe ta da lambobin. Nace tabbas ya na cikin nan,in kuwa haka ne to abin yafi ƙarfina. Nafita nace Juma ta saka turare a cikin ɗakin. Shamaki dama ya tashi da azumin sitta shawwal sakamakon matsa masa da nayi akan ya fara kawai, kuma fa nayi haka ne saboda na duba wayar shi naga alƙawuran haduwa da wata da suka yi da zarar anyi salla da kwanaki kaɗan. Na yi ta mamaki,nace anyi ibada kuma daga yin salla za a bi ibadar da zunubi. Yace "Wai me yasa na damu ya yi azumi ana cikin bikin salla. " Nace saboda ka saba da azumin kafin cikin ka ya buɗe kayi kayan ka in yaja Lokaci ƙila ya yi masa wuya. Yace Gaskiyar ki kam domin bara haka ce ta faru, ina ta furta zanyi amma ban samu na yi ba." Ni na tashe shi ya ɗauka. Hajiya ta iso gida lafiya muka tare ta da murna da farin ciki Ni da yaran. Ta ji daɗin yadda ta samu gidan muka bita har cikin ɗaki, ta yi turus ta dubi Juma mai riƙe da jakar Hajiya. Tace "Wanene da wannan aikin ko maman Umar ta zo ne?" Juma ta kalle ni, tace 'A'a ɗiyar ki ce dai ta yi gyaran. Hajiya ta kalle ni, sannan ta zauna baki gado. Muka fita domin ta kimtsa. Ina falo ta fito ta yi wanka ta shirya tsaf cikin doguwar riga. Sai lokacin na buɗe mata kujerar zaman ta wadda na saka wani farin kyalle na rufe, ko masu shara sai dai su kakkaɓe su share su mayar su rufe. Ta zauna tace Alhamdulillahi Allah mun gode maka, ya Allah ka amshi ibadarmu. Muka ce ameen. Sai da ta yi salla sannan Juma ta soma gabatar mata da abinci. Na zauna ina zuba mata. Tace Juma sannu da ƙoƙarin wannan hidima. Juma tace matar Shamaki za a yi wa godiya ita ce ta bada umarni a yi komai. Hajiya ta ɗaga kai ba tare da ta dube ni ba. Shamaki ya shigo, cikin murna yana yi wa Hajiya sannu da zuwa. Ya zauna suka gaisa. Ta gama cin abinci na soma matsa mata ƙafa, tace a ɗakko maganin nan domin ƙafafun sunyi tsami. Na je na ɗakko lokacin da na dawo na samu Azima ta na zaune a gaban Hajiya. Hajiyar tana cewa Azima. "Kina nufin baki ji ba duk wannan hayaniyar kusan awa biyu da suka wuce? Tace "Wallahi ni dai banji ba." Hajiya tace shike nan. Na zauna na ci gaba da matsa mata ƙafa. Washe gari na tashi cikin shirin zuwa gida. Naje gaida Hajiya tace "Ga akwatuna nan an kawo na tsaraba, na kwana biyu banyi tsaraba ba in naje Ummara ko aikin Hajji. Nace sannu da ƙoƙari. Tace "Yanzu sai ki buɗe ki raba." Nace Hajiya zan iya kuwa? Bata amsa ba dan haka sai na buɗe akwatunnan na dinga ɗaga wa ina kallo zannuwan gado, dardumai, kayan yara da dai sauransu. Na cire wa su Anisa riguna yaran su Maman Umar kowa ɗanta ɗaya ya samu. Dogayen riguna Jallabiyu. Na cire wa Azima guda biyu su Juma hijabai. Shamaki wata Jallabiya bulu ta yi kyau na ce wannan dai tamuce, masu gadi dama nasan adadin su tun a biyan albashi, na cire musu dardumai da carbi. Nace Hajiya gashi na cire na waɗan da na sani. Na lissafa mata, tace "Bari in zana miki sauran tana ta fiɗi ina cirewa aka gama. Tace ina nawa. Nace ai ko ban ɗauka ba babu komai. Ta ce shike nan tunda baki so cirewa Ummar ki. Na ciri Hijabi irin na su Juma. Abbanmu kuma carbi da dardumai. Tace shike nan aba kowa na shi a kai mata sauran stor. Hajiya tace in bari sai ƙarfe goma sannan in tafi. Tace me zanje dashi ina cincin da nama ko haka zanje hannu rabbana? Nace ai gida ne ko ban kai komai ba babu wata matsala. Tace "To da aka fitar da zakkar fidda kai an kai masu?" Nace gaskiya bansani ba dai domin shi ya raba. Ta ɗauki waya ta kira shi, yana waje Shamsu ya yi sallama da shi. Tace "Ankai zakkar fidda kai gidan su matar ka?" Yace baki faɗa min cewa za a kai ba. Na bayar ne a guraren da aka saba kaiwa. Tace "Ya Salam! Ban ji daɗin wannan lamarin ba sam. To yanzu me zata kai gidan su? Yace duk abinda ki ka ce . Hajiya ta kashe waya sannan ta dube ni. Kira Juma. Na kirata. Tace Juma A samu manyan ledoji a zubo dambun kajin nan,sai kuma na naman shanu, wata ledar a zubo cincin,aka kawo gabanmu, tace Juma ki sa rabe ya fitar da lemo kat an goma ya saka a mota akai waɗannan ledojin." Ta duba ni, kije ɗaki na kija wannan durowar da kika gama bince su ki ɗakko sabbin 'yan ɗari biyu ki riƙe saboda taɓawa yara. Nace "To. Amma jikina ya yi sanyi da jin kalma durowar da ki ka bincika. Na ɗakko na fito. Tace in gaishe su,sannan kuma Shamaki zai zo ya ɗakko ni daga nan sai ya gaishe su,,ko hakan bai yi ba?" Nace ya yi na gode sosai. 🖊️🖊️🖊️ Gida ya kaure da murnar zuwana. Direba ya na ta shigo da kayan lemo na saka yaran maƙotanmu su taya shi ɗakkowa. maƙota harda leƙe ance Baby ta zo. Wani abu da ya ɗaure min kai shine yadda naga buhunan shinkafa guda biyu a ƙofar ɗakin Umma. Nace wannan fa? Tace "Wadda mijinki ya kawo mana ce ta salla buhu biyar muka rabawa dangi da maƙota guda biyu, Abban su Zuhra kuwa muka bashi rabin buhu, rabin ce muke dafawa, sai sauran biyun sune kin gansu nan." Nace Kuma ni sam bai faɗa min ba, Hajiya ma bana zaton ta sani. Domin ta tambaye shi ko ya kawo muku zakkar fidda kai, yace a a. Umma tace "Ikon Allah wato su dai mutanen kirki haka suke, to kaji goman ma bai faɗa miki ba kenan?" Na saki murmushi nace Allah ya saka masa da alkhairi, kuma sam bai faɗa ba. Daɗi ya lulluɓe ni, take wani son shi ya ƙaru a zuciya ta. Tsakar gida muka shinfiɗa tabarma aka baje muka zube kayan da na kawo. Abba ya shigo muka gaidasa cikin murna yana ta sawa Shamaki albarka da ni. Yara masu shigo da lemo suka gama Umma ta basu ɗai ɗai suka tafi suna murna. direba ya tambaya ƙarfe nawa zai dawo ? Nace ba sai ya dawo ba Shamakin ne zai zo mu tafi. Nan Umma ta shiga rabon lemo Jafar da Habu suna miƙawa maƙota, tana cewa kowa dai ya lasa, domin duk wanda ya ci shi kaɗai tofa shi kaɗai zai mutu. Muka sa dariya. Jamila tace Umma in ka ba wasu tare zaku mutu? Umma tace "Ba haka ake nufi ba, abin nufi shine zaku mutu ne da ladan abinda ka bayar, in kuwa ka ci kai kaɗai tofa babu maganar wani lada da zai bika kabari." Ni kai na sai yanzu na san ma'anar wannan Hausar. Nace gaskiya ne. Allah ya bamu ikon aikata alkhairi. Gidansu Zuhra kuwa sai aka kai katan ɗaya. Sai kuma ake ta shigowa godiya, nasan da biyu ne dan a ganni kuma aga me na kawo. Umma dai sai ta koma duk wanda ya shigo sai ta basu cincin da naman da na zo da shi. Muka baje munata hira ina yi wa Umma mitar su Jamila basu zo min ba. Jamila tace Abba ya hana mu kuma ga aikin gida. Umma Tace "Yaran gidan masu niƙa waɗanda su ka yi miki biki wai sunzo an hana su shiga." Nace basu faɗa muku bane lamba ta kawai duk wanda zai zo zai karɓa, ya kirani ya faɗa min cewa zai zo. Shikenan in faɗawa masu gadi. Duk wanda yazo zasu tambaye shi ne, gun wa kazo ko ka faɗa in sukace tasan zaka zo kace e, to zasu ce ka kirata a waya yanzu zata kira mu. In kuma kace bata sani ba,, kai tsaye zasu ce ka wuce ka tafi hazaka shiga ba. Umma t ace "To in kana da shi ne sai da tsaro rayuwar babu tabbas kana bacci wasu suna yi maka minshari." Haka dai muka yita hira, sannan na tashi na shiga maƙota da 'yan uwa muka gaisa tsofaffi da ƙananan yara su na bai wa goron salla ta. Shamaki ya kirani muna ƙofar na'isa ni da Jamila gidan wata ƙanwar Abba. Yace sai dare zai zo mu tafi na yi murna. Har hankali na ya tashi ko dai sun shirya da wata ne za su haɗu, sai kuma na tuna yana Azumi. Take na sauke ajiyar zuciya tare da faɗin to sai ka zo. Zan je gidan wasu 'yan uwan mu a Fage. Yace "Dama kuna da 'yan 'uwa a Fage ne?" Nace E mana, ya ce "Shikenan gaida su. Ko in turo miki direba ya kai ku bana son matata a kekenapep?" Nace barshi kawai babban baƙo. Yace 'To don Allah ki ɗauki shata karki cakuɗu da mutane kuma daka kike ke kaɗai wani ya taya min mata ya zata budurwa ce. Nace ni da Jamila ne dama ko ni ɗaya ce drop zan ɗauka. Muka yi sallama akan sai ya zo. Jamila ta dube ni. Ke kuma ina ki ka samu dangi a Fage? Nace ke dai muje kya gansu. Gidan gidan sama ne irin tsohon ginin nan na cikin Fage. Muka shiga cikin gidan benan tamkar sai faɗo ƙasa, muka yi sallama. Wadda ta zo karbar zakkar nan ce,tana ƙoƙarin hura gawayi. Ta taso da sauri ta tare mu tana faɗin Hajiya sannunku da zuwa.Muka amsa,tace "Kunzo gurin tsohuwa ne ko?" Nace Gurin ta muka zo. Tace tana sama muje in kai ku?" Muka shiga saman kamar zai faɗo nake ji. Tana kwance akan wata tsohuwar katifa tayi fale fale cikin tsummuna.sai dai da alamu ana kula da ita in aka yi la'akari da ɗakin fes yana ƙamshin turaren tsike, sannan kayan jikinta da tsummunan duk suna wanke fes. Ta shimfiɗa mana tabarma a gaban tsohuwar tace mata Hajiya ce wadda ta bamu zakka yazo ta gaishe ki. Tsohuwar ta ɗan taƙarƙara ta tashi tana ɗan tari ƙutul ƙutul. Irin na tsufa. Nayi mamakin yadda na ganta a waya kuwa muryar tar kamar matashiya. Nace sannu Kaka. Tace "Sannu yarinya sannu da zuwa, matar Shamakin ce kokuwa dai cikin yayun nasa ne? Domin ba muryar Zeena bace, ina tiƙe da muryar Zeena Zeena adon kyawawa maganar cikin ƙasaita ta ke yin ta. Tana lafiya dai ko?" Nace lafiya lau Kaka, matar Shamaki ce ni, na zo in gaishe ki gaisuwar salla, sannan muɗanyi hira irin ta jika da kaka in samu tarihi iyayena su Hajiya Zeena. Jikarta ta yi 'yar dariya tace kun kuwa same shi, domin ko mu radda abin ya motsa muna shan hirar gidan Alhaji Baita. Tsohuwa ta yi kaki ta ɗauki wani ɗan gwangwani ta tofa a ciki, sannan tace "To yarinya me ki ke son ki sani?" Nace. Hajiya tarihi nake som ji na Hajiya Gwamma. Tace "Allah sarki Duniya labari Gwamma da ke Hajiya uwar Ali Baita. Jikata duk inda ki ke neman mace mai kirki da mutunci in kika samu Gwamma zance ya ƙare. Hatta "yan aikin gidan Hajiya Gwamma suna zuwa aikin hajji. Ni nan banje ba,amma mai gidana yaje saboda shine direbanta kuma ita ce ta haɗa aurena da shi. Nace masha Allahu. To kinsan lokacin da aka yi auren Ali Baita kenan? Na tambaye ta. Tace sani kai, a gidan fa muke zaune da mai gidana. Na gyara zama nace ashe kinsan lokacin da aka auro Hajiya Zeena. Tace "Ƙwarai kuwa, Ni ce nan aka fara baiwa Zeena a matsayin mai dafa mata abinci, aka maidani kicin ɗinta. Jikata ban taɓa ganin soyayya ko jin labarin soyayya irinta Zeena da mijinta Ali Baita ba, kirarin da yake yi mata kullum shine Zeena adon kyawawa. Gata da gayu ban taɓa ganin mace 'yar gayu mai kula da miji tare da tattalinsa kamar wannan baiwar Allah ba. Ta sake yin ɗan tarin ta sannan taci gaba da faɗin "Biyayya kuwa kinga.Ta ɗaga yatsun hannunta tana lissafi. Kiga ita ce ke girkawa Hajiya Gwamma abinci daga ranar da likita ya ce ta daina cin farin magi. Sannan masu aiki a lokacin nan mutum tara ne har ni goma, amma Hajiya Zeena ita ce ke yiwa Hajiya Gwamma gyaran ɗaki ta fidda mata kayan wankin ta shirya mata gogaggu a durowar ta. Komai Hajiya Gwamma ta ke so Zeena ta ke yi wa magana. Zeena ga kyauta dangin Hajiya Gwamma kuwa duk wadda ta zo gidan tamkar ta bata ranta dan nuna ƙauna, ko daga ƙauye mace ta zo ba ruwan ta zata jata jika ta cika ta da alheri, sannan tana taimakawa mijinta da abinda ya shafi harkokin kasuwanci sa tunda ita ma layin tane. In taƙaice miki cikin hikima da basira da wayo dan tana da dan bazan wayo. saida ta mallake zuciyar kowa na gidan da ƙauna da mutumci ta maida dangin shi tamkar nata. Ta ɗan yi shiru tana maida numfashi. Sannan ta ɗora. Rashin samun haihuwa shine ƙalubalen Ali da Zeena. Hajiya Gwamma ce ke kwantar musu da hankali tana faɗa musu tsawon shekarun da ta share kafin ta haifi shi Ali. Cikin haka sai Allah ya amshi rayuwar mahaifin Zeena." Nace tsohuwa ban katse ki ba,duk wannan labarin lokacin shi Alhaji Baita baya raye? Tace "Yaushe rabon shi da Duniya a wannan lokacin? Ya rasu tuni Ali ya ci gado mai yawa, ance a yankin nan namu na baƙar fata in an samu na ɗaya to kuwa Ali ne na biyu a dukiya dai." Ta sake numfasawa tace "Kina jin wannan taɗi ko 'yannan Zeena ta rungumi gadon ta cancakat ta danƙawa Ali,shi kuma da ya tashi sai ya gina mata gidajan mai, ai duk gidan mai da kika ga ansaka Shinkafi to na Zeena ne a wancan lokacin ban san yanzu ba. Sai kuma wani abin mamaki da zan faɗa Miki yanzu. Mutuwar mahaifin Zeena sai ya tona wani sirri wanda shi Ali da Zeena suke ɓoyewa . Ashe dai Zeena ba a Budurwa Ali Baita ya aure ta ba." Kuna jina jin wannan zance?" Na kasa magana saboda tsabar mamaki,yaya ma za a yi haka, ko dai tsohuwar nan takanta ya fara juye wa ne?. Hajiya ta ɗan faɗa min wani abu daga cikin daren farkonta. Amma sai na yi shiru domin inji ƙarshen zance. Tace duk munsha mamaki a ranar da Ali Baita ya shigo da yara mata guda huɗu ya gabatar da su ga Hajiya Gwamma a matsayin yaran da Zeena ta haifa da wani miji kafin haɗuwar su da Ali.Wai ya ɓoye mata ne saboda kar ta hana shi auren Zeena a matsayin shi na saurayi. Hajiya Gwamma ta girgiza da wannan baƙon lamari harta nuna fushin ta ga Ali da Zeena wadda ta ɓoye kanta tun daga ranar da Ali ya kwaso yaran daga Shinkafi. Hajiya Gwamma ta daina cin abincin da Zeena ke dafa mata, ta faɗawa Uwar gandu da Tabawa tace su faɗawa Zeena ta daina yi mata girki domin ta daina ci. Ina falon Zeena lokacin da Ali Baita ke lallashin Zeena wadda ta haɗa kayanta da kuma 'ya'yanta tana roƙon ya sawwaƙa mata auren shi zata koma Zamfara da yaranta." Nice na je na faɗawa Hajiya Gwamma halin da a take ciki. Da kanta ta taso zuwa falon ta ce in tafi da yaran sasanta. Zeena ta zube a gaban Hajiya Gwamma tana kuka. Hajiya Gwamma tace Zeena na yi fushi da ke fushi mai tsanani, ban taɓa tsammanin cewa ƙarya ne alaye ne baki ɗauke ni a matsayin Uwa ba, sai wannan karon. Kinsani Sunnar gidan nan ce ba a yin ƙarya, me yasa ke da Ali ku ka yimin ƙarya, me yasa da akayi auren baku zo kun fayyace min komai ba? Kenan ni muguwa ce kuka ɗauke ni wadda bansan ina yake min ciwo ba. Bansan ƙaddara ba,ko da ni bansan ràɗaɗin soyayya ba lokacin da aka aura ɗaura min ubanka amma ai ina jin labarin masoyan ko. Dan haka ni na karɓi yaran zan riƙe su, domin nasan cewa a can ɗin suna hannun masu aiki ne da mahaifin ki, kasancewar tun bayan rasuwar mahaifiyar ki bai sake aure ba. Ta girgiza kai, ina son kusani cewa ba ku kaɗai kuka iya shayar da mamaki ba, zan baku nawa kusha yanzu. Ina son kusan wani abu,duk wata uwa Hamshaƙiya bata zama karabiti mai yara da yawa ma bare ni mai ɗara rak." Tsohuwa ta mufasa sannan tace, Kunsan abinda yasa na nemi guri na zauna bayan na kai yaran sasan Hajiya na dawo? Nace a a. tsohuwa ta ci gaba da faɗin. Kalaman Hajiya sun firgita ni lokacin da tace. Zeena kin auri Alhaji Uzairu wanda ya kasance shine mai kula da dukiyar mahaifin ki, kuma ya haɗa aure ne saboda yarda da yayi cewa ko bayan ransa zai kula da ku da kuma dukiyar ku. Bayan ya ga cewa ya same ki, har kin haifa mishi yara sai ya fara shirya yadda zai ga bayan mahaifinki domin ya mallaki dukiyar sa. Asirin sa ya tonu ne lokacin da ɗaya daga cikin ma'aikatan da yake tunanin ya haɗa baki da su ya tona shi ya sanar da mahaifin ki abinda ke faruwa kuma ya roƙi kar yasha duk wata fura da wani zai bashi. Dan haka tuni Mahaifin ki ya sanar da jami'an tsaro suka zo cikin farin kaya suka kamashi dumu dumu da furar da ya kawo Office ɗin Alhajinki. Bayan bincike an gano cewa guba mai kisan mummƙe aka sawa mahaifin ki wanda zai ɗauki tsawon wata uku yana jinya kafin ya mutu. An kashe auranku a kotu ne lokacin da alƙali ya iza ƙeyar shi zuwa gidan kaso. Ta dubi Zeena wadda ta cika da mamaki tace, duk da ni banyi karatun zamani ba,na tabbata ni ba jahilan bace. Kuma in har Uwa takai uwa dole tasan duk wani shigi da fici na ɗanta. Sannan duk tsanani karki yi ƙarya tana zubar da kima kuma tana saka aji kunya kamar dai yanzu gashi ke da mijinki. Hajiya Gwamma zata juya Zeena ta tashi da sauri ta zube a gaban Hajiya tana neman gafara. shima ya zo ya zube. Tace ku ki roƙi Allah gafara. Kunsan wani abu? Ko masu aikin gidan su dai sunga yara amma basu san yaran Zeena bane ,sai ni da mai gidana wanda shima ni ce na sanar da shi. Hajiya Gwamma ta yarda da ni matuƙa amma duk da haka sai da ta jamin kunne tace matsawar zancan ya fita to kuwa ni ce, dan haka na ja baki na nayi gum. Aka kai yara makaranta da sunan Ali Baita. Gwamma ita ce ta riƙe yaran nan tamkar kakarsu. An samu tsawon lokaci kafin aka samu cikin Shamaki. Faɗin gatan da Zeena ta samu kanta a ciki ma ai ƙauyanci ne a gurin Hajiya Gwamma . Nace tsohuwa Kina nufin Aliyu Shamaki shine kadai ɗan Ali Baita? Tace ƙwarai kuwa, duk wata dukiya ta shamaki ce, sai ta Zeena wadda bata fi cikin cokali ba in aka karata da ta Shamaki." Nace to kuma kin ci gaba da zama da Zeena ne bayan Hajiya Gwamma ta rasu? Tsohuwa tace 'Ai Shamaki bai rufa wata uku ba ciwo suga ya tasarwa Hajiya Gwamma aka fita da ita ƙasar waje, ashe dai tafiyar kenan. Sai gawa aka dawo da ita. Zeena ta yi kuka kamar zata yi me har sai da aka yo mata rubutun dangana tasha sannan ta haƙura. Ni kuma da suka gina sabon gida za su tashi sai suka saya mana wannan gidan,a wancan lokacin gida irin wannan sai wane da wane muka dawo. Sai saidai muje muyi aiki lokacin mai gidana ya fara tsufa sai aka kawo sabon direba kuma ta canza wasu masu girki domin nima lokacin girma ya fara shiga kuma ga yara amma dai ina zuwa in yini domin tana son ina zauna kusa da ita kasancewar tana da son labarai. Daga baya kuma sai larurar ido ta kamani, sun kashe min kuɗi amma haka na rasa idanun, sai na hakura da zuwa, Ali Baita shine ya budewa mai gidan nan kati a nan ƙofar gidan muka ci gaba da riƙe kanmu amma Zakka ta fidda kai da ta azumi baya wuce mu har ya rasu Hajiya Zeena bata dai na ba. Sai shekarun nan ne ma aka canza to Gara wannan karon an baku komai da ake bamu. To kinji." Nace Lallai Hajiya Zeena ita ma tana da kirki kamar surukar ta.. Tace "Ƙwarai banbanci su kaɗan ne, ita wannan Zeena tana da zafi sosai kuma tana da iko da yawa koda dai mako ance sun shafi sarauta acan garin na su." Na ce me yasa ake kiran Shamaki da wannan sunan mai makon sunan su na gado wato Aliyu? ....... *Assalamualaikum* *Naga addu'o'inku game da sace man waya da akayi, nagode😍* Tsohuwa Ta ce bani kofin can insha ruwa, ina Maryama ta zo ta kawo muku ruwan kuma." Jamila ta ce yanzu muka sharuwa . Tsohuwa tace, , "Nima karambani ne 'yannan, nasani gidan Zeena ko masu aiki basa shan ruwa dan awo sai na roba." Ta daga ta sha sosai har ta dan kware, muka tsaya muna yo mata sannu. Tace "Me ki ke tambaya ne? "Nace game da sunan Shamaki. Ta ce "Anyi haka. Yadda Zeena ta fada min tace Ya samu sunan ne daga asalin mahaifin su acan Sudan Wato shi Baita shine babban yaron sarki kuma duk babban dan sarki to Shamaki ne kuma yana dai dai da Hakimi. Sai Ana ganin shi taro ne bai dace a bashi Shamaki ba. Ya za a ce Sarki yana ji dashi harma ya kasa boye soyayyar sa, har taja aka fara neman rayuwar sa. Sarki ya kira malamai su yi masa istihara akan wannan matsalar, baki uku ya hadu daga malamai daban daban akan cewa mafi alkhairi shine ya bar garin domin kuwa taurarinsai masu haske suna nesa. Sannan hadari yana kusa da shi. Haka suka ba Sarki shawara ya nesanta shi daga garin, ya hada shi da amintattu suka kawo shi kasarnan suka juya suka barshi da guzurin shi." todai . Kinji inda ya samo sunan Shamaki. Ali Bauta da Zeena ai suje can kasar a wata shekara. Kuma sunga dangin su dawo suna yaba karbar da suka samu haka kuma sun zo a rasuwar Ali Baita Na Kali Jamila nace kinji kuma. Da alamu dai in zamu kwana ba zan daina jin sabbin abubuwa daga bakin tsohuwar nan ba. Tsohuwa tace "Kwarai kuwa. " Nace to wai Kaka Kina gidan Shamaki ya zama saurayi? Tace "Yana dan makaranta lokacin da na bar gidan ana zancan za a fiddashi kasar waje." Na kada kai, da alamu dai bata da wata masaniya akan Shamaki sosai. Nace Na gode Kaka dajin Wannan labari na bude jakata na ciro kudi ban kirga ba na kama hannunta na saka mata ina fadin Baba ga su nan a sai miki goro. Tace "kuma dai ba a gajiya 'yannan Allah ya saka miki da albarka. Kuma naji dadi da wannan ziyara a san da kai ma acrayuwa Ai arziki ne." Muka fito mukayi musu sallama muka wuce. Muna dansahu na kasa magana ina juya wannan lamari ace wai su Maman Iman ba Uban su daya da Shamaki ba. Jamila tace "Wai in tambaye ki? " Na sauke ajiyar zuciya nace ina jin ki. Tace "Me Wannan labarin zai amfane ki da shi.? "Nace Jamila bazaki gane ba, assignment na ke yi zan hada rahotanni ne tsayo shekara daya. Ta juyo tana kallona alamun bata gane ba. Nace bazaki gane ba. Lokacin da Hajiya Zeena ta juyo da ni zuwa gida da takarda ta ta zaki zaki fi dahimta. Ta zaro ido "Auren shekara daya ku ka yi? " Nace in har shekara ta cika ban san waye Shamaki ba, to zata sa ya sallame ni. Jamila ta taba baki, wannan gida naku sai kace wani gidan gwamna ko na shugaban kasa." Nace Ai gidanmu ya wuce nan, domin daga gwamnan har shugaban kasa suna girmama Zeena sun san abinda suke samu daga gareta. Jamila tace "Wai ma dan ku kuma san hakan Allah ya kyauta." Da dare Na shirya tsaf Jamila sai tsiya take min wai haka na zama sai wani kakale na ke yi akan miji. Umma ta shigar min tace barta ta yi aikin ladane, ke ai ba a san abinda zaki yi ba. Bayan ishai sai ga kiran Shamaki wai ga shi a hanya. Dan wani salon da ya zo sai ya tsaya a kofar gida wai in fara fitowa, Nace ka shigo kai tsaye. Ya ce fara fitowa mana. Na saka mayafina na fita, yana tsaye a inda ya saba tsaya lokacin da yake zuwa zance. Na gane cewa yana son tuna baya ne, dan haka nima sai naje gurin da nasaba zama na zauna. Nace sannu da zuwa dan samari,. Yace yawwa 'yan mata dazu na ganki ke da wata kanwarki kuma dai na fada sonki irin ta ka dinnan, ya miko tafin hannhu sa, shin ko zaki bani soyayyarki? " Na dora tafin hannu na ina fadin na baka ya kai wannana kyakykkyawan basarake ina fata zaka rike ni amana bazaka sake ni ba.. Ka sani babu wata mace wadda zaka yi mata tayin soyayyarka ta kauda kai. Ina sonka. Sai ya janwo ni jikinsa yana fadin nima ina sonki yake wannan yarinya mai kyau da iya kalami. Sai duk muka sa dariya ya sake ni tare da fadin muje in gaida su Umma. " Muka nufi cikin gida. Tuni an shinfida masa shinfida, suka gaisa daga nan sai Abba da Umma suka yi masa godiyar sako. Ya ce babu komi ya dada ciro kadi ya aje wa Umma sannan ya aje wa Abbbanmu. Suka sake yin godiya, sannan Abba yace kuje ki raka shi ya gaida Abban su Zuhra kafin ku wuce ko?" Nace to. Muka fita yace mu taka a kafa muje." Abarandar da suke salla muka same shi, shida wasu makotan su. Muka durkusa muka gaida su, yace Uwata ce sannunku muka gaisa ya ciro kudi ya ba Abban su Zuhra, sannan suma na zaune ya ciro ya basu. Suna ta saka albarka, daga nan muka koma mota, muna shiga ya rungume yana neman bakina, na biye shi na tsawon lokaci kafin daga baya na zame nace atiti muke ya sake kamoni, my Baby mu bivu ne anan ba mai ganinmu. Ya yamutsani son ransa, da kyar na lallabashi. Ya figi mota da gudu. Ni dashi babu wanda ya iya furta wata kalma. Kaina na jingina sa a bayan kujera na lumshe ido kamar mai bacci. Duk ya saukar min kasala, gashi yanzu in munje gida gurin Hajiya zamu yada zango. Shims nasan damuwar kenan. Koda ya yi hon har aka bude mana gate ban iya dago kaina ba. Sai da ya tsaya ya sa hannu ya shafi wuyana,sannan ya daga wayarsa ya soma magana cikin harshen turanci, duk da banajin sosai kunsan karatunmu na Kano in ba makarantar kudi ka yi ba sai a hankali na tsinci kalma biyu. My wife sai kuma da ya gama maganar naji yace ok. Na tashi da niyyar fita sai na ga ashe ba gida muka zo ba. Nace Babban bako ina ne nan? Yace karanta can ya nuna min wasu rubutu masu kawo wuta. Hotel din ne ya dauki hankali na ba sunan Hotel din ba. Na dubeshi da sauri, Subahanallahi Auzu billahi minasshaidanin rajim! Me zamuyi a Hotel da mutuncinmu da komai! Me zan gani Shamaki? Yace "Me ake yi kuma me ake gani a Hotel din da zaki gigice haka? " Nace 'Yan iska ke zuwa Hotel yin iskanci. Yace "Muma iskancin muka zo muyi." Na zaro idanu har zuciyata zunubi ne zuwanmu gurin nan dan haka na bata rai nayi shiru. Ya daga wayar shi sai naji ya sake furta ok. Ya bude mota, fito muje." Na ki motsi ya fita ya zagayo ya bude yace fito mana baby." Na soma zubo hawaye domin take zuciyata take fada min wai inda yake zuwa da matan banzan shi ne. Ya katse ni, ina miki magana kina jina? Da alama ya soma fusata. Cikin kuka, nace yanzu fisabililllahi in wani ya gammu yaje ya fadawa Abbanmu cewa ya ganni a Hotel tsine min zai yi fa. Ya saka hannu ya dakko ni ya rike ni kamar wata jinjira, sannan ya rufe motar ya sabani a kafa yace a haka kinga baby bawanda zai ganeki. inata wutsil wutsil ina dan kuka. Muka shiga,. Mutum daya ne a Reception na rufe ido da bayan shi wai kar yaga fuskata. Ina ta dukan bayan Shamaki, wani yana tsaye bakin wata kofa shine ya bude mana kofa sannan suka sake yin magana ya shiga ya rufe kofar ya zube ni kan gado. Na diro da sauri nace nifa bazan tsaya ba, ni ba karuwa bace. Kalmar ta fusata shi da alama. Yace karki fusata ni Baby. Nace nafison ka fusata din ko ka kai ni gida. Hajiya ma nasan yanzu tana jiranka kuma zan shafa mata maganinta a kafa. Ya turani na fada gadon ta baya, na san a raina ni dai bazan yarda ya kwanta da ni a Hotel ba, domin hakan zunubi ne. Ya cire kayansa ina ta kuka, ya fizgo ni, rigata ma da ta bashi matsala yagata yayi. Karfi ya nuna min ko ince Shamaki fyade ya yi min kuma har saida ya min rauni. Na kasa tashi, shi kuma juya min baya ya yi ya kama bacci. Nima dai bansan lokacin da baccin ya yi gaba dani ba. Farkawa na yi na ganshi yana salla. Na tashi zaune da sauri, sai lokacin na ke karewa dakin kallo, ya yi matukar kyau, kamata ya yi ace wannan dakin a gidan sure yake. Na tashi na sauka ina dingishin iskanci waini amin fyade, duk da ina jin zafi amma bai kai yadda na dauki abin ba. Na dube shi Nace ko isha'i bai yi ba ashe amma ya iya kawo ni Hotel Allah dai ya sani kuma bazai rubuta min zunubi ba. Na zauna baki gado ina mitar gashi duk an jima mutum ciwo. Bini da kallo yana murmushin mugunta. Sannan yace in kin gama mitar sai ki tashi kiyi sallar asbahi tunda kin ja mana makara gashi nan yanzu har shida ta yi. Na mike da sauri na dafa kirji nace wai kana nufin gari ya waye!? Yace "Ina wayar ki tana mota da kin duba lokaci yawwa kali agogo gashi nan. Na kalli bangon da ya nuna da sauri, take na rikice nace na soma kukan gaske da hawaye masu dumi, nace Shamaki ka kashe ni, yanzu me zan fadawa Hajiya fisabililllahi! Yace ke ki ka ja komai da kin tsaya awa daya kacal ko biyu zamu tafi, kina ta wani ihu wai ke ba karuwa bace, shikenan dan karuwanci aka gida Hotel ke ma kina cikin sahun mutane marasa fahimta, to ko a Saudiya ki ka je ina zaki sauka in ba Hotel ba?" Na kalle shi a makka ba gidaje bane na dama kowa ya zo zai kama bide ya shiga? Ya yi dan murmushi waye ya fada miki wannan din to a Hotel ake sauka, zaki je ki gani wa idon ki. Sannan kuma ni mijin ki ne dan munzo nan mu dan huta sai kawai mu samu zunubi, irin ladan da muka samu a dakina ko naki irinshi ne dai zamu samu a nan. Amma ke jiya na san baki samu komai ba kila ma sai zunubi amma na yafe miki. Jikina ya yi sanyi nace to ai kaine baka gaya min ba. Ya harare ni, in fada miki me bayan kina ta hauka, kuma zaki ce duk baki san komai ba kinyi makaranta fa. Na turo baki, nace dan nayi makaranta ta gwamnati ce ina cikin lokon mu ni ba kallon TV ba ba jin radio ba, garama ina dan karance karance. NI ban san me ake ciki ba. Yace to yanzu jeki kiyi salla dai." Na shige bandaki, na kalli ko ina gwanin shi shi'awa, na kalli kaina a madubi nace ni Baby a Hotel yau. Nayi wanka na yi alwalla na fito. Na saka siket na daga rigata nace to ni yanzu sai ka biyani rigata. Ya daga rigar tayi kaca kaca, ya yi murmushin mugunta yace, ni ma dai jiya na yi wa wata yarinya fyade, kuma fa naji dadin hakan. Kinsan namiji yana son style kala kala. " nace Ni baruwa na yanzu kasan yadda zakayi da ni. Ya cire janfar da ke jikinsa sai singiletin shi yace "Sa wannan ni sai inje da malun-malun tana mota." Na dauka na saka a jikina. Ya kalle ni ya yi murmushi ya kuma Hajiya ba a yi mata karya. Na tashi na ja baya da sauri gaskiya kai zaka fada mata. Cikin shagabar da bansan na hi ba na yi maganar. Yace "In ba haka ba fa? " Na soma kuka nace sai dai ka kaini gida. Ya tashi ya fara daura agogonshi yana fadin can gidan sai kice musu munje Hotel kin ki bani hakkina na yi miki fyade mun kwana gashi Hajiya bata sani ba." Shikenan said Umma ta raka ki gida. Ya karasa maganar cikin dariyar da yake ta kunshewa. Nace kenan dariya ma ka ke yi ko? Yace "Kowa tashi ta fisshe shi." Ya fada yana hada kan wayoyin shi. Na zauna bakin gadon nace In kuwa haka ne gara in zauna a nan. Yace "Shabiyu tana cika zasu kore ki ne, su gyara dakin su. Ya zura takalmi ya dauki yagaggiyar rigata ya ce shike nan ni na tafi.... 🖊️🖊️🖊️ Da gudu na tashi na bi bayansa har ya shiga mota ya tada, ban damu da rigarsa da ke jiki na ba. Koda dai mutum biyu ne a Reception din, na nufi motar yana kallo na sai ya yi hanyar waje. Na kwasa da gudu na nufi gunsa, na bude gaban motar na shiga, da alamu dariyarsa ya sha domin har lokacin ita yake kunshewa. Nace da gaske da tafiya zaka yi? Yace "To me zai hanani tafiya tunda kince ke bazaki tafiba. " Nace tsoro nake ji Hajiya zata yi fada, da wane ido zan kalli Hajiya, sannan kuma dubi yadda ka maidani kayan ka ne a jikina fa.. Ya ce "Ki dai shirya bayaninki tun a nan kafin aje ki kasa magana. Ki fara shirya fada mata inda ki ka kwana da kuma dalilinki ". Nace mu fara biyawa ka saya min ko doguwar riga ce in baka taka ka saka mu fara zuwa gida a mutuce. Ya ce ba inda zani. "Ki barni inji da me zan fadawa Hajiya kema ki tanadi abinda zaki kare kanki." Nace kai ne zaka fada mata tunda kai ka ja komai, ni ban taba zuwa Hotel ba. Ya sake fafin kowa tashi ta fisshe shi. " Na kifa kaina a cinya takaici ya ishe ni. Ga tsoro ga kunyar Hajiya da zanji, ko yaya zata kalli abin? Nasan bazata ji haushin danta ba, abin akai na zai kare. Muna shiga kan ya gama fakin na kama kiciniyar bude kofa. Yace ki tsaya in fada miki wata magana, na kalle shi ya daure fuska, in har ki ka yarda na rigaki zuwa gaban Hajiya ke ce zakiyi yi mata bayani." Nace Allah ni ba zaka dora min laifi ba. Na soma kawo ruwan hawaye. Yace Au kuka zaki yi to shikenan ki yi. Daga nan zata fara gane cewa baki da gaskiya. " Ya bude mota ya fita. Nima na fita na bi bayan shi da sauri a falon daf dana Hajiya muka hadu. Ya kalle ni, "Gabana faduwa yake. " Ya fada yana kallona. Na tsoro ya kara kamani, in shi yana jin tsoro ni kuma yaya kenan? Ya sake fadin "In har na riga ki shiga ke ce wadda zaki yi wa Hajiya bayani. Da sauri na tura kofa na shige kafin ya rufe baki. Kamar yadda na zata Hajiya tana zaune a inda take salla da carbi a hannunta na shiga da sauri, na zauna a gefen ta. Ta waiwayo da sauri kamar ta firgita da ganina, ta kuma kafe ni da ido. Nace sannu Hajiya. Ta dauke fuskarta ba tare da ta amsa min ba. Jikina ya yi sanyi ko ba a fada min ba nasani dole ne in dauki Wannan Zunubin lokacin Ya yi sallama kamar wani salihi, ga mamakina sai Hajiya ta amsa sallamar harma ta kara da fadin an shigo. Ya iso ya zauna daf da ita ya yi kasa da kai yana gaishe ta. Ta amsa cikin fara 'a. Ya kalle ni ya yi wani murmushin mugunta, sannan ya dora min yagaggiyar rigata akan jikina ga rigar ki je ki cire min tawa. Na yi zaton Hajiya zata tambaya dan in samu in wanke kaina amma sai naga ta kalli rigar sannan ta sake kallon ta jikina. Sai kuma tace masa, in ka shiga ina bukatar takardun filin nan da aka siya a Fandanka? Yace suna jakata a kawo su ne? Tace ka fito da su domin a kwai wata magana akan gurin jiya lauya ya kira ni nace ya same ni a gida in kuma zaka fita kasuwa yau sai ku karasa can. Shamaki Yace zamu fita kasuwa sai dai kuma yau ina da meeting kashi uku ki hadu da lauya kawai. Akwai wadannan 'yan China da suke son stor dinmu na Sharada a nawa ganin gara mu saida musu tunda kinga bama komai a gurin, kuma zai yi daraja saboda su suke bukata. Ni dai na mike na nufi dakina a sabule. Na shiga ban daki na dan gasa jikina da ruwan dumi sannan na canza kayan jikina na hau gado na kwanta, ina tunanin wannan zama namu. Ina ta fadi tashin ganin cewa na samu zama na har abada amma wani lokacin sai inji jikina ya yi sanyi. Kamar dai yanzu da muka yi laifi amma sai ta wanke danta fes. Na fita lokacin karin kummalon su ya yi, Na samu Juma tana jere abinci, na shiga cikin dari dari, Hajiya tana zaune a kan kujerarta Shamaki a gefe ga takadu kusa da shi yana sanye da Jallabiyya. Na yi wa Hajiya sannu. Ta amsa ba tare da ta kalleni ba. Na fara da goge teburin ta na jikin kujerar ta wanda da shi take cin abinci. Nace me za a saka? Tace kunu zata sha na gyada. Na san abubuwan da zan hada mata in kunu zata sha. Na hada mata komai. Tace wa Shamaki "Ya kamata gobe a tashi da azumi a gidan nan tunda bikini salla ya kare sai a yi sitta shawwal ko? " Shamaki ya ce wannan tsuntsuwar data sani a gaba tin washe garin salla na fara, in nayi yau da gobe na gama". Na kale shi ya zuba min ido. Na yi kasa da murya nace na ci maka bashi ne da zaka zura min ido? Wai da Hajiya ta ji mu sai ya daga murya. Me ki ka ce? Na kalli Hajiya ta maido hankalinta garemu kuwa. Nace me zakaci in zuba maka? Yace ina azumi fa kin sani. " Nace Baka yi sahur yau ba, gaskiya bazaka yi dore ba, ka bari sai gobe tunda ka ga ai ba wai farilla bane. Yace "Baki tashe ni ba ne ai." Na harare shi, haka ma zaka ce? Ya yi murmushin mugunta, yace ashe fa gurin maulidi muka kwana. Hajiya ta kalle ni, ni kuma na kalle shi ya kauda kai. Azuciya ta nace karyar da ya yi kenan to wane maulidi kuma a salla. Ya katse ni, "Dama ke ki ka takura inyi in gama amma yanzu zaki zo da zamiya. Na soma zubo masa kunu, sai na tuna da wayon da nake yi wa Jafar din mu in ya ki cin abinci a ramadan ya ce wai shi yana azumi. Sai in zuba masa kunu in ce ya sha baya karya azumi.. Na mika wa Shamaki kunu cikin tsokana na ce kasha wannan baya karya azumi. Ya karba ya kurba, nace Allah ya yafe maka. Ya ce "Ameen amma alhaki a kanki. Ke ki ka sa na karya azumi. Ya dauki kosai daya da na zuba na tura masa. Ya gutsira yace na sani fa bakya son insha wahala ne ko? "Nace ta yaya zan so ka sha wahala, amma kai kana son insha ai tunda kai da kanka ne ka shayar... Ya nuna min Hajiya da ido, ya gane maganar jiya zanyi. Na rasa wani lokacin in muna tare da Shamaki gaba daya sai in manta da akwai wani a gurin. Juma ta sake shigowa tana fadawa Hajiya cewa man shanu ya kare tace za a kawo shi yau kuwa domin miyar danyar kubewa nake son ci. Tace to sai an kawo naman rago shima ya kare. Hajiya tace a yi ta kaza. Na tuna da irin yadda Tsohuwa ta bani labarin yadda Hajiya Zeena ta ke yi wa Hajiya Gwamma abinci da kanta, sai naji ina shi'awar in aikata hakan. Na ce Hajiya ina son in roki wata alfarma don Allah. Ba Hajiya ba hatta Shamaki ya dakata dan ya ji me zance. Ita kuma Hajiya da alamu yadda na yi maganar cike da kwarin gwiwa shine ya sa ta dakata, ko da dai na lura Hajiya tana son jin magana ko tsegumi amma bata nuna cewa ta damu da hakan. Ta ce ina jinki. Nace ina son ki yi min izini inna dafa miki duk abinda ki ke so. Ta dan yi kasake, sannan tace " "Ai baki iya girki ba, amma zan baki dama ki fara koyon girki a gurin su Juma, in hannunki ya fada zuwa lokacin da ki ka cika shekara daya sai mu duba muga ko zaki iya din ko? Haka ya yi miki? " Nace Na gode Hajiya, insha Allahu zan sa hankalina in koya. A zuciya ta nace in banci Jarabawa ba shikenan. Kukan Anisa ya dauki hankalinmu ta karaso da gudu Shamaki ya bude hannu amma sai ta fada Jikina tana fadin Mommy kinga Meema ko ta shanye min icecream kuma ba ni ce na bata ba." Shamaki zai yi magana Hajiya ta daga mishi hannu alamun ya yi shiru ta gefen ido na lura da su. Na rungume ta, nace, yi hakuri, na fara share mata hawaye. Nace. ba na fada miki Yaya meema zaki ce ba? Tace Yaya Meema ta shamin abuna. Nace zomuje daki zan baki wani amma ki ce kin yafe mata wancan din. Tace "e na yafe amma mommy za ki yi mata fada? " Na ce a a zan yi mata nasiha ne zakigani bazata kara ba. Na mike muje na bata Icecream ta tafi na dawo in tambayi Hajiya ko yaushe zan fara koyon. Tace "Ni da bani ce wadda zan koya miki ba, ai saidai ki tambayi Juma din ta fada miki ko? " Nace to Sai ga Meema da Mubina da gudu suma gurina suka zo Mommy mufa Icecream? Nace yawwa Yaya meema akn wane dalili ne ki ka amshi abin Anisa ki ka shanye shi? Tace Mommy tayi abazanci ne fa ta jiye kuma kin fadavmana cewa ba kyau." Muka sa dariya har Shamak, nace almunbazaranci aka ce, Duk da haka ba sha mata zaki yi ba, a matsayin ki na Yaya zaki sa mata a cikin fridge ne. Bana ce ke zaki na kula da su ba?Ta daga kai alamun E. Na ce in kuma bazaki na kula da su ba, to zan bawa Mubina ta zama Yaya. Ta kama kunneta "Na daina Mommy har yanzu ni ce Yaya ko? " Nace ke ce mana, amma in kuwa kin kara kuma zan ba Mubina. Muje in ba ku. Muka tafi. ...... A cikin satin na soma koyon girki, tunda Allah ya bani damar shiga kicin sai nayi amfani da wannan damar na ke yi Caearching da waya ta ina nemo kalolin girki na zamani, saidai Hajiya bata bukatar su, kuma ni ina son in koya, na fara tunanin yadda zanyi, sai na kuma zuwa na nema iznin Hajiya, nace ina son in ke dafawa su Anisa abincin zuwa makaranta maimakon Indomie kullum. Tace in fada mata dalilina kawai wannan ba shine ainihin dalilin da nake son yiwa yaran abin tafiya makaranta ba, nace ina shi'awar inga ina hadawa yaran abin kari ne. Tace "Bata Hana ba, amma in fada mata ya zanyi da Babansu? " Nace ai lokacin yana nan kafin Juma ta gama komai na karin kummalon gidan zan sallame su. Tace "Bana son a shigar min rayuwar da na saboda jika. " Nace zan kiyaye haka. Tace in gwada so daya a gani. Ranar na saka a zuciya ta zanyi. Daga sallar asuba na shige kicin. Dama tun dare na tanadi kayan girki na, soyayyar taliya mai kaza na fara yi musu Allah ya taimake ni nayi yadda naga an koyar kamshi ya cika gidan Shamaki ya tambayi Juma cewa yau kuma me ake dafa mana ne? Tace Mommy yara ce ta shiga kicin da kanta yau, tace yaran ta sun gaji da Indomie da planten yace "kice za su ci dadi. " Juma tace ga shi nan dai yana ta kamashi a range mana. Na hada musu lemon Apple da kwakwa da madara. Na zuba musu a cikin jarkokin su na makaranta wanda ake sa musu shayi. Tare da Juma muka kammala, na shige da sauri na yi wanka sannan nazo na samu suna jiran abin kari, na zuba musu lokacin yaran suka fito suka gaida Hajiya da Daddy sannan suka gaida ni. Anisa ta sunbaci kumatuna Mommy bye, nace bye kada ku manta da addu'ar fita gida, suka ce tom. haka suka tafi ina binsu da kallo cikin kauna. Haka kuma da Shamaki ya tashi ya nufi Cikin domin shirin tafiya Kasuwa haka nan kuma na tashi fatana Allah ya sa kar ya zo min da bukata tun da ya zamar masa jiki.Ni kuma na gaji tulus farko yi na yi kamar bazan je dakin ba. Hajiya tace "Kina son dai ya makara fita ne ke? " Haka na tashi na nufi ciki. Yana shirin shiga wanka na yi sallama, yace yawwa zo ki min wanka yau duk na gaji. Sai da na shiga don in masa wanka, ashe wai yau kuma a bandaki ya ke son biyan bukata da ni. Haka na yarda. Ina mamaki yadda Shamaki ke min. Ko haka kowane namiji ya ke yi wa matarsa shine bansani ba. Sai da ya tafi na dawo na karya na kwanta, aikuwa sai azahar na farka. Azima ta shigo kicin muna yin girkin dare, ta kalli Juma ta ce. "Ina son a yi min jolof na kuskus. Juma tace, sai mun karasa tukunna. Ta bata rai yanzu nake so. Na dago na dube ta kamar zanyi magana sai kuma na fasa. Juma tace yanzu sai Allah wannan 'ya me zan sauke in bai dahu ba in dora naki? Tace ko ma meye a sauke ina jin yunwa gaskiya." Nace Haba Azima kicI ga tuwo can angama, ko ga sauran abincin rana in kina so, amma ayi miki sabon abinci bayan ana aiki da gurin sai ki jira. Ta kalle ni a fusace tace, "Amma dai kin jira na saka sunanki ko? " Raina ya baci domin bana yin rashin kunya kuma bana son me yinta ko kada. Nace bazata dafa miki ba, in kin matsu ki dora da kanki. Ta dube ni ke a wa kuma!? " Na yi mata banza, Juma tace Kiyi shiru 'yarnan ki rabu da ita a dafa mata. Nace wallahi baza ki dafa mata ba, ko mun gama zangani ni da ita.. Ta fice fuuu Juma tace yanzu zataje ta zanawa Hajiya. Nace taje mana waye bawanta? Tace ai matsalar Hajiya tana da kwatanta gaskiya amma tana da son nata, amma dai yanzu bari muga yadda abin zai zama. Shiru bata dawo ba har muka gama wai Juma bari ta dafa ta kai mata, nace bazaki dafa ba. Na zaci Hajiya zata min magana amma shiru har zuwa washe gari da na tambayi Juma ko Hajiya ta yi mata magana tace ai na yi mamaki Hajiya bata yi maganar ba. Amma da ace da ne fada zatayi sosai tace dan haka ta dauki masu aiki su kula mata da gida, kuma kowa a bashi abinda yake so yadda muma bata taba yi mana Shamaki da abinda muke so ba. Nace ni dama haushina take ji Azima bansan me nayi mataba. Tace ga abinda ki ka yi mata nan kin auri wan da take mutuwar so, yarinya karama kar kiga irin yadda ta ke kicifi a kan sa. Nace ai gashi nan zata aure shi ni menene nawa. Juma tace auren ma ai ba wata daraja zata yi ba, tunda ta zubda kai, a waje sai dai ina mamakin yadda Hajiya ta yi gaggawar saka rana duk da cewa yarinyar ta yi ciki, kuma ya ce ba shi bane amma ta kuma ce shi zai aure ta. Son kai irin na Hajiya ina mamaki sai dai da yake duka nata ne. " Nace Allah ya kyauta amma ai dole ta yi abinda zata rufawa 'yar dan uwanta asiri. Juma tace haka ne, amma abin da mamaki. Nace to ke kina tunanin ko shine ya yi mata? Tace 'A'a ni bance ba. Ina zan sani 'yannan karki daure ni, Hajiya ta ji na fadi haka ai sai tasa an rataye ni. " Nace Juma ai dan Adam bashi da garanti kuma zuciya bata da kashi. Tace Hamm haka ne, Allah dai ya shirya uwar wannan yarinyar ta biyun bana rike sunanta. " nace Mubina tace, "ai bata cika magana ba, amma ta kamashi da wata yarinya amma Hajiya ta shafawa idon ta toka tace anyi wa danta sharri." Nace abin dai sai addu'a. Tace shike nan kin gama magana. Bisa ga dukkan alamu Juma suna zargin shine wanda ya yi cikin kamar yadda nake zargi. Amma zan yi kokarin bincikar haka. Wata asabar ta karshen mako, ya fita motsa jiki da safe, lokacin da na fita gaida Hajiya baya gurin, na zauna na gaishe ta, ta amsa, zan tashi tace ina da magana da ke, gaba ya fadi, na koma da sauri na zauna. Tace "Da anyi babbar salla da sati daya za a daura auren Azima da Shamaki. Na hadiye yawu da kyar, tace gaba, "zai aje ta a daya daga cikin gidajensa dake unguwar nan ko kuma wata unguwar dake kusa da wannan, amma kije ki yi shawara in ke ce ki ke son ki zauna a can to na baki kwana biyu ki yi tunani ki zo ki fada min . " Na ce ba sai na yi wani tunani ba, duk yadda ya yanke ai shine mai gida. Hajiya Tace "Kije dai ki yi tunani karki yanke shawara cikin fushi, yau saura kwana arba'in a yi biki, bana son danasani ne a rayuwa, kuma bana son yin abu ba hujja shiyasa na baki dama, kiyi tunani kuma ki yi shawara a inda ki ke da yarda da aminci. Bana son jayayya ba halinki bane kije sai na jiki. Na ce to na tashi na nufi daki jiki ba karfi. Nafada kan gado na saki kuka, bansan ina son Shamaki har haka ba. Hajiya bata san zafin kishi ba tunda ba ayi mata kishiya ba. Shiyasa take fada min maganar auren mijina kamar yadda zata fada min abin arziki. Na dau lokaci ina yi sannan na lallashi kai na, na nufi dakinsa don inga ko ya dawo. Ya kashe wayoyin sa ya zube su a kan gado. na kunna wadda nake bincike na shiga ina bi, har yanzu dai yana nan akan halinshi akwai wadda na lura sun dinke da alamu yana matukar son ta kuma ya nuna ya matsu su hadu. Na dakko wayata na dauki lambarta. Na saka wayata na kashe masa na koma daki. Ina ta shawara in kira ta ne ko kuwa in goge, me yasa nafi kishin wadannan matan wajen akan Azima wadda zai aura. Nasan yana fada min kalamai, amma meyasa baya fada min irin wadanna. Me yasa ina masa duk yadda yake so koda ni bana so amma hakan bai hana shi bin matan baza ba. Na kira Umma muka gaisa na fada mata cewa maganar auren Shamaki ce saura kwana arba'in yau. Sai naji zuciya ta ta karye, na soma kuka. Umma Cikin sigar lallashi tace menene abin kuka, ki share hawaye mu yi magana. Nace Umma wadda aka yi wa kishiya kawai zata iya gane me nake ji a halin yanzu. Umma tace, "Ni dan ba a yi min ba shine yasa bazan fahimci radadin da ki ke ji ba? " Cikin kuka nace Umma kirjina kamar zai fado, ni sai inji ma kamar ince masa ya sawwake min, ina cikin damuwa Umma. Tace "Amma ban taba jin ance wata ta fadi ta muru dan kawai anmata kishiya ba. Dan haka kema bazata gagare ki ba, abu ne ma kowa ya zauna da halinsa. Shi mijin naki ya canza miki ne? Nace A'a bai canza ba. Shi ko maganar so daya ya min, Hajiya ce tana fada min kamar mai fadin alkhari ko a mijinta. "Umma tace alkhari ne mana insha Allahu. Ke dai ki kwantar da hankalin ki kar ki nuna cewa abin ya dame ki ko da wasa. Ki zuba ido akwai Allah Karki yarda ko da kalmar magana ki cutar da wani, ki sa zuciya daya tsakanin ki da kowa, kuma gara a ce kai aka cuta da ace ka cuci wani. Nace insha Allahu. Yanzun ma Hajiya ce tace wai wani gidan za a kai Azimar amma in ina son ni a kaini can to inyi shawara ni ina ganin gara in bar gidan nan domin Hajiya ni ba wai ina son ganinta bane tunda ta min wannan maganar. Umma tace ko kusa karki matsa ko ina. Hajiya tana bukatar ki kusa da. Ki nutsu ki fahimci maganar, Zai aje amarya a wani gida, amma in kuma na so sai ke ki koma can. Ina fatana kin gane cewa can din ba naki bane. Nace shikenan zan zabi nan din. Tace yawwa Allah ya miki albarka ya baku zamavlafita dukanku. Na cw ameen. Na dan samu sauki da Umma ta taushe ni. Idanu sun min jawur fuska ta kumbura. Na koma kan lambar yarinyar nan. Na yanke shawarar in kira ta. Na kira tayi ringing ta katse a na biyu sai aka daga, bance komai ba na yi shiru sai naji ance "Waye ne.? " Gaba ya fadi kunsan muryar wa naji?? Muryar Azima naji wadda na yi sauri na kashe jiki na ya kama rawa yanzu Shamaki saboda Allah ya yi wa kansa adalci kenan? Na yi shiru ko zan iya tuna kalaman da suka yi musaya na batsa. Na mike na nufi dakin dan in sake dubawa, muka ci karo da shi a corridor din dakin. Muka kalli juna. Yaune na fara jin wani abu na tsanarsa a zuciya ta na kauda kaina sannan na juyo Yace "Baby/" Na tsaya can ya tako zuwa gurin ya kama kafada ta ya juyo da ni, ya dago fuska ta "Kukan me ki ke yi? " Nace ni banyi kuka ba. yace "kar ki yi min karya ga nan fuskar ki a kumbure." Na ce bacci na tashi. Ya ja hannu Na muka nufi dakin shi. Bakin gado ya zaunar da ni wai in fada masa me aka yi min. Na kafe akan ba komai har ya fara fusata, yace shine nan tashi kije tunda kin kafe. " Na mike na nufi dakina, dama ni zantukan shi sun dame ni. Na kwanta ina mai bankin cikin auren Shamaki da na yi. Yanzu banda ta'addanci me zai sa ya lalata rayuwar Azima. Aure za su yi amma yana son ya lallaba ya lalata auren ta hayar kwanciya da ida. Wai shi baya jin kunya ne sam? Wannan ce rana ta farko da na ki fita gurin saka musu abinci domin kowa na gidan haushi yake bani. Na kwanta na rufa. A falo Hajiya ta kalli agogo "Me yake faruwa matarka bata fito ta zuba mana abin karyawa ba?" Yace Zazzbi ne ya rufe ta bari in zuba mana. Na shiga dakin tana kunshe cikin bargo. Hajiya ta yi dan murmushi sannan tace Allah sarki, kishi kumallon mata. Dazu nake fada mata maganar aurenku da ya karato shi ne abinda ya sa ta a dumuwa. Shamaki yace Ai da kunrabu da ita baku fada mata ba. Hajiya tace "Ai hakki ne kowa a fita hakin shi, ba zai kyautu a rufe mata ba ba adalci bane. Amma yanzu in abin ya sauka bazata kuklaci kowa ba. Shamaki yace to yanzu ta san kwanakin kenan.? Hajiya tace ta sani harma na bata zabi in tana son komwa gidan da za a kai Azima ne shikenan sai ta koma." Shamaki Yace zai fi kyau ta zauna nan ga ki sannan ga yaran nan suna sun saba da ita. Hajiya tace zabinta shine adalcin ta, kar ma ka nuna mata kasan munyi wannan zancan bare ka ce zaka bata wata shawara, nace ta yi shawara a gurin da take da aminci. Yace bazan yi maganar ba. In takaici da bakin ciki suka hadunmin guri daya sai na yi wani dan baccin wahala kafin in samu zuciya ta ta sauka. Dan haka yanzun ma baccin ne. Lokacin da na farka shabiyu ta gota, na tabbatar Shamaki ya fita kasuwa. Na yi wanka sannan na fita falon Hajiya. Hankalinta ya dauku ga TV na zauna ina yi mata sannu. Ta waiwayo ta dube ni. "Kin fito ashe baki hi sadi ba?" Nace lafiyata lau Hajiya bacci ne ya dan sace ni, kuma sai be tashe ni ba ya fita. Hajiya tace baki saba bacci a irin wannan lokacin ba, in ba Zazzbi bane to maganar da zu ki ka sawa zuciyarki damuwa kenan? " Nace Kai haba ta yaya zan damu bayan na sani tuni. Hajiya tace to na dai fada miki run kwanaki karki dagawa kanki hankali akan abinda babu fashi. Yanzu ma sun fita tare da Azima din zai aje ta gidan maman Nana domin za su fara yi mata gyaran jiji. Sun fita tare? Na tambayi Hajiya da sauri, tace "Ayya karki damu fa, wata rana a gidanta zai kwana, ya kamata ki sawa zuciyarki salama. Nace Hajiya kina da tabbacin can sukaje? Ba ina zargi bane amma a kalla su yi aure mai tsarki. Fuskar Hajiya ta canza "Me kike nufi kenan zargi zaki jefa wa auren su? Nace a a ba zargi zanyi ba a yi hakuri. Na tashi na shige daki. Hajiya ta dinga juya maganar Baby, kodai yarinyar nan ta san wani abu ne game da Azima da kuma Shamaki. Ta dakko wayarta ta kira layin Azima, ta daga. Tace kina ina? Tace gidan Maman Nana ta ma fita bata sameta ba. Hajiya tace ina Shamaki?"Azima ta ya wuce kasuwa. Hajiya ta kira Maman Nana suka gaisa tace tana "Kina Vida ne? "Maman Nana tace ina gida Ina jiran Shamaki yace zai kawo Azima gashi har mai bata magungunan ta iso. Hajiya tace suna hanya.. Da sauri ta kira Shamaki tace ka kai kasuwa ne? Ina son Zuma ne. Yace e na kai zaki aiko direba ne ko kuwa har in zan dawo in taho da shi? Tace a bari har in zata dawo. Sai da kira Hassan ta ce Shamaki ya kara so? " Yace a a bai iso ba. Tin saga nan Hajiya ta san akwai matsala.. Ta mike tsaye zumbur kalaman Baby suka fara zuwa mata a kai. Ba ina zargi bane amma a kalla su yi aure mai tsarki! Hajiya ta koma ta zauna ranta ya ba ci. Ta kuma Kiran wayar Shamaki Ya daga tare da fadin an kawo zum.. "Dakatar da wasan kwaikwayon haka. Kar ku sake ku aikata wani abu ka dawo yanzun nan, na san a inda ku ke kuma nasan me kuke shirin aikatawa. Minti shabiyar na baku ku dawo.! " Ta kashe wayar. 🖊️🖊️🖊️🖊️ Ni dai a daki in kai mari in kai gwauro na kasa sanin tabbas sun tafi yin shshanci ne lokacin ya yi da ya kamata inyi magana da Shamaki ya sani cewa na fa san me ya ke ciki. Na zauna ina magana ni da kai na. Ina tambayar kai na da wane lokacin ya kama in masa magana? Me ya kamata in fada masa? Kuma a fusace zanje masa ko ta ruwan sanyi? Wata zuciyar tace duk wata matsala ta duniya ana iya warware ta ne ta hanyar masalaha haka malamin mu ya fadamana. To in har haka ne zan biyo ta hanyar masalaha, kuma zan fada masa na san duk wani abu da yake aikatawa, kuma zamuyi magana da daddare. Shamaki ya kalli Azima yace an samu matsala. Azima ta aje Jakarta a kan durowar gefen tangamemen gadon dakin Hotel din. Tace me ya faru? Yace Hajiya tace muje yanzu. Azima zaro ido tace na shiga uku Yaya Shamaki ya akayi Hajiya ta gane ne? Shamaki ya ce yadda ta yi ta kiranmu na tabbatar tana son ta fahinci wani abu ne. Azima tace yanzu ya za a yi kenan? Ya ce zuwa zamuyi illar daya ce karyar da muka yi mata. Azima tace ina zargin matarka ko ta san wani abu fa. Ya dube ta da sauri. "So nawa zan fada miki cewa ki daina saka matata a cikin damuwarmu? " Ta yi shiru ya dauki makullin mota ya fice, ta ja tsaki wannan shegiyar matar ta sa natsane ta zan iya kashe ta in har zan samu dama. A mota ta same shi ta shiga. Ta dube shi Yaya Allah ya baka hakuri. Ya dube ta, abinda ki ka iya kenan anjima kuma sai ki sake kiran sunanta, bayan ita da zaki auran mata miji ko kallo baki ishe ta ba. " Tace ai ni ta auran wa mijina. Ya taka wani uban birki zaki fita Yanzun nan a motar nan sai dai ki koma a ta haya. Azima ta taba baki, babu damar ta yi masa magana tasan akan wannan figigiyar zai iya aikata komai. Azima ta shiga cikin gida kai tsaye zata wuce sasan su. Hajiya tace zonan. Azima ta dawo kai a kasa tace ki je dakina. Hajiya ta kulle kofa, tana kallo Azima ki fada min gaskiyar inda ki ka je, ko kuma in kashe ki a nan, iya kacin dai a sanar cewa kin mutu aje a binne abar banza kowa ya huta. Azima cikin firgici tace, ba inda mukaje mun biya ne ta gurin siyan Icecream zai sayawa yara. Hajiya tadan yi shiru kodai zargin su ta ke yi. Amma dai bari ta kara latsawa. tace "Ba can kuka je ba, har hoton ku an turo min lokacin da ku ke fitowa daga mota ku ka shiga dakin Hotel. Azima ta gigice cikin firgici tace Hajiya Shine wanda yace muje Hotel tun da ya biya sadakina. "Shi wa? "Hajiya ta katseta. Yaya Shamaki mana. Hajiya ta daka mata tsawa "Ki rufe min baki makira, kece wadda ki ka ja ra'ayinsa, bayan na roke shi ya amince ya aureki a haka babu kimar shine sai kin gwada masa cewa ke 'yar barikice. To me kuka aikata a inda kukaje? Tace zuwanmu ke nan kika kira wallahi namu yi komai ba. Haushi ya sa Hajiya daukar robar turaren wuta ta bugawa Azima a goshi. Har kina iya fada miki min haka kin zubda kanki mara daraja kawai. Fita ki jira hukunci na. Azima ta dafe goshinta sannan ta fice da sauri. Hajiya ta zauna bakin gado tana maida numfashi ta rasa wane irin tunani ya kamata ta yi. Shamaki yana zaune a falo, duk da karfi irin na Ac amma bai daina zufa ba. Fargaba yake yi, in Hajiya ta fito bai san abinda zai fada mata ba. Fitowar Azima a guje ta nufi dakinta da gudu, Abinda zai sa Hajiya ta shiga dakinta ba a lokacin bacci ba yana da girma. Tana sako kafa falo suka hada ido. Ta juya zuwa daki, baya bukatar sai ta fada masa cewa ya biyota. Ya aje hula kan kujera ya fada dakin cikin fargaba. Kafin ya gama gano ina Hajiya take tuni ya ji saukar tafi a kuncinsa dau. Hajiya ta aje masa. Cikin mamaki ya dafe kuncin ya sunkuyar da kai. Yaudai karya ta kare,. Shamaki ya furta a zuciyar sa. Hajiya ta soma magana a hasale. "Nayi mamakin ka sosai Shamaki Na dauka cewa duk wani uzri da nake yi maka zai sa ka gane cewa ina yi maka karane kawai, nasan abinda ka ke ciki nasan kaine ka yiwa Azima ciki. Kuma shiyasa nace kaine zaka aure ta. Taimako daya Allah ya yi maka dana fada maka baka min gardama ba. Wa zan kaiwa ita ka gama kwakuleta. Nasan kana bin mata meke damunka ne? To ina son ka bude kunne da kyau ka jini. Bayan la'asar za a daura muku aure yau din nan in ya so sai kuje duk inda zakuje. Sannan matarka ta soma gano cewa kana bin mata, saura ka yi sakaci har ka bata tabbaci. Shamaki ya kasa dago kai ya kalli Hajiya, kunya ta ishe shi. Tabbas ya kai makura tunda har Hajiya ta sa hannu ta zabga masa mari, abinda bai taba fuskanta ba a iya tsawon rayuwar sa. Hawaye wanda bai san ko na menene ba suka soma kwaranya daga idanun shi, ya zube kasa ya kama kafafunta. Na san cewa a yau na kai ki makura. Ki yafe min insha Allahu bazan sake ba. Ta zauna a bakin gado ita ma ta soma zubar da Hawaye, yau da mahaifinka zai dawo Duniya zai yi bakin cikin ganin ko jin cewa kai dansa daya jal kana aikata laifi irin Zina harda ta cin amana a cikin gida. Kana da dama ta yin mata har hudu kana da karfin rike mace dubu me ka ke lake ne a wajen matan banza? " Yace na daina Hajiya wallahi naji kunya da yawa, ina yin dana sani sosai. Ni ina can bansani ba, ya fice. Lokacin da na fito tamkar wani abu bai faru ba domin banga komai ba. Hajiya tana mazau nin ta na yi mata sannu na shiga kicin domin gabatar da abincin rana. Juma tace "Uwar dakina me yake faruwa a gidan ne? "Nace wani abu ki ka gani? Tace Uban dakina Shamaki yaudai ya fusata Hajiya da rana suka rufe kofa suna tattaunawa, sannan wannan yarinyar Azima sai gata da kuka. Nace Juma bansan komai ba, suda basa gidan? Juma tace "To sundawo nace amma bai shigo gurinmu ba. Tace to bandai sani ba, amma Allah yasa inga Annabi haka yadda na ganshi." Na tsaya ina kallon Juma ta ce, "Hajiya dai cin zarafin su ta yi, domin yadda na ga yarinyar nan kamar ma kuka ta ke yi. Na sauke ajiyar zuciya kila maganata ta yi tasiri na ayyana a zuciya. Nace ke to ina ruwan ki Juma, kince bakya gulma amma dai kina sa ido. Tace "A a "yannan karki yi min mummunar fahimta. Bayan an idar da la'asar sai naga kawu ya shigo da wasu maza, da goro da kuma dabino. Na tashi na basu guri ina zaton an saka rana ne. Da dare na samu Hajiya da Shamaki kamar yadda na saba amma shi kamar yana ta dan dari-dari. Yau Ni kai na ya kasa kallo na. Hajiya tace in shafa mata magani da wuri yau zata sha magani ta kwanta. Nace Hajiya bakijin dadi ne? Tace yau kam jikina ya yi nauyi zan kwanata da wuri. shima ya yi mata sannu kafin ya dauki carbinta ya bi bayan ta. Na koma dakinsa ina jiran zuwan shi. Suna shiga Hajiya ta hau gado ta zauna ya dakko mata magani ya mika mata, ta amsa ya bata ruwa ta sha. Ta kalle shi, "Yinin yau da bakin cikin ka na yi shi. Amma na yafe maka, ina son ka roki Allah ya yafe maka. Yace na gode Hajiya insha Allahu zan roke shi kuma har abada na daina. Tace Allah ya sa haka. Tun lokacin da na fahimci cewa kana bin mata na baka dama ka yi mata hudu kuma bani da zabi ka zabo mace ba ta shi'awa ba wadda ka ke so kuma ka ke kauna. Ka auri yarinyar nan domin kana son ta na tabbatar kana son ta amma me yasa ka ke fita waje neman mata? " Yace ki yafe ni Hajiya amma ba kamar yadda ki ka zata ba ne. Bani da sauran abin cewa dai amma ina neman yafiyar ki insha Allahu, ban taba jan kunya kamar yau ba a duniya. Hajiya tace ya wuce, gata can a daki yanzu kam matarka ce duk abinda ku ka ga dama kuje ku yi, sannan ka gyara inda zaka sakara ba wani taron biki da za ayi, na baka sati daya ku tare bana bukatar zama da Azima a gidan nan. Sannan ka sani yin adalci a tsakanin matanka shine abu mafi mahimmaci da ya kamata ka maida hankali a kai. Yace insha Allahu. Yanzu dai bansan yaya zan fuskaci Baby da maganar auren nan ba. Hajiya tace wannan ya rage na ka, duk a baya ni ce nike fada mata wannan karon sai ka fada mata. Ta bishi da kallo, banda soyayyar da da uwa wadda Allah ne ya dora min da tuni na fita a sabgarka. Ka tafi zanyi bacci. Ya shigo dakin jiki ba karfi Ina kwance ina kallon TV, na bishi da kallo ya cire kayan jikinsa ya fada bandaki. Ya yi wanka ya fito, ina ta share shi wai ni irin ya tambayi dalili sai mu zauna a zube magana, amma sai naga shi bama ta ni yake yi ba. Ya hau gado ta kwanata kamar dai nima share ni ya ke yi. Na kalle shi ina mamaki. Nace ka tashi zamu yi magana dama kai nake jira. Yace a yau ba wata magana da zan yi da zai yiwu da sai kawai ki tafi dakin ki. " Gaba ya fadi, nace ni kake Kira? " Ya ce to kwanata amma ki min shiru ina son inyi wani nazari ne. Ban kuma magana ba, na tashi na fice daga dakin na nufi daki na. Na sha kuka a daren naga bazai kaini ba na dauro alwala. Akan sallayar na kwan bayan nayi ta salla na gaji na zame na kama bacci. Washe gari na nufi gaida Hajiya amma bata falo, lallai akwai damuwa jiya ta kwanta bata jin dadi. Na nufi dakinta. Tana cikin bargo sai fuskar Shamaki yana zaune a bakin gadon yana waya da likita. Na isa na durkusa a bakin gadon nace Hajiya ya jikin tace da sauki bacci na kasa yi a jiya gashi dai har yanzu.. " Nace Allah ya baki lafiya Hajiya. Tace ameen. Likita ya zo jinin Hajiya ya hau da yawa, ya zuba mata allurai a cikin ruwan da ya sa mata. Ba a jima ba bacci ya yi gaba da ita. Shamaki ya kalle ni fuska ta a daura yace Baby jiya kin yi fushi ko? Na zura mishi ido ya ci gaba. Kiyi hakuri ni kaina ina da magana amma Hajiya bata jin dadi shine dalili. Bari ta samu sauki sai mu y maganar. 🖊️🖊️ A ranar dai Hajiya daki ta yini Shamaki ma sai azahar ya fita kasuwa, ni kuma na yini da Hajiya a daki saboda baccin bai yi tsawo ba ta farka. Na bata fura ta sha, sai kayan marmari da na matsa mata ta ci. Har zuciya ta ji nake kamar in baiwa Hajiya lafiya. Lokacin shan magani ya yi na bata. Lokacin salla na yi mata alwala ta yi salla tana daga kan gado. Shamaki kunsan duk minti goma sai ya kira waya ya ji batun jikin. Yace min ko ya fadawa su maman Umar ne. Nace a a karya daga masu hankali ka barsu. Hajiya da ke kwance tana jin mu sai ta daga. Nace ya fada musu, ta girgiza kai alamun a a. Umma ta kira ni, nake fada mata jikin Hajiya tace Allah ya sawake, sannan tace akwai wani magani da Abbanmu ya siyo mata lokacin da ta yi wannan haihuwar na hawan mini ne ana sha da zuma taji dadin sa ko ta aiki Jamila ta kawo mana. Nace bari dai in fara tambayarta domin nasan su basu cika bawa maganin gargajiya muhimmanci. Na fadawa Hajiya tace a kawo mata. Kwanan Hajiya biyu tana jinya ta murmure ta samu sauki. Duk bansan an daura auren Azima da Shamaki ba. Sai a rana ta uku. Wadda ta kama juma'a. Shamaki yaje daurin auren wani abokinsu daga can ya dawo gida, nace ai na yi tsammanin Kasuwa zaka wuce, yace kayan jikina zan canza bana son fita kasuwa da babban riga musamman ta shadda. Na amshi rigar da hular na nufi dakin shi. Ya shigo dai dai lokacin da nake saka hular a mazauninta. Ban ankaraba sai naji ya cakulkuli a gefen cikina na saki hukar nayi zillo nace wayyo, na fara dariya. Yace kwana biyu dai kin share ni, har wani shakkar taba ki nake yi." Nace ni din ka ke shakka babban bako, ni a suwa zakaji shakkata? Ya zauna ya janyo ni ya zaunar da ni a cinyar sa. Yace Baby dan Allah kifahimce ni akan abinda zan fada miki yanzu. Na ce ina jinka, kaima ka san cewa zan fahimce ka. Yace "Wallahi an daura auren mu da Azima shekaran jiya Waccan. ' Yawun baki na ya kafe, kirjina ya buga, sai naji cinyarsa ta zame min kamar na zauna a kan kaya. Dan haka sai na zame na zauna a bakin gado. Ya zuba min ido, ni kuma na kasa magana domin bani da yawun da zan sarrafa. Kallon shi kawai nake yi. Yace "Ban yi domin cin fuska ba, Hajiya ta yanke hukunci itama bisa wani dalilinta wanda bata fada min ba. Kuma ta bani sati daya in tare da Azima a wani gidan, ko da dai tace ta baki zabi ko? " Har lokacin ban furta komai ba, na dai mike ina dan kai kawo a gaban gadon so nake indan samu makoshi na ya yi danshin da zan yi magana. Na isa karamin fridge na dakin na bude na dauka ruwa na bude ina kwankwada kamar wadda ta kai azumi a cikin sahara. Sai da na shaye tas na aje robar, na kalle shi kamar zanyi magana, amma sai na fasa, na sa kai na nufi dakina domn bana son in masa kuka. Ina son inyi tunani kafin in yi masa magana, sannan ina son in sauka daga giyar kishin da ya danne ni ya duramin ita babu zato ba tsammanin. Na fuskaci kuka rahma ne duk lokacin da ma ace in yi shi don in samun salama a cikin duk wata damuwa da na samu kaina, amma yau kukan ya ki zuwa ko zuciyata zata rage radadin azaba. Na fada bandaki nayi alwala na fito duk da ba lokacin yin salla bane sai na zuba sujja ina kiran sunayen Allah. Kar ku ga laifina ina da mugun kishi, wanda ba ni nayi wa kaina halittar shi a zuciyata ba, Allah ne ya dasa min. Na kwanta kan sallayar ina furta hasbunallahu wa ni'imal wakil. Sannu a hankali sai wani sanyi ya ke sauka a zuciyata. Ina jin taku tafiyar shi da kamshin turaren shi, ban dago ba har ya yi zaman dirshan a gabana. Yace "Baby. " Yanzu kam na shiraya yin magana da shi, na dago a hankali na kalle shi. Yace kiyi hakuri ni ma banso haka ba. " Sai lokacin wasu hawaye suka soma zirya a kumatuna. Cikin rawar murya nace tambaya daya zan yi maka, ina son ka daure ka fada min gaskiya. Dasauri yace "Insha Allahu. " Na ce nasha karantawa a littattafan hikaya kuma na yi imani haka ne, so daya ne tak ya ke, kuma mutum daya ake yi wa. Mu kuma a gurin ka Allah kadai ya san adadinmu sai kuma kai, ina son in san wakafi so ina nufin wannan son kwaya daya tak. Ya mike da Sauri tare da fadin "point of correction! Baby,! ke da Azima zaki ce ba wai baki san adadi ba. Ina da wasu kenan ko ya ki ke nufi? " Na tashi na koma baki gado na zauna. Ya zo ya zauna shima, dole ne in latsa masa basira domin in fahimci wasu abubuwa. Nace Duk da na kasance karamar yarinya ba haka yana nufin bani da wayo ko basira ba, sannan duk da kasancewar iyayena talakawa ba haka shima yana nufin baza su binciki wa za su baiwa 'yarsu ba. Sa a daya akayi a lokacin sakamakon ya biyo ta hannu na, sai dai wutar sonka da ta ruru a zuciyata ta sa na boye sakamakon ko nice na canza gurin mummanan shima ya koma kyakykyawa. Ina tunanin wai ko zan iya zama silar canza warka, amma Sai gashi na kusa cinye rabin shekara ban iya wani katabus ba. Na lura Ya firgita, amma da yake namijin duniya ne, sai naga ya dake, yace "To me aka fada a kaina wancan lokacin? Kuma me ya baki tabbaci game da zargin har kuma ki ka gaskata? " Na yi murmushin takaici, ka san abinda nake nufi Shamaki, ina jin nauyinka har yanzu bazan so muna tattauna wannan maganar gatsal ba. Ka sani magace ta neman matan ka. Kuma na samu tabbaci ne daga cikin da ka yi wa Azima. Sannan auran ku da aka daura a shekaran jiya, ya samo asaline daga fitar da ku ka yi kai da ita kuka fake da zuwa gidan Maman Nana. Ya yi shiru ya sunkuyar da kai. Na ci gaba, har yanzu ina son ka, ina jin ka a zuciyata, ina son ka bani amsata kafin muci gaba da tattaunawa game da wannan matsalar. Ya juyo ya kama hannuwana biyu, " Me ki ka sani game da ni? " Na daga ido na kalle shi. Abubuwa da dama. "Fada min wani abu guda daya." Na juya masa baya Cikin bakin ciki nace, A tafiyar da ka yi zuwa kasar waje ka tafi da wata yarinya. Ya sa hannu ya juyo da ni, muka kalli juna cikin ido hawaye suka soma zubowa daga cikin gida nuna. Nace me ya sa haka Shamaki? Me yasa bazaka aure su ba.? Kai babban mutum ne, kai uba ne na yara mata, ka kare musu mutucin su mana. Ya dora yatsa a kan laben na, ki yi shiru ki taya ni da addu'a Kuma, zanyi iya kokari na inga cewa na daina. Sannan maganar Azima ita ce ta yi ta shige min tana kawo kanta dakina da sunan tambayar wani abu, zuciya bata da kashi Baby amma dai komai ya wuce Insha Allahu. " Na sauke ajiyar zuciya. Sannan na rungume shi na ce don Allah in ka ga wata a waje ta birge ka to ka zo gida ina nan ina jiranka. Sannan ga Azima, in kana da bukatar karin aure kar ka damu da ni. Gam ya katse ni a jikinsa, yace na gode da ki ka Fahimce ni, dan kuma nasan zaki rufa min asiri ko su Umma baza su ji ba. Nace karma damu. A cikin satin aka yi gyaran gida ranar lahadi aka kaita, ba kowa sai wasu 'tan uwan su sai yayun Shamaki. Ni kuwa na fito falo gurin su aka gaggaisa ko a jiki na. Maman Iman tace wai meyasa ban yi kunshi ba. Nace mata na ga ba taro za ayi ba shine kawai ban damu kaina ba. Ta taba baki tare da fadin aifa. Wata matsala sai da ya zo wai in hada mishi kaya a karamin akwatin sa, na zuba masa harda jallabiyu da yakan sa da safe, komai da na san yana amfani da shi, na rako shi Hajiya suna zaune da wata kakar Azima. Ya yi musu sallama ya tafi. Na dan zauna gurin su Jim kadan na tafi daki na na kwanta. Bacci fa sai ya gagara zuciyata sai hasko min su take yi, gaskiya kishi bala'i ne. Yadda na ga rana haka na ga dare, ina yin salla na fito na shiga kicin Hajiya tana lazimi lokacin. Na gama na zo na gaida Hajiya, tace ya kadaici. " Nace haba ai ba wata damuwa ai yana tafiya kuma in zauna ni daya. Tace haka ne ayi ta hakuri dai. Na yi dan murmushi. Na yi ta zuba ido inga ya zo da safe shiru, ba ango sai wajen azahar sannan ya shigo lokacini ina hadawa Hajiya fura. A ciki muka amsa masa gaisuwa daga ni har Hajiya. Ya zauna ta kalle shi, me ya hana ka fita kasuwa? Yace hadari ne aka yi dazu sai na kwanta Kuma bacci ya dauke ni. Na mike na nufi sasana, yau sai naji gaba daya haushin sa nake ji. Bansan ya suka kare da Hajiya ba, na garkame dakina. Ina jin kwankwasawar shi na share shi. Domin na zaci cewa zai zo da safe, ko dan Hajiya. Ya kira waya ta ina kallo, sai da ya yi kira biyar a jere sannan ya hakura ya tafi. Sai da na tabbatar ya tafi sanna na fito. Haka na yi ta masa har kwana uku muna wasan buya. Ranar ya ritsani a kicin muna girkin dare, yacc wa Baba Juma da Tabawa su dan fita. Ya dube ni, "Saboda ke na dawo daga kasuwa yau da wuri. " Na dubw shi kamar wani abu bai faru ba. Nace lafiya zaka dawo saboda ni? Ya zaki fada min memene abinda na yi miki wanda ya sa kake guduna? Nacc ban gane gudu ba. Yace Kinga nifa bazaki yi min wannan azabtar war ba. In wani laifi na yi miki don Allah ki fada min in baki hakuri. " Na yi 'yar dariya . Nace baka min komai ba. Juma ta shigo tana fadin gafaradan ku dai, naji girki na yana kauri. 🖊️🖊️🖊 ️Na kalli Juma wadda ta je tana kashe gas ta dan tsaya ko zata tsinci wata Magyar a raina nace kai Juma akwai ta da son jin zance. Yace Juma kin kashe gas din? " Tace na kashe Dannan Ta fice ba don ranta ya so ba. Ya dube ni. "Yi magana ina jinki." Nace Dan Allah ka tafi sabgogin ka, ni ba wani laifi da ka min, haka kuma banga abinda na yi maka ba. Yace "Ke da Hajiya duk kun canza min ko kinsan wani abu game da haka ki kara min haske? " Wani sabon haushin sa ya kamani, wato shi bai san ma ya yi wa Hajiya laifi ba, tunda ya yi auran nan bance sun yi zaman minti talatin da shiba wanda na san hakan yana cin ran Hajiyar. Kuma babu tabbacin cewa yana zuwa kasuwar a kan lokaci. Na tabbata Hajiya tana cike da datasanin auren nan. "Ki min magana kin yi shiru. " Ya katse min tunani Nace kaje ka tambaye ta mana ba mahaifiyar ka ba ce? Dan Allah ka rabu da ni, bana son ka sa raina ya kai ga baci. Na kai karshen maganar cikin daure fuska da fusata. Yace "Wata magana zamu yi ki zo muje daki. " Nayi masa wani irin kallo, Nace a yi ta anan koma wace magana ce. Ya dan yi shiru ya zura min ido, ya ce 'Sai ina ganin kamar ba ke ba, wai munata gaddamar magana zamu yi akan kwana nawa ya kamata in ke yi muku, sai mu yi shawara. " Na yi murmushin takaici, sannan nace yau kuma za ayi shawara da ni, tun da na zo gidanan waya taba jin koda ra'ayi na akan komai ma, da Hajiya ka ke shawara hatta akan abinda ya shafe ni, sai yau ne kuma za ayi shawara da ni saboda za a kwana da ni? Menene a cikin kwanan ne, ka kwana da ni ne fa kawai. Na yi 'yar dariyar takaici, dan Allah kaje in domin kwana ne Shamaki na bar mata kai, kuje ku yi ta kwana. Zaka iya tafiya yanzu ko dai ni in bar maka kicin di? Ya kasa magana na san yana mamaki na wai kuwa ni ce nake yi masa magana haka. Ganin ba zai fita ba, sai na fice fuu na nufi dakina ko gurin da Hajiya ta ke ban kalla ba. Ko minti biyar ban yi ba, sai wayar cikin gida ta yi kara, na daga Hajiya tace inzo falonta. Nace a zuciyata yanzu zabga son kai. Suna zaune ita da shi, a nasan yanzu zata goye masa baya. Na zauna tare da fadin gani. Tace "Me ki ka fada masa game da kwana da ya zo ku yi magana a kai? " Nace ya je ya kwana can na hakura. Hajiya ta yi dan murmushi, wannan hakkin ki ne in kin sarayar musu ba zance komai ba, amma ba zai taba yiwuwa ya zauna a can gidan ba, zai zo nan duk kwana biyu ya je can kwana biyu. " Nace Ai na fada masa dama ni bansan ya ake yi ba da yace wai zamuyi shawara nace yasan da ku ake yin shawara kune kula san abinda y kamata ayi, shine ya zo gurina. Hajiya ta ce ni dai na gama magana." Nace to amma Hajiya yanzu dai ai sati daya zai yi tukunna ko,? Tunda dai budurwa ce. Suka kalli juna da Hajiya ni kuma na kauda kai ina murmushi nasan dai sunsan magana na yi nima. Hajiya ta ce "Haka ne." Nace Hajiya zan iya tafiya? Ta daga kai. Na wuce a raina nace na dai aje muku magana. Haka dai ya cika sati a gidan amarya. Ranar da zai da wo gidan Tun safe da naje gaida Hajiya tace min yau mijinki zai kwana a nan, "Me ki ke shiryawa? " Nace bana shirya komai. Tace kina ganin kuma hakan dabara ce a gurin ki? Na sunkuyar da kai, na san nufin ta in zubar da duk wani haushina in rugumi danta kar in bata masa rai. Ta katse ni. "Kar ki taya fushin kishi kin san dai namiji shi kamar yaro yake, inda ake lasa masa zuma can ya ke zuwa yawo." Nace bana fushi da shi. Tace to kamata ya yi kije yau ki yi kunshi ki gyara kanki duk da cewa na lura sosai bakya zama da rashin tsabta. " Nace to zanje. Ina zuba mata abin karin ya shigo. Na gaida shi kafin na tashi, duk da kokarin da nake yi na kar in kalle shi sai da ya yi yadda ya yi muka hada ido. Na daure fusaka sannan na mike na nufi dakina. Da gudu na karasa na kullo kofa na sai zai biyoni. Ya gaji da kwankwashen shi ya tafi. Sai da na tabbatar ya bar gidan sannan na fito da shiri tafiya unguwar su Maman Iman dama na mata waya. A gidan aka samin lallen muna ta labari. Tace min Baby wai kuwa ni kullum ina son in tambaye ki amma ina jin tsoro kar Hajiya ta san na tambayi wani abu game da cikin gidanta, kinsan bata son maganar gidanta na fita waje harmu sai iya abinda ta ke son mu sani muke iya sani. " Nace To Anty dan munyi magana tsakanin mu wa zai fada mata.? Tace "Bansani ba, amma na lura kin karbu a gurin Hajiya duk da bata da korafi da yanzu ko so daya ne munji ta yi maganar ki ko da yaya ne. In kika fahimci Hajiya zakiga saukin kanta sosai, Soyayyar Hajiya daban ce ba lallai kiyi saurin fuskanta ba,. Wanda Hajiya ta ke so yana da wahala ya gane ta na son shi lokaci guda. Son mutum daya ne bata iya boye shi ko a gaban waye, son Shamaki shike sa Hajiya ta yi ba dai dai ba, kullum cikin uzri take masa. Kunsan Allah mun sha yin tunani akan wace mace ce zata iya zama da Shamaki saboda irin yadda Hajiya ta ke matukar son shi da boye laifin shi, shi kanshi ya na son Hajiya fiye da kowa a rayuwar shi kafin ya yi aure lokacin Hajiya take gudanar da harkokin kasuwanci, shi lokacin yana dan makaranta da ya taso daga makaranta office din ta zai wuce, lokacin da aka kai shi China karatu ya dawo kusan so uku, sai da Hajiya ta aje komai ta je can ta yi wata uku tare da shi kafin ya zauna. Dan haka duk matarshi sai ta yi hakuri ta kauda kai. " Nace na lura da haka, amma ko hakan yana da alaka da rabuwar sa da matansa? Maman Iman ta ce duk da Hajiya bata bari a san dalilin ke inaga ko shi kanshi Shamaki ba zai ce miki ga cikakken dalilin sa na rabuwa da matansa ba. Hajiya ce ke sa ya sake su, amma tana da wani dalili da ita ce ta bar wa kanta sani. " Nace shiyasa kullum a fargaba na ke, in Shamaki ya sake ni Anty na shiga uku, son sa nake har bana iya boyewa a gaban kowa, kuma ga shi yana min abinda ya kamata in nuna masa jin haushina amma bana iya wa. Maman Iman ta yi dariya. Tace "Shimaki yana son ki fa, na sani in Hajiya tace ya sake ki zai iya, amma za a sha fama. Sai dai kuma kamar bana zaton Hajiya zata ce din duk da ita kadai ta san dalilin ta." Nace ina ta fadawa Allah ya zaba min abinda ya fi zama alkhari a rayuwa ta. "Kin gama magana, ni ma abinda ya sa na kawo wannan maganar saboda na ga bakya kiba sam, har yanzu kina nan firit sai dai fatar ki ta goge kin murje alamu hutu." Nace haka kowa ke cewa, Ummana har cewa ta yi wai ko zan dinga yin madarar waken suya tana saurin gina jiki. Nace mata muna cin abubuwan gina jiki sosai, kila dai ni haka nake. Amma shi fa bai damu da kibar ba, domin bai taba min maganar ba. Tace zan baki wasu kwayoyi na gargajiya ne 'yan waje za su fidda miki shef ki yi kyau. Nace ta bani. Ranar na yini munsha hira irin wadda bamu taba yi ba, na kuma sake fahimtar wasu abubuwa game da su. Sai karfe hudu na dawo ga turaruka ga kayan gyara na mata duk ta hada ni da su. Hajiya ta sa anyi girki na musamman ana kiran sallar magriba sai ga Azima ta kwankwaso tare da sallama na gyarawa Hajiya gurin salla. Na amsa Hajiya ta shiga alwala. Azima ta min wani kallo sannan ta kama kujera ta zauna. Hajiya ta fito sai naga ta bi Azima da kallo cikin mamaki . Azima ta sakko ta rusuna ta gaida Hajiya. Ta amsa, sannan tace "Me ki ka zo yi? " Azima Tace shine ya ce wai mutaho bazai iya barina ni kadai a can ba. Hajiya ta kalle ni. Da wutsiyar ido na lura Hajiya ta kalle ni, kila tana son ta ga ya na dauki abin, ni kuwa na yi kamar banji su ba, na kalli Hajiya nace, bari in shiga inyi salla. Hajiya tace "Azima kin gaida 'yar uwar taking? " Azima ta ce mun gaisa. Na yi murmushi lallai yarinyar nan makira ce ko a ina muka gaisa. Na shiga daki ina tambayar kai na me yasa zai ce ta zo nan? Tsabar ya raina min wayo, dan tsabar sone ko me? Bayan da yana gidan ta hatta Hajiya sai daya daga mata kafa, amma bari muga ikon Allah. Ban fito ba sai da nayi wanka na saka riga da siket na atamfa na daura dankwali na zubo da gashin kaina a kafada. Ina zuwa sai na samu tana zuba musu abinci. Kamar in juya amma sai na fasa, na shiga na ce sannunku. Duk suka amsa har Azima, sai na kasa zama na nufi kicin duk da cewa babu abinda zan dauka a can din. Juma tana goge goge tace "Uwar dakina wani abin ki ke so? " Nace yau bana jin cin abinci, me zan samu ne mai dan romo? Tace da akwai kayan ciki a freezer ko a dumama ne, kuma naga da kina ta zakwadin cin farar shinkafar nan" . Nace ji nayi kuma duk ta fice min a zuciyata. Ta dakko ta zuba nace ta barshi haka, tace shima dai ki ce "Dantabawa zaki yi ne kenan? , Ta matso wai kuma me yarinyar nan ta zo yi?" Nace wa fa? Tace Azima mana. " Nace ita da gidansu. Baba Juma tace "Ko gidansu ne ba an aurar da ita ba, ki bi a hankali dai yarinyar nan tana da makirci, nifa ba a banza ki ka ga ina shakkar ta ba, ta iya hada zance taje ta fadawa Hajiya abinda ba a yi ba. Hajiya ta hau kai ta zauna daram. Sai dai in anyi a gabanta. Nace Allah ya kyauta amma ni ban dauki wannan a bakin komai ba, domin ta yi min kadan a kishiya. Juma tace "Na raba ki da wannan tunanin ba karami a kishi zage damtse ki karbi mijinki dan hakin da ka raina shi ke tsole maka ido, amma fa kar ki tsorata, ki fiddo da wannan wayon naki ki yi amfani da shi a matsayin ki na uwargida ki rike kambun ki gam. Nace ina godiya Baba Juma zan kula. Na fito da kayan ciki a plate, suka bini da kallo, su duka ukun har kaman in tambaya ko lafiya? Amma sai na share na zauna a gurin da nafi zama a kan kafet. Sam ba dadin abinda nake ci nake ji ba, amma bani da yadda zanyi domin bana son su gane halin da nake ciki. Na maida kaina ga kallo TV amma inzaka yankani bansan me ake fada ba. Hankali na yana kan su, duk sun yi tsit, sai ma na ji zuciyata ta zargi ko dai yi da ni suke yi da nazo suka yi shiru sai karan cokulan abincin su, ita ma Azima sai cin nata take yi. Na gama Juma ta zo tana tattara kwanuka. Na ce Hajiya zan shafa maki magani da wuri yau domin ina son inyi bacci da wuri. Shamaki ya kalle ni, yau dai kinsan a nan nake." Na kalle shi, har yanzu haushi yake bani, nace Au gashi ban gyara maka dakin ba." Na kalli Azima nace ko zaki gyara masa? Da sauri ta ce" To" Zata mike Hajiya tace "Jimana. " Ta kalli Azima zauna mana." Azima ta kalle Shamaki. Ya ce baki ji me tace ba? " Ta zauna nikam share su na yi, dama latsawa nayi domin da sun barta taje bansan wane irin hali zan samu kaina ba. Hajiya da Shamaki suka kama lissafin kasuwanci su. Na shafawa Hajiya magani sannan nayi musu sallama. Ina shiga dakin na tsaya ina kallon ta yadda zan fara, domin tun ranar da ya bar gidan ban shiga dakin ba shi kuma yana shiga in ya zo duk ya birkita ko ina. Na gama kwashe kayan wanki na gyara durowa, sannan na koma gado na canza zanin na kunna borna ta turaren wuta. Na fito falo da nufin in tafi daki na, turus na yi ganin su zaune shi da ita a falon.... ..... Wani takaici ya zomin iya wuya, narasa me ya kamata in yi. Na tako ta gabansu zan wuce, yace "Baby zo." Yi nayi kamar banji me yake fadi ba, na wuce har na kai bakin kofa ya taso da sauri, wai ina magana kina jina Baby? " Na kalle shi, nace me zanyi kuma bayan na gama gyara muku gadon.? Yace "Kina da matsala ni ba maganar gyaran gado bace, zanyi magana da ku ne ke da ita, ya kama hannuna muje ki zauna." Ma bishi fuska daure cikan fushi da tsananin kishi. Ya zauna a mazaunin shi da ya taso, ya zaunar da ni kusa da shi,. ta dube ni, ta taba baki. Sai na gyara zama a kusa da shi din, ita dama ta zauna ne akan Kujerar da ta ke daf da tashi. Ya kalle "Dan jawabi zanyi muku ba mai yawa ba, Ya kalli Azima yace "Azima da ke zan fara magana, ina son ki sa hankalin ki ki kuma san wacece Baby a gurin ki bana son fitina ki rike ta kamar yayarki., ina nufin ki yi mata biyayya. Ya dube ni, ke kuma hakuri zan baki, ina mai kuma baki hakuri a karo na ba adadi. Nasan cewa ba sai na fada miki cewa ki zaune lafiya da ita ba domin nasan zakiyi haka, Allah ya hada kanku a zauna lafiya. " Duk da ina jin haushin sa naji dadin jawabin na shi sosai. Har na rage jin haushin sa. Ya sake kallonta "Ki tashi kije ki kwanta kuma in har ki ka sake na ganki online cikin dare ranki zai baci." Ta mike ta nufi hanyar Bedroom, yace "Ina za kije? Kina da gurin kwana anan ne? " Tace Ina zanje to? Yace dakin ki na da mana. " Ta zaro ido ka san haka ne ya baka barni na kwana a gidana ba ka ce sai na biyo ka! Yace "Dan iska ne ni da zan barki ke daya a gidan kimin jaye jaye." Na zaro ido don mamaki ina kallon shi na kalle ta ta turo baki ta fice. Na kalle shi, kasan ma a'nar abinda ka fada kuwa? Yace na sani mana inhar kin fahimta to nufiana ke nan." Nace Kana zarginta fa kenan.Kuma in har haka ne to ka tafka kuskure, domin an hana zargi a cikin aure. Yace "Ai ba wai maganar zargi bane, zata iya janyo min wani kato gida. " Nace Ta taba kawo wani ne a tsawon kwanakin nan bakwai da ku ka yi? Yace bata kawo kowa ba amma bazan samu kwanciyar hankali ba zan fadawa Hajiya cewa ta bamu Tabawa ko Juma domin a saka mata ido, kin san Allah bana iya fita da wuri, in na fita din ma Allah-Allah nake in koma, sai ina ji a zuciya ta kamar zan samu wani a gidan tunda ita dai ballagaza ce." Yanzu na sake fahimtar cewaLallai kuskure ne babba ki yarda namiji ya rike koda hannun ki kafin aure domin zai tafi yana zargin ki cewa kowa ya zo zaki iya ba shi hannunki ya rike.Ya katse min tunani da fadin. "Menene ki ka yi shiru abinda na fada har zuciyata na fada miki. " Nace Amma dai Babban bako tsakani da Allah kai ka yaudareta kuka yi ta sharafin ku kai da ita, yanzu kuma sai ka ke zarginta? Yace ta yaya bazan zarge ta ba, kaddara ni nazo nace mata ina son muna fita sai kawai ta yarda mu fita? Ta yaya zuciya ta zata nutsu dan na aureta, da aurena sai wani ya ganta ya taya ta sallama mishi. In kece zaki bini Ko fuskar da zan taba yatsanki ban gani ba lokacin da nake zuwa gurin ki. " Nace to ai ita yarinya ce karama kuma banda haka tana sonka zata so ta faranta maka rai. Yace "To kema ai kina sona sai dai ki kirani ka tambaya ta da gaske zaka aure ni? Ina jin kamar zan mutu in ka fasa aure na." Ya yi maganar cikin kwaikwayon muryata da tsokana. Na dan kai masa dukan wasa ma ina fadin its dai yaudararta kayi. Yace "Ke Lauyar ta ce shike nan amma dai har abada bazan iya bata amana ba tunda taci amanar kanta ma." Nace itama ai haka taza kalleka a yadda ka ke kallon ta. Ya kamani ya mike tsaye don Allah ki bar maganar ta muje ki biya basukan da ke kanki kema din. Abin mamaki Shamaki kamar wanda ya dawo daga tafiya, sai kace ba daga gidan amarya ya dawo ba. Da safe kamar yadda muka saba haka komai ya tafi normal. Na kuma gane Azima bata da wata martaba a gurin shi dan haka sai na sauke duk wani fushina na rungume mijina. Haka kuma wannan mummunar dabi a ta bibiyar wayar sa na nake yi ban fasa ba, haka kuma ban daina ganin takaici ba, domin har yanzu da neman matan sa. Zuwa yanzu kuma na gama koyon duk nau'in na girkin da Hajiya ta ke so. Na kuma karbe girkinata a hannun Juma, har nama na fahimci tafi jin dadin nawa, tunda ga su Juma za ta kirani tace in sada mata abu kaza. Yaran gidan nayi nasarar janyo su zuwa jikina, ta hanyar yin ruwa da tsaki ga bukatun su tare da jure amsar korafinsu da kuma yin sulhu tsakanin su, har ya zama in sun kai wa Hajiya kara zata ce ku tafin gurin Mommy ku. Haka nan su Juma sun na janye su ta hanyar nuna musu cewa duk daya muke da su, da kuma girmama su.Duk ranar da Shamaki ba ya gidan Azima to fa a dakinta na da zata kwana. Tun ina dariya kunsan halin kishi har na zo ina jin tausayin ta. Domin gaba daya Shamaki baya ganin kima ko darajar 'Azima. Wata ranar lahadi na shigo falon Hajiya dan zuwa kicin muyi aikin abincin rana, sai na sha mamaki ganin Shamaki turus a gaban Hajiya ga Maman Umar zaune. Na gaida Maman Umar sannan nan na kalli Shamaki ransa a bace yake, Nace sannu da zuwa. Hannu kawai ya daga min. Hajiya kuma bata daina maganar da ta ke yi ba wai dan ganina. Na tsinci tana fadin " Na gama magana ya rage naka gidanka ne kuma matar ka ce duk abinda ka ga dama kuma zaka iya yi amma ni a nan na tsaya. " Na nufi kicin cikin faduwar gaba ko a kaina akeyin maganar na fara lissafi yanzu dai watana shidda a gidan Hajiya bare ince ko wa a dina ne ya iso a mugun yanayi, wato banci nasara ba. Juma wadda na samu suna kuskus da Tabawa ta kalle ni, tace "Yawwa Uwar dakina, dama dai ina ta fatan ki fito domin kiji wani mugun labari, ni dai ina ganin lokacin barin aikina a gidan nan ya zo. na zaro ido cikin fargaba. Me zai sa ki bar inda ki ke samun abinci Baba Juma? Tace wai gidan yarinyar nan za a maida ni wannan marakunyar Azima. Ni kuma da in koma gurinta gara in hakura da aikin kawai gaba daya. " Nace A a Baba Juma, ki fara zuwa ki ga kamun ludayin zaman Idan kinga ba dama to sai ki zo ki fadawa Hajiya . Tace "To kin kawo shawara kema, zan gwada in gani, amma dai na san wajibi ne ta bata min rai Indai wannan yarinyar ce." Nace Ki kwada haka. Juma ta ce wai wani abu ta ke yi wai shi ko tintam irin na wayar nan ana rawa gashinan malamai suna ta wa''azin abin ba kyau ashe yarinyar nan tana yi. Tun a gidan nan. Hajiya bata sani ba. " Nace Tiktok ki ke nufi? Juma ta ce "Yawwa shifa." Na saki baki wai ina kallon Juma. Hajiya dai ta samu kalubale a gidanta. Ya yi da take ganin wasu ba su iya tarbiyya ba sai gashi A gidanta karkashin tarbiyyar ta Allah ya jarabce ta. Juma tace wai Maman Umarce ta gani a wayar ta, shine ta zo ta sanar da Hajiya shine mitin din gaggawa ya tashi, aka kira Shamaki yana kasuwa. Nace Allah ya kyau ta. Ranar a gurina ya ke dan haka Juma ta hada kayanta ta koma gidan, Shamaki ya je ya amshe wayar Azima ya taho da ita. Ni dai naga waya a kan durowar sa ban yi magana ba. Da kanshi yace "Kinsan wannan wayar? Nace bansan ta ba. Yace "Ta Azima ce. " Nace wata ka canza mata ke nan Allah ya sanya alkhari. Yace,, " In canza mata waya saboda itace wa,? Kinsan yarinyar nan wai Tiktok ta ke yi a she?" Nace Haba dai! Kai to kana ina? Yace "Humm na sha mamaki ta jima tana rawa da waka, a Tiktok ba mu sani ba tunda ba mai lokacin kallon shi s ciknmu, na dai sata dai ta goge, sannan na rufe account din, shine kuma na amshe wayar. An tura mata Juma. Nace Aiiah ya basu zaman lafiya amma da ka barta da wayar ta. Nikam ina kewar Juma aiki zai mana yawa yanzu. Yace "Na san in Hajiya ta lura dole zata samar da mafita. Nace Allah ya sa angane da wuri sai a hanata. Yace "Wannan yarinyar ce zata hanu, nifa in fada miki yarinyar nan tsoro take bani, tunda akayi auren nan kullum cikin nadama nake. " Nace duk kai ka ja wa kanka da baka tabata ba, na tabbatar Hajiya baza tace sai ka aure ta ba in har baka sonta. Ya shafa kai, Baby ke dai ki bar sharrin shedan, kinsan Allah ni bazance miki ga yadda aka yi ba amma ita takawo kanta har dakina. " Nace Sauran fa? " Yace "Su wa? " Nace kana nufin akanta ka fara Newman mata kuma daga ita baka neman wata? Ya dan daburce, sannan yace ni bana neman kowa." Nace Kaima yanzu kana son yin karya wanda kuma kasan ba al'adar gidannan bace. Ya ce "To Yanzu da ki ka tsara ni me ki ke son in fada miki ne Baby? "Nace Abinda ke birge ka a jikin matan wanda ni bani da shi. Kasan me ke bani mamaki da kai, in na kalle ka sai inga wai ta yaya ka ke gane mace "yar iska kuma har ka tinkare ta gabanka gadi ki yi magana ku yi ciniki sannan ka dauke ta kuje ku kebe, bakasan ta ba, baka san ko tana dauke da wani ciwo ba, yadda tsaftar jikinta ma take duk baka da tabbaci. Kunya tasa ya kasa kallo na kuma ya kasa magana. Nace to wai Tun tsawo wane lokacin ka fara irin wannan karfin halin? Cikin tsawa ya ce, "Ke! Har sai da na firgita, yace kina da hankali kuwa? Kin dame ni fa, an fada miki mu ne mike zuwa mucewa mata muna son su? Ni nan da kika ganni mace ce tafara lalata ni, ita ce ta kawo min kanta har na san amfanin mace a gurin da namiji. Zuwa yanzu zan iya kirge miki matan da ni na taba cewa ina son su da kaina. Dan haka ki daina yimin tambayar da bata shafe ki ba. Nace Allah ya baka hakuri, amma zan baka shawara ka bi a sannu, sannan in har da gaske kana daukar Maman Anisa to ka bawa Hajiya hakuri ku maido auren ku. Na fadi haka ne don in latsa inji gaske ne. Sai naga ya zura min ido, "Ina ki ke jin maganganu haka? " Nace Kana mamaki ko? Ka daina mamaki domin cikin mafarki na ina iyaganin duk wani abu da ake boye min. Na daure fuska tamkar gaske. Ya zura min ido kila yana mamaki ko Kuma bai kama ba. Amma dan abar maganar sai yace "Zan fadawa Hajiya gobe a kai ki a yimiki International passport ban sani ba ko Hajiya zata ce a tafi da ke aikin hajji. Na lura baya son maganar nima sai na barta, nace Allah ya sa ina da rabon zuwa amma Hajiya bata ayyana ni a cikin 'yan wannan shekarar ba. Wani abin mamaki washegari sai Hajiya ke ce min Shamaki ya bada kujeru goma kamar yadda ya saba a rabawa dangi ina son ki duba ki lissafo min mutum takwas ni da Shamaki mu ne cikon goman." Nace Hajiya don Allah ki taimaka domin ni ba kowa na sani a cikn dangin ku ba. Tace "Mijinki ya bada su, dan haka duk yadda ki ka yi ba mai cewa don me kuma ke ma ai kina da dangi ga iyaye. Nace Hajiya in muna raye kuma ina gidan nan shekara me zuwa lokacin na kara sanin abubuwa sai in yi wannan aikin amma yanzu ki yafe min ba jayayya zanyi da ke ba. Na fada cikin zanyi jiki da sanyin murya. Hajiya tace "Shike nan, ashe Maman Mubina ta fiki kokari tunda har ta iya rabawa tsaf a dangi ta, kuma sukaje lafiya suka dawo lafiya. " Nace Ba damuwa wata shekarar sai in yi idan Allah ya sa hakan za a yi. Haka dai suka shirya tafiya aikin Hajji ciki harda Azima. Ban damu ba domin Hajiya ta ce a tafi da Azima na ayyana cewa domin hankalin dan ta ya kwanta ne cewa tana kusa da su, bazata janyo masa wani ba kamar yadda ya ke fada. Shi da Hajiya kuwa dama duk shekara bata wuce su. Kafin tafiyar su nan ma aka sake wata diramar, an kawo ragunan layya, Hajiya ta ta sani wai in raba raguna, har sai da na kusa kuka ina fada mata bazan iya ba, musamman da na tambaye ta ko wadan da aka baiwa sadakar Azumi za a baiwa tace "A a. Daga baya sai ta ce in zabi na gidan mu. " Nace su kowanne aka ba su, tace lallai saina zaba. Ban ko kalli layin manyan ba na nuna wani dan tsaka tsaki nace to akai musu wannan. Budar bakinta sai cewa ta yi. "Au ke bazaki zaba ki darje ki zabi narkeke ba irin yadda Maman Meema ta yi ko ki dauki biyu kamar yadda maman Anisa ta yi kuma duk sunci lafiya, iyayen ki nefa?" Na yi Dan murmushi na kara yadda duk wani motsi mai karfi na gidan Hajiya jarabawa ce. Nace Wannan din ma Allah ya amfana. Ranar da zasu tafi karfe biyun rana ce zasu wuce, dan bai fita kasuwa ba. Muna kwance a dakinsa ya hanani sakat ina masa mitar me yasa yake yawan damuna. Yace "Baby kullum addu a ta in ganki da ciki ina tsoro kar ki shekara ba ciki Hajiya ta ce kun fadi jarabawa. " Nace dama a cikin gwajin nata harda ciki? Yace "Bansani ba, amma dai ni na zaci haka. Nace duk da bansani ba, amma bana zaton Hajiya zata shiga hurumin Allah domin shine yake da ikon bayarwa kuma bai Bayard ba. Yace "Haka ne, ga shi Azima tana da ciki, Hajiya ta so a barta nace ta yi hakuri mu tasa ta kar ta kama yawonta kafin mudawo. A nan na gane dalilin tafiya da Azima kamar dai yadda na zarge. Wanda da farko har na zarge su da son zuciyar su a farko. Yace zan roko miki Allah ya baki ciki da zarar mundawo." Nace masu albarka zaka rokofa amma, yace "Insha Allahu masu albarka za a samu, na shawo Zam Zam da Laban na ciyo dabinon mai daraja na yo addu'o'i ke kinsan zamu samu 'Dan albarka ko? Nace haka ne. To haka dai suka tafi aka barmin gida amma Juma nan ta dawo saboda aiki harma sai da ta karo mana wasu matan. Na bigi cikin Juma dan in samu labari. Nace Juma tunda naji ki shiru na san cewa ana zaune lafiya dama shiyasa nace kije dai a gani. Tace "Injiwa ya fada miki so biyu dai ina hada kaya Zan tafi sai tazo tana bani hakuri domin tasan in na tafi zataci gidansu gu Hajiya da shi uban dakina. shine ya sa take dan shakka ta, dan duk radda ya kaini karkiga yadda ya ja mata kunne a gabana, har sai da ta bani tausai." Nace To ai haka yafi, kuma tunda tana sanshi ya na santa ai baza kiji suna husuma ba, tunda shi tashin hankali ko ba da kai ake yi ba kinsan bashi da dadi. Na fada tare da baza kunne inji me zata ce. Tace "To wani lokacin su yi tsiya wani lokacin kuma su yi dadi, amma fa akwai radda ya yi mata dukan tsiya,. Na zaro ido tare da maimaita fadin duka! Juma tace Nima dai nayi mamaki, domin ban taba gani ya daki mace ba duk matansa na baya." Nace kuma ke baki je ceto ba? Tace Ai bari nai sai da ya lallasa ta sannan naje ceto, ina fadin wannan ba dabi'ar ka bace uban dakina. Yafice yana fadin ki sake min bincike a waya. Ita kuma zan je in bata hakuri sai ta huce a kaina wai infice bata son gulma. Shine nace, a a kinga "yarnan bani ce na kar zomon ba kuma ratayar ma ni ba a bani ba. Na tafi ina dariya. Nace duka dai Juma Shamaki ne da dukan mace? Tace "Af sai dai kar a kuma. Waya fa ta bincike masa, kin taba ganin mace mai binciken wayar miji ta zauna lafiya? A zuciyata Nace Ai ko bai dake ta ba da ya barta iya ciwon zuciyar abinda zata gani ya ishe ta. A fili nace ummm ai shike nan amma dai magana ta gaskiya wannan bai kai abin duka ba shima. Juma tace Ni kuwa har Allah ya kara nayi mata saboda rainin da ta yi min. " Haka dai akayi salla ta wuce mahajjata suka shiga dawowa. Ni a sallar banje gida ba, amma su Jamila da wasu 'yan unguwarmu sun zo. Ranar da zasu dawo munsha aiki, ni sai lokacin na yi gayun sallana, wato kitso da kunshi, sannan nayi dinki. Na yi kyau cikin leshi. Shamaki bai ji nauyin Hajiya da Azima ba ya rungume ni. Yace "Na yi kewar ki Baby. " Nima nace na yi kewar ka Babban bako. Sannan na rungume Hajiya. Sunci sun sha sannan aka kama hirarraki. Azima tace Juma ta zo su tafi Juma tace sai dare zata zo. Hajiya ta ce min "Mijinki ya shiga ciki amma kina nan. Nace yau ai gidan Azima zai tafi domin ranar da zaku tafi ai yana nan. Hajiya tace "To ai da Azimar aka tafi suna tare ai. Na tashi na shiga dakin yana kwance kan gado yana chatin motsin taba kofata da sallamar tawa sai suka dan tsorata shi alamun rashin gaskiya suka bayyana a fuskarshi. Ya aje wayar ya tashi zaune, Baby me yasa ki ka ki zuwa kinsan abinda ya shigo da ni. Nace ce ni tsoro ya hani zuwa na yi mafarki na dauki wayar ka ina bincike sai ka kamani shine kamin duka. Ya zaro ido, "Ai bazaki taba daukar min waya bama bare ta kaimu ga haka. " Na ce Kenan zaka iya dukana in abin ace an daukar maka wayar? Yace Baby waya sirrin mai ita ce, kar ki fara bin al aurar wani, ko Allah baya son kana bin diddigin neman sanin sirrin wani bawansa da ke boye wanda shi bai bayyana ba." Nace haka ne. Ya kama hannu na, Baby ina son ki, ina son mu haihu da ke Baby, na yi ta rokon Allah ya baki ciki duk shekara." Na kwace hannuna ya zaka min wannan addu'ar in Allah ya amsa fa? Yace haka nake fata sai inyi murna, ya amsa addu'a ta." Nace ni kuma in tashan wahalar goyo da ciki? Yace zan taya ki, kuma ga su Mubina za su taya mu. Sai mu karo masu raino mu hada da Rahin. " Na kai mishi dukan wasa tare da fadin dubu nawa zan haifa ne har da lissafin 'yan raino babu adadi? Yace zo in baki amsa. Ranar sai da Shamaki ya shafe min duk wani kokwanto da ke zuciya ta, ta sake amincewa da shi, harma na yarda cewa ni daya ce a zuciyar sa. Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya, na dan ja baya da duba masa waya sai jifa jifa. Abinda na lura shine bazan iya raba Shamaki da neman mata ba. Kuma tunda yana boye min in tafi a haka. Dan haka na duka fadawa Allah. Kwanci tashi har shekara ta gabato, saura sati uku in cika shekara, na zama cikin tunani da yawan addu'a Allah ya zaba min abinda yafi alkhari, sannan na sanar da Umma dan ta tayani da addu'a kuma dan kar suga na dawo gida kwatsam. Shi kanshi Shamaki ya fahimci cewa ina cikin damuwa 'yar kibar da na fara duk na jeme, hakan ya jefa shi cikin damuwa wanda har sai da ya tsarani don jin ba a si. Na fada masa. Yace "Baby Allah ya jarabce ni da son ki, na tabbata in har na kuskura na sake ki Hajiya ce zatafi kowa yin da ta sani, wanda hakan shine zai kawo taje da kanta ta nemo ki. Ya numfasa sannan yace ina son kimin alkwari, ko da Hajiya ta sa na sake ki, karki kula kowa na san zata kawo kanta in taga zan mutu." Na girgiza kai tare da fadin Aiko sai dai ka mutu, domin ni bazan taba dawo makaba matsawar ka sake ni, sai dai in sonka ya zama ajalina. Na daga yatsana dan manuni, na ce na rantse da girman Ubangijin daya busa min numfashi in har ka sake ni har.... Sai sai naji ya toshe min baki, yana fadin "Bazan sake ki ba Babyna. Karki rantse, ni mijinki ne na har abada, zan san ya zanyi in fahimtar da Hajiya cewa ke din mace ce mai wahalar samu. " Haka dai muka yita gardama, wannan lamarin ya hana Shamaki sakat shima ya rage bacci ya shiga addu'a Allah ya sa Hajiya ta hakura. Cikin kwankin Hajiya ta zama cikin yawan damuwa tare da ganawa da lauyoyin su har na fara tunani duk cikin aikin hada sakamako na ne. Azima ciki yana ta girma har ya fito, amma daga Hajiya har Shamaki banga suna wani marari akan cikin ba. Mubina ta wayi gari tana irin wannan suman wanda yara ke ayi a yananyin karshen damina. Aka kwatar ta a Asibiti ni ce a gurinta. Randa muka kwana biyu tana kwance ta tada kai da cinyata tana cin ayaba. Sai ga wata mata ta turo kofa ta shigo da sallama. Na amsa tare da yi mata sannu da zuwa, na nuna mata kujera, ta zauna muka gaisa. Tace baki sanni ba ko? " Kafin in amsa sai naji Mubina ta dago da sauri tace, Anty. Matar ta janyo kujerar ta matso gaban gadon tace Mubina ya jiki? " Take na gane mahaifiyar ta ce, Na daga ta na zaunar suna kallon juna. Ta kamata ta rungume tsam sai hawaye a idon Uwar, nace Allah sarki, ki yi hakuri ai jikin nata da sauki. Tace 'Yar uwa ya mai jikin nace da sauki. Tace kece matar Shamaki? " nace e. Tace "Kin shekara a gidan Shamaki? " Nace A a, saura kwanaki. Tace "Kin haihu? " Nace ban haihu ba. Tace ki godewa Allah domin da kin haihu sai kin fi fuskantar tashin hankali da damuwa. Mutuwa ita kadai ke iya raba da da mahaifi sai kuwa gidan Alhaji Baita. Da ana kawo su hutu yanzu kuma an daina gaba daya. Jiya na yi wani mugun mafarki game da Mubina. Na kira Shamaki da farko bai fada min ba, sai na soma kuka ina fada masa cewar ina son ganin yarinyata, nayi wani mafarki a game da ita, in har na rasata zan bi ba a sin haka. Shine ya fada min wai kuna nan bata da lafiya. " Nace sai hakuri, domin bawa baya tserewa kaddarar sa. Ni kam tuni na yi imani cewa zan bar gidan na saka raina cewa ta ina cika shekara. Tace "Haka zai zo miki da dan sauki, ni dama ba wata soyayya muka yi da shi ba, amma ya iya kalamai ga iya wanka, sannan mutum yana ganin daula, kinsan dole ya rikice rana daya a diro a ce ka fice. " Nace Dama ba wata tambaya da aka ce Hajiya na yi duk karya ce? Tace zata tambaye ki game da wasu abubuwa musamman na rabon zakka da kujerun hajji, kamar ni dama da tace in raba uwa da ubana sune farko sai kannasu, san nan na sirka danginta biyu. To ko banza dai sun meta hazo. Sai kuma ta tambaye ki waye Shamaki. Ni cemata nayi danta ne mana. Saine tace in fice mata. Amma rabani da 'yarnan yafi komai ciwo a gurina. Nace dole zata nemeki bare "ya mace in ta samu gidan mijinta lokacin da zata ke zuwa ina za su sani. Tace "Amma kafin hakan ai an wahala da sauran lokaci. Nace kiyi ta mata addu'a muma ko bana gidan zan kasance mai musu addu'a domin ina so su yarannan dukansu. Tace Na gode ke ma Allah ta baki ko ba a nan ba, ya kula mana da su baki daya. " Nace Ameen muna ta hira tana bani wasu 'yan bayanai, kuma na yi mata alkawarin zan binciko dalilin da yasa aka daina daina kai yaran hutu. Da kyar ta iya tafiya sai da wanda ya kawota ya shigo ya lallasheta. Haka ta barmu cikin jimami. ..... *HAMSHAƘIYAR UWA🧕🏻* *NA* *HALIMA ABDULLAHI K/ MASHI* *💃🏻💃🏻💃🏻Masoya masu jiran littafin HAMSHAKIYAR UWA Complete Document,a yanzun haka ya kammala akwai document din HAMSHAKIYAR UWA Complete game bukata zai iya tura kudi kai tsaye ta wannan account number ₦600👇🏻* *0700549935 Halima Abdullahi Access Bank a turo shaidar biya ta wannan number 08140004302 ko katin Mtn* *Phone 08140004302* Shamaki ya shigo dakin Asibitin da dare, ya same mu muna hira da Mubina tana bani labarin Antynta yace wacece Antinta. " Nace wai Maman ta, yace to mu hada kaya mutafi an sallame mu". Nace to. Mubina ashe tana rike da maganar sai cewa ta yi, Mommy ba kince zaki tunawa Daddy a kaini gidan Anty ba. " Shamaki yace "Wacece kuma Anty? Nace Mamanta, mana meyasa yanzu aka daina kai su hutu ne? Yace "Uwar Meema ta ja musu, tana fadawa yarinyar abubuwan da basu kamata ba, kuma tana yi mata tambayoyi yarinyar ta zo tana min tambaya a gaban Hajiya Wai Maman ta tace Hajiya tana yi musu wasa ko sai fada. Sannan wai in an basu kudi tana boyewa in za a kawo ta sai ta saka a kayanta ta kaiwa maman. Shine Hajiya tace baza a kara kai su ba." Nace gaskiya bata kyauta ba gashi ta sa an shiga hakkin saura, domin su baruwan su, amma ba zai yiwu a kai su sukadai ba. Dakatarwar dai shine abinda ya dace a yanzu ha na har abada ba. . Muka isa gida Hajiya tana kwance a gurin da take salla, ban taba ganin ta kwanta a gurin ba, na isa na zauna kusa da its nace Hajiya lafiya kuwa naga kin kwanta. Ta tashi zaune fuskar ta ta fada. Nace bakya jin dadi ko? Tace bana jin dadi amma da sauki. Shamaki ya iso shima ya tsugunna, yace Hajiya tun jiya nace baki da lafiya kin ce a a. Ta yi dan murmushi zazzabi ne kuma na samu sauki, karfine kawai bani da shi. Muka yi mata sannu, ya zauna ni kuma na shiga ciki dan in watsa ruwa. Satin da Zan cika shekara Shamaki ya sanar da ni cewa zai tafi China daga can zashi Dubai. Kuma gaba daya tafiyar sati biyu zai yi. Nace to in ka tafi gashi saura kwana shida in cika shekara to kuma in banci jarabawa ba, yaya za ayi baka nan? Yace "Yadda za ayi ke nan ta yi hakuri domin haka na kirkiri wannan tafiyar sai dai na yi mamaki da ya kasance bata hana ni ba, kila hakan yana nufin cewa bazata raba mu ba. " Nace kar ka saki jiki akan haka kuma sai ka tafi tace ka turo sakin ta waya. Yace "Wai ke baza ki taba fadi alkhari ba saboda Allah?" Nace to ai bana son in yaudari kai na ne, saboda ko zan tafi dai dama na dangana. Ya rungume ni insha Allahu muna tare har abada, sai naji dumin hawaye a kafatata. Nace dago dasauri, kuka kuma Shamaki? Na fada cikin mamaki. Yace Tunda shekara ta gabato sai ina samun kaina cikin yawan kuka da damuwa, wanda nasan cewa tsoron rabuwa da ke ne. Na sa hannu a fuskar shi ina shafo hawayen nima sai naji nawa sun soma sauka. Ya tafi ya barni cikin jimami. Ranar da ya tafi da dare wayar cikin gida ta bugs misalin Karfe biyu na tashi na fita. Nasan cewa munyi sallama da Hajiya na kuma shafa mata man zafi. Na fito ba kowa a falon Hajiya na nufi dakinta, Tana zaune a tsakiyar gado, na shiga da sauri ina fadin Hajiya lafiya? Tace lafiya kalau zauna. " Na zauna jikina sai kyarma ya ke yi. duk na firgita. Ta kalle ni sosai tace "Me ya ke baki tsoro? " Nace Ba komai na yi tsammanin baki da lafiya ne. Tace lafiya ta kalau kwantar da hankali. Ta kara matsowa, kin kuwa san dalilin da yasa na bar mijinki ya yi tafiya? " Gabana ya yanke ya yi wata muguwar faduwa, nace a a. Tace "Saboda in har yana nan bazai taba barina in yi hukuncin da ya dace ba, saboda son da ku ke yi wa juna wanda ni kadai na san dalilin son. Ina fata kina aje da lissafin kayan azumi wanda ki ka raba, shine zaki gabatar min da lissafin." Na tashi cikin fargaba naje na dakko takardar na dawo. Nace gata nan. Tace to kowanne zaki fada min dalilin da yasa ki ka bashi abinda ki ka bashi. " Na kalle ta cikin rashin fahimta, naji zuciya ta ta fara zuwa wuya, tana fadin wai gidan nan na Aljanna ne da nake ta fuskantar damuwa da wasu ka idoji? Wata zuciyar ta bani amsa da cewa ba gidan Aljanna bane amma na neman Aljanna ne. Dan haka sai lallashi zuciyata sannan nace ban gane abinda ku ke nufi ba Hajiya. Tace misali ai kin ba kanina kayan abinci da kudi ko?" Nace E, Tace to fada min dalilin da yasa ki ka bashi. " Nace To gaskiyar magana ni dai na yi la'akari da kusanci, domin musulunci ya nuna mana muhimmanci fara taimako daga kusa kafin kaje nesa. Tace "su Juma fa? " Nace ai na fada muku kwanaki, suma kusancin ne sannan suna yi mana hidima duk da muna biyansu kyautatawa yana da dadi. Sannan taimako ne. Na numfasa, don Allah Hajiya kar ku tambaye ni dalilin da yasa na baiwa sauran domin ban san su ba. Tace 'To ya akayi kika basu? " Nace nabi layin sunayen ne har zuwa adadin kudin daga nan na fara da wadan da ba kudi, su kuma daya zan iya fada miki wani abu akan su ba, saboda suma layin na bi, sai guda daya wadda itama ta fada min ne da kanta. Tace "Wa kenan? Nace Wata tsohuwa makauniya. Ta zuba min ido da alamun mamaki a tare da ita, a hankali ta ce "Kinje Fage kenan? " Gabana ya yanke ya fadi, ba shakka bazan yi wata karya ba, ko da banci jarabawa ba na san dai bazan zargi kai na da kar ya ba. Nace naje Fage Hajiya gurin tsohuwar nan. Hajiya ta yi shiru tana kallon gefe daya, kamar tana tunanin wani abu. Can ta numfasa sannan tace, "Ban tsammaci cewa kema irin wannan hanyar zaki bi ba, amma dai zan yanke hukunci ne kawai daga abinda kika fada. Ta sakko daga kan gadon ta yi dan tattaki a hankali, ta kai kan wata kujera dake manne a jikin gadon ta zauna, sannan ta ce. "Jikina ya yi sanyi domin na gama yanke shawara cewa ke ce matar gidan nan, amma sai gashi kuma kin kama hanyar neman jin sirrin da da kin yi hakuri da na fada miki shi daga bakina kuma sahihin labari. Amma zan yi miki uzrin na sauraronki sannan in auna, zan kuma baki makin ki cikin adalci. Kafin inji abinda ya kai ki gidan tsohuwa da kuma abinda ki ka jiyo da sauran abubuwan da suka biyo baya ina son ki taya ni kallon wannan. " Ta kunna TV da Remote din hannun ta. Cikin sauri na maida kai na ga kallon TV. Ba kamar fimba da za a nuna can da can ko sunaye, Hotona ne ya bayyana. Gani lokacin da ake shigo da ni, babu magana hoton ne kawai, ga lokacin da za a kaini daki na, sai kuma ga ni ina neman dakin Shamaki, Sai kuma aga Juma ta nufi dakina da kayan abinci. Sai kuma lafon Shamaki, duk ga shinan lokatan da muka zauna ko muka ci abinci ko wasu dai 'yan wasanni ba masu yawa ba. Haka kuma ga lokacin da Azima ta shigo falon kuma ga lokacin da ta shiga dakin Shamaki. Zuciya ta dauki zafin takaici kamar a lokacin abin yake faruwa. Har na tambayi kai na ina ina a wannan lokacini. Sannan ga lokacin data fito. Haka dai muka yi ta kallo, akwai gurare da na yi ta fargabar kar a gani gurin duba wayar Shamaki amma sai da wani guri daya ya fito da na dauka a falon. Sai anan Hajiya ta yi magana idanunta suna kan TV din, tace 'Wannan ba wayar Shamaki bace? " Nima ba tare da na dauke kai ba, nace ita ce. Me kika yi a ciki? Nace duba masa sakwanni na yi. Sai lokacin ta waigo ta kalleni, kina zarginsa ne a lokacin? " Nace kwarai kuwa. Tace me yasa ki ke zargin sa? " Nace akwai wani guri da aka wuce, inda zan shiga dakin na dawo baya har nayi karo da fulawa ya zo yana kirana ban dawo ba, shine dalilin da yasa na binciki wayar sa. Ta tsada TV din, Me ya faru a lokacin? " Nace samu yana waya da wata mace wadda ta turo masa hotuna na sassan jikinta, yana yabawa da hotunan, yana fadin wasu kalamai da suke nuna jin dadin kasancewar su da ita. Na juyo da sauri domin bana son ya ganni bare yaji kunya tunda ya san na yarda da shi kuma in wani ya fada min cewa Mijina yana neman mata bazan yarda ba. Kuma sai Allah ya kaddara na ji da kunne na. Garin in gudu karya ganni sai fulawa ta fado shine ya biyoni. Hajiya ta sauke ajiyar zuciya. Tace "sai me ya faru daga nan? " Nace kawai naje nayi kuka ne a daki ban fada masa abinda ya faru ba har zuwa yau? "Me yasa baki fada masa ba? "Hajiya ta katse ni da tambaya. Kila ya musa, domin ban kamashi ido da ido ba, ko ya fusata ya dauki matakin da bai dace ba a cikin borin kunya. Na san cewa ta hanyar tattaunawa ne kadai ake iya warfare matsala. Shine na fara bincikar wayar sa domin in samu tabbbain abinda naji. Anan na gano yadda suka shirya da wata yarinya zasu hadu a wani Hotal a ranar wata lahadi. Hajiya tace "To na fahimci cewa lahadin da ki ka yi karyar ciwo ce domin kar ya fita." Na jima ina tunanin dalilin wannan karyar. Na. Ce yawwa haka ne, sai kuma ciwon duba wayar ya kamani wanda kullum na duba sai na ci karo da sabon bakin ciki wanda sai dai in shiga daki insha kuka na. Hajiya ta dube ni, ta girgiza kai, sannan tace "Wane matakin ki ka dau ka". Nace fatan shiriya nake ta yi masa a gurin Allah, kuma dai har zuwa lokacin da ya yi wa Azima ciki ina cike da tashin hankali game da zaman mu. Zubur Hajiya ta mike tsaye, ta tsura min ido, "Da wane lokacin ya yi wa Azima ciki.? "A raina nace kaji wani raining wayo. Sai nace. Ban san da wane lokaci bane amma doke zai zama a cikin lokutan da take zuwa dakin shi ne ko suke fita, bana zaton cewa ko su zasu iya sanin lokacin. Hajiya tace "Ke nan kinsan tana zuwa to kina matar shi ke kina ina? Nace Hajiya bansan tsawon lokacin da suka dauka suna yin abin su ba. Kilama kafin in zo ne, haka kuma ai suna fita Hotel kamar dai yadda ki ka datse yin hakan ta hanyar daura musu auren gaggawa. Hajiya ta zauna a bakin gado, sannan ta kure ni da kallo. "Wane kokari ki ke yi zuwa yanzu domin ganin ya bar duk wadannan dabi u.? " Na ce zuwa yanzu ya san na san komai, ban yi rigima da shi akan haka ba, kuma na fahimci Allah ne kawai zai rabashi da haka, saboda haka shi nake fadawa, ina saran zai shirya shi lokaci daya. Sannan ina kokari fita hakkin shi yadda ba zai zama cikin bukata ba sai dai wani abu na sharrin shaidan. Hajiya ta kada kai cikin gamsuwa. Sannan tace, bazaki nemo wani taimako ba ga masana domin hana shi aikata duk irin wannan biye biyen? " Nace Hajiya Allah shine mafi girman mai bada taimako nasan zai yi haka, sannan bazan tauye shiba in yana da bukatar sake aure fa tunda na karanta a wani group cewa maganin hana maza su nemi mata wani sihiri ne sai dai su tsaya ga ke kadai in sunje gurin wata baza su iya yin komai da ira ba. Hajiya ta ce je ki hau gadonki ki kwanta zamu dora gobe,. Saura kwana uku jara bawarki. Kin yi kokari sauran tun a text suka fadi,. Na kalle ta, ba wannan ce Jarabawar ba? Tayi murmushi Ai kin san kafin Jarabawa ana yi Text ko? Ban iya amsawa ba har sai da na kai kofar fita na waiwayo nace sai da safe. A daki ina kwance in tunani in har wannan text ne to ya jarabawar zata kasance? *💃🏻💃🏻💃🏻Masoya masu jiran littafin HAMSHAKIYAR UWA Complete Document,a yanzun haka ya kammala akwai document din HAMSHAKIYAR UWA Complete game bukata zai iya tura kudi kai tsaye ta wannan account number ₦600👇🏻* *0700549935 Halima Abdullahi Access Bank a turo shaidar biya ta wannan number 08140004302 ko katin Mtn* *Phone 08140004302* ..... Da safe bayan na yi salla na koma bacci saboda zaman cikin dare da muka yi da Hajiya Bacci mai nauyi ne ya sani na makara. Kwankwasa kofar da Juma ke yi shine ya farkar da ni, ashe wayar cikin gida ta jima tana ruri amma ban ji ba saboda bacci. Na tashi da sauri na bude kofar Juma ce nace lafiya Juma na ganki da sassafe? Tace ni da matter gidan muka taho, Hajiya ta kira mu. " Nace har na zaci ko haihuwar ce. " ta ce a a, lafiya baki fito ba? Nace lafiya lau. Tace Hajiya tana neman ki, na shiga ban daki na yi fitsari sannan na fita. Hajiya bata falo na shiga dakin ta. Tana zaune akan kujera ta nuna min wani akwatin ga kayan ta a kusa da akwatin tace, " Shirya min kayan nan a cikin jakarnan. Yawanci dogayen riguna ne marasa nauyi, sai wani farin yadii wanda lokacin da na dago shi sai da gabana ya fadi, duk da cewa bansan likkafani sosai ba, ba shakka shine wannan. Sai wasu turaruka da kuma ganyan magarya. Na gama tsaf. Tace "Kin karya? Nace 'a 'a, tace kije ki karya sai ki zo. Nace Hajiya bana jin yunwa. Haka nan naji duk firgici ya kamani. Tace to inje in shirya kayana kamar kala biyar a karamin akwatina in zo. Na shiga uku, Hajiya kodai gida zata maidani ne! Ko yaya abin ya ke? Na tambayi kaina, amma bani da amsa. Na yi yadda tace. Na dawo nace Hajiya na shirya. tace in kira Juma na kirata, tace in fita suka gama magana tukunna. Na fita Juma ta fito. Nace. Wai Juma ya na ganki a nan? Tace za kuyi tafiya ke da Hajiya. Ni da Azima ne muka dawo nan na fada miki tun dazu. " Mamaki ya kamani amma sai na yi shiru. Na koma dakin Hajiya. Tana rubuta wata takarda ta gama. Sannan ta amsa wayar da aka kira ta ana fada mata ce karfe daya jirginmu zai tashi, tace kije za a kai ki a yi miki passport yanzu ai kina da Karin zabe ko? Nace sai na dan kasa, tace duk daya kije dashi in kin dawo ki ci abinci kiyi wanka ni kuma zan dan saka kalle a kafa da hannu kafin lokacin. Ki kira Ummarki ki fada mata zamuje India baifi muyi kwana bakwai ba. Nace to. Muka fita da direba zuwa Immigration office, wanda mukaje gurinshi ya ce, maimakon Hajiya ta turo aje ayi miki har guda. Nace ba damuwa ai duk daya ne. ko a wa daya banyi ba na dawo da ID card dina na fita kasashen duniya, wanda ni ban ma san wai dai anyi shi sannan za a fita wata kasa ba. Na ci abinci sama sama, ina ta yin tufka da warwara, domin bansani ba ko jarabawar acan za a yi ta . Na shirya tsaf sannan na kira Umma na fada mata zamuyi tafiya zuwa kasar India da Hajiya. Ta yi addu'a Allah ya sa mu je lafiya mu dawo lafiya. Na samu Juma a kicin nace wai ni abinda ya daure min kai, naga Hajiya ta saka likkafani da gayan magarya a jar tafiyar ta. Juma tayi dariya, tace to ai ita Hajiya ko Zamfara zataje sai ta tafi da wannan guzirin nata, tun muna tunanin in ta tafi bazata dawo ba har muka saba muka dai. Na sauke Ajiyar zuciya nace har na tada hankali na wallahi. Tace "Dan tafiya bata taba hada ku lokaci daya bane. Na sake shiga gurin Hajiy sai yanzu ta fara saka lalle Tace ani naki ya yi sauri,. " Nace haka ne, na amshi lalle ina saka mata. Tace inyi mata sukuf gaba daya, nace tsohuwa ta fada kwanta da na miki irin lallben da ki ke yi. Tace "Kayya zamu bata lokaci kinsan jirgi baya jiran kowa. " Nace to shikenan, Tace amma baki sanar da mijinki cewa zamu yi tafiya ba ko?" Nace ai baki ce in fada masa ba ne shiyasa. Tace Yawwa ina jin dadin yadda baki da gaggawa da rawar kai. bana son ya sani har sai mun dawo." Nace kuma ba laifi inna tafi babu izninsa ko? Hajiya ta dube ni,. "Har yanzu baki yarda cewa kai da kaya duk mallakar wuya bane kenan? " Nace na yarda mana. Karfe daya saura mukayi salla, Hajiya ta sa aka kira kowa kamar yadda ta yi lokacin da za su tafi aikin Hajji. Ta shafa kan kowa tace na yafe muku kuma ku yafe ni. Duk aka yafi juna nima nace a yayyafe. Daireba ya jamu zuwa filin firgi. Mun samu wasu mutane guda biyu wadanda nake zato ko lauyoyin ta ne, amma ba wadanda na sani bane masu zuwa gida, ko kuma sune ban gane su bane oho. Tare da su muka hau jirgi zuwa Legas daga can muka rabu da su bayan sun yi wata ganawa ta musamma da Hajiya na misali minti talatin zuwa. dare aka kwashe mu zuwa India. Duk a tsorace nake domin ban taba hawa Jirgi ba, daga Kano ma da zamu ta so sai da na kama hannunuwan Hajiya na kankame, ji nayi kamar hanjin cikina ne zai koma kirji. Salati kuwa da na kama sai da Hajiya ta girgiza min kai tana fadin ki samu nutsuwa addu'a a hankali ake yinta. To da zai tashi daga legos kuma sai naji kamar zanyi amai kafin daga bisani na daina ji sai kuma fargaba da tsoron Allah. A zuciyata nace ganin damar Allah ne faya sa jirgin nan ya fadi da mu, gaskiya Ubangiji yana son bayinsa. Na shiga istigfari ga shi na shigo duniya bada iznin mijina ba. Koda yake mahaifiyar sa ce ta gayyace ni. Naji an kama hannuna a hankali na daga ido na kalli Hajiya wadda ta tsura min ido, tace Rabi 'atu tsoro ki ke ji ne? Nayi dan murmushi nace Tsoron Allah ne ya yake ratsa zuciya ta. Tace kar ki damu haka duk wanda bai saba hawa jirgi ba ya ke fuskanta. Ki kwantar da hankali. Ta sake sauke ajiyar zuciya, sannan tace, "Zan dora miki wani nauyi wanda Allah shine ka dai wanda zai taya miki. " Na ce na am! Hajiya cikin mamaki da fargaba nayi maganar, tace "Zan baki amanar Aliyuna. Na ma manta waye Aliyu. Nace waye kuma Aliyu? Tace "Shamaki nake nufi. Na zaro ido, tace na baki amanar 'ya'yan Shamaki." Nace me yasa zaki bani amanar su banyan muna nan tare da ke su kuma suna gida? Tace "Zan baki dama ki min tambaya amma sai mun isa can zaki tambayi duk abinda ki ke so. Cikin tsanaki. Ta sake rike hannu na Na baki amanar Azima kar kiyi amfani da son da Shamaki yake miki ki cutar da ita ki yi mata adalaci kar ki bar kishi ya yi tasiri a zaman ku. Na baki amanar zumunci Shamaki da ''yan uwanshi, duk yadda za ayi kar ki bari zumuncin su ya samu tangarda! Na baki amanar dangina da dangin Shamaki." Jikina ya hau bari na soma tunanin ko jirgin ne zai fadi. Nace Hajiya in jirgi ya fadi ai har ni ne baza mu rayu ba. Tayi murmushi, sannan tace ba jirgine zai fadi ba, ina son ki kwantar da hankali ki amshi duk wannan amanar da nake baki, domin zaki iya. Dan Allah kar duk wani me aiki ko wani wanda muke dangantaka da shi ya ce, wayyo yau ina ma Hajiya tana nan. " Nace to Hajiya duk da kince kar in tambaye ki, a can zaki zauna in munje? Tace za kiji komai. Ta sakar min hannu. Na zura mata ido ina tunanin abinda Hajiya take magana kamar me wasiyya kuma gata dai lafiyar ta lau. Ko kuma dai in mun koma ne zata koma gefe ta sakar min komai? Na sauke ajiyar Allah ya sa ma haka ne zai fi sauki aka ace Duniyar ta ke maganar bari. Haka dai muka isa Kasar wata mota ta zo ta dauke mu da kayanmu zuwa wani katafaren gida. Mun samu wasu hadimai kamar dai irin wadannan da muke gani a fina finan India. Sune suka amshi kayanmu zuwa wani daki da ke sama. Muka shiga dakin kato ne sosai gadon da kujerun duk a ciki suke. Muka yi salloli sannan muka kwanta duk da cewa garin ma yariga ya waye. Na farka naga Hajiya zaune kan kujera tana shan shayi suna tattaunawa da wani mutum Baindiye wanda nake zaton likita ne, saboda rigar likitoci dake jikin shi. Nabi mamakin yadda mutumin ke yin magana da Hausa duk da cewar Hausar bata goge ba. ..... Yace "Hajiya ciwo ya zo matakin karshe kamar yadda muka fada miki a wancan lokacin. Abinda Gwajin mu ya nuna shine kin shiga matakin karshe na ciwon Allah zai iya ganin dama ya barki. Sannan a ka ida bai kamata muna fada miki halin da kike ciki ba, yaranki sune ya kamata su sani ke kuma a boye miki amma kin ce a a. Banda kina da karfin hali da yanzu kin mutu saboda fargaba. " Tace Dr ni musulma ce tun daga lokacin da ku ka fada min ciwona zuwa matakin da nake kai yanzu ban taba jin cewa bazan mutu ba. Kuma fasa yin bautar Allah ba, kuma nasan cewa dole zan mutu watarana ko babu wannan ciwon. Ina da dalilaina da bana son yara na su samu labarin wannan ciwo tsawon shekaru biyar da kuka ce zan iya kaiwa na rayu, da su cikin farin ciki, in da sun sani ni da su zamu rayu cikin damuwa da tashin hankali. Nakasan ce ina boye musu, kuma ina neman mafita ba wadda zata hana mai aukuwa ta auku ba, ina neman mafita ne kawai wadda zata zama madadi a gare su. Nasan babu madadin mahaifiya tabbas, amma ana samu mai share hawaye. Cikin jimami yake ce mata "Kin samu? " Tace Ina fatan cewa na samu. Ka ga waccan ta nuno inda nake da yatsa tare da waiwayo ta kalli Inda nake kwance, sai muka hada ido fuskarta sharkaf da hawaye ina yin wata irin ajiyar zuciya mai hade da kunshe kuka irin na tashin hankali. Da sauri Hajiya ta mike ta nufo ni. Maman Umar ta shigo da sallama Falon shiru. Ta nufi ciki, Juma ce take hada miya yayin da Tabawa ke firar doya. Tace "Juma kina ciki?" Juma tace Sannu da zuwa Maman Umar yanzu ki ke tace? "Wallahi nice, ina Mamanmu take ban ganta a cikin ba. " Juma ta bi Maman Umar da kallo, domin bata taba jin ta kira Hajiya da Maman su ba. Maman Umar ta yi yar dariya tace "Juma mamaki ki ke ji ne?" Juma ta ce Ato ai dole inji mamaki na ga wata sabuwar Shagwaba. Ta kawaikwayi muryar Maman Umar wai Mamanmu. Maman Umar ta yi dariya tace kin san Allah ina zaune naji kawai ina son ganin Hajiya na kira wayar ta sai naji bata shiga, shine na ca bari dai inzo." Juma ta saka dariya tace wannan karon Hajiya ta yi wa kowa bazata, nifa kawai kira na tayi tace tanason za su yi tafiya da matar Shamaki Uwargidan. Tace mudawo nan gidan har Azima, a kula da gida da kuma yara. Nace ina za suje tace kasar waje. Cikin tsananin mamaki Maman Umar ta ce, Hajiya ce kuma yau tayi tafiya ba tare da saninmu ba?" Juma tace ina zaton Uban dakina shine kadai zai iya sanin tafiyar nan. Maman Umar tace to ina taje kuma wai harda matar Shamaki? " Juma tace ni dai bansan kasar ba, ta dai cemin kasar waje. Maman Umar ta danno lambar Baby tana fadin ba lallai a samu Baby a waya ba saboda layinta in ba anyi masa aiki ba to fa ba zai yi amfani tana wata kasar ba. Layin kuwa bai shiga ba. Ta kira layin Maman Nana wadda tasan ko Hajiya ta boye ma wani wata magana sai ta fadawa mata. Suka gaisa, tace "Wai kuwa Maman Nana Hajiya ta fada miki zata yi tafiya? Maman Nana tace a a gaskiya bata fada min ba, ina taje? Ban sani ba, ji nayi ina son ganinta na zo sai kuma wai ashe sun fita waje da matar Shamaki. "Wace kasa?" Maman Nana ta tambaya cikin mamaki. Maman Umar tace bansani ba nima, ga wayoyin ta duk basa shiga. Maman Nana ta yi shiru, can tace "Tofa! To kuma Shamaki ai ya sani ko? " Maman Nana ta ce Shamaki yana da masaniya ki kira lambarsa ta Dubai ko ta Chaina Nima zan kira. Har Maman Umar ta tafi bata samu layin Shamaki ba, kuma duk su Maman Afra da Maman Iman babu wadda bata kira ba amma basu san komai game da tafiyar Hajiya ba. Gashi wayar Shamaki ta kasa samuwa. Maman Umar ta kira su gaba daya zuwa gidan ta, tace itafa tana ji a jikinta akwai wani abu, tana zargin Shamaki ya gudune domin kar Hajiya ta sa shi ya saki Baby. " Maman Iman tace ni kuma na kula Hajiya tana son Baby, kila dai ta fita da ita ne a dubata ko zata samu haihuwa domin kusan so biyu tana yi min magana akan rashin haihuwar Baby.? " Maman Nana tace "Hakan ma zai iya yiwuwa. " . Maman Afra tace in har batun Haihuwa ne nasan Hajiya India zata nufa a duba mata lafiyar Baby, dan haka sai mu bincika mu gani ko can ta tafi idan canne sai mu daina daga hankalinmu. Take Maman Umar ta kira wani a office din masu yin bizar wanda tasan shine Hajiya ke yin Hulda da shi. Ta tambaye shi ko bizar wace kasa ya yi wa Hajiya? Yace ta India ce, maman Umar ta tambaye shi tsawo lokacin da bizar zata dauka. Yace "sati biyu ne ta yi masa godiya suka yi sallama. Daga nan suka ce bari su jira har su dawo, sai dai cikin su kowa na mamakin abinda yasa Hajiya ta ki tayi musu sallama. Domin koda Hajiya take boye musu wani abu na sirrin gidan ta, bata taba boye musu cewa zata yi tafiya. Tana yin sallama da su koda a wayane kuma ta nemi gafarar su ta kuma ce ta yafe musu, tun suna jin babu dadi game da sallamar ta ta harma suka saba bama sa jin komai game da hakan. Shamaki wanda shima ya kashe wayoyin shi domin kar Hajiya ta kira shi ta ce ya turo mata sakin Baby tun da yaje Dubai ya kasa tafiya China domin rayuwar bata yi masa dadi, tsawon wane lokacin zai dauka yana gujewa Mahaifiyar shi, yasan yana son Baby amma ko kusa bazai hada sonta da na Hajiya ba. Yanzu gashi tun da ya zo tunanin ya gujewa Hajiyar ke damun shi. Baby sai dai kewa da tunani rabuwarsu ke samun shi. Ranar da ya cika kwana biyar a kasar, ya yanke shawara cewa ya kunna waya ya san zuwa yanzu Hajiya ta kira shi sau babu adadi. Sai dai har aka yi kwana biyu Hajiya bata kira shi ba. Tabbas Hajiya tayi fushi da shine domin da yanzu ta kira shi. Yace bari ya kira ta. Wayoyin Hajiya basa shiga. Ya kira wayar Baby ita ma bata shiga. Dan haka ya soma shiri tafiya gida domin ya gyara kuskure da ya bata. Sakna wata yarinya ce 'yar Niger wadda suke soyayya da Shamaki, yana sonta sosai amma fa bada batun aure ba, yana ji da ita a matan da ya ke nema. Duk lokacin da zai fita zuwa wata kasa, to da ita yake fita, Ko wannan tafiyar ma da ita suke tare, sai dai tana ta yi masa korafin cewa wannan zuwan bata san meyasa ba, kamar ya fara gajiya da ita, domin tun da suka zo, babu wata shakatawa da suka fita kamar yadda suka saba, sannan bashi da labari sai na Baby da Hajiya har ta gaji da jinsa. Gashi yanzu yana maganar zasu koma. Shamaki yana hada kaya tana tambayarsa cikin rashin jin dadi, "Wai Sweetheart mun fasa zuwa kasar China din ne? "E " ya amsa kawai ba tare da ya kalle ta ba. Tace "Gaskiya nifa bazan tafi yau ko gobe da ka ke magana ba. Ya aje jakar da ya gama hadawa sannan ya zauna tare da daukar wayar sa yana kara danna kiran Hajiya da Baby. Kamar kullum dai layuka a rufe. Sakna ta maimaita cewa ita fa ba yau zata tafi ba. Yace kina iya zamanki mana, bani da matsala akan haka. Tace zaka biya min kudin Hotel din kenan da abinda zan ci abinci da wanda zan kashe? " Yace akan wane dalili kenan zan yi hakan? Tace akan dalilin cewar kaine ka kawo ni." Yace ni dana kawo ki maidaki kawai zan iya yi amma ba wai in dauki nauyinki ki zauna kici gaba da karuwanci a nan ba. Ta fusata, nice karuwa? Ya dago a fusace to fada min sunanki matar aure? Ta lumshe ido cikin ta kaici sannan tace na gode ba laifinka bane. Shamaki ya yi tsaki ya tashi ya fice daga dakin. Hajiya ta juya ta kalli likitan tace zaka iya lafiya, sannan maganin da nake sha ya kare, yana taimaka min gurin rage radadin da jikina ke yi. Dr yace Hajiya kiyi hakuri maganin ba zai ci gaba da amfani a jikin ki ba, mana ana ko kinsha nazai yi amfani ba saboda matakin da kika shiga. Amma akwai abu daya, zan zo da wani magani zamu sa shi a ruwa sai mu jona miki, anyi gwajin maganin a jikin wani balarabe kuma ya samu sassauci. Hajiya ta daga kai kawai. Sai lokacin na lura da wata rama da baki wanda Hajiya ta yi. Tafiyar da take yi a hankali nake kallon kasaita ce ashe karfin haline. Tana zama kusa da ni sai na fashe da kukan da nake kunshewa. Na dora kaina a kafadarta ina fadin Hajiya da gaske ne wai baki da lafiya? Ni fa banyar da ba, suna karya ne, Allah shine kadai yasan ranar mutuwar ki kawai ki tashi mu koma gida. Insha Allahu bazaki mutu yanzu ba. Na sauka na soma hada kayan mu ina fadin ki daina sauraron su. Na sauke akwatuna ina kuka ga hawaye ga majina. Hajiya tana ta kallona cikin yanayin da bazan iya fassarawa ba. Na zo na kama hannunta tashi Hajiya mu tafi gidanmu. Hajiya ta janyo ni tare da fadin zo nan Rabi'atu. Ta zaunar da ni kusa da ita, ta kama gefen mayafinta ta share min hawaye, tace yi hakuri ki yi shiru za muyi magana ne Na dora kaina a kafadar Hajiya ina ajiyar zuciya tana shafa bayana tana fada min cewa "Kiyi hakuri muyi magana, na zo da ke nan ne domin mu tattuna abinda ya kamata, ina son ki sani ba karya likitocin nan suke yi ba, ilmin ne Allah ya basu, ciwona na Cancer ya bayana ne tun a ranar da na haifi Shamaki. Babu wanda ya sani daga ni sai mahaifinsa, Kafin rasuwar mahaifinsa ya tada hankalinsa sosai saboda likitocin su fada mass cewa canser a bakin mahaifata yake, za a iya yanke ta, sai muka amince aka yi aiki aka yanke kamar na samu lafiya lokacin Shamaki yana guje gujenshi ya fara wayo sai ciwo ya dawo. Lokacin da likita ya fadawa mahaifin Shamaki cewa Cancer nan ce ashe ta yadu a wasu sassan jikina hankalisa ya tashi kuma ya gama likitan ya fada min, ya dage gurin nema min magana. Na gargajiya daba bature. Na samu sauki ba tare da nasan meke damunka ba. Har zuwa lokacin da Allah ya yi wa mai gidanta rasuwa bani da masaniyar ciwona. Soyayyar Mahaifinsa na tara ta a kansa, munyi wata irin shakuwa wadda ta sa har 'tan uwansa suke min mita akan nafi sonshi. Gado daya muke kwana har sai da yakai matakin balaga sannan na yakice shi. Dakyar ya fita waje karatu lokacin da ya kai matakin Jami'a, bai zauna ba sai da na bar komai naje muka kama gida na zauna da shi tsawon wata uku..... ..... , Hajiya ta ci gaba da fadin. "Bayan ya gama karatu 'yan uwanshi duk sun kama dakunan su, nice nake kula da kasuwancin dukiyar Shamaki da kuma tawa. Allah cikin ikonsa ya gama karatunsa yazo ya kama kasuwaci. Iyaka biyayya Shamaki yana min, addu'a ta kullum a gareshi ita ce, ta samun mace mai hankali wadda zata kula da rayuwar shi bayan mutuwa ta. Shekaru biyar da suka gabata ciwona ya sake tashi ya tsananta lokacin ne aka fita da ni aka kawo ni nan kasar. Likitan ya gano cewa Cancer ta riga ta cini, Kafin ya yi magana da su Shamaki nace masa nasan ina da ciwon Cancer ina rokonsa don girman Allah kar ya fadawa duk wani ahalina zasu rayu a bikin damuwa kafin in mutu, ko menene ina son muna magana da shi cikin sirri. Yace min nan da shekaru biyar zan iya mutuwa na yi tsawon rai in shekara biyar zuwa watan uku kamar dai irin wannan watan. Ina matukar kaunar yarana ina tausayin su, ina soyayyarsu irin wadda Allah ya dora min kamar yadda ya dorawa ko wace uwa akan yaranta. Na kan shiga daki inyi kuka sosai domin nasan mutuwace take tinkaroni kuma zata rabani da su, dan haka sai na damu da lamarin Shamaki, wanda zai tattara dukkan soyayyarsa ga matarsa gashi bai iya kai matsalarshi ga wani abokin shi bare 'yan'uwan shi komai nice abokiyar shawarar shi. Ko zai iya samu wadda zata tallafe shi ta yi hakuri da shi a duk yadda ta same shi? Farko ni ce na bashi dama ya memo wadda yake so, suka hadu da Maman Meema a bikin abokin shi Shamsu. Na samu kaso shidda a cikin goma lokacin dana sa a gabatar da bincike akan yarinyar, na hakura ya aureta aka soma zama, amma sai na yi kokarin gwada halayenta ta hanyar gwaji. Sai na gano cewa ba itace matar da ta dace da shi ba, bata da rufin asiri ko kada, ga son kanta kuma bata shiri da 'yan uwansa, bugu da kari ga ta sai ta dauki wayar sa ta yi transfer na kudi masu yawa daga bankinsa zuwa nata, kuma tace ba ita bace. Dan haka na sa shi ya bata takardarta ya kuma bata ba tare da ya nemi jin daliliba. Kasancewar bamu da ishasshen lokaci saboda kwanakin mutuwata kara kusantowa ya ke yi. Sai na saka Kawata Hajiya Zaliha ta memo masa mata, ta so ta bashi 'yarta, amma sai na nuna mata ta hakura bana son yara su shiga tsakanin zununcinmu, na fada mata haka ne domin bazan iya kara akan Shamaki ba. Dan lokacin da ya rage min ina son in nuna masa duk wata soyayya ta. Dole ta hakura ba domin ta so ba. Maman mubina. Ita kuma banda kokarin azurta kanta da danginta bata komai, duk lokacin da nayi mata gwaji akan wani abu kamar sadaka ko zakka ba ruwanta da dangin Shamaki kanta ta sani. Gashi bata san girma ko darajar kowa ba. Tana son ta yi mulki har da ni. Abinda yafi daga min hankali shine yadda ta ke tauye masa hakkin sa na kwanciya wanda hakan ne sanadin nitsawar. shi a neman mata. Shima na sa ya rabu da ita. Kuma bai tambayi daliliba Na ci gaba da yi masa addu'a Cikin haka ya samo Maman Anisa yana sonta itama tana son shi amma sai tana kula tsofafin samarinta, har ta taba ziyartar gidan wani saurayinta wanda bani da sheda akan abinda ya faru, sannan tana waya da maza daban daban. Har zuwa yau batasan na sani ba, haka kuma Shamaki bai sanI ba domin ban fada mishi ba kar ya fara zargin ko ma 'yarsu ba tashi bace. Ya jinjina kuma ya girgiza lokacin da na ce masa ya sake ta. Dan yana sonta, tsabar ladabi da biyayya har zuwa yau bai taba tambaya ta me ye dalilin sa shi ya saki matansa ba. Abinda ya yi Imani shine bazan taba cutar da shiba. Gashi zan mutu bansan takamaiman gurin wa zan bar shi ba. Muryarta ta sarke hawaye suna kwaranya a kan kumatun ta, na sa hannu ina share mata hawayen, ga nawa suna kwaranya. Na kama hannunta. Nace Hajiya ki barshi a hannun Allah ki barshi a hannu na. Ta saka hannunta ta damke nawa ta ci gaba da fadin Na yanke shawarar in bashi Azima wadda ta zama raino na ce, kuma sai ina kallon zatabi duk wani tsari nawa, sai Allah ya nuna min ban iya ba, wayo da dabarata, ba su isa su sani in samu biya bukata ta ba. "Tun daga ranar da ya kawo min labarinki na fahimci yana matukar son ki, to ina ta tsoro kar a kuma ga lokaci yana ta kure min. Na saka ayi min bincike, naji dadin yadda aka kawo min sakamakon talauci ne kurum abinda suke ganin zai zama aibun ki, na nuna musu talauci ba aibu bane, dan haka ban dakatar da shi ba. Ba dabi a ta bace in saka malamai wani aiki bayan saukar karatun kur, 'ani wanda ake yi mana duk litinin da Juma a, domin neman kariyar Allah da falalarsa, amma sai gashi na saka ayimin bincike a kanki, bayanin Malamin ya yi min dadi ko da ba gaskiya ya fada min ba. Matsalar daya ce bana son yafi sonki ina tsoro kar kiyi amfani da haka ki cutar min da shi, sai nasa aka hado wani sihiri wanda zaki so shi, da Allah ya ta shi nuna min ban isaba, sai gashi kunci dabinon tare ke dashi. In zaki tuna shine dabinon da na baki wanda kika ci a ranar farko da ki ka kawo ziyarar gaishe ni ke da kanwarki. Ki yafe min wannan cutarwar da na yi miki. Ta sauke a jiyar zuciya. Ta saka hannunta ta sake share min hawayen kan fuskata hannuwan ta sanyi kalau. Tace "Kafin kasa ta rufe idona, kuna zargina da son kaina game da 'ya'yana, ba haka bane ina kokari ne in nuna musu dukkan soyayyata a cikin kwanakin da suka rage min a duniya. Zuwanki na yarda Allah ya amshi addu'a ta, ya kawo wa Shamaki wadda zai dora kai a kan cinyarta ya yi kuka ta lallashe shi. Kowata uku baki rufa ba ki ka cinye duk wata jarabawa tun kafin in miki ita. Abu daya ne kinyi karama da jan ragamar amma kamar yadda nace Allah ne zai taya ki. Tun a farkon shekarar nan jikina ya motsa likitana muka yi waya, ya turo min likitocinsu na nan suka dubani, ya sanar da ni cewa ba shakka in har ina da wani abu da zan gabatar in gabatar kafin watannin farko na sabuwar shekarar nan da muka shiga. Abinda Azima da Shamaki suka aikata na dauke shi a matsayin fada Allah ya ke min, in gane wayona da dabarata baza su kaini ba. Ciwona ya tashi saboda damuwar da suka jefani a ciki, wanda tun daga ranar jikina ya motsa gaba daya. Maganin da nake amfani da shi ya daina min aiki. Likitana yace in taho amma in tabbatar cewa na yi duk wata wasiyya kafin in taho domin ba lallai in koma da raiba. Muka fashe da kuka a tare sannan ta dora kanta a cinyata, munyi kuka mai tsuma zuciya tsawon minti biyu, sannan ta dago tana lallashi. Kiyi hakuri Rabi'atu, ki dauki girman da Allah ya baki. Cikin dashasshiyar murya da makyarkyata nace bazan iyaba Hajiya abubuwan suna da yawa. Tace zaki iya kinyi na gani, har abinda ya shafi kasuwar Shamaki zaki shigo ciki domin taimaka masa. Na rubuta na aje masa a cikin wasiyyar da na rubuta musu kowa da tasa. Abinda ya shafi sadaka ko zakka kinyi na gani, sannan za a samu karin wasu duk Allah zai haska miki tunda shi ya kawo ki. Ranar da na kiraki cikin dare jikina ya matsa na zaci ranar zan mutu gashi ina son in tabbatar ko kinsan waye Shamaki. Duk abinda Juma ta ke fada miki da tattunawar da ki ke yi da ita nice na tsara domin in kara tabbatar da wacece ke, haka kuma tura Juma gidan Azima shima nayi ne domin in gano ko za su baki wata matsala bayan bana nan. Dan haka ki rike Juma sosai tana da Amana zata taimaka miki. Na hanaki zuwa aikin Hajji da Ummara domin in auna hakurinki, na tafi da kishiyar ki domin in jaraba kishinki sai na samu Allah ya miki baiwa ta hakuri kawaici da kuma tsaida zuciya daya tare da dayanta Allah. Ba bukatar sai na fada miki tsakanin Shamaki da "yan"uwansa, domin kin binciko duk ina da bayanin yadda kuka fara, ni ce nasa Juma ta fada miki cewa zan tambaye ki waye Shamaki saboda ina son ki saka hankali ki gano waye shi din. Ni ce na aje littafin da kika karanta. Kuma ina sane da zuwanki gurin tsohuwa a Face. Ta nuna akwatin ta, dakko min waccan akwatin. " Na mike jiki babu karfi na tafi dakko akwatin Hajiya wadda na jasu zuwa hanyar fita danzun nan. A kasan muka bude dan tashin hankali ya sa bani da karfin da zan iya daga ta in dora saman gado. Muka zauna kasa muka sa akwatin a tsakiya. Ta ciro littafin tarihin Alhaji Ali Baita. Tace ga mai kyan duk da kinji komai, amma komai yana cikin nan. wancan wanda kika karanta wanda aka yi kuskure ne aka kawo na duba, shine aka rufe gurin kar wani ya karanta. Ta ciro wata folda ta miko min wannan ki adana masa su, duk wata sheda ta dukiyar Shamaki tana cikin nan. Lauyoyinsa amintattune mutanan Lagos, sune suka je na gabatar musu da ke a matsayin matar Shamaki wadda zata saka ido akan dukiyarsa." Na zabura, bazan iya ba, banajin yaren turanci bansan Hajiya ta dafa kafadata, ki kwantar da hankalinki, sannu zaki gane komai, abin duk mai sauki ne, kuma su sunajin Hausa. Taci gaba. Zuwa yanzu dai Allah ya sa zan mutu cikin natsuwar cewa zan bar Shamaki a gurin ki. Kar ki manta kuma karki shagala, amana ce. Kin riga kinsan waye Shamaki ma ana, kinsan dabi'unsa masu kyau da marasa kyau, kinsan halayen shi, kin san me yafi so da kuma abinda baya so, kinsan me zai iya da kuma abinda ba zai iya ba. To dan haka kin san ya zaki zauna da shi. Ta dube ni cikin ido, haka ne?" Na daga kai, alamun eh. Tace kinsan Shamaki Allah ya baki hakurin jure duk wasu matsalolin da zaki fuskata. Ta ce ciro likkafani da ganyen magarya ki saka a waccan durowar domin kar ya yi nisa. Ta ciro wani makullin karami ta bani, tace "Wannan ki saka a jakarki, makullin wannan durowar ce ta daki na, akwai gwalagwalan da nake amfani da su wanda yanzu zai zama gadon yarana, bana son makullin ya fada hannu da ba daya daga cikinsu ba, amana ce ki ba Maman Umar. Ta saka hannu ta ciro dan kunen kunnenta ta ce ki saka wannan a kunnen ki ta ciro zobe daga karamin yatsanta ta ce saka wannan shima, duk lokacin da ki ka kalla sai ki tuna cewa nice na baki, kuma ki yi min addu'a. Wani irin kunci naji zuciya da idanuna suka kafe da hawayen sai radadin yaji. Nace Hajiya to wai yaushe suka ce miki abin zai faru? Ta lumshe ido cikin fargaba wadda nake gani a idanunta. Tace "Su kansu baza su iya sani ba, bare ni. " Nace ni nafi zargin cewa ba gaskiya bane kuma in Allah ya yarda ba zai faruba, ga ki lafiyar ki lau. Hajiya tace "Ba ki san abinda nake ji ba da kuma wanda nake gani a mafarki na. Ina tabbatar miki abin zai faru, ki tayani addu'a in hadu da Allah lafiya. In amsa tambayin kabari. " Na sake rike kai. Mutuwa fa, kuma kasan cewa zaka mutu har ma da wa'adi, gaskiya Hajiya jaruma ce wadda ta cancanci a bada labarinta. Na dago kai nace kuma nace Hajiya me yasa ki ka zo dani domin inga wannan tashin hankali? Tace saboda kar ki shagala da Duniya, kuma hakan zai baki dama ki rike amanar da na bar miki. Ta ciro turaruka guda biyu, ki aje su kusa da ke za a yi amfani dasu gurin wanka gawata da kuma likkafanina. Shamaki ya kira direban su Malam Bala lokacin da zasu taso daga filin jirgin Abuja. Sakna wadda take fushi tun da suka taso ta dauki jakarta tana yi masa kallon sama da kasa "Zan iya tafiya yanzu ko?" Domin nan ba Dubai bane ina da masu daukar nauyin na. Shamaki ya kalleta. "Ko a can ban rike ki ba kece baki ga damar zama ba, Sakna zan fi son haka kije abinki. Haka ka fada ko, zaka nemeni babu shiri. Ta wuce. Ko kallo bai bita da ba, ya maida kanshi ga abinda ke damunshi, har a Abuja ya kasa samu su Hajiya. Ya danna kiran Maman Umar ta shiga, a ringing na biyu ta daga. Ina ka shige ne mun nemeka mun gaji? Yace farko dai "Hajiya fa wayoyinta basa shiga. " Tace Hajiya suna India suda Baby, muna sa ran ta kaita ne a duba ko akwai matsala ne game da rashin rashin haihuwar ta... ..... Shamaki ya ji wani dadi ya rufe shi, yace "Alhamdulillah! Ba shakka Hajiya ta gamsu da Baby, Maman Umar Hajiya zata yi min bazata ne. Allah na gode, " Maman Umar ko dai in bisu ne? " Cikin dariya ta ce dan autan Hajiya, to in kace zaka bisu kwana nawa ne kafin ka samu visa? Kilama har sun dawo. Yace akwai yadda zanyi sai dai ina son in bar Hajiya ta ida muradinta." Fari ciki fal zuciyarsa ya sauka a filin jirgi tun yana mota ya fara waya yana neman visa ta India gaskiya gara ya bi su shima ya yi musu bazata. Domin ya kasa fasssra yanayin da yake ciki. Yana shiga falon Hajiya sai ya ji gabanshi ya yanke ya fadi, falon ya yi masa duhu domin ga mazaunin Hajiya amma bata nan. Juma ta fito tana yi masa sannu da zuwa, ya amsa sannan yace "Baba Juma gidan wayam. " Juma tace har ka tuna min da Uwar dakina takance Baba Juma. Yace ashe sun tafi India. " Juma tace ah dama Hindiyar ne kasar waje? Shamaki yace "E canne kasar waje mana.,, " Tace Allah ya dawo da su lafiya. Yace "Ameen. " Ya nufi dakinsa kewar Baby ya ke yi a kalla ko muryarta ya ji, amma wannan bazata da Hajiya ke son yi masa tana azabtar da shi, ba Hajiya ba Baby, gaskiya dai ba Mutum. Ya furta yana cire kaya. Ya fito falonsa ya zauna yana ta kiran yayunsa yana fadin Hajiya zata yi mishi ba zata, suma suna tsokanar cewa ya gudu domin kar ya rabu da Baby. Juma ta shigo ta same shi. Uban daki me za a dafa maka ne? Yace "Baku dafa komai ba? "Tace mun dafa taliya kai kuma ba layinka bace sosai. Yace inda a kwai kayan ciki ko wani dai farfesun a dumamamin shi. Tace akwai na kaza. Yace to shima zai iya yi. Har ta juya sai yace mata, wai Ina Azima ne? Tace tana ciki bari a kira ta. Har ya manta da cewa za a kirata, sai gata ta shigo, ya bita da kallo, duk ta kumbura, Ta yi masa samnu da zuwa ta zauna. Yace kin koma Asibitin kuwa? " Tace Ni banje ko Ina ba, ta turo baki, bayan duk kun tafi ba mai kula da ni Hajiya ma ta dauki wannan matar sun barmi. Shamaki ya bata rai, in basu barki ba ina zasu da ke?" Ko kuwa wani zai tsaya gadinki ne, sannan kuma baki motsa jiki sam kamar yadda likita ya fada. Ta bata rai kamar zata fa she da kuka, tana fadin shi likitan da zaice haka dan ba a jikin shi cikin yake ba, Ina zan iya wani motsa jiki! Shamaki yace to naji yanzu dai tashi kije bana son ki kai ga hasalani karki bata min farin cikina." Ta taba baki sannan ta tashi ta wuce. Haka dai Shamaki yaji gidan babu dadi sam. Fatanshi yasamu visa da wuri ya bisu. A dai dai wannan lokacin Hajiya ta kalli Baby bayan likitan ya gama daura mata ruwa tare da zuba magungunan a ciki, yace zata samu bacci kar a tashe ta. Baby tace to. Ta zauna kan kujera wadda ke daf da gadon ta shimfida tafin hannunta cikin na Hajiya, tace Hajiyata Allah ya baki lafiya. Ta bude ido ta kalle ni, ta cije lebenta da alamu wani guri yana mata ciwo. Nace Hajiya me yake miki ciwo? Ta bude ido, ta kalle ni, ko ina ma ciwo yake min. Nace sannu insha Allah zaki samu sauki. Can tace Amanar me na baki? Nace Amanar duk wani wanda ke karkashin ki insha Allah amanata ne Hajiya. Ta bude ido, sunyi jajir. Tace ina jin Bacci ne amma na kasa hamma tun jiya, kila har hammata ta kare." Nace zaki yi insha Allah. Ta lumshe ido, ki ci abinci fa Rabi'a ki sa a kawo miki abinci kinji?" Nace to. Amma ina wani cin abinci ni ko yunwar ma banaji. Ta bude ido ta rufe tana dan cije lebe sannan ta na motsi da baki kamar salati ta ke yi, can kuma bacci ya kwashe ta. Likita ya shigo ya ce kar inyi wani motsi mai karfi domin ta samu bacci mai kyau. Na fada masa tace ta kasa yin hamma, yace kar ki damu komai zai yi dai dai. Na idar da salla ina zaune ina addu'a sai naji motsinta. Da saurin na tashi na tafi gurinta. Ta bude ido tace zanyi salla. Nace to zata iya zuwa bandaki? Tace bari ta gwada. Mukaje na rike ta domin jikin ba karfi. Gani nake kamar ma su ne suka dora mata ciwon domin lafiya muka zo. Na zaunar da ita tayi fitsari na yi mata tsarki na yi mata alwalla na maida ta kan gado ta kasa zama, tace duk ji take yi ta gaji. Dan haka a kwance ta yi sallar. Haka dai har bacci ya kuma daukarta. Shamaki ya kasa bacci ya mike ya shiga falon Hajiya yaje yana shafa kujerar zamanta. Har yanzu kamshin turarenta kujerar ke yi, ya zauna kasa ya dora kansa a saman kujerar yana fadin ina kaunara ki Hajiya Allah ya dawo min da ke lafiya. Can kuma ya tashi har ya nufi dakinsa sai kuma ya fasa ya nufi nata dakin, da duhu fitilar dakin a kashe. Bai kunna ba ya nufi gadon ya laluba ya kwanta. Cikin bacci yake mafarkin ana biki a gidan gida ya yi cikar kwari ba masaka tsinke ga Hajiya ta caba ado cikin kaya na alfarma amma kuma shi da ''yan uwansa duk suna cikin damuwa. Ya farka ya ji ana kiran sallar farko ya tashi ya lalubi makunna ya kunna haske ya gauraye dakin ya shiga bandaki ya dauro alwalla bai san me ya sa zuciyar shi duk yaji babu dadi ba. Ya tafi kan dardumar Hajiya da ta ke yin sallar dare ya tada sallar raka a ta 'i nil fijir. Ya, na zaune yana tasbihi ya jiyo za a tada salla, ya mike ya nufi fita zuwa masallaci. Kamar ance ya kalli kan madubin Hajiya. Wayoyinta guda ukun duk suna kan madubi. Gabanshi ya fadi, yace wai Hajiya manta wayoyinta ta yi ko ya abin yake? Ya sa hannu ya dauka ya kunna duk suka kunnu, amma abin alajabi duk ba komai an goge komai, sannan kuma babu layikan a ciki. Kamar dai ba a taba amfani da su ba. Jikin sa ya hau rawa ya aje su ya nufi masallaci jin ana sujjada. Suka idar ya fito da sauri sam baiji maganar da liman ke masa ba. Ya nufi dakin Hajiya ya kuma daukan wayoyin, me kuma haka ke nufi. Ya nufi dakin shi ya dauki waya ya kuma kiran duk layikan su Hajiya a kashe. Sannan ya nufi dakin Baby ko ita ma ta bar wayarta. Ya duba bai ga komai ba, ya fito ya nufi falo yana kiran wayar Maman Umar. Ta daga a firgice domin ta rasa abinda ya sa bata da kwanciyar hankali a ciki kwanakin nan. Ko sallama baiyi ya yace Maman Umar wayoyin Hajiya na gani duka ukun an share komai na ciki kuma babu layukan. Gabanta ya fadi, tace to me hakan ke nufi? Yace bani da wata basirar da zan gane haka. Tace Kaje ka duba ko zakaga sim din, in zanje kai yara makarantar sai in biyo. Ya je yana duba kan gado. Yana daga bargo sai ga wasu takardu guda biyar. Ya kai hannu jikin shi yana bari ya dauki guda daya. Ya ga an rubuta Aisha. Ya kuma dakko wata ya duba yaga Maryam. Kanshi ya kulle, waye kuma masu sunan nan? Ya manta da batun sunan 'yan 'uwansa kenan. Sai da ya kuma dakko wadda aka rubuta Aliyuna. Sannan ya fuskanta. Ya zauna a bakin gadon ya warware takardar cikin sauri da rawar jiki ya soma karantawa kamar haka.... Dana Aliyu nasan lokacin da zaka samu wannan takardar kasa ta jima da rufe idona, ko kuma numfashina ya jima da tsayawa. Ka yafe ni Aliyu na zabi in nesanta kaina daga gareku, ina auna yadda zakuji in kuka ga na mutu a gabanku, na tabbatar baza ku manta da wannan ranar ba. Ina son ka rike Baby da amana duk wata damuwarka ka sameta kubtattauna, na yaba da halayenta, itace matar da na sa ka saki mataye uku saboda sa ran zuwanta. Ina fata zakaci gaba da yin dukkan wani taimako domin dauka a taskar Allah. Na yafe maka dukkan wani laifi wanda ka yi min a cikin sani ko akasin haka. Ina son ka yafe min kuma ka ci gaba da yi mini addu'a domin ita na fi bukata. In kunga wayoyin na to ku saka su a gadon ku na goge komai na ciki na kuma zubar da layukan, duk wata mamba mai amfani na kwashe muku su a cikin wani karamin littafi yana durowa. Sauran bayani zaka samu a gurin matar ka. Sai mun hadu a darrussalam!!! Yasa hannu a wani jirwaye wanda ya tabbatar jirwayen hawayen Hajiya ne. Ya mike da sauri yana fadin Innalillahi wa inna ilaihirraji un.!! Maganar nan ba gaskiya bane! ! Juma!!! Ya shiga kwala mata kira da karfi. Da gudu Juma ta fito daga kicin ya kama hannuwan ta da karfi ya jijjiga ya ce, "Wai Hajiyata ce tabar wasiyyar mutuwa! Ina Wayata. Ya koma dakin Hajiya da gudu ya dakko wayar shi numfashin sa na fita da karfi. Ya danna lambar wayar Maman Umar. Tana dagawa sai kawai ya fa she da kuka. A razane ta ce Menene! Yace Hajiya ta! ta! sai ya saki wayar kawai ya zube gwiwoyinsa a kasa ba zai iya furta cewa Hajiya ta mutu ba. Juma wadda tafita da gudu tana kiran masu aikin gidan maza tana cewa su zo ba lafiya sun samu Shamaki yana kuka sosai ya durkushe a kasa. Kafin minti talatin Gidan Hajiya ya cika da ahalinta, ba wanda ke iya rarrshin wani a cikin 'ya'yanta, kowa yana rike da takardar wasiyyar da ta bar musu. Maman Umar itace mai karfin halin bin hanyoyin da za su sami tabbacin halin da ake ciki. Ni kuwa ina nan , banyi barci ba, inma ya dan sace ni, kadan sai na farka sai na kira sunanta, sai ta amsa. Karshe dai na tashi nayi alwalla zan tada salla sai naji muryar ta tana cewa lokacin salla ya yi ne? Nace a a ina son inyi salla in fadawa Allah ya baki lafiya da nisan kwana. Ta ya fito ni da hannu naje, tace zan sake neman alfarma. Nace To Tace "Dan Allah in Shamaki ya yi miki laifi dan Allah in zaki masa hukunci ki tausaya ki tuna da ni ki yi masa rangwanme. Hawaye suka sakko mata. Na ce Hajiya na fahimci kaunarki da Shamaki insha Allah zai baki sauki. Tace je kiyi salla ki roka min sassauci a gurin Allah. Na juya na tada salla zuwa yanzu bana iya kuka sai dai suyar zuciya. Na kasa ci ko ruwa na kurba sai inji daci. Lokaci da na idar bacci ya dauketa domin ina jin numfashinta da karfi ya koma. Na ji dadi bacci ya dauke ta. Da safe likita ya shigo, muka gaisa ya tambayi jiki lokacin ya nufi gurinta, sai naga ya firgita, ya dakko jakar da ya zo da ita ya bude ya ciro wata allura ya hada ya yi mata. Ya daga wayar sa ya kira yana Indianci. Ba jimawa kuma sai naji motar Asibiti. Haka muka tafi asibitin ina jin zuciya ta kamar ta fado kasa. Likitoci suna ta kai kawo an hana ni shiga dakin amma ina kallo window. Cikin dare Hajiya rai ya yi halinsa. Ashe bacci da nake zaton ta yi ta shiga doguwar suma ne. Likitan ya maida ni wannan gidan ya fada min za su adana gawar Hajiya sannan zai kira lambar da Hajiya ta bashi tace ya kira in ta cika a kira a sanar musu. Cikin wannan jimamin aka kira Shamaki aka sanar da shi rasuwar Hajiya. Ta fiyar ba shiri ta tashi dan haka Shamaki da mazan yayin shi guda biyu suka tafi domin taho da gawar Hajiya. Gidan likitan ya kai ni domin ba zan iya zama a wannan katon gidan ba, na kasa ci na kasa sha kuma na kasa kuka, ajiyar zuciya kawai nake yi iyalan likitan suna ta faman lallashina. Duk da banajin yarensu. Dole likitan ya daura min ruwa saboda na Ki cin komai. Shamaki kawai nake son gani..... ...... Bacci ya fara fizagata sai naji an dafa goshina, da sauri na bude ido. Shamaki ne, yana tsaye. Na tashi da sauri ina kallon shi kamar wadda na warke makanta duk ya fita a hajjacin shi. Zanyi kuka sai na tuna da muryar Hajiya kamar a lokaci tana fadin na baki amanar Shamaki. Na bude baki zan yi masa magana, sai kuka ya kufce min. Ya zauna a bakin gadon bai iya furta komai ba. Na ce Shamaki mun rasa Hajiya. Ya daga kai, da kyar ya furta ta so muje. Munyi sallama da iyalan likita ya rakamu har mota. Ashe sunje sun kwaso kayanmu a wannan gida. Lagos muka sauka, daga nan muka wuce Kano. Naga dauriyar Shamaki duk da ko magana baya iyawa sai dai da kai. Dama anyo mata wanka tun acan na ba su duk wani abu data bada ayi mata amfani da shi kuma sunyi. Gidan ya yi cikar kwari dam da Jama'a haka muka iso Muna shigowa Falon Hajiya aka aje ta. Na zauna ina kallon yadda yaranta suke zuwa suna yi mata addu'a, na kara tabbatar wa Duniya zancen banza ne, da kudi ko kauna ko dangata ko sanayya suna hana mutuwa da baza a fita da Hajiya daga wannan Hamshakin falon nata ba. Haka suka gama yi mata addu'a aka fita da ita. 'Ya'yanta suna ji suna gani, Maman Nana har suma ta yi, Maman Iman ta tada aljanu amma haka aka tafi da ita. Ummana suna gidan su da su Umman Amina, Abba da Abban Zuhra duk da su aka yi jan iza sun dawo daga makabarta su ka kirani muna gaisawa suna min ta aziyya aka ce ga Shamaki can anyi Asibiti da shi ya ki tasowa daga gaban kabarin Hajiya, da aka kamoshi sai ya zube a sume. Da sauri na ce wane Asibitin aka kai shi, sai aka ce wai inyi hakuri maza suje. Nace a a ni sai naje. Maman Umar ta dauke ni a mota muka tafi. Yana kwance a gadon tamkar mai bacci, nace Maman Umar ya farfadone? Tace "E bacci yake yi. Nace zan jira ya farka, tace inzo muje akwai su Baban Umar a nan din in ya farka sai a dawo da ni.". Nace kuyi hakuri ba taurin kai zan muku ba kubarni na soma kuka ina fadin Hajiya ta bani amanar shi, ta maimaita min har a kalamanta na karshe tsakanina da ita. Dole suka barni suka tafi. Kamar awa daya, sai ya yi mika da salati ya farka sai kuma ya mike zaune da sauri yana kallona, ya kalli dakin,yace "Baby da gaske ne Hajiya ta rasu? " Na ce Shamaki muyi hakuri Hajiya ta yi kyakykyawan karshe kuma ta tafi tana sa muku albarka. Ba ta bukatar komai sai addu'armu. Ka kwantar da hankali muna yi mata kyakykyawa zato. Yace nifa Baby abinda ya bani mamaki Hajiya lafiya lau take sai dan zazzabi dama ba ke ta kai ba kamar dai yadda muka zata. Nace haka muke kallo. Ashe Hajiya tana dauke da ciwon Cancer tsawon lokaci. Ta fada min cewa tun a lokacin haihuwar ka, kuma ta fada min shekaru biyar baya likitoci suka gano cewa bazata wuce wannan lokacin ba. Ya soma girgiza kai hawaye suna zuba, yace "Amma me yasa Hajiya zata boye min wannan maganar. " Nace na gamsu da dalilin Hajiya, tacev in ta rasa muku baza ku rayu cikin farin ciki ba, zaku rayu a cikin damuwa da fargaba da lissafi. Ya sauke ajiyar zuciya ya ce "Allah sarki Hajiyata, shike nan mun rabu, Allah ka sakata a dausayin rahama. Baby ina ganin fa na gama farinciki a Duniya,. " Ya sake fashewa da kuka. To a haka likita ya same mu. Shamaki yace zamu tafi tunda shi ba wai maganin damuwarshi zai samu a wannan Asibitin ba. Likita ya kada ya raya, aka Shamaki ya kwana a kara duba shi, amma Shamaki ya ki. Gashi ba mota da zamu tafi, ba wanda ya zo da waya cikinmu. Sai likitan ne ya kaimu gida . Haka aka ci gaba da zaman makoki, na tausayawa, Azima, ga tsohon ciki ga tashin hankalin rashin Hajiya. Aka yi addu'ar uku aka watse, kullum Shamaki a kabarin Hajiya ya ke yini kamar mahaukaci sai an Kamo shi an sako a mota. Abinci kuwa sai na matsawa Shamaki yake iya kurbar dan shayi ko 'yar fura. Yace shifa ba zai iya ci gaba da zama a wannan gidan ba matsawar dai ba Hajiya a cikin shi. Duk da na sa an dauke kujerar Hajiyar ankai dakinta. A daddafe aka yi bakwai ya sa aka yi feti a wani gidan sa dake Rafin Danana yace can zamu koma. Duk ya birkice kasuwa ma baya fita. Wai in ya dawo wa zai taya shi lissafi nace masa ni ce. Yace "To ya nake gani game da Azima in zata zauna da mu. Nace kar muyi gaban kanmu ka kira Maman Umar ta kira duk sauran yayinka mu zauna a kira Azima aji ra'ayinta. Yace shikenan tunda Hajiya tace komai inyi shawara dake mu tattauna ai duk yadda ki ka ce haka zanyi. Aka kira su muka zauna gaba dayanmu aka kirata. Jikinta ya yi sanyi tace tafi son mu zauna tare. Kowa ya ji dadin haka. Maman Iman tace Allah sarki Hajiya ta, yanzu shikenan haka gidan zai ci gaba da zama tarihin gidan ya shafe! " Shamaki yace "Za a samu ko a dangi a ba wasu aro su zauna matsawar ina gidan nan har in mutu zan rayu a cikin tashin hankali. Aka sa ranar tarewarmu sati biyu da rasuwar Hajiya. Jamila da Zuhra sunzo mana aranar tarewar. Shima dai gida babbane kowacce da gefenta shima da nasa, a nawa gefen na fidda dakin su Meema da Rahin mai kula da su. Su Tabawa da Juma dakinsu yana kusa da babban kicin. Haka muka dawo wata sabuwar rayuwa mara kan gado, abubuwa duk sun dagule mana sun canza. Munfi karfin wata biyu ko yatsana Shamaki bai kama ba da sunan auratayya zamu kwanta guri daya muna manne da juna kila kafin muyi bacci sai mun yi maganar Hajiya munsha kuka, ko yaushe maganar shi bata wuce ta Hajiya. Gashi kullum yana hanyar makabarta. Sai da fa Maman Umar ta amso mishi tofi a gurin malamai wandan da suke yi mana saukar kur'ani so biyu a sati. Sannan aka dan samu ya dangana. Azima ta wayi gari da ciwon nakuda, Shamaki ya kaimu Asibiti, ta sauka lafiya dama tun a hoto ya nuna mace za a haifa. Ita ma dai Zeena ce, amma aka sa mata Safna. Shamaki yace babu taron suna domin shi dai farin cikin shi ya tafi, yanzu kawai yana rayuwa ne kafin tashi mutuwar ta zo. Haka dai ina lallabashi har ya fara fita kasuwa a hankali ya fara warwarewa, wata safiyar lahadi an tashi da ruwan sama gari ya dauki sanyi ya kara kankame ni muna baccin safe, a kunne ya rada min cewa Baby ina jin kamar shi 'awata ta dawo. Nace to ko zamu gwada mu gani. Yace gaskiya dai. To ranar kwanan Hajiya dari ba uku da rasuwa wata uku da kwana bakwai sannan Shamaki ya iya saduwa. Tun daga ranar kuma sai komai ya soma canzawa. Ina matukar kokarin ganin naji da kowa a cikin dangin nan. Shawara komai Shamaki dani yake yi. Haka nan lissafin dayake ina dan sauraren da Hajiya ina dan fahimta kuma ina taimaka masa a yanzu. Yara kuwa duk yadda na tsara zan kula da yarana in Allah ya bani haka nake kula da su, Meema ina mu amalantar Azima daidai da yadda nake ganin nayi mata adalci ba nai mata kallon kishiya.haka nan bana bari Shamaki yana hantarar ta kamar da. Ina fada mishi itama amana ce a gurina. ''Yan uwanshi kuwa komai ina shawara da su wanda ya shafi su sani, abinda kuma ba hurumin su ba, ni da Shamaki zamu kashe shi mu rufe. Bana bukatar sai an fada min Shamaki ya daina neman mata, domin mutuwar Hajiya ta saka Shamaki a tashin hankali ya kuma hankalta, macen sunna ma sai da ya manta yadda zai kusance ta bare ta banza. Sai dai sannu a hankali sai naga ya shiga wani yanayi na damuwa, sannan yakan kebe yana waya in ya ganni sai ya maza ya kashe, wani lokacin sai inga ya zuba tagumi. Na tambaye shi in da wata damuwa ya fada min amma yace shi dai babu komai. Araina nece Dan Adam yana da mantuwa bari dai in sake caje wayar bawan Allah nan na gano ko ya koma ruwa ne. Sakna naga an rubuta a lambar da suka yi chat, nabi chat din na karanta. Sanka ta fara da yi masa ta a ziyyar Mahifiyarsa, sanna ta ce masa "Dama jira nayi ka dawo cikin hankalinka daga mayen mutuwar mahaifiyar ka. Zan turo maka wani Video ka daure ka kalla in yaso sai ka nemeni in kana da magana. Sai kuwa ga Video Na bude. Na girgiza sosai har na saki wayar Allah ya sa a kan gado nake zaune bata kai ƙasa ba. Jiki na bari yake na sake dauka ina kallon yadda Shamaki yake haihuwar Uwarsa ga fuskarshi da komai yana saduwa da yarinyar. Na aje masa wayar dama ya fita motsa jiki ne,na koma daki ina tunanin wane mataki ya kamata in dauka domin fidda shi a wannan damuwar. Tunda na duba shi rokonta ya ke yi tare da fada mata cewa ta fadi duk abinda take so zai bata ta goge wannan Video kar matarsa da a halinsa su gani. Ita kuma tace "Ai ba matar ka ba,Duniya ma sai ta gani,dan bayan naturawa matarka sai kuma in tura a Internet. Sannan tace ita shi take bukaƙa su ci gaba da soyayya. Shikuma ya fada mata cewa ya dai yin duk wani abu na sabo domin shi ba zai yi abinda za a tada Hajiya ace ta kalli abinda tabari a baya ba. To ta bashi kwana talatin kodai ya yarda su ci gaba da Soyayya ko kuma nan da kwana talatin ya tsinci Video su yana yawo. Dole ta tashi ta share masa wannan hawayen domin kuwa yanzu ita garkuwar shi.... ..... Gama wannan tunanin ke da wuya na tashi na kira Hassan yaron Kantin Shamaki da yake yanzu sun saba da ni, ina kira ina tambayar Shamaki ya ci abin ci kodai wani abu kamar dai yadda Hajiya kanyi, sannan Shamaki yana aiko su su kawo wani abun in ya siya kamar Zuma da dai sauran su. Nace masa ina son ganinsa. Ya kuwa zo cikin sa`a , Shamaki ya fita. Muka zauna a falo. Nace Hassan dan Allah so nake ka kaini guri 'yan sanda zan shigar da ƙara ne. "Karan wa za ki kai kuma?" Ya tambaya cike da mamaki. Nace wata mata ce zata takura min. Yace "Anty matsayin ki a kasar nan ai kin girgimi ki je karamin ofishin 'yan sanda. Kina da kimar da zaki daga waya ki kira kwamishina ki fada masa bukatarki, yanzu dai ki fadawa maigida zai iya kiran kwamishina yana da wannan alfarmar." Nace aiko labarin bana son yaji, yanzu dai ya ka ke ganin za a yi so nake ma ka tafi kafin ya shigo. Yace "In kuma kina son ´yan sandan farin kaya ina da wani aboki Dss ne zan baki lambarshi sai ki kira shi ki fada masa kece matar Aliyu Baita, kudi kawai za su yi aiki. Nace to ba matsala. Muka yi sallama ya tafi. Domin yanzu bani da wata damuwa akan kudi saboda ya bude min account dina kuma ya bude na harkokin gida kamar dai lokacin Hajiya. Washe gari Hassan ya turo min Number. Sai da Shamaki ya fita sannan na kira Nace masa nice matar Aliyu Ali Baita. Yace . " Ranki ya dade Hassan ya fada min zaki kira ni." Nace Yawwa wata ce take yi wa maigidana barazana zata saki wani Video na batanci a gurin sa, to ina son batare da ita da shi sun sani ba, ina dakatar da abin, Hassan yace in maka magana. Yace "Ranki ya dade maigida da kanshi kuma yabarta araye? Nace yanzu ma ba zata zan yi mishi domin shi yana nan yana lallashinta a karbi kudi to gara ku kuci kudi. Yace Angama Haiiya zan je in hadaki da oganmu yanzu." Ya hadamu da shi nayi masa karin bayanin komai, nace masa abin da ya faru tun can baya ne yanzu baya tare da ita. Ita Kuma ga bukatar ta yanzu wai sai sun koma soyayya shi kuma yace ya ma daina gaba daya. Ogan yace "Ki turo min da Number dinta da kuma hoton ta. Take na tura masa duka saboda na ga hoton ta akan dp din ta na whatsapp na kira shi yace ya gani in jira zai neme ni. Shamaki ya shigo dakina ya same ni muna Homework yace "Wai ina malamar Lesson din yaran nan ne ki ke ta fama da lesson?" Na ce ta bada uzri wai yau zata je wata gaisuwa shine nace ba matsala zan kula da su yau. Yace "Ya yi kyau. in an gama da su ki sameni a dakina." Na barsu na nufi gurin shi dama akwai hanyar da ta hada ni da shi haka ma Azima ta cikin Falonmu. Na same shi yana kokarin kunna talbijin. Ya wai wayo yace " Au wai dama kina baye da ni ne? " Na ce to me zan jira in ban amsa kiran sanyin zuciyata ba. Ya yi Murmushi ya zauna, "Zonan" ya fada yana kallo na. Naje na zau a kan cinyarsa domin nasan nufinsa ke nan. Ya sulmiyo da ni ya dora hancinsa a kan nawa. "Mota zamuje ki zaba yanzu." Da sauri na zuba kwayar idanuna cikin nasa. Mota fa! Yace " To menene a cikin mota Allah na tuba. Na rungumeshi na sunbaci kirjin shi, zaka kai ni in zaba, to kuma wa zai koya min? Yace "Samu ya fi iyawa Baby zan koya miki kafin sati kin kware. Sai muna fita dasafe a ranar asabar da lahadi. Na sake kankame shi cikin kauna. Naje na sako Jallabiya da mayafinta nace wa su Meema Dady zai sai min mota yanzu zamuje.Suka kwashi murna nace da Juma bari mu dawo. pShi na baiwa zabi ya darzarmin mai kyau fara kal kirar Yaris sabuwar zubi. Muka dawo gida yara sai murna duk yawan motocin gidan amma sai fadi suke Mommy zaki kaimu makaranta gobe? Nace Sai na koya. Muna zaune da Shamaki kira ya shigo waya ta. Na tashi da sauri na fita zuwa tsakar gida. Yace Ranki ya dade zaku iya zuwa yanzu mun kama wannan matar. Nace Inane Office din? Ya yi min kwatance' nace zamu zo yanzu. Na koma na shiga na same shi, ya bini da kallo ya ga na yi abinda ban saba ba nafita waje na daga waya. Nace taso muje. Yace "Yace ina kuma da wannan daren?" Nace Yanzu zamu dawo. Ya taso yana fadin Baby bazan yi miki musu bane amma bana son fita yanzu. Na kama hannunshi yi hakuri. Kai zaka jamu bazamu fita da direba ba. Saida muka hau titi nace Office din Dss zamuje. "Mu yi me?" Ya da sauri, nace taimako? Yayi shiru har muka isa,. Shugaban yana ta kallona yana mamaki wai dashi muka yi waya,ya sa rai zaiga wata babbar mace. Nace ni ce Shamaki tunda suka gaisa sai naga ya kame guri daya,da alama bai son wannan tattaunawar da muke yi da dansandan farin kayan ko ince kishi ne ya sa shi daure fuska. Dansandan yace Hajiya kinsan a ina aka kama matar nan? Nace a a Yace a Kaduna tunda muka sa layinta a trak muka gano tana Abuja yaranmu sun kama hanya sai kuma muka ganta a Kaduna. A Hotel aka kamata sun sha ita da saurayin ta sun bugu. wayar muka fara karba yanzu kuma sai abinda megida yace za a yi, ya dubi Shamaki yace Ranka ya dade. Shamaki wanda ya kasa gane me muke nufi ya ce "Kunsani a duhu." Dansanda ya daga waya yace ku kawo wannan "yar iskar. Shamaki ya mike tsaye da sauri yana kallon ta. Ya nuna ta da yatsa yace Sakna. Wata zuciya ta zo wa Shamaki wuya ya daga hannu ya falla mata mari sannan ya kalle ni ida nunsa suka kawo hawaye. Na girgiza kai, nace wannan ba wata damuwa. Na kalli Dansandan nace ina wayarta? Ya miko min wayar tare da fadin ta cire cord din wayar. Na ba Shamaki nace ka yi yadda ka ke so. Yace a bata ta l goge Video da hannun ta. Nan take ta goge Sannan Shamaki yace ku bata layinta ne kawai shima in kunga dama amma ku rike wayar domin ni ne na saye ta. Sannan kar ta bar nan sai ta tabbatar muku cewa tafita harka ta. Ogan Cikin son tsorata ta yace ai kasar nan zata bari ba ta ce ita ba 'yar Najeriya bace wai 'yar Nijar ce. Na karya ta ke yi domin 'yan Nijar sun san karamci da mutunci ta dai fadi daga inda ta fito. Yace koma dai daga ina take ko dai ta koma can, ko kuma mu kashe banza mu ba karnukanmu namanta su cinye. Shamaki yace na gode sannan ka tura lambar asusunka zan baka sako kai da yaranka. Dansanda ya yi godiya sannan yace ka kara rike madam sosai domin a sanin da nayi wa halin mata a wannan lokacin da wahala matar ka ta ga wannan abin ta yi shiru sai ta yada ka a gurin kawayenta da 'yan gidan su, sannan ta ce ka sake ta. Shamaki yace Na gode zan kula sosai. Ya rako mu har mota. Mun fara tafiya ba wanda yace kala, sai ya tsaida mota a gefen titi ya Juyo ya kalle ni. Baby naji kunya yau nayi..... Nasa hannu na rufe masa baki,sannan nace tawuce wannan maganar fatana ka kara kiyayewa kuma idan ka ga wata mace wadda ranka ke sonta ka zo ka fada min zaka aureta akwai gurbin mata biyu a gidanka. Yace haba Baby Allah ya bani ke me zanyi da wasu matan kinsan Allah ko Azima darajar Hajiya ne amma wani lokacin ko kallon ta bana son yi." Na ce amma na jima da hanaka fadin haka taci gaba da cin albarkacin Hajiya Ka dinga sakar mata fuska. Yace jiya da kika sani gaba dole na kwanta da ita sai naga duk ta bani tausayi kinga yadda ta ke yin rawar jiki kuwa? Nace ka gani sai ka dauki alhakinta. Yace shikenan duk na bari zan yi yadda ki kace. Na kama hancin shi nace to mijin tace muje gida.... .... Sannu a hankali rayuwa ta canza girma ya hau kaina da kananan shekaru. Ina kokori sosai ganin cewa na kula da kowa yadda ya kamata. Bangaren su Maman Umar ina mu 'a mala da su kamar 'yan uwana na jini kuma sai dai munfi shiri da Maman Iman. Duk da cewa wani lokacin suna dan nuna min wai na mallake musu kani, sai dai na barshi a wasa suke sai dai inyi dariya ince dan Amana ne shi ko dana mallake shi bazan cutar da shiba. Ko zaman minti biyar ka yi da mu ni da Shamaki sai ka fahimci akwai kauna mai yawa kuma mai karfi tsakanin mu. Ance zomu zauna zo mu saba amma muna kiyaye wa domin ban tuna wani rikici da muka yi ba a tsakaninmu. Sannan ga fahimtar juna. Bayan hannu na ya fada da tukin mota wata asabar nace yau zan kwashi yarana muje ziyarar dangi. Yace "Ina ne? Nace gidanmu mana. Yace "Karfe nawa za atafi a kuma dawo karfe nawa? " Nace haba Gaye kai dakana kasuwa ma. Yace ni bana son a kai magariba ne Baby wallahi in na dawo bakyanan wani irin kunci nake ji a zuciya ta. " Nace to insha Allahu ana yin la asar zamu dawo. Nace tun jiya nake jin marmarin tuwon Ummanmu. Yace "Allah ya bada sa'a in kuma ba tuwon suka yi ba fa?" Nace dama izni nake jira in kira Jamlla in ce amin tuwona sukuma yaran nan zan tafi musu da abinci kasan basa kaunar tuwo kuma bana son in saka Umma girki kashi biyu. Kafin ya yi magana Azima ta yi sallama ta shigo da yake muna zaune a falonsa ne. Ta zauna sannan ta gaishe damu. Muka amsa tayi shiru alamun zatayi magana da shi. Zan tashi ya kamo kunnena yace ina zakije?" Nace zamuje mu yi shiri ne. Yace "Ban sallame ki ba,ki jira." Na kalli Azima wadda ba hakan ta so ba. Nace Ina Safna yau ba a kawo taba. " Tace tana bacci. Nace ta zo ta rakamu cikin gari. Na fada da tsokana. Azima tace "Cikin gari zaku ke nan yau?" Na ce I. Tace "A gaishe su. Ta kalli Shamaki tace "Yaya Dama zantuna maka maganar wayar ne ina son ina kiran su Maman mu muna gaisawa don Allah." Yace in siyo waya ki ci gaba da Tiktok kenan. nace miki sai dai mai botira kin ce ke bakya son mai botura ba sai ki sha zamanki ba. Na zuba mishi ido ina kallon shi, Ya ki kallona domin ya san na fada mishi ya sai mata wayar tunda ya zo ya fada min yadda suka yi. Ta ta mike zata tafi. Nace Azima wace iri ki ke so? Ta ce Ipone ita na saba rikewa. Ya yi karaf yace "Wallai baza a sai Ipone ba." Na ce ka yi hakuri ka sai mata duk wadda ka ga dama amma banda mai botura. Ya rike min hanci dakarfi tare da fadin "Ya zanyi tunda kin ce ayi. Na saki yar kara nace Azima knga Yayanki zai ciran hanci ko? Tace "Ummm sai anjima sai kun dawo ku gaishe su." Nace za su ji. Tana fita nace yanzu kai dama baka sai mata wayar ba. Yace to Allah ya baki hakuri yau zan siyo. Yanzu muje ciki dan Allah ki dan yi min tausa ko da minti goma ne. Nace Amma dai iya tausa zanyi maka dai domin na san hali yanzu sai ka canza labarin. Yace banyi alkawarin iyatausa ba sai abinda hali yayi.Na kira wayar cikin gida na fadawa Rahin cewa ta shirya min yaran nan zamu fita. Na dube shi Nace to goyani muje in yi maka. Ya duka na haye bayansa ina dariya, yana fadin sai in goya irinki goma. Tare muka fito dashi wai shima muje ya gaida su Umma sannan mu aje shi a kasuwa nace dawo wa fab? Yace zan kira Malam Bala. Har mukaje layin mu ba wani gyara da ya yi min atuki. Muna fakin yace "Kin san Allah Baby zaman su Umma a lugun nan ya ishe ni,da zasu yarda sai a sai musu wani gidan koda awata unguwar ne." Nace za su yarda mana kuma kaga wannan gidan na nuna masa wani gida, a bakin titi. Nace masa maigidan ya rasu kwanaki an saka gidan a kasuwa za a saida saidai bansani ba ko an siyar domin Abba naji wani abokin shi ya taya ba a sallama ba,nazo gida lokacin naji suna maganar. Yace ai bashi da girma. Nace kuma ba laifi dan ya yi biyun na su Umman. Yacc "Inda wannan za su sai da (ya nuna na kusa da gidan.)ai da sai a hada ayi musu harda karamin masallaci Allah ya kai ladan a Hajiyarmu. Nace wallahi kuwa, amma bari zan tambaya. Muka shiga layin muna dan gaisawa da wadanda muka sani har muka shiga gida. Jamila ta shimfida tabarma yazauna sukagaisa da Umma ya tambayi Abba tace ya fita. Su Jafar suka gaida shi. Ya mike yace to shi kam zai wuce kasuwa kar in manta duk yadda akayi sai in fada masa. Nace ka manta ne ni zan kai ka yace to ko dai in amshi makullin . Nace ba girman ka bane. Ni zan kaika, Kuma ina son in zaga in nuna wa "yan uwa motata. Nace da Jamila ga sunan ki kai su gidan kitso kafin in kai Dadyn su kasuwa. Tace "To". Muka fita muka hau mota. Muna tafe muna hira. Nace sai na bishi naga office din sa. Yace "Bana son a kalle min ke. Nace ai ba a sanni ba. Muka taka zuwa gurin Kantin na su yana ta gaisawa da mutane har muka shiga ciki. Nayi murmushi na tuna lokacin da muka zo siyayya da bikinmu. Su Hassan da Dahiru suka taso suka gaishe mu,sannan muka nufi sama inda office dinsa ya ke. Ofishin kato ga kujeru ga bandaki, ga Dininig ga talbijin ga Firji. Nace in tambaye ka wani abu baza kaji haushi ba? Yace "Tambayi." Nace ka taba amfani da wata mace a nan? Yace Haba Baby ai duk abinda mutum zai yi a rayuwa ya tsare kimar shi a gurin sana'ar shi da kuma unguwar da yake, saboda su za su fara bada shedar sa in ya mutu. Ko na Azima wata kaddara ce ko ishara Allah ya nuna mana. Ya zuro hannayen shi a kuguna yace kuma fadin haka da kika yi har kinsa naji ina shi a war yi a nan din." Na ce haba dai Yalabai da zu fa a gida daga tausa ka zarce a ringa daga kafa mana yau ma dai girkin Azima ne.Yace ai sai dare, kuma kinsan irin wannan abin da kwakwalwa ta amsa abinda tunani ya bata sai ya taso ba maganar anyi dazu bane. Mu maza muna samun karin lafiya. Haka dai yaje ya rufe kofa Hassan ya kira yawar Ofishin wai yana da baki, yace su jira akwai wata bakuwar a ciki. Abin mamaki Shamaki ya kusance ni a ofishinsa cikin wani irin doki kamar ranar ya fara gani na. Sai da muka nutsu nashiga na yi wanka tsaf harda ruwan zafi a bandakin. Nace abin mamaki yanda naga kayi kamar ba dazu a gida sai da ka samu natsuwa muka fito ba.Yace "Yace Baby akwai abinda mata basa ganewa. Wato kinsan ita shi'awa da ki ka ganta wata abace da bata da madakata, sannan ba komai ke motsa ta ba, haka karamin abu kan iya motsata.Mu maza muna son abubuwa irin wani abu da ba a saba yi ba. Misali kamar wannan, in ba dama irin haka ta samu ba ai bazaka dakko matar ka daga gida ka yi auratayya da ita a Office ba. Watarana a mota wata rana kaje da matar ka Hotel kamar yadda na taba yi kina ta yi min shirme." Mukasa dariya. Nace Na gane yanzu kawai duk inda ka ke so a shirye na ke. Yace na gode da wannan damar da ki ka bani, domin ina son ire iren haka. Wannan shine yake sa mazan da dama neman mata, saboda suna son irin wannan kalolin amma mata basa ganewa wata sai tace mijinta dan iskane, ko tace yara ita ta girma. Nace Allah ya kare mana ku da daga sharrin matan waje da duk musulmi yace "Amine." Nace muje karaka ni ance kana da baki. Muka fito yana fada min cewa "Da yawa matan da muke nema awaje ba su kai matanmu na gida komai ba, wata sai ka gama bukatar ka kana kallonta sai kaji duk ranka ya baci." Nace ga zunubi kuna yawo da shi. Daidai lokacin mun sakko kasa bakin da ke jiran shi har kashi biyu, nace masa kawai ka koma bari in tafi. Yace "A a, ya dube su suka gaisa, yace barin raka Madam Ya kalli Hassan yace wanda suka fara zuwa ka kai su sama. Su Hassan suka ce Anty sai anjima. Nace to sai anjima. Muka fito yace kina cewa in barki ta yaya zan barki a kasuwar nan ba sai wani ya nemi ya miki magana ba, a haka ma ina jin kar wani ya kalle ki. Haka na isa gida cikin kwanciyar hankali sai gajiya. suna gidan kitso na shantake muna ta hira da Umma nake yi mata zancan gida. Atake ta kira Abba yace ginda yana kasuwa har yanzu sannan kuma na can bayansa shima yana kasuwa mai na gefe ba zai saida ba. Nace to in na koma gida Tac za muyi maganar da shi. Nima nayo kitso da lalle . Umma ta soya wa su Meema gyada mai gishiri sun ce suna so a saya musu su ci, shine ta auno kwano tace sa kwana biyu suna ci. Tunmuna hanya naji zuciyata natashi nayi mugunci. Muna isa gida kuwa sai amai kamar zan amayar da hanjin cikina. Kafin washe gari duk na yi zuru zuru. Mukaje Asuibiti da safe bayan gwaje-gwaje aka gano ina da shigar cikin sati daya. Murna a gurin Shamaki nace kamar ba ga yaran nan muna da su ba. Yace Baby Haihuwa ita ce ribar Soyayya sai dai in ba a samu ba,sai a hakura. Washe gari ya tashi da azumi a she wai bakance ya yi zai yi azumi bakwai in Allah ya ba ni ciki. Haka muka taru ina jinya yana Azumi, amai kuwa arana sai inyi sau goma. Ban samu dan sauki ba sai da na yi wata biyu. Ummara da zamutafi har da yara duka Azima ce dai yaki yace ai yaje da ita. Na kada na raya amma yaki. Sannan a wadan da ya biya mawa har da kawaye Hajiya kamar Hajiya Zaliha da kuma wata Hajiya Zainab wadan da ni na bashi shawara. Nace yana da kyau ka girmama 'Yan uwan da kawaye na mahaifiyarka. Bayan mundawo lafiya na ga kula da riritawa ni da yarana. cikina har ya soma girma lokacin tuni Shamaki ya saye wannan gidan ya hada da na bayan shi aka bige wa su Umma a nan ana ginawa. Duk da ina da ciki Shamaki bai daina makale min ba, Wai har nafi lokacin da bani da ciki komai a gurin sa. To duk da ina da ciki ban zauna ragwaf ba. Kitso kunshi, gyaran jiki bana wasa tun da na gane shi din dan kwalliya son gayu ne. Abinda na rage sha shine kayan mata, sai irin su zuma kayan marmari da romon farfesu sai madarar shanu. Cikin haka haihuwa ta riske ni cikin dare, ranar ba a gurina yake ba. Da yake Umma tace min ana yin juyin wata kuma kuma dama Edd dina bai kai ba, dan haka na daure na cije. Aikuwa haka na kwana ina juyi ana kiran sallar farko kan jariri ya danno bashiri na danna lambar Shamaki na dai ji tana ringing ina nishi sai ganin shi na yi da gudu. Ya kamani nace kan jariri ya turo amma ina ganin zan mutune. Yace "A a zaki haihu lafiya bari a kira likitanmu. Ya kira likita ya fada masa cewa kan Baby ya fito. Likita yace a kwantar da ita, rigingine zai turo Nurse . Haka dai likitan ke fadin ga yadda za a yi cikin yardar Allah sai wani nishi ya taho wanda na sa araina cewa mutuwa ce rai na ne zai fita, ina yi ina salati sai wani yunkuri ya zo min na rike Shamaki gam sai fitar da mukaji gaba daya da mahaifa. Lokacin da Nurse ta iso Baby na cikin bargo likita ya gayawa Shamaki yadda zamu yanke cibiyar, du munyi faca faca cikin jini. Nurse tace "Ikon Allah yau naga wata haihuwa a kan gado. To me aka haifa? Muka kalli juna, nace ina ganin mace ce ta zo ta bude ta duba gaban yaron ta ce ai namiji ne. Dasau Shamaki ya ciro shi yana dubawa, yace da gaske ne amma sam bamu lura ba, domin a hoto mace ce. Shamaki ya yi hamdalar godiya ga Allah. Zuwa Safiya mun yi fes ni da dana. Muna zaune da Azima sai ga Maman Umar da murnar ta, Abban su ya zo. Kafin wani lokacin gida ya cika da dangi har su Ummanaphora. Tawaje na Juma dama ita ce ta wanke min dana nima ta yi min wanka ta gashe ni ras. Harda kuka wai ta so ace Hajiya ta ga wannan rana. Shamaki ya shigo anan dai aka yi wa dan huduba da Aliyu. Ko wa fadi ya ke dan sak Shamaki. Shima nace baza ayi taron suna ba. Shamaki ya ce sam ai wannan namiji ne ya san cewa Hajiya ma tana can tana tare da farin ciki. Azima tace "Anty na san saboda ni ki ke yi, wallahi ba komai ki bari a yi, tunda haihuwar Safna ai mutuwar Hajiya tana sabuwa. Haka dai na hakura dan dole na. Aka yi taron suna a Zeena Event Maganar ga yu ko samun wata gudunmawa kauyanci ne. Tunda Shamaki Gayyata ya yi wadda baiyi ba a bikinmu ba. Manyan mutane kuwa ba a magana harda Gwamna mai ci a wannan lokacin. Ranar na kara sanin waye Shamaki a kasar nan. Jariri har da mota ya samu ba a maganar chaki na kudi. Naci gaba da wankana cikin kwanciyar hankali sai lokacin na soma kiba namurnure na yi kyau. Ina mamaki idan na kalli madubi, na nemi kasusuwana na rasa na zama Hamshakiya matar manya. Shamaki ya taso ni a gaba saina amshi girki ni kuma Maman Iman ta zigani tace kar in koma sai na gyara jikina. dan haka na dukufa gyara ciki da wajen. Rannan dai ya gaji ya shigo yace "Baby wai saura kwana nawa ki yi arba'in din nan ne? " Nace sati daya jal ya rage. yace "To ranar za a daura min aure nagaji." Na zaro ido tare da fadin wasa ka ke. Yace "Da kamar bazan karba ba, Hajiya Zaliha ta bani yarta Na ima. Nace kana ba'a ne. Yace "Wallahi." Na mike tsaye da sauri. Kuma ka karba ka yarda?" Yace to ke me kika gani? Na taba baki nace ina ruwa na bayan sai da ku ka gama shawara sannan zaka ce me nagani. Na tashi na fice abina. Ranar na fara yin fushi maitsanai da Shamaki. Dama Azima ce ke da girki dan haka na asali.ban leka dakinsa ba duk da ina zuwa in taya shi wasu Lissafe lissafe. Shima naga ya share ni bai zo ba, nace mu zuba. Ina bacci na yi mafarkin Hajiya ko dan na kwanta da tunanin maganganunta. Wai tazo tana ce min ina rokon ki rike amanar da na baki ki cika all.kawarin da ki ka dauka. ...... Ki yi masa sassauci a hukunci. Da safe abin ya tsaya min a raina. Duk sanshi da Junior daga masallaci sai ya zo ya tashe shi amma yauv bai shigo ba. Bayan yara sun tafi makaranta na je dakin sa. Juma ta kai abin kari Azima tana zuba masa. Muka gaisa da Azima na gashe shi ya amsa amma ko kallo ban ishe shi ba. Na juya ina mamaki wane laifi na yi mai zafi haka. Washe gari na amshi girki bai dawo gidan ba har tara mutumin da a gida ya ke yin magariba. Dama ranar ban kira shi ba, shima dama ya daina kirana tunda ya fara fushi, muda sai mu yi waya so biyar a rana. Na dauki waya na kira shi ya daga bai yi magana ba. Nace Ina ka tsaya? Yace "Da sakon ki a hannu na ne? Nace E mana kai kanka ai amana ne a gurina maganar aure ce dan Allah ka daina min wadannan dabi'un ka yi aurenka shike nani? Yace "Ba shike nan ba hakkina da aka hani fa? Nace kai da za a daura maka aure me zaka yi da ni? Kawai dai ka dawo gida. Yace ina hanya daga zance nake. Duk daukana wasa ne sai gashi ya tabbatar domin a gaba na ta kira shi tana tambayar ya zo gida lafiya. Lallai fushi ba nawa bane. Na dake nace ka fadawa Azima domin ita zaka yi wa kishiya ba ni ba. Yace "In fada mata itace zata biya min sadaki? Nace Hakkinta ne ta sani, yanzu sauran kwana nawa daurin auren? Yace ba a tsaida ba ni dai ina so da wurine sabosa gaskiya a takure nake. Nace Ta kura kamar yaya baga baga Azima ba. Yaja tsaki tare da fadin bana gane mata gaskiya ke kinsani ke kadai ce me maganin matsalata, kin bani mamaki dan kin haihu kike gudu Baby bayan nasan kin warke, banda kullum sai na roki Allah ya yafe miki da yanzu ki na cikin tsinuwar mala'iku." Nace na gode da ka yafe min. Yace yauma hakura zanyi kenan? Nace kasan Allah tsoro nake kar in kuma samun ciki domin har al 'adata ta dawo. Yace ki samu mana ke zaki sai min ragon suna? Nace jikina wahalar da zan sha ga baby. Yaga dai da alamun bazan yarda ba. sai naga ya tashi ya shiga ciki. Jim kadan ya fito sanye da kananan kaya yaki kyau kamar wani matashin saurayi. Ya dauki wayoyi da makullin mota yace " Mu kwana lafiya. Nace bangane ba, har zai yi magana sai kuma ya fasa ya fita. Na tashi da sauri na bishi ya nufi mota. Na dawo na goya Junior na dauki makullin mota ta na dauki wayata da mayafi na fito har ya harba motarsa a gate na nufi tawa na dauka nima na bi bayanshi. Na kalli agogon shadaya na dare. Ina ta binsa na dan bada tazara kar ya ganni har muka isa wani Katafaren gini wanda na tabbata Hotel kafin in karasa ya shige, nima ina zuwa na amshi number na shige. Naje mota ta kusa da tashi. Ina zuwa Reaseption nace akwai wanda na zo gunsa Aliyu yanzu a shigo. Sai naga sun kalli juna. Suka ce ya sunana na fada musu suka rubuta suka ce bari a kira shi a waya. Jim kadan wani ya ce bari ya rakani. Muna kwankwasa kofar ya bude sai ya zaro ido alamun mamaki, yace me ki ka zo yi? Na zata Ashanti ce wadda mukayi waya zata zo ta same ni wai ya ki ke son in ne Baby kin tauye min halas na taho neman haram shime kun biyo n. Nace wacece Ashanti? Yace ki shigo mana. Me ya sa kika fito da wannan daren? Kin zo kin bata min shirina." Hawayen da bansan ko na menene ba suka soma zubowa. Na kwance ya ro na shinfide shi a kan kujera na soma cire kayan jikina ina jifa da su, na cire tas na nufi gadon na kwanta. Yazo ya zauna duk ya gigice. Gaskiya na dauki alhakin Shamaki domin har kuka ya min akan kar in kara yi masa irin wannan horon. Amma fa nima na gayawa yan garinmu. Yarona kuma sai Allah ya dora masa bacci. sai da Asbashi bacci ya dauke ni. Bai tashe ni ba, cikin bacci na ji ana shamin Mama ashe wai Junior ne ya tashi shine ya zo yana bashi nono. Na tashi da sauri nace banyi wanka ba ba a ba yaro nono jiki da najasa. Yace ban sani ba. Nashiga wanka na fito nayi salla sannan na dauke shi. yace "Baby inje in dakko mana kaya mu dan kwana biyu a nan? Nace kasuwar fa? Yace Hutu zan bata. Nace yarana fa? Yace me zai cinye su? Ga Rahin ga su Juma. Nace to Azima kuma fa ai zamu shiga girkinta. Yace "Kai! Wannan Azima tana takura min fa, Allah ni na kalle shi. sai ya ce "Tom shike nan mu kara kwana daya shike nan? Bani da mafita dole na ce to amma in kaje gidan ka hadani da Juma zanyi mata magana. Yace "Ba damuwa duk yadda ki ka ce haka za ayi." Nace ka fada min kuma wace ce Ashanti? Yace ga ki nan ai nasan zaki biyo ni dama ba wata Ashanti kawai wayo na yi miki." Na yi Murmushi har na ji dadi. Da mota ta ya tafi. Nace kai namiji ma dai sai abarshi. Yana shiga Juma ta tare shi Uban daki na lafiya Ina 'yarnan ta shige ne na juye ruwan zafi bata ba dalilinta dan ma baya nan. Yace gata a waya za ku yi magana. Muka gaisa tace ga ruwan zafi an juye. Nace nayi wata yar tafiya sai gobe zan dawo, ayi komai yadda ya kamata sannan a kula min da yaran nan a lallashe su musamman Anisa yar Mommy na san sai ta yi rigima. Abinda babu a tambayi Azima zan kira ta a waya. Tace to ba komai amma dai lafiya ko? Nace lafiya lau tace to acan za kiyi wankan kinsan haihuwar fari sai an kula.Ya amshi wayar yana fadin Juma wane kuma wanka ai ta gama wanka. Juma ta bishi da kallo baki bude tana fadin ikon Allah Uban daki Haihuwar farice fa lokacin mu arba'in biyu ake yi. Ya shige dakina yana fadin dama Juma ta zigaki ko? Ina dariya nace ba ruwan Baba Juma. Na fada masa duk abinda nake bukata ya dakko min shima ya dakko nashi ya shiga gurin Azima ya fada mata zai yi tafiya. Sanan ya sa Bala direba ya kai shi sai ya bar motata a gida. Haka muka yi gayu cikin kaya masu kyau da yaronmu muka sauka gurin cin abinci na Hotel din muka ci sannan yace mufita. Ni ke tuki shi kuma yana rike da yaro muka yita yawo guraren shakatawa sannanmu kaje gurin cin abincin mutanen kasar Labanon. Sannan mukayi siyayya muka dawo Hotel Muka yi salla muka sha Soyayya muka sake fita. Shamaki yana ta kokarin nuna min irin son daya ke min kuma yana lallashi na da in yarda mu fita kasahen ketare acan ne akwai guraren shakatawa. Nace Zamu fita ka bari sai na yaye wannan yaron don mu barshi a gida. Yace dashi zamuje ke dai ki yarda kawai. Nace mu tafi har Azima da kuma yaranmu. Yace an fasa. Haka dai rayuwa ta ci gaba. Hajiya Zaliha tana ta turo masa yarta. Na gaji nace muje a ne mi auren nan dai ko na huta ni suke ta zagi wai na hana.Yace Baby ke kin sani ke kadai nake so dubi Azima hakuri ta ke yi dadi, dan Allah kada ki kawo maganar wata, nacc barta ta shigo. Rana daya na kwashi yara da shi muka je gidan Hajiya Zalihar. Ta shiga zare ido muka gaisa nace zance muka rako Dady taje yana jiran ta awaje.Mamaki ya kama Hajiya Zaliha da kunya. Na'ima ta fita gunsa muka ta shi muka yi mata sllama muka fita. A mota suke nace ku fito ku bamu guri ko? Suka fito na dura ya'yana muka shige amma kishi hankalina yana gurin su. Na fito nace hirar ta isa haka zo muje na kalle ta nace sai anjima, Shima yace mata sai anjima na tura shi mazaunin direba nace kai zaka tuka yanzu. Ta saki baki tana kallonmu Ni dai tun daga wannan zanca ban sake jin maganar ba. Na san dai na sha tsinuwa. Su Umma suka tare a gidansu ya keru, na canzawa su Jamila makaranta. Gashi su Umma suna cikin jerin masu zuwa aikin Hajji bana har sun yi passport komai abin shi a wa. Sai da nayi addu a sannan na dauki tsinken gwajin na shiga bandaki bayan nayi fitsari ciki roba sai na tsoma. Take ya gwada min cewa ina da ciki. Na fashe da kuka sai na fita da gudu zuwa dakin Shamaki. Ya baje yana kallo kwallo, naje fa masa tsiken ina fadin shike nan ka yi min ciki ga jaririn yaro ka huta. Ya tashi da sauri ya rungume ni wai da gaske?Allah na gode maka sai muje gurin likita ya bamu shawara yadda zamu kula da Junior da kuma cikinmu. Na gama mana komai ranar talata jirginmu zai tashi zamuje Istanbul daga can kasashe goma zamuje. Na bude baki zan yi magana ya sa yatsa ya rufe min tare da fadin mun gama magana da Azima ta yarda. Yara zasu koma gidan Maman Umar har mudawo. Alhamdulillah! *ALHMDLLH, ALHMDLLH Allah Nagode maka daka bani ikon kammala littafin nan lafiya, Allah ka yafe min kurakuran dake ciki, Allah ka bamu ikon amfani da darussan dake ciki.* *Masoya makaranta littafin HAMSHAKIYAR UWA Nagode da haƙurin bibiyar labarin da kuka yi, waɗanda na ɓatawa a cikin ku ina roƙon su yafe min,ɗan Adam ajizine amma banida nufin ɓatawa kowa* *Game da jinkirin posting da aka rinƙa samu kuyi min uzuri saboda wannan shine littafi na na farko a online, amma insha Allah next littafi idan zan ƙara yi bazan fara posting ba sai na gama rubuta shi. Nagode Nagode🤝😍🥰* .